Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dudduba wannan daji ko zamu sami inda zamu sameshi koda suka ji jawabin markazulu sai hankalin gaba daya mutanen ya kara tashi fiye da ko yaushe wasu ma har kuka suka dinga yi domin su aganinsu yarima saiman ya zama gawa koda jarumi zamnal yaga halinda suka shiga sai ya daka musu tsawa yace wai waya fada muku cewa shugaba ya mutu? ku sani koda ma ace zai mutu dolene saidai ahannunmu don haka kowannenmu tare dashi za'ayi wannan tafiya don haka zamu kasu ne zuwa kaso biyu kaso daya zasu tsaya ne akarkashin kulawar aljani markazulu kaso na biyu kuwa suna karkashin kulawata ne inaso mu dudduba gefen wannan tsauni ko'ina da ina hatta cikin ciyayi sai mun duba dukda nasan markazulu ya bincika daya bangaren na wannan tsauni to mu sai mu duba wannan bangare domin mu ya kamata mu zage damtse wajen nemansa tunda duk irin halin da ya shiga ya shiga ne domin kubutar da rayuwarmu zamnal yana gama wannan jawabi sai ya raba dakarunsa biyu, mutanen gari ma haka wasu sukayi bangaren hannun hagu na tsaunin wasu kuma sukayi bangaren hannun damansa haka sukayi ta tafiya suna duba cikin ciyayin dake cikin dajin idan sukazo wajen koramu kuwa sai su tsaya su shiga ciki suyi nutso akarkashin ta har sai sun tabbata baya ciki sannan zasu fito hakama idan sukazo kwazazzaban duwatsu ko cikin koguna sai sun bincika cikinsa saida suka shafe yini guda suna yawon neman yarima saiman amma sama da kasa suka kasa ganinsa bisa dole suka dawo izuwa inda suka rabu jikinsu asanyaye aka rasa me cewa uffan, wasu ma kuka suka kamayi domin sun tabbata yarima saiman ya zama gawa da ganin haka sai zamnal ya daka musu tsawa yace yarima yana raye ina da tabbacin cewa bai mutuba domin aljani markazulu ya duba mana kan wannan tsauni yace baiga gawarsa ba sannan muma da kanmu mun duba wannan bangaren na tsaunin nan bamu sami gawarsa ba don haka dolene ya kasance rayayye domin inda ya mutu da mun sami gawarsa sai dai ina da tabbacin cewa yana cikin mawuyacin hali yanzu haka babban bakin ciki na shine rashin sanin tsayayyen gurin da yake balle muje mu kai masa dauki, amma ina da tabbacin cewa indai ahalin yanzu yana raye to dolene ya tsira da rayuwarsa ya dawo garemu don haka ya zama dole agaremu mu tsaya adaidai wannan wuri mu jirayi dawowarsa koda kuwa zai kai shekara guda bai dawoba don nasan idai yana raye dolene ya dawo garemu domin rayuwarsa da kuma burinsa suna nan babbar matsalarmu ayanzu itace gimbiya suhaila idan ta farka daga barcin da takeyi me zamuce mata dangane da lafitar mujinta? dajin wannan tambaya sai markazulu yace ai ba zata taba farkawa ba daga wannan barcin da takeyi ba harsai dai idan nine na tasheta domin yanzu kula da rayuwarta data abinda ke cikin cikinta duk suna hannuna ni na gama nawa kai kuma mai karatu mai kake ganin zai sami yarima saiman? sai na jiku LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME ART 13 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR To yau rahoton dana samo akansu yarima saiman shine al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da santsi ya kwasheshi ya fadi kasa sumamme akan wannan tsauni sai ya dinga gangarawa izuwa kasansa yana buguwa da jikin duwatsu hakan ya haddasa masa manyan ciwuka ajikinsa har sai da takai hannunsa na hagu ya karye yana cikin wannan haline kawai ya gangaro izuwa kan wani katon dutse wanda da zarar ya fado kan dutsen take kansa zai dagargaje adaidai wannan lokacine kwatsam sai wani katon tsuntsun ya taho daga sama ya sure shi yayi sama dashi nantake ya luluka izuwa cikin sararin samaniya cikin azababben gudu tamkar kiftawar tauraruwa mai wutsiya cikin kankanin lokaci tsuntsun ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba sai da tsuntsun ya shafe 'yan dakiku yana tafiya sannan ya iso kan wani katon tsuburi yana zuwa bakin sai tsuburin ya dare gida biyu ya samar da wata katuwar hanya nantake tsuntsun ya shige cikin tsaunin sannan kofar ta mai da kanta ta rufe sannan tsuntsun ya rikide ya koma siffar wani katon aljani tsoho tukuf cikin sauri wannan aljanin ya fara gyarawa yarima saiman karayar dake jikin hannunsa tareda kuma saka masa magunguna akan raunikan da yaji ajikinsa bayan ya gama gyara masa jikin nasa sai ya samo ruwa ya yayyafa masa faruwar hakan keda wuya sai yarima saiman ya farfado daga doguwar sumar da yayi yana farkawa sai ya tashi zaune firgigit da nufin ya mike tsaye cikin sauri wannan aljani yasa hannuwansa guda biyu ya dafa yarima saiman yace haba yakai wannan sadaukin zamani kuma gwarzon karnin da muke ciki kayi hakuri ka zauna mana domin mu tattauna wadansu muhimman maganganu tsakanin ni da kai koda jin haka sai saiman ya dubi aljanin afusace yace mai zan zauna nayi anan kana ganin halin da mutanena suke ciki akasan wannan tsaunin koda jin haka sai wannan aljanin yayi murmushi saboda ya fuskanci cewa yarima saiman baisan inda yakeba ahalin yanzu kuma baisan cewa ya sami raunika ba tareda karaya ajikinsa sai ya sake cewa yakai wannan jarumin dan sarki ai yanzu haka komai ya riga ya wuce dajin haka sai ya kalli aljanin afusace yace mekake nufi da wannan maganar taka? ba tareda aljanin yace uffan ba sai ya nuna jikin bangon dutsen da hannunsa nan take sai hoton duk abinda ya faru ga gareshi ya bayyana tun daga lokacin da santsi ya kwasheshi har zuwa sanda aljanin yaje asiffar tsuntsu ya daukoshi da kuma abinda ya faru tsakanin dakarun yarima saiman da wadannan manyan zakuna ya bayyana har zuwa sanda aljani markazulu yaje ya taimaka musu ya kashe wadannan sihirtattun zakunan da kuma wahalar da suka sha ta yawon nemansa koda gama ganin wannan al'amari sai nantake yarima saiman yaji duk jikinsa ya hau ciwo sai sannan ya lura da cewa akwai ciwuka ajikinsa koda ya kalli hannunsa na hagu sai yaga ashe ya sami karayane harma an gyara masa ita sannan an saka masa magunguna ajikin dukkan ciwukan nasa da ganin wannan abu yarima saiman baisan lokacin da hawaye ya zubo masa ba cikin sauri wannan aljani yasa hannuwansa ya share masa hawayen nasa sannan yace haba yakai jarumin jarumai hawaye bai dace da irin ku ba kadafa ka manta ayanzu kaine shugaban dukkan wani sadauki na wannan zamani ina mai tabbatar maka da cewa ayanzu duk hatsabibanci jarumi, sarki, ko kuma matsafi dolene yayi shakkar tunkarar ka domin ana cewa mai laya ya kiyayi mai zamani to yanzu zamanin nakane kai kadai sai yadda kaso zakayi inaso ka sani ba don naje na taimakekaba a lokacin da kake gamgarowa ba daga kan wannan tsaunin ba da tuni ka dade da shekawa barzahu kuma dolene ka zauna anan kayi jinyar jikinka koda ta sati biyuce domin ka sami kwarin jikin da zaka iya tunkarar fadar sarkin aljani na birnin hamshak dajin haka sai saiman ya kwallara uban ihu saboda tsananin bakin ciki sannan ya kalli wannan aljani yace yakai wannan aljani ina godiya bisa taimakon da kayi mini sannan inaso insan wanene kai da kuma dalilin da yasa ka ceci rayuwata? dajin haka sai aljanin yace da farko ni sunana ramzas asalina nine sarkin yaki abirnin hamshak ina da mata guda daya sunanta zumaira sannan ina da wani da maisuna harisul mar'uf tun harisul mar'uf yana yaro nake koyar dashi dabarun yaki iri iri har saida ya zama sadaukin gaske kuma gagara badau domin tun awannan lokacin yana fafata kazamin da dakaru masu yawan gaske kuma matasa masu jini ajika ya bazar dasu gaba daya ya sami nasara akansu ba tareda an sami wanda zai iya lakutar koda jikinsa ba wannan jarumtaka dasa da yake yi tasa ya shahara aciki da wajen birnin mu har ake masa kirari da jarumi dan jarumi jikan jarumai aduniya babu abinda nakeso sama da wannan da nawa guda daya da matata don haka banason abinda zai bata musu rai komai kankantarsa sarkin dake mulkin birnin hamshak a wannan lokaci ana kiransa da suna darkusma sarki darkusma ya kansance adalin sarki mai matukar kaunar jama'ar kasarsa fiye da yadda yake kaunar kansa tun lokacin da ina yaro karami mahaifina yake zuwa dani gidan sarautar birnin mu ina wasa agaban sarki darkusma hakanne yasa sarki yake matukar kaunata kuma yake riritani wani lokacin ma idan akayi baki wadanda basu san alakar dake tsakanina da sarki sai su zata cewa shine mahaifina saboda tsananin shakuwar dake tsakanin mu sarki darkusma yana da da guda daya wanda ake kira da suna mafazil dukda cewa sarki darkusma ta kasance adali sai halinsa ya banbanta dana dansa mafazil wato mafazil ya kasance azzalumin gaske mara tausayin talakawa ga kuma tsananin girman kai da rashin imani, domin shi bai dauki zalunci abakin komai ba wannan daliline ya haddasa 'yar tsama tsakaninsa da mahaifinsa sarki darkusma har sai da takai jama'ar birnin mu sun kasa hakuri da irin zaluncin da yarima mafazil yake musu da suka ga mahifinsa adaline saiya zamana duk lokacin da yayi musu ba daidai ba sai su zo su kawowa mahaifinsa kara shi kuma nantake agaban wadanda suka kawo karar zaisa a hukunta shi wasu lokutan da wannan abu yake faruwa duk ina tareda sarki suke faruwa har zuwa nake gaban sarki na fada inyita rusa kuka ina rokonsa akan yayi hakuri ya kyale yarima mafazil amma sai yace shi bazai hakura ba domin ba adalci bane ya hukunta talakawansa agaban idon kowa amma yace bazai hukunta dansa ba saboda shi daban ne wannan daliline ya haddasa kiyayya mai karfi tsakanina da yarima mafazil domin shi a tunaninsa nine na haddasa kiyayya tsakaninsa da mahaifinsa saboda kaunar da yake yi min tasa hatta makarantar yaki da muke zuwa wacce mahaifina yake koyar wa acikin ta waje daya muke tsayawa da yarima mafazil akullum yarima mafazil bashida burin da yafi yaga bayana ya sha dana mini mugayen tarkunan mutuwa amma ina tsallakewa da tsananin wahala wadanda ni kaina bana taba tunanin tsallakesu a haka muka girma ni dashi har zuwa lokacin da mahaifina ya mutu aka nadani sarkin yaki na birnin hamshak koda na sami wannan mukami sai ya kara saka mini kusanci da sarki darkusma ya zamana ko zaman fada sarki baya zama sai ina nan kuma ba kowacce shawara yake karbaba sai wacce na bayar a lokutan da ake irin wadannan abubuwa kuwa yarima mafazil yana gefen karagar mahaifinsa yana zaune yana kallon abubuwan da suke faruwa don haka sai ya fara tunanin anya kuwa sarki ba so yake ya munafurce shi ya hana shi sarautar da ya gada tun iyaye da kakanni ba? tun sarki darkusma baya fuskantar abinda yake cikin zuciyar yarima mafazil har ta kai ta kawo yana iya fuskantar komai don haka wata rana sai ya kirashi izuwa cikin turakarsa bayan ya karaso sai sarki ya dubeshi yace yakai dana hakika na fuskanci dukkan abubuwan dake cikin zuciyarka a kullum idan na kalli cikin kwayar idanunka babu abinda nake face tsananin gabar da kake yiwa abokinka sarkin yaki ramzas da kuma zargin da kakeyi akaina na tunanin anya kuwa ina kaunar ka kuma ina da burin barmaka gadon karagar mulkina? abinda nakeso ka fuskanta shine hannunka baya taba rubewa ka yanke ka wullar ba koda kuwa zakayi hakan to dolene kaji radadi ajikinka kuma dolene kayi kuka harka zubar da hawaye ta dalilin hakan to aduk lokacin da kayi laifi kai kana jin bakin ciki ne guda daya shine na matsayinka na dan sarki ana hukunta ka agaban talakawa ni kuma bakin cikina guda biyu ne sune yau ace na saka dakaru suna dukan dana guda daya tilo wanda bani da wani magajin inba shi ba bakin cikina na biyu shine yaya zaka kasance anan gaba bayan babu raina yayin da ka zama sarkin wannan birnin na tabbata idan har ba sauya rayuwarka kayi ba to talakawa zasuyi maka biyayyar dolene ba zasu taba kaunar ka ba kuma akullum zasuyi ta addu'ane akan ubangiji yakawo karshen mulkinka domin mulki da zaluncin baya taba dorewa kaga da zarar hakan ta faru shikenan sarautar birnin hamshak ta bar birnin mu har abada wannan daliline yasa nake kokarin hukunta ka domin ka gyara rayuwarka ta nan gaba amma ba wai don bana kaunar ka ba lokacin da sarki yake wannan bayani babu abinda yake yawo acikin zuciyar yarima mafazil face yana rayawa ne aransa kawai karyar banza mahaifinsa yake fada masa don haka bai tsaya sauraren karashen maganarba ya fice daga cikin turakar mahafin nasa gaba daya lokacin da yarima mafazil fice daga cikin turakar sai mahaifinsa ya fashe kuka ya tabbatar da cewa lallai karshen mulkin gidan su ya kusa kwacewa daga hannun zuriyarsu don haka sai yayi amfani da karfin sihirinsa ya bace daga cikin turakarsa ba tareda kowanne badakare ya ganshi ba hatta dansa mafazil kuwa ya bar gidan sarautar kai tsaye ya wuce izuwa gidan sarkin yaki ramzas da zuwa kofar gidan sarkin yaki sai ya bayyana tsulum sannan ya aika wani badakare yaje yayi masa sallama dani nantake kuwa badakaren ya cika umarni lokacin da badakaren ya sameni ya sanar dani sakon sarki sai abin yayi matukar dauremini kai kenan domin dukda kusancin dake tsakanin mu dashi duk da cewa ya dauke ni kamar dansa na cikinsa bai taba zuwa gidana ba don haka saina biyo badakaren da sauri azatona wani gagarumin yakin ne ya taso koda na fito nayi arba da sarki darkusma saina kamu da mamaki domin banga alamun tashin hankali ba atattare dashi don haka sai ya ruke hannuna yace yakai dana kuma garkuwar birnin hamshak yau maganar danake son yi dakai ta sirri ce don haka sai mu shiga daga ciki mu tattauna akan wannan magana dajin haka sai na wuce gaba nayiwa sarki darkusma jagora muna isa cikin gidan sai mukatarar da harisul mar'uf yana baiwa kansa horon yaki awannan lokaci yana yaro karami yana ganin sarki darkusma sai ya rugo da gudu yazo ya tsugunna ya gaisheshi cikin fara'a sarki darkusma ya dauke shi ya dagashi ya shafa kansa sannan yayi masa addu'a irin ta addininmu ya tofa masa a tafin hannuwansa ya ajiyeshi ya tafi ya ci gaba da baiwa kansa horon yakin sannan muka wuce izuwa cikin wata turaka muka zauna zaman mu keda wuya sai sarki darkusma ya dubeni yace yakai dana lokaci yazo wanda zamu rabu dakai kuma mulkin kasar nan zai koma hannun dana mafazil ni nasan mutanen kasar nan zasu shiga tsananin tashin hankali hatta kai kanka da matarka da danka sai kunfi kowa shiga cikin tashin hankali abinda nakeso da kai shine ka sallami matarka da danka su tafi can wata nahiyar daban su cigaba da rayuwa domin tsira da rayuwasu, domin nasan yadda dana yarima mafazil ya tsaneka to dolene ya shafi 'ya 'yanka kuma kaima dole sai yayi farautar ranka aduk inda zaka shiga aduniya aguri dayane zaka iya rayuwa ba tareda an ganoka ba wannan guri shine nantake ya nuna mini wannan kogon dutse da muke ciki ayanzu bincike ya tabbatar da cewa nan da shekaru masu yawa a cikin wata masarauta ta bil'adama za'a haifi wani gawurtaccen jarumi mai tarwatsa maza wanda bincike ya nuna cewa zaizo wannan birnin namu domin daukar kubar miftahul sihir akan hanyar zaizo wucewa takan tsuburin hijrul maut har ya fadi ya kusa hallaka to awannan lokacin zakaje ka dakoshi ka taimaka masa harya sami lafiya sannan ka taimaka masa ya mallaki kubar miftahul sihir nasan cewa dolene sai yarima mafazil ya mutu awannan yaki don haka awannan lokaci sai ka je ka nemo danka harisul mar'uf ka dora shi akan karagar mulkina idan kayi mini haka to shikenan raina zai kwanta lafiya acikin kushewa ta dajin wannan bayani sai kwalla ta zubo mini na dubi sarki darkusma nace akan wanne dalili kake maganar na taimakawa makiyanmu wadanda zasu zo domin su raba mu da abin bautarmu? sarki yayi murmushin yake yace ai kaddara ta riga fata ba komai ne ya janyo wannan kaddarar ba face halin dana inda ace dana zai koma adali to da duk wadannan abubuwa ba zasu taba faruwaba maganar kubar miftahul sihir da kake kuwa inaso ka sani ai ita wannan kubar ba guda daya bace ba acikin gidan sarautar birnin nan muna da irinta kwaya biyu kuma duk amfaninsu daya don haka daga yau inaso ka rabu da iyalinka ba zaku sake saduwaba sai nan da shekaru masu yawa kuma nima ayaune zanyi bankwana dakai domin rayuwata tazo karshe lokacin da yazo nan azancensa sai duk mu biyun muka fashe da kuka da kyar muka rabu dashi sannan ya koma cikin gidan sarautarsa ni kuma naje na kebanta da matata zumaira nasanar da ita abin da yake faruwa kuma na fada mata cewa subar cikin wannan garin a wannan daren sannan na mika mata takobin da nake fita yake yake da ita nace idan dana ya girma ta damka masa ita domin nima na gajetane tun iyaye da kakanni da kyar muka itama muka rabu da ita ta dauki harisul mar'uf alokacin yana barci ta gudu dashi suka bar birnin hamshak kashe gari da sassafe sai naji ana yada jita jitar sarki darkusma ya mutu kuma wai yarima mafazil yace nine na kasheshi sannan aka taho da dakaru masu yawa karkashin jagorancin yarima mafazil sun nufo gidana don su kasheni koda ganin haka sai nayi sauri nayi shigar yakina sannan na sallami dakarun da suke gadin gidana na karbi takobin daya daga cikinsu na kama hanyar fita daga birnin hamshak akan hanyata ne nayi kicibus da dakarun birnin mu da kuma yarima mafazil nantake muka ruguntsume da masifaffen yaki hakika badon na kasance jarumin gaske ba da tuni na dade da shekawa barzahu saboda saida muka shafe kwanaki ina yaki dasu nini kadai dakyar na samu na tsira da rayuwata harna iso zuwa wannan kogon dutse sai bayan na iso ne na gane cewa yarima mafazil ne ya kashe mahaifinsa,don ya gaje karagar mulkinsa kuma duk bala'in da matata zumaira take shiga ahalin yanzu shine yake turo mata dasu domin yasan indai bata da lafiya danta harisul mar'uf zaije ya samo mata magani burinsa shine harisul mar'uf ya mutu awajen neman magani kaga idan ya mutu itama kamar ta mutune yanzu haka ma harisul mar'uf yana tareda boka ulumanu domin yayi masa alkawarin zai samarwa da mahaifiyarsa lafiya idan har ya taimaka masa ya kashe masa macijiyar da birnin ku suke bautawa kai kanka kasan fada da wannan macijiyar ba karamin tashin hankali bane sai tsananin sa'a da rabone zasu ceceka daga hannun wannan macijiyar wannan shine labarin da na samo dangane dasu to mai karatu mai kake tunanin zai faru nan gaba ? LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCORAGEMEN BAKAR GABA PART 14 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Nidai labarin dana samo dangane dasu yarima saiman shine saiku saurara kuji koda aljani ramzas yazo daidai nan alabarinsa sai yarima saiman ya nutsu yana nazari dangane da labarin daga can saiya dago da kansa ya ramzas yace yakai wannan adalin aljani tabbas rayukar tana da ban tausayi kuma tana kama da irin rayuwata gaskiya na tausaya maka yadda ka iya jure rashin matarka da danka kuma kanaji kana gani babu yadda zakayi ka taimaka musu lallai yarima mafazil ya cika azzalumi kuma mara imani tabbas karshensa yana nan zuwa nan bada jimawa ba haka dai su yarima saiman suka dinga hira har dare yayi sannan yarima saiman ya sami guri ya kwanta barci abinsa WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN Acan sansaninsu sarki abu saiman kuwa lokacin da ya sana'anta mutum mutumi yaturasu izuwa hanyar da su boka ulumanu zai biyo yazo birnin ramlatul saif tare da dakarunsa sai nantake dakarun mutum mutumin suka bace bat basu bayyana ako'ina ba sai dajin farkon na iyakar birnin ramlatul saif ,koda bayyanarsu sai suka sami wasu manyan bishiyoyi masu duhuwoyi suka hau kansu suka zazzauna suka dana tarkunan kibiyoyin allurai a saman bishiyoyin dake cikin dajin gaba daya sannan suka hau kan wasu bishiyoyi mafiya tsawo da duhuwa suka buya yadda ko alamun su bazaka iya gani ba haka suka zauna jiran abokan gaba tsawon 'yan sa'o'i basu ji ko alamar tahowarsu ba sai bayan sa'o'i biyar sun shude sannan suka fara jiwo sautin tahowar rundunar boka ulumanu tun daga nesa suka dinga jiyo sautin bugun manyan ganguna masu karar gaske koda rundunar suka iso kurkusa sai dakarun mutum mutumin suka fara harba musu wadannan kananun sihirtattun alluran nan nantake kuwa alluran suka dinga huda jikin dakarun ba tareda sun sani ba akalla kibiyoyin sun shiga jikin dakaru akalla guda dubu daya da dari biyu da doriya amma duk wannan abu dake faruwa dakarun da boka ulumanu basu ankara ba sai da sukayi tafiyar rabin sa'a sannan dakarun suka dinga yanke jiki suna fadowa daga kan dawakansu suna kakarin mutuwa kafin cikar dakiku goma sai duk gaba dayansu suka zama gawarwaki koda ganin abinda yake faruwa sai ragowar dakarun da kuma boka ulumanu suka ja linzaman dawakansu cikin firgici domin basu san menene ya jawo hallakarsu ba nantake boka ulumanu ya sauko daga kan tsuntsun tsafinsa ya dubi gawarwakin yaga wata farar kumfa tana fitowa daga cikin bakunansu sai ya mika hannunsa ya dangwalo kumfar bakin daya daga cikinsu ya shanshana ta sannan ya juyo ya kalli dakarunsa yace tabbas an kawo mana harin bazato akan hanyarmu don haka bara na duba naga silar faruwar hakan nantake ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi domin ganin gaskiyar al'amarin mai makon madubin tsafin yayi haske yaga abinda yake faruwa amma sai madubin tsafin yayi baki sidik ya fara kumbura yana shirin yin bindiga ya fashe koda ganin abinda ya faru sai boka ulumanu ya takarkare ya kwarara uban ihu sannan yace ko shakka banayi tabbas abokan gabar mune suka fara kawo mana farmakin sumame don haka dole ne muyi taka tsantsan yanzu akan hanyar mu don gujewa sake shiga cikin wani tarkon mutuwar yana gama fadin haka sai ya koma kan tsuntsun tsafinsa ya zauna sannan ya shige gaba aka fara tafiya domin zuwa birnin ramlatul saif da yaki duk abinda ya faru gasu boka ulumanu sarki abu saiman ya gani acikin madubin tsafinsa kuma shine ya hana boka ulumanu ganin abinda yayi silar mutuwar mutuwar dakarunsa ta hanyar karfin sihirinsa don haka sai ya kara tashin wasu mutum mutumin ya tura su izuwa da jijjikan da suke kan hanyar birnin guda biyu kaso na farko ya raba musu turarrukan da zasu kunna a daji na biyu kaso na biyu kuma ya ya basu basu tarkunan da zasu binne akarkashin kasa tareda tsumin tsafi wanda yake tsotse jinin jikin duk abinda ya taba jikinsa nantake kuwa wadannan dakarun mutum mutumin suka je sukayi abinda aka umarce su kaso na farko sukaje daji na biyu suka kunna wuta sannan suka watsa wannan turaren sihirin faruwar hakan keda wuya sai kasa ta dinga tsagewa wasu irin manya manyan kunami suka dinga fitowa daga karkashin kasa su dai wadannan kunamai adadinsu ya kai dubu biyu kuma kowanne daya daga cikinsu yana da fuka fukai guda biyu wadanda dasu ne suke amfani wajen tashi sama koda bayyanar wadannan sihirtattun kunamai sai daya daga cikin dakarun mutum mutumin ya kallesu yace mai girma sarki abu saiman ya umarceni da in sanar daku cewa duk gaba dayanku yana so ku bace da gani da zarar dakarun boka ulumanu sun iso sai ku afka musu da yaki dajin haka sai dukkan kunaman suka durkusa alamar mubaya'a nantake kuwa kunaman suka bace da gani bat gaba dayansu shi kuwa boka ulumanu lokacin da yabar dajin da alluran sihiri suka farmakesu sai ya tafi cikin tsananin bacin rai babu abinda yafi tayar masa da hankali face ganin yadda madubin tsafinsa yaki yayi aiki yayin da yayi nufin bincike akan dalilin faruwar hakan tabbas yana da tabbacin cewa sarki abu saiman ya kawo masa wannan hari amma kuma baisan tarkon da sarki abu saiman ya kafa masa nan gaba sai a sannan yayi nadamar rashin yin cikakken bincike akan sarki abu saiman domin tabbas yanzu shima yasan cewa sarki abu saiman ya cika gwarzon jarumi kuma matsafi duk da cewa yana da tabbacin samun nasara akansa amma yana shakkar haduwarsu domin kar ta san kar ce a tsakansu amma wannan tunani bai saka shi tunanin komawa da baya ba haka suka dinga kusantar birnin ramlatul saif cikin mugun nufi tafiyar sa'a guda suka shafe sannan suka iso bakin iyakar daji na biyu koda isowarsu daidai wannan daji sai boka ulumanu ya daga kansa sama ya karewa dajin kallo tsaf yana nazarinsa ta hanyar karfin sihirinsa amma sai awannan karon ma baiga alamar wani abin cutarwa ba don haka sai ya juyo ya kalli dakarunsa yace to nidai abinciken na tabbatar da cewa babu wani abin cutarwa acikin wannan daji amma duk da haka ina mai shawartarku da kada mu kuskura mu saki jiki da wannan daji domin ako da yaushe al'amura suna iya sauyawa koda gama fadin haka sai ya zare takobinsa ya juya ya shiga cikin dajin cikin jin izza da yarda dakai ragowar dakarunsa nasa ma sai suka biyo bayansa tareda zare nasu makaman amma fa duk wanda ka kalla acikin su take zaka fuskanci cewa lallai amatukar tsorace suke amma ban da aljani guda daya wannan aljani kuwa ba kowa bane ba face aljani harisul mar'uf daga sarkin yaki ramzas na birnin hamshak domin shima tafiya yake yi cikin yarda da kansa ba tareda ya zare makami ba koda suka iso tsakiyar dajin ba zato ba tsammani sai suka ga wasu manyan manyan kunamai sun bayyana sukayi musu kawanya nantake kunaman suka afka musu aka muse aka ruguntsume da azababben yaki kunaman suka dinga harbin dakarun boka ulumanu nanfa suka ruguntsume da masifaffen yaki kunaman suka dinga harbin dakarun boka ulumanu suna faduwa kasa matattu babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda kunaman ko aljani suka harba sai dai kaga ya fadi kasa matacce nan take cikin kankanin lokaci nanfa kunaman suka firgita dakarun boka ulumanu suka zare takubbansu gaba daya suka afkawa kunaman da masifaffen yaki lokaci guda suka kasuwar rayuka ta dinga ci acikin dajin domin in banda sautin kukan dakaru da kuma ihun wadannan kunamai babu abinda kunne yakeji boka ulumanu kuwa da aljani harisul mar'uf duk inda suka shiga sai dai kaga kunaman suna zubowa kasa matattu domin harisul mar'uf wata irin jarumtaka ya dinga yi ta ban al'ajabi duk inda yakai sara ko suka sai dai kaga kunaman suna zubowa kasa matattu kamar ana sassabe a gona shi kuwa boka ulumanu yana amfani ne da karfin sihirinsa koda boka ulumanu yaga idan idan suka sake daukar lokaci mai tsawo kunaman zasu iya yiwa dakarunsa mummunan barna domin kunaman suna da matukar karfin sihiri koda gama yin wannan tunani sai boka ulumanu ya runtse idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai wata irin zazzafar wuta ta bayyana take wutar ta dinga bin kunaman tana konasu kurmus koda kunaman suka ga haka sai suka fara kokarin tserewa daga filin yakin amma sai wutar ta dinga binsu duk inda sukayi tana konasu abinda zai baka mamaki dangane da wannan wutar shine ko kadan bata kona dakarun boka ulumanu domin zakaga har ratsawa suke ta cikin wutar ba tareda tana konasu ba kafin cikar dakiku goma gaba daya kunaman sun

Chapter 7 of 14