Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
basu labarin duk abinda ya faru dashi asaman wannan tsaunin Harda ceton rayuwarsa da aljani ramzas yayi Awannan lokaci anyi shagali sosai. Na murnar dawowar yarima saiman Saboda haka sai jarumi zamnal ya zo gaban saiman yace ya shugabana yaushe kake ganin zamuci gaba da tafiya zuwa birnin aljanu na hamshak .? Dajin haka sai yarima saiman yace Ai sai gobe zamuci gaba da tafiya Saboda yanzu akwai gajiyar gudu wacce mutanenmu suka sha Dajin haka sai jarumi zamnal yace to ya shugabana inba zaka damuba inaso ka bamu izinin fita gasar farauta ta karshe Kamar yadda muka saba gudanarwa a can birnin mu aduk shekara arana irin wannan domin nasan idan muka Isa kogon tsafin boka awaisul masawi Ba Zamu sake fitowaba sai bayan shekaru masu yawa Dajin wannan batu sai nantake yarima saiman ya tuno da mahaifinsa sarki abu saiman Kuma tabbas yasan cewa ayanzu haka 'yan lokuta kadan ne suka rage masa arayuwarsa Kuma gashi bashi da ikon zuwa ceton rayuwarsa Don haka saiya kasa yin magana kuma nantake idanunsa suka kada sukayi jawur kamar zai fashe da kuka Koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta matso gabansa ta tsugunna tace Saboda me bazaka amsa masa bukatarsa ba kwaya daya tak awajenka Kada ka zama mai manta alheri mana Badan Shiba ko don soyayyar da kakeyi mini ya kamata ka amsa masa bukatarsa Kuma Awannan gasa da za'ayi nice nakeson na zama alkalin wannan gasa Tana gama fadin haka saita Mike tsaye Yayinda shi kuma ya bita da kallo Tareda cewa shin kinsan hatsarin dake cikin wannan gasa kuwa da har kikeso kisa kanki acikinta.? To indai haka ne to nima zan shiga cikin wannan gasar ayi dani Dajin haka saitace ai idan har ka shiga cikin wannan gasar to zaka zama maison zuciya domin kuwa tabbas kaine zaka lashe wannan gasa Don haka dolene kabarni na yi alkalancin wannan gasa Kuma Ina mai tabbatar maka da cewa babu abinda zai sameni kamar yadda ka tabbatar mini da cewa Sirrin karfinka yana jikina to haka nima Sirrin karfina ajikinka yake Don haka kuwa babu abinda zai same ni na tabbatar maka da hakan Kafin yarima saiman yake wani wani abu tuni gimbiya suhaila ta taka da kafafunta taje wajenda dakaru suke tareda jarumi zamnal Da zuwa sai ta dubesu gaba daya tace Yaku ababan alfaharin birnin ramlatul Saif shin Acikinku mutum nawa ne suke da ra'ayin binmu zuwa gasar farauta..? Kafin ta gama rufe bakinta tuni wasu zaratan dakaru guda goma sha biyu Matasa majiya karfi sun fito Gimbiya suhaila ta kare musu kallo gaba daya sannan ta fara yi musu bayani akan wannan gasa kamar haka Tsarin wannan gasa shine zamu bazama acikin daji neman dabbar da tafi kowacce dabba girma acikinsa A yaketa gaba da gaba ba tareda an harbeta da kibiyaba ko an Dana mata tarko ba Za'a yaketa ne da karfin damtse duk Wanda ya sami nasarar wannan gasa to nayi masa alkawarin kujerar waziri acan birnin mu ramlatul Saif bayan mun dawo daga fadar boka awaisul masawi Idan kuma Kafin lokacin ajali ya riskeka To zamu baiwa danka wannan matsayi kuma zamu ajiye gawarka a inda bazata Lalace ba har mu koma birnin ramlatul Saif mu binne gawarka a inda ake binne sarakunan birnin mu Kodajin hakan sai dakarun suka fara tsallen murna ba shiri suka kama dawakansu suka hau Sannan gimbiya suhaila ta shige gaba suka bita Abaya yarima saiman kuwa ya bisu da kallo LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEM BAKAR GABA PART 17 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR lokacin da su jarumi zamnal suka shiga cikin daji domin gasar farauta sai suka dinga yin azababben gudu atsakaninsu har suka shiga cikin daji saboda tsananin jin dadin gasar da zasuyi saida suka yi nisa da barin sansaninsu sai suka karawa dawakansu karfin gudu domin suga wanda zai fara gajiya da wuri koda suka karawa dawakansu karfin gudun sai suka cika da mamaki bakomai bane ya basu mamaki ba face ganin cewa itama gimbiya suhaila ta iya jure karfin gudun da suke iya yi har tana sarrafa dokinta , duk yadda taga dama fiye da yadda suma suke iya sarrafa nasu dawakan domin kutsawa takeyi cikin sarkakiyar bishiyoyi, ciyayi, aka za, idan kuma tazo bakin rami sai kaga Tayiwa dokinta kaimi yayi tsalle ya tsallake ramin wani lokacin ma sai kaga har mikewa takeyi tsaye akan dokinta ta rike linzaminsa ba tareda ta fado kasa ba nanfa suka cika da tsananin mamakin irin wannan bajinta da takeyi domin duk cikinsu babu wanda zai iya sarrafa doki irin yadda takeyi nanfa suka fara tunani acikin zuciyarsu suna cewa shin gimbiya suhaila a ina ta koyi sarrafa doki irin wannan? anya kuwa yarima saiman ma kansa yasan ta iya sarrafa doki kamar haka? to idan kuwa hakane menene dalilin dayasa ta boye masa? tambayar da kowannensu ya dinga yiwa kansa kenan ba tareda sun san amsartaba haka dai suka yita yin gasar tseren gudu har suka bar dajin da suke cikinsa suka shiga wani daji wanda akewa lakabi da harjazul maksi dajin harjazul maksi dajine wanda ya yi kaurin suna wajen manyan dabbobin daji masu matukar hatsari domin agaba daya dajin baka samun kananan dabbobin daji irinsu barewa,gada, kunkuru dadai sauransu dabbobin da kawai suke rayuwa acikin wannan daji sune manyan dawa kamarsu zaki, damisa, kura, maciji, da kuma manyan tsuntsaye masu iya daukar mutum alokaci guda da dai sauran dabbobi masu hatsarin gaske suma kansu manyan dabbobin idan suka rasa abinci saidai kaga suna kama 'yan uwansu da karfin tsiya sun cinyesu wannan daliline yasa kananan dabbobi sukayi hijira daga wannan dajin suka gudu izuwa wasu dajijjikan don su tsira da rayuwarsu koda suka iso wannan daji sai dukkaninsu suka rage karfin gudun nasu tareda dora hannuwansu akan kuffinan takubbansu suna kallon kowacce kusurwa ta dajin domin suga dabbar da zasu farauta jarumi zamnal ya dubi gimbiya suhaila wacce ta basu tazara sosai jarumi zamnal ne yake biye mata baya yace ya shugabata zaifi kyau ki koma bayanmu kici gaba da alkalancinki mu ki kyale mu muyi wannan farauta koda jin haka sai gimbiya suhaila ta juyo tayi masa wani murmushi mai kama dana mugunta wanda ya kasa gane me nene manufar wannan murmushi nata nantake ta juyo ta koma baya su kuma suka shiga gaba tana biye dasu lokacin da suka isa tsakiyar dajin alokacin yamma tayi dokunansu sun gaji saboda tsananin kishirwa da yunwa har sun fara yin sassarfa kwatsam sai suka hango wasu manya manyan dabbobi suna fitowa daga cikin kowacce kusurwa ta dajin sunyi musu kawanya babu hanyar da zakabi ka wuce kowannensu yana dalalen harshe saboda tsananin yunwa koda suka yi arba da wadannan dabbobin daji sai dukkaninsu suka figice suka fara nadamar kawo kansu cikin wannan daji saboda sun tabbatar da cewa yau sun kawo kansu dajin HALLAKA shi kuwa jarumi zamnal hawayene ya zubo masa sakamakon tunawa da yayi cewa yanzu bashi da damar da zai iya ceton kansa balle ya ceci rayuwar gimbiya suhaila kwatsam sai suka jiyo wani irin gurnani mara dadin ji yana tahowa daga can nesa koda ragowar namun dajin suka jiyo gurnanin wannan zaki sai dukkaninsu suka tarwatse suka bar wannan wajen da alama suna matukar tsoronsa nanfa dakarun suka tattare jikinsu waje daya jikinsu yana kakkarwa saboda ganin mutuwa muraran koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta ce dasu haba ababan dogaron birnin ramlatul saif kada ku baiwa birnin mu kunya mana a idon duniya inaso kusa ajikinku cewa kune masu nasara akan wannan zaki ku cire tsoronsa daga zuciyarku zaku sami nasara akansa na tabbatar muku da haka koda jin haka sai dukkaninsu suka ji duk wani tsoro ya gudu daga zuciyarsu take suka zare makamansu aka fara kallon kallo atsakaninsu alokacin da zakin ya fara karta kafafunsa akan kasa yana kokarin afka musu suna cikin hakane kwatsam sai suka jiyo kukan wata rikakkiyar mikiya daga can samansu koda ganin haka sai suka ga gimbiya suhaila ta daga doguwar rigarta ta zaro wata sharbebiyar takobi mai matukar kaifi da tsini kawai saita kalli dakarun tace ku kuji da wannan zakin ni kuma zan tunkari wannan mikiyar koda jin haka sai zamnal yace ya shugabata karki aikata haka tunda ke baki iya yin yaki ba dajin haka sai tayi murmushi tace shin kasan lokacin dana fara koyar tseren doki? zamnal ya girgiza kansa alamar bai sani ba suhaila tace to kamar yadda na iya tseren doki to haka na iya yaki da takobi don haka saika zuba ido ka gani….. suna cikin yin wannan magana ne wannan katuwar mikiya ta sunkuyo da kanta kasa da nufin ta suri gimbiya suhaila nantake kuwa gimbiya suhaila tayi tsalle ta tsallake harin nata sannan ta sake yin wani tsallen ta haye kan mikiyar suka ruguntsume da masifaffen yaki da ita da wannan katuwar mikiyar take mikiyar ta tashi sama dauke da gimbiya suhaila ta luluka da ita cikin gajimare tana kokarin wulluta daga gadon bayanta ita kuwa gimbiya suhaila sai ta rukunkume jikin mikiyar tana kokarin danno kanta kasa nanfa suka fara kokawa ita dai mikiyar burin da take yi shine ta sami damar wullota kasa daga gadon bayanta yadda zata hallaka nan take wannan daliline yasa gimbiya suhaila taki yarda ta fado kasa koda ganin haka sai wannan mikiyar ta kwallara kara wacce tasa dajin gaba daya ya amsa amon karar tata faruwar hakan keda wuya sai ga dangin wannan mikiya suna bulbulowa daga sassan dajin kafin cikar dakiku sun kachame da yaki asararin samaniya mikiyoyin suka dinga yunkurin daukar ta da kafafunsu ita kuma tasa takobinta tana mai da musu da martani da ita wohoho sai gashi gimbiya suhaila tana ragargazar wadannan mikiyoyin tamkar ana sassabe agona duk inda ta ratsa sai dai kaga sassan jikinsu yana zubowa kasa daga sama kamar ganyaye suna zubowa kasa daga kan bishiya sai gashi ta zame musu kamar annobar mutuwa duk inda takai sara sai ta zubar da akalla guda goma jini kuwa ya dinga fallatsi daga sama tamkar ana ruwan jini wohoho saboda wannan gumurzu da sukeyi sai wannan murgujejen zakin ya tsaya ya fasa afkawa su jarumi zamnal shima ya zama dan kallo daga can kuma sai zakin ya afkawa su jarumi zamnal din suka kachame da sabon fada koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta kara zage damtse wajen yakar wadannan mikiyoyin kafin cikar dakika sittin ta kashe su gaba daya saura wanda take kansa shi dinma sai ta kama wuyansa ta danno shi kasa da karfin gaske koda suka dira akasa saita gabza masa naushi atsakiyar gadon bayansa take gadon bayan nasa ya karye ya fadi kasa matacce kuma awannan lokacin wannan zakin ya tarwatsa dakarun saura zamnal shi dinma dashi da dokinsa zakin ya turo su kusa da wani katon rami mai zurfi wanda duk wanda ya fada cikinsa sai ya hallaka koda ganin haka sai gimbiya suhaila ta falfala da azababben gudu ta tsinko wata murtukekiyar jijiyar bishiya ta wullawa jarumi zamnal ya cafe adaidai lokacin da kafafun dokin nasa suka zame ya fada cikin wannan ramin BAKAR GABA PART 18 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Lokacin da jarumi zamnal tareda dokinsa Cikin wannan ramin sai gimbiya suhaila ta rike wannan murtukekiyar igiyar da hannun ta na hagu dokin ya fada cikin ramin shi kadai Nanfa suka fara kallon kallo atsakanita Da wannan zakin kai da gani kasan kallo ne na shakkar juna Daga can sai Zakin ya daka tsalle ya taho kanta da nufin ya bangajeta da kirjinsa Nantake ta murgina kasa zakin bangaji iska yq fadi kasa shi kadai Kafin ya dago gimbiya suhaila tayi sauri ta daure Wannan murtukekiyar jijiyar bishiyar ajikin kugunta Sannan ta gyara tsayuwarta tana mai shirin tunkarar zakin Take zakin ya juyo zuwa gareta cikin gudun gaske da nufin ya cafi makoshinta Koda yazo inda take sai ta sa hannunta na dama ta gabzawa wannan zakin naushi Amma sai zakin ya shanye dukan nata suka ruguntsume da fada mai muni Wohoho hakika gimbiya suhaila ta kasance jarumar gaske Domin dukda kasancewarta mace Kuma akwai ciki ajikinta sannan akwai mutum adaure akugunta Sai gashi tana yakin da cikakken kuzari Tamkar babu wani kayan nauyi atattare da ita domin wannan cikin baya hanata tsalle tsalle da zulle zulle takeyi taki bari zakin ya sami nasarar taba jikinta duk lokacin da ta sami nasarar yankar jikinsa ko saransa da takobi sai dai taji kara ta tashi kamar haduwar karfe karfe amma shikuwa yakasa samin nasarar tabata saboda tsananin zafin namanta ana cikin wannan fafatawa ne kawai sai ta hangi wata bishiya akusa da inda take koda ganin wannan sai ta daka tsalle daga inda take ta haye kan wannan bishiyar kamar ta kasance biranya ba mutum ba nantake ta daure wannan jijiyar bishiyar da jarumi zamnal yake rike da ita yake kokarin fitowa daga cikin ramin su kuwa ragowar dakarun mikewa suka yi zaune daga inda suke dukda cewa zakin yaji musu mugayen raunika saboda tsananin mamakin irin jarumtakar da takeyi domin sun tabbatar da cewa tabbas itama ta kasance jarumar gaske wacce samun kamar ta acikin mata awannan nahiyar zaiyi wahala domin ko yarima saiman suna ganin kamar da kadan zai fita karfin damtse koda ta gama daure wannan jijiyar bishiyar sai ta sauko daga kanta sannan suka sake kachamewa da sabon fada awannan lokaci sai fadan nasu sai ya kara muni fiye da farko domin ragargazar junansu suka dingayi tun afarkon haduwarsu zakin ya yakusheta akafadarta ta dama take wajen ya dare jini yayi tsartuwa harsaida ta kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da taji cikin zafin nama itama ta suri zakin ta daga sama dukda irin girmansa da karfin damtensa ta gwara shi da jikin wata bishiya take bishiyar ta karye ta fadi kasa cikin sauri zakin ya sake tasowa kanta zumbur da nufin ya turmusheta ya kachalchala mata fuska koda ta lura da nufinsa sai itama ta daka tsalle sama ta tari zakin dukkansu suka mirgino kasa atare suka fara kwarmatsuwa da juna nantake zakin ya fara kokarin kama fuskarta da hakoransa da faratansa da nufin ya gatsa sai itakuma taki ta bashi damaryin hakan dukda cewa kaifi da tsini yaki yayi tasiri ajikin zakin saita dinga gabza masa wawan naushi afuska sannan tayi kukan kura ta daga wannan zakin sama tayi hajijya dashi sannan ta cillashi acikin wannan katon ramin wanda duk wanda ya fada cikinsa sai ya mutu komai hatsabibansa alokacin da suke wannan fafatawar da wannan zakin ashe bata saniba jarumi zamnal ya fito daga cikin wannan ramin koda yaga irin tsananin jarumtakar gimbiya suhaila saiya kame kyam ya fara tunani acikin zuciyarsa abinda ya fara tunani shine anya kuwa wannan gimbiya suhaila ce wacce na sani ba wani aljanin ne ya sace taba yazo yake shirin yaudararmu? yana cikin wannan tunanin ne ta karaso inda yake cike da murmushi tace kada kuyi mamakin abinda ya faru yanzu domin dole ce tasa na bayyana jarumtakata agareku na tabbatar idan har banyi haka ba da yawanmu sai mun hallaka awannan fafatawa maganar sakamakon nasarar wannan gasa kuwa duk cikinku babu wanda yayi nasara amma kuma na jinjina muku gaskiya domin na tabbatarda cewa kuma ba kananun jarumai bane saboda duk dabbobin da suke cikin wannan dajin ba irin dabbobin da suke nahiyarmu bane ma'ana dukkansu akwai bakaken aljanu ajikinsu wannan dalilin ne yasa suke da matukar kwarjini agurin duk wani bakon halitta daya shigo cikin wannan dajin shikuma wannan zakin aljanin da yake jikinsa yafi na ragowar karfi da kuma kwarjini wannan dalilin ne yasa yafi ragowar kwarjini har suma suke jin shakkar sa saboda haka yanzu zamu koma izuwa can sansaninmu Kuma abinda zancewa yarima shine gaba dayanmu babu wanda ya sami nasara acikin wannan gasa kodajin haka sai gaba daya dakarun suka dubi junansu gaba daya sannan wani daga cikinsu yace ya shugabata mu mun yarda bamu sami nasara ba awannan gasa amma kuma ai kece kika cinye ta don haka mun yarda kece kika cinye ta dajin haka sai tayi murmushi tace aini bana daga cikin dakarun gasa amma ni alkalancine aikina saboda haka saimu juya yanzu mu tafi tana gama fadin haka saita tsuke bakinta tayi fito take dawakansu wadanda suka tarwatse acikin daji suka dinga dawowa sannan taje ta kama dokinta haye ta kama hanyar komawa sansaninsu suma kuma suka biyota abaya suka zabureshi sukayita tafiya ba kakkautawa har suka iso sansaninsu da isowarsu suka ga jama'ar sansaninsu sun tsaya sunyi cirko cirko suna jiran karasowarsu don ganin wanene jarumin wannan gasar nantake suka taho suka taresu cikin murna kowanne daga cikin tawagar burinsa shine ace dan uwansa ne ya cinye wannan gasa itakuwa gimbiya suhaila kai tsaye ta wuce gaban yarima saiman tayi masa wani tattausan murmushi sannan tace naje wannan aiki daka sakani kamar yadda ka bukata naje nayi shi amma agaba daya dakarun mu babu wanda yayi nasara dajin haka sai yarima saiman ya juya da sauri ya shige cikin tantinsa sannan gimbiya suhaila tabishi abaya suna isa cikin tantin ya juyo ya kalleta kallo mai nuna alamun rashin yarda yace inada tambayoyi ne kawai gareki nakeso ki amsa mini su cikin gaskiya tun daga lokacin dana aureki shin na taba boye miki wani abin acikin raina? dajin wadannan tambayoyi sai zuciyar gimbiya suhaila ta buga da karfi har taji kwalla ta zubo mata sannan tasa hannu ta goge hawayen tace gaskiya ne tunda nake dakai baka taba kokarin boye mini wani abuba acikin zuciyar ka kuma baka taba neman wata alfarma ba gurina koda jin haka sai yace kiyi hakuri da tambayoyi na bawai ina zarginki bisa cewa zakici amanata bane ba ko kuma zaki yaudareni bane to menene dalilin dayasa kika boye mini jarumtakar ki tsawon lokaci mai tsawo baki taba nuna mini itaba? kuma menene dalilin dayasa kika yi yaki da wannan murgujejen zakin alhalin kina dauke da juna biyu ko kuwa bakya tsoron wani abu ya same kine? dajin wadannan tambayoyi sai gimbiya suhaila tayi shiru nadan tsawon lokaci sannan tace *** *** *** kamar yadda ka sani azahiri ka nemi aurena ne agurin attajiri manhas amatsayin mahaifina to ina bakin cikin sanar dakai cewa bashi bane mahaifina ba sai dai kuma shine ya rukeni amana tamkar shine ya haifeni sakamakon rashin samun haihuwa dashi da matarsa sun kula dani kamar sune suka haifeni tun daga kuruciyata har z uwa girmana basu taba yi mini wani abuba wanda zai cutar dani ba har zuwa sanda suka aurar dani agareka hakan ne ya haddasa soyayya mai tsanani ta shiga tsakanina dasu mahaifina na asali shine mafarauci mabwas mabwas yakasance adalin mutum ne mai tsananin jarumtaka ta ban al'ajabi wanda ya karar da rayuwarsa gaba daya acikin daji kuma namijin gaske wanda baisan tsoro ba mahaifiyata ma ta kasance mafarauciya kamar mahaifina ana kiranta da suna mubnaika itama jarumace ta gaske kuma kyakkyawar gaske ta gaban kwatance LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME BAKAR GABA PART 19 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Farkon haduwar mafarauci mabwas da mahaifiyata shine wata rana ma haifiyata mubnaika ta fita yawon farauta acikin wani daji dake can nahiyar bakaken fata domin ta sami labari abakin abokan sana'ar farautarta cewa akwai nau'o'in dabbobin daji acikinsa wadanda suka banbanta dana wannan nahiyar tamu don haka idan har ta sami nasarar samun dabbobi masu yawa idan ta koma can nahiyar su zata sami kudade masu yawa saboda haka kane ta sayar da rayuwarta ta shigo cikin wannan daji saboda ta yarda da kanta sosai lokacin data shigo cikin wannan dajin sai ta kama hanya tana tafiya cikin sanda yadda babu dabbar da zata ji motsin tafiyarta awannan lokaci tana sanye da kayan farauta wadanda suka nuna tsantsar kwarjininta wannan daji data shiga kuma cike yake da dogayen bishiyoyi masu manyan ganyaye wadanda suka sa dajin yayi duhu saboda ko hasken rana ba sosai yake haska cikin dajin ba ita kanta jaruma mubnaika tasan cewa ruwa baya tsami banza ma'ana dole ne asami munanan dabbobi acikin dajin kamar yadda dajin ma ya kasance mai ban tsoro koda tayi nisa acikin dajin sai ta fara hango wani katon kogon dutse agabanta tana ganin wannan katon kogon dutse saita kara sauri harta iso gaban dutsen sannan ta tsaya cak tana kallonsa da nazarinsa domin sanin menene acikinsa kawai saita sunkuya ta debi kasar bakin kogon ta shanshana ta da hancinta don tasan irin halittar da take cikinsa bisa mamaki sai taji bataji kamshin ko wacce halitta ba koda ganin haka sai taji bata yarda da abin da kasa ta nuna mata ba don haka sai ta nemi itace ta kunna wutar kyastu ta sannan ta shiga cikin kogon don ganewa idonta gaskiyar lamari tana fara shiga cikin kogon saita cika da mamaki domin kashushuwan mutane dana manyan dabbobin daji ta dinga gani acikinsa da alamu sun shafe shekaru da zama matattu tana taka kashushuwan jikinsu nan take yake karyewa koda ganin wannan al'amari sai ta cika da tsananin mamaki sai tace azuciyarta shin wacce irin hatsabibiyar dabbace acikin wannan kogo da har ta dade tana hallakar da mutane da dabbobi? gaskiya ko wacce irin dabbace wannan ta cika shu'umar gaske abar tsoro shin kuwa ya kamata in shiga cikin wannan kogon? ta tambayi zuciyarta sai wata zuciyar ta daka mata tsawa tace kada ki mayar da zuciyar ki raguwa mana keda kika fito domin. neman suna mai zai sa kiji tsoron abinda kika hadu dashi yanzu bayan kinsan shine abinda zaisa kiyi suna aduniya idan har kika kuskura kika ja da baya tabbas kin barwa kanki abin kunya kuma duk wahalar da kika sha abaya ta tashi abanza da ki mutu a acikin gida gwanda ki mutu afagen daga ko ba komai za'a dinga tunawa dake tana gama wannan tunanin sai taji shakkar komai ta gushe daga cikin zuciyarta don haka sai ta ci gaba da tafiya tana haska ko ina da wannan wutar itacen abinda ya dada bata mamaki da wannan kogon dutsen shine ganin tsananin girmansa kamar unguwa guda ahankali ta iso karshen dutsen tana zuwa karshensa sai taji an daka mata tsawa sannan wani irin ruri ya ratsa dodon kunnenta wanda ta kasa gane ko na menene sannan taji an sake kwallara kara wacce ta sa kogon ya amsa kuwwa tamkar kunnuwanta zasu dode kafin ajima sai taji wata gagarumar iska ta taso ta ta kowacce kusurwa ta kogon sannan sannu ahankali iskar ta dinga kadawa aguri guda sannan tace dunkule ta zama wata irin murtukekiyar macijiya wacce tsawonta yakai girman bishiyar dabino kaurinta kuwa yakai na rikakkiyar bishiyar kuka wani irin hucin turirin hayaki yana fita daga cikin kofofin gashin jikinta nan take ta tsaya ta karewa mubnaika kallo sosai sannan ta bushe da dariya tace barkanki da zuwa kogon hallaka kuma kushewa ga duk wani mai yawon neman suna aduniya yake wannan matashiyar budurwa ki sani cewa nice uwar hatsabiban aljanu na duniya kuma abar tsoro ga duk wani mahaluki da yayi arba dani ke bama mutane jinsinki ba hatta aljanu suna shakkar haduwa dani balle dabbobi tunda na wanzu acikin wannan kogon dutsen nake shayar da kaina jinin bil'adama da kuma aljan sannan ina da karfin sihirin d zan iya janyo ruhin duk wani mai burin neman suna a ko ina yake a duniya wannan daliline yasa kema kika kawo kanki nan da yawan mutane ire irenki sun kawo kansu izuwa wannan kogon amma babu wanda ya taba fita araye dajin haka sai jaruma mubnaika ta kyalkyale d dariya itama sai ta dakawa macijiyar tsawa tace karya kikeyi tsohuwar azzaluma ina rantsuwa da karfin tsafi karshenki yazo baki isa ki iya wuce wannan ranarba domin koda zan mutu sai dai muyi mutuwar kasko tare dake kafin ta gama fadar abinda take fada sai macijiyar ta bushe da dariya akaro na biyu sannan ta shammaci mubnaika ta kawo mata duka da jelarta cikin bakin zafin nama ta sunkuya jelar ta harbi iska itama sai tayi sauri ta zaro takobinta daga cikin kufe ta fadawa macijiyar suka kachame da azababben yaki mai tsananin firgitarwa da tayar da hankali kai inda ace akwai wani mutumin akusa dasu lokacin da suke wannan fafatawar idan bai kasance gawurtaceccen jarumiba zai iya haukacewa ko kuma idan bai iya zulliya da kauce kauceba cikin 'yan dakiku zai hallaka saboda tsananin tashin hankalin da sukeyi atsakaninsu domin duk sanda macijiyar ta kawowa mubnaika duka ko kuma harbi da bakinta da zarar ta kauce saidai kaga duk abinda ta samu nan take yake dagargajewa koda kuwa dutsene ya zama kamar nukakken gari idan kuwa ta kawowa mubnaika harbi da bakinta idan ta goce saidai kaga wani bakin dafi ya zubo kasa nan fa fadan nasu ya karayin tsanani duk sa'adda mubnaika ta sami nasarar sarar jikin macijiyar da kaifin takobinta saidai kaji wata kara ta tashi kamar karar haduwar karfe da karfe kogon dutsen saiya fara girgiza kamar zai ruguje saboda tsananin bala'in da fadan nasu yake haifarwa inbadon mubnaika tana da tsananin zafin nama ba da tuni ta hallaka farat daya a gurin macijiyar domin wannan macijiyar tana da tsananin karfin damtse nesa ba kusa ba ita kanta macijiyar tayi mamakin yadda suka dade suna fafatawar da mubnaika domin tunda take bata taba shafe dakiku sittin ba suna fafatawa da wata halittaba face ta hallaka ta amma sai gash yau ta hadu da bil'adama guda daya wacce suka shafe dakiku masu yawa suna fafatawa a wannan lokaci sai da jaruma mubnaika ta raina kanta taji tana nadamar shigowa cikin wannan kogon domin ta fuskanci cewa indai suka jima suna fafatawa ahaka nan da "yan dakiku kadan zata iya gajiya da zarar ta gajin kuwa shikenan wannan hatsabibiyar macijiya ta sami nasara akanta babu abinma da yake kara firgita ta face ganin cewa ko kadan karfin sihirinta yaki yayi takanta akanta domin ta jarraba yin hakan sau da dama amma babu alamar nasara don haka saita kara zage damtse wajen yaki da ita ana cikin wannan fafatawar ne maciyar ta shammaci mubnaika ta gabza mata wawan duka da jelarta saboda karfin dukan saida tayi sama taje ta gwaru d jikin wani dutse take gudan jini yayi fitar burgu daga hancinta da kuma bakinta saida taji kamar kashushuwan bayanta sun karye saboda karfin naushin tayi kokarin mikewa tsaye awannan lokaci amma sai taji ta kasa koda mikewa zaune saboda tsananin jigatar da tayi ita kuwa wannan maciyar da taga haka sai ta sake kyalkyalewa da dariya sannan tace dama na fada miki baki isa ki iya kwacewa ba daga hannuna don haka yanzu kinaji kina gani zanzo na tsotse jinin jikinki sannan kuma na hallaka ki gaba daya macijiyar na gama fadin haka saita taho zuwa kanta gadan gadan ta sunkuyu da katuwar fuskanta mai kama da ta mutane kasa nan take wasu kananan allurai suka fito daga cikin

Chapter 9 of 14