Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iya ganin abinda yake faruwa ihun da karajin dodannin ya cika dajin gaba daya karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne bala'i yayi bala'i duk inda su yarima saiman suka danna shida markazulu sai dai kaga dodannin suna zubewa kasa duk da tsananin karfin damtsensu ba komai ya jawo hakaba face tsananin karfin damtsen su yarima saiman da kuma zafin naman su cikin kankanin lokaci suka hargitsa dajin gaba daya cikin sa'o'i kadan suka kashe da yawa daga cikin dodannin koda ganin haka sai dodo garjaju ya kwarara uban ihu sannan ya dakawa dakarun nasa tsawa nan take duk suka fadi suka zama gawarwaki ko daya daga cikinsu bai tsira ba nantake dodo garjaju ya falfalo da gudu izuwa kan su yarima saiman yana zuwa saiya kawo musu mummunan sara da wata siririyar addarsa nantake sukayi tsalle suka tsallake harin nasa koda addar ta karci kasa saita haifar da wani wawakeken rami wanda za'a iya binne mutum goma acikinsa nantake ya fara kawo musu mugayen here hare domin ganin ya hallakasu amma sai abu ya gagara saigashi 'yan kananun halittun daya raina suna kokarin bata masa lokaci koda ganin haka sai dodo garjaju ya shammaci aljani markazulu ya gabza masa wani wawan sara agadon bayansa nantake markazulu ya ya sulale kasa sumamme koda ganin abinda ya faru sai zuciyar saiman ta fusata yaji wani irin gagarumin karfi ya shige shi nantake ya juya suka sake kachamewa da sabon yaki fiye da ko yaushe saigashi yarima saiman yana wata irin jarumtaka taban al'ajabi domin har tashi sama yakeyi kamar tsuntsu yana kaiwa garjaju sara da nufin ya hallakaahi koda dodo garjaju ya gano manufar saiman kuma ya tabbatar da cewa idan har ya bari wannan takobin ta sauka ajikinsa to shikenan anci galaba akansa sai ya kara zage damtse ya hada da kaiwa saiman naushi da bugu da nufin yi masa rotse koda ganin haka sai yarima saiman ya dinga goce goce yana kaucewa harin garjaju duk sa'adda garjaju ya kawo masa idan ya sami gini ko wani abu nantake ya ke ragargaza shi kamar an nika gari shima abinda ya sa ya kasa hallaka yarima saiman shine yarima saiman yana da tsananin zafin nama fiye da tunanin mai tunani duk sanda yakai masa hari kafin harin ya sauka. akansa sai kaga ya goce koda dodo garjaju yaga ya kasa hallaka yarima saiman da karfin damtse sai ya wangame bakinsa nantake wata irin iska mai karfin gaske ta fito daga cikin bakinsa ta suri yarima saiman tayi sama dashi ta dinga wulwulashi asama yana hajijiya acikinta cikin kankanin lokaci yarima ya soma fita daga hayyacinsa koda yaga zai hallaka saiya fara karanta wadansu dalasiman tsafi acikin zuciyar sa faruwa hakan keda wuya sai wannan iskar ta bace sannan ya sauko kasa ahankali bisa turba rike da takobinsa ahannu sai awannan lokacin dodo garjaju ya gane cewa bakomai ne yabaiwa yarima saiman wannan gagarumin karfi ba face wannan takobin sihiri da take hannunsa koda gano hakan sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi koda ya gama karantawa sai aka fara ruwan wasu manya manyan duwatsu masu girman gaske koda ganin hakan sai yarima saiman ya falfala da azababben gudu don gujewa wadannan duwatsu sannan ya fara karanta wadansu dalasiman tsafin domin tsayar da wadannan duwatsu, amma bisa mamaki saiyaga duwatsun sunki su tsaya kamar kara zubosu ake dada yi koda kafinya ankara wani dutse yazo yayi bal dashi yafadi can gefe daya sannan itama takobin ta fadi can gefe daya koda ganin haka sai dodo garjaju ya bushe da dariya sannan yaje ya nuna saiman da dan yatsansa nantake wasu murtuka murtukan sarkoki suka daureshi sannan yaje ya dauki takobin yana mai kyalkyala dariyar samun nasara nantake ya kulle su yarima saiman da aljani markazulu da wata murtukekiyar sarkar tsafi sannan ya sakasu acikin wani katon keji ya tafi dasu cikin gidan sarautarsa WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU YARIMA SAIMAN BAYAN SUN ISA DAJIN AJALI liҠɛ ąŋɖ ĆơmmɛŋŧŞ iŞ ơųř ɛŋĆơųřąɠɛmɛŋ BAKAR GABA PART 9 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Al'amarin su jarumi zamnal kuwa lokacinda suka nufi hanyarda zata kaisu birnin askandariya sai suka wanzu suna masu sauri da gaggawa domin su isa birnin cikin kankanin lokaci sannan su koma izuwa sansaninsu tafiyar sa'a takwas sukayi sannan suka fara hango kofar shiga birnin askandariya don haka sai suka tsaya sannan suka hada hannuwansu waje guda tareda karanta dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai dukkan su suka rikide suka koma siffar fatake sannan kuma jikinsu duk raunika da kagansu zaka zaci cewa sun sha gwagwarmaya akan hanyar tafiyarsu sannan suka nufi kofar birnin tareda hajarsu 'yar kadan koda suka isa bakin kofar shiga cikin birnin koda suka iso dafda kofar sai dakaru masu tsaron kofar birnin suka suka zagayesu tareda zare makamansu ta yadda babu wanda zai iya fita daga cikin su koda ganin haka sai su jarumi zamnal sukaja linzaman dawakansu suna jiran suga abinda zai faru daga can saiga wani badakare kakkarfa wanda shine shugaban masu tsaron kofar ya fito daga cikin kofar birnin yana tafiya cikin jin izza da takama ya fito gaban wadannan dakarun mya tsaya ya karewa su jarumi zamnal ido tsawon 'yan dakiku yana nazari akansu akansu daga can sai yace yaku wadannan baki inayi muku marhaban da zuwa birnin askandariya kuma birnin sarki marhus birnin da babu kamarsa a fannin kere kere awannan nahiya yaku wadannan matafiya shin zan iya sanin daga inda kuke da kuma dalilin zuwanku wannan birni? kodajin wannan tambaya sai jarumi zamnal yace mu fatakene daga can wata nahiyar daban hanyace ta biyo damu ta wani daji dake can bayan birninku ayarinmu yakai mutum dubu hudu to ahanya ne muka gamu da wasu guggun 'yan fashi muka fafata kazamin yaki tsakanin mu dasu suka kashe dukkan abokan tafiyar mu muma da kyar da sidin goshi muka tsira da rayuwarmu muka gudu akan hanyar mune muka zo giftawa ta hanyar wannan birnin saboda haka ne muka bukaci ataimaka mana a barmu mu shiga wannan birni mu dan huta tsawon 'yan kwanaki dan sayi abubuwan da zamu saya mu kama hanya mu tafi izuwa kasarmu koda jin wannan bayani sai shugaban dakarun ya nutsu ya sake kurawa zamnal idanu yana karayin nazarinsa tsawon 'yan dakiku daga can saiya matso gaban zamnal yace ba zamu baku damar shiga wannan birnin ba sai munfara caje kayanku don muga abubuwan da suke ciki koda jin haka sai zamnal yayi murmurshi sannan yace babu matsala jeka dubasu nantake shugaba masu tsaron kofar ya umarci wasu dakarunsa dasuje su duba kayan kafin ya gama rufe bakin nasa tuni dakarun sun fara caje kayan ko zasuga wani abu wanda ba'aso ashiga dashi birnin amma aka rasa 〇 sai gaba dayansu suka dubi shugaban nasu suka fada masa cewa babu komai aciki dajin haka sai ya girgiza kansa yace shikenan abude musu kofa nantake kuwa aka bude kofa suka shiga gaba dayansu sannan aka maida kofar aka rufe lokacinda su jarumi zamnal suka shiga cikin birnin askandariya sai suka sake rikidewa izuwa siffar dakarun birnin hindu sannan suka kama hanya suka shiga cikin gari duk inda suka shiga acikin garin saidai kaga ana kallonsu ana mamakin yadda suka baro can nahiyarsu suka iya zuwa wannan birni alhalin tafiyace ta shekara talatin kuma duk wanda ka kalla acikinsu zamnal zakaga shekarunsa basu wuce ashirin da biyar ba haka dai su zamnal suka dinga kutsawa cikin birnin suna kallon irin gine ginen da akayi awannan birni masu ban sha'awa wadanda suka fita daban da irin gine ginen birninsu nanfa suka kamu da tsananin mamaki suna ayyanawa aransu ce lallai tafiya mabudin ilimi ce wanda bai yi yawon duniyaba bai more kallo ba lokacinda suka iso tsakiyar birnin sai jarumi zamnal yaga wasu matasa guda biyu suna tafiya suna hira abinsu sun fito daga wani dan karamin gida koda ganinsu sai jarumi zamnal ya dakatar da dakarunsa sannan yaje gaban wadannan matasa ya mika musu hannu suka gaisa cikin fara'a sannan jarumi zamnal ya dubesu cikin yarensu yace yaku wadannan matasa mu bakine daga birnin hindu hanyace ta biyo damu izuwa wannan birni naku shine muka hadu daku akan hanya don haka nake neman taimako wajen ku kodajin wannan batu sai daya daga cikin matasan yace kai kuwa wacce irin bukata kake da itaa? jarumi zamnal yace munaso ne ku nuna mana hanyar da zamubi muje kasuwar garin nan? kodajin wannan tambaya sai wannan saurayi yayi murmurshi sannan yace lallai na yarda ku bakine domin na fuskanci baku san tsarin wannan birnin ba aka'idar wannan birni kasuwarsa tanaci ne sau daya acikin kowanne sati tun farkon kafuwarsa domin burin sarakunan wannan birni shine sunason wannan ranar cin kasuwa ta dinga zama ranar tunawa da ranar da aka kafa wannan birni don haka koda kun shiga cikin kasuwar wannan gari ba zaku sami koda kwayar hatsiba koda jin wannan batu sai jarumi zamnal ya girgiza saboda ya fahimci cewa dolene su kwana a garin har zuwa ranar cin kasuwa sannan su sayi abinda zasu siya su kama hanya su tafi izuwa sansaninsu….. yana cikin yin tunani ne daya daga daga cikin matasan ya katse shi da cewa kasuwar wannan birni tanaci ne a kowacce ranar laraba don haka saura kwana biyu kacal sati ya zagayo kodajin haka sai jarumi zamnal ya ce to ko zaku iya nuna mana unguwar da zamu samo gidan kwana domin yada zango kafin ranar cin kasuwar tayi? dajin wannan tambaya sai matashin yace babu damuwa kuzo mu rakaku jarumi zamnal yace to bara naje nayiwa 'yan uwana bayanin abinda ake ci nantake ya juya yaje garesu yayi musu bayanin yadda ake ciki sannan gaba dayansu suka bi bayan wadannan matasa akan hanyar tafiyarsu ne jarumi zamnal ya dubi matasan yace ni sunana zamnal inba zaku damu ba zanso ku fada mini sunanku domin daga yanzu mun zama abokai nida ku daya daga cikin matasan yace ni sunana hasuf sannan ya nuna abokin tafiyarsa yace wannan kuma sunansa zasif ni dashi hassan da usaini kuma wancan gidan da kukaga munfito shine mahaifar mu iyayen mu sun mutu ne sakamakon wani sihiri da wani boka wanda ake kira ulumanu ya jarraba shine sihirin ya fada kan iyayen mu duk suka mutu tundaga wannan rana duk wani mutum idan ya shiga cikin gidan take anan yake daskarewa ya zama kamar kankara daga baya kuma saiya ruburbushe ya mutu alokacinda wannan abu ya faru mu bama cikin gidan mun tafi kasuwa domin sayowa iyayen mu abinci shine muka dawo muka tarar da wannan danyen aiki da yayi mana mu kanmu munyi mamaki da mukaga kowa yana mutuwa ta sanadiyar shiga cikin gidan mu amma mu babu abinda yake samun mu kodajin haka sai jarumi zamnal ya jijjiga kansa sannan yace lallai boka ulumanu babban azzalumi ne kuma nima na samu labarinsa awajen wasu fatake akan hanyar mu ta zuwa nan kuma sunce dani tabbas nan da 'yan watanni za'a haifi jarimin da zai hallaka shi kodajin wannan batu sai su hasuf suka tsaida dakata da tafiya suka sake duban zamnal suka ce yakai wannan bako mai cikar kama dagas ke ne abinda kake fada kuwa? kodajin wannan tambaya sai zamnal yace tabbas maganata gaskiya ce amma ba zaku tabbatar da maganata ba sai idan lokaci yayi kun gani da idon ku suna cikin wannan hirane suka iso kofar wani babban gida zasif ya ce dasu zamnal wannan shine saukar baki kuma mai gidan ya kasance mutumin kirkine shi gidan yana da tsaro sosai ta yadda ba sai anbukaci dakaru masu tsaron lafiyar kuba domin da zarar wani abu ya shiga wannan gida wata mummunaar manufa nantake zai kama da wuta ya kone kurmus wannan dalili ne yasa duk wani mai laifi baya yarda ya kusanci gidan nan kodajin haka sai jarumi zamnal ya yayi murmurshi sannan yace yaku abokai na nida dukka abokan tafiyata muna godiya agareku kuma duk sanda kuke da sha'ar sake ganin kuna da ikon shiga wannan gida nantake suka juyawa su hasuf baya suna masu daga musu hannu suka nufi kofar shiga wannan gida koda sukazo bakin kofar sai nantake kofar ta bude kanta suka kutsa kansu ciki suna shiga cikin gidan sai kofar ta sake kulle kanta suna shiga cikin gidan sai suka yi arba da wani dattijo fuskarsa cike da furfura nantake ya karaso gaban su jarumi zamnal yace inayi muku lale marhaban da zuwa gidan amana yaku wadannan baki ku sani cewa mugu baya taba samun damar shigowa wannan gidan ba tunda ga lokacinda na ginashi kawo iyanzu kodajin haka sai su jarumi zamnal suka rissina suka gaishda wannan dattijo sannan suka ce sunaso ya basu aron dakunan da zasu kwana biyu kacal sannan su kama hanya su tafi subar wannan birnin dajin haka sai dattijon yayi murmurshi yace yaku wadannan baki ku sani cewa bana gina wannan gida bane don neman tara dukiya mai yawa ba na ginashi don saukar mutanen kirki wadanda suka san mutuncin manya tabbas ku mutanen kirki ne domin tun daga sanda kuka shigo cikin gidan nan don nayi muku ragi ku bada dirhami hamsin kacal don haka koda kun karamin ko drhami dayane akan kudin dana bukata to bazan karba ba lokacinda wannan dattijo yazo nan azancensa sai mamaki ya kama su jarumi zamnal sukace aransu tabbas mutanen wannan gari suna da matukar mutumci da karrama bako don haka sai dukkansu yi masa sannan suka kirga darhami hamsin cif cif suka bashi sannan shi kuma yayi musu jagora izuwa cikin gidan ya kai kowa izuwa masaukinsa tareda basu abinci da abin sha suka cika cikin su kasancewar awannan lokaci dare yayi sai duk gaba dayansu suka sami waje suka kama barci abinsu domin huce gajiyar tafiyar da suka sha acikin wannan gida suka kwana biyu kuma kullum sai su hasuf sunzo sun tayasu hira akwana na biyun ne wanda yake shine ranar cin kasuwa sai su jarumi zamnal suka hada kayansu suka fito sukayiwa mai wannan gida godiya daya basu masauki sannan suka fito wajen gidan koda fitowarsu sai sukaga su hasuf sun nufo wannan gida koda suka hadu sai suka gaisa sannan suka dunguma gaba daya suka tafi kasuwar garin tafiyar rabin sa'a kacal sukayi sannan suka isa kasuwar itadai wannan kasuwa ta kasance babbar kasuwace wacce 'yan kasuwa suke zuwa daga sassa daban na duniya suna kawo hajarsu asaya sannan su sayi wata su tafi babu abinda yafi yawa a wannan kasuwar sama da kayan kira, irinsu, takobi, garkuwa, sulke, mashi dadai sauransu mutane suna zuwa suna ta neman abinda suke bukata koda isowarsu wannan kasuwa sai suka wuce kai tsaye izuwa gidan sarkin makera koda zuwansu sai sarkin makera ya taryesu hannu biyu sannan ya tambayesu abinda suke bukata nantake jarumi zamnal ya fada masa suna bukatar keken doki mai inganci kodajin haka sai sarkin makera yace yakai wannan barde akwai wani keken doki guda daya tak agurina wanda jiya jiyan nan muka gama hadashi don haka zo muje na nuna maka nantake ya bishi abaya sukaje yaga keken dokin sannan akayi cinikinsa akan dirhami dubu hudu suka suka bashi kudinsa sannan suka samu kosassun dawakai suka daurawa keken dokin suka fara jansa domin tafiya inda sansaninsu yake kwatsam sai sukaji hayaniya abayansu gami da ihun mutane yara da tsofaffi nantake suka juyo bayansu don ganin abinda yake faruwa ashe wasu guggun 'yan fashi ne suka shigo cikin kasuwar suketa yiwa mutane kwace duk wanda kuwa yayi yunkurin hanawa nantake suke sare masa kansa nanfa mutane suka fara gudun ceton ransu koda 'yan fashin suka kyallara idonsu sukaga keken dokin da su jarumi zamnal suka saya sai suka yo kansu da nufin su kwace keken dokin koda ganin haka sai jarumi zamnal ya zare takobinsa tareda sauran dakarun da suke tareda shi zamnal ya dubisu hasuf yace ku ku koma gefe kada wani abu ya shafeku nantake su jarumi zamnal suka sakarwa dawakansu linzami suka shiga cikin dakarun sumamen nanfa aka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne duk inda su jarumi zamnal suka shiga saidai kaga dakarun sumamen suna zubewa kasa duk da tsananin yawansu sai gashi ya zama na banza domin sun kasa tsinana komai akan su jarumi zamnal wani irin yaki suka dinga yi suna suna hadawa da tsalle tsalle kamar tsuntsaye suna yawo a saman 'yan fashin suna sare musu kawuna cikin rabin sa'a kacal suka gama kashe gaba dayan 'yan fashin adai dai wannan lokacin ne sarki ya iso tareda dakarunsa koda sukaga su jarumi zamnal sun gama kashe 'yan fashin sai ya kamu da tsananin mamaki ya tsaya yana kallonsu daga can sai ya karaso garesu koda ganin haka sai su jarumi zamnal suka durkusa suka gaisheshi sarki marhus ya dubesu yace yaku wadannan baki masu jarumtakar al'ajabi muna godiya da taimakon da kukayi mana sannan kuma ina gayyatarku zuwa gidan sarautata domin karrama ku dajin haka sai jarumi zamnal yayi charaf yakai wannan sarki muna godiya da wannan karramawa taka da kuma wacce mutanen ka sukayi mana amma yanzu bamu da lokacinda zamu tsaya walima saboda shugaban mu yana can yana jiranmu kodajin haka sai sarki marhus yace waye shugaban naku? jarumi zamnal saiya sake rissinawa yace kayi hakuri ba zamu iya fada maka ba amma nan da 'yan wasu shekaru masu zuwa kaida kanka zakasan shi jarumi zamnal suka sukayi ban kwana dasu hasuf sannan suka juya suka tafi suka bar birnin askandariya tafiyar sa'a takwas sukayi kamar farko sannan suka isa sansanin su da zuwa sai suka kwankwasa kofa lokacinda suka kwankwasa kofa sai wani badakare yazo ya bude musu kofa suka shige WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA SU JARUMI ZAMNAL BAYAN SUN JE SUN SAYOWA GIMBIYA SUHAILA KEKEN DOKIN DA ZATA HA BAKAR GABA PART 10 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR al'amarin su yarima saiman kuwa lokacinda dodo garjaju ya kamasu ya kulle acikin keji ya shiga dasu cikin gidan sarautarsa bai zame ko inaba sai cikin wani katon dakinsa wanda yake kulle masu manyan laifuka aciki shidai wannan daki an ginashine da zallan duwatsun wuta babu wata halitta data taba shiga cikinsa ta fito araye tun daga sanda aka gina wannan daki yana zuwa sai ya ajiye su agefe daya amma bai fito dasu daga cikin wannan daki ba sannan ya tsaya ya kura musu ido sosai yana kallonsu koda ya kalli fuskar aljani markazulu sai fuskarsa ta fara gyatsine kamar an aiko masa da sakon mutuwa saboda sanin cewa shine ya kashe masa dansa nantake yaji kamar ya zura hannu acikin kejin ya zaro shi ya wulla abaki ya cinye amma saiya fasa saboda yasan babu abinda zaiyi ya huce bakin cikin daya darsa masa azuciya harsai yayi masa hukuncin da yayi alkawarin yi tun farko sannan ya kalli yarima saiman yace lallai wannan yaro anyi hatsabibin gaske tunda nake aduniya ban taba haduwa da halittar da muka shafe dakiku biyar muna yaki da itaba face na hallaka ta amma sai gashi na dau lokaci mai tsawo ina yaki da wannan karamin halittar inda badan nayi da gaskeba da zai iya samun nasara akaina yana zuwa daidai nan azancen zucinsa saiya fice daga cikin dakin ya janyo kofa ya rufe bayan fitarsa da kamar rabin sa'a sai su yarima saiman suka farfado suna farfadowa sai suka tsinci kansu acikin kejin karfe aljani markazulu ne ya fara farfadowa sannan saiman shima ya farfado koda ya farfado kuma ya kalli gefensa yaga yarima saiman kuma ga sarkoki an saka masa hannu da kafa sai kuma ya tabbatar da cewa bazasu taba tsira ba daga sharrin dodo garjaju ba sai nantake nadama tazo masa don ya fuskanci yarima saiman bazai iya cetonsa ba koda yarima saiman yaga markazulu ya zurfafa cikin tunani sai yayi murmurshi sannan ya dube shi yace yakai abokina kaga yadda rayuwa ta juya damu ko? to haka duniya take yau nasara tana gareka gobe kuma tana hannun waninka abinda nake nufi dakai shine duk sanda zakayi wani aiki kasa gaskiya acikin zuciyar ka duk lokacin da ka sami wani aboki na zaman gida ko akan hanya ka zama mai gaskiya 'yan uwanka zasu zama masu kaunarka da girmamaka afadin duniya munafuki baya zama mai nasara mai gaskiya kuwa duk irin tsananin wahalar daya shiga baya taba faduwa kasa don haka inaso ka sani tun afarkon tafiyar na san cewa kazone da nufin ka tayani yakar dodo garjaju mu debo tsuminsa tare dakai idan muka gama kai kuma sai kaci amanata ka kasheni duk da yanzu nasan cewa kai da kanka kasan nafika duk irin abinda kake takama dashi walau karfin damtse, iya yaki da sanin tuggunsa ko sihiri babu wanda ban fika ba domin ka gani da idanunka duk wani motsi da kakeyi tamkar atafin hannuna kakeyinsa to yanzu na fuskanci tunanin da kakeyi na nadama ne bisa ganin ni cewa ni dakai gaba daya zamu hallaka ba tareda mun sami ribar komai ba acikin wannan tafiya shin wannan hali daka shiga bazaisa kayi madaba akan abinda kake shirinyi? dajin haka sai hawaye ya zubowa markazulu yace tabbas maganarka gaskiyace na yarda da duk abinda ka fada kuma nayi nadama akan duk abubuwan danayi arayuwata abu daya ne kawai banyi nadamarsa ba wannan abu kuwa shine bijirewa boka ulumanu da nayi tabbas boka ulumanu ya sakani zalunci wadanda bansan adadinsu ba bansan adadin mutanen daya sakani na hallakabA duk irin bakin halin dana kowa to awajensa na samo iliminsa tabbas ko yanzu idan na mutu bazan taba yafe masa ba yarima saiman ya tashi ya matso kusa da markazulu yadda suna iya kallon juna sannan yace naji dadi da wannan magana taka amma ina mai tabbatar maka da cewa ni ba zan mutuba awannan gida kuma kaima ba zan bari ka mutuba tare dakai zamu fita dajin haka sai markazulu ya dubeshi cikin rashin yarda yace tayaya kake maganar zamu fita daga nan alhalin nida kai duk mun zama fursunoni? dajin wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace ai tun daga lokacin dana bar gida na fara tanadin zuwan wannan rana don haka sai ka zuba idanu zaka gasgata zancena suna cikin yin wannan saiga babban dan dodo garjaju nan ya shigo wato jurishan tareda kannensa sunzo don suga halittun da suka wahalar da mahaifinsu akaron farko na rayuwarsa koda suka gansu 'yan kananu sai suka bushe da dariya suna nunasu da dan yatsa suna cewa wadannan sune suke ganin zasu iya ja da mahaifin mu lallai sun yaudari kansu abubuwan da basufi mu sa kafa mu talitsesu ba dajin haka sai ran markazulu ya baci yana daga cikin kejin ya tofawa wani dodo yawu afuska da ganin haka sai ragowar dadannin suka fusata suka kafa zasu fasa kejin sai suka jiyo mahaifinsu yana daka musu tsawa nan take kuwa suka dakata da abinda suke shirin yi garjaju ya karaso gabansu ya kwadawa jurishan mari sannan yace daga yau kada ka sake janyo 'yan uwanka ka kawo su gurin wadannan fursunoni domin suna da matukar hatsari koda kannen jurishan sukaga yadda mahaifinsu ya zabgawa jurishan mari duk sai suka kyalkyale da dariya alokacinda shikuma hawaye ya zubo masa kenan sannan ya juya ya fice daga cikin dakin mahaifinsu yana biye dasu abaya sannan ya janyo kofa ya rufe fitarsu keda wuya sai saiman ya dubi markazulu yace kaga wannan abu daya faru? markazulu yace wannan wacce irin tambaya ce ni da ba makaho bane taya zan kasa ganin abinda akayi saiman yace to duk wannan da kake gani yana daga cikin irin tsare tsaren da nayi akan wannan tafiya nan gaba shi da kansa zai dawo nan domin mu hada kai dashi kuma ka zuba ido ka ga abinda zai faru haka dai sukayita fadi in fada har dare yayi barci ya sacesu basu saniba al'amarin dodo jurishan kuwa lokacin da suka fito daga cikin dakin tsaron fursunoni saiya wuce izuwa bayan gidan sarautar tasu cikin bacin ran abinda mahaifinsu yayi masa agaban kannensa da kuma yadda suka dinga kyalkyala masa dariya sai hawaye ya zubo masa yace amatsayina na babba a wannan masarauta ni mahaifina zaiyi wa haka alhalin ko a yau ya mutu nine zan haye kan karagar mulkin kasar nan lallai sai mahaifina ya gane kuskurensa sai dai inyaso ayi biyu babu ko dai ni na hallaka ko shi mahaifin namu ya mutu ni ban damu da wata karagarsa abinda na damu dashi kawai kimata da mutuncina dolene mahaifina yayi nadamar abinda yayi mini yana zuwa daidai nan azancen zucinsa sai ya mike tsaye ya koma cikin gidan sarautar kai tsaye ya wuce izuwa cikin dakin da aka kulle su yarima saiman ya bude ya shiga ciki yana zuwa sai ya tarar dasu duk sunyi barci ya zura hannunsa ya tabasu suka farka daga barcin da sukeyi firgigit cikin tsoro aljani markazulu ya mike domin azatonsa kashe su dodo jurishan yayi koda ganin haka sai yarima saiman yayi murmushi sannan ya ruko hannunsa yace ka nutsu mana tsoron me kake ji ka nutsu kaga abinda yazo dashi mana dodo jurishan ya kallesu cikin nutsuwa yace yaku wadannan jarumai ku kwantar da hankalinku nasan duk irin bukatarda kuke da ita kuma ni zan taimaka muku don na huce bakin cikin abinda mahaifina yayi mini ammafa ku sani koda na same ku sani koda na samo muku shi dale sai kunyi da gaske wajen kasheshi domin ba karamin hatsabibi bane koda jin wannan batu sai yarima saiman yace yakai jurishan nasan cewa kai kana da sabanin ra'ayi da mahaifinka don haka nayi maka alkawarin idan har ka samo mana tsumin tsafinsa ba zamu bari ka hallakaba kuma kaine zaka gajeshi dajin haka sai jurishan yayi murmushi yace ni koda ban sami gadon mahaifina ba abinda nake da bukata kawai shine ku hallakashi domin mu huta da bakin mulkin da ya dade yana yi mana yana zuwa nan azancensa saiya juya ya fice daga cikin dakin fitarsa keda wuya sai yarima saiman ya kalli markazulu yace na dade da cusa kiyayyar dodo garjaju azuciyar dansa jurishan domin tun sanda muka baro gida nake tura masa da mugayen labarai akan mahaifinsa sannan na sanar dashi cewa mahaifinsu ne ya kashe mahaifiyarsu amma duk wannan abu da nakeyi ban taba zuwa masa acikin siffata ba ina zuwa ne awata siffar daban bana zuwar masa a siffata don haka jurishan shine zai zama makamin mu awannan lokaci al'amarin dodo jurishan kuwa lokacin da ya fita daga dakin tsaron da aka kulle su yarima saiman sai ya wuce izuwa dakin da mahaifinsu ya ajiye tsumin tsafinsa shidai wannan daki yana wani bangare ne na cikin gidan babu mai iya shiga cikinsa sai 'ya 'yan dodo garjaju domin ya lamuncewa kowa ya shiga ciki yayi duk abinda

Chapter 5 of 14