Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kan aljanin Sannan ta zauna bisa turba ta kwantar dashi akan cinyarta Sai a sannan ne ya kula da karayar da take jikin kafarsa Cikin daka tsawa tace da lamakus yaje ya samo kiraren da za'a gyara masa kayar tasa Nantake aljani lamakus ya bace cikin abinda bai wuce dakika biyu ba ya dawo dauke da kirare sirara tare da danyun bawon bishiya Sannan tace da aljani lamakus shin ka iya gyaran karaya ? Cikin biyayya aljanin yace eh ranki ya dade Mubnaika tace to ai saika fara aikinka ko Take kuwa lamakus ya fara gyara karayar amma abin mamaki sai yaga babu alamar jin zafin gyara atattare da marwan Ba komai ya jawo hakanba face kallon fuskar jaruma mubnaika da yakeyi a wannan lokaci ita kuma sam bata fahimci hakaba Ana cikin gyaran ne sai tayi tunanin ya kamata taje ta yi masa shinfida Kafin a gama yi masa gyaran Take kuwa ta sauke kansa daga kan cinyarta ta juya ta shige cikin tantin Shigarta keda wuya sai taji jarumi marwan ya kwarara uban ihu Cikin firgita ta fito daga cikin tantin Koda ta fito sai tayi arba da aljani lamakus hancinsa yana zubar da jini Cikin razana aljanin yace Ya shugabata hakika gyaran nan ba zai taba yiwuwa ba muddin bakya nan wajen domin ganinki ne yake hanashi jin radadin gyaran karayar nan dake jikinsa Don wanna jinin da kika gani akan hanci na ba komai ya jawo hakanba face naushinsa saboda barin gaban fuskarsa da kikayi Dajin wannan magana sai kuwa ta dawo daidai inda fuskarsa marwan take Ta sunkuya tanayi masa murmushi Shikuma lamakus yaci gaba da yin aikinsa ba tareda sun sami wata matsalaba haka suka gyara karayar suka gama Ana gama gyaran ne kuwa barci mai nauyi ya sace jarumi marwan Bayan ya farkane ya bata labarin irin gwagwarmayar da yasha da wannan sihirtacciyar dorinar ruwa Koda gama bata wannan labari sai kawai ta rungume shi tare da fadin cewa Tabbas na yarda dakai ne zanyi rayuwa Kuma ba'a halicceni ba saidon na zama matarka don haka Tashi yanzu take zamuyi aure ni dakai Shikuma aljani lamakus saiya zama shaida atsakanin mu Tana gama fadin haka sai ta kama kafadunsa ta tasheshi tsaye suka fita daga cikin tantin Sannan ta zaunar dashi suna masu fuskantar juna Shi kuma aljani lamakus saiya dauko wannan kan dorinar ruwan ya ajiye shi acan gefensu kadan Take mubnaika ta tashi taje ta dora hannunta akan mushen kan dorinar ruwan tare da rufe idanunta Tsawon dakiku kamar mai sauraron wani labarin Bayan nan kuma sai ta dauki kyastu ta kunna wuta ta cilla jikin kan dorinar ruwan Take wuta ta kama kamar ansa karmami sannan ta dawo inda jarumi marwan yake Ta mika masa hannunta cike da murmushi yasa wata 'yar karamar zabira ya yanka Sannan shima ya yanki nasa tafin hannun ya kara akan nata hannun jininsu yana haduwa da juna Atare cikin hadin baki duk su biyun suka ce Munyi alkawarin zama daya tare har abada kuma ba zamu taba rabuwa ba Suna gama fadin haka Sai dukkansu suka fara murmushi farinciki Haka suka kasance suna rayuwar aurensu a cikin wannan daji har aka sami cikina aka haifeni A ranar da suka haifeni sun yi farinciki sosai na samun haihuwar jaririya kyakykyawa Kuma suka rada mini suna SUHAILA a lokacinda na fara girma da kansu suka dinga koyar dani horon yaki da iya yin farautar manyan namun daji A wannan lokaci banida abokin yawo face aljani lamakus tare dashi mukeyin duk wani wasa da nake sha'awa Har na kai shekara bakwai Ashe Ita kuma wannan dorinar ruwan da mahaifina ya kashe Ba komai baceba face baiwar wani babban sarkin birnin aljanu Ana kiransa da suna sarki mafazil shine wanda ya sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwan domin aiwatar da wani sihirinsa na tsafi wanda bincike ya tabbatar masa da cewa bazai taba samun cikar burinsa ba face ya hallaka duk halittun da suke rayuwa akarkashin ruwa Wannan daliline yasaka shi sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwa Kuma duk abinda ya faru ya riga ya gani kuma yasan cewa tabbas ya aikata masa kuskure Koda gama ganin wannan al'amari saiya rusa uban ihu sannan yace Dolene na dauki fansa akan abinda yayi mini kuma fansar nan ba akan iya shi kadai zata tsaya ba saita shafi duk wani makusancinsa LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA PART 23 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Inda muka tsaya Ashe Ita kuma wannan dorinar ruwan da mahaifina ya kashe Ba komai baceba face baiwar wani babban sarkin birnin aljanu Ana kiransa da suna sarki mafazil shine wanda ya sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwan domin aiwatar da wani sihirinsa na tsafi wanda bincike ya tabbatar masa da cewa bazai taba samun cikar burinsa ba face ya hallaka duk halittun da suke rayuwa akarkashin ruwa Wannan daliline yasaka shi sana'anta wannan sihirtacciyar dorinar ruwa Kuma duk abinda ya faru ya riga ya gani kuma yasan cewa tabbas ya aikata masa kuskure Koda gama ganin wannan al'amari saiya rusa uban ihu sannan yace Dolene na dauki fansa akan abinda yayi mini kuma fansar nan ba akan iya shi kadai zata tsaya ba saita shafi duk wani makusancinsa Cigaba Wannan shine alkawarin da sarkin aljanu mafazil ya daukarwa kansa Ni kuma mafarauci marwan tareda mahaifiyata suka cigaba da horar dani dabarun yaki dana farauta Har y zamana cewa tun ina da shekara bakwai ina iya fita farauta ni kadai Kuma na sami nasara akan duk abinda nayi karo dashi HAKIKA MASU IYA MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKACE BAREWA BATA YI GUDU BA DANTA YAYI RARRAFE BA DOMIN DUK IRIN JARUMTAKAR SADAUKI MARWAN DA KUMA MAHAIFIYARTA SAIDA TA GADOSU KAI HATTA A BANGAREN KYAU SAITA ZAMA KAMAR AN TSAGA KARA DOMIN DUK WANDA KA KALLA TSAKANIN MARWAN DA MUBNAIKA SAIDAI KAGA SUNA TSANANIN KAMA Ana cikin wannan haline wata rana aljani lamakus tareda suhaila sun fita yawon shakatawa domin babu abinda suhaila takeso sama da taga suna yawo a cikin samaniya tana giftawa Ta saman dajijjika da kuma birane tana ganinsu kanana shi kuma jarumi marwan tareda mubnaika suna cikin daki suna gudanar da zaman takewar su ta aure sai suka wata irin iska mai karfi tana kadawa kafin su ankara sai suka ji duk jikinsu yayi sanyi kamar an zare musu lakar jikinsu Take barci mai nauyi ya sacesu sai farkawa sukayi suka gansu a cikin wata tangamemiyar fada mai girman gaske Cike da dakarun yaki masu matukar kwarjini da ban tsoro hannuwansu rike makaman yaki masu matukar hatsari Bisa kan wata katuwar karagar mulki kuwa wani katon mummunan aljani ne Mai girman gaske cike da kwarjini da ka ganshi kasan dole ne kura taci nama Ma'ana dole ne ya kasance jarumin gaske gaske kuma mashahurin matsafi kowa afadar yayi tsit kamar mutuwa ce ta gifta babu maiyin koda tari atsakiyar fadar kuwa wata katuwar katangace mai tsawon gaske Kasanta kuma wutace takeci kamar an zuba mata makamashin mai Aljan Sarki mafazil ya mike tsaye ya dubi jama'arsa cikin wata irin kakkausar murya yace Yaku mutanen birnin hamshak Dukkanku kun sani cewa babu wanda ya isa ya shiga cikin hurumi na ya fita lafiya Shi wannan bakon saurayi da kuke gani ba karamin hatsabibi bane Domin shine bil'adama na farko daya taba rusa mini shirina sai shi Dukkanku kun sani cewa banida burin da yafi naga naga bayan babban abokin gaba ta wanda aka shayar damu tare wato sarkin yaki ramzas mahaifin aljani harisul mar'uf Hakika yanzu daf nake da cika burina amma sai gashi wannan saurayin ya rusa mini komai saboda haka yanzu agaban idonku zan dauki fansa akansu Yana gama fadar haka saiya juyo ya kalli su jarumi marwan yace Ku kuma yanzu zan baku zabi guda biyu saboda nasan yadda kuke matukar kaunar junanku Zabi na farko shine ku sasanta atsakaninku daya ya mutu ya bar daya domin ku karya alkawarin da kuka daukarwa junanku tun a farkon haduwar ku ko kuma ku mutu gaba daya shikenan an manta da tarihin jarumtakarku..... Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa sai yaji jaruma mubnaika ta daka masa tsawa tace Karyarka tasha karya tsohon azzalumi baka isa ka kasa mu karya alkawarin da yake tsakanin muba Koda jin haka sai shima yayi murmushi sannan yace Ai dolece zatasa ku karya alkawarin don haka mu zuba mu gani Yana gama fada haka saiya karanta wasu dalasiman tsafi Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin sihirtattun kunamai suna shigowa ta saman fadar Adadin su yakai guda dubu kuma kowacce daga cikinsu tana Da fuka fuki ajikinta wanda zasu dinga tashi sama dasu Take kunaman suka yo kansu marwan Nanfa marwan da mubnaika suka juya baya suka hade jikinsu Suka ruguntsume da kokawa da wadannan kunaman Duk kunamar da suka daka nan take take faduwa kasa Amma saboda taurin rai irin nasu sai kaga sun sake tashi anci gaba da fadan dasu Ashe alokacin da aljani mafazil ya dauko su marwan acikin gidansu saidaya zuba musu wata irin guba acikin jikinsu wacce zata rage musu kuzari da karfin jiki Koda aka shafe sa'a daya ana fafata wannan kazamin yaki Sai wadannan kunaman suka fara samun damar harbin su jarumi marwan da wani irin mummunan dafi mai karfin gaske Nantake sukaji duniyar ta canja musu wani irin mummunan radadi ya dinga ratsa sassan jikinsu Take jiri ya dinga dibarsu dukkansu suka tabbatar da cewa tabbas lokacin mutuwarsu yayi Don haka sai marwan ya ture mubnaika ta fadi kasa Sannan shima ya fada kanta ya lullubeta yadda babu wata kunamar da zata iya harbinta suka ci gaba da harbin gadon bayansa sannan yace Ya masoyiyata saboda alkawarin da muka dauka ni dake kada mu zama masu son kanmu Kada ki manta yanzu fa bamu kadai bane muke rayuwa ba Harda 'yarmu wacce muka haifa wato suhaila Don haka ni na yarda na hallaka ke kije kici gaba da rainonta... Kan ya gama fadar abinda yake bakinsa sai itama ta tureshi Ya koma kasa ita ma ta danne shi irin yadda yayi mata tace Ai ba kaine ka fara yin alkawari ba a tsakanin mu Nice wadda ta farayi don haka kuwa ni ya kamata in fara mutuwa bakaiba fatana kawai ka ruke soyayyata acikin zuciyarka Haka dai sukayi ta murgin murgin atsakaninsu Kunaman nan kuwa sukayita harbinsu a jiki har yazamana jinin jikinsu ya gurbace da dafi Daganan basu san sanda suka mirgina cikin wannan katon ramin ba wanda wuta take ci acikinsa ba Suka mutu duk su biyun Al'amarin 'yarsu kuwa suhaila da aljani lamakus bayan sun gana yawon shakatawarsu Sai dawowa sukayi gida suka tarar da gidan babu kowa saidaima hargitsewa da yayi Alamar babu lafiya nantake suhaila tashiga cikin daki ta dauko madubin tsafin mahaifinta ta shafeshi taga hoton duk abinda ya faru Dukda kasancewarta yarinya karama saida tayi kuka sosai na rashin iyayenta Da kyar aljani lamakus ya rarrasheta sannan yayi mata alkawarin zai sadata da wasu iyayen daban masu kirki Wadanda zasu riketa amana tayi rayuwar farinciki tareda su Daga wannan rana lamakus ya dauketa suka bar wannan dajin da suke da zama ++++++++++++++++++++++++++++++ +++++++++++ Acan birnin ramlatul saif kuwa akwai wani hamshakin attajirin dan kasuwa wanda ake kira da suna manhas Manhas attajirin gaske ne yana da matar aure guda daya mai suna sadwisa Tunda sukayi aure basu taba samun haihuwa ba sai bayan shekara hudu dayin auren nasu Sannan suka haifi 'ya mace kykykyawa wacce suka kwallafa soyayyarsu gaba daya suka dora akanta Aranar da suka haifeta ne suka sanar da mutane haihuwar da sukayi sannan sukayi alkawarin ba zasu bari kowa yaga wannan yarinya ba hatta ma'aikatan gidansu sai alokacin da balaga alamun girma suka fara bayyana ajkinta A wannan lokacin ne zasu nunawa duniya 'yar da suka samu domin nema mata mijin aure Wannan yarinya da suka haifa kuwa sai lokacin haihuwarsu yazo daidai dana suhaila ma'ana dai sa'annin juna ne Bayan shekara bakwai da haihuwar wannan jaririya sai wani irin gigitaccen ciwon zuciya ya kamata ba irin maganin da basu nema mataba amma yaki yayi aiki har gurin bokaye sunje sunyi musu bayanin irin ciwon Amma kowanne boka sai yace shi baisan maganin wannan ciwoba Amma saboda tsananin soyayya ta da da mahaifa sai suka ki hakura da neman magani Wata rana acikin yawonsu ne suka hadu da wani b oka Bokan yace masa yakai wannan attajiri Ka sani cewa Saidai kayi hakuri domin 'yarka ba zata taba samun lafiyaba Domin mutuwa zatayi amma kayi hakuri abin bauta yayi alkawarin bazai baka kunyaba akan alkawarin daka dauka ba Daga ranar da 'yarka ta mutu aranar zaku sami wata yarinyar wacce zata maye maka gurbin 'yar taka Kuma zaku so juna fiye da yadda kuke soyayya da 'yarku Kuma zata kasance jarumar gaske wacce zata auri dan sarkin garinku wato yarima saiman Sai dai ina mai umartarku daku kira wannan yarinya da sunan da tazo muku dashi Kuma ku tilasta mata akan ta boye jarumtakarta karta bayyana ta ga kowa sai bayan shekaru ashirin masu zuwa alokacin da zasuyi wata tafiya tareda mijinta yarima saiman da wannan bayani sukayi bankwana da wannan bokan suka tafi suka barshi Suka zuba ido suga ranar da maganar wannan bokan zata tabbata Bayan dawowarsu daga wajen wannan bokan da kwana talatin kuwa sai wannan 'ya tasu ciwonta ys kara tsanani sosai Fiye da farko har rai yayi halisa ta mutu suka zubar da hawayen shakuwar da sukayi Amma basuyi kukan da zaisa mutane susan me ake cikiba Attajiri manhas ya fito wajen dakarunsa yace da guda uku ya umarsu suje kasuwa su sayo masa katuwar akatin katako Domin yanaso ya zuba kayansa aciki Take kuwa hadiman suka je kasuwa suka sayo cikin abinda bai wuce sa'a daya ba suka dawo Sannan attajiri manhas ya tashi shi kadai yayi bad da kama ya ha kan doki ya fice ta bayan gidan ya tafi makabarta ya binne 'yar tasa Yakamo hanya zai taho gida kenan sai yaji an kira sunansa ta baya Cikin firgita manhas ya juyo Take yayi arba da aljani lamakus har manhas ya figita zai ruga da gudu kenan Sai lamakus yace saboda me zaka gudu bayan abinda kake nema yana hannuna Cikin rawar murya manhas yace me kake nufi nifa ban gane maganar ka ba Lamakus ya kwantar da jikinsa akasa Take saiga suhaila tayi tsalle ta diro daga gadon bayan nasa Nanfa ya kura mata idanu cike da tsananin mamakin yadda yaga suna matukar kama da 'yarsa kamar an tsaga kara Saidai ita tafi 'yarsa marigayiya kyau sosai saboda tafita haske da shekin fata da kuma gashi Amma hatta tsawon jikinsu dayane babu wani banbanci Take yaji ya kamu da tsananin soyayyar wannan yarinya Tamkar dama can sun dade da sanin juna Itama kuma suhaila tabi attajiri manhas da kallo ya zamana suna ta kallon juna ko kiftawa basayi Aljani lamakus ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa Ya kai wannan attajiri kaine kadai ya kamata ka rike wannan yarinya a duk fadin duniya Don haka ne muka kawo maka ita sannan kuma samun wannan yarinya zai debe maka kewar 'yarka marigayiya Kuma ina tabbatar maka da cewa zatayi biyayya agareka sosai Sannan ya kalli suhaila itama yace Yake 'yata wannan shine lokacin da zamuyi bankwana dake Domin ba zaki sake ganina ba har abada amma ina mai farincikin cikawa iyayenki burin da yake cikin zuciyarsu Sannan ina mai gargadinki cewa kiyi biyayya sosai ga wannan sabon mahaifi naki Da wannan furuci nakeyi miki bankwana sai wani lokacin idan da rabon zamu sake haduwa Yana gama fadin haka saiya bude fukafukansa. Ya tashi sama ya bace bat Yayinda ita kuma suhaila tabi shi da kallo idanunta suna ta zubar da kwalla TABBAS MASU KARIN MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKA CE IDAN AKA SABA DUK RANAR RABUWA SAI JUKATA SUNYI ZAFI ba komai ne ya haddasa wannan hawaye a idanunta ba face Tunawa da tayi da mahaifanta wadanda ta rabu dasu a rana tsaka Sannan kuma gashi yanzu ta rabu da abokinta wanda ta saba dashi sosai Daga can sai attajiri manhas ya rarrasheta yace kiyi hakuri yake 'yata Komai na duniya bashida tabbaci amma yanzu mu zamu yaye miki duk bakin cikin da yake cikin zuciyarki bayan nan saiya umarceta data shiga cikin wannan akwatin Baya ta shiga sai ya ciccibeta ya dorata akan dokinsa Ya kama hanyarsa ta komawa gida Tafiyar rabin sa'a kacal yayi ya isa gida ya kaita turakar da 'yarsa marigayiya take Daga wannan rana suka ci gaba da rainonta kamar sune suka haifeta Soyayya da shakuwa mai tsanani ta shiga tsakaninsu Fiye da wacce take tsakaninsu da marigayya kuma tun daga wannan lokaci Ya dinga samun daukaka acikin arzukinsa Har zuwa sanda ta girma ya bayyana ga jama'ar garin a matsayin 'yarsa ta cikinsa a wannan rana anyi shagali sosai domin saida 'ya'yan manyan attajirai da sarakuna da jarumai saida suka shiga neman aurenta a wannan rana Saboda hakane attajiri manhas yace ta zabi wanda zata aura atsakaninsu Amma saitace ita bata da zabi kawai dai tanaso ta auri wanda yafi kowa jarumtaka akasar Da manhas yaji abinda ta fada saiya je ya fada musu Saboda haka suka shirya gasar fada acan wani daji inda manyan jarumai na nahiyar suka halarta Amma aka rasa wanda yaci gasar face YARIMA SAIMAN Koda tazo nan a labarinta sai idanun yarima saiman suka ciko da kwalla Ya kamu da tsananin tausayinta domin sai yanzu ne yasan asalin tarihin rayuwarta Kuyi hakuri kan dogon lokacin dana dauka banyi muku post ba LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN BAKAR GABA PART 24 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Koda tazo nan a labarinta sai idanun yarima saiman suka ciko da kwalla Ya kamu da tsananin tausayinta domin sai yanzu ne yasan asalin tarihin rayuwarta harsaida hawaye ya zuba daga idanunsa saboda tausayi Suhaila tace Wannan shine tarihina amma ina mai baka hakurin boye maka wannan sirri Dajin haka sai yarima saiman yace Ashe dai bamu kadai bane muke shirya BAKAR GABA acikin zuciyarmu ba Harda ke saboda haka ina mai yi miki alkawarin cewa dole saina daukar miki fansar abinda aljani mafazil yayi miki Adaidai wannan lokaci da suke wannan hirane suka lura ashe har gari Ya waye ba tareda sun ankara ba koda ganin haka sai ya fito Daga cikin tantinsa Yace da jama'arsa gaba daya su shirya yau zasu tafi aiki na karshe Wato birnin hamshak Domin dauko kubar muftahul sihir ko ta halin kaka sannan su dauki fansar abinda yayiwa iyayen gimbiya suhaila Yana gama fada musu haka sai ya shiga cikin tantinsa ya dauko wani garin magani ya watsa acikin bakinsa Sannan yace to daga yanzu bazan kara jin barciba har tsawon wata guda Inda zai daukeni kammala wannan aiki da yake gabana Cikin rabin sa'a jama'ar tasa suka gama shirye shiryensu tsaf Sannan yarima saiman ya shige gaba su kuma suna biye dashi a baya suka nufi hanyar zuwa birnin hamshak +++++++++++++++++++++±++++++++ +++++++++++ Acan filin yaki kuwa inda ake fafatawa da dakarun sarki abu saiman Da dakarun boka ulumanu kuwa abin yayi muni Domin babu bangaren da basajin jiki acikin wannan duk inda sarki abu saiman yasa gabansa saidai kaga dakarun boka ulumanu Suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe a gona Haka shima bangaren boka ulumanu bai tsaya saurarawa dakarun abu saiman ba Hakika tashin hankali ba abin so bane domin komai rashin imanin mutum idan yaga yadda dakarun suke mutuwa kamar annobar mutuwa ce ta fada kansu Jini kuwa ya dinga fallatsi akan kasa kamar an bude idaniyar ruwa Sassan jikin bil'adama ya dinga shawagi asararin samaniya A bangaren manyan gwarazan kuwa sai neman junansu sukeyi amma har asannan sunki haduwa Saida aka kwana kuma aka yini ana wannan yakin amma an rasa bangaren da yake yin nasara Wannan al'amari ba karamin dugunzuma hankalin boka ulumanu yayi ba Domin shi azatonsa baifi cikin sa'a biyuba zasu gama da dakarun birnin ramlatul saif ba Bisa dole duk bangare biyun suka buga kugen tsayar da yaki Kowa ya koma sansaninsu Sannan suka debe gawarwakin jama'ar da suka rasa rayukansu Acikin dakarun sarki abu saiman kaso biyune suka mutu awannan rana Acan bangaren boka ulumanu kuwa kaso uku da rabi ne suka rasa rayukansu a wannan fafatawa Ba komai ne ya baiwa dakarun sarki abu saiman nasaraba face Cewa suna yakin ne da dukkan karfinsu kuma su basu da burin ci gaba da rayuwa a duniya Tunda sun tabbatar da cewa basu da nasara awannan yaki Sannan kuma sunaso su kare martabar kasarsu da kimarta yadda har duniya ta nade baza'a mantada ita ba Awannan rana sunyi farinciki sosai saboda ganin wannan nasara da suka samu Kashe gari kuwa da sassafe dukkan dakarun bangarorin biyu suka sake fitowa filin daga domin ayita ta kare Sannan aka buga kugen ci gaba da yaki Nanfa suka ruga kan junansu suka sake kachamewa da azababben yaki fiye da wanda suka yi ajiya Awannan safiya saida kasar gurin ta dinga jijjiga kamar zata dare biyu Ihun mutane dana karafkiyar karafa ya cika dodon kunne Kowanne bangare ka duba babu abinda zaka gani sai sassan jikin bil'adama Babu abinda zai baka tausayi sama da kaga mutum an sare masa kafafu an barshi da gangar jiki Yana neman taimako amma saikaga memakon a taimakeshi saidai atakeshi abarshi awajen har ransa ya bar jikinsa Ana cikin wannan yakin ne boka ulumanu yaga tabbas neman ayi ragas tsakanin dakarunsa dana sarki abu saiman Da ganin haka saiya umarci dakarunsa da cewa su dasawa dakarun abu saiman tsawa Take kuwa aljanun sukayi tsalle suka tashi sama da nufin su dingayi musu dauki daidai Koda ganin abinda yake shirin faruwa sai shima abu saiman ya karanta wasu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya saiga wata irin wuta ta fito daga cikin bakinsa Ta tashi sama ta dinga bin aljanun daya bayan daya tana konawa Kafin kace meye ta gama kona aljanun kurmus Kuma adaidai lokacin ne dakarun bangarorin biyu sukayi ragas dayansu bai tsira da rayuwarsa ba Ya zamana daga sarki abu saiman sai kuma boka ulumanu Suka dubi junansu kallo wanda ake cewa kar ta san kar Alokacin fuskar boka ulumanu tana wani gyatsine da nuna tsantsar kiyayya Shi kuwa abu saiman saiya bushe da dariya yana mai nuna ulumanu da yatsa yace Kana mamakin ganin yadda akayi ragas tsakanin jama'ata da kuma taka ko? To kadaina mamaki domin shirina ya zarce tunaninka Ni farinciki na kawai shine kada ka sami nasara akan mu cikin sauki Burina kawai shine naga na hanaka cika burinka cikin sauki sannan kuma naga na fitar maka da jini daga jikinka kafin ajalina ya riskeni Don haka saika shirya tarata Yana gama fadar haka saiya falfala da azababben gudu zuwa kan ulumanu takobinsa Na ruke a hannunsa suka ruguntsume da azababben yaki Hakika fadan manyan zakuna daban yake dana kananan karnuka Domin kuwa wannan fadan nasu sai ya zama abin sha'awa ga duk wanda yake da damar tsayawa kallo Duk sanda takubbansu suka hadu da juna saidai kaga tartsatsin wuta yana tashi Tamkar ana hura wuta a makera sai gashi karfinsu yana kokarin zuwa daya Kura kuwa ta tashi kamar ana tada kura Tamkar jikinsu bana jini da tsoka bane ba Saboda har wani tashi sama sukeyi idan suna fadan tamkar tsuntsaye masu fuka fukai saida suka yini suna wannan gumurzu dare ya raba Amma basu daina gumurzun ba tamkar wadanda dama can basa gajiya Har zuwa safiya alokacin ne takubbansu suka dakushe gabaki dayansu Saboda haka sai duk suka watsar dasu sannan suka afkawa junansu da naushi hannu da kafa Nantake kuwa suka hadawa junansu jini da majina Domin wani irin naushi suka dinga yiwa junansu tamkar kayan tsummo kara Nanfa duk suffofin fuskar su ta fara canjawa gaba dayanta duk ta kukkumbura saboda karfin naushi Da alama idan aka ci gaba da wannan fadan a haka to babu wanda zai yi nasa a cikinsu saidai duk suyi kare jini biri jini daga baya kuma suyi ragas Koda yin wannan tunani sai boka ulumanu ya shammaci sarki abu saiman ya debo kasa ya watsa masa ita a cikin idanunsa Take idanun suka rufe ya daina ganin komai kafin yayi wani yunkuri boka ulumanu ya shuri takobin wani mataccen badakare ya jefo masa ita Nantake takobin tazo ta cake ajikin wuyansa Take jini yayi feshi daga jikin wuyan Amma saboda taurin rai kafin ya fadi kasa sai shima ya shuri takobin wani badakaren sannan ya daka tsalle daga inda yake ya a saman ya sarewa boka ulumanu hannunsa guda daya na hagu Nantake ya diro kasa tareda hannun ulumanun Amma duk da haka bai fadi kasa ba sai ya dire akan gwiwarsa ta dama Ta hagu kuma sai ya tsayar da ita ya dora hannunsa na hagu akai Hannun damansa kuwa takobin daya sare hannun ulumanu ce ya caketa akasa tana digar da jini Fuskarsa cike da fara'a yanayin murmushin farinciki har ransa ya fita daga jikinsa Koda boka ulumanu yaga ya rasa hannunsa guda daya saiya kwarara uban ihu Nantake ya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa akan dungulmin hannun nasa don tsayarda jini Nan da nan kuwa jinin ya tsaya a daina jin radadin da yakeji Sannan ya kwarara uban ihu wanda yasa dajin gaba daya ya amsa kuwwa Sai ya waiwaya yaga duk yawan dakarun daya taho dasu sun mutu babu ko guda daya face aljani harisul mar'uf Don haka saiya kwallawa harisul mar'uf kira kafin ya rufe bakinsa ya bayyana Yace to ai mu mungama aikinmu sai kai kuma kazo mu shiga cikin garin domin ka hallaka mana abin bautar tasu Da jin haka sai yace an gama ya shugabana Amma ina fatan kaima ka zama mai cika alkawari Yana gama fadar haka sai ya kunna kai cikin birnin ramlatul saif Ulumanu yana biye dashi abaya tunda suka shiga cikin garin boka ulumanu yaga baiga kowacce irin halittaba mai rai acikin birnin koda kuwa kaza babu har suka karade birnin gaba dayansa nantake ulumanu yace Acikin zuciyarsa to ina mutanen wannan gari suka gudune na nemesu na rasa? Gaskiya ya zama wajibi na bincika madubin tsafina domin na gani da idanuna Yana gama fadar haka saiya zaro madubin tsafinsa Ya shafeshi da hannunsa lafiyayyen take yaga lokacin da mutanen birnin sukayi gudun hijira zuwa wasu kasashen dake nahiyar wasuma barin nahiyar sukayi gaba daya yadda bazai iya binsu

Chapter 11 of 14