Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka gwaru da wata bishiya .nantake kashin bayansu ya karye . cikin karaji ya hausu da sara da suka tako ina sai ga kawunan bila'adama yana yawo a sararin samaniya . jini Kuwa yadinga yawo kamar anbude idaniyar ruwa . sassan yadinga yawo kamar ana sassabe agona . sai gashi mutun daya ya zamewa mutane dubunnai alakakai tamkar guguwar zame masu guguwar annoba.su kansu sunsan cewa yau sun hadu da gamonsu rana ta baci domin basu taba haduwa da wani jarumi ba kwatankwacin sa.domin fada yakeyi tamkar ba jikin jini da tsokane da shiba. kafin cikar sa'a biyu ya karar da rabinsu. koda shugaban yan fashin ya lura da abin dake faruwa,sai ya daka musu tsawa. nan take kuwa suka dakata da fadan. shugaban nasu ya matso inda yarima yake ya tsaya agabansa,sai ga yarima saiman ya zamo dan kankani agabansa. shugaban nasu ya dubi yarima yace tabbas jarumtakarka ta burgeni don haka ina gayyatarka daka shigo cikin kungiyarmu,zan baka babban mukami idan kayarda. idan kuwa kaki ni da kaina zan kasheka. koda jin haka sai yarima ya daka masa tsawa yace kai lalataccen banza kune kuka bata mana nahiya da kashe kashen rayukan wadanda basu jiba basu ganiba. don haka nadau alkawarin ganin bayanku babu wani sulhu a tsakaninmu. da gama fadin haka sai ya afka masa suka kachame da azababben yaki fiye dana farko. ya zamana suna kaiwa junansu sara da suka cikin kwarewa.sai gashi yarima yazama dan karami agaban wannan dan fashi amma abinda zai baka mamaki shine. a fannin iya yaki yarima ya tattaka dan fashin. wohoho hakika jarumtaka baiwace wanda allah ya baiwa ya huta duk da tsananin karfi irin na wannan dan fashi sai ya zama na banza domin kokarin kare kansa yake yana neman hanyar tsara. koda yarima ya fuskanci nufin wannan dan fashi sai ya shammace shi yasa takobi ya sare masa kai. nantake gangar jikin ta fadi kasa. koda raguwar yan fashin sukaga gawar shugabansu akasa .sai duk suka zubar da makamansu suka ruga da gudu. nanfa yarima saiman ya dinga bin dakarun daya bayan daya yana kashesu har sai da ya karar dasu gaba daya sannan ya dawo wajen sansaninsu. da isowarsa sai ya tarar da dakarunsa da jama'arsa suna ihun farinciki. a gaban dakarun kuwa babu kowa sai gimbiya suhaila. tayi shigar wata jar riga mai tsananin kyau.ta daure gashin kanta agadon bayanta sai sheki da walwali yakeyi. cikin murna ta jawo hannun yarima saiman izuwa cikin tantinsu,sannan ta dauko wani daddadan abinci ta ajiye masa. nantake kuwa ya faracin abincin cikin nishadi da annashuwa. da gamawarsa saita dubeshi tace ina tayaka farin cikin samun nasararka a wannan yaki. ya dubeta yace nayi wannan aikine domin kare mutuncin al'ummarmu. don haka yanzu zamu tashi mubar wannan guri muci gaba da tafiya don biyan bukatarmu. yana daga cikin tantin nasa yakira shugaban dakarunsa mai suna zamnal. cikin kankanin lokaci shugaban dakarunya iso cikin tantim dare da fadin gani ya shugabana. yarima yadube shi yace inaso ka umarci dakarunmu dasu gaggauta hada kayansu don muci gaba da tafiya.zamnal yace angama ya shugabana. nantake zamnal ya tashi ya fice daga cikin tantin nasu. cikin kankanin lokaci kuwa suka hada inasu inasu suka cigaba da tafiya izuwa hanyar da zata kaisu dajin kurusul saudam saida suka shafe lokuta masu tsawo suna tafiya sannan suka iso wata mararrabar hanya wacce ta kasu kaso hudu. nantake sukaja birki suka tsaya sukayi cirko cirko cikin rashin sanin hanyar da yakamata subi ana cikin wannan hali sai yarima saiman ya tuna da maganar da mahaifinsa yayi masa akan zoben hannusa. koda gama wannan tunani sai ya zaro zoben daga hannunsa sannan ya murza. faruwar hakan keda wuya sai wani haske ya fito daga jikin zoben ya nuna musu hanyar data nufi yammcin dajin. inda yake musu nuni da cewa itace hanyar dajin kurusul saudam. koda ganin haka sai yarima saiman ya juyar da linzamin dokinsa zuwa hanyar da hasken ya nufa.cikin tsala azababben gudu. WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU GA YARIMA SAIMAN AKAN HANYARSU TA ZUWA DAJIN KURUSUL SAUDAM ++ +++ ++ Al'amarin aljani karkazulu kuwa lokcin daya bar kogon daya kashe samriya da babanta kuwa. sai ya kasance yana tsala gudu nagaban kwatance asararin samaniya ba tare da sanin inda zaijeba.cikin jin izza da takama. yana cikin tafiyarne ya fara tunane tunane akan wanne shiri yakamata yayiwa kansa. tabbas yanada bukatar karawa kansa shiri ta yadda zai iya hallaka boka ulumanu cikin sauki batare da wata wahalaba. sannan kuma ya tuna da batun dodo garjaju yanzu yana cikin fushi dashi. yana cikin wannan tunanine kuma ya tuno da batun yarima saiman. i dan hada kai dashi to tabbas zai sami nasara.sannan kuma bayan bukatarsa ta tsira sai ya yaudari yarima saiman ya hallakashi. koda gama wannan tunani sai ya bushe da dariyar mugunta. sannan ya juya ya nufi hanyar dajin kurusul saudam (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) LITTAFIN BAKAR GABA PART 5 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR koda sarki abu saiman yazo nan azancensa sai mutane suka kamu da murna har sunayi masa jinjina da kirari tamkar suna da tabbacin samun nasara awannan yaki koda ganin haka sai farinciki ya kamashi sannan yace daga wannan rana inason makeran dake cikin birnin nan da su dage wajen kera miyagun makaman yaki wadanda zamuyi amfani dasu awannan yaki. sannan mayakan mu su dage wajen baiwa kansu horon yaki tare da sauran mutanen gari sannnan duk wanda yakasance yana da ilimi wajen sanin tarkunan yaki ina nemansa yanzu a tsakiyar fada yana gama fadin haka sai dakaru suka dare sai ga wani dattijo yafito fuskarsa cike da furfura amma da kaganshi kasan y asaba da kwarmatsuw a filin daga. sannan wasu samari guda biyu suka fito daga cikin jama'ar gari suma suka tsaya akusa da wannan dattijo. dukkansu suka rissina agaban sarki. dattijon ya rissina ga sarki sannan yace ni sunana zamnur kuma ina daga cikin manyan dakarun wannan birni kuma ina da ilimi na musamman wanda na koya a makarantar horon yaki tun ina matashi. dajin haka sai sarki yace to wacce irin shawara zaka bamu game da wannan yaki? dattijon yace ina da wasu tarkuna wadanda nake ganin zasu taimaka mana a wannan yaki sudai wadannan makamai bakomai bane face wasu kananan allurai wadanda ake daurasu asaman bishiyoyi. dazarar abokan gaba sun iso sai a tura dakaru kamar guda ashirin su watso wadannan allurai da zarar anyi haka zasu cake ajikin abokan gaba ba tare da sun lura ba saboda tsabar kankantar su. saidai daga baya dakarun zasu dinga fadowa daga kan ababan hawansu matattu koda jin haka sai sarki abu saiman yayi murmuashi yace tabbas wannan dabara taka tayi dai dai don haka zanuyi amfani da ita. sannan saurayi na biyu yafito ya tsaya gaban sarki yace ni sunana ruslan da ga sarkin dajin wannan birni mu a gidan mu akwai sihirin tsafin da mahaifin mu yabar mana na wadansu kunamai maau fuka fukai wadannan kunamai suna nan a cikin dajijjikan dake kewaye da birnin nan mahaifin mu a bincikensa ya gano da akwai wadannan kunamai sannan ya boyesu da karfin sihirinsa. kafin ya mutu saida ya barmana turaren da za'aje akunna shi acikin daya daga cikin dajijjikan wannan kasa. da zarar anyi haka bayan sa'a uku wadannan kunamai zasu baiyana su cigaba da aikin su na tsaron wannan birni. koda ya gama fadin haka sai ya koma kusa da tsoho zamnur ya tsaya. sai saurayi na uku shima ya fito gaban sarki ya tsaya yace nine sadauki huskan masanin taswirar dajijjikan dake wannan kasa. sannan nasan wadansu tarkuna da ake binne su a karkashin kasa. sudai wadannan tarkuna za'a hadasune da wani sinadarin magani wanda ake jikashi acikin sanan a sami manyan tuluna azubashi aciki sannan a sami igiyoyi adaure tulunan dasu. bayan anyi haka sai asami wasu dakaru su hau saman bishiyoyi da zarar abokan gaba sun iso sai suja wadannan igiyoyi. nantake tulunan zasu watsawa maykan ruwan dake cikin tulun. da zarar ruwan ya taba jikinsu nantake jinin jikinsu zai kafe su zama gawarwaki. koda wadannan mazaje suka gama fadar fasahar su sai sarki abu saiman ya bushe da dariya sannan yace tabbas kun bada shawara mai kyau,da kuma babbar gudun mawa don haka zamuyi amfani da ita. nan take ya sallami jama'ar gari baki dayansu sannan sannan ya shige cikin gidan sarauta WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN RAMLATUL SAIF BAYAN SARKI ABU SAIMAN YA HADA ZAMAN FADA ++ ++ ++ al'amarin yarima saiman kuwa lokacin da suka durfafi dajin kurusul saudam kuwa sai suka kasance cikin tsala azababben gudu saida suka shafe kwana goma suna tafiya sannan suka iso dajin kurusul saudam suna isowa sukayi arba da wasu dogayen bishiyoyi wadanda sai an daga kai sannan ake ganin karshensu suna isowa daidai wannan guri sai yarima saiman yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sannan jama'ar dake bayansa suma suka ja nasu linzaman dawakan. yarima saiman ya juyo ya dubesu yace wannan shine farkon dajin kurusul saudam don haka nanne gurin da zamu rabu daku nina tafi izuwa naman takobin sihiri bana bukatar taimakon kowa daga cikin ku har naje na dawo. taimako daya kurum nake nema agurinku. shine ku kula da lafiyar gimbiya suhaila har izuwa lokacin da zan dawo. koda gama fadin haka sai yarima yaga zamnal jikinsa yayi sanyi kawai sai yaji tausayinsa ya kamashi. nantake ya matso kusa dashi yace. kayi hakuri ka zauna kusa da jama'ata bana son arasa ko mutun daya daga cikin ku. don haka nake kokarin hanaku shiga cikin abubuwa masu hatsari. yana gama fadin haka sai ya nuna jama'arsa da hannunsa nantake wata raga mai kamar kejin karfe ta fito daga cikin hannunsa ta kewaye su yadda babu wanda zai iya fitowa daga cikinsu. sannan yace dasu daga yanzu babu wani hatsari dazai sameku har naje na dawo yana gama fadin haka haka sai ya juya da nufin ya shiga cikin dajin kwatsam sai yarima saiman yaga sararin samaniya tayi duhu. kawai sai ga aljani markazulu ya baiyana a saman kan yarima saiman. nan danan aljanin ya sauka a gaban yarima sainan nanfa aka soma kallon kallo atsakaninsu na tsawon lokuta sanan yarima saiman ya dubi markazulu yace kai kuma me ya kawo ka wannan dajin? kodajin haka sai markazulu yace nine markazulu tsohon hadimin boka ulumanu nazo gurinka ne don na nemi hadin kanka mu yaki boka ulumanu. kodajin haka sai yarima saiman ya turbune fuska sannan yace dashi bana bukatar taimakonka har abada don haka nan ne wajen daya kamata mu rabu dakai. bana bukatar na sake haduwa dakai nan gaba domin bazatayi kyauba. yana gama fadin haka sai ya kada linzamin dokinsa ya shige cikin dajin yabar markazulu atsaye. nan take ya bace bat tamkar bai taba wanzuwab. shikuma yarima saiman kutsa kai cikin dajin cikin gaggawa. a wannan lokaci zuciyarsa cike take da zumudin isa tsakiyar wannan daji don biyan bukatarsa. sai daya shafe sa'a shida yana tafiya acikin dajin sannan ya iso karshensa tun daga nesa ya dinga ganin dake cikinsa wasu irin many manya kirar mutanen farko jikinsu amurde yake tamkar sassaka su akayi da itace. fuskokinsu cike suke da gashi kai kace gwaggwan birine suna da jajjayen idanuwa tamkar angasa dan buda awuta. koda suka lura da tahowar yarima saiman sai daya daga cikinsu ya zaro wani kahon giwa ya busa nan take wata kara ta cika dajin gaba daya tare da amsa kuwwa. nan dan ragowar dakarun dake dajin suka lura da abin da yake faruwa nantake suka ruga da gudu suka soma debo makaman yakinsu domin tunkarar yarima saiman. sudai wadannan arnan dajin sunada matukar yawa domin zasu kai su dubu goma. sannan suna karkashin mulkin wani hatsabibin matsafi wanda yake shugabantarsu. kuma yasan dalilin zuwan yarima saiman don haka yasananr da ragowar dakarunsu don su san da zuwansa yarima saiman yana isa kusa da inda dakarun suke sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak sannan ya budi baki yace ku ma'abota rayuwar daji kananun jarumai wadanda suke tsoron rayuwa da mutane yan uwansu tamkar dabbobi to yau ni saiman na zo wannan birni domin na yakeku na zubar da jininku na hana zuluncin da kukeyi adoron kasa da kwacen da kukeyiwa matafiya akan hanyarsu. nayi alkawarin saina hallakar daku muddin bazaku yarda da sharadin danazo muku dashiba. sharadin kuwa shine inaso ku mikomini takibin sihirin da kuke bautawa cikin ruwansanyi domin mu rabu lafiya daku batare da an zubar da jini ba… kafin ygama fadar maganar dake bakinsa sai su shugaban wadannan arnan daji yafito asukwane bisa wani ingarman doki ya tsaya agaban dakarunsa. sannan ya bushe da dariya ya dubi yarima saiman yace lallai kayi kuskure da kake tunanin zaka kwaci maigirma takobin sihiri a hannunmu. inaso kasani cewa koda mutanen duniyane zasu taru basu isaba balle kai mutum daya tak yana zuwa nan a zancensa sai ya umarci arnan dajin dasu harbowa yarima saiman kibiyoyinsu nantake kuwa suka dana baka sukaharbo masa . saiga sararin samaniya tacika da kibiyoyi sannan suka durfafo kan yariman saiman nantake yarima saimanya zare takobinsa. sannan yasawani silken sihiri ya lullube dokinsa da ita gaba daya sanna ya shiga kade kibiyoyin da suke harbo masa cikin zafin nama,juriya da bajinta. wohoho hakika jarumtaka baiwace duk wabda allah yabaiwa ya huta. wani abin mamaki shine gani yadda yarima saiman yake kare hare haren da kibiyoyin suke kawo masa cikin kankanin lokaci. sai gashi anrasa kibiya ko guda daya wacce zatq iya lakutar jikinsa. sai bayan yan dakiku sannan kibiyoyin suka kare. nan fa dakarun suka rufo kansa aka kachame da azababben yaki nagaban kwatance. idan kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne bai zoba. domin duk da karfin damtse irin na wadannan dakru sai yarima saiman shi kadai ya gagaresu suka rasa yadda zasuyi dashi. domin yana wata jarumtaka ne taban al'ajabi wacce na tsaya fasaltamaka itama bata lokaci ne domin duk kwatancen mai kwatace bai isa ya fasalta maka irin yaki da yakeyi ba. awannan lokaci kasa ta soma girgiza,kura ta turnuke sararin samaniya saboda kwarmatsuwar da suke yi akan kasa. karar karafa ta cika dodon kunne,tare daihun mazaje,jini ya dinga fallatsi akan kasa tamkar an bude magudanar ruwa awannan lokaci sabodane saboda tsananin bala'i tsuntsaye suka dinga tashi suna chanza sheka. barewa suka dinga fadawa garken zakuna basu sani ba don su ceci ransu. duk inda yarima saiman yasa gaba saidai kaga mazaje suna zubewa kasa tamkar ana sassabe agona. duk da irin wannan mummunar barna da yake musu batasa sunja da bayaba.saboda tsananin naci tamkar basu ake kashewaba. sai wani irin karaji sukeyi suna dada kunno kai cikin rashin tsoro da yarda dakai. shi kuwa ya wanzu yana mai zare musu ruhin numfashinsu tamkar mala'ikan mutuwa Sai da suka shafe sa'a uku suna fafat wannan kazamin yaki tsakanin arnan dajin da yarima saiman. an rasa wanda zai sami galaba akansa ana cikin wannan haline yarima saiman yaji an gabza masa naushi da kafa agadon baya saboda karfin naushin sai da yarima saiman yayi tsalle kamar an janye shi da majaujawa. kamar zai fadi kasa amma saboda tsananin jarumtaka sai yarima saiman ya juya jikinsa a sararin samaniya sannan ya dire bisa kafafunsa. amma kafin ya dawo cikin haiyyacinsa sai ya sake jin an kara gabza masa wani sabon naushin a kirji wanda yafi na farko. saboda karfin naushin sai da yaji kamar kashushuwan kirjinsa sun kakkarye. bakowa ne yayi masa wannan duka face shugaban wadannan arnan daji. nan take ya takarkare ya bushe da dariyar farinciki sannan ya dubi yarima saiman yace lallai ka cika mai tsautsayin wahala tunda har kake shirin raba mu da takobin sihirin mu yanzu kai a haka zakaje ka yaki dodo garjaju har ka sami tsumin tsafinsa. sannan kaje fadar sarkin aljanu ka rabasu da miftahul darul sihir? hakika yanzu zaka hallaka sannan naje na kama ragowar mutanen da suke tare da kai namai dasu bayin mu. yana zuwa daidai nan a zanncensa saiya zare takobinsa ya nufo kan yarima saiman da nufin tsige masa kai. ba zato ba tsammani sai yaji wata irin iska mai karfi ta taso ta shureshi ta damfara shi da kasa bakowa bane yayi wannan aikiba face aljani markazulu nan take ya tashi yarima saiman zaune yace kai jeka ka tari shugaban yan fashin ni kuma zanje na tari ragowar dakarun in yaso idan na gama dasu sai in taimakama. yana zuwa daidainan azancensa sai ya shige cikin dakarun ya hausu da sara da suka ta ko ina babu kakkautawa duka inda ya nufa saidai kaga arnan dajin na zuba a kasa tamkar ana sassabe agona. shi kuwa yarima saiman sai ya gyara rukon takobinsa ya nufi inda shugaban arnan dajin yake kai tsaye. nan fa aka soma kallon kallo a tsakaninsu kai da gani kasan kar ce ta san kar. har na tsawon dakiku daga chan sai suka ja da baya kamar tazarar taku goma atsakaninsu. sannan suka gyara rukon takobinsu suka rugo kan juna suka kacame da azababben yaki mai matukar muni fiye da wanda akeyi tsakanin aljani markazulu da ragowar dakarun arnan dajin. sai fadan nasu ya zamo abin tsoro kuma abin sha'awa sakamakon yadda suke fadanda dukkan karfin su. shidai shugaban wadannan arnan daji wani irin gabjejen mutum ne mai kirar muatanen farko sannan yana da manya manyan idanu jajaye masu matukar kwarjini. kirjijsa faffada ne cike da gashi.sai kace zaki. yana da manya manyan damatsa kamar jerasu akayi. kai duk inda mutum mai suffar karfi yakai to wannan mutum yafishi cika ido shi kuwa yarima saiman sai ya zama dan karami akansa. amma duk da haka sai gashi ya kasa samun nasara akan yarima saiman saboda matukar karfin damtsensa. dajuriyarsa da kuma nacinsa. hakika yarima saiman ya isa a jinjina masa ganin yadda yake yaki da mutumin da ya fisyi kwarjin da cika idanu. dukkansu suna yi fadanne cikin mugun nufi da burin salwantar da rayukan juna. koda suka dau wani lokaci suna wannan fafatawa . sai dukkansu suka ja da baya. suna hararar juna kamar zakaru. daga chan suka sake falfalowa da gudu suka sake kachamewa azababben yaki fiye da farko. sai gashi suna hadawa da sara da suka sama da kasa. har tsalle sukeyi suna kai farmaki ko kuma wani lokacin kaga suna zamiya akasa. awannan karon ma sai aka kasa samun wanda zai nasara daga chan sai shugaban arnan dajin yayi wurgi da takobinsa. sannan yace da yarima saiman tunda dai munga salon fadan namu iri dayane to mai zai hana mu gwada karfin damtsen mu banbance tsakanin aya da tsakuwa. kodajin haka sai yarima saiman yayi murmushin yadda dakai sannan yayi wulli da takobinsa. nan take suka kachame da kokawa. awannan lokaci sai fadan nasu ya chanja salo domin ana fara fadanne kowanne daga cikinsu jikinsa ya fara gaya masa. duk sa'adda yarima saiman ya sami nasarar dukan shugaban yan fashin sai kaga shima ya rama kamar dama chan sun tsara haka fadan zai kasance. ana cikin haka yarima saiman yaga idan suka ci gaba da fadan ahaka to zasu iya yi ragas. kawai sai ya shammaci shugaban arnan dajin ya yi tsalle ya kama kansa ya murde sannan ya wullar da gawarsa gefe daya. koda ragowar arnan dajinsuka ga gawar shugabansu a kasa sai suka zubar da makamansu. suka ruga da gudu nan take yarima saiman ya tashi ya dinga taimakawa markazulu suka dinga binsu suna rafkewa. kafin cikar wasu yan dakiku sun gana hallakasu. koda suka karar dasu sai yarima saiman ya juyo ya dubi markazilu sannan yace . wai kai meyasa kake bibiyata ne shin ban hanaka biyoni ba? kodajin wannan tambaya sai markazulu yace kayi hakuri yakai wannan jarumin jarumai bana biyo ka bane don na cuce ka ba. na biyo kane kawai don nasan ra'ayin mu daya dani dakai ma'ana na yakar boka ulumanu. kodajin haka sai yarima ya sake tambayar sa yace to menene dalilin da yas a kake da burin yakarsa? kodajin wannan tambaya sai aljani markazulu yayi shiru kamar bazaice komi ba. daga chan sai yace mun sami sabani da uban gidanane sakamakon nima na sami babban matsayi a fannin sihir. koda gama jin haka sai yarima saiman jinjina kansa azuciyarsa yace tabbas akwai wani boyayyan sirri a zuciyar markazulu. don haka dolene nasa idanu aknsa. kawai sai yace da markazulu. shikenan na amince da tafiya tare da kai. amma da sharadi. sharadin kuwa shine bazakaci amanarmu ba. kodajin haka sai markazulu yace na amince da wannan sharadi naka. nan take suka kama hanya suka shiga cikin garin arnan dajin. sai da suka wuce sa'a biyu sannan suka iso kofar wani babbar fada. LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME DOMIN SAMUN CIGABAN SAI KU KASANCE DA MU A KODA YAUSHE DAGA SHAFIN WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG BAKAR GABA Littafin HABIBULLAH Muhammad kabara Kashi na biyu 2 Ebook created by Shuraih Usman 99% Published at WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) LITTAFIN BAKAR GABA PART 6 LBR HABIBULLAH KBR TYPING HABIBULLAH KBR Ita dai wannan fada an ginata ne da zallar duwatsun wuta. kuma tana da girman gaske tamkar fadar wata babbar masarautar. kofar fadar an sana antatane da zallar bakin karfe mai matukar karfi. koda suka iso daidai wannan wuri sai suka tsaya sukayi cirko cirko sakamakon rashin sanin makullin da za'a bude wannan kofar. daga chan sai yarima saiman yace da aljani markazulu yanzu taya kake tunanin zamu iya bude wannan kofar dajin haka sai markazulu ya bushe da dariya sannan yace don dai wannan kofar aini kadai zan iya budeta. nan take markazu ya karasa jikin kofar ya tattara karfinsa ya kamata da nufin ya budeta. nan take jijiyoyin jikinsa suka tashi sukayi burdin burdin gumi ya dinga tsatstsafowa daga jikinsa. amma saidaya shafe yan dakiku kuma kofa taki buduwa. bisa dole ya saki kofar ya koma gefe yana mai zare idanunsa. sannan yace da yarima saiman tunda dai karfina ya kasa bude wannan kofar to mai zai hana muyi amfani da karfin sihirin mu? kodajin haka sai yarima saiman shima ya matso kusa da markazulu yace to shi kenan mu jarraba mu gani. nan take suka bude tafin hannuwansu sannan suka karanta wadansu dalasimai na tsafi. nantake wata irin iska mai matukar.karfi ta fito daga tafin hannunsu ta tafi da gudu izuwa jikin wannan kofa. koda saukar wannan iska sai wata irin tsawa mai karfi ta tashi. amma duk da haka ko kwarzane babu ajikin kofar koda ganin abinda ya faru sai yarima yace da markazulu koda ace zamu hada sihirin mu gaba daya bamu isa mu iya bude wannan kofa ba. don haka ina tunanin makullin wannan fada yana jikin shugaban wadannan arnan daji don haka sai mu gaggauta zuwa mu duba jikinsa mu dauko makullin. koda gama fadin haka sai markazulu yace an gama nan take ya bude fuka fukansa ya luluka cikin gajimare kafin cikar dakika uku yaje ya dawo da kubar kogon itadai wannan kuba yar mitsitsiyace kamar misalin allura haka girmanta da kaurinta yake. koda dawowarsa sai ya mika wa yarima saiman wannan kuba. yarima saiman ya karbi kubar sannan yaje jikin wannan kofa ya zurata sannan ya murda. nantake wata irin kara ta cika dajin gaba daya sakamakon zarewar wasu manyan sakatu. koda kofar ta gama budewa sai suka kunna kansu cikin fadar. suna shiga cikin fadar sai suka cika da mamaki domin fadar ta kawatu ainun fiye da tunanin mai tunani. saboda komai na fadar an kerashine da zallar karfen zinare. sannan kuma akarshen fadar an ajiye wata karagar mulki ta alfarma sai kace fadar wani babban basarake. ahankali su yarima ci gaba da tafiya acikin fadar har suka iso dai dai kan karagar mulki. koda suka iso dai dai wannan karaga sai yarima saiman yaga wani dan karamin.littafi mai ban sha'awa kuma.littafin a manne yake .ajikin wani dan karamin teburi dake gaban karagar mulkin. ma'ana shidai wannan littafin ba'a daukarsa saidai duk amfanin da zakayi kayi dashi a inda yake. nantake wannan littafi ya baiwa yarima saiman sha'awa don haka sai yafara duba littafin shafi shafi yana karantawa. littafin yana daukene da hotuna kala na abubuwan ban sha'awa. yana cikin karanta littafin ne sai yayi arba da wani kyakkyawan fure mai jan launi. babu abindaya bashi sha'awa kamar wannan fure don haka yakai hannu ya shafa wannan fure yana shafarsa sai yaji wata kara ta cika fadar gaba dayanta. nan take kasa ta tsage saiga wata siririyar hanya ta bayyana izuwa wani gidan karkashin.kasa. koda ganin abindaya faru sai aljani marakzulu ya kalli yarima saiman cikin firgici yace. karka sake ka shiga wannan gida domin zai kaikane izuwa ga hallaka idan zaka karbi shawarata karka shiga cikinsa. koda jin haka sai yarima ya bushe da dariya yace haba abokina kar ka bani kunya mana. kadafa ka manta sadauki baya amsa sunansa sadauki sai ya sha wahala a arayuwarsa sannan kuma ni ina da tabbacin cewa a.cikin wannan gidan karkashin kasa zamu samo takobinda mukazo nema. yana gama fadin haka saiya.shige cikin wannan gida nan take markazulu ya bishi a baya suka.shige cikin wannan gida. koda.suka.gama.shiga sai suka gansu a wani dan karamin daki. a tsakiyar dakin suka ga wani dan karamin teburi na.dutsen lu'u lu'u asamansa an ajiye wata takobi wacce aka sana'anta ta da zinare nantake suka karasa da sauri kusa da takobin suna zuwa sai aljani markazulu yakai hannu da nufin daukar takobin koda.ganin haka sai yarimA saiman ya daka masa tsawa yace kana.taba wannan takobi zaka kama da wuta ka kone kurmus kuma.in baka yardaba sai ka.gwada tofa.yawu ajikinta ka gani. kodajin haka sai markazulau ya cika da mamaki sannan yace da yarina to menene dalilin haka. yarima saiman yace ai bakaine ka kashe shugaban wadannan arnan dajinba nine na kasheshi. don haka nine nake da alhakin gadon abubuwan daya mallaka. yana gama fadin hakan sai ya je ya dauki takobin. faruwar hakan keda wuya sai kogon ya soma girgiza yana shirin ruguzowa. nan take su ka juya suka kama hanya cikin tsala azababben gudu suka nufi hanyar fita daga kogon.duk inda suka wuce saidai kaga gini yana zabtarowa kasa. cikin sa'a suka fice daga fadar ba tare da wani abu ya sami daya daga cikinsu ba. suna gama fitowa daga cikinta sai fadar ta gama rugujewa gaba dayanta sannan ta nutse a karkashin kasa. nan take duk su biyun suka tsuguna bisa kafafunsu suna haki kamar ransu zai fita. sai da suka shafe yan dakiku suna hutawa sannan yarima saiman yace yau na wuce mataki na farkon wanda shine mai mugun sauki don haka zama bai kamaniba yanzu zan tashi na.koma cikin jama'ata kai kuma markazulu sai kaje zan nemeka nan gaba don indai ina tare da kai mutanena bazasu taba samun kwanciyar hankaliba.. dajin.haka si markazulu yace nima dama abinda nake tunani kenan dan uwana sai an jima.ina yi maka fatan alkairi yana gam fadin hakan sai ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba. shi kuwa yarima saiman sai busa wani kaho dake jikinsa.wanda yake kiran dokins.da shi. kafin cikar yan dakiku saiga dokinsa ya taho da gudu yana harbin iska. koda yazo dai dai inda yarima yake sai ya tsaya chak. nan take yarima saiman yayi tsalle ya haye kan dokin sannan ya sakarwa dokin nasa linzami ya nufi inda yabar jama'arsa cikin sa'a guda yarima saiman ya isa sansaninsu koda jama'arsa suka ganshi ya dawo cikin samun nasara sai suka cika da tsananin murna suna shewa daga inda suke domin basuda damar fitowa daga cikin ragar sihirin da yasaka su aciki koda ya gama karasowa inda suke saiyaja linzmin dokinsa ya tsaya cak sannan ya sauka daga kansa yaje gaban wannan ragar sihirin ya shafeta da hannunsa na hagu nantake ragar ta bace bat nantake jama'artasa suka kamayin tsallen murna har suna dagashi sama suna yi masa kirari saida suka dan shafe yan dakiku suna wannan shagali sannan yarima saiman ya daga musu hannu nantake kuwa wajen yayi tsit kamar mutuwa ta gifta yarima saiman ya dubi gaba daya mutanensa yace yaku ahalin birnin ramlatul saif kuyi sani cewa yanzu haka munshafe tsawon kwanaki muna wannan tafiya alhalin anaso muyi wannan tafiyar acikin watanni goma don haka ni bansan tsawon lokacin da zamu dauka awannan tafiyaba saboda haka nake so mu tsawaita tafiya mu rage yada zango don mu isa da wuri kuma acikin wannan tafiya inaso idan mun isa bakin wani garin zan shiga na sayo keken doki saboda na baiwa matata cikakken tsaro saboda duk burin mu gaba daya akanta yake itace nasarar tafiyarmu gaba daya yanzu inaso mu yada zango awannan wurin zuwa gobe da safe sai muci gaba da tafiya gaba koda yagama bayaninsa sai ya juya ya dubi shugaban dakarunsa zamnas yayi murmushi yace yakai zamnas na sani cewa hakika kai kana daga cikin masoyana na gaskiya wadanda suke kokarin sayar da rayuwarsu domin tawa tabbas ina godiya agareka sosai kuma ka sani daga wannan lokaci kana da damar ganawa dani aduk sanda ka bukata saidai ina da bukata guda daya awajenka bukatar kuwa itace inaso ka kasance mai kula da bukatar jama'armu fiye da yadda kake kokarin kula da tawa domin nasan kaima jarumi

Chapter 3 of 14