Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
turakar amatukar razana Sai kuyanga dayace ta iya jurewa ta tsaya jikinta na rawa ta dauki jaririn Ta yanke masa cibiyarsa sannan tayi masa wanka Koda wadannan kuyangi suka ruga wajen wannan daki sai suka je suka sami yarima saiman sukace Ya shugabanmu hakika wannan abu daya faru a wannan kogon ba komai ne ya jawoshi ba face haihuwar matarka gimbiya suhaila Yanzu haka ta haifi wani kyakykyawan jariri mai siffar sadaukai kuma yanzu haka yana cikin wannan daki…… Kafin su gama fadar abinda yake bakinsu tuni ya ruga da gudu zuwa cikin wannan daki Ya dauki jaririn ya daga shi sama ya kura masa ido take kwalla ta zubo daga cikin idanunsa Gimbiya suhaila wacce take kwance agefe daya koda taga wannan kwallar daga cikin idonsa sai hankalinta ya tashi sannan ta rugo gareshi tace Yakai abin kaunata menene yasaka zubar da hawaye sakamakon ganin wannan jaririn nawa? Kodajin wannan tambaya sai ya juyo mata da fuskar jaririn donta gani Nantake itama ta cika da mamaki sakamakon ganin yadda jaririn yake matukar kama da sarki abu saiman kamar an tsaga kara Yarima saiman yace to wannan shine dalilin ganin kwalla a cikin idona kuma wannan kwallar kwallace ta farinciki Tabbas yanzu mun sami yaron da zai dawo mana da martabar masarautar mu Kuma ya haye kankaragar kakansa koda kuwa mu bama raye domin wannan alkawarine abin bauta ya dauka agaremu 0======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Daga wannan rana suka ci gaba da rainon wannan jariri cikin kulawar daya kamata iyaye su dinga baiwa jariransu Kuma aka rada masa suna basdar Har ya cika shekara hudu a duniya kuma tun a wannan lokacin kyawunsa ya dinga bayyana afili har wasu suna ganin kamar shi ba mutum baneba kamarsu domin wasu cewa suka dinga yi waishi dane daga ubangijinsu Kuma awannan shekarun mahaifinsa ya fara koyar dashi yaki da bashi horo mai tsanani Har ya zamana idan ya shiga cikin wadanda suka girmeshi da shekaru bakwai ma basa samun nasara akansa Kuma kirar karfi ta dinga bayyana ajikinsa Musamman ma lokacin dayakai shekara goma a rayuwarsa sai mahaifinsa ya dinga bashi horo mai tsanani Wanda harsaida wasu daga cikin mutane suka dinga cewa Baya kaunar dansa domin abinda yakeyi masa wannan ya wuce soyayya Saboda sai a sakashi yayita naushin karfe mai kauri Har sai yan yatsunsa sun kakkarye sannan aje agyara masa Wani lokacin kuma sai yasa a hanashi abinci tun safe harsai yunwa taci karfinsa Sannan ace idan yana bukatar abinda zaici saidai ya fita daga cikin kogon ya shiga cikin daji ya farauto naman jeji sannan yazo ya gyara shi yaci babu wanda zai taimaka masa Kuma koda ace ya farauto idan ba irin manyan namun jeji bane Take yarima saiman zai kwace shi ya ajiye shi a gefe duk tsananin yunwar da yake ji Saidai ya koma cikin dajin ys farauto wata dabbar ita kuwa wacce ya farauto da farko anan za'a barta har ta rube Sannan a daukeshi a jefashi cikin teku sai ya shafe dakiku masu yawa ba tareda ya dago ba Idan kuwa ya dago za'a maidashi cikin ruwanne harsai ya ninka lokacin da aka dibar masa da farko A kwai ranar da akaje aka sami saiman aka shawarceshi akan ya daina baiwa wannan yaro irin wannan horon yaki Amma sai yayi murmushi sannan yace Duk abinda kuka ga inayiwa basdar ba wai ina kinsa bane tsananin soyayya ce tasa nake masa domin babu abinda zai sa mutum ya haifi da da jininsa kuma yakishi saidai da wani dalilin Idan har banyi masa hakaba to bazai zama irin danda muke bukata ba Kai har saida takai cewa wannan yaro ya saba da duk abinda aka koya masa Ya zamana idan ya naushi karfe komai kaurinsa da kuma kwarinsa saiya lankwashe Ko kuma ya loba ciki Idan Kuwa ya fita farauta baya shakkar shiga cikin garken manyan namun daji irinsu zakuna ya tarwatsasu da karfin tsiya kuma ya kama adadin wadanda yakeso Idan kuwa sukaji wahala suka gudu saiya bisu daya bayan daya ya kure musu gudu ya kamosu sannan ya dauresu da sarkoki ya jawosu gida ba tare daya gajiba idan kuwa yayi nitso akasan teku yana iya shafe sa'a biyu ba tareda ya dago da kansa ba Kuma yana iya daukar dutse mai nauyin daukar katti hudu shi kadai ya yini yana gudu dashi akafadarsa Sannan yazo gitfawa ta gaban yana iya kamashi ya hau komai girmansa da kuma santsinsa Kuma ko kadan wannan yaro bayajin tsoron tsoron mutuwa Domin kullum idan ya fita farauta yana shiga cikin manyan dajijjika ne masu hatsari Wannan baiwa tasa ba karamin baiwa mutane mamaki takeba Domin ko a tarihi basu taba jin yaro mai irin shekarunsa da wannan baiwarba Har saida takai cewa idan ya fita daji idan dabbobi ko wasu mugayen halittun suka ganshi saidai kaga suna tserewa Idan kuwa yarima saiman yana bashi horo sai kaga duk irin wahalar da zaisha take yake jureta saboda allah ya halicceshine amatsayin mai kwarin kashi da kuma juriya da kaifin kwakwalwa Soyayya kuwa mahaifinsa suna nuna masa ita sosai idan aka gama bashi horon yaki Aka shiga domin shimfida daya suke kwanciya da iyayensa Kuma komai yake da bukata sai anyi masa ba'a kinyi WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN SU YARIMA SAIMAN BAYAN SUN TSIRA DAGA GUDUN TSIRAN DA SUKAYI 0======[]:::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Al'amarin boka ulumanu kuwa bayan ya sami nasarar cin birnin ramlatul saif da yaki Sai ya koma cikin fadarsa cikin farinciki bisa sanin cewa ya sami abinda yake da bukata Take ya shiga cikin dakinsa na tsafi ya zuba jinin wannan macijiyar wacce mutanen birnin ramlatul saif suke bautawa Domin ka idane cewa sai wannan jinin yayi mako biyu acikin wannan tukunyar tsafi sannan zaisha Daga wannan rana hankalin boka ulumanu bai kara kwanciyaba Sakamakon mugayen mafarkai wadanda ya dinga yi Kullum acikin barcinsa sai yaga an nuna masa wata gagarumar wuta tazo har cikin gidansa ta konashi da dukkan abinda yake cikin gidan Haka yake gani acikin mafarkinsa kullum ba'a taba samun bacin ranaba Wannan mafarki ba karamin tayar masa da hankali ba Kuma saidaya yi bincike acikin hallarar tsafinsa ko zaiga fassarar wannan mafarki amma sai tsafin nasa yaki ya nuna masa komai Daga baya sai ya gayyato dukkan manyan matsafan da suke nahiyarsu dama wasu nahiyoyin domin suzo su taya shi bincike Lokacin da suka gama hallara suka dukufa gaba daya wajen yin bincike saida suka kwana suna yi amma basu sami fassarar wannan mafarkiba Abinda kawai suka gani shine Dolene boka ulumanu yayi hakuri zuwa sanda zai kammala sihirinsa Na tsafi to sannan ne zai iya sanin fassarar wannan mafarki Daga wannan rana kullum boka ulumanu yazauna jiran lokacin da zai kammala sihirinsa Haka kuwa akayi bayan mako biyu ya gama kammala sihirinsa Yana shanye jinin take yaji jikinsa yayi karfi sosai kamar zai iya daukar duniya gaba dayanta Nantake ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi bisa mamaki sai yaga s wannan lokacin madubin ya bude masa abinda yake da bukatar gani Saiga hotonsu yarima saiman tun daga lokacin da suka fita daga birnin ramlatul saif zuwa sanda suka suka isa kogon darul sihir hardama jaririn da suka haifa wato basdar Koda ganin wannan al'amari sai boka ulumanu ya takarkare ya kwarara uban ihu Take ya tashi da nufin ya fita yaje ya yaki su saiman a can kogon Kawai sai yaji wata murya ta fito daga cikin madubin tsafinsa Tace kada ka kuskura kace zaka fita kaje ka tunkari wannan kogon dutsen Domin ba makawa kana zuwa zaka hallaka domin sihirin da yake cikin wannan kogon dutsen yafi na jikinka karfi Saidai ka jira idan basdar ya girma shi da kansa zai fito nemanka A sannan ne zaka sami damar hallakashi tareda iyayensa Koda gama sauraron wannan zance sai hankalin boka ulumanu ya kwanta Daga wannan rana yaci gaba da yakar kasahen da suke nshiyar Yana kwace karagar mulkinsu da karfin tsiya bayan ya kashe sarkin garin sai ya dora wakilinsa agarin Sannan ya kara gaba ya nufi wata kasar Saidaya cinye kasashen da suke nahiyarsu kaf Harya shiga wasu nahiyoyin duk karfin mulkin sarakuna suna tsoronsa Kuma babu yadda basuyi ba akan su kare kansu amma sun kasa Saidai kawai kullum suji ance musu su kara hakuri akwai lokacin da wani zaizo ya taka masa birki akan abinda yakeyi WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA BOKA ULUMANU 0====={{::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'ajeba Kuma kowanne abu idan aka saka masa lokaci to tabbas wannan lokacin zaizo Kamar yadda aka fada afarkon labari cewa basdar bazai sami dama tunkarar boka ulumanu ba saiya cika shekaru ashirin a duniya Saboda tsabar karfin damtsensa daga awannan lokaci idan ya naushi dutse saidai kaga hannunsa ya burma jikin dutsen ya nutse Ahaka jikinsa ya murde tamkar curin duwatsu da tarin kwarjini Kuma gashi da tausayi da girmama na gaba sannan baya yarda yaga ana zalunci a ko ina A ranar da ya cika shekaru ashirin din ne yana cikin barci Yayi mafarki a cikin mafarkin aka nuna masa Wata irin macijiya tana bin mahaifinsa da gudun tsiya tanaso ta kamashi Shi kuma yana ta tika gudu don ceton ratuwarsa Da kyar ya samu ya shige cikin wani kogo ya buya ita kuma macijiyar ta tsaya a bakin kogon tana jiran fitowarsa Koda yazo daidainan acikin mafarkin nasa saiya farka a matukar razane Take mahaifinsa suka fito daga cikin dakin da suke kwance Alokacin tsufa ya fara kamasu suka taho dakinsa suka sameshi Suka tambayeshi abinda yake faruwa Take ya kwashe labarin komai ya fada musu Koda sukaji haka sai suka girgiza kai Sannan saiman yace Yakai dana hakika lokaci yayi da zamu fada maka sirrin da muka boye maka Kuma shine dalilin dayasa muka dinga baka horo mai tsanani har wasu suke zaton bama kaunarka Nandai suka kwashe labarin komai suka fada masa tarihinsu da birninsu da dalilin dayasa suka gudo wannan kogo Koda gama jin wannan labari sai idanunsa suka ciko da kwalla Yaji ya tsani boka ulumanu fiye da komai aduniya Nantake ya mike tsaye da nufin fita daga cikin kogon Take suhaila ta ruke masa hannu tace Ina kuma zaka? Basdar yace zanjene domin daukar fansar abinda akayiwa iyayena da kuma kasata Kodajin haka sai tace ai wannan aiki bana gaggawa bane dole kayi hakuri gari ya waye mu zamuyi maka jagora mu tafi nemansa LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU BAKAR GABA PART 27 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Nandai suka kwashe labarin komai suka fada masa tarihinsu da birninsu da dalilin dayasa suka gudo wannan kogo Koda gama jin wannan labari sai idanunsa suka ciko da kwalla Yaji ya tsani boka ulumanu fiye da komai aduniya Nantake ya mike tsaye da nufin fita daga cikin kogon Take suhaila ta ruke masa hannu tace Ina kuma zaka? Basdar yace zanjene domin daukar fansar abinda akayiwa iyayena da kuma kasata Kodajin haka sai tace ai wannan aiki bana gaggawa bane dole kayi hakuri gari ya waye mu zamuyi maka jagora mu tafi nemansa Cikin sanyin jiki jarumi basdar ya fara yi musu magiya akan su barshi ya tafi amma suka ki Da kyar suka iya shawo kansa ya hakura Amma acikin wannan daren saboda tsabar kaguwar da yayi barci ma kasawa yayi sai ya zauna kurum yana jiran gari ya waye Kashe gari kuwa da sassafe ya fito daga cikin turakarsa Ya nufi dakin da iyayensa suke ciki Koda ya bude kofa ya shiga sai yayi arba da mahaifan nasa Azaune idanunsu sun kada sunyi jawur da alama suma a wannan daren basuyi barci ba Koda sukayi arba da basdar sai suka taso da sauri suka tareshi Fuskarsu cike da murmushi sannan suka ruko hannuwansa Suka jashi sukazaunar dashi suka fuskanci juna sukace Yakai basmar hakika wannan itace ranar da muka jima muna jiran zuwanta Ayaune mukeso kayi mana aikin damu muka kasa yinsa Kuma kai kadaine zaka cikawa jama'armu burikansu Kafin yace wani abu sai suka kama hannunsa suka jawoshi waje daga cikin wannan dakin Suka fita waje dashi suka nufi wani bangare daban na cikin kogon darul sihi Shidai wannan waje tunda jarumi basdar ya taso bai taba zuwa gurinba Asalima bai sanda shi ba domin kuwa wajen wata irin katangar sihiri ce ta katange gurin Azahiri idan ka taba wajen ko kuma ka kalleshi zakaji katangace agurin Amma bisa mamaki sai basdar yaga awannan lokaci ya sun ratsa ta cikin wannan katangar kamar yadda haske yake ratsa gilashi Saida sukayi tafiya mai dan nisa sannan suka iso wani babban daki Wanda ya fita daban da sauran dakunan da suke cikin kogon darul sihir Komai na wannan dakin ba azaune yake bisa turba ba Yana yawo ne akan iska amma hakan batasa wani abu ya lalace ba Su kansu yayinda suka shiga cikin wannan dakin sai suma suka fara yawo akan iska kamar yadda komai na ciki yakeyi Har saida yarima saiman yayiwa jarumi basdar nuni da wata rantsatstsiyar kujerar mulki wacce gaba daya an san'anta tane da lu'u lu'u Kuma wani irin haske mai sheki yana yake fita daga cikinta Sannan ya umarceshi daya zauna akanta Dukda cewa jarumi basdar sadaukin gaskene wanda ya gaji jarumtaka ta gurin iyayensa da kakanninsa gaba da baya Saida yaji zuciyarsa ta buga alokacin da yaji mahaifinsa ya umarceshi da zama kan wannan karagar Sakamakon wasu irin birkitattun tunani da suka dinga zuwar masa a cikin zuciya Saida yaji mahaifinsa ya daka masa tsawa yace tunanin me kakeyi ne? Ka gaggauta yin abinda na umarceka nantake yaji hantar cikinsa ta kada sakamakon jin irin kakkausar muryar da mahaifinsa yayi masa magana da ita Don haka baisan sanda ya damki kujerar ba alokacin da suke yawo dashi da ita acikin iska ba ya zauna akanta Faruwar hakan keda wuya sai komai na cikin dakin ya daidaitu suka dawo suka zauna bisa turba Kuma wani irin haske mai karfi ya dallare dakin gaba daya Nantake jarumi basdar yaji wani irin radadi a jikinsa kamar ana tsotse jinin jikinsa Tareda wani irin zafi kamar an dorashi akan garwashi Nantake ya fara rusa ihu alokacin da jikjnsa gaba daya ya fara karkarwa kamar mai jin sanyi Haka dai ya kasance tun yana iyayin motsi da jikinsa har ya kasa Faruwar hakan keda wuya sai kuma ya daina jin wannan abin da yake ji Nantake yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi kamar zai iya nada gammo ya dauki duniya Kuma yaji wani irin kuzari ajikinsa kamar idan akace yayi gasar tsere da iska zai iyayi Su kansu iyayen nasa da suka lura da yanayinda yake ciki sai suka kamu da farinciki Nantake suka rungumeshi sannan suka sumbaci goshinsa Saiman yace yakai dana to yanzu ne kakai matakin da muke da bukatar kakai Duk duniya babu wanda bazaiyi shakkarka ba amma duk da haka sai kayi kokari ka zage damtse sannan zaka sami nasara akan boka ulumanu Kuma ina gargadinka da cewa Ka zamo mai tausayi da jinkan talakawa da kuma ruke alkawari Idan har ka ruke wadannan abubuwa musamman ma ka hada da gaskiya To ina rantsuwa cewa babu wani abu da zai gagareka aiwatarwa a wannan duniya Koda jin haka sai jarumi basdar yace Ya abbana nayi alkawarin zan ruke wadannan shawarori naka Saidai kuma ina jiran naji wadanda zasu fito daga bakin mahaifiyata Kodajin haka sai gimbiya suhaila tayi murmushi yadda har saida hakoranta suka fito Sannan tace Ai duk abinda zan fada tuni mahaifinka ya fada maka saidai ina shawartarka daka zamo mai dakakkiyar zuciya acikin duk abubuwan da kasa a gabanka idan kayi haka to ina mai tabbatar maka da cewa bukatar ka zata biya komai wahalarta Domin akwai abinda karfin dantse ko na sihiri basa yinsa saidai zuciyace take iya aikatashi Tana gama fadin hakan sai suka juyo suka kamo hanya suka fito daga wannan bangaren da suka shiga Koda suka dawo izuwa ainihin harabar kogon sai mutane suka dinga kallon jarumi basdar Domin gani sukayi halittarsa ta kara wani irin kwarjini fiye da farko Alokacin kowa yana waje suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum Koda ganin haka sai yarima saiman yace dasu Yaku mutanen birnin ramlatul saif Inaso dukkanku ku shirya domin yanzune zamu koma izuwa can birnin mu na haihuwa Don haka kowa ya hada kayansa Koda suka ji abindaya fito daga bakin yarima saiman Sai kowannensu ya kamo da murya suka fara shewa harda tsalle Ba tareda bata lokaci ba suka shiga cikin gidajensu suka fara harhado kayansu duk da cewa a sannan mafi yawansu duk girma ya fara kamasu Shi kansa yarima saiman a sannan shekarunsa sunkai shekaru hamsin da 'ya'ya Cikin 'yan a wanni suka kammala hada kayayyakinsu Bayan kowa yafitone sai yarima saiman ya dauko wannan takobin sihirin 0======={}:::::::::::::::::::::::::::::::::::> Ya mikawa jarumi basdar ita sannan yace Wannan takobin saboda kaine naketa ajiyarta tun tsawon shekaru Don haka yanzu lokaci yayi da zan mallaka maka ita Dajin haka sai jarumi basdar ya karbeta da hannu biyu Sannan yarima saiman yace dashi Saika shiga gaba domin yanzu bani bane shugaban wannan ayari ba Kaine saboda haka alhakin kare wadannan mutane gaba daya ya dawo kanka Ba tareda gardama ba juwa jarumi basdar ya shige gaba suka kama tafiya Sai gashi wani abin al'ajabi yana faruwa Domin hanya kawai sukaga yana bi tamkar damacan yasan taswirorin wannan daji Kuma komai yawan manyan dabbobin daji da manyan aljanu Idan sukayi arba da jarumi basdar tun daga nesa saidai kaga suna rugawa da gudu Domin kowa yana shakkar tunkararsa idan kuwa sukayi kuskuren aikata haka to sunsan dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba Idan kuwa sukazo giftawa ta gaban dutse ko wani tsauni Sai kaga ya tsage gida biyu ya basu hanya sun wuce Idan kuwa kogine ko teku sai su dinga taka ruwan suna tafiya akansa kamar suna tafiya akan kasa WANNAN SHINE ABINDA YA FARU BAYAN SU YARIMA SAIMAN SUN BARO KOGON DARUL SIHIR ABISA JAGORANCIN DANSA WATO MATASHIN JARUMI BASDAR 0======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::> Acan fadar boka ulumanu kuwa cikin watanni kadan ya gama cinye kasashen da suke nahiyar da yaki Ya zamana cewa kowanne sarki akasansa yake kuma sunayi masa biyayyar dole Sannan ya kammala hada sihirinsa na tsafi Wannan ne ya bashi damar yin abinda yakeso da karfin sihirinsa Wata rana kawai yana zaune a cikin dakin tsafinsa kawai saiya tuna da batunsu yarima saiman da kuna dansu jarumi basdar Koda gama tunawa dasu sai ya mike ya shiga bincike akansu cikin madubin tsafinsa Nantake yaga cewa yanzufa sun fito daga cikin kogon darul sihir sun nufo nan fadarsa Koda gama ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariyar farinciki Domin yasan idan ya kashesu bashida sauran fargaba Yana gama wannan tunani sai yace azuciyarsa Dolene naje na taresu tun akan hanyarsu kafin su iso wannan kogon Yana gama fadin haka saiya tashi sama kamar dama can yanada fuka fukai Take ya ratsa ta cikin ginin saman fadar tasa ya fice Daga cikin fadar ya luluka acikin gajimare cikin tsala azababben gudu kamar na tauraruwa mai wutsiya Sai gashi cikin cikin kankanin lokaci yaje gurin da suke ya tare su Alokacin suna cikin wani daje mai yawan bishiyoyi da kuma duwatsu Kawai sai gani sukayi wata irin bakar guguwa ta taso ta tokare sararin samaniya kai kace hadarine ya hado za'ayi ruwan sama Kura ta turnuke dajin gaba daya har saida dawakan dasu yarima saiman suka hawo suka fara ja da baya kamar zasu zubar dasu a kasa Har saida jarumi basdar ya daka musu tsawa sannan komai ya tsaya ya koma yadda yake Bakar guguwar itama ta disashe kamar bata taba samuwa ba Dawakan nasu ma suka nutsu kamar wani abu bai taba samunsu ba Ba komai ne ya janyo haka ba face bayyanar boka ulumanu Cikin gagarumar shigar yaki taban tsoro tamkar wanda zai yaki duniya A hankali komai ta lafa har boka ulumanu ya bayyana yadda kowa yana iya ganinsa Wohoho nanfa aka fara kallon kallo a tsakaninsa dasu yarima saiman Daga can sai yarima saiman ya kalli boka ulumanu cikin murmushi Sannan yace Ka gaji kenan da zaman jiran mu fadarka shine yasa ka kawo kanka zuwa hallakarka Gaskiya na jinjina maka wannan kasadar da kayi Koda jin haka sai shima boka ulumanu ya bushe da dariya yace Gaskiya indai kayi wannan tunanin ka yaudari kanka domin mahaifinka ma yayi mini irin wannan cika bakin da kayi amma duk da haka saida naga bayansa Kodajin haka sai shima ya kyalkyale da dariya sannan yace Ai yanzu ba dani zaku fafata ba da dana ne don haka nida sauran mutanena 'yan kallo ne Yana gama fadin haka saiya koma da baya shida sauran jama'arsa Ya zamana anbar boka ulumanu da jarumi basdar a tsakiyar fili Suka fara kallon kallo na tsawon 'yan dakiku daga can sai jarumi basdar da ulumanu Suka falfalo da azababben gudu suna kwalla ihu wanda ya razana kowa da yake wajen Nantake suka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance Sai gashi suna kaiwa junansu mugayen hare hare masu matukar razanarwa Duk sanda suka kawowa junansu hari idan ya goce duk abinda suka samu saidai kaga ya dagagaje kamar an nuka gari Idan kuwa makamansu suka hadu da juna sai kaga tartsatsin wuta yana tashi Sai gashi sun hargitsa dajin gaba daya dabbobi suka fara gudun ceton rayukansu Tsuntsaye suka fara canja sheka Bishiyoyi kuwa suka dinga karyewa suna zubewa akasa Dukda cewa dajin cike yakeda bishiyoyi saida sukayi masa fata fata Ya zamana cewa gaba dayansa sun mai dashi fili fetal babu sauran bishiya guda daya a tsaye Tun suna wannan gumurzu a doron kasa saida ya zamana sun daina Suka tashi sama akan iska sannan suka ci gaba da wannan fada Kuma kowa acikinsu ya kasa samun nasara akan abokin gwaminsa Koda ganin haka sai suka fara jifan junansu da sihiri kala kala Duk wanda ya jefi wani da nasa sihirin idan ya goce saidai kaga ya fada kan dutse Duk abinda sihirin ya fada kansa take yake ruburbushewa sannan ya kama da wuta Kai saida suka yini suka kwana suna wannan fafatawa amma babu wanda ya sami nasara akan wani Ganin hakane yasa sadauki basdar fusata yaga cewa ya za'ayi ace shi amatsayinsa na matashi ya kasa samun nasara akan wannan tsohon mutumin Koda yin wannan tunani Saiya kara zage damtse ya dinga kai masa mugayen hare hare Cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta tamkar jikinsa bana jini da tsoka bane Sai gashi tun boka ulumanu yana iya kare hare haren har ya zamana cewa ya kasa saidai kokarin kare kansa Yakeyi wannan ne ya baiwa sadauki basdar damar yiwa boka ulumanu mummunan yanka a kan damtsen hannunsa na dama Nantake boka ulumanu ya kwarara uban ihu sakamakon zafi da zugin da yaji Nantake yaji wani irin mummunan dafi ya shiga jikinsa har idanunsa suka fara lumshewa Koda ya tabbatar da cewa idan akaci gaba da wannan gumurzun a haka bazai sami nasara ba a wannan yakin sai nantake ya shammaci jarumi basdar ya ruga aguje domin ceton rayuwarsa Har basdar ya yunkura zai bishi sai yaji mahaifinsa ya daka masa tsawa Yana mai umartarsa da kada ya bishi Cikin sanyin jiki basdar ya dubi mahaifinsa yace ya abbana mainene dalilin da yasa ka hanani na bi wannan tsohon abokin gabar tamu Dajin haka sai yarima saiman yayi murmushi yace Ai bai kamata ka bishi ba a yanzu domin shima ya yarda yanzu cewa kai ba kanwar lasa bane Nafiso mu bishi har fadarsa mu rusheta kamar yadda shima ya rushe birnin mu Yana gama fadar haka sai duk su biyun suka sauko suka koma cikin tawagarsu Sannan suka ci gaba da tafiya zuwa fadar boka ulumanu Saida suka shafe yini guda suna tafiya har rana ta fara neman faduwa kawai sai suka yi arba da wata wata kyakykyawar budurwa Ta sanya kaya wadanda suka rufe duk jikinta A zaune gefe daya ta fuskanci gabas ta tattara hankalinta gaba daya aguri daya kamar wacce takeyin ibada Koda sukayi arba da wannan budurwa sai gaba dayansu Suka labe a wani sako na wannan dajin suna leken wannan matashiyar budurwa Sai Jarumi basdar ya kalli mahaifinsa yace Yakai abbana shin kasan irin wannan ibadar da wannan budurwa takeyi? Dajin wannan tambayar sai yarima saiman yace Gaskiya ni tunda nake ban taba ganin ibada makamanciyar wannan ba Kai ni ko atarihi ban taba jinta ba amma bansani ba ko ita mahaifiyarka ta sani Dajin haka sai itama suhaila ta gyada kai alamar bata santa ba Sannan tace lallai wannan ibadar bantaba ganin ibada mai irin nutsuwarta ba Kadai duba ka gani duk ilahirin jikinta ta rufe shi sannan ta zauna a guri daya ba tareda tanayin raye raye ba Suna cikin wannan hali ne wannan budurwar ta idar da ibadar da takeyi Sannan suka ga ta dauko wani dan karamin littafi ta fara karantashi Saboda dadin karatun da takeyi saida sukaji gaba daya tsigar jikinsu ta tashi Sukaji wata irin nutsuwa tazo musu wacce basu taba jin irinta ba Don haka basu san lokacin da suka fara 'yan surutaiba har suka fara zubar da abubuwan da suke hannuwansu Karar faduwar kayan ce tasa budurwar ta juyo baya da sauri don taga mene yake faruwa Tareda karanta wani lafazi wanda basu san ma'anarsa ba Koda taga su jarumi basdar a tsaye a bayanta saita mike da sauri Tana mai ja da baya tareda fadin suwaye ku? Ina mai rokonku da kada ku ce zaku cutar dani Koda jin haka sai yarima saiman yace yake wannan budurwa Kada ki tsorata damu domin mu ba masu cutarwa bane a gareki ba Amma ina mai rokonki don girman abin bautarki da ki fada mana sunan wannan addini naki Domin ko a tarihi ban taba jin labarin irin wannan addini naki ba Sannan inaso ki fada mini sunanki da kuma abinda ya kawoki wannan nahiyar tamu? Kodajin wannan tambaya sai wannan budurwa tace da farko dai kamar yadda ka tambayeni game da addini na Shidai addini na shine addinin musulunci wanda ake bautar ubangiji guda daya Wanda bai haifaba kuma ba'a haifeshi ba Shine wanda ya halicci sammai da kassai da kuma abubuwan da suke cikinsu Kuma ya haliccesu ne domin su bauta masa amma sai wasu daga cikin mutane da aljanu suka bijire masa suke bautar wasu abubuwa sabaninsa Kuma yana sane da hakan kawai yana

Chapter 13 of 14