Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BAKAR GABA littafin Habibullah Muhammad Kabara Kashi na daya 1 Ebook created by Shuraih 99% Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG BAKAR GABA PART 1 LBR HABIBULLAH KBR rungume suke da juna suna masu kukan rabuwa kamar bazasu daina ba. inda uban ya dubi dansa mai suna yarim saiman.yace yakai dana bakomai ne yasa boka ulumanu yakeson yakarnuba face tsananin zalunci irin nasa. saboda haka nake umartarku da kuyi shiri kai da matarka kubar wannan gari ku tafi izuwa kogon darul sihir kuci gaba da rayuwa acan shidai wannan kogo asalin mallakin wani kasurgumin boka ne.wanda ya kirkiri tsatsuba guda dubu. saidaya shekara dari yana aikin bokancinsa a ciki sannan ajali ya riskishe tundaga lokacin da ajali ya riskeshi aka rasa mahalukin da zai shiga wannan kogo yafito a raye . saboda haka nake umartarku da kuyi shiri ku tafi izuwa kogon darul sihir ku ci gaba da rayuwa. koda yazo nan a zancensa dai hankalin yarima ya dugun zuma.sannan ya dubi yarima yace.bawai inaso ku durfafi kogon darul sihir kai tsaye bane.yanzu haka na hada maka dakaru guda dari wadanda zasu zamo yan rakiya agareka. sai kuma kuyangi hamsin wadanda zasu kula fa lafiyar gimbiya har zuwa sa'ar da gimbiya zata haihu. a lokacin ne zata haifi ya mace ko namiji wanda zai zama gagara badau kuma sadaukin da da'a taba kamarsa kuma gwarzon mayaki. a lokadaya cika shekara ashirin aduniya alokacin ne zai mallaki duk wani sihirin tsafi da boka awaisul masawi ya bari.kuma alokacin ne zaku mallaka masa wata takobin sihiri da zaku dauko.yanzu hakazaku tafi dajin kurusul saudam domin dauko ita wannan takobi amfaninta shine komai karfin sihiri tana iya karya shi.kuma idan tana tare da kai inzaka shekara kana yaki bazaka gaji ba. abu na biyu da zaku samo shine tsumin dodo harjaju. shikuma dodo garjaju yanzu haka yana can wani daji wanda akewa lakabi da dajin ajali. shi wannan dodo shikadai ya isa ya mallaki duniya saboda karfin damtsensa dana sihiri.du wanda yasha。i tsumin dodo garjaju babu wani kaifi da tsini da zai kara tasiri ajikinsa da ku sai kuma abu na uku wanda zaku samo shine makullin kogon darul sihir wanda dashine za'a iya bude kofar kogon darul sihir. shi kuma wannan makullin ana kiransa da miftahul sihir. yanzu haka yana hannun sarkin aljanu na birni hamshak. ayanzu haka wadannan aljanu sun mai da wannan kuba a matsayin abin bautarsu.kuma akwai tsaro a tattare da ita na sihirtattun aljanu masu tsnanin karfin damtse. koda abu saiman yazonan abayaninsa sai ya dada rungume yarima ajikinsa.sannan a sake dubansa yace hakika bincike ya tabbatar mana cewa matarka gimbiya suhaila nada ciki na wata biyu saboda haka kasan yadda zakayi ku takaice wannan tafiya acikin wata goma. yanzu haka na samar muku yan gudun hijira mutun dari hudu da kuma kayan guzurinsu. ba komaine yasa mukayi hakaba face don asami raguwar kashe kashen da za'ayi a wannan yaki.da kuma burin sake kafa wannan birni sabida haka yaune ranar bakin ciki agareni wacce ban taba tunanin zuwanta ba. yanzu bada dadewa ba ina mai umartarku daku kama hanya kutafi aikin dake gabanku. nan take kuwa yasa hannu ya bude wata barauniyar hanya dake kusa da gadon mulki. wata katuwar rijiyace wacce akalla sai mutum dubu sun shiga cikinta kuma wani abin mamaki shine acikin wannan rijiya cike yake da haske yadda ko allura ce ta fadi zaka ganta.bude wannan rijiya keda wuya sai sarki abu saiman ya juyo ya dubi yarima yace acikin wannan rijiya zakuyi ta tafiya har tsawon mako guda inda zaku iso wani daji mai tsananin ban tsoro. da kun iso wannan daji sai ka zare zobenka na sihiri ka cillashi sama to duk hanyar da kaga ya nuna itace hanyar da zata kaiku dajin kurusul saudam sai kubi hanyar.bayan kun dawo daga dajin kurusul saudam sai ka sake cilla zobenka sama.zai sake nuna maka hanyar da zata kaiku dajin ajli. to haka zaku dinga yi aduk wani abu daya shige muku duhu har ku karasa kogon tsafin boka awaisul masawi. sannan yaci gaba da cewa da zarar kakama hanyar tafiya karka sake kace zaka sake juyowa ka kalleni don yin hakan kan iya janyo tarwatsewar shirin mu baki daya. koda yazo nan abyaninsa sai ya daga hannunsa sama ya tafa. faruwar hakan keda wuya sai ga dakaru guda dari dauke da guziri akan dawakai da kuma kuyangi dauke da ginbiya suhaila. sai kuma jama'ar gari maza da mata.lokacin da wadannan dakaru da jama'ar garin ramlatul saif suka suka shigo turakar sarki abu saiman sai dukkansu sukayi sujjada agareshi. sarki ya dubi jama'ar garin yace yaku jama'ar garin ramlatul saif kuyi sani cewa yaune zaku fara tafiya mai tsananin hatsari. saboda haka nake umartarku dakubi duk wani umarni da yarima saiman zai baku idan kuka bishi zaku tsira don munaso ku dawo ku sake kafa wannan birni bayan wasu shekaru masu zuwa.yana zuwa daidai nan abayaninsa sai ya taka da kafafunsa yaje wajen wata akwatin zinareya budeta ya dauko wani gunki wanda aka kerashi da zallan zinare.sannan ya juyo ya bawa yarima ya damka masa ahannunnsa yana mai cewa. wannan gunkine wanda aka kera mai siffata.dama nasa an kerashi ne saboda irin wannan rana.yana zuwa nan azancensa sai ya sake rungume yarima ajikinsa suna masu bankwana. sai bayan dakiku sannan ya sake janye jikinsa daga jikin yarima idanunsa cike da hawaye.nan take ya juyawa yarima saiman baya tare da fadin cewa yanzu haka na umarceka daka gaggauta kama hanya ka tafi aikin dake gabanka don cika burin dake gabannu baki daya.don haka ina gargadinka kada ka sake juyowa da zummar kallona don yin hakangangancine a garemu.yana gama fadin haka sai wani irin hawaye ya zubowa yarima saboda bakin ciki amma bisa dole ya kama hanya ya tafi don cika umarnin mahaifinsa.ma'ana suka shiga cikin wannan rijiya. yarima ne a gaba sannan kuyangi,gimbiya suhaila,mutanen gari.sai dakaru don tabbabtar da tsaro. lokacin dasu yarima saiman suka shiga cikin wannan rijiya sa isarki yajuyo yaje ya sake rufe wannan rijiya. WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR SARKI ABU SAIMAN a can fadar boka ulumanu kuwa yau yana cikin farunciki sakamakon binciken da yayi na rushe birnin ramlatul saif kuma binciken ya tabbatar masa da samun nasara a wannan yaki. dalilin hakanema yasa ya baiwa dakarunsa hutu na jinsin mutane da aljanu don nuna farin cikinsa.don hakane ma ya hada walima afadarsa tsakaninsa da hadimansa.bangaren aljanu daban na mutane daban. abisa karaga kuwa boka ulumanu ne ya zauna bisa karagar mulki yaci ado irin na manyan bokaye. kai wannan fada ta kawatu da kayan alatu sosai.hatta iskar da take kadawa acikinta tatacciyace ba irn wacce aka saba shaka bace. bayan yan dakiku kadan boka ulumanu ya tashi ya fara bayani kamar haka. yaku hadimaina duk cikinku babu wanda baisan burina ba. burin nawa kuwa shine na mallaki na hiyar nan baki daya. Adalilin hakane na shiga bincike,kuma tsafina ya tabbatarmin bazan taba samun nasara ba.har sai naje na yaki wani birni wanda ake kira da ramlatul saif na rusheshi baki dayansa na debe dukiyar kasar. sannan na shiga dakin bautar su in hallaka macijiyar da suke bautawa nasha jininta. da zarar nasha jinin wannan macijiya to awannan lokacinne duk wani boka dake nahiyar nan zai dawo karkashina,saboda babu wanda zai kaini karfin sihiri aduk cikin wannan nahiyar. koda yazo daidai nan a zancensa sai ya juya yayiwa wasu yammata da makada inkiya. nan take kuwa wadannan yna mata suka shiga tsakiyar fada suka fara tikar rawa,su kuwa wadannan makada suka fara kade kade da bushe bushe. nan take kuwa fadar ta cika da hayaniyar mutane da aljanu. bayan wasu yan dakiku sai wasu kuyangi na jinsin mutane da aljanu suka fara debo tulunan giya da kuma kayan abinci suka fara rabawa hadiman gidan. koda wadannan hadimai suka ga wannan abinci sai suka dasa masa wawa hannu baka hannu kwarya sabo da sun dade basu sami abinci kamarsa ba.kai wasuma har faduwa kasa suka dingayi basu saniba saboda tsananin dadin abincin. koda boka ulumanu ya lura da abin dake faruwa sai ya fusata sannan ya dakawa hadiman nasa tsawa,nan take kowanne ya dawo cikin hayyacinsa. sannan yaci gaba da cewa bawai nataraku bane don ku dinga yin shashanci ba,nataraku ne don kutayani farinciki,don haka yanzu zan rubuta wasika naba daya daga cikinku ya kaita fadar sarki abu saiman.sanan ya dawo fadata. nan take boka ulumanu ya bude tafun hannunsa tare da karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku,yin hakan keda wuya sai wata farar takarda ta bayyana ahannunsa,koda bayyanar wannan takarda sai boka ulumanu ya nuna wani aljani mai suna markazulu da wannan ta kardar.nan take wannan takardar t koma hannun wannan aljani.sannan boka ulumanu yace na umarceka daka tafi kakaiwa sarki abu saiman wannan wasika cikin abin da bazai gaza kwana guda da yini daya ba. cikin biyayya markazulu yace angama ya shugabana nan take ya bude fuka fukansa ya luluka cikin srarin samaniya cikin azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya WANNAN SHINE ABIDAYA FARU AFADAR BOKA ULUMANU al'amarin yarima saiman kuwa tun lokacin da suka bar birnin ramlatul saif ta cikin wannan rijiya sai suka wanzu suna tafiya cikin karkashin kasa har suka isa bakin wannan rijiya. sai ganinsu sukayi cikin wani makeken daji mai ban tsoro. daga bayan wannan rijiya kuma wasu ingarmun dawakai ne sunata faman harbin iska. koda su yarima suka tsinci kansu awannan daji duksai suka ji wani tsoro ya darsu a zuciyarsu..yarima saiman ne kadai hankainsa bai tashi ba,kai tsaye ya durfafi inda wadannnan dawakai suke ya zabi daya ya mikawa gimbiya suhaila sannan ya umarci dakarunsa suje su zabi nasu dawakan.nan take suka je babu hayaniya kowa ya zabi guda daya ya hau. bayan kowanne badakare ya hau nasa dokin sai yarima saiman ya umarci jama'ar gari da suma suje su hau nasu dawakan. batare da bata lokaciba suma sukaje suka cika umarni.saida kowa ya zabi nasa dokin sannnan shima yaje ya zabi nasa dokin yahau sanna ya zaburi dokin zuwa gabashin dajin batare da sanin inda ya nufaba. nan da nan suma dakarun suka saki linzaman dawakansu suka bi bayansa cikin tsananin gudu mai tada hankali. hakika alokacin da yarima saiman kejan wannan zuga tasa duk irin halittar da tai karo dashi a wanna lokaci to kwananta ya kare WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU YARIMA SAIMAN BAYAN SUN BARO BIRNIN RAMLATUL SAIF Al'amarin aljani markazulu kuwa bayan ya baro fadar boka ulumanu da nufin kai sako izuwa fadar sarki abu saiman sai ya wanzu yana mai tsala azababben gudu nagaban kwatance har sa'a uku ta shude. kwatsam ba zato ba tsammani sai yaci karo da wani murgujejen dodo mai tsananin muni. kafin markazulu yayi wani yunkuri tuni dodon yasa hannu ya makoshi kasa. nan take kuwa markazulu ya fadi kasa sumamme. koda faduwar markazulu kasa sai wannan dodo yasa hannu ya dauki markazulu ya dorashi akafadarsa sannan ya nufi wani kogon dutse dake tsakiyar dajin cijin tsananin farinciki domin yau shekararsa uku rabon dayaci naman aljani,naman mutane kuwa shekararsa goma sha biyar kullum sai dai yaci naman dabbobi. Lokacin da dodon ya iso bakin kogon nasa sIai ya kwankwasa wata kofa ta bakin karfe,ita dai wannan kofa an sana'anta tane da zallan bakin karfe, fadin ya kai kamu hamsin tsawon kuwa yakai kamu talatin. amma bisa mamaki sai wata yar karamar yarinya ta leko ta wata yar karamar taga. koda taga mahaifinta ya dawo da wani murgujejen aljani akafadar sa sai rugo da gudu tazo ta budewa mahaifin nata kofa tamkar yadda zaka janye murfi daga jikin tulu. nan take wata kara mara dadin ji ta cika dajin baki daya sakamakon bude wannan kofa. ba tare da bata lokaci ba wannan shid ge cikin kogon ya jwo wani kejin bakin karfe ya jefa aljani markazulu ciki ya rufe sannan ya juyo ya dubi yarsa yace yake yata mafi soyuwa agareni ki sani cewa yau nayo farautar da ban taba yin kamarta ba domin wannan aljani yana dag cikin manyan dakarun boka ulumanu wanda ya kashe miki mahaifiyar ki a shekarun da suka gabata kuma ina mai yi miki albishir cewa kece da kanki zaki kashe wannan aljani kisa mafi munin da mukewa halittun da ke doron kasa yadda zamu kunsawa boka ulumanu bakin cikin da bazai taba mantawa da shiba lokacin da dodo shrmanu yazo nan a zancensa sai yarsa samriya ta bushe da dariya har zuwa wasu lokuta sannan tace ya abbana hakika yau kacikan babbab burina koda ban kashe boka ulumanu ba sa'ad da samriya tazo nan a zancenta sai ta mike tsaye cike da farinciki ta shige wani daki dake cikin kogon ta kwanta. kwanciyar samriya keda wuya sai barci ya dauketa. sannan shima dodo sarmanu ya tafi shima ya sami guri ya kwanta nasa barcin don huce gajiyw kash hakika rashin sani ya fi dare duhu inda dodo sarmanu ya san abinda zai faru da baiyi gangacin kwanciya barciba domin ya manta bai dauke makullin kejin dayasa aljani markazulu a ciki ba.kwanciyasa jeda wuya sai wani hadari mai karfi ya ta so nan take aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya. da ike kejin da aljani markazulu yake ciki yana daga bakin tagar kogon sai nantake aljani markazulu ya farfado daga dogon suman da yayi sakamakon ruwan da yake shigow ta cikin tagar lokacin da markazulu ya farfado daga dogon suman da yayi kuma ya ganshi cikin keji sai ya cika da tsananin bakin ciki akan abu biyu. abu na farko shine bai taba tunanin akwai wani acikin duniya da zai iya yi masa irin wannan kamu ba kamr dabba abu na biyu kuma shine mai zai cewa boka ulumanu idan ya koma can fadarsa alhlin sunyi alkawarin zai kai wannan acikin kwna guda da yini daya. koda ya gama wannan tunani sai ya sake cika da bakin ciki mara misaltuwa. kwatsam ba zato ba tsammani sai yayi kicibus da kubar wannan keji da yake ciki koda yaga wannan kuba sai y sake jin murna t akama shi har ta disa sar da bakin cikin da yake ciki. ba tare d bata lokaciba kuwa ya zuro hannu ya dauki wannan kuba ya zura ta a cikin gidanta sannan sannan ya murda nan take kuwa wannan kofa ta bude. nan take marlazulu ya fito daga cikin kejin da yake ciki sannan ya zare takobi ya nufi kan dodo sarmanu kai tsaye ba tare da fargababa ya daga takobin ya caka masa ita acikin ido nan take kuwa dodo sarmanu ya kwalla uban ihu wanda yayi sanadiyar farkawar samriya daga barci koda taji karar mahaifinta sai tayi tsalle ta zare wata sharbebiyar takibi dake jikin bangon kogon ta rugo dq gudu izuwa inda mahaifinta ke kwance kwatsam sai taci karo da gawar mahifinta kwance cikin jini ga kuma bakon aljanin da suka kamo rike da takobi tana yoyon jini.sai ranta yayi matukar tashi nan take ta falfalo da azababben gudu tana mai kwarara uban ihu koda tazo daf da markazulu da nufin tai masa kwaf daya sai aljani markazulu yayi tsalle ya tsallake harin nata nan take aka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwtance tsakanin markazulu da samriya wohoho hakika fadan manyan dawa yayiwa yara nisa domin ana fara wannan yaki samriya ta toshewa markazulu kofofin tsira amma saboda tsananin bakin naci irin na markazulu sai yaki yarda yaje kasa Azahirin gaskiya samriya tafi aljani markazulu karfin damtse shi kuma markazulu yafita juriya naci da iya yaki. samriya ta wanzu tana mai kaiwa markazulu sara da suka ta ko ina. shi kuma ya wanzu yana mai kare saran nata cikin zafin nama.sai da suka sahafe lokuta suna wannan fada kowaya kasa samun nasara akan dan uwan fadansa bisa dole dukkansu suka ja da baya suna masu hararar juna kamar zakaru. daga can sai samriya ta dubi aljani marjazulu tace yakai wannan la'anannen aljani kayi sani cewa yau ka tsokanowa kanka bala'in da ba zaka iya fita ba domin mahaifina daka kashe shine dan autan sarkin dodannin duniya wato dodo garjaju wanda yanzu haka yana can dajin ajali don na tabbata yanzu yasan ka kashe dansa don haka akoda yaushe zai iya turo yan uwan mahaifina domin daukar fansa akanka . koda samriya tazo nan a zancenta sai markazulu ya bushe da dariya sannan yace ke yarinya ki sai wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi domin ni da kike ganina na girmi mahifinki nesa ba kusaba don haka koda yaushe ashirye nake dayin mugun gamo ni da yanuwan mahaifinki koda yazo nan abayaninsa sai ya shammaci samriya ya cilla mata wata allurar sihiri nan take kuwa samriya ta fAdi kasa ma tacciya faruwar hakan keda wuya sai aljani markazulu ya sake bushewa dadariya akaro na biyu sannan ya durfafi kofar kofar fita daga kogon don ya budeta ya fita. koda ya kai hannu da nufin budeta sai yaji tamkar zai dauki duniya saboda tsananin nauyi bisa dole ya saki kofar kogon cikin tsananin ta shin hankalidomin yasan indai yace zai zauna aciki wannan kogo bazai dadeba zai mutu LITTAFIN BAKAR GABA PART 2 TYPING HABIBULLAH KBR Amma sai ya yanke hukuncin yakoma cikin kogon kozaiga makullin kofar kogon. nan take kuwa ya nausa cikin kogon batare da sanin inda ya dosa ba.saida ya wuce yan dakiku yana shige da fuce acikin kogon sannan ya ido wani daki mai dauke da kayan tsafi iri iri.koda isowar markazulu bakin wannan daki sai ya cika fa farincikidomin yasan cewa tabbas zai sami abinda zai taimakeshi ya fita daga wannan kogo acikin wannan daki. nan take yashiga cikin dakin ya hau lalube baji ba gani kwatsam sai yaci karo da wani gurun tsafi acikin wata battar karfe mai dauke da ruwa aciki. Al'amarin dayasa aljani markazulu cikin tsananin mamaki kenan kuma yji tsoro ya darsu azuciyarsa amma daya tuna cewa yana cikin halin rai da mutuwa, ma'ana ko sa'a ko kishiyarta kawai sai yaji ya daina jin tsoron komai acikin zuciyarsa nan take kuwa yasa hannu ya zaro gurun tsafi daga cikn battar ya zura shi ajikin hannunsa na hagu sanna ya daga battar ya zura a bakinsa ya shanye ruwan da yake ciki. nan take kuwa yaji wani gagarumin karfi ya shiga jikinsa wanda bai tabajin kamarsa ba tamkar zai iya nada gammo ya dauki duniya gaba dayanta. koda aljani markazulu yaji sauyin yanayi ajikinsa sai yayanke hukuncin ya debe ragowar kayan tsafin gaba dayansu.bayan ya kwashe kayan tsafin ne sai kuma sai ya juya ya nufi kofar fita daga kogon koda aljani markazulu ya iso bakin kofar kogon sai yasa hannu ya bude kofar kogon tamkar yadda shaho yake daukar dan tsako sannan ya fita daga kogon. koda markazulu ya fito daga kogon sai ya cika da tsananin farin ciki don ganin ya tsira d rayuwarsa bai halaka ba aciki. sannan kuma yaji wani irin girman kai ya shiga jikinsa. nan take kuwa ya daga kansa sama ya fara yiwa kansa kirari yana cewa saini hadari malafar duniya ayaune nacika sunana markazulu kuma ayaune zan addabi duk wani abu mai rai dake doron kasa. kuma daga yau nafi karfin nayi bauta ga kowanne bil'adama dake doron kasa,ballantana ulumanu kaskantaccen boka. sai ni rugugin bala'i saini rijiya gaba dubu saini gobara daga kogi koda yazo daidai nan a kirarinsa sai ya bude fuka fukansa ya tashi sama ya luluka acikin gajimare. ++ ++ ++ ++ ++ wanna shine abindaya faru a kogon dodo sarmanu da aljani markazulu ++ ++ +n+ ++ ++ a can fadar boka ulumanu kuwa yaga duk abindaya faru ga aljani markazulu da dodo sarmanu da irn bakaken magan ganun daya fada masa.saboda haka sai yaji ya tsani markazulu saboda bakaken magan ganun daya fada masa da kuma asarar babban hadiminsa da yayi wanda ya yarda dashi. tabbas yasan cewa yanzu baida karfin sihirin da zai yaki markaulu yanzu saboda sihirin da yake cikin battar karfen dodo sarmanu sihirine mai karfin gaske. don haka sai boka ulumanu ya yanke hukuncin sai bayan ya gama mamaye nahiyar da karfin sihirinsa dana sarauta sannan zai kama aljani markazulu yayita gana masa azaba har sai ya mutu nan take ulumanu ya tashi wani hadimin aljaninsa ya bashi wata wasikar yaki ya aikashi ya kaiwa sarki abu saiman. nan take aljanin ya cika umarni bayan kwana daya aljanin ya fawo da wasikar raddi ya mikawa boka ulumanu. cikin kankanin lokaci baka ulumanu ya fara hada rundunar yakai ta gaban kwatance kai kace duniya zasu yaka. bayan kowanne badakare ya hallara sai boka ulumanu ya daga hannunsa sama yana mai nuni da kowa yayi shiru nan take kuwa gurin yayi tsit kamar mutuwa ce ta gifta bayan shudewar wasu yan lokuta sai ya soma jawabi kamar hak. yaku daukacin hadimaina kuyi sani ayanzu zanfara shirin yakin daban tabayin kamarsa ba atarihin rayuwata. saboda haka ubangiji na ya umarceni na fada muku cewa ni zan barku anan kuyita baiwa kanku horon yaki na tsawon wata guda nikuma zanje kudancin birnin kisra domin na samo wani wanda zai iya kashe macijiyar da birnin zaharul maswur suke bautawa amatsayin ubangijinsu..amma idan d mai tambaya sai yayi. nan take kuwa wani hadimi yada ga hannunsa sama alamar yana da tambaya. sai boka ulumanu ya bashi umarnin yayi tamabayar. sai wannan badakare yce ya shugabana tambaya itace menene abin dogaron shi wanna aljani da zai iya yaki da abar bautar sarki abu saiman? da jin wannan tambaya sai boka ulumanu ya bushe da dariya sannan yace yakai marwan kayi sani cewa shidai wannan aljanj ana kiransa da suna harisula mar'uf kuma baya dogaro da wani karfin sihiri sai wata takobi da yake da ita itace kadai abr dogaronsa. sannana kuma yanada matukar karfin damtse. don a yanzu babu alanin daya kaishi karfin damtse da iya yaki a duk fadin duniyar nan yazu haka harisul maruf yayi rantsuwa akan bazai sake aiki a karkashi kowanne mutumba face wanda ya dawowa da mahaifiyarsa ainihin siffarta daga siffar gunki zuwa ainihin kamarta kuma aduk duniy ni kadaine nakeda sihirin d zan iya wannan aiki. Koda boka ulumanu yazo nan a zancensa sai wani aljani mai suna arman yace ya shugaba na muna so muji tarihin harisu maruf dakuma gwagwarmayar dayasha a rayuwarsa dajin haka sai boka ulumanu yabushe da dariaya sannan yace hakika kunyi mini tambaya mai matukar mahimmanci don haka zanyi kokarin takaice muku tarihin shi wannan sadaukin aljani. nan take ya soma labari kamar haka a wasu shekaru da suka gabata a can kudancin birnin kisra anyi waji sadaukin aljani mai tsananin karfin damtse wanda duniyar sadaukai ta yadda dashi shi dai wannan aljani ana kiransa da suna harisul mar'uf wata rana harisul ya tafi tarauta don samo abinda zasuci shida mahaifiyarsa. koda ya dawo gida sai yayi bakin gamo da abinda ya tsana aduniya. bakomai ya gani ba face mahaifiyarsa mai suna zumaira a kwance akasa kafafunta a nan nade da alama ta zama gurguwa. nan take harisul mar'uf ya ruga da gudu gareta ya dauketa ya dorata akan gadonta na itatuwa. sannan ya dubeta yace yake ummina ki gaggauta fadamini abindaya sameki bayan tafiyata faruta. koda aljana zumaira taji wannan tambaya daga bakin danta aljani harisul mar'uf sai aljana zumaira tace yakai dana bayan tafiyarka sai na wanzu ina mai zaman jiran dawowar ka a wannan waje. ina cikin wannan haline kwatsam sai naga wannan gida da nake ciki ya soma girgiza da kuma wani irin jan hayaki. wanda bansan ta inda yake shigowaba ina cikin wannan haline kawai sai naje kafafuna sun soma nan nadewa.harsaida suka zuke suka koma kanana.yadda bazan iya taka suba. koda tazonan a zancenta sai ta dada fashewa da kuka. lokacin da harisul mar'uf yaji bayanin mahaifiarasa sai sai nan take ya rungumeta akirjinsa tare da fashewa da wani sabon kukan. daga can kuma sai ya janye jikinsa daga nata sannan yace yake ummi na nayi rantsuwa da wannan hawye naki duk wuya duk rintsi sai na samo miki maganin wannan lalura duk wuya duk rintsi. kuma sai na hallaka duk wanda nagano dasa hannunsa acikin wannan aiki. nan take harisul Mar'uf ya bde fuka fukansa ya nausa cikin daji don samowa mahaifiyarsa duk wani kayan amfani da zata bukata na tsawon shekaru dari uku. sannan yayi sallama da mahaifiyarsa ya tafi wajen wani amintaccen bokansa. sai da yayi tafiya sa'a bakwai sannan ya isa bakin kogon garmanu nan take ya saki fuka fukansa ya sauka bisa turba. saukarsa keda wuya sai ya cika da mamaki bakomai yaganiba face boka garmanu fuskarsa cike da fara'a. nan take ya fara yiwa harisul mar'uf kirari yana cewa lale marhaban da sadaukin duniya tarwatsa maza. ajali kake bakasan hakuriba dodo kake mai razana manyan sadaukai duhu kake mai firgita manyan maza afilin daga kabari kake makomar duk wani mahaluki ya sarkin sadaukan duniya. lokacinda boka garmanu yazo nan a kirarinsa sai yace da harisul mar'uf yakai sadaukin zamani kasani cewa bakowane yayi mahaifiyarka wannan sihiriba face sarkin bokayen duniya. wato boka salban sakamakon binciken da yayi a cikin tsafinsa ya nunamai cewa kai kadaine saka iya zame masa matsala acikin al'amuran da yake guda narwa a doron kasa.har kayi yunkurin hanashi saboda hakane yakara tsananta bicike a madubin tsafinsa daga karshe yagano cewa dolene ka shiga sha'anin zaluncinsa muddinsa muddin bai zaunarda mahaifiayrka awaje dayaba. ma'ana ya aika mata da sihirin da zata daina tafiya baki daya. koda boka garmana yanzo nan a zancensa. sai harisul mar'uf yace. to yanzu a ina zansami boka salban na hallakashi don nadauki fansar abinda ya yi mini? dajin wannan tanbaya sai boka garmana ya bushe da dariya kamar bazai daina ba. dagachan kuma saiya tsuke bakinsa kamar an aiko masa da sakon

Chapter 1 of 14