Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutuwa. sannan yace yakai gwarzon shekara mahaifiyarka bazata taba samun lafiya ba hsar sai kaje kowanne bakgare na duniya ka samo mata wasu tsumummuka ka hada su waje daya ka bata tasha sannan zata sami lafiya kamar babu abindaya sameta. sai kaje ka samo wadannan abubuwa sannan zakayi shirin tunkarar boka salban kodajin haka sai harisul mar'uf ya ta karkare ya kwarara uban ihu yace narantse da darajar hawayen mahaifiyata saina samo mata wadannan tsumummuka koda zan rasa rayuwata sannan na yanko kan boka salban na tsireshi atsakiyar birnin da yafi kowanne birni yawan matsafa don hakan ya zamo gargadi agaresu. dajin haka sai boka garman yace ina da wani taikako da nakeson baka na wani sihiri mai karfin gaske wanda zai kareka dga dukkan wani hatsari da tsautsayi. sai harisul mar'uf yayi murmushi ga boka garmana sannan yace ina da takobin da indai ina tare da ita zata dinga bani kariya.don haka daga yau abzamu sake haduwa ba ni dakai sai ranar da naje na samo wannan magani. kuka daga yau mun kulla bakar gaba da boka salban. koda gama fadin haka saiya bude fuka fukansa ya tashisama ya luka acikin gajimare cikin azababben gudu na gaban kwatamce. duk inda ya gifta ya tarar da wani ayari na aljanu da sun ganshi saidai kaga sun chanja hanya saboda tsananin kwarjiinsa. idan kuwa tarom yan fashine cikin kankanin lokaci yake tarwatsasu. sai daya shafe kwanaki bakwai yana tafiya sannan ya iso bakin wani birni na aljanu don haka ya yanke shawarar ya shiga wannan gari ya kwana idan gari ya waye sai ya kama hanya ya cigaba da tafiyarsa. nan take kuwa ya sauka abakin kofar wannan kasa sannan ya matsa gaban kofar ya kwankwasa. bisa mamaki sai wani aljani ya leko yan cewa wannan wanne me karar kwanane yake bugu mana kofa alokacin da muke morewa da kyawawan matanmu?kowanene ya gaggauta juyawa da baya tun kafin fishina ya sauka akansa. koda wanna me tsaron kofa yazo nan a zancensa sai ran aljani harisul mar'uf ya baci.amma saiya basar yace nine harisul maruf wanda yake neman mutuwa da kudinsa kuma akoda yaushe. dajin haka sai ran mai tsaron kofa ya baci. nan takekuwa ya bude kofar wannan kasa. sai dakaru sukayita fitowa da makamai iri iri tamkar duniyar zasu yaka. bayan wadannan dakaru sun gama zagaye harisul maruf sai sukayi kukan kur suka afka masa da sara da suka.cikin tsananin zafin nama d ajuriya da bajinta nan take aljani harisul mar'uf ya shiga kai sara da suka cikin salo irin an manyanyan jarumai. cikin kankanin lokaci ya karar dasu ya zamana saura shugabansu. nan take kuwa shugaban masu tsaron kofar ya ruga aguje domin ya fadawa sarki abindaya faru. tafiyar keda wuya sai sai harisul maruf ya matsa gaban kofar wannan birni wacce takeda girma sosai.idan ta fadi sai an sami manyan giwaye guda dari biyar sannan zasu iya dagata.yasa kafarsa ya doki kofar. nan take kuwa wannan kofar ta rufta ciki. kuma adai dai wannan lokacin ne sarkin wanna garin ya iso. koda yaga abindaya faru sai ya kwarara uban ihu. Koda yaga irin muguwr barnar da yayi masa sai ransa yayi matukar baci tare d kwalla ihu. domin bincike ya tabbatar da cewa aduk lokacin d wani sadauki ya balla wannan kofar to daga ranar to daga bashi ba mulki acikin kasar harsai ya nemi hadin kan wannan sadauki sun tari masifar d zata afko musu. nan take kuwa ragazalu yasa hannu ya finciko sarkin kofa sannan ya dubeshi yace ka jawo mana bala'in da bamu taba shigaba,tundaga sanda aka kafa wannan kasa,tunda ka janyo mana sadaukin aljanun duniya harisul mar'uf,don haka hukuncinka shine kisa. nan take yasa takobi ya datse masa kai,sannan yayi wurgi da gawar,tare da bawa dakarubsa umarnin suyi mubaya'a ga harisul maruf nan take dakarun suka cika umarni sannan sarkin ragazalu ya tao da kafafunsa yazo gaban harisul maruf yayi mubaya'a tare da fadin kagafarceni ya sadukin duniya bisa irin tozartar da akayi maka acikin kasata. bakomai ya jawo hakaba face tsaurin ido rin na sarkin kofa, yakai wannan babban jarumi dagani har jama'ata mun mika wuya agareka,kuma muna neman taimakonka sakamakon karya alakadarin kasarmu dakayi na balla mana kofa, kuma bincike ya nuna cewa daga lokacin da aka balla wannan kofa zaman lafiya zai kare a wannan nahiya,sakamakon kawo mana farmaki da kasashen ahokan gaba zasu dingayi badon komaiba sai don su mallaki dukiyarmu ta dangin zinare da lu'u lu'u yanzu haka.maganar da nake maka wasu kasashen sun fara shirin kawo mana mamayar bazato yau ko gobe. lokacin da sarki ragazalu yazo nan azancnsa sai ya fashe da kuka, al'amarin da yasa zuciyar harisul mar'uf tayi sanyi kenan don haka sai yadubi sarki ragazalu yace yakai wannan adalin sarki zan taimakeku,saboda banason ganin anzubarda jinin wanda baijiba bai ganiba. don haka nayi alkawarin taimakon mayakanku,don haka yanzu sai kuyi shirin gyara kofar wannan gari tun kafin abokan gaba su cimmaku. koda sarki ragazalu yaji haka saiya kamu da tsananin farinciki sannan ya umarci wani badakare da yaje yayi shelar ana neman duk wani magini da yake cikin kasar da ya hallara abakin kofar wannan birni nan take kuwa wannan badakare angama ya shugabana sannan ya bace. kafin cikar.sa'a biyu duk wani magini ya hallara sannan sarki ya basu umarnin fara gini kafin cikarsa'a bakwai sungama gini wannan kofa sannan aka aka dada kara dakarun tsaro ako ina acikin garin aka cigaba da jiran ta inda dakarun zasu bullo a.haka.suka.kasance cikin shigar yaki taban tsoro. saida suka shafe yini guda sannan abokan gaba suka iso. awannan rana anyi gagarumin yakin da ba'ataba kamrsaba awannan nahiya.sannan anyi asarar dukiya mai tarin yawa. bisa dole kowanne bangare yajanye dakarunsa gaba daya. tundaga wannan rana kasashen dake duniya suke matukar tsoron wannan birni saboda arin sa'ar da suka samu awannan yaki. a zatonsu har yanzu harisul mar'uf yana cikin kasar. wash gari kuwa da sassafe harisul mar'uf yatashi yabar kasar bayan sunyi sallama da sarkin garin da yan majalisarsa. sannan yanausa cikin gabashin duniya don nemowa mahaifiyarsa magani, sai da yayi tafiyar shekara guda sannan ya iso dajin da yake dagashi sai bangon duniya.na gabas saboda haka sai harisul mar'uf ya zaro sihirtacciyar takobinsa dake daure a kugunsa. sannan ya zaro wata yar taswira wacce ya samu agurin sarki ragazalu yabudeta ya duba. nantake yayi arba da wani kogo acikin taswirar,wanda yake nuni da shine hanyar da zata kaika bangon duniya nagabas. nantake kuwayasake bude fukafukansa yana mai kusantar kogon kai tsaye. yana shiga cikin kogon sai yayi arba da wata yar siririyar hanya wacce take da tsananin nisa. nantake kuwa ya nufi wannan hanyar kai tsaye yana mai gyara rukon takobinsa. kwatsam sai yayi arba d wata bakar kunama wacce ta tokare hanyar kogon gaba daya.sannan wannan kunamar tasa kafa ta daki wani dutse da kafarta guda daya nantake kuwa wannan dutse ya gangara yaje ya toshe hanyar da harisul maruf ya shigo. mai makon ma harisul mar'uf ya firgita sai abin ya bashi mamaki don ganin irin wannan azababben karfi irin na wannan kumama. bakomai yabashi mamakiba face gani yadda ta iya ture wannan dutse da kafarta daya. alhalin inza'a tara manyan aljnu guda ashirin bazasu iya mirgina wannan dutseba. yana cikin wannan tunanine yaji kunamar takawo masa harin bazato. cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle ya koma gefe daya don ya soma tunanin ta hanyar dazai bullu mata. nanfa aka soma kallon kallo tsakanin sa da wannan kunamar na tsawon yan dakiku.daga chan sai harisul mar'uf ya nufi kunamar cikin mugun nufi, suna haduwa aka ruguntsume da masifaffen yaki nagaban kwatance suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka. shidai yana amfanine da takobin sihirinsa ita kuma tana amfanine karinta da kuma hannayenta wajen kai masa hari. duk sa adda harisul maruf ya sari jikin kunamar sai sai yaji kamr dutse ya sara. ita kuma kunamar duk sanda ta kawo masa hari ya kauce duk abindata samu nan take yake ruburbushewa ko kuma ta haddasa wawakeken rami. sai da suka shafe sa'a guda suna fafatawa,sannan kunamar ta sami nasarar yankan harisul mar'uf agadon bayansa. nantake harisul mar'uf ya kwalla ihu.saboda zafi da zugin da yaji.cikin tsananin dauriya ya daka tsalle tsalle kamar daga cikim baka aka wullashi ya fada kan gadon bayan kunamar sannan ya caka mata takobi a ido. nan take kuwa idon kunamar ya fashe jini yayi tsar tuwa.nantake kunamar ta haukace ta dinga kawo masa mugayen hare hare LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) LITTAFIN BAKAR GABA PART 3 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR nan fa wannan fada ya dawo sabo kogon ya soma girgiza tamkar zai ruguje. cikin dan kankanin lokaci aljani harisul a fita daga hayyacinsa saboda tsananin wahalar da yakesha awajen kunamar. saidaya zamana yakasa maidawa kunamar da martani saidai yunuri kare kansa kawai yakeyi. koda aka shafe wata sa gudar sannan harisul mar'uf yasami nasarar cakawa kunamar takobi atsakiyar wuyanta. nantake kunamar tafadi kasa ko shurawa batayi ba. sannan shima ya fadi kasa sumamme. sai bayan sa'a uku sannan ya farfado daga suman da yayi. yana farfadowa ya tuna da ciwon dake gadon bayansa nantake yadauko magani daga cikin jakar guzurinsa.yazuba aciwon dayake bayansa.sannan ya tashi yagyara damararsa ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga wannan kogo,sai bayan yan dakiku sannan yafita daga cikin kogon. yana fita yayi arba da wani tafkeken daji mai matukar kwarjini daban tsoro, shidai wannan daji yakasance babban daji mai dauke da ababan tsoro, don hatta bishiyoyin dajin siffofin dodanni ne dasu, kuma awannan lokaci rana ta bude.hakanne ya haddasa wata iriyar zazzafar iska acikin wannan daji. duk haka baisa harisul mar'uf tsoroba ya dada kutsa kansa cikin dajin cikin azabbaben gudu acikin sararin samaniya da nufin ya wuce ta saman dajin. kwatsam sai yaji tamkar an ruke fuka fukansa yadda bazai iya motsa suba. bisa dole yaci burki asama don yaga abin da zai faru. yanacikin wannan haline yaji wata kakkarfar iska ta zukoshi kasan wannan dajin. alokacinda wannan iska ta sauke harisul mar'uf akasan wannan dajin. kwatsam sai yayi arba da wasu manya manyan macizai masu matukar ban tsoro. sudai wadannan macizai adadinsu yakai dubu daya.haka girman kowannensu yakai giman bishiyar dabino haka kaurinsu yakai bishiyar kuka. idanunsu kuwa tamkar angasa dan buda a wuta. alokacin da wadannan macizai sukaga harisul mar'uf asararin samaniya sai suka bace tamkar basu taba wanzuwa ba,sannan itama wannan iskar ta dauke tamkar bata taba samuwaba. kuma alokacin ne harisul mar'uf ya daina ganin macizan. al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan sannan ya fara tunanin irin masifar da take cikin wannan dajin,domin yasan ta hanyar dazai bullu musu. gashi kuma azahiri yaga halittu agun amma yanzu kuma yaga basa wajen yanzu. nan take azuciyarsa kawai ya shiga dajin kai tsaye,amma ya dinga kula da motsin kowacce irin halitta ya gani. sannan ya zaro takobinsa ya kutsa kansa batare da fargaba ba. awannan lokaci rana ta bude tamkar zata gasa masa kansa. sai dayaje tsakiyar dajin sannan kasa ta fara tsagewa tamkar zai rufta cikinta,bishiyoyi suka soka karyewa,duwatsu suka dinga mirginawa. kwatsam sai harisul mar'uf yayi arba da wadannan macizai suna saka shi atsakiya yadda babu wanyar da zai iya wucewa. daya daga cikin macizan ya sari wani dutse dake kusa dashi,nantake dutsen ya rbe gid biyu wata bakar kumfa tayi tsartuwa daga bakin macijin. alokacin da wannan abu ya faru harisul mar'uf yana tsaye yana kallon ikon allah. kwatsam sai wadannan macizai suka taso masa da harbi suna wani irin kuka mara dadinji. nantake aka ruguntsume da azababben yaki nagaban kwatance yana zamana suna masu kaiwa juna sara da amakamansu. shidai harisul mar'uf yana amfni da takobinsa. su kuma suna kai masa harin da bakinsu dakuma jelarsu,wajen kai masa sara, nanfa guri ya rincabe da hucin macizai saboda tsananin bala'i, cikin kankanin loakci suka hargitsa dajin da buge buge. duk sa'ar da suka kawo masa duka ya kauce duk abinda suka samu nan take yake ruburbushewa, idan sara suka kawo masa da bakinsu idan ya kauce suka sami kasa,nan take suke haddasa wawakeken rami mai zurfin gaba biyar. shikuwa harisul' maruf saran macizan yake baji ba gani.wani lokacin idan ya daki daya daga cikinsu sai kaga kamar an janshi da majaujawa,duk da irin wannan girma nasu, hakika jarumataka baiwace duka wanda allah ya bawa ita ya dace kaduba girma irin na wadannan halitttu amma sai gashi aljani guda daya yana neman rinjayarsu. lokacin da gumurzu yakai gumurzu sai macizan suka fuskanci nasarar da yake samu akansu sai duk gaba dayansu suka ja da baya suka tsaya ana kallon kallo atsakaninsu. shidai harisul mar'uf game da wadannan macizai shine. dukda yana samun damar saransu da sukarsu amma daya daga cikinsu yaki ya mutu saboda tsananin taurin eansu. sukuma macizan shine suna tunanin hamyar da zasubi su hallakashi cikin sauki batare daya sami nasarar hallaka daha daga cikinsu ba. nantake kamar hadin baki suka sake afkawa kan juna da azabben yaki wanda yafi na farko. awannan lokacin suaknsu macizan sai suka chanza salon fada suna masu kai da kansu da jelarsu lokaci guda. duk sa'adda ya kauce duk abinda suka samu nan take yake ruburbushewa ya zama kamar gari. ana cikin hakane wani maciji mai matukar sa'a ya shammaci harisul mar'uf ya gabza masa jelarsa agadon baya, saboda tsananin karfin dukan sai da harisul mar'uf yayi sama ya gwaru da jikin wani katon tsauni. nan take wani gudan jini yayi fitar burgu daga bakinsa,sannan yaji gaba daya jikinsa yadau zafi. ya mike tsaye tare da gyara tsayuwaarsa. nan take ya sake rugawa izuwa kan wadannan macizai,cikin mugun nufi yana mai karaji da kuwwa yana mai kai sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta fiye da farko. a wannan lokaci sai ya canja salon yaki ya koma kai sara a tsakiyar makwallaton wuyan macizan,cikin sa'a kuwa wadannan macizai suka fara halaka,ihun su da rurinsu ha cika dajin baki daya. babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda harisul mar'uf yake hallaka wadannan macizai farat daya. wani lokacin ma har tsalle zakaga yanayi akan kawunansu yana wasa da hankalinsu. cikin kankanin lokaci yagama hallakar dasu baki dayansu. sannan ya tashi ya bude fukafukansa ya luluka acikin sararin samaniya,yanufi hanyarda zata kaishi karshen dajin. sai da yayi tafiyar sa'a biyu, sannan yayi arba da wata siririyar gada wacce farkonta wasu gumakan dodanni ne akame. kasan gadar kuma wutace takeci wani lokacin ma.idanta lashi gadar sai wani turirin hayaki ya tashi sama. adaidai inda harisul mar,uf yake ga wani dan karamin allon sanarwa an rubuta. yakai bakon wannan daji ka sani . wannan itace gadar da zata sadaka da abin da kazo nema.dolene kabi ga kanta kaje karshenta sannan zaka sami abinda kake nema. wadannan gumakan daka gani ba gumaka bane dodannine bazasu taba mutuwaba face kaje karshen wannan gada kadau abinda kake nema. yana gama karanta wannan allo sai ya sakejin wannan iska ta sake zuko shi kasan dajin baga ajiyeshi ako inaba sai bakin wannan gada.tazarar dake tsakaninsa da iga bata wuce taku dayaba. kuma har awannan lokaci wadannan dodanni suna cikin siffar gumaka. kawai sai harisul mar'uf ya daga kafarsa ta dama ya dorrta akan gadar kawai sai yaga idanun wadannan dodanni ya bude,alamar cewa ruhinsu ya soma dawowa. batareda tsoroba ya sake dora kafarsa ta hagu kan gadar. nantake wata irin walkiya ta baiyana ta haskake dajin baki daya dukda cewa ranace ba dareba. walkiyarna daukewa ruhin wadannan dodanni ya dawo. nan taki suka biyo harisul mar'uf abaya,nanfa suka kasa tseren gudu dashi domin su kamashi su hallakashi. wohoho dan kaji ance ga k gudu to sa gudune baizo ba. ana fara wannan tseren gudune gadar da su ke kai ta soma girgiza kamar zata karye. bakomai ya janyo hakaba face tsananin karfin takunsu. saida suka wuce sa'a uku sannan suka iso tsakiyar gadar,inda nanne wutar tafi gasawa, nanfa tsananin zafi ya soma ruda harisul mar'uf inda matukar galabaitar dashi kenan hartakai cewa,baya iya gudu sosai. cikin kankanin lokaci wadannan suka iso inda harisul ma'uf yake. cikin shammace daya daga cikinsu yasa kafa yayi bal dashi. sabo da karfin dukan sai dayayi sama kamar anjanyeshi da majajjawa ya tafi kamar zai fada cikin wutar amma sai ya wulkila jikinsa ya rike karfen da akayi gadar dashi. da hannunsa na dama sannan yadawo kan gadar akaci gaba da tseren gudun atsakaninsu. a lokacinda wannan abu ke faruwa sai gadar ta fara girgiza tana neman tsinkewa. koda dodannin suka lura da haka sai gaba dayansu sukayi tsalle suka sha gaban harisul mar'uf suna masu kaimasa duka da kafafunsu nantake kuwa suka rikirkita saboda tsananin zafin namansu,da kuma karfin damtsensu. koda aka dau tsawon lokaci ana wannan artabu sai ya fuskanci. tabbas idan aka dau tsawon lokaci ana wannan artabu tabbas zai iya hallaka. koda yagama wannan tunani sai yayi yataka kan daya daga cikin dodannin cikin azababben gudu yadinga tafiya akan kawunansu harya isa kan na karshens.sanna ya sauka izuwa kan gadar yana tsala gudu fiye da farko saigashi awannan lokaci yayiwa dodannin mugun nisa. sai bayan sa'a daya sannan ya fara hango wata yar karamar bishiya.adaidai kuma wannan lokaci gadar da suke kai ta tsinke.. cikin zafin nama harisul mar'uf wani itace da akayi gadar dashi ya dinga kamawa yana hawa sannan ya iso karshen gadar. yannzuwa karshen gadar ne ya hango dodannin sunyi wani irin tsalle suna kama gadar. koda ganin hakan sai harisul mar'uf yayi tsalle ya haye kan wannan wannan bishiya sannan ya tsinko wata ciyawa dake kana bishiyar. yan tsinkar ciyawar yaga duk gaba daya dodannin sun kama da wuta sun kone kurmus koda boka ulumanu yazo nan a labarinsa saiyaga gaba daya hadiman sun nutsu suna sauraronsa. da ganin haka sai yayi dariya sannan yace wannan shine takaitaccen tarihin harisul mar'uf bayan bukata ta biya zan karasa muku tarihin nasa. yana gama wannan magana sai duk gaba dayan hadiman sukai sujjada agareshi suna masu cewa. nasara ta tabbata agareka ya sarkin matsafan duniya.... kafin sukarasa maganar tasu boka ulumanu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba. +++ ++++ ++++ ++++ wannan shine abinda ya faru afadar boka ulumanu mai shirin mulkar duniya. al'amarin yarima saiman kuwa alokacin da suka kutsa kai izuwa cikin wannan daji sai suka kasance cikin suna masu tsala azababben gudu nagaban kwatance tamkar zasu fita daga duniyar gaba daya. basu tsaya da tafiyaba saida suka fuskanci dare yayi sannan suka yada zango awani daji mai matukar duhuwa. a sannan ne yarima saiman ya umarci dakarunsa dasu tsaya da tafiyar d suke. nantake kuwa suka cika umarni. wani badakare mai suna zamnal ya matsa kusa da yarima saiman yace yashugabana ni aganina bai kamata mu yada zango awannan dajiba domin baza'a rasa mugayen namun daji acikinsa ba. dajin haka sai yarima saiman ya juyo ya dubi zamnal yace shin baka ganin muna tafiyane tare da mata,yara da tsofaffiba? kasani tafiyarmu dasu awannan yanayi yafi hatsari akan zaman mu a wannan daji. saboda haka ina umartarku dakuje ku kafa mana tanti inyaso gobe da safe sai muci gaba da tafiya. dajin haka sai badakaren yace angama ya shugabana. sanna ya tafi ya umarci yan uwansa dasu kafa tantunan da za'a kwana aciki. sannan wasu kuyangi sukaje suka shirya musu abincin da zasu ci.aka mikashi ga kowanne tanti. bayan angama shirya komai sai yarima saiman yafito ya dubi dakarunsa yace yaku yanuwana duka gaba dayanku kunsan abindaya baro mu daga gida. adalilin hakane na yanke hukuncin da nake ganin shine zai amfanemu.wannan shawara itace ni banaso ko mutum daya daga cikinmu ya mutu,domin yin hakan babbar asarace agaremu. shawara ta farko dazan baku itace kada daya daga cikinku yace zai tayani fada da duk irin abinda kukaga na hadu dashi. shawara ta biyu itace aduk inda kuke ku kasance kuna tare da juna koda kuwa wani abin tsoron kuka gani,muddin bagani kukayi zaku hallaka gaba daya ba. shawara ta uku itace aduk inda muke kada mudinga yin barci gaba dayan mu idan dare yayi,saidai midinga raba dare. aduk sanda wani ya nemi taimako to mu taimaka masa koda bai kasance dan kabilar mu ba. idan mukayi riko da wannan shawara to tabbas bukatarmu zata biya. da wannan kalami nake muku bankwna sai bayan wayewar gari zamuci gaba da tafiya. da gama fadin haka sai ya wuce izuwa cikin tantinsa. sannan suma ragowar tawagar suka tarwatse kowa ya koma abakin aikinsa. bayan ya isa cikin tantinsa saiya tarar da gimbiya suhaila taci ado.ga wasu kuyangi guda biyu suna bata abinci abaki,biyu kuma suna yi mata tausa. daganin sigowar yarima saiman sai wadannan kuyangisuka tashi suka fice daga turakar suka bar yarima da gimbiya suhaila kadai a zaune acikin tantin. cikin farinciki gimbiya suhaila tace lale marhaban dababban masoyina na duniya. nantake ta rugo da gudu ta rungume yarima saiman sannan zo muje mu zauna yakaimijina domin tsawon wannan lokaci da muka dauka banganka ba ji nake tamkar shekara guda ce bamu haduba. dajin haka sai yakama hannunta sukaje suka zauna akan wata shimfida mai taushi. sannan yadubeta yace. kamar yadda kika kasance haka nima nakasance domin dalilin halin dana shigane yasa nina umarci dakarunmu dasu dakata da tafiya. haka kuma acikin tafiyata bana tunanin wahalar dake gabanmu muddin kina kusa dani. yanzu haka muna cikin daji hayatul arzum akwai muggan dabbobin daji acikinsa kuma acikinsa zamu nemi hnayar zuwa dajin kurusul saudam. dajin haka sai tace dashi hakane amma akwai wata matsala. LIKE AND COMMENTS IS OUR (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) LITTAFIN BAKAR GABA PART 4 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR koda boka ulumanu yazo nan a labarinsa saiyaga gaba daya hadiman sun nutsu suna sauraronsa. da ganin haka sai yayi dariya sannan yace wannan shine takaitaccen tarihin harisul mar'uf bayan bukata ta biya zan karasa muku tarihin nasa. yana gama wannan magana sai duk gaba dayan hadiman sukai sujjada agareshi suna masu cewa. nasara ta tabbata agareka ya sarkin matsafan duniya.... kafin sukarasa maganar tasu boka ulumanu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba. +++ ++++ ++++ ++++ wannan shine abinda ya faru afadar boka ulumanu mai shirin mulkar duniya. al'amarin yarima saiman kuwa alokacin da suka kutsa kai izuwa cikin wannan daji sai suka kasance cikin suna masu tsala azababben gudu nagaban kwatance tamkar zasu fita daga duniyar gaba daya. basu tsaya da tafiyaba saida suka fuskanci dare yayi sannan suka yada zango awani daji mai matukar duhuwa. a sannan ne yarima saiman ya umarci dakarunsa dasu tsaya da tafiyar d suke. nantake kuwa suka cika umarni. wani badakare mai suna zamnal ya matsa kusa da yarima saiman yace yashugabana ni aganina bai kamata mu yada zango awannan dajiba domin baza'a rasa mugayen namun daji acikinsa ba. dajin haka sai yarima saiman ya juyo ya dubi zamnal yace shin baka ganin muna tafiyane tare da mata,yara da tsofaffiba? kasani tafiyarmu dasu awannan yanayi yafi hatsari akan zaman mu a wannan daji. saboda haka ina umartarku dakuje ku kafa mana tanti inyaso gobe da safe sai muci gaba da tafiya. dajin haka sai badakaren yace angama ya shugabana. sanna ya tafi ya umarci yan uwansa dasu kafa tantunan da za'a kwana aciki. sannan wasu kuyangi sukaje suka shirya musu abincin da zasu ci.aka mikashi ga kowanne tanti. bayan angama shirya komai sai yarima saiman yafito ya dubi dakarunsa yace yaku yanuwana duka gaba dayanku kunsan abindaya baro mu daga gida. adalilin hakane na yanke hukuncin da nake ganin shine zai amfanemu.wannan shawara itace ni banaso ko mutum daya daga cikinmu ya mutu,domin yin hakan babbar asarace agaremu. shawara ta farko dazan baku itace kada daya daga cikinku yace zai tayani fada da duk irin abinda kukaga na hadu dashi. shawara ta biyu itace aduk inda kuke ku kasance kuna tare da juna koda kuwa wani abin tsoron kuka gani,muddin bagani kukayi zaku hallaka gaba daya ba. shawara ta uku itace aduk inda muke kada mudinga yin barci gaba dayan mu idan dare yayi,saidai midinga raba dare. aduk sanda wani ya nemi taimako to mu taimaka masa koda bai kasance dan kabilar mu ba. idan mukayi riko da wannan shawara to tabbas bukatarmu zata biya. da wannan kalami nake muku bankwna sai bayan wayewar gari zamuci gaba da tafiya. da gama fadin haka sai ya wuce izuwa cikin tantinsa. sannan suma ragowar tawagar suka tarwatse kowa ya koma abakin aikinsa. bayan ya isa cikin tantinsa saiya tarar da gimbiya suhaila taci ado.ga wasu kuyangi guda biyu suna bata abinci abaki,biyu kuma suna yi mata tausa. daganin sigowar yarima saiman sai wadannan kuyangisuka tashi suka fice daga turakar suka bar yarima da gimbiya suhaila kadai a zaune acikin tantin. cikin farinciki gimbiya suhaila tace lale marhaban dababban masoyina na duniya. nantake ta rugo da gudu ta rungume yarima saiman sannan zo muje mu zauna yakaimijina domin tsawon wannan lokaci da muka dauka banganka ba ji nake tamkar shekara guda ce bamu haduba. dajin haka sai yakama hannunta sukaje suka zauna akan wata shimfida mai taushi. sannan yadubeta yace. kamar yadda kika kasance haka nima nakasance domin dalilin halin dana shigane yasa nina umarci dakarunmu dasu dakata da tafiya. haka kuma acikin tafiyata bana tunanin wahalar dake gabanmu muddin kina kusa dani. yanzu haka muna cikin daji hayatul arzum akwai muggan dabbobin daji acikinsa kuma acikinsa zamu nemi hnayar zuwa dajin kurusul saudam. dajin haka sai tace dashi hakane amma akwai wata matsala. cikin tsananin mamaki yadubeta yace me kike nufi ? gimbiya suhaila tace idan muka fiya yada zango to hakan zai baiwa magauta dama akan mu shin baka tunanin cewa akwai wata sabuwar masifar da take shirin fadomana bayan ta boka ulumanu ? kodajin haka sai hankalin yarima saiman ya tashi yaji gaba daya zuciyarsa ta dugunzuma nantake ya nuna bangon tantin nasu da yatsansa na hannu faruwar hakan keda wuya saiga hoton fadar boka ulumanu ta baiyana tundaga lokacin da sukayi walimar farko afada ,har izuwa lokacinda ya aiki aljani markazulu ya kashe dodo sharmanu da yarsa . koda sukazo daidainan sai hoton komai ya dauke tamkar baitaba wanzuwaba. da ganin haka sai gimbiya suhaila ta dubeshi tace to wannan abu daya faru bakaramin tashin hankali bane anahiyar nan baki dayaba ,domin dodo garjaju bazai taba hakuriba akan wannan abu daya faruba . kodajin haka sai yarima saiman yabushe da dariya sannan yace . nafiki sanin kowaye garjaju don haka kafin muje inda yake zansan hanyar da zamubi mu hallakashi farat daya nantake ya tashi yaja hannun gimbiya suhaila izuwa kan wanish luntsumemen gado suka kwanta . kwanciyarsu keda wuya sai bacci ya daukesu acikin tantin. acan sansanin dakarun su yarima saiman Kuwa sai raba kwanciya kamar yadda ya tsara musu suka raba kansu gida biyu kaso nafarko suka fara kwanciya sannan kaso nabiyu suka kwanta kash hakika rashin sani yafi dare duhu ashe awannan wuri da suka yada sansani akwai wasu mugga muggan yanfashi amma su akaidarsu basayin fashi acikin dare sai da asuba ta doso kai sannan suke farawa zuwa faduwar rana . wannan daliline yasa basu kawowa su yarima hariba tun sanda shigo dajin. amma kuma tundaga shigowar su yarima sai suka fara haka tarkuna yadda zasu kashesu farat daya . acikin tantin yarima Kuwa lokacin da suka nutsa cikin barci .gimbiya tayi wani mafarki inda ta hangi wasu kananan karnuka akan hanyarsu suna kokarin yi musu kisan farat daya . koda daidainan amafarkin nata saita farka afirgice,tasa hannu tatashi yarima . cikin firgice tadubi yarima tace yakai masoyina kayi hakuri bisa tashinka daga barci da nayi . hakan ta farune sakamakon wani mummunan mafarki da nayi .tun ina yarinya idan nayi mafarki yana zama gaskiya ba'a taba samun akasiba to a darennan nayi mafarki inda aka nunamini wasu muggan yanfashi akewaye damu suna dana mana tarkunan mugunta.idan har bamu dauki matakiba to tabbas zamuyi asarar rayuka da yawa . kodajin sai ya dubeta yace madallah da mata tagari hakika ina matukarjin dadi da irin taimakon dakike bani nantake ya tashi yafita daga cikin tantin nasa ya nufi inda dakarunsa suke,koda sukaga yarima sai suka durkusa cikin girmamawa.yarima ya dubesu yace akwai wani abu dake shirin faruwa idan har bamu dauki matakin gaggawa ba shawarar dazan baku itace dakunga alfijir yafara fitowa kusami kibiyoyinku,kusaita hanya guda daya daidai inda tarkon yake saiku harbata,to dazarar kunyi haka tarkunan abokan gaba zasu lalace.gurin da aka birnine tarkunan Kuwa yana nan gaba damu daga barin gabas tafiyar rabin sa'a idan har muka sami nasarar lalata tarkunan to zamu sami nasarar fita daga san saninmu lafiya nine kadadai wanda zai taresu da yaki da zarar munyi gaba da gaba dasu.kukuma saiku zama yan kallo . ku aikinku shine bawa jama'armu tsaro.idan mukayi haka to zamu sami nasara akansu . haka suka kasance cikin wannan halin hr izuwa lokacin da alfijir yafara ketowa nan take Kuwa dakarun suka Debo kibiyoyi suka dana ajinkin baka sannan suka sukayi tafiyar rabin sa'a.sannan suka saita gabansu kadan suka harba kibiyoyin,kwatsam saiga wasu muggan tarkuna suna fitowa daga karkashin kasa masu matukar hatsari ga rayuwar dan adam. faruwar hakan keda wuya saiga wasu muggan yanfashi suna fitowa daga cikin maboyarsu suna masu karji gami da kuwwa nufo su yarima saiman . koda ya rage baifi saura taku gomaba tsakaninsu da sansanin sai yarima saiman yafito cikin muguwar shigar yaki . nantake yasa kafa yadoki wasu dakaru dake gabansa .saboda karfin dukan saida sukai tsalle

Chapter 2 of 14