Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne wanda baisan tsoro ba kuma kana da matukar sa'a da rabo adukkan abubuwanda kasa agabanka ni ina da tabbacin duk irin tsananin wahalar da zansha dole zan rayu to amma fargabata akan abu dayane wannan abu kuwa ba komai baneba face rayuwar jama'ar kasar mu aduk lokacin dana tuna da halin da kasar mu take ciki da kuma wasiyyar da mahaifina ya bar mini sai naji gaba daya rayuwar bata mini dadi.. ... koda yazo daidai nan azancensa sai kwalla ta zubo masa don haka sai ya yi shiru ya wuce izuwa tantin da matarsa take koda gimbiya suhaila taga yanayin da yarima saiman ya shigo dashi saita taho da sauri ta ruko hannunsa ta jashi izuwa kan shimfidarta sannan tasa hannu ta share masa hawayensa tace haba yakai mijina gwarzo guda daya tak acikin mazajen duniya ka tuna fa kaine fasa taro kuma sa gudu maganin ki gudu bai kamata karamin abu ya dinga saka gwarzon jarumi kuma uban jarumi kamar ka kwalla ba ka sani cewa komai na rayuwa kaddarace take tafiyar dashi don haka sai kayi kokari ka manta da duk kaddarar data faru abayanka ka tunkari ta gabanka don hakane alamar cika gagara badau k0dajin wannan batu sai yarima saiman ya dago da idanunsa ya dubeta yace haba tayaya kike tunanin zan manta da mahaifata da aka haifeni acikinta? kuma tayaya zan iya mantawa da mahaifina wanda tundaga randa aka haifeni gado daya muke kwana tare dashi har izuwa sanda mahaifiyata ta mutu? wannan abune wanda bazai taba yiwuwaba awajena farinciki na guda daya ne arayuwar nan sannan kuma burina shima guda dayane farincikin nawa kuwa shine samunki amatsayin matar aure domin wannan babbar nasarace agareni burina kuwa shine naga jama'ar mu sun isa kogon awaisul masawi lafiya har ki haifi jarumin d zaizo ya dauki fansar abinda akai mana akan boka ulumanu koda yagama fadin wannan zancen saiya kishingida bayansa ajikin wani matashin kai WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN BAYAN YA SAMI NASARAR MALLAKAR TAKOBIN SIHIRI Acan dajin da dodo garjaju yake kuwa dajine mai matukar ban tsoro irin wanda komai hatsabibancin aljani yana shakkarsa saboda komai na dajin siffar ban tsoro ne dashi fiye da shekara dubu uku baya sawu ya dauke awannan daji mutane da aljanu suka daina shigarsa saboda har ikirari ake masa da dajin mutuwa koma duk duniya sun canfa cewa babu halittar da zata iya shiga wannan daji ta fito araye kai hatta kananun halittu irinsu kuda, cinnaku, sauraye, da kiyasai basa wucewa ta cikin wannan daji wannan daji shine ya zamo duniyar dodannin da suke rayuwa aduniya duk wani sarki mai jida karfin mulki azamanin sa to yana iya aiko da wasikar sihiri wannan nahiya don neman aron dakarun yaki acikin wadannan dodanni idan sarkin dake mulkin wannan nahiya ya yarda amma da zarar sarakuna sun aiko aljani ko bil'adama ko kuma yazo da kansa wannan daji to bai isa ya fita araye ba wannan daliline yasa sarakuna da bokaye suke aikoda wasika kadai ba tareda manzo ba ba kowa ne ke mulkin wannan daji ba face dodo garjaju dodo garjaju ya kasance hatsabibin dodo jarumi kuma sadauki mai tarwatsa maza kuma mai tsananin karfin sihiri duk tsananin jarumtakar jarumi ko kuma sihirin mai sihiri yana matukar shakkar tunkararsa shikadai yana da jarumtakar da zai iya yakar duniya shi kadai bakomai ne yasaka shi kebance kansa awannan daji ba face yayi bincike ya gano cewa bazai taba samun nasarar mulkar duniya ba face ya mallaki kwayar idon bil'adama guda miliyan biyu da kuma na aljanu guda miliyan biyu ya hadasu da tsumin tsafinsa tsawon kwanaki dari da casa'in da tara acikin tukunyar tsafinsa yana dafa su sannan zai sami nasarar mallakar duniya adalilin hakane yayi shiri da kansa da nufin fita farautar bil'adama da aljanu domin cikar burinsa amma koda yazo daidai iyakar wannan daji da suke rayuwa shida dakarunsa da nufin su fita sai sukaji kamar ana watsa musu ruwan dalma bisa dole suka koma cikin daji dodo garjaju ya cikagaba da binciken hanyar daya kamata yabi domin samun biyan bukatar sa acikin binciken nasane ya gano cewa bazai taba samun damar fita daga wannan dajiba shida jama'arsa gabadayaba sai daya daga cikinsu wannan kuwa ba kowa bane face dodo sarmanu wanda shine dan auta ga dodo garjaju koda yagama wannan bincike saiya kwarara uban ihu saboda duk cikin 'ya'yansa babu wanda yakeso sama da sarmanu kuma sarmanu shine mafi rauni acikin 'ya'yansa don haka bayaso abinda zai taba lafiyarsa ko kadan dakyar da sidin goshi ya hakura ya yarda sarmanu ya fito farautar bil'adama da aljanu amma kafin sannan saidaya tsumashi acikin tsumin tsafinsa bayan tafiyar dodo sarmanu kullum sai garjaju ya dauko madubin tsafinsa yaga halinda dansa yake ciki sannan yake samun kwanciyar hankali da nutsuwa aransa to ana cikin wannan hali wata rana dodo garjaju ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi don sanin halinda dansa yake ciki koda ya shafi madubin tsafin saiyaga irin kisan da aljani markazulu yayi masa tareda 'yarsa saiya kwarara uban ihu wanda karar ihun nasane yasa dajin gaba daya ya kama girgiza su kansu dodannin da suke rayuwa awannan daji saida suka shiga tashin hankali domin gaba dayan birnin babu wanda baya tsoronsa wasu atake suka dinga haukacewa wasu kuma suka dinga kurmancewa saboda tsananin karfin ihun nasa koda yagama wannan ihu saiya fashe da kuka sannan ya daga kansa sama yace lallai wannan aljani yayi matukar kuskuren da sai ya yi madamarsa arayuwar sa farinciki na daya ne shine shida kansa zaizo wannan daji shida sabon abokin tafiyar daya samu da zummar diban tsumin tsafina dolene sainayi masa kisan gilla kisan da ba'a taba yiwa wani mahalukiba lallai sai yayi nadamar abinda yayi mini lokacin da yake fadar wannan magana akwai babban dansa awajen wanda ake kira da jurishan koda dodo jurishan yaji maganar mahaifinsa saiya dubeshi yace ya abbana wane irin kisa zakayi musu? dajin haka sai garjaju ya bushe da dariya yace zan kamasu ne gaba daya na tsoma su acikin tsumin tsafi su zama mulmulallu kamar kwallo sannan nasa a ajiyesu ababban fili dodanni suyita bugasu da kafafunsu bayan nan sai na sake mayar dasu sandarar ru dodanni suyita dukansu da manyan bishiyoyi hakadai zanyita canja musu halitta har tsawon kwanaki goma sannan na hallakasu gaba daya koda yagama wannan bayani sai dodo jurishan ya bushe da dariya sannan yace ya abbana lallai wannan hukunci ya dace dasu gaskiya nayi farinciki da haka WANNAN SHINE ABINDA YA FARU ACAN DAJINDA DODO GARJAJU YAKE DAJINDA SHINE WAJE MAFI HATSARI A RAYUWAR DUKKAN HALITTA LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMELITTAFIN BAKAR GABA PART 7 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da suka kadaita acikin tanti shida matarsa sai yarima saiman ya zauna yana ta tunani tsawon yan dakiku sannan ya shafi zoben da yake hannunsa nantake wani dan siririn aljani dan siririn aljani ya bayyana shidai wannan aljanin yakasance dattijo fuskarsa rafkekiyace yana da idanu kwala kwala kuma yakasance mai cikar kwarjini dan gajere koda bayyanar wannan aljani saiya sunkuya yayiwa yarima saiman sujjada sannan yace ya shugabana mai kake da bukata na biyamaka koda jin wannan tambaya sai yarima saiman yace yakai aljani zulkam tundaga lokacin da mahaifina ya damka maka ni ban taba neman wata bukata ba awajenka sai wannan karon idan na tambayeka zaka biya mini ita? kodajin wannan tambayar sai aljani zulkam ya sake rissinawa yace ai ni mai biyayyane agareka don haka ina sauraron duk bukatunka dajin haka sai yace shin kana da masaniya akan dajin ajali da abubuwan dake cikinsa kodajin wannan tambaya sai aljani zulkam ya takarkare ya kwarara uban ihu har yana birgima akasa sannan yace ya shugabana dajin ajali dajine daya zamo kamar kushewa mai cike da masifu da bala'o'i iri iri wadanda suka fi karfin mutum ko aljan su ketaresu kai wannan daji yana da duk wani irin kalar masifa wacce ake gudun shiga cikinta su ya shugabana zaka iya shiga cikin dajin ajali lafiya sakamakon wannan sihirtacciyar takobi daka mallaka amma inda tashin hankalin yake shine shiga cikin fadar dodo garjaju lafiya harka iya debo tsuminsa saboda duk abinda kake takama dashi dodo garjaju ya fika karfin damtse, sihiri, dabarun yaki dodo garjaju ya kasance azzalumin gaske mara tausayi ko kadan yanzu haka aljani markazulu ya kashe daya daga cikin 'ya'yan dodo garjaju saboda haka dole ne ya dana muku mugayen tarkuna wadanda bai zama lallai ku iya wucewa lafiyaaba idan harka sami nasarar shan tsumin tsafinsa to tamkar ka gano lagonsa ne saboda duk irin abinda yake takama dashi to kaima saika sameshi to amma ya shugabana inda matsalar take shine kan aljani markazulu da alama shima yana da bukatar tsumin dodo garjaju ka tuna cewa yanzu haka markazulu ya bujirewa maigidansa boka ulumanu sannan kuma ya kashe daya daga cikin 'ya'yan dodo garjaju shiyasa ya zo wajenka ya rabeka zargin da nakeyi anya kuwa baka ganin akwai wata makarkashiya acikin zuciyar sa? dajin haka sai ya takarkare ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa sannan yace yakai aljani zulkam indai akan maganar aljani markazulu ce karka damu ni nasan yadda zanyi dashi to bukata ta ta biyu itace akan birnin mu na ramlatul saif koda fadin haka sai ya yi nuni da hannunsa izuwa jikin bangon tantin da suke ciki nantake sai hoton birnin ya bayyana da yadda ake ta tafiyar da harkokin yauda kullum da zaman fadar da sarki abu saiman mahaifin yarima saiman ya yi da dukkan 'yan majalisarsa koda gama ganin duk abinda ya faru sai yarima saiman ya juyo yaceda aljani zulkam yanzu haka nasan boka ulumanu ya kusan gama shirye shiryensa akan yadda zai yaki birninmu bincike ya nuna cewa boka ulumanu ne yake da nasara awannan yaki koda kuwa zamu tara dukkan mayakan duniya acikin dakarun mu yanzu haka boka ulumanu ya tafi neman aljani harisul mar'uf wanda shine kadai zai iya hallaka macijiyar macijiyar da muke bautawa to aikin da nakeso kayi mini shine ka taimaki dakarun mahaifina yadda zakuyi boka ulumanu babbar barna acikin wannan yaki saboda wannan yaki zai kasance yakin da ba'a tabayin kamar saba atarihin duniya nasan cewa mahaifina jarumi ne kuma dan jarumai wanda baisan tsoro atarihin rayuwarsa don haka dole kafin ya mutu saiyayiwa boka ulumanu babban tabon da harya mutu bazai baceba daga jikinsa koda jin wannan batu sai aljani zulkam ya bushe da dariya sannan yace indai wannan ce bukatarka karka damu koda gama fadin haka sai ya bace bat kamar bai taba wanzuwaba WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA SAIMAN *** ***** **** **** **** al'amarin boka ulumanu kuwa lokacin daya bace daga cikin jama'arsa bai nufi ko ina ba sai dajin d aljani harisul mar'uf yake rayuwa tamkar kiftawar ido haka ya baiyana agaban harisul mar'uf. alokacin yana gaban mahaifiyarsa wacce take cikin siffar gunki yana ta zubar da hawaye. amma koda ya jiyo motsi sai ya juya bayansa yana mai zare takobi. cikin mamaki sai yaga bil'adama abayansa nantake ya share hawayen dake fuskarsa yadubi boka ulumanu yace. yakai wannan bil'adama menene yakawo ka wannan daji mai matukar hadari alhalin ire iren jinsinku basa iya shigowa cikinsa. dajin haka sai boka ulumanu ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa. sannan yace nine boka ulumanu mai shirin mulkar nahiyarnan baki dayanta yanzu haka nazo wajenka ne don neman taimakonka akan wani shiri da nake son yi ina fatan zaka bani hadinkai dajin haka sai harisul mar'uf ya turbune fuska.sannan yace nayi alkawarin har duniya ta tashi bazan sake bautawa ga wata halittaba har sai lokacin da mahaifiyata ta dawo izuwa ainihin siffarta. kodajin haka sai boka ulumanu yayi murmushi sannan ya nuna mahifiyar harisul mar'uf mai suna zalzila da dan yatsa. nantake kuwa ta dawo izuwa ainihin siffarta. sannan ya dubi harisul mar'uf yace juya kaga abin mamaki. cikin gaggawa sai ya juya,yana juyawa saiyaga mahaifiyarsa azaune tamkar yadda take kafin ayi mata wannan sihiri. nantake ya ruga da gudu domin ya rungumeta.kafin ya karasa sai ta sake komawa zuwa siffar gunki nantake boka ulumanu yasake bushewa da dariya sannan yace da harisul mr'uf kana tunanin zan mayar da mahaifiyarka yadda take batare da kayi mini wani aiki ba, dajin haka sai harisul mar'uf yace yakai wannnan bil'adama me kakeso nayi maka n arantse har da darajar mahaifiyata zanyi maka wannan aiki komai tsananin wahalarsa. boka ulumanu yace yakai wannan hatsabibin aljani inasone kataimaka mini na yaki wani birni da ake kira madinatul saif aikin danake so kayi mini awannan yaki shine ka kashemini macijiyar da suke bautawa amatsayin ubangijinsu. dajin haka sai harisul mar'uf yace tayaya zan amince dakai alhalin ku bokaye baku da amana? sai boka ulumanu yace idan har na yaudareka tsafina saiya daina tasiri domin haka ka'idar sihirina take. sai harisul mar'uf yace shikenan na amince. nantake ya kwanta boka ulumanu ya hau bayamsa sannan ya bude fuka fukansa ya luluka cikin gajimare. WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA ALJANI HARISUL MAR'UF DA BOKA ULUMANU Al'amarin yarima saiman kuwa lokacinda suka rabu da aljani zulkam saiya kishin gida ya kwanta barci domin ya huce gajiyar dake tare dashi aikuwa nantake sai barci ya saceshi bai sani ba koda gimbiya suhaila taga ya kwanta barci sai itama ta sami waje ta kwanta itama ta kamayin barci basu farka ba sai bayan gari yayi haske sannan suka farka gimbiya suhaila ce ta fara farkawa don haka saita tashi yarima daga barcin yana farkawa saiya dubi tagar dakin yaga hasken rana koda ganin haka sai yayi sauri ya fito daga cikin tantin ya fara duba jama'arsa koda ya fito wajen tantin saiyaga dukkan su sun gama yin shirin tafiya sunci kalacinsu su kawai ake jira suci nasu sannan aci gaba da tafiya koda ganin haka sai yarima ya dawo cikin tantinsa awannan lokaci tuni wata kuyanga ta kawo abinci da abin sha ta ajiye nantake yarima da gimbiya suhaila suka kimtsa cikinsu suka sha ruwa sannan yarima ya mayarda kayan yakinsa jikinsa sannan ya nufo kofa da nufin ya fita bazato ba tsammani saiyaji an ruko hannunsa ta baya koda juyowa saiyaga ashe gimbiya suhaila ce ta rukoshi tana murmurshi sannan tace yakai mijina karka mantafa idan ka fita daga wannan tantin bai zama lallai ba mu sake haduwa dakaiba sai rana ta fadi kuma zuciyata zata kasance cikin kewarka da begenka awannan lokaci don haka inaso kayi mini wani abu wanda zai rage mini zugin rashinka akusa dani kodajin haka sai yarima ya buda hannayensa biyu ya rungume gimbiya suhaila tareda sumbatarta agoshi sannan yace yake tauraruwar datake haske acikin zuciyata ki sani cewa tun daga ranar dana fara ganin ki da idanuna na kamu da sonki ban taba yin koda dakika dayaba ba tareda tunaninki ba, ki sani cewa kece bugun zuciyata duk numfashin da yake fita daga cikin hancina sakamakon bugun zuciyata yana fitane tareda furta sunanki saboda burin ganinki ne ma yasa idan munje wucewa ta wani birnin agaban mu zan tsaya na saya miki keken doki domin ki dinga kasancewa atare dani kodajin wannan magana sai wani hawaye mai zafi ya zubo daga cikin idanun gimbiya suhaila sannan ta sakeshi ya fita daga cikin tantin ya nufi inda dakarunsa suke koda sukaga yarima saiman ya fito sai suka dare suna masuyi masa jinjina da kirari yarima saiman ya matsa gabansu ya tsaya sannan yace yaku ahalin birnin ramlatul saif ku sani cewa a yaune zamu doshi dajin da yake gaban mu wanda akewa lakabi da dajin mutuwa amma kafin mu isa dajin zamu wuce ta gaban wani birni agaban mu wanda akewa lakabi da askandariya birnin askandariya birninine wanda ya sha hara afannin kira kayanda suke kerawa kayane masu inganci don haka awannan abakin wannan birnin zamu rabuda shugaban dakaruna. wato zamnas ya shiga wannan birni don samo keken dokin da za'asa gimbiya suhaila aciki koda gama fadin hakan sai yarima saiman kama dokinsa ya hau sannan ya cire zobensa daga hannunsa ya cillashi sama nantake wani farin haske ya fito daga cikin zoben ya nuna kudancin wamda hakan yana nufin nan ne hanyarda zata kaisu dajin ajali sannan ya dake rikida ya koma zobe zoben ya shiga jikin hannunsa ba tareda bata lokaci ba suka sake tattara kayansu suka sake shiga cikin dajin yarima saiman ne agaba tawagarsa suna tare dashi LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME AKAR GABA PART 8 LBR HABIBULLAH Ҡცř TYPING HABIBULLAH KBR lokacinda suka zaburi dawakansu suna masu tsala azababben gudu sai abin ya zama abin sha'awa kuma abin al'ajabi domin cikin lokaci kankani suka dinga shafe doguwar tafiya acikin kankanin lokaci tamkar basu kasance mutane ba aljanu ne ba komaine yasa hakan ba face tsananin karfin sihirin da yarima saiman ya dinga amfani dashine ya jawo haka saboda bashida burin da yafi yaga ya shiga dajin ajali ya debo tsumin dodo garjaju sannan yaje fadar sarkin aljanu ya sato makullin kofar kogon darul sihir domin tsira daga sharrin boka ulumanu haka suka dinga kutsawa cikin dazuzzuka masu matukar hatsari amma cikin kankanin lokaci yarima saiman yake gamawa dasu komai tsananin yawansu saida suka shafe kwanaki biyar suna tafiya basa tsayawa sai idan lokacin cin abinci yayi sannan ake tsayawa kowa yaci yasha wanda kuma yakeda wata bukata saiya tsaya yayi sannan atashi aci gaba da tafiya akwana na biyar dinne suka iso bakin wata mararrabar hanya wacce ta rabu kaso biyu kaso na daya ya nufi kudancin dajin daya kuma kason ya nufi arewa koda sukazo daidai wannan waje sai yarima saiman ya ja linzamin dokinsa ya tsaya nantake kuwa kowa ya tsayar da nasa dokin ana jiran aji mai yarima saiman zaice koda kowa ya gama nutsuwa sai yarima saiman yace yaku ahalin birnin ramlatul saif nan ne mararrabar hanyarda zamu rabu daku domin daga nan inda nake tafiyace ta sa'a uku da rabi zuwa dajin ajali anan zamuyi bankwana daku ni na tafi aikin dake gabana koda yazo daidai nan azancensa saiya kwallawa jarumi zamnal kira nantake kuwa zamnal ya fito gabansa ya tsaya yana mai rissinawa yarima saiman yace yakai zamnal yanzu zan baka kudi ka tafi izuwa birnin askandariya inaso ne idan kaje kasan kalar dabarar da zakayi ka shiga cikin wannan birni duk yadda za'ayi kada ka bari mutane kasar su san cewa kai dan birnin ramlatul saif ne dakai da dakarun da suke tareda kai inaso ku je ku dawo da wuri ku tadda jama'armu awannan sansanin sannan ku jiramu idan kuma mune muka riga ku dawowa zamu jiraku anan wajen koda yazo nan azancensa saiya zabo wasu dakaru guda ashirin sannan ya dauko dukiya ya basu yace idan kuka shiga cikin birnin askandariya inaso ne ku shiga kasuwar birnin ku nemi gidan sarkin makera na wannan birni ya nuna muku irin kalar kirar keken dokin da sukeyi da kuma wanda yafi kowanne kwari sai kuyi cinikinsa ku dawo kada ku bari ashaida ko su waye ku nantake ya nuna musu hanyar da tayi kudancin dajin sannan yace wannan itace hanyar da zaku bi don shiga birnin askandariya da wannan furuci nake umartarku daku kama hanya ku tafi aikindake gaban ku kodajin haka sai wadannan dakarun suka rissina sukace angama ya shugabana nantake suka kama hanya suka nufi birnin askandariya cikin azababben gudu bayan tafiyarsu sai yarima saiman ya runtse idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai wani dan karamin gari ya bayyana shidai wannan gari girmansa bai wuce na unguwa guda ba koda bayyanr wannan gari sai yarima saiman ya umarce su da gaba dayansu su shiga ciki shigarsu keda wuya sai kofar birnin ta kulle kanta sannan ya sake ce dasu wannan gari wajene mai matukar sirri da kwanciyar hankali zaku zauna acikinsa har izuwa sanda zan dawo babu wanda zai iya ganin wannan gari sai dan kabilar mu komai karfin sihirin mutum kuwa don haka kada ku kuskura ku bude wannan kofa sai kunji ana kwankwasata to da zarar kunji haka to nine ko kuma su jarumi zamnal yana zuwa nan azancensa saiya juya ya nufi kofar fita daga cikin birnin ba zato ba tsammani saiyaji ana kwalla masa kira ba kowa bane ba face gimbiya suhaila nantake ta rugo gareshi ta rungume shi tana cewa akan wanne dalili zaka tafi ka barni ka sani fa kaine kadai burina arayuwa idan ka mutu babu shakka nima saina mutu saboda sonka ne zai zamo sanadiyar ajalina kodajin haka sai jikin yarima saiman yayi sanyi sannan ya dago da fuskarta suna kallon juna sannan yace akan wanne dalili zan mutu na barki alhalin banga dana da yake cikin cikinki ba sannan kuma ban cika mafarkin da mahaifina ya dade yanayi ba dangane da rayuwar da samar anan gaba ba ina tabbatar miki da cewa koda zan mutu sai bayan mun isa kogon tsafin boka awaisul masawi lafiya yana zuwa daidai nan azancensa saiya hura mata wata iska daga cikin bakinsa faruwar hakan keda wuya sai wani irin nan nauyan barci ya dauketa koda faruwar hakan sai ya kira wasu kuyanginta yace su dauketa su kaita cikin turaka nantake kuwa kuyangin suka cika umarni tafiyar kuyangin keda wuya sai yarima saiman ya ratsa wannan kofar birnin ya fita daga cikinta kamar yadda ruwa yake ratsa kasa ya fice bai bayyanaba sai abakin kofar birnin da tazarar tafiyar da bata wuce taku hamsin ba koda bayyanarsa a wannan waje sai ya bude bakinsa ya kwallawa aljani markazulu kira faruwar hakan keda wuya sai wata irin iska mai karfin gaske ta fara kadawa cikin dakiku kadan saiga aljani markazulu ya bayyana bayyanarsa keda wuya sai ya dubi yarima saiman yace ai tun daga sanda muka rabu dakai ina tare dakai batareda ka sani ba duk inda ka shiga ina biye dakai amma banda waje daya wannan guri kuwa shine cikin tantin da kuka zauna kaida matarka babu yadda banyiba akan na shiga ciki ba amma na kasa shiga ko naji abin da kuka tattauna acikin sa kodajin haka sai yarima saiman ya bushe da dariya sannan yace to kai atunaninka bansan da haka bane? kamar yadda kake kallona haka nima nake kallonka abinda yasa kuwa ka kasa shiga cikin tantina shine nine nayi amfani da karfin sihirina na hanaka shiga cikinsa ko kaji abinda muke tattaunawa da ita kuma babu wanda ya isa ya iya shiga cikin wannan tantin nawa awannan lokaci face boka ulumanu saboda shima yana da irin wannan sihirin koda yarima saiman ya zo nan azancensa sai jikin aljani markazulu yayi sanyi ya tabbatar da cewa lallai yarima saiman ya sha kansa abangaren karfin sihiri don haka sai ya dakatar da wannan maganar don gudun kar ya gane abinda yake cikin zuciyar sa sannan yace ya kai abokin tafiya ta to ta wacce hanya kake ganin zamu shiga cikin dajin ajali har mu debo tsumin dodo garjaju? koda jin wannan tambayar sai yarima yayi murmurshi sannan yace lallai baka san ko waye dodo garjaju ba duk abinda kake takama dashi to dodo garjaju ya sha kanka abinda nakeso dakai kawai shine ka zamo mai juriya acikin duk wahalar da zamu fada ccikinta koda gama fadin haka sai ya ya kama hanyar shiga dajin ajali gadan gadan batareda fargabar komaiba koda ganin haka sai aljani markazulu ya bi bayansa da sauri saida sukayi tafiyar sama da sa'a uku sannan suka iso kusa da iyakar dajin aajali koda sukazo daidai wannan guri duk sai suka cak yarima saiman ya dubi markazulu yace ba zamu shiga cikin wannan dajinba kai tsaye dolene muyi amfani da karfin sihirin mu don mu isa karshen wannan dajin da wuri ba tareda an farga da zuwanmu ba abin da zamuyi kuwa shine duk mu biyun zamu rikide mu koma siffar kibiya sannan mu cilla kanmu cikin tsananin gudu duk abinda kuwa ya shiga gabanmu to mu hudashi mu wuce koda kuwa ginine koda jin haka sai aljani markazulu ya bushe da dariya domin shi azatonsa yarima saiman wasa yakeyi haryana birgima da kasa koda ganin haka sai ran yarima saiman ya baci nantake ya soma karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai duk su biyun suka rikide suka zama kibiyoyin bakin karfe sannan kibiyoyin suka cilla kansu suka tashi sama suna masu falfala azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya haka suka dinga gudu acikin sararin samaniya duk abinda suka tarar agabansu nan take suka dinga hudasu komai kwarinsa koda kuwa ya kasance karfene koda dodannin suka lura da abinda ke faruwa sai suka taho gaba dayansu suka dinga kawowa kibiyoyin sara amma kafin ya sauka ajikin kibiyar saikaga sun wuce da gani tamkar anyi ruwa an dauke nan da nan suka dinga huda kirajen dodannin suna wucewa da karfin tsiya kafin cikar 'yan dakiku sun iso inda gidan sarautar wadannan dodannin yake ba zato ba tsammani sai sukaji ansa kafa an buga su da ita nantake duk kibiyoyin biyun suka ja da baya kamar an janyesu da majajjawa saboda karfin dukan da akayi musu suka je suka gwaro da wani dutse nantake duk su biyun suka dawo izuwa ainihin siffarsu lokacinda suka ji kamar an balla kashushuwan bayansu lokaci guda suka dago kawunansu domin suga wanda yayi musu wannan mummuna duka bakowa baneba face dodo garjaju shidai garjaju yakasance babbar halitta mai matukar tsawo da kauri idan suka kalli tsawonsa sai suga kamar ya hade da sararin samaniya tsawon hannunsa kowanne guda daya yakai tsawon babbar bishiyar dabino kaurinsa kuwa yafi kaurin katuwar bishiyar kuka yana da jajayen idanu kamar an gasa dan buda awuta kai duk inda siffar jarumta da kuma rashin imani takai to dodo garjaju ya wuce wannan siffa sai abinda idanu suka gani akansa nantake ya tsaya ya karewa su yarima saiman kallo atsanake sannan ya bushe da dariya yace yaku wadannan kananun halittu yan da wannan kankanuwar jarumtakar taku kuke tunanin har zaku iya fadata domin diban tsumin tsafina? lallai tsafinku ya yaudareku tunda har ya turo ku inda ajalinku zai riskeku tunda sauran kuruciyarku kodajin haka sai yarima saiman ya daka masa tsawa yana mai cewa kai tsohon azzalumi karyarka tasha karya kai waye da har kake tunanin zaka hana mu biyan bukatar mu? ka sani zalunci baya taba dorewa don haka karshen zaluncinka ne yazo ayau dinnan wannan ce ma silar da tasa muka shigo cikin wannan daji na rantse da abin bautana bazan fita daga cikin dajin nan ba harsai na debi tsumin tsafinka koda kuwa ban sami nasarar hallaka ba kodajin wannan batu sai dodo garjaju ya bushe da dariya sannan yace kai yaro lallai maganar ka ta burgeni da kuma izzar da kake da ita don haka zanso na gwada jarumtakar ka akan ta dakaruna domin naga iyakar jarumtakar da har kake takama da ita koda gama fadin hakan sai ya umarci wasu zaratan dakarunsa dasu kamo masa su yarima saiman nantake kuwa dakarun suka afka musu aka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance fara yakin keda wuya sai suka tashi kura ta cika dajin har bama ka

Chapter 4 of 14