Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yake bukata lokacin da ya iso wannan daki kai tsaye ya wuce izuwa inda tukunyar tsafin mahaifinsu take ya zura wata battarsa aciki ya cikata taf da tsumin tsafin sannan ya koma cikin dakin dasu yarima saiman suke ya mika musu tsumin cikin tsananin farin ciki yarima saiman ya karba sannan yace mun gode da irin wannan gagarumar gudunmawar daka bamu domin inba don ka taimake mu ba to ba shakka acikin wannan garin zamu mutu dajin haka sai jurishan yayi murmushi yace ni dai burina kawai shine ku samu ku kashe mahaifinmu domin in bakuyi haka ba banida wata riba ataimakon danayi muku yana zuwa nan azancensa saiya juya ya fice daga cikin dakin fitarsa keda wuya sai saiman ya daga wannan battar ruwan ya sakata abakinsa yana sha sai da yasha kamar kaso daya cikin uku sannan ya mikawa markazulu battar yace shima yasha kaso daya dajin haka sai markazulu yaki karba sannan yace ai ni yanzu banida wani buri arayuwa yanzu zuciyata ta canja daga yadda take ada ni kawai ina da burin in zama mai yi maka hidima don haka banida bukatar wannan tsumin yarima saiman ya hade fuskarsa kamar zayyi kuka sannan yace yakai markazulu wanne irin hukunci ka yankewa kanka haka kana nufin kace duk wahalar da kasha ya dalilina ta tashi abanza kenan? indai ba zakashaba to anan tafiyarmu dakai zata tsaya koda markazulu yaga halinda saiman ya shiga sai nantake ya karbi tsumin shima yasha sannan ya baiwa saiman ragowar tsumin faruwar hakan keda wuya sai wani irin gagarumin karfi ya sake shiga jikinsu nantake sarkokin jikinsu suka tsutstsunke Markazulu ya balle kofar kejin da suke ciki suka fito daga cikin dakin suna fitowa sai sukayi arba da tsubi tsubin dakarun dodanni abakin dakin nantake saiman ya nunasu da hannunsa wata murtukekiyar sarka ta dauresu sannan kai tsaye suka fito izuwa wajen gidan sarautar suka kwallawa markazulu kira kafin su gama rufe bakinsu saiga markazulu ya bayyana fuskarsa amurtuke kamar an aiko masa da sakon mutuwa nantake suka ruguntsume da azababben yaki su saiman suka saka garjaju a tsakiya suka dinga kai masa mugayen hare hare shikuma yna karewa abinda yafi tayarwa da yarima saiman hankali shine markazulu baya yarda takobinsa ta sauka ajikinsa domin da zarar yaga zata tabashi sai ya bace ya bayyana a wani bangaren daban duk wannan abu da yake faruwa gaba daya mutanen birnin sun tsaya suna kallon wannan bakin artabu da akeyi wanda babu tabbacin ga bangaren da zaiyi nasara awannan lokaci markazulu ya taka muhimmiyar rawa fiye da farko sakamakon tsumin garjaju da yasha nan da guri ya hargitse gumu yayi gumu duk abinda wani daga cikinsu ya sara saidai kaga sun tsargeshi gida biyu koda kuwa katuwar bishiyace kai tun dodannin suna tsaye suna iya kallo har ya zamana cewa an fara yiwa rayuwarsu barazana suna hallaka don haka duk sun gudu saida aka kwana aka yini ana wannan yaki sannan yarima saiman ya shammaci markazulu ana cikin yakin kafin ya kula da motsinsa ya zabga masa sara da takobin sihirinsa atsakiyar kansa nantake markazulu ya kwarara uban ihu sannan jikinsa ya kama da wuta ya kone kurmus koda ragowar dadannin wadanda suka labe suna kallon abinda ke faruwa ga abinda ya faru ga shugabansu sai duk suka ruga aguje domin su tsira da rayuwarsu koda mutuwar garjaju sai su saiman suka ruguntsume juna shida markazulu suna masu farinciki ba tareda bata lokaciba aljani markazulu ya sunkuya saiman ya hau gadon bayansa suka kama hanyar wucewa sansaninsu LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEME DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN SAI KU KASANCE DA SHAFIN WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG AKODA YAUSHE BAKAR GABA Kashi na uku 3 Littafin habibullah Muhammad kabara Ebook created by Shuraih Usman Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG BAKAR GABA PART 11 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR lokacinda markazulu ya suri yarima saiman a gadon bayansa saiya kasance yana mai tsala azababben gudu cikin 'yan dakiku suka iso kusa da dan karamin garin da yarima saiman ya sana'anta koda ya rage saura baifi taku hamsin ba atsakaninsu sai aljani markazulu ya saki fukafukansa ya sauko kasa ahankali koda saukarsa sai yarima saiman ya sauko kasa daga kan gadon bayansa sannan sukayi bankwana da aljani markazulu ya tashi sama ya bace bat da gani nantake yarima saiman ya nufi sansanin nasu da sauri da isarsa bakin kofa saiya ratsa ta ya shiga cikin birnin kamar yadda haske yake ratsa gilashi awannan lokaci mutanen garin kowa yana tafiyar da harkokinsa na yau da kullum koda suka ga yarima saiman ya bayyana agabansu tsulum sai suka kamu da tsananin farinciki tamkar wanda yayi shekaru dubunnai bai dawoba nantake suka rugo gareshi suka shureshi suka dagashi sama suna farincikin dawowarsa tamkar dan karamin yaro saida aka shafe sa'o'i ana wannan shagali na murnar dawowar yarima saiman sannan yarima saiman ya juyo zuwa inda dakarunsa wadanda ya aika suke ya kare musu kallo dakyau yana maiyin nazari, daga can sai yayi murmushi ya dubi jarumi zamnal yace naga duk abinda ya faru ga ku ayayin tafiyar da kukayi izuwa birnin askandariya lallai na jinjina maka sannan kayi matukar kokari da ka iya rufe mana sirrinmu domin mutanen birnin askandariya duk da irin amanar da suka nuna muku to su mutane ne masu matukar son kudi domin akan kudi babu abinda bazasu iyaba ma'ana zasu iya cin amanar ku idan suka san ko ku suwaye dajin haka sai mamaki ya kama su zamnal saiman yace to yanzu ina aiken da nayi muku yake? dajin wannan tambaya sai zamnal ya baiwa wasu dakaru umarnin su fito da keken dokin, nantake suka umarni sukaje suka janyo keken dokin suka kawo shi gaban saiman saiman ya karewa keken dokin ido sannan yayi murmushi yace lallai kun iya zabe domin wannan keken dokin zaiyi kwari sosai, don haka nima ga sakayyar da zanyi maka nantake yarima saiman ya janyo jarumi zamnal gefe daya sannan yasa hannu ya kwanto battar da tsumin dodo garjaju yake ciki ya mikawa zamnal yace wannan shine abinda zan saka maka dashi domin ta sanadiyar nemansa saida na kusa rasa rayuwata don haka duk wanda na baiwa mutum ne mai matukar daraja dajin haka sai jarumi zamnal ya kamu da tsananin farinciki har yana faduwa kasa yana yiwa yarima saiman sujjada koda yarima saiman ya mika masa wannan battar bai tsaya jiran komai ba daga gareshi saiya wuce izuwa tantin matarsa gimbiya suhaila awannan lokaci gimbiya suhaila tana kwance tanayin barci batama sanda dawowarsa ba yarima saiman yasa hannu ya kara hannunsa akusa da fuskar gimbiya suhaila alokacin da takeyin wannan barcin sannan ya fita daga cikinsa ya sami waje ya buya koda ta shaki kamshin hannunsa tana cikin yin barcin saita mike zumbur domin tagani ko da gaske shi dinne amma koda ta bude idanunta sai taga bata ganshiba nantake tace azuciyarta lallai gaskiyane wannan ba mafarki baneba masoyinane ya dawo kuma yana kusa dani cikin sauri ta fito wajen tantin ko zata ganshi amma kuma ta rasa shi kawai saita dubi wasu dakaru guda hudu da suke gadin tantin nata ko sunganshi amma sukace basu ganshi ba dajin haka sai gimbiya suhaila ta daka musu tsawa tace saboda me zakuyi mini karya ko kuma a hada baki daku domin a tayar mini da hankali? bata tsaya jin amsar wannan tambayarba ta juya ta koma cikin tantinta ta zauna ta kifa kai da gwuiwa tana kukan bakin ciki tana cewa tabbas ina daf da haukacewa saboda soyayya amma kuma ni ina da tabbacin masoyina yana raye kuma akusa dani inma dai bashi bane to ruhinsa yana tareda ni idan kuwa ruhinsa ne to shi yamutu kenan? tana cikin wannan zancen zucine sai taji an dafa kafadarta ta baya koda ta dago kai sai tayi arba da yarima saiman sai tayi tsalle ta rungumeshi tana cewa saboda me zakayi mini wasa da hankali? ka sani cewa tun daga lokacin da ka tafi kullum zuciyata cikin begenka take sannan kuma inayi maka fatan nasara domin azahiri ka tafi ka barni ne agida amma zuciyata tana tareda kai aduk irin halin daka shiga dajin haka sai yarima saiman yayi murmushi tareda shafa gashin kanta yace lallai maganarki gaskiyane ki sani cewa aduk lokacin da jikina ya gaji sakamakon wahalar dana shiga to tunaninki ne yake karfafa mini gwuiwa koda kuwa faduwa kasa nayi sai naji muryarki akunne ne tana cewa ka kara taku daya tak domin nasara tana tareda kai ma'ana dai duk wata nasara danake samu to kece sila haka dai su yarima saiman sukayi ta hira har barcin dare ya sacesu basu saniba ++++ +++++ ++++++ ++++ al'amarin boka ulumanu kuwa bayan yaje ya samu nasarar hadin kan da aljani harisul mar'uf akan yarjejeniyar cewa aljani harisul mar'uf bazai taimaka musuba wajen yaki da mutanen birnin ramlatul saif ba sai dai in sun gama yakin shi zai kashe musu maciyar da mutanen birnin suke bautawa sannan ulumanu zai mai dawa mahaifiyarsa ainihin siffarta daga siffar da aka tsafanceta ta gunki zuwa ainihin siffarta ta aljana, bayan harisul mar'uf ya kashe macijiyar da birnin ramlatul saif sai nantake boka ulumanu yayi tsafi suka dawo izuwa fadarsa inda anan ne yake tara dakarunsa na yaki wadanda adadinsu ya wuce dubu dari biyu wadanda suka hada mutane da aljanu koda bayyanar boka ulumanu tareda aljani harisul mar'uf sai duk gaba daya dakarun suka fadi kasa suna masuyi masa sujjada ulumanu ya dubesu sannan ya nuna aljani harisul mar'uf yace wannan shine sadaukin aljanin da nake baku labarinsa kuma duk duniya shikadai ne wanda zai iya kashe macijiyar da birnin ramlatul saif suke bautawa don haka yanzu bada jimawaba zamu dunguma gaba ki dayan mu domin muje mu baje birnin ramlatul saif domin biyan bukata yana zuwa daidai nan azancensa saiya rufe idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi marasa dadin ji nantake aka fara wata irin walkiya mai matukar firgitarwa saida aka shafe 'yan dakiku anayi sannan komai ya lafa saiga wani irin katon tsuntsun tsafi ya bayyana tareda wadansu ingarmun dawakai wadanda zasu ishi gabaki daya bil'adaman da suke wajen, sannan boka ulumanu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mara dadin ji tareda umarta dakarunsa da kowanne ya kama doki guda daya ya hau domin tafiya wannan yaki domin yakine za'ayi irin wanda ba'a taba yin kamarsaba atarihin duniya nantake kuwa dakarun suka cika umarninsa sannan boka ulumanu ya shige gaba akan tsuntsun tsafinsa tareda aljani harisul mar'uf saboda sune shugabannin wannan tafiya idan babu daya daga cikinsu tafiya bazata yiwuba bayansu kuma dakarun bil'adama ne sannan aljanu akarshen sahu sai suka nufi hanyar da zata kai su birnin ramlatul saif idan mutum yagansu awannan lokaci zata zaiyi gaba daya dakarun duniya ne suka hadu awaje guda WANNAN SHINE ABINDA YA FARU AFADAR BOKA UULUMAN BAYAN SUN FITO YAKI DA BIRNIN RAMLATUL SAIF ++++ +++++ ++++++ +++++ acan birnin ramlatul saif kuwa bayan sarki abu saiman yayi zaman majalisa tareda mutanen birninsa an yi shawarwari akan yadda za'a bullowa wannan yaki tun daga wannan rana hankalin kowa ya kwanta tamkar babu wani tashin hankali da yake kusanto su tundaga wannan rana mutanen birnin suka dage wajen kera sababbin makaman yaki 〇 da kuma mugayen tarkuna suna zuwa suna binnewa a iyakar dajijjikan da suke kewaye da birnin awannan lokaci kuwa sai abu saiman da kansa yake baiwa dakarun birninsa sababbin horon yaki dare da rana cikin kwanaki kadan dakarun suka kware a dukkan fannin da ake koya musu sai da ya zamana gaba daya mutanen birnin ramlatul saif sun daina tsoron mutuwa ana cikin wannan haline wata rana sarki abu saiman ya shiga cikin halwar tsafinsa yana bincikensa kwatsam saiyaga hoton boka ulumanu da aljani harisul mar'uf tareda dakarunsa mutum dubu biyu sun nufo birnin ramlatul saif koda ganinsu sai sarki abu saiman ya kwarara uban ihu sannan yace hakika karshen birnin mu da kuma karshen abar bautar mu saboda haka dolene muje mu fita mu kare kimar kasarmu cikin gaggawa sauri abu saiman ya fito daga cikin dakin halwar tsafinsa ya tara gaba ki daya dakarunsa wadanda adadinsu bai wuce dubu sittin ba ma'ana basufi kaso daya cikin ukun suba abu saiman ya dubesu yace. yaku ahalin birnin ramlatul saif zaku iya sallama rayuwarku domin kare kimar kasarku da kuma abin bautarmu? cikin hadin baki gaba daya dakarun suka amsa mun yarda mun amince sarki abu saiman ya sake cewa to yanzu haka dakarun boka ulumanu suna kan hanyar zuwa birnin nan saboda haka inaso gaba daya muje mu taresu kafin su iso nan birnin sannan ya umarci kowa yaje yayi nasa shirin yana zuwa daidai nan azancensa saiya juya ya shiga cikin gidan sarauta yayi shigar yaki farin sulke sarki abu saiman ya sanya tareda farar hular sannan ya rataya wasu zabga zabgan fararen takubbai guda biyu agadon bayansa kallo daya zakayiwa sarki abu saiman awannan lokaci ka fahimci cewa lallai ya cika sadauki mai tarwatsa maza hakika sarki abu saiman yana da matukar kwarjini da cika ido domin duk inda ake neman jarumi idan aka same shi to bukata ta biya atarihin jarumtakarsa bai taba jagorantar yakiba face an sami nasara kuma tunda yake fita filin daga bai taba haduwa da masifar data sanya shi ya ja da bayaba koda kuwa tazarar taku daya sau ashirin yana shiga gasar jarumtaka ta nahiyarsu yana cinyeta ajere kai duk wata kalma ta tsoro sarki abu saiman baisanta ba don haka akace barewa batayi gudu ba sannan kuma danta yayi rarrafe ba ma'ana dai shi yarima saiman ya gado afannin jarumtaka lokacin da sarki abu saiman ya gama yin shirinsa na yaki saiya fito kofar fadarsa ya tsaya kyam yana jiran dakarunsa su gama shirinsu suzo su same shi anan wajen domin su tafi yakin dake gabansu cikin rabin sa'a dukkan dakarun birnin ramlatul saif suka gama hallara nantake suka dunguma gaba daya suka nufi hanyar fita daga birnin ramlatul saif tafiyar sa'a biyar sukayi sannan suka fita daga birnin sannan suka kafa sansani suna jiran abokan gaba sannan sarki abu saiman ya sana'anta wasu mutum mutumi na tsafi ya tura su izuwa dajin farko su jira zuwan abokan gaba da zarar sunzo sai su tura musu da kibiyoyin tsafi WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A BIRNIN RAMLATUL SAIF BAYAN SUN FITO JIRAN ABOKAN GABA +++++ +++++++ ++++++ acan sansanin su yarima saiman kuwa lokacin da barci sacesu basu farkaba sai da safiya tayi suna farkawa sai suka tarar da abinci anzo an ajiyesu musu tareda abin sha kafin su fara cin abincin saida suka zagaya kewaye sukayi wanka sannan suka fito suka kamacin abincin suka cika cikinsu bayan sun sami nutsuwa sai yarima saiman ya fito bakin tantin nasa ya tsaya sannan ya tara gaba daya mutanen da suke tareda su awaje guda bayan kowa ya hallara sai ya fara jawabi kamar haka yaku ahalin birnin ramlatul saif a yaune zamu nufi can birnin hamshak ne inda acan ne zamu samo makallin miftahul darul sihir wanda dashine kadai za'a iya bude kofar shiga kogon tsafin boka awaisul masawi inaso ku sani cewa zuwa karbo makullin kogon darul sihir afadar sarkin aljanu na birnin hamshak daidai yake da mutum yace zaije farautar ajalinsa da kansa domin duk abinda kake takama dashi walau karfin damtse, iya yaki, ko karfin sihiri to da zarar kaje wannan fada shikenan kaje gidansa da kanka duk masifar dodo garjaju bata kai rabin ta fadar sarkin aljanu na birnin hamshak ba don haka awannan karon nikaina banida tabbacin zan tsira da rayuwata don haka nake me rokonku daku dage dayi mini addu'a akan abinda zan fita nema yanzu sai kowa ya hada kayansa domin a yanzune zamu bar wannan birnin mu shiga daji mu ci gaba da tafiya yana gama fadar haka sai nan da nan mutane suka fara har hada kayayyakinsu kafin rabin sa'a sun gama bayan kowa ya gama shirin tafiyarsa sannan kowa ya sami dokinsa ya hau sai yarima saiman ya sake karanta wadansu dalasiman tsafin akaro na biyu yana gama rufe bakinsa sai wannan dan karamin gari ya nutse acikin karkashin kasa sannan yarima saiman ya ciro zoben tsafinsa ya wullashi sama nantake wani jan haske ya fito ya nuna hanyar yamma cin dajin inda yake nuni da itace hanyar da zata kaisu birnin hamshak nantake suka dau hanya suka nufi hanyar da zoben ya nuna musu cikin azababben gudu WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A SANSANIN SU YARIMA SAIMAN liҠɛ ąŋɖ Ćơmmɛŋŧ iŞ ơųř ɛŋĆơųřąɠɛmɛŋŧ PART 12 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Nidai rahoton dana samo akansu yarima saiman ayau shine ku saurara kuji Lokacinda su yarima saiman suka kama hanyar zuwa birnin aljanu na hamshak sai suka wanzu suna masu tsala azababben gudu kamar zasu tashi sama yarima saiman ne ya kasance agaban wannan tawaga sai kuma gimbiya suhaila wacce ta kasance a hannun damansa acikin keken dokinta, daga barin hannun hagun gimbiya suhaila dakarune atsatstsaye cikin shigar yaki rike da makaman yaki abayansu kuma mutanen gari ne sannan su jarumi zamnal ne don tabbatar da tsaro haka suka dinga kutsawa ta cikin mugayen dazuzzuka masumatukar hatsari, wadanda sukahada da mugayen 'yan fashi, manyan dabbobin daji da mugayen aljanu amma cikin kankanin lokaci su yarima saiman suke gamawa dasu akan hanyar sune ta tafiya birnin aljanu na hamshak suka iso wani mummunan daji mai matukar hatsari da firgitar da duk wata halitta wacce ta kusanci dajin shidai wannan daji yana cike ne da manya manyan duwatsu masu duhuwa yadda ba'a iya ganin abinda yake cikin duhuwowin sannan kuma duwatsun sun kewaye hanyar wucewa ta cikin dajin sun zamewa hanyar kamar kofa, gabas, yamma, kudu da arewa na dajin duk inda kake kallo babu hanyar da zakabi ka wuce gaba koda suka iso daidai wannan wuri sai suka ja linzaman dawakansu suka tsaya sukayi cirko cirko ana jiran maganar da yarima saiman zaiyi saboda shine shugaban tafiya daga can sai yarima saiman ya dubi tsaunin sosai ya kare masa kallo yana nazarinsa tsawon 'yan dakiku sannan ya juyo ya dubi jama'ar tasa yace idan har munaso mu san hanyar da zamubi mu ketare wannan tsauni dolene na hau saman wannan tsauni domin na samar mana hanyar da zamubi mu ketare wannan tsauni don haka sai ku jirani awannan wuri ni zan hau saman tsaunin dukkaninku kuna karkashin kulawar jarumi zamnal yana zuwa daidai nan azancensa sai ya sauko daga kan dokinsa awannan lokaci gimbiya suhaila tana kwance acikin keken dokinta bata ma san abinda yake faruwaba yaje ya bude kofar keken dokin ya sumbaci goshin gimbiya suhaila sannan ya maida kofar ya rufe kai tsaye yarima saiman ya tunkari wannan tsauni ya fara kamashi yana hawa kamar bai kasance bil'adama ba kayi zaton cewa kadangare ne shi ba mutum ba dukda cewa dutsen ya kasance mai santsi babu kafar kamawa da yawa amma saboda tsananin jarumtaka irin ta sa sai gari yana hawa kan tsaunin cikin salo mai ban sha'awa saida yarima saiman ya ya shafe sa'a hudu yana hawa kan tsaunin sannan ya isa karshen wannan tsauni ya fara tafiya asamansa domin ya samo musu hanyar wucewa kash! ! hakika rashin sani yafi dare duhu inda ace yasan abinda zai faru da baiyi kuskuren hawa kan wannan tsaunin ba yabar mutanensa akasa domin yana gama hawa kan tsaunin sai ga wasu irin murtuka murtukan zakuna masu matukar firgitarwa suna fitowa daga cikin duhuwowin dajin koda bayyanar wadannan zakuna sai suka fara yin wani irin gurnani wanda ya cika dajin baki daya mutanen dake biye da yarima saiman kuwa duk sai suka figice suka kama koke koke koda ganin halin da mutanen suka shiga sai jarumi zamnal ya zare takobinsa tareda sauran dakarun suka afkawa zakunan suka ruguntsume da azababben yaki shi kuwa yarima saiman koda yaga abinda ya faru sai hankalinsa ya tashi ya fara kokarin sauka daga kan tsaunin yana cikin hakane sai ya taka wani waje mai santsi ba tareda ya sani ba nan take kuwa santsi ya kwasheshi ya fadi kasa sumamme sannan ya dinga gangarowa kasa su kuwa su jarumi zamnal sai suka dinga fafata yaki tsakaninsu da mugayen zakunan har tsawon sa'a biyu amma sun kasa kashe koda guda daya kuma tun awannan lokaci tuni dakarun sun gama gajiya jarumi zamnal ne kawai yake iya tabuka wani abu awannan lokaci da yawan dakarun duk sun sami mugayen raunika shi kuwa jarumi zamnal ya kasa kashe ko daya acikin zakunan sai yana iya yi musu mugun luguden duka duk wanda ya daka saidai kaga ya tashi sama kamar an janyeshi da majaujawa yaje ya gwaru da jikin dutse amma sai kaga ya tashi ya karkade jikinsa ya dawo an ci gaba da yakin hakika jarumi zamnal ya kasance jarumin gaske mai ban al'ajabi domin shi kadai ya hana wadannan zakuna cutar da koda mutum daya daga cikin mutanen da suke tareda su ana cikin wannan azababben yaki ne sai su jarumi zamnal suka ga wani katon aljani yana tahowa daga sama koda suka ga wannan jibgegen aljani sai suka kara firgita domin a zaton su yazone domin ya hallakasu ba zato ba tsammani sai suka ga wannan aljanin ya fada cikin wadannan zakuna sun kara kachamewa da azababben yaki sai gashi awannan lokaci fada ya canja salo domin sai gashi ba kowa bane wannan katon aljani ba face aljani markazulu sai gashi ya shiga cikin zakunan yana ragargazarsu duk da tsananin yawansu sai gashi ya zama na banza domin daga su ya dingayi yana gwara su da juna duk wadanda ya hada su gware saidai kaga suna kansu ya dagargaje kwakwalwarsu tana kwaranyowa kasa koda zakunan sukaga yadda aljani markazulu yake ta ragargazarsu sai suka kara zage damtse domin suna ganin ya hanasu cin abincinsu ne domin yanzu suna tsaka da matsananciyar yunwa amma duk da haka sai hada karfin nasu ya zama na banza domin bai rage musu komai ba face kara baiwa markazulu damar hallakasu cikin kankanin lokaci ya gama hallakasu gaba daya bayan ya gama kashe zakunan ne sai dakarun da sauran mutanen gari suka kara firgicewa banda jarumi zamnal domin shi kadai ne agaban markazulu suna kallon kallo gaba daya mutanen da suke wajen sunyi zaton cewa markazulu so yake ya kashe su domin a zaton su shine yake mallakin wannan dajin da suke ciki koda markazulu ya kula da yanayin da suke ciki sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuskarsa yace haba ahalin birnin zaharul maswur saboda me zaku dinga firgita dani bayan kunga kalar taimakon da nayi muku ayanzu ai ya kamata kusan cewa ni ba mai cutarwa bane ba agareku domin tun farkon tafiyar ku ina tareda akan hanyar ku na boyene saboda tsoron ku shiga irin halinda kuka shiga ayanzu sakamakon ganina kuma shugaban ku ne ya bani umarnin buyan amma yanzu bisa dole ce tasa na bayyana kaina sakamakon kuskuren da shugaban ku yayi na tafiya ya barku anan shine naga kuna dafda hallaka ni kuma nasan burin yarima saiman gaba daya akanku yake ni kuma burina na gyara kuskuren da nayi abaya don haka nazo domin na ceci rayuwarku dajin wannan batu sai jikin mutanen yayi sanyi suka dan fara sakin jikinsu dashi don haka sai zamnal ya dubeshi yace yakai wannan jarumin aljani muna godiya da irin wannan taimakon da kayi mana amma muna so musan ko wanene kai sannan kuma munada tambaya guda daya dajin haka sai markazulu yace ni sunana markazulu tsohon hadimin boka ulumanu bayan wannan kuma wacce tambaya ce dakai indai na sani zan fada maka iyakar gaskiyar dana sani zamnal yace menene ya sami yarima saiman naga har yanzu bai dawoba domin na tabbata indai yana lafiya bazai barmu mu shiga halinda muke cikiba yanzu aljani markazulu yayi murmushi yace me zaisa ka tayar da hankalinka akan yarima ina mai tabbatar maka da cewa duk irin halin da yarima saiman zai shiga dole ne ya tsira da rayuwarsa domin mutum ne shi mai matukar sa'a da rabo a dukkan abubuwan da ya saka agabansa amma dai bara na nuna maka halinda yake ciki nan take aljani markazulu ya nuna jikin dutsen da hannunsa nan take wani haske ya fito ya bugi jikin dutsen saiga abindaya faru ga yarima saiman tun daga lokacin da yake hawa kan wannan tsauni har zuwa lokacin da santsi ya kwasheshi ya fadi kasa sumamme sannan ya gangara izuwa kasan tsaunin koda hoton yazo daidai wannan guri sai hoton komai ya dauke koda suka ga abinda ya faru ga yarima saiman sai hankalinsu gaba daya ya tashi don haka sai markazulu ya bude fuka fukansa cikin sauri ya tashi sama ya hau kan tsaunin ya fara neman yarima saiman amma sama da kasa ya kasa ganinsa saida ya shafe sa'o'I biyar yana nemansa amma bai ganshi kuma baiga wata alama da zata nuna cewa ga inda yakeba bisa dole ya sauko daga kan tsaunin ya bude baki da nufin yin jawabi kenan sai a daidai wannan lokaci gimbiya suhaila ta farka daga barcin da takeyi tana farkawa sai ta kwallara ihu tana fadin cewa ina mijina yake ! ina masoyina tabbas wani abu ya faru dashi nan take ta fito daga cikin keken dokin da take ciki tana tambayar su zamnal ina masoyinta yake amma aka rasa wanda zai wanda zai iya bata amsa sai dai su sunkuyar da kansu sun kasa fadin komai hawaye ya zubo mata sannan ta dubesu gaba daya tace yanzu duk cikin ku babu wanda zai iya sanar dani halin da yake ciki lallai inaji ajikina wani abu ya sameshi amma duk da haka ina da tabbacin cewa bazai mutuba domin masoyina jarumi ne na gaske don haka nima dole ne asanar dani inda yake yanzu. domin naje na taimaka masa jarumi zamnal ya kalleta kansa asunkuye yace ya shugabata yanzu haka ya tafine domin ya samo mana hanyar da zamubi mu wuce wannan daji ,amma kiyi hakuri ba zamu iya fada miki inda ya tafiba domin tsaron lafiyarki dajin haka sai tayi murmushi tace yanzu na gane manufarka wato kana nufin ya hau kan wannan tsaunin ne ko? to inaso ka sani menene amfanin rayuta idan babu muradina masoyina ne kadai muradin rayuwata don haka koda na zauna anan indai baya raye to nima bazan karasa kogon boka awaisul masawiba araye to dolene naje na taimaka masa koma mene zai sameshi saidai ya samemu tare kafin zamnal yayi wani yunkuri ta shammaceshi ta zare takobin da ke jikinsa ta falfala da azababben gudu ta nufi wannan tsauni domin ta hau kansa koda ganin abinda yake shirun faruwa sai aljani markazulu ya ya hura mata wata iskar tsafi faruwar hakan keda wuya sai barci mai nauyi ya sake dauketa nantake kuyangi suka je suka dauketa suka kaita cikin keken dokinta suka ajiyeta sannan markazulu ya kallesu gaba daya yace hakika saiman yana cikin hatsari domin babu irin duban da banyi masaba amma na rasa inda yake don haka nima bansan hukunncin da zan yamkeba akan dawowarsa domin tabbas yana cikin halin mutuwa da rayuwa dolene mu zage damtse mu

Chapter 6 of 14