Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ." gyaran murya aunty shahida tayi kana ta soma mgn "burinka ya cika AD domin kuwa maryam taki amincewa da aurenka juyin duniya munyi daita tace bata sonka bata ga abinda zatayi da aurenka ba shikenan sai hankalinka ya kwanta ka zuba ruwa a kasa kasha tunda kai ma alal lalurati zaka aureta ba dan kana sonta ba , amman kasan da sani bazaka cigaba da zama haka ba dole ka fito da mata Kuma cikin wannan lokacin kayi aure dan kwancinyar hankalin mahaifiyarmu .." ban san dalilin da yasa kake kin yarinyar nan ba  batare da wani huja ba wallahi sam banji haushinta ba kaso mai sonka haka zalika Kaki mai kinka inji cewar aunty khadeja wacce ta k'arasa maganar cikin tsananin fushi tana jan tsaki a fili wani mugun kallo ya watsa mata mai had'e da harara yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa , ta kawar da kanta gefe tana zuba tagumi ." Shiru kowannensu yayi bayan sun gama zayyane abinda ke ransu shi kuwa yafi minti ashirin yana zaune zuciyarsa na wani irin bugawa batare da yace uffan ba kafin daga baya ya motsa lip's dinsa a hankali "sweetheart tasan da wannan maganar ?ya tambaya yana kafesu da Kyawawan idanunshi masu matukar kyau da bugar da zuciya sai dai a yanzu kallosu kawai zai sa ka fahimci tashin hankali da balain dake cikinsu "bata sani ba amman dole zata sani Kuma a yanzu "A hankali ya dinga girgiza kafarsa d'aya yana cizan lip's dinsa na kasa yana maimata Kalmar da aka fada masa mrym tace " bata sona ? wannan karon a fili ya fad'a yana kallon aunty shahida zuciyarsa na zafi da quna da tuttukin bakinciki mara misaltuwa ,kai tsaye tace "tabbas abinda ta fad'a mana kenan kai daga gani ma tana da wanda take  so....."stop aunty shahida karki fad'a min haka mana taya zatace bata Sona?" wacece ita dan ubanta da har zata ce bata son Adam Tariq Abdullah ?"mace mai daraja da zuciya mai kin wanda yake kinta" ta bashi amsa da haka tana zabga masa katuwar  harara." murmushin gefen baki yayi wanda yafi kuka ciwo yana girgiza Kai "impossible babu wannan macen a fad'in duniya da zata ce bata son ni Adam wallahi ta raina muku hankali ne sannan tayi balain rainaku ni ko giyar wake ta sha bazata ta'ba fada min haka ba , numfashi ya sauke a maganarsa ta karshe sannan ya mike tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin ajihun wandonsa ya soma taku kamar baya son taka kasa yana k'okarin barin parlour'n a matukar fusace har ya Kai bakin kofar fita ya tsaya cak batare da juyo ba "abar maganar nan a tsakankanimu banason sweetheart tasan komai zan san abunyi .." "Da dai ya fiyye maka ka ajiye wannan shegen girman kan naka ka fuskanceta da kanka wata Killa zata yarda "inji cewar aunty shahida " ai ni idan na fuskanceta umarnin kawai zan bata Kuma dolenta tabi umarnina koda kuwa mutuwa zatayi yana gama fad'ar haka ya k'arasa ficewa  daga parlour'n bai tsaya jin abinda zata ce ba . girgiza Kai sukayi a tare "kinji ba aunty , kinji abinda yake cewa ko ?"wato shi bazai rusunar da kai ba, Komai ta karfi zai yi byn ita mace yar rarrrashi ce ." Allah dai ya shirya AD yasa ya gane kuma ya wanke masa wannan zuciyar tasa aunty shahida ta fad'a . bedroom din hajiya zulaiheart suka shiga suna qoqarin danne damuwarsu dan karta fahimci komai a hankali suka dinga nuna mata babu wata matsala sunyi mgn da maryam kuma ta amince "masha Allah "Kai alhamdulillah amman naji dadi Allah yayiwa rayuwarsu albarka wannan aure Ina son shi Ina qaunarsa Ina farinciki dashi yanzu sai a sanar da baba babba  shi kuma ya nemi sauran yanuwansa aje neman aurenta gurin saidu ko ? "wannan haka ne amman ki dan tsaya tukun kinsan halin 'yan kayanki muna son ya dan saki jiki da mrym din su samu fahimtar juna sai ayi maganar aure hjy zulaiheart ta gyada Kai tana murmushin jin dadi  "wannan ma shawara ce  mai kyau Allah ya daidata tsakaninsu dan mrym bani da matsalata daita , nan sukayita biyewa hjy zulaiheart dan basa son tasan abinda ke faruwa ta shiga damuwa , domin kuwa muddin tasani akwai gagarumin tashin hankali a gidan ." "Yana shiga d'akinsa zariya ya soma yi daga farkon d'akin zuwa karshe ya kasa zama kamar wanda yayiwa sarki karya can ya tsaya cak yana jan tsaki har lokacin mamakinta yake dan yasan aunty shahida baza ta'ba fad'a masa qarya ba daya qaryatata cikin zafin nama ya soma balballe botiran gaban farar rigar dake sanye ajikinsa ya cire sannan ya zame ash three quarter din da yake sanye dashi ya shiga toilet yana sake jan tsaki ya kunnawa Kansa ruwa yana jan numfashi da rarrashin zuciyarsa tare da son karyata zuciyarsa akan jin haushin maganar yarinyar shiru yayi ruwan na sauka ajikinsa " dole yana bukatar saita kanshi dan ya samu damar tarwatsa zuciyarta cikin ruwan sanyi ban da ma hauka da jakanci irin nata Ina ita Ina shi Adam ai sai dai darajan iyaye ? shi da yake da mace kamar  princess yarinyar da ta samu kyakkyawan mazauni a zuciyarsa me zai yi da mai jiki kamar na turkey, abinda batasani ba da abashi mace irinta gara ya kare rayuwarsa babu aure yana cikin toilet ya dinga jin sautin qarar wayarsa bai fito ba sai daya samu natsuwa sannan ya fito d'aure da white towel iya gwiwarsa ya tsaya gaban mirrow yana karewa kanshi kallon tsab sannan ya sauya kaya riga armygreen da wando baki kafafunsa sanye da takalmi fari sol ya zauna shiru akan kujera duk yadda yaso ya cire damuwar rashin son shi da'akace mrym batayi abun ya cutura wani irin zabura yayi ya mike  ya kwashi wayoyinsa ya fito zuwa haraban gidan Inda security da escort dinsa ke faman safa da marwa suna ganinsa suka hau kikiniyar bud'e masa bayan mota suna furta" barka da fitowa ranka ya dade ya shiga ya zauna fuskarsa a hade batare daya amsa ba direbansa yayi saurin shiga mazaunin direba "aka bude makeken get din gidan ,motor daya da direba da wasu escort sukayi gaba sannan motar da Mr ATA ke cikin sai daya a bayansu suka bar gidan suna hawa kan titi kira ya shigo wayar direba sai daya nemi izini agurin A Mr ATA sannan ya d'auka mgn daya ya katse kiran Tare da tmbyr mr ATA"ranka ya dade Ina muka nufa ne ? "gdn mb ya fada ataikace yana kallon gefe titi zuciyarsa na zafi ,tafiya mintuna kadan sukayi suka k'araso ikeja gra a kofar gidan suka ja suka faka suka yi saurin firfitowa suka zagaye motar da Mr ATA yake ciki ,daya daga cikinsu ya bude masa murfin mota , masu gadin gidan muhd bello na ganinsa suka fara rawar jikin da kokarin kawo gaisuwa. " Kai tsaye ya shiga gidan batare da neman iso ba waje ya samu a rumfar dake ajiye da kujera na alfarma dake haraban gidan ya zauna ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya wannan ya rigada ya zame masa jiki no matter how ya zauna sai ya d'aura kafa daya a kan d'aya , hannunsa daya ya d'aura a kan table yayinda wayarsa ke manne da kunneshi yana neman layin MB cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa ."sai da gabansa yayi mugun bugawa hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Mr ATA , ya zauna kusa dashi yana kallonsa "Lafiya friend na ganka haka kmr kana cikin damuwa ?" shiru yayi masa zuciyarsa na zafi da tafarfasa kmr zata kama da wuta "please talk to me friend what's wrong with you ?"yin duniya mr ATA yaki magana shiru Shima yayi yana kallonsa zuwa sanda mai aikinsa ta k'araso rike da tire dake d'auke da ruwa da lemuka masu sanyi tun kafin ta k'araso ya amsa a hannunta dan yasan yadda mr ATA ya tsani ganin fuskokin masu aiki ya ajiye akan table ita Kuma ta juya da sauri .ta kasan idanunshi yake kallon yadda take daga ka'fafunta haka nan ya tsinci kanshi da kallon every step of her  zuciyarsa na quna ." MB ya tsiyaya masa ruwan ya mika masa "Kar'ba ka sha ka dan ji sanyi ATA ya numfashi ya sauke numfashi kana ya nuna masa kan table "ba ruwa nazo sha ba MB wai har ni wanan stupid monkey din zata ce bata so ......?"yayi maganar yana nuna qirjinsa da d'an yatsansa . a matukar firgice MB yace "who's she ?"wannan monkey revenble person din mana har ni zata ce bata so? " is a lie she just say it "ka natsu plz nifa ban ma fahimceka ba amman duk da haka nasan babu macen da zata ce bata sonka "wannnan yar iskar yarinyar diyar kanin sweetheart dake fama da danyen jiki kmar daga alhalin china aka samota yayi maganar a tsawace yana dukan table din gabansa nan take tire da glass cup suka tarwatse MB bai tsaya bi ta kansu ba ya riko hannuwansa duka cikin nashi dan gbdy zuwa yanzu ya fahimci ko wa yake nufi  "calm down ATA ba fushi yakamata kayi ba soyayya haka take kayi hakuri ka natsu musan abunyi tunda kaji kana sonta yanzu shawo kanta bazai yi mana wa......" MB yayi saurin katse maganarsa sakamakon wani mugun kallon da ATA ya  watsa masa yana zare hannuwansa dake cikin nashi "nace maka Ina sonta ne ? MB yayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "to me yasa kace Ina Sonta ?wai naga kamar ka damu ne" "to bana Sonta kuma har abada bazan sota ba Koda kuwa tazamo mata agareni wallahi bazan sota ba kai bancin darajan sweetheart bazan ta'ba iya aurenta ba, bugu da kari ni mallakin princess ne ba kowace mace ba ,Ina son yarinyar  nan MB Ina zaka nemo minta ?na saka 50 billion ga duk wanda ya nemo min ita ka taimakeni abokina ka tayani nemota wallahi muddin na auri yarinyar nan zan cutar da zuciyata sannan zan cutar da yarinyar mutane dan bana son mace irinta bazan yi mata adalci ba bazan iya italic ba  ." "Is okay ATA Ina iyakar kokarina wallahi amman zan qara ya kife kanshi akan table kmr wani karamin yaro zuciyarsa na zugi da rad'adin bakinciki "kayi hakuri friend ka sanyaya zuciyarka maryam bazata kika ba sai dai ta furta hakan ne adalilin yadda kake mata amman ni zan sameta muyi magana kune da kune da fahimta nasa zata fahimceni km zata yarda da au.. ."karka yi MB ka barta kawai kar Allah yasa ta amince  "no no !! baza'a yi haka ba ai ba saboda ita ba darajan sweetheart zata ci, kasan yadda ta damu kayi aure , hakuri kawai zakayi  a shawo kanta " ai bana sonta  MB , ta'ba kaji yadda qirjina yake bugawa ,km  yana bugawa ne duk akan yarinyar mafarkina tunda na fara mafarkinta ban sake samun natsuwar zuciyata ba burina na ganta na mallaketa " yayi mgnr yana furzar da iska tare da kamo hannun MB ya kai daidai saitin zuciyarsa dake beating very fast . " ban taba jin soyayya ba irin wanda kake wa yarinyar nan " "wallahi ni kaina nakan zauna Ina wannan tunani MB ban taba gajiya da tunaninta ba daidai da second daya soyayyarta bata raguwa sai ma karuwa ya karasa maganar tare da yin shiru qirjinsa na dokawa da matsanacin karfin gaske". maganganu masu sanyi MB ya dinga rarashinsa dashi har zuciyarsa ta dan yi sanyi a karshe yace "ka rage tsanar yarinyar nan ATA saboda baka da hujja tsanarta kabi umarnin mahaifiyarka kawai ku rabu Lafiya ita irin wannan tsanar idan ta juyi zuwa soyayya abun ba'a magana please aboki kabar komai a hannuna zan san abun yi ". shiru ATA yayi kawai yana jinsa amman sam baya jin zai sota a rayuwarsa ko neman soyayyarta tare suka je matsalaci basu dawo ba sai da suka gabatar da sallahar ishai sannan suka dawo MB yayi dashi ya shigo suci abincin dare amman sam ATA yaki sai ma cewa yayi ya gaishe masa da madam da yaransa sadiq da hanif ya shiga mota suka d'auki hanyar gida ."hancin motar da yake ciki na shiga haraban gidan idanun maryam ya sauka akansa hakince a byn mota kanshi na sunkuye da alamun Idanunsa na kallon screen din waya ne , motacinsa na kokarin daidaita tsayuwa ita Kuwa tana zaune a baradan dake zagaye da kofar shiga ainin babban falon gidan akan fararen kujerunsa tare da lawan d'an PA din gwana kano,da kyar da balai ta fito gurinsa har sai da hjy zulaiheart tasa baki tace "taje su rabu lfy wulakanta dan adam bashi da amfani ,Jin motor  ya tsaya ya dago idanunshi a hankali karaf ya sauka akansu Aiko ya balain had'e rai har sanda aka bud'e masa murfin mota ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ta kasan idanunshi yake kare musu kallon tsaf acikin hasken daya haskaka gurin sai dai idan ba kwakwaran sani kayi masa ba bazaka gane su yake kallo ba .." Gabanta sai luguden bugawa da ganinsa yake sai dai hakan bai sa ta tsaida maganar da ta fara ba "Lawan ka daina zuwa gurina saboda banason abinda zai sa na dinga maka wulakanci, "idan har kina ganin daidai ne abinda kike min ki cigaba mrym , numfashi ta janyo da kyar ta sauke" ni dai lalla'baka nake amman ka gagara ganewa ,"to meye dalilin da bazaki amshi soyayyata ba ? yayi mata tambayar adaidai lokacin da AAT ya k'araso gurin. tayi shiru saboda buguwar zuciyarta daya qaru Shima lawan shiru yayi yana kokarin mikewa domin gaisawa da ATA Amman Ina bai tsaya bin ta kanshi ba tuni ya shige ciki . ya koma ya zauna yana kallonta "Uhm ki bani amsar tambayata Ina jinki me yasa baki Sona me na rasa mrym? yayi mgnr yana kallon jikinsa a ranta tace "many things lawan hatta sunanka bai min ba bare akai ga surar jiki sai data hadiye abinda ya tsaya mata a makoshi kana ta cigaba "Ina son namiji fari sol dogo sannan intelligent abinda zai kara kashe ni ya zamanto yana da tsoron Allah shikenan ya gama da rayuwata zan iya mutuwa akanshi " kasancewar mu bakake yasa ba'a sonmu kenan ? a'a bance bakin mutun bai yi ba amman ni dai a gurina mutun fari sol nake so Irina wallahi ni ko nmj baki zai bani rabin duniya akan sadakina bazan amsa ba na fison kalata dan banason black .."sake baki yayi yana kallonta gbdy yaji ya munzata aguri dan shi baki ne sitik kuma ba wani mai tsawo bane can sai dai baza'a Saka shi cikin sawun gajeru ba tun bai kai ga magana ba ta mike tsaye  "to malam lawan ni zan shiga ciki ta nufi hanyar part dinsu bayanta yabi da kallo yana aiyana abubuwa dayawa akanta sai dai baya jin zai iya hakura daita dan yana son farar mace koda kuwa mayya ce . Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 8 "Ahankali  take tafiya cikin sand'a  tamkar   wata  'barauniya  yana   hankalce  daita  duk da idanunshi a runtse  suke amman bazaka ta'ba gane hakan ba  sai wanda yayi masa cikakken sani , da d'an sauri   ta nufi  hanyar d'akinsu  tana sauke numfashi  Tare da ajiyar zuciya ,ta cire mayafinta ta wula saman katifa sannan ta samu waje ta zauna tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa zuciyarta a matukar tsorace take  duk da tasan ba wani laifi tayi ba amman tasan tsoronta baya rasa nasaba da muguwar kiyayya da tsana mai tsananin  da ya adam yayi mata  tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta sam  bata hango ta inda zata iya amincewa aurensa ba gara kowa yaje ya nemo abokin rayuwarsa a waje domin rayuwar aure dashi daidai yake da kamuwa da cuttutuka kala dabam dabam ."        "mr ATA ya cigaba da zama a parlour'n yana karkada kafarsa daya har sanda  hajiya  zulaiheart ta shigo parlour'n fuskarta a sake amman ganin  yanayinsa yasa ta d'an shiga damuwa muryarta a raunane ta soma mgn "Adamcy nah  har ka dawo ? ya had'e rai sosai  tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa  tare da gyada mata Kai kawai batare da yayi magana ba "Lafiya naga duk kayi wani iri ?fuskarshi a murtuke ya soma magana cikin tsananin fushi "wa yace waccen yarinyar tayiwa saurayinta masauki  akan  kujerun zamana ?mami ta numfasa irin nasu na manya kana tace " ban da abunka Adamcy wa zai sa tayi haka ?" ta dai yi haka né dan tayi ra'ayi  tô ma  menene aciki dan ta zauna da bakonta  akan kujerarka kwana nawa ne ma ya saura ?"ni  dai babu ruwana da wani kwana nawa ne   ya saura ni dai banaso  dan  ba ra'ayi bane kawai  raini  ne  idan ba haka ba kujerun da  nake zama akai shine ya zama na zancenta?yayi maganar yana shan kamshi ." "Kai dai wallahi anyi rigimamme wannan zuciya wannan zuciya !! Allah ya sausauta maka, bakaken magana ya dinga fad'a akan maryam batare da yayi la'akari da matsayinta a gurin mahaifiyarsa ba  mami batace komai ba har sanda ya dasa aya sannan ta kira sunansa a tsanake  "Adam !bai amsa ba illa ya tsura mata kwayar idanunshi dake cike da bakinciki yana kallonta ta sake kiran sunansa "adam ! "a karo na biyu  shiru yayi still yaki amsawa tunda yayi haka tasan bazai amsa ba yasa ta soma magana cikin kaukausan murya "zaka iya yin komai da kake so  amman at least kayi respect din emotion din wani idan kai baka  son maryam ka girmama masu sonta  kuma naji dadi da hakan ya faru domin kasan diyata  ba rasa masoya tayi ba yasa zan  hadaku aure." wani kallo yayi wa mami yana mai rausayar mata da kwayar idanunshi cikin nata muryarsa can kasa yace  "alright  sweetheart amman da me zai hana ku  bar masa ita  ya aureta dan zata fi bukatarsa   da duk wani abinda kuke bukata daga gurina "tabbas nasa zata samu, zata samu duk wata kulawa a wajen duk wanda ta aura acikin masoyanta domin kuwa suna mata   tru love  most especially lawan kalli kaga irin abubuwan daya zo mata dashi ."ta fad'a dan qara masa haushi dan babu abinda ya tsana sama da wannan arayuwarsa ,ai kuwa tayi nasarar takalosa."      " He most be a fool  da har yake bayyanawa common mace emotiona dinsa  ta wannan hanyar , Kinsan allah sweetheart  ko mafarkina na hadu daita a zahiri bazan iya mata  irin wannan haukan ba ta zabga masa harara alokacin da yake kokarin yunkura wa  zai mike  ta dakatar dashi "adam !koma  ka zauna ya koma ya  zauna a kufule yana dubanta "kowani dan adam da yadda yake irin tashi soyayyar idan kai abubuwan bai maka ba watakilla su samarinta  ya masu ,dan  kyauta yana da matukar kyau ga masoya domin yana qara damkon soyayya  dan haka kar na sake jin  ka fadi haka ,kai kullum kana yin kuskure amman kai gani kake daidai kake aikatawa ,kowani dan adam yana kuskure amman wannan bana tunanin akwai wani kuskure acikisa sai ma kyautatawa soyayya sam  sam bana jin dadin abinda kakeyi ...." "to ku aura mata shi dan allah kunga ni  na huta daman ni wallahi bana sonta dan wannan auren babu abinda zai jawo sai damuwa I really has to tell you the truth before everything could mess up ya fad'a a matukar zuciye ."murmushi hjy zulai tayi dan gbdy ta fahimci dan nata haushi yaji koma tace kishi yake yaga maryam da wani ,ta  girgiza kai "ai kasan bana magana biyu tunda muka tsaida  magana  da mahaifinta idan kaga baayi auren nan ba to mutuwa nayi ,idan ba mutuwa nayi ba kuwa na rantse da girman allah  adamcy sai ka aureta kai ko yau na mutu a daura maka aure daita zan bar wannan wasiya  maryam takace ta har abada haka zalika kaima nata né mutuwa ce kawai zata rabaku sannan kai ma muna jiran naka gift din soyayyar tunda ka kamu  idanushi ya ware sosai akanta  yana kallonta a rude tare da furta kalmar "what ? " your gift ! ta fad'a tana tsare shi da idanunta "Allah ya tsareni da wannan shirmen hau..."shut up Adamcy ai baka da wannan bakin dan ka rigada ka haukace tunda kake son abinda babu shi a duniya kuma lallai ka tabbatar da ka kawo naka gift din soyayya ranka shi dade a matukar zuciye ya juya ,da sauri sauri ya dinga taka step zuciyarsa kamar ta kama da wuta ta sake saida shi "adamcy nah !wannan karon a fusace ya juyo kamar zai yi kuka  yace "what again ?  "kaje kayi wanka ga dinner dinka ya kammala "bana bukata ya fad'a a kufule  ."this is totally nonsense my love ta furta tana sakar masa murmushi dan tasan bancin itace da abinda zai fad'a kenan a fusace ya sake  juyawa  yana girgiza kai ." Hjy zulai zaune  tana sake duba  kayan da lawan ya kawo  ta kiran maryam ta fito da sauri tana amsawa cike da girmamawa "maza tattara kayanki ki kai daki  shi kuma Lawan din kin fad'a masa an tsaida miki miji dan ya daina wahalar da kanshi ? ta sauke numfashi sannan  ta girgiza mata kai alamun" a'a ! "okay kice masa yazo gobe ina son ganinsa ta gyada mata kai kawai ta tattara kayanta ta shige dakinsu cike da zullumi ta bar Hjy zulai cikin zullumin wannan auren da take kokarin hadawa sam sam bata jin maryam domin ita din yarinya ce mai tsananin biyayya da hakuri akan komai adam take ji tasan shi tasan halinsa shine matsalarta tunda yace bai só tô har cikin ranshi bai só né sai ta tashi tsaye da rarrashi da addua ,zata bari adduarta yayi karfi da sadaka , sosai tayi zurfi cikin tunani ." Bayan kamar  wasu mintuna ya fito sanye  da wasu kayan wondo da riga farare sol kana ganin shigar  kasan fita zai yi ,lokacin daya sauko parlour'n babu kowa zuciyarsa nayi masa wani irin zafi kamar zai fito waje ,sai dai ya  kasa fita koina Kmr yadda yayi niyya ya bude bayan motarsa  ya shiga ya zauna yana sake jin bacin rai mara iyaka yana marmarin shan sigari domin shansa na rage masa bacin rai sai dai tunanin illarta yasa baya son yawo daita domin yana bukatar ya bar shanta na har abada ." mr ATA  bai shiga  gidan ba sai karfe shabiyu  na dare yana daf da  wucesu ya haye step  yaji sautin muryar mami  "adamcy  !cak ya tsaya yana ciccin magani "zakazo ne ranka dade koni na taso nazo ?"tayi mgnr cike da tsokana." jin ta fadi haka ya soma qokarin qarasowa inda take su maryam naganin hk duk suka mike suka kama gabansu  byn sun masa sannu da zuwa bai amsa masu ba ya cigaba da tsayuwa "zauna ta nuna masa wuri kusa daita "laifin me mahaifiyarka tayi maka da ka dauki  fushi mai tsanani daita ? "what ?! "Yes fushi kake daita mana tunda gashi kaki cin girkin data sha wahala ta girka maka da kanta sannan ka tsallake ka bar gidan nan  tun 9:00  sai yanzu batare da kai mata sallama da zaka fita ba wanda hakan ba dabiarka bace muddin kana kasar nan duk inda zaka sai ka sanar min  sannan ka dawo km kana kallona zaka wuce baka da niyyar ce min komai ya dan kalleta ta kasan idanunshi yana cewa "Wannan  yake nufi ina fushi dake ? yayi mgnr a shagwabe Kmr zaiyi kuka ?shine mana idan ba fushi kayi ba fad'a min abinda kayi ?shiru yayi kawai dan bai san me zai ce ba dan fushi fushin yayi dan bai

Chapter 8 of 43