Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bakinta da niyyar kafasu a jikin wuyan mubnaika ba zato ba tsammani sai macijiyar taji an daka mata tsawa daga bayanta cikin tsananin mamaki saita tsaya cak ta fasa yin mugun abinda tayi niyyar aikatawa ta juyo domin taga wane mai tsaurin idon ne yake yi mata wannan tsawar ba kowa baneba face wani kyakykyawan saurayi mai suffa da shiga irin ta mutanen daular larabawa rataye da wata sharbebiyar takobi da kuma kwari da baka abayansa mubnaika ma da take kwance saita juyo da fuskarta ahankali don taga abin dake faruwa koda taga wannan kyakykyawan saurayi sai yaji nan take zuciyarta ta buga da karfin gaske kamar zata fasa kirjinta ta fito waje kuma wannan ne karon farko data fara jin irin wannan yanayi ajikinta ba komai ya janyo mata hakaba face ganin wannan kyakykyawan saurayi wanda yake tsaye abayan wannan macijiya kai da gani kasan cewa ya cika jarumi na gani na fada mai tarwatsa maza kuma afagen kyau kuwa ko acikin mata asami mace mai kyan sama sai an bincika ga shin kansa kuwa ya sauka har gadon bayansa idan ka ganshi saika zata cewa ya fito daga wani babban gida sarautar ne fatar jikinsa kuwa tamkar ta jariri wajen sheki da walwali kai duk inda kyau yakai wannan saurayi LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA PART 20 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Nan take mubnaika ta kurawa wannan saurayin ido ko kiftawa ma ta kasayi sai gani tayi ya dako tsalle daga inda yake ya bayyana tsulum agaban wannan macijiyar itama macijiyar saita juya ta fuskance shi suka kachame da sabon azababben yaki mai cike da razanarwa nan take mubnaika ta raina kanta a fannin jarumtaka ta sallamawa wannan kyakykyawan saurayi domin ta fahimci cewa ruwa ba sa'an kwando bane saboda ta gani da idanunta cewa duk sanda wannan bakon jarumi ya sami nasarar sarar jikin macijiyar da takobinsa duk da cewa takobin bata tasiri ajikinta sai taga macijiyar ta kwallara ihu saboda tsananin zafi da radadin da yake ratsa cikin tsokarta da kuma jijiyoyinta har saida aka shafe dakiku dari biyu amma macijiyar bata sami nasara akan wannan saurayin ba saboda tsananin zafin namansa da ulliyarsa har saida takai cewa kogon ya fara tsattsagewa yana ruguzowa kasa yana danne abubuwan da suke kwance akasa kuma har a wannan lokacin mubnaika tana kwance a kasa ba zata iya mikewa tsaye ba saboda buguwar da tayi koda bakon jarumi ya fuskanci cewa idan har baizo ya dauketa ba to tabbas za'a iya samun akasi wani dutsen yazo ya danne ta ta mutu koda gama yin wannan tunanin sai nan take ya shammaci macijiyar ya sannan ya daka tsalle ya gabzawa macijiyar naushi acikin kwayar idonta guda daya sannan ya sake yin wani tsallen a saman ya dira a inda mubnaika take kwance ya shureta ya azata agadon bayansa ya daure. ta Tamau da wani rawaninsa a wannan lokacin macijiyar tana ta matagugu sakamakon tsananin zafi da zugin da take ji sannan macijiyar ta fara rikida sannu ahankali ta rikide ta zama wata mummunar aljana mai matukar ban tsoro amma babu ido guda daya sai kurmin ido wanda yake zubar da jini cikin karaji da kururuwa aljanar ta nufo shi gadan gadan cike da mummunan nufi domin ta kamashi tayi gunduwa gunduwa dashi koda ta kawo masa cafka da hannunta sai ya daka tsalle sama ya kaucewa harin nata ta cafki iska cikin zafin nama ya kai mata wani wawan sara da takobinsa koda takobin ta hadu da hannunta sai wata kara ta tashi kamar ta haduwar karfe da karfe nan take ta dinga kawo masa mahaukatan hare hare da nufin ta kamashi ta tsinkashi biyu amma sai abu ya gagareta saboda tsananin zafin namansa da kuma karfin gudunsa ta kasa samun damar chafkeshi domin wani lokacin idan yayi tsalle sai kaganshi kamar tsuntsu mai fuka fuki saboda karfin tsallen nasa domin yaki yarda ta ritsashi awaje guda saboda yasan indai ya bari haka ta faru tasa ta kare babu abinda zai baka mamaki face cewa duk wannan gumurzu da akeyi akwai mutum agoye abayansa saida ya zamana sun rushe kogon gaba daya saboda gumurzun da suke yi ya zamana cewa guri ya zama filine fetal kuma har sannan babu wanda ya sami nasara akan wani domin jikin aljanar gaba daya makami baya hawa sai sannan bakon jarumin ya fuskanci cewa acikin idonta ne kawai makasarta yake saboda haka dolene ya dinga kaiwa idonta farmaki ita kuwa koda ta fuskanci manufarsa sai taki ta bashi damar yin hakan daga can saita sami nasara ta yanki kafarsa guda ta dama da kaifin facenta harsaida jini yayi tsartuwa daga jikin kafar tasa sannan ta shureshi da hannunta ta dagashi sama tayi jifa dashi harsaida ya fadi can nesa da rufda ciki sannan tayi tsalle guda daya ta bayyana a inda yake ta sake shurarsa ta sake yin jifa dashi akaro na biyu amma sai jarumin ya juya jikinsa yaki yarda ya fadi kasa ya dira a tsakiyar kanta sannan yasa takobi ya caka mata acikin ragowar idon nata nan take jini yayi fashe daga cikin idon nata cikin zafin nama ya kara daka tsalle daga kanta ya dira akasa sannan ya falafala da azababben gudu alokacinda itakuma ta haukace da kawo masa mugayen hare hare domin awannan lokaci bataji kuma bata gani don haka duk inda taga dama kai farmaki takeyi saboda taga ta sami nasara akansa cikin kankanin lokaci ya bar wannan waje itakuma tayita magagin mutuwa har saida ta mutu saida ya tabbata ta mutu sannan ya sami waje y ajiye mubnaika wacce awannan lokaci tayi doguwar suma sannan yaje ya tsinko wata siririyar jijiyar bishiya bushashshiya ya dinke raunin dake jikin kafar tasa sannan ya zuba wani garin magani akan raunin kafar tasa bayan ya gama da raunin jikinsa ne ya sake juyawa kan mubnaika koda ya kalleta awannan lokaci sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske tamkar zata tsaga kirjinsa ya fito ba komai ya haddasa hakaba face sai asannan ne ya kula da tsananin kyawun da allah ya bata tamkar itace tayi kanta atsawon yawon da yayi aduniya ya hadu da mata kala kala amma bai taba cin karo da mace mai kyawunta ba kuma gata jaruma tabbas wannan kyakykyawar budurwa ta kasance 'yar baiwa irin wacce yake da burin samu amatsayin matarsa nantake ya dauketa ya dora akan cinyarsa ya kura mata ido sannan ya dauko ruwa acikin battarsa ya zuba mata afuskarta take ta farfado daga suman da tayi ahankali ta bude idanunta koda tayi arba da shi sai ta zaune zumbur ta na mai kallon fuskarsa cikin rashin yadda tace kai wanene ? kuma me ka aikata mini? ka gaggauta sanar dani gaskiya inba hakaba na yakeka harsaina hallaka ka ko kuma ka hallaka nice dajin haka sai ya bushe da dariya yayi ta yi kamar bazai dainaba sannan ya kalleta yace yake wannan kyakykyawar budurwa me kike zaton na aikata agareki inbanda abinda duk wani da namiji mai lafiya zaiyi idan yayi arba da wannan kyakykyawar surar jikin naki koda jin haka sai mubnaika ta fusata tazare wata gajeriyar adda a kugunta ta kawo masa wani mummunan sara da nufin ta tsarga kansa gida biyu take jarumin ya sunkuya ta sari iska LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME DOMIN SAMUN CIGABAN SAI KU KASANCE DA SHAFIN HAUSAEBOOKS.COM.NG BAKAR GABA Kashi na biyar 5 Littafin Habibullah Muhammad kabara Ebook created by Shuraih Usman Published at http://Hausa brooks com.ng BAKAR GABA PART 21 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Cikin zafin nama shima ya zare tasa takobin ya mike tsaye tsam yana kallonta yana murmushi take ta sake afkowa kansa cikin mugun nufi tana kawo masa mugayen hare hare tamkar tsofaffin abokan gaba shi kuwa sai ya kasance yana mai kare harin nata fuskarsa cike da murmushi wanda yasa mubnaika ta kasa tantance wanne irin murmushi yake yi mata shin murmushin mugunta ne ko kuma na raini ne saboda yana ganin kamar ba zata sami nasara akansa ba? wannan shine tambayar data ayyana acikin zuciyarta sannan tayi kwafa aranta tace lallai dan saurayi ka yaudari kanka domin dan hakkin daka raina shine yake tsone maka ido yau saina baka mamaki tana gama ayyana hakan sai ta daka wani mahaukacin tsalle sama ta sake kai masa wani mahaukacin saran da nufin ta tsarge bayansa inbadon ya sa takobinsa ya kare ba ya kare da tuni ta aiwatar da nufin dake cikin zuciyarta da ganin haka sai shima ya sake yin wani tsallen ya koma baya chan taku goma sannan ya kalli mubnaika cikin wani irin tattausan murmushi yace tabbas na yarda ke jaruma ce amma ina mai shawartarki daki sake zage damtse idan har kinaso ki aiwatar da nufinki akaina don huce fushin abinda na aikata agareki kafin ya gama rufe bakisa ta sake daka tsalle asama kawo masa wani harin cikin zafin nama yasa hannayensa guda biyu ya daki kafafunta dasu take ta rikito kasa mai makon jarumin yaje shi ya kasheta tunda tayi yunkurin kashe shi sai taga ya mika mata hannu fuskarsa cike da kwalla don ta kama ta tashi tsaye nantake kuwa ta kama hannun nasa tana mikewa tsaye sai ta shammace ta kai masa wani suka acikinsa cikin bakin zafin nama ya juya ta soki iska sannan yasa hannu ya rike ta baya da hannun sa hagu hannun sa na dama kuwa sai ya ritsata da takobi yadda ba zata iya kwacewa ba yace haba yake wannan kyakykyawar budurwa saboda me kike burin ki hallaka wanda ya zo gareki da alheri koma dai wanne irin laifi na aikata miki ai ya kamata ki gafarta mini saboda ceton rayuwarki da nayi a hannun wannan hatsabibiyar aljana dajin wannan maganar sai jikin ta yayi sanyi ta saki addar ta kasa sannan ta juyo itama ta kalli wannan jarumin lokacin da taji kunya ta kamata kanta a sunkuye cike dajin kunya tace yakai wannan bakon jarumi kayi hakuri abisa abinda ya faru nida kai tsananin bakin ciki ne bisa zargin cewa ka lalata mini rayuwa alokacinda nake cikin halin suma ne yasa nayi maka haka amma sai yanzu na fahimci cewa zargin da nake akanka ba gaskiya bane amma ka sani bani kadai ba dukkan wata mace idan irin wannan abu ya sameta dolene tayi yunkurin daukar fansa. sannan kuma ina mai godiya agareka bisa taimakon da kayi mini ka ceci rayuwata daga wannan shu'umar aljana kai kuwa wanene kai kuma menene ya kawoka wannan daji mai hatsarin gaske? dajin wannan tambaya sai bakon jarumin yayi murmushi sannan yace ni sunana marwan kuma bakone ni a wannan nahiyar hanyace ta kawo ni nan zan wuce domin gabatar da sana'a ta ta farauta sai na zo giftawa ta bakin wannan kogon dutsen na tarar da bakin gumurzun da kukeyi ke da wannan aljana na dade a tsaye ina kallon yanayin fadanki kuma nayi matukar jinjina miki domin kin cika basadaukiya kuma jarumar jarumai wacce ta chanchanci ajinjina mata amma kuma sai naga an sami akasi macijiyar tana nema tayi nasara akanki wannan daliline yasa na bayyana kaina agareta na hanata aiwatar da mummunan nufinta akan kyakykyawar budurwa kamarki dajin haka sai mubnaika ta tari bakinsa tace kada ka fadi haka domin kaine jarumin jarumai kuma gagara badau saboda duk abinda ka fada akaina ka fini kyau, karfin damtse da iya yaki gaskiya dole ne na jinjina maka kaima nan take ta mika masa hannunsa suka gaisa sannan tayi masa murmushi tace nikuma sunana mubnaika sana'ar farautace ta shigo dani cikin wannan daji duk da cewa ban sami abinda nazo nema ba ina mai matukar farinciki bisa samun abinda zai maye mini gurbin abinda nazo nema wannan nasarar kuwa da nayi bata komai bace ba face ta samun abokin da zan dinga ganin haskensa acikin zuciyata wanda zai dinga maye mini gurbin duk wani abu wanda na rasa arayuwata kuma shine zai zamo fitila agareni wannan abu kuwa ba komai bane ba face kai nan take ta tsugunna akasa bisa gwiwoyinta tace ni tabbas na yarda dakai na yarda kai mutumin kirki ne zaka iya rikeni amana ina fatan zaka yarda ka bani soyayyarka kamar yadda nima nake nuna maka tawa soyayyar azahiri na cire kunya da girmankai irin namu na 'ya'ya mata idan har ka yarda dani to nayi maka alkawarin ko mutuwa bata isa ta raba ni dakai ba koda jin wadannan kalamai na jaruma mubnaika sai nan take jarumi marwan yaji kamar an zare masa lakar jikinsa ya kame kyam atsaye kamar gunki sai wani siririn hawaye da ya digo daga cikin kwayar idanunsa jikinsa ya fara karkarwa kamar mai jin sanyi ba komai ya haddasa haka ba face jin dadadan kalaman soyayya daga bakin mubnaika kawai sai ya rungume mubnaika yace mene zaisa na ki yarda da wannan kyakykyawan tayi da kikayi mini hakika nayi farinciki da kika shigo rayuwata yake mubnaika tun kafin ki furta mini soyayya zuciyata ta tafi cikin shaukin begenki tabbas na yarda soyayya ta kan iya mayar da mutum biyu su zama daya idan har kuwa hakane to dani dake mun zama daya zuciyata ta zama tsagin zuciyarki haka kema taki zuciyar rayuwata kuwa daga lokaci zata kasance cikin tunaninki tabbas na tsinci soyayya adaidai lokacin daya dace kuma koda zan tsinci wata to ina yi miki rantsuwa bazan dauketa ba kece zaki zama abokiyar rayuwata ta har abada daga wannan lokaci shida mubnaika suka zama masoyan juna kuma suka shaku sosai duk farautar da zasuje tareda suke zuwa bayan 'yan kwanaki kadan sai suka yanke hukuncin yin aure domin samun dorewar soyayyarsu nandai marwan ya tambayeta akan me take bukata amatsayin sadakin aurenta dajin wannan tambaya sai mubnaika tayi dariya sannan tace ai sadakin zaratan masoya guda biyu kamar mu dolene ya zama abu mai matukar wahalar samu domin ranar aurenmu ta zama abar tunawa agaremu cikin murmushi ya kalleta yace me kike da bukata nayi rantsuwa da girman soyayyata agareki ko menene sai na kawo miki indai akwaishi acikin duniyar nan sai na kawo miki shi mubnaika tace abinda nake bukata agareka kawai shine ka samo mini kan dabbar da tafi kowacce dabba girma acikin dajin nan idan har kayi haka to tabbas ka zama mijina dajin haka sai marwan yayi murmushi yace indai wannan ne karki damu ki bani sa'a biyar zanje na dawo nantake kuwa ya debi kayan fadansa ya daura su ajikinsa sannan ya kalleta cike da alamar bege yace na rantse harda soyayyar da kike yi mini idan na fita sai nayi nasara koda kuwa abinda zan farauto miki yafi karfina domin shi karfin soyayya yafi karfin damtse tasiri acikin zuciyar masoya wannan shine dalilin da yasa na tabbatar miki da cewa saina sami nasara yana gama fadin haka sai ya falfala da azababben gudu na gaban kwatance wanda saida ya baiwa mubnaika mamaki saboda yanzu ne ta gane cewa tabbas tayi dacen masoyi domin marwan ya tara duk wata baiwa da mace take bukata gashi kyakykyawa kuma jarumi sannan ga kuma karfin gudu cikin lokaci kankani ya bace mata da gani haka dai marwan yayi ta yawo a cikin dajin yana haduwa da manyan namun daji amma abin mamaki shine duk irin dabbar da ya hadu da ita sai yaga taki ta kawo masa farmaki hasalima saidai yaga ta juya baya aguje don ceton rayuwarta abinda bai sani ba shine duk dabbobin da suke cikin dajin sun jiyo sanda yake fafata yaki da wannan aljanar kuma sun jiyo karar ihunta a lokacin da ya kasheta shine dalilin da yasa suke tsoron rabarsa wannan shine damar da ya samu ya dinga bin dabbobin daya bayan daya yana nazarinsu amma bai sami wata dabba ba wacce yake ganin ta cancanci ta. zama sadakin aurensa da mubnaika ba don haka sai ya yanke shawarar ya kara kutsawa yaje har karshen dajin koda gama wannan tunanin sai ya kara falfalawa da gudun tsiya bai tsaya ba saida yazo bakin gabar wani katon teku wanda gabarsa ta biyo ta cikin dajin ga igiyar ruwa nan tanata kadawa har wani tsiri takeyi acikin sararin samaniya babu hanyar da zakabi ka wuce face ka ratsa ta cikin tekun koda yayi arba da wannan teku sai ya tsaya cak shi baiyi gaba ba kuma baiyi baya ba yana tunanin me ya kamata yayi shin ya koma cikin dajin ne ya farauci dabbar data samu ya kaiwa mubnaika ko kuma ya shiga cikin wannan teku tunda har ta ratso ta cikin wannan dajin don haka itama ai tana daga cikin dajin idan har yanaso ya auri mubnaika dolene saiya sayar da rayuwarsa ya shiga cikin wannan tekun tunda har ya riga yayi mata alkawari to bai kamata ya canja shawara ba koda ya gama wannan zancen zuci sai kawai ya falfala da gudu sannan yayi tsalle yadda kasan kifi ya fada cikin wannan tukun da shigarsa cikin tekun sai gashi yana tafiya yadda kasan wannan babban kifi ba bil'adama ba domin tafiya yakeyi tamkar yana gudu bisa kan turba amma wani abin mamaki shine tunda ya shiga cikin tekun sai yaga babu wata babbar halitta guda daya acikinsa sai kananan kifaye wadanda ko kasuwa idan kaje basayin daraja sosai wannan al'amari ba karamin bashi mamaki yayi ba domin wannan ne karo na farko daya taba ganin irin wannan a rayuwarsa sai ya tambayi zuciyarsa yace to menene ya hallakar da dabbobin da suke cikin wannan tekun ? amsar daya kasa baiwa kansa kenan amma sai ya kudurce a cikin zuciyarsa cewa koma dai wacce irin halitta cewa tayi wannan aiki saiya nemo ta kuma ya kasheta da karfin tsiya yana cikin wannan tunani ne kawai sai ya hango wani abu a gabansa kamar tsuburi kuma a wannan lokaci ya fara gajiya da tafiya acikin ruwan dole yana bukatar ya samu ya huta saboda tafiyar da ya sha nantake kuwa ya tunkari wannan tsuburin ya samu ya hau kansa ya zauna sosai kamar yana zaune a makwancinsa ba tareda shakka ba HAKIKA RASHIN SANI YAFI DARE DUHU INDA ACE YASAN MENENE WANNAN TSUBURIN DA BAIYI GANGANCIN ZAMA AKANSA BA Koda ya zauna akan wannan tsuburin Bai wuce dakika sittin ba sai ya ga wannan tsuburin ya dare gida biyu take wata kofa ta bayyana mai kama da baki cike da wasu zako zakon hakora marasa kyan gani in ba don marwan yayi saurin kaucewa ba da tuni ya fada cikin wannan wawakeken baki ba komai bane wannan halittar ba face wata rikakkiyar jiminar ruwa kuma itace ta kashe duk halittun da suke cikin tekun dama tun lokacin da marwan ya shigo cikin wannan tekun ta kula dashi lambo tayi masa don ya kansa gareta Anan alkalami na ya tsaya sai na sayo wani LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME BAKAR GABA PART 22 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Lokacin da jarumi marwan ya kaucewa faramakin da wannan dorinar ruwa ta kawo masa Saiya nutse acikin teku ita kuma saita hadiyi iska Ba shiri ta juyo izuwa bangaren da yake domin ta hadiye farat daya Cikin bakin zafin nama ya zare takobinsa ya kare harin nata Nan take suka kachame da azababben yaki acikin ruwan Babu abinda zai baka mamaki da kuma sha'awa sai ganin yadda jarumi marwan yake iya fada da wannan dorinar ruwa tamkar akan kasa yake ba wai acikin teku ba Domin har nutsu sukeyi shida wannan halittar na tsawon dakiku sama da dari uku akasan tekun suna bakin artabu Amma saikaga ya sake tasowa sama domin shakar numfashi Sannan kuma sai ya sake nutsewa akasan tekun idan suna fada Babu abinda yake tayar masa da hankali da wannan dorinar face ganin yadda take da tsananin karfin damtse da kuma zafin nama Kuma bayan haka kaifi da tsini baya tasiri ajikinta Kuma aduk sanda ya sari jikinta ko ya soketa da takobi sai dai yaji wata kara ta tashi Kamar haduwar karfe da karfe Idanuwanta kuwa idan ta budesu sai kaga suna haska can kasan wannan teku tamkar an haska da fitila Marwan ya tambayi kansa yace wannan wacce irin halitta ce ? Tabbas wani shaidanin shahararren matsafin ne ya sana'anta ta Don ya cimma wata muguwar bukatar tasa To amma wannan wacce irin bukatace? Tambayar da yayiwa kansa kenan kuma baisan amsarta ba Yana cikin wannan tunanin ne yaji wannan dorinar ruwan ta gabza masa duka da kafafunta na gaba take ya jishi kamar an janyeshi da majaujawa ya nutse akasan tekun Saboda karfin dukan harsaida ya sha ruwa ta hancinsa da bakinsa Yana cikin wannan halin ne sai ya ga ta biyoshi kasan ruwan da nufin ta dira akansa ta karya masa kashu shuwansa sannan ta cikinye shi Tabbas ya san cewa indai ya kuskura tazo ta sameshi anan kwanansa ya kare Koda yin wannan tunanin sai ya mike zumbur ya bugi ruwa da dukkan karfinsa Take yayo saman ruwan itama dorinar ruwan saita biyoshi nanfa suka kasa azababben tsere Shidai burinsa kawai shine ya bar tsakiyar tekun yaje gaba Domin acan ne zai sami cikakken kuzarin da zai iya fada da ita Itama kamar tasan abinda yake cikin zuciyarsa don haka saita biyoshi da dukkanin gudunta Wohoho hakika wahala bata da magani kuma duk wanda yake labarinta to tabbas bai santa bane (harda ni da naketa suburbudo kuku karya kuma kuke saurarata) Sai gashi ana falfala gudu kamar barawo da kuma me kaya Kowa yana da burin cika burinsa Abinda yake dada tayar masa da hankali shine Duk lokacin da ya juyo bayansa sai yaga kamar baifi taku biyu ba atsakaninsu Koyaya yayi sakaci ga barin gudunsa zata iya cimmasa Wannan shine dalilin dayasa shi ya kara zage damtsen nasa Cikin lokaci kankani suka iso bakin gabar tekun suna Zuwa daidai wannan gabar sai kawai jarumi marwan Ya tsaya cak ya juyo yana mai fuskantar wannan dorinar ruwan Nantake itama ta tsaya cak domin tasha jinin jikinta cewa Tabbas wannan jarumi akwai wani abu wanda ya boye acikin zuciyarsa Kafin ta ankara sai taga shima ya falfalo da gudun tsiya izuwa kanta Kafin ta ankara ya gabza mata wani mahaukacin sara atsakiyar Kanta, take wata kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe Saboda tsananin karfin saran sai da wani tartsatsin wuta ya tashi Itama kuma taji kamar an sa wani katon dutse an kwankwatsa mata kanta Nantake ta rusa wani irin mahaukacin ihu wanda yasa gaba daya tekun ta amsa kuwwa Ruwa kuwa ya dinga ambaliya kamar igiyar ruwan zata tsinke ta tafi dasu gaba daya Take dabbar ta shuri jarumi marwan ta falfala da gudu dashi zuwa cikin tekun Cikin zafin nama yayi sauri ya mayarda takobinsa cikin kufe Ya zare wata 'yar karamar adda ya ruketa da hannunsa na dama Hannunsa na hagu kuwa yana ruke da wani kaho wanda yake kwaya daya tak a tsakiyar kanta Nanfa suka kachame da sabon azababben yaki Mafi muni fiye da karon farko Inda ace kana nan lokacin da suke wannan bakin artabu sai kayi zaton cewa ba mutum bane marwan Saboda wani lokacin sai dabbar ta nutse a can kasan teku Bazata dago ba sai sun shafe sa'o'i masu yawa akasan ruwan domin taga ya mutu Amma sai taga kamar ma kara masa kuzari takeyi Ba komai ya jawo hakaba face tsananin horon da yake baiwa kansa tun lokacin da yake yaro karami Ita kanta wannan jimina ta tabbatar da cewa yau ta gamu da gamonta Saboda bai yarda ya sassauta mata ba munanan sara kawai yake zabga mata Duk da cewa batajin yanka amma tana matukar jin radadin saran da yake yi mata acikin jikinta Kuma yaki yarda ta saki kahon nata Suna cikin fafawarne kawai saiya kula da cikin bakinta Take yayi arba da wasu kwala kwan abubuwa kamar idanu Koda yin arba dasu sai yace acikin ransa Tabbas wadannan abubuwa sune ruhin wannan dorinar ruwa Kuma acikinsu babu abinda yake gani face fuskar wani mummunan aljani Sanye da hular mulki fuskarsa cike da kwarjini kai da kaganshi kasan cewa Shine yake sarrafa wannan dorinar ruwan Cikin sauri ya saki kahon nata sannan ya fara kai mata sababbin hare hare ta ko ina ajikinta Koda dorinar ruwan taga tabbas yana wahalar da ita sai ta shammaceshi Ta gabza masa wawan naushi da kafarta ta gaba Saboda karfin naushin saida kafarsa ta dama ta karye Take ya kwallara uban ihu sannan yayi sauri ya daka tsalle Tamkar akan turba yake sannan ya dira akan bakin dorinar ruwan Sannan ya saka hannunsa na hagu ya tokare hakoran bakinta na sama Kafarsa ta hagu kuwa saiya tokare hakoran bakinta na kasa Hannunsa na dama kuwa yana ruke da addarsa Nanfa aka soma kokawa tsakaninsu Ita tana ganin wannan ce damar data samu wacce zatayi kalaci da shi Shi kuma yana tunanin yadda zai ya fasa wadannan abubuwa masu kama da idanuwa Nan take dorinar ruwan ta tattare karfinta gaba daya wajen ganin ta tauna jarumi marwan sannan ta hadiye shi Shima kuma sai ya tattare karfinsa guri guda ya hana ta aiwatar da nufinta Nantake damatsansa suka tattashi jijiyoyin jikinsa sukayi burdin burdin Tamkar jijiyoyin bishiya rigar jikinsa kuwa saida ta yayyage kamar an sa kaifi an yanka Cikin zafin nama ya daidai ci tsakiyar wadannan idanuwa Ya jefa takobinsa daidai tsakiyar su, Take takobin taje ta fasa wadannan idanuwa wani irin tiriri ya fito daga cikin su Sannan jarumi marwan ya sakeyin wani tsallen ya fito daga cikin bakinta Ya nutse acikin ruwan ya jira ta gama matagugun mutuwarta Sannan ya dawo ya hau kanta ya saka takobinsa ta dinga yanka wuyah harsaida ya rabu da gangar jikinta Sannan ya nutse a cikin tekun ya kama hanya ya fice daga cikin sa Yaje ya rarrafa ya shiga cikin daji ya samo murtukekiyar jijiyar bishiya Sannan ya koma cikin tekun ya dauro kan dabbar ya fito daga cikin tekun Yana fitowa daga cikin sa ya fadi kasa yana numfashi da kyar Saboda wahalar dayasha Ga kuma kafarsa guda daya akarye ba'a gyara masa itaba har tayi tsami ta kumbura Cikin karfin hali ya bude bakinsa da karfi tareda karanto wadansu Dalasiman tsafi Take sararin samaniya tayi duhu wata irin inuwa ta mamayeta kamar za'ayi ruwan sama Kafin cikar dakika biyu wani matashin aljani ya bayyana Aljanin ya rissina a agareshi yace gani na amsa kira ya shugabana me kake da bukata? Jarumi marwan yace Yakai aljani lamakus ina so ne yanzu ka daukeni ka kaini Inda sansanin mu yake tareda kan halittar nan Cikin biyayya aljanin yace an gama ya shugabana Take ya shuri jarumi marwan tareda kan dorinar ruwan ya tashi dasu sama kamar kiftawar ido haka ya bayyana a sansanin su A wannan lokaci mubnaika tana zaune tana jiran dawowar sa Har ta kosa ta zaci ya mutu ta fara zubar da hawaye Koda taga aljani lamakus ya bayyana dauke da jarumi marwan kwance yana numfashi sama sama Saita kwallara uban ihu sannan ta rugo da gudu tazo inda yake ta goyoshi agadon bayansa ta sauke shi daga

Chapter 10 of 14