Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kamosu ba Yana cikin binciken ne ya tuna cewa sarki abu saiman yana da da guda daya mai suna saiman kuma tunda aka fara wannan yakin ya nemeshi ya rasa Domin kuwa da ace ya halarci wannan yaki dolene ya ganshi saboda shima matashi ne kuma jarumi uban sadaukai har an tabbatar da cewa yafi mahaifinsa jarumtaka Koda yin wannan tunani sai ya juyar da akalar bincikensa kan yarima saiman Amma saiyaga tsafin nasa yaki yayi tasiri domin koda ya matsa wajen yin binciken saiyaga madubin tsafin nasa yayi baki sidik harya fara kokarin yin bindiga ya fashe Bisa dole ya tsayar da binciken nasa yace acikin zuciyarsa Tabbas akwai boyayyen al'amari akan wannan yaro kuma tabbas idan ban gaggauta bincike akansa ba Zai iya zamowa silar hana cikar burina Haka dai ya cigaba da zancen zuciya har suka iso kofar gidan sarauta Adaidai nan ne boka ulumanu ya dakata da tafiyar da yake yi sannan yace da harisul mar'uf Yakai gwarzon jarumi Anan ne zan dakata na jira ka kaje ka hallaka wannan maciyar wacce suke bauta mata Ka bincika sosai kofar da zata sadaka da wannan macijiya tana cikin wannan gidan sarauta ni zan jiraka a awannan gurin Koda jin haka sai harisul mar'uf yashige cikin wannan katon gidan sarautar Hakika gidan sarautar birnin ramlatul saif ya cika kato Domin idan ka ganshi kamar ba mutanene sukayi gininsa ba saboda tsananin girmansa shi kansa aljani harisul mar'uf saida ya zama dan karami yayinda ya shiga cikinsa Haka dai ya dinga bincike sosai har saida ya isa wannan dakin bautar Hakika dukda girman wannan gidan sarautar saiya zama kankani akan wannan dakin bautar Daga can karshensa kuwa wata tsohuwar macijiya ce wacce masana suka tabbatar da cewa tafi shekaru dubu aduniya Domin tun kafin agina wannan birnin take Sai bayan an ginashi ne mutanen zamanin suka maida ita abar bauta saboda ganin irin abubuwan al'ajabin da take yi Koda ganin wannan macijiya sai harisul mar'uf ya bude fukafukansa ya tashi sama ya afka mata domin yayi mata kwaf daya Koda ya rage baifi saura kamu ukuba atsakaninsa da ita Sai kawai ta hura masa wata iska daga bakinta Nantake kuwa yaji kamar an daure masa jikinsa da manyan sarkoki Sannan tayi wulli dashi zuwa saman rufin dakin take yaje ya gwaru da ginin Ya fado kasa sannan ya sake dawowa suka kachama da masifaffen yaki a wannan rana harisul mar'uf yaga tashin hankalin da bai taba ganiba arayuwarsa Domin saida ya raina jarumkarsa Yayi nadamar tunkarar wannan macijiya Harsaida ta kai sun rushe wannan gidan sarautar gabaki dayansa Da sauran gidajen da suke cikin birnin Hatta kasashen da suke makwabtaka da birnin ramlatul saif saida suka shiga tashin hankali domin gaba daya nahiyar babu inda wannan tashin hankali bai shafaba Aljani harisul mar'uf saida yayi nadamar karbar wannan kwangila ta kashe wannan maciyar a hannun ulumanu Saida ya suma sau uku yana farfadowa Karaya kuwa yayita sau goma ajikisa Da kyar da sidin goshi ya iya hallaka wannan maciyar Yana kasheta kuwa jini ya balle daga cikinta kamar an bude magudanar ruwa Awannan lokacin ulumanu yana saman wani katon tsauni yana kallon fafatawar da sukeyi ta cikin madubin tsafinsa Koda yaga harisul mar'uf ya hallaka wannan macijiya sai ya rusa ihun farinciki sannan ya tashi sama kamar tsuntsu ya diro a inda aka harisul mar'uf yake Take ya nunashi da yatsansa wata iska ta shureshi tayi sama dashi Sannan shima ya cika wata battarsa da jinin wannan macijiya Ya tashi sama Wannan iskar kuwa wacce ta dauki harisul mar'uf tana biye dashi abaya Basu zarce ko ina ba sai kogon da mahaifiyar aljani harisul mar'uf take wato aljana zamira Nantake boka ulumanu ya sauke harisul mar'uf akasa sannan ya gyara masa duk karayar da take jikinsa Ita kuma nantake ya karya sihirin da akayi mata ya dawo da ita ainihin siffarta daga siffar da aka mayarda ita ta gunki Bayan ta dawo ainihin siffarta sai shi kuma ya bace bat ya barsu su biyu kacal A wannan lokaci harisul mar'uf da zamira sunyi matukar farincikin ganin junansu Shi kuma ulumanu ya koma zuwa kogon tsafinsa ya ci gaba da shirin tsafinsa da wannan jinin WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FILIN YAKI BAYAN SARKI ABU SAIMAN YA MUTU SHI KUWA BOKA ULUMANU YA SAMI ABINDA YAKE NEMA A BIRNIN ++++++++++++++++++++++++++++++ +++++++++++ AL'amarin yarima saiman kuwa lokacin da suka kama hanyar tafiya birnin hamshak Sai da suka shafe sa'a hudu suna tafi saida tsakar rana suka iso wani daji mai yalwar 'ya'yan itatuwa Suna isowa daidai wannan daji sai yarima saiman ya dakata da tafiya ya juyo Yace da mutanensa Dukkan ku anan zamuyi bankwana daku kuci gaba da zaman jirana har naje na dawo domin daganan inda muke zuwa birnin hamshak tafiyar rabin sa'a ce Sannan ya karasa bakin keken dokin suhaila sukayi bankwana akan cewa zata tsaya jiran dawowarsa Amma sai yaga a wannan lokaci itace take karfafa masa guiwa akan zai sami nasara akan abinda zaiyi a cikin birnin Daga baya kuma sai yaga hawaye ya zuba daga cikin idanunta Ganin wannan hawayene ya tabbatar masa da cewa tabbas aikin gama ya riga ya gama Ma'ana tayi bincike ta gano cewa anci birninsu da yaki Mahaifinsa ya zama matacce Take kwalla shima ta zubo masa Nantake yaji ya kagu da yaje birnin hamshak ya dauko wannan kubar ta muftahul sihir Sannan ya kawo karshen wannan bakar gabar da take tsakaninsa da boka ulumanu Ana cikin hakane saiga aljani markazulu shima ya iso wannan sansanin Nantake duk su biyun suka tashi sama cikin gajimare Tabbas tsafi gaskiya ne agurin ma'abotansa Sai gashi yarima saiman yana gudu a sararin samaniya bisa kafafunsa Harma yana kokarin gifta aljani markazulu Ba komai ne ya jawo hakaba face kaguwa da burin cika aikin da yake gabansa Allah ya hadamu da alkairinsa ameen LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN LITTAFI SAI KU KASANCE DA WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG BAKAR GABA Kashi na shida 6 Littafin Habibullah muhammad kabara Ebook created by Shuraih Usman 99% Published at hausaebooks.com.ng BAKAR GABA PART 25 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR yarima saiman kuwa lokacin da suka kama hanyar tafiya birnin hamshak Sai da suka shafe sa'a hudu suna tafi saida tsakar rana suka iso wani daji mai yalwar 'ya'yan itatuwa Suna isowa daidai wannan daji sai yarima saiman ya dakata da tafiya ya juyo Yace da mutanensa Dukkan ku anan zamuyi bankwana daku kuci gaba da zaman jirana har naje na dawo domin daganan inda muke zuwa birnin hamshak tafiyar rabin sa'a ce Sannan ya karasa bakin keken dokin suhaila sukayi bankwana akan cewa zata tsaya jiran dawowarsa Amma sai yaga a wannan lokaci itace take karfafa masa guiwa akan zai sami nasara akan abinda zaiyi a cikin birnin Daga baya kuma sai yaga hawaye ya zuba daga cikin idanunta Ganin wannan hawayene ya tabbatar masa da cewa tabbas aikin gama ya riga ya gama Ma'ana tayi bincike ta gano cewa anci birninsu da yaki Mahaifinsa ya zama matacce Take kwalla shima ta zubo masa Nantake yaji ya kagu da yaje birnin hamshak ya dauko wannan kubar ta muftahul sihir Sannan ya kawo karshen wannan bakar gabar da take tsakaninsa da boka ulumanu Ana cikin hakane saiga aljani markazulu shima ya iso wannan sansanin Nantake duk su biyun suka tashi sama cikin gajimare Tabbas tsafi gaskiya ne agurin ma'abotansa Sai gashi yarima saiman yana gudu a sararin samaniya bisa kafafunsa Harma yana kokarin gifta aljani markazulu Ba komai ne ya jawo hakaba face kaguwa da burin cika aikin da yake gabansa Domin birnin hamshak ba a doron kasa yake ba Asararin samaniya akayi gininsa kuma a tsaye yake cak akan iska baya wani girgidi saboda karfin sihirin masarautar Agaba daya duniya awannan zamanin babu masarauta mai karfin mulkin wannan birnjn da kuma karfin sihirinsa Komai karfin sihirin mutum ko aljan idan ya shiga cikin wannan birni Saiya hadu da wadanda suka fishi ko mai da yake takama dashi Sannan ga yawan dakarun yaki da suke dashi wadanda su kadai zasu iya yakar duk kasashen duniya Mata kuwa da kayan alatu babu kalar wadanda babu acikin birnjn Domin su kansu gidajen da suke cikin birnin mafi yawansu anyi musu adone da zinare Hakan ns zai tabbatar maka da cewa wannan birnin ya cika aljannar duniya Domin komai sarautar mutum idan ya shigo birnin hamshak saiya zama kamar dan kauye Saboda zaiga abubuwan da bai taba ganinsu ba arayuwarsa Duk da tsananin kyau da kawar da wannan birni yake dashi duk sai ya zama abanza Domin jama'ar kasar gaba daya Basa kaunar garin saboda tsananin zaluncin sarkin garin wato sarki mafazil Wanda ya kasance azzalumin gaske Wanda baya tausayawa jama'ar kasar Ko kadan wajen karbar haraji Sannan komai kankantar kuskuren da aka aikata masa hukuncin kisa yake yankewa Baya sassauci ko kadan tsakanin talaka dame kudi Kuma duk irin wannan kyale kyale da yake cikin birnin ya zuba shine saboda ya tara dukiya mai yawan gaske Saboda dole yayiwa jama'ar kasar cewa duk wanda yake da burin ci gaba da rayuwa dolene ya sayi wadannan kayan kawa ya saka a gidansa Ko kanaso ko bakaso Idan kuwa kaki hukuncin kisa ne akanka Lokacinda su yarima saimsn tare da markazulu suka tashi sama suka nufi birnin hamshak Sai suka yita tsala azababben gudu Tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya Ahanksli suka dinga kusantar birnin tun suns hangoshi daga nesa har suka fara ganinsa akusa dasu Nantake duk su biyun suka cika da tsananin mamaki Domin ganin kofar birnin sukayi a bude babu mai gadi ko guda daya Koda suka karaso bakin kofar birnin sai suka tsaya cak Sannan yarima saiman ya dubi markazulu yace Yakaj abokina hakika tunda kaga haka to sarki mafazil yasan da zuwanmu Domin tabbas ruwa baya tsami banza Akwai wani tuggun da suka shirya mana Don haka dolene mu canja siffarmu yadda dakarun wannan birnin ba zasu gane mu ba Yana gama fadin haka sai aljani markazulu ya rikide zuwa wata siffar daban Sannan shima yarima saiman ya rikide ya koma zuws siffar da aljani markazulu sak Idan ka gansu sai kayi zaton cewa hasan da usaini ne Domin hatta girman jikinsu da fuka fukansu Take suka shiga cikin birnin tamkar dama sun kasance haifaffun garin Haka dai sukayita kutsawa cikin birnin su shiga nan sufita can Kuma duk inda suka gifta sai suga kamar babu wanda yake kallonsu Domin duk inda suka kutsa saidai suga kowa yana gudanar da harkokinsa na yau da kullum Saida suka yini cur suna tafiya kuma babu inda suka nufa face gidan sarautar birnin Domin dauko gatarin sihiri na miftahul sihir Adaidai wannan lokacine suka iso wani gindin wata rijiya Wacce abakinta wani yaro ya tsaya yana kokarin tura murfin rijiyar don ya debi ruwan da yake cikinta Koda suka iso bakin wannan rijiya sai sukaji wannan yaro ya kallesu yace Yaku wadannan baki ku taimaka mini na janye wannan murfi saboda girman iyayenku Kodajin wannan magana sai duk su biyun suka cika da tsananin mamaki Cikin matukar kaduwa suka kalleshi sukace Yakai wannan saurayi shin tayaya akayi ka iya ganemu? Alhalin duk mu biyun mun rikida daga ainihin siffarmu? Dajin wannan tambaya sai saurayin yayi murmushi sannan yace Shin a tunaninku babu wanda yake kallonku acikin siffar ku ta ainihi tundaga lokacin da kuka shigo wannan birnin? To indai hakane to kusani kun yaudari kanku domin babu wanda baya kallonku Kawai dai an zuba muku ido ne don aga iyakar gudun ruwanku Da zarar kun shiga cikin gidan sarauta to shikenan kun shiga inda ba'a fitowa Domin ko gawarku ba'a isa agani ba Dajin wannan batu sai duk su biyun sukayi cirko cirko suna kallon juna Daga can sai yarima saiman yace da markazulu To indai hakane to wannan canja siffarmu da mukayi to bata da wani amfani don haka sai mu kara sauri har mu isa cikin gidan sarautar ayi abinda za'ayi Yana gama fadin haka sai ya kara gaba markazulu na binsa a baya Cikin 'yan dakiku suka iso gidan sarautar tun daga nesa suka sha jinin jikinsu Domin sun tabbatar da cewa a wannan rana sun kawo kansu gidan mutuwa inda karfin damtsensu dana sihirinsu ba zaiyi tasiri ba Domin dakaru suka gani na jinsin bakaken aljanu girda girda masu kirar halittun farko Wadanda adadinsu yafi kwatancen mai kwatance Sun kasu kashi uku Kashi na farko suna tsatstsaye abakin kofar gidan sarautar ruke da miyagun makamai Kashi na biyu kuma suna zaune ne akan katangar gidan sarautar Kaso na uku kuma suna yawo ne akan iska sunyiwa katangar gidan sarautar kawanya ta yadda babu halittar data isa ta wuce face ta ratsa ta cikinsu Koda ganin wadannan dakaru sai markazulu ya kalli yarima saiman yace Yakai maigidana tabbas yau mun kawo kanmu zuwa ga hallaka domin bamu isa mu iya ketara wadannan dakrunba har mu shiga cikin gidan sarautar nan mu dauko kubar miftahul sihir ba Koda jin haka sai yarima saiman ya daka masa tsawa yace Saboda me zaka karyawa kanka gwuiwa akan abinda muka dade muna shiri akansa Ina mai tabbatar maka da cewa koda zaka tafi ka barni ni ni kadai saina shiga cikin wannan masarauta na dauko abinda nazo nema don haka idan ba zaka iya ba sai kayi ta kanka domin nasan ko ka gudu ba zasu kyalekaba Yana gama fadin haka sai ya sake rikidewa ya koma zuwa ainihin siffarsa Sannan ya falfala da gudu ya tunkari wadannan dakaru Take suma suka falfalo da gudu zuwa kansa nantake suka lullubeshi kamar wasu kudaje sunga kazanta Suna masu kai masa sara da suka koda suka gama lullubeshi Sai yayi kukan kura yana daga inda yake ya tarwatsasu da kaifin takobinsa Markazulu da yake can gefe daya koda yaga abinda ya faru ga yarima saiman Sai shima ya falfalo da gudu zuwa inda suke wannan fafatawa Suka kachame da azababben yaki mai matukar munin gaske Duk sanda makaman yakinsu suka hadu sai kaji wata irin kara ta tashi tareda tartsatsin wuta Haka kuma duk inda su jarumi saiman suka durfafa saidai kaga dakaru suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agona Jini kuwa ya dinga fantsama a sararin sama kamar an bude idaniyar ruwa Sassan jikin wadannan dakaru kuwa saita cika filin da ake wannan yaki Duk sanda wadannan dakaru suka sari jikin jarumi saiman ko kuma aljani markazulu Sai suji kamar sun sari karfe domin ko kwarzanewa jikinsu bayayi saboda wannan tsumin na dodo garjaju wanda suka sha Amma fa suna jin zafi da radadin bugun da aljanun sukeyi musu Kuma duk da cewa suna samun nasara akan aljanun sai abin ya zama abanza domin duk da cewa gashi dai suna kashe dakarun amma sai kara ciccidowa suke kamar daga sama ake zubo su Koda aka jima ana wannan gumurzu sai su kayi tunanin tabbas idan aka jima ana wannan fafatawa zasu iya gajiya kuma da zarar sun gaji shikenan abokan gaba zasuyi nasara akansu Koda yin wannan tunanin sai duk su biyun suka daka tsalle sama da nufin su haura katangar Koda dirarsu akanta sai sukaji an dakesu da kafafu take duk su biyun suka rikito kasa Sakamakon wannan wawan naushi da suka sha daga wajen dakarun da suke zaune akan katangar Kafin aljanun su yi musu rubdugu sai suka mike tsaye zumbur kamar babu abinda ya samesu suka sake kachamewa da yakin kuma sunayine suna budawa kansu hanya ta karfi da yaji har suka isa bakin katangar Take suka karayin wani tsallen akaro na biyu suka dira kan katangar Cikin zafin nama suka saka takubbansu suka tsarge dakarun da suke gabansu Suka budawa kansu hanya Nanfa aka kasa azababben tseren gudu tsakanin su yarima saiman da wadannan dakaru Alokacin dakarun suka dinga jefo musu masu da kuma kibiyoyi Amma sai kaga suna kadesu da takubban dake hannunsu suna dada kutsawa gaba Su kuma dakarun basu fasa binsu kamar dada karosu akeyi Suna cikin wannan azababben gudu ne kwatsam sai suka yi arba da wani murgujejen aljani wanda ya ninka ragowar aljanun da suka baro abaya girma da kuma siffar karfi Ku ina ajikinsa a murde yake kamar jikin tsohuwar bishiyar kuka Kafin su ankara ya cafkesu duk su biyun ya daga su sama ya wulwulasu kamar yara sun sami 'yar tsana sannan ya wullasu sama take duk su biyun je sukayi sama kamar an wulla tsakuwoyi Sannan suka rikito Bisa sa'a sai rigar jarumi saiman ta makale ajikin wata azarar gini Shi kuwa markazulu saiya fado kasa tim kafin yayi wani yunkuri Wannan shirgegen aljanin yazo ya cafkeshi ya kama fuka fukansa guda biyu ya karya su Take aljani markazulu ya kwarara uban ihu sannan ya fadi kasa sumamme Koda ganin haka sai yarima saiman ya cire wannan rigar data makale ajikin ginin Sannan ya kwarara ihu yana mai kusantar wannan aljanin Da ganin haka sai aljanin ya bushe da dariya sannan yace Lallai wannan yaro ka cika mai tsaurin ido yanzu kai da bakafi in talitseka ba Kaine kake tunanin zaka iya tarata da yaki to gaskiya ka yaudari zuciyarka Don haka ba'a sanin maci tuwo sai miya ta kare Yana gama fadar haka sai ya kawowa yarima saiman mummunan sara Wanda inbadon yayi gaggawar kaucewa ba da sunansa shekakke Gurin kuwa da wannan takobi ta sauka saiya samar da wani wawakeken rami A wannan lokacin da abun yake faruwa ne sarki mafazil ya iso daidai wannan guri don yaga abinda yake wakana Koda yaga yarima saiman dan kankani kuma shi kadai saiya bushe da dariya Sannan ya tsaya yana kallon wannan fafatawa domin yasan babu ta yarda za'ayi ya sami nasara akan sarkin yakinsa damasuru ba Balle har ya zo su fafata dashi gaba da gaba Nanfa aka sake ruguntsumewa da fada fiye da na farko Sai a sannan ne ya gane cewa damasuru ba karamin sadauki bane Wanda shi kadai ma daidai yakeda wata babbar rundunar Ko mai da yarima saiman yake dashi saiyaga wannan aljanin ya ninkashi sau dari Domin bama ya isa kare hare haren da yake kawo masa Kuma har ya hadamasa jini da majina babu kyan gani Idanunsa sun fara gani dashi dishi Ba zato babu tsammani sai akaji wata irin guguwa mai karfin gaske tana kadawa a saman fadar tamkar zata yaye rufin fadar Nantake kowa ya daga kansa sama don ganin abinda yake faruwa Koda suka ga abinda yake saukowa sai kowa ya kame kyam Ba komai suka gani ba face tsohon sarkin yakin birnin kuma babban masoyin sarkin garin wato mahaifin sarki mafazil Shine sadauki ramzas mahaifin aljani harisul mar'uf kuma yaba dauke da gimbiya suhaila agadon bayansa Shi kansa sarki mafazil saidaya razana sakamakon yin arba da sadauki ramzas Yadora hannunsa akan kufen takobinsa kamar ya zareta ya afka masa amma saiya dake A hankali aljani ramzas ya sauka kasa sannan ya ajiye gimbiya suhaila agefe daya Ya juyo ya fuskanci sarkin yaki damasuru yana mai yi masa nuni da ya afko masa Nantake kuwa damasuru ya kawo masa mahaukacin sara da nufin ya tsargeshi biyu Cikin zafin nama ya kaucewa saran sannan yasa takobi ya yanka wuyan aljani damasuru Koda ganin abinda ya faru ga damasuru sai hankalin kowa ya tashi sannan suka shiga taitayinsu Cikin takama aljani ramzas ya kalli aljani mafazil yace Yakai abokin gabata kuma daga babban masoyina marugayi sarki darkusma Ka sani cewa yau itace ranar da zaka girbi sakamakon bakin zaluncin da kake aikatawa tsawon shekaru Kuma kamar yadda mahaifinka ya fada maka cewa dana harisul mar'uf ne zai ci gaba da mulkin wannan birni to tabbas haka za'ayi Domin yau nazo ne da shirin tsira ki halaka bana tsoron mutuwa Idan kaima ka shirya saika taho yana gama fadar haka sai ya falfalo zuwa kan sarki mafazil Suka kachame da masifaffen yaki wanda yafi wanda sukayi abaya muni Wohoho Hakika fadan manyan dawa bashida dadin kallo domin ana fara wannan yaki hankalin duk wanda yake cikin fadar ya tashi Saboda wani irin tartsatsin wuta daya dinga tashi asanadiyar fadansu duk wanda yakaiwa wani hari bai sameshiba to duk abinda ya samu take suke raba shi biyu komai girmansa da kwarinsa Hakika tashin hankali ba abin so bane domin a wannan lokaci saisu yarima saiman da kuma ragowar dakarun birnin suka zama 'yan kallo suka kame kyam kamar gumaka Shikuwa aljani markazulu da yake cikin halin suma karar haduwar makamansu ce ta sa ya farka Amma saiya manta da karayar da take jikinsa shima yabisu da kallo Tabbas wadannan aljanu guda biyu sun cika sadaukan gaske kuma fasa taro Cikin lokaci kankani suka hargitsa fadar ragowar dakarun da suke ciki suka fara hallaka Sakamakon dirkar ginin data fara fado musu Ba shiri suma suka fara gudun ceton ransu Koda aka jima ana wannan fafatawa sai duk suka hadawa junansu jini Domin sarki mafazil ya sami nasarar saran aljan mafazil a damtsensa na hannun hagu Amma kafin ya ankara shima ya rama yasare shi atsakiyar gadon bayansa Kuma ciwon yayi zurfi sosai har saida ya kwallara ihu saboda zafi da radadin da yaji Adaidai wannan lokacine suka fara jiyo ihun wasu dakarun daga wajen fadar Cikin sauri aljani ramzas da sarki mafazil suka juya domin suga abinda yake Faruwa Take sukaga aljani harisul mar'uf yana ragargazar dakarun da suke tsaron kofar gidan sarautar yana shigowa da karfin tsiya Mahaifiyarsa tana binsa abaya Kafin wasu 'yan dakiku ya gama tarwatsasu ya iso inda ake wannan fafatawar Take ya bude bakinsa yace Yakai abbana ka yau nine danka harisul mar'uf kuma ina tareda mahaifiyata zumaira Kodajin haka saiyaji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsa Take ya fara kaiwa sarki mafazil mahaukatan hare hare tun yana iya kare kansa har ya kasa Nan danan yayi masa jina jina yadda ko dan ya tsansa bazai iya dagawa ba Sannan ya juyo ya kalli gimbiya suhaila yace Ke kuma sai kizo ki dauki fansar ran iyayenki akan wannan azzalumin Koda jin haka sai ta taho fuskarta cike kwalla a lokacin data tuna da mahaifanta na asali Take ta karbi takobin hannun yarima saiman ta falfala da gudu Sannan ta daka tsalle sama ta caka masa takobin a tsakiyar kahon zuciyarsa Take ya kwallara mahaukatan ihu take ya kama da wuta ya kone kurmus saboda karfin sihirin jikinta Nantake suka garzaya inda aljani markazulu yake tsaye suka kama karayarsa aka gyara masa ita Sannan suka shiga cikin gidan sarautar aka dauko kubar miftahul sihir A wannan rana aljani ramzas dasu harisul mar'uf sunyi kukan farin cikin sake haduwa da junansu Bayan an kwana biyu kuma aka dora aljani harisul mar'uf amatsayin sabon sarki a birnin hamshak Shi kuma mahaifinsa ya koma kan mukaminsa na baya wato sarkin yakin birnin Sannan su yarima saiman suka kama hanya dauke da miftahul sihir Suka bar cikin birnin suka koma can sansaninsu Daga nan suka tafi can kogon tsafin boka awaisul masawi wato kogon darul sihir Saida suka shafe kwanki goma suna tafiya kuma basu hadu da wani abu mai cutarwa ba sannan suka iso bakin wannan kogo LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT TO ENTERTAIN YOU BAKAR GABA PART 26 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Sannan su yarima saiman suka kama hanya dauke da miftahul sihir Suka bar cikin birnin suka koma can sansaninsu Daga nan suka tafi can kogon tsafin boka awaisul masawi wato kogon darul sihir Saida suka shafe kwanki goma suna tafiya kuma basu hadu da wani abu mai cutarwa ba sannan suka iso bakin wannan kogo Shidai wannan kogon yakasance babbane kuma yakai girman gari guda Domin tsaunine guda aljanu suka fafake cikinsa ya zama tamkar gari bisa umarnin shugabansu boka ulumanu Kuma ajikin wannan kogo babu wata kofa da zaka gani ka iya bude shi Amma koda suka iso wannan wuri sai jikin dutsen ya fara tsagewa take sukaga wata irin katuwar kofa ta bayyana wacce take da girma sosai kuma an sana'antatane da zallan bakin karfe Take yarima saiman ya umarci wasu dakaru guda hudu wadanda suke dauke da kubar miftahul sihir da suzo su zirata a mazauninta Cikin sauri dakarun suka taho dama ba akan dawakai sukeba Sannan suka zira kubar ajikin kofar take suka koma baya suka tsaya Sai gani sukayi kubar ta fara juya kanta wata irin kara ta dinga tashi tana cika dodon kunne Bayan 'yan dakiku sai kofar ta bude kanta Nanfa suka cika da tsananin mamaki domin ganin yadda wannan kogo aka kawata cikinsa tamkar wata babbar masarauta Kuma acikinsa sai sukaga gida gida acikinsa kamar yadda tsarin cikin gari yake Nanfa dukkansu suka kame kyam kamar gumaka ana jiran aji mai yarima saiman zai fada Daga can sai suka ga ya bushe da dariya cikin farin ciki Sannan yace Yaku 'yan uwana tabbas yau na sami kwanciyar hankali sakamakon ganin na cikawa mahaifina burinsa Na kawo ku kogon tsira wato darul sihir inda zaku ci gaba da rayuwa Sannan mu koma daga baya zuwa can birnin mu don mu sake rayashi Yana gama fadin haka sai ya kutsa kansa cikin kogon dutsen Sauran mutane suna biye dashi Hakika a wannan ranar sunyi matukar farin ciki mara misaltuwa Kuma ana cikin wannan halin farin cikin ne sukaga gimbiya suhaila ta fadi kasa alokacin da cikinta yake murdawa yanayi mata ciwo Nantake hankalin kowa ya tashi kuma murna ta koma ciki Shi kuwa yarima saiman hankalinsa yafi tashi akan na kowa domin ganin irin halin da matarsa ta shiga Cikin gaggawa wasu kuyangi suka zo suka dauketa suka shige da ita cikin wani gida Dake cikin kogon suka fara kokarin karbar nakudarta Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai akaga kogon dutsen ya fara amsa kuwwa tamkar zai tsage Komai na cikinsa ya fara girgiza kamar zai fado kasa Wani irin haske ya mamaye kogon tare da wata irin kara wacce ta cika kogon Sannu a hankali komai ya fara lafawa kuma adaidai lokacin ne gimbiya suhaila ta haifi wani kyakykyawan jariri Kuma mai kirar mazaje domin har a sanda aka haifeshi Hannuwansa a rufe suke kuma yana da matukar kwarjini da siffar jaruman gaske Kuma ana haifar tasa sukaga wani irin haske ya fito daga can wani sako na kogon dutsen ya shiga cikin kirjin jaririn Koda kuyangi sukayi arba da wannan jariri sai duk suka ruga da gudu suka bar cikin

Chapter 12 of 14