Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
maryam kwashe wannan kayan ki maida su sama, jiki a sanyaye ta dauki kayan ta ajiye kamar yadda mami ta buqata sannan ta maida murfin kwaban ta rufe ta raba ta gefensa ta fice daga dakin ." Ya sauke numfashi "ammm sweetheart "kada kace min komai please dan banason jin komai daga bakinka yadda na zuba maka ido kaima ka zuba min ido kowa yayi tsabgar gabansa kayi abinda kaga ya fiyye maka arayuwarka mami ta fad'a tana nuna masa kofa .."sweetheart "dan allah adamcy ka bar min daki tunda ba kai ka gina min shi ba fita kafin nayi maka abinda bazai mana kyau ba "sweetheart ." ya fad'a a karo na biyu zuciyarsa cike da matsanan cin tashin hankali "ka fita adamcy ka fita bana son ganinka fita ta fad'a tana kawar da fuskarta ." "Da gaske dai sweetheart dinsa bata son ganinsa me yayi da zafi haka ?a ganinsa shi bai yi laifin komai ba juyawa yayi ya fita yana waiwayenta yana jin kuna acikin rashi tun daga lokacin mami ta fita harkarsa shi kuwa abun ya damesa idan ya sauko yaga bata nan baya tsayawa karya wa zai wuce office washegari ya kasance weekend yana saukowa kai tsaye dakin mami ya shiga ya sameta zaune ya gaisheta cike da ladabi ta amsa tana qoqarin mikewa saboda har lokacin tana jin zafi da radadin abinda yayi mata har tayi taku biyu taji ya riko hannunta "dan girman allah sweetheart kiyi hakuri da abinda nayi ya fad'a cikin rawar murya." wani sanyi dadi taji ya lullubeta daman abinda take bukata kenan daga garesa sai dai taki kallonsa ahankali ya dawo gabanta ya tsugunna bisa gwiwowinsa "ina mai neman afuwarki sweetheart ki yafe min nima ba yin kaina bane ki fahimceni wallahi bana jin son yarinyar nan araina ." "amman sai kayi mata mummunar fata ?ta fad'a abun na ta'ba ranta ayi ganganci da rayuwar yarinya tankar mai fa adamcy wallahi a tunanina ko dabba na ajiye a gidan nan akayi mata haka bazaka fad'a haka ba bare mutun wacce kasan tana da mahimanci arayuwata" ta qarasa maganar adaidai lokacin da aunty shahida da aunty khadija suka turo kofar dakin suka shigo shiru kawai tayi tana dubansu ." A natse suka qarasa shigowa cikin dakin sosai suka samu waje suka zauna mami ma ta zauna tana dubansu daya bayan daya "mami kin tashi Lfy?lafiya lau ya kwanan yaran ?"duk suna lafiya suka amsa mami ta dubi babbar diyarta tana cewa "a yau nake sa ran jama'a zasu fara sauka domin zuwa bikin adamcy da maryam amman sakamakon abinda yayi na janye maganar aurensa da maryam ya d'ago kanshi da sauri ya zuba ma mami idanunshi ." "Ku sheida na yafe masa duniya da lahira yaje ya kawo min wacce yake son ya aura ita kuma mrym in sha allahu zan samo mata wanda zai min biyayya ya aureta" wani sanyi dadi ya lullubesa na farinciki jin maganarta ta farko amman kuma a karshe yaji wani irin tarin damuwa na shiga zuciyarsa matsowa yayi daf daita yana cewa "sweetheart ai na baki hakuri dan allah kiyi hakuri "na hakura adamcy amman da wani abu yaje ya sameta a sanadiyyarka kazo kana murna da jin dadi gara a fasa ." Shiru yayi ya kasa cigaba da magana "mami dan darajan allah kiyi hakuri tunda yayi nadama har ya baki hakuri sannan babu abinda zai samu maryam zata cigaba da rayuwa kamar kowacce yar adam Kiyi hakuri ki yafe masa kin rigada Kinsan halin adam bai iya magana ba duk maganar data fito bakinsa haka yake cabawa inji cewar aunty khadija wani mugun kallo ya wurga ma mai hade da harara ." "Me yasa bazai zama mutun na farko da zai ji ciwon abinda akayi mata ba? maryam fa matar da zai aura ce, matar da zai raba duk wani farinciki da akasin haka ce daita ,kuma yaruwa mafi kusanci da rayuwarsa amman ya dinga nunawa duniya baya sonta , wallahi ina matukar qaunar zamansu tare amamn tunda abun ya kai ga haka nima na hakura sannan bana fushi dashi na yafe masa duniya da lahira ya kawo wacce yake so ta qarasa mgnr kuka na kwance mata .."cikin muryar kuka aunty shahida da khadija suka durkushe agaban mami suna kuka suna bata hakuri "dan allah mami Kiyi hakuri karki bari a fasa auren nan bayn an gama komai ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.              Page 27   Cikin muryar kuka mami tace  "har yau na kasa fahimtar me yasa adamcy baya son maryam ?me maryam ta rasa ? me yasa yake jin idan ta mutu zai ji dadi zai  huta?" ta qarasa mgnr tana goge hawayenta "Kiyi hakuri mami  zai sota in sha allahu nan suka dinga  rarrashin mami shi kuwa ATA ya qasa cewa komai sai ma ya mike   cikin yanayi na tashin hankalin ganin mahaifiyarsa na zubar da hawaye akanshi  ya bar  d'akin  zuwa nashi yana furzar da  numfashi  mai zafi ." ko bayan fitarsa hakuri sosai  aunty shahida da aunty khadija sukai  ta bawa mami da kyar suka samu ta sauko ta hakura "kiyi hakuri mami ki yafe masa sannan ki kwantar da hankalinki muddin muna raye adam bashi da wata mata sai maryam kuma bazamu ta'ba barin tasha wahala a gidansa ba sai inda karfinmu ya qare ."sanyayyen numfashi mami ta sauke tana mai sake gyara zamanta  tare da riko hannuwansu cikin nata "na yafe masa dan ko baku nemar masa  yafiya  ba  zan yafe masa domin iyaye ne kadai suke iya yafewa ya'yansu batare da ya'yan  sun nemi yafiya daga garesu ba  ,gaba dayanku allah yayi maku albarka allah kuma ya albarkaci rayuwar ya'yanku kuje ku cigaba da shirye shiryen  biki ina alfahari daku ta qarasa  mgnr tana murmushi ". wani farinciki ne ya mamaye zukansu suka mike  suka  fito daga dakin mami  zuwa  d'akin ATA alokacin yana kwance flat akan  kujera  yana fidda numfashi sama sama ."Jin motsin shigowarsu ya sashi bude idanunshi da kyar sai dai  bai mike  ba har sanda suka samu waje suka zauna  suka tsura masa idanuwansu suna kallonsa, kusan mintuna goma suka d'auka suna kallonsa da nazarinsa sannan   aunty shahida ta kira sunansa "adam !" yana jinta amman yaki  amsawa  sai ma sauke ajiyar zuciya yayi tare da furzar da zazzafar iska daga bakinsa " "kana jina fa  adam ?"eh ina jinki ki fad'a abinda zaki fad'a  ya fad'a a takaice tare da mikewa ya zauna  yana kallon wani bangaren dabam  yana ciza gefen lip's dinsa  yayinda idanuwanshi suka canza kala dan bai ta'ba shiga tashin hankali  irin na yau ba ganin mahaifiyarsa na zubar da hawaye ,"shi kuwa me zaiyi da maryam arayuwarsa ?ai har abada bazai ta'ba sota ba zai dai yi biyayya wa mahaifiyarsa  ." Aunty shahida ta danne abinda taji na haushin abinda yayi mata yanzu ta  soma magana cikin fushi "wallahi adam kabi duniya ahankali da girmanka da komai amamn ka dinga  sa mahaifiyarka kuka a zatonka yadda kake yiwa mami zaka ci bulus ne ?cikin yanayi na tashin hankali ya waigo ya tsura mata tsumammun idanunshi dake cike da matsanamcin tashin hankali duk da magana yake son yi amman ya kasa bude bakinsa dan haka ya runtse idanuwanshi kawai  yana janyo wani irin numfashi mai zafi yana fesarwa ya maida kanshi jikin kujera ya kwantar ." "tsawon shekaru fa take binka akan aure ,ka mance kaine kaki fito da mata har yasa ta yanke wannan hukuncin akanta  ?"iyaye ne kadai suke son  ganin cigaban ya'yansu mami na son ganin gobenka tayi kyau ne yasa  ta hadaka da mrym sannan  karka manta kai ma aure zakayi  yanzu kuma zaka haihu yaya zakaji duk ranar da kacewa d'anka  ko 'yarka ga abinda kake so suka  ce aa ba zasu maka  biyayya ba abinda suke  só shi zasuyi   ? "to ni yanzu me nayi kuma ?ya fad'a a matukar hassale tare da gyara zamansa ya  bude idanuwanshi a hankali ya zuba masu ya cigaba da motsa labbansa "yarinyar nan ce  bana só kuma bana jin zan sota ,sai kuma na kasa fad'ar albarkacin bakina ko ana so dole ne  ? yayi  tambayar  a dan fusace yana kallonsu ,ku tsaya na tmbyeku daga Ke har khadija auren dole mahaifinmu yayi maku ?"sukayi shiru suna kallonsa dan basu da amsar da zasu bashi "gbdynku kuna son mazajenku kuka  auresu  to me yasa sai ni dana kasance nmj  zaa wa auren dole kuma a hanani mgn ?". "amman ai ba dole sai ka fad'a a gaban mami ba ,wannan kalmar da kake fad'a ita Ke sa mami jin wani abu aranta , dannewa ya kamata kayi ka rungume maryam ."har yanzu baku bani amsar tmbyta ba tukun kafin ku shigo da wata ,auren dole akayi maku ?"zuba masa idanu sukayi kowannensu da abinda yake sakawa aransa ,ahankali ya lumshe tsumammun  idanunshi tare da sanya hannunsa daya a saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take beating very fast "gbdynku bazaku iya fahimtar quna da radadin da nake ji acikin zuciyata ba  ,so ne dai na fad'a bana sonta kuma wallahi ko yanzu aka fasa auren nan murna zanyi  mutun daya ce kawai ta samu kyakkyawan mazauni anan  itace mafarkina ,me zaayi da wannan guntuwar yarinya yarinyar Kmr agwagwa  kawai fari ne ya taimaketa ya qarasa mgnr yana cigaba da shafa zuciyarsa yana lumshe ido ." "Wani haushinsa ya kama aunty khadija  ranta a matukar bace tace "Idan zaka  manta mafarkinka ka manta ka sanya mrym  a zuciyarka dan wannan auren mutuwa ce kawai zata ra.."Kafin ta qarashe  maganar ya jefa mata wani mugun kallo wanda yasa tayi gaugauwar yanke maganarta babu shiri ,dan girman allah adam kayi qoqari kasanya maryam ko kad'an a zuciyarka "bazan iya ba"ya fad'a atakaice "zaka iya adam kayi qoqarin kwatantawa please."   "bama da ikon waye zamu so waye zamu fad'a soyayya dashi   bazan iya yi maku karya cewar zan sanyata a zuciyata ba   daga baya kuga akasin haka dan bazan iya karya maku zuciya daga baya kuji haushina ba ,kuyi hakuri  kawai  bazan iya ba ,sannan kusan wani abu  a kullum ina fad'a  maku amman kun kasa fahimtata kuskure zaayi a auren  nan yakamata abar maganar auren nan haka mu cigaba da rayuwarmu daita  irin ta yan'uwantaka." "zamuyi rayuwa daita ta har abada shine maanar aure,  akwai abubuwa acikin rayuwar aure,aure   ba abu bane na takaitaccen lokaci idan anyisa anyisa kenan sai fatan mutuwa ce zata raba zata bukaci farinciki ni  km bazan ta'ba bata farinciki ba saboda ni kaina zuciyata bata tare da farinciki komai zuciyata a rufe take da soyayyar wata wato mafarkina kenan ,itama ina neman adduarku allah ya yaye min tunaninta na huta yayi maganr Kmr zai zubda hawaye . yayi shiru tare da rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana jin wani irin tuttukin bakinciki." "to Allah  yaye maka tunaninta kai bama tunaninta ba ni zanyi addua allah ya mantar da kai ita gbdy  kaji ka tsaneta  fiyye da komai a duniya inji cewar aunty khadija ,numfashi kawai ya sauke yana kallonta a dage batare da yace komai ba dan shi yasan ba abune mai sauki ba ya mantata.yanzu ga shirye shiryen biki  zaa shiga daga jibi ya kenan ?" "babu ruwana da duk wani abinda zaayi na shirin biki ,ni dai abinda nasani aure ne na amince zan aureta amman batun wani shirye shirye babu ruwana" har maganar rabon iv ?"ya ina fad'a maku bani da wata damuwa da komai  da zaa gudanar kuna qara shigo min  da wani maganar rabon Iv ."yayi mgnr da fushin zuciya . "rabu dashi aunty  shahida duk abinda ya dace salim da hisham  sunyi  ,kai kuma kaje can  ka karata da mugun halinka allah ya ganar da kai mu zamuyi komai kuma aure babu fashi sai an cikawa mami burinta  sai dai idan mutuwa zakayi ka mutu nonsense kawai  "bai sake cewa komai ba har suka mike suka bar d'akin ya koma ya kwanta lamo yana kallon saman d'akin ,ranar yini yayi kwance a d'aki cikin tsananin damuwa ." da misalin karfe takwas na dare ya sauko kamr yadda aka saba an shirya masa dining da kalolin abinci dabam dabam ya zauan akan kujera shiru babu mami haka nan ya kasa ci ya kai hannu ya shafa kanshi zuwa fuskarsa duk tsananin yunwar da yake ji ya kasa sakawa cikinsa komai ya cigaba da zama shiru sai kusan karfe tara mami ta fito daga dakinta sanye ciki riga da zani na atamfa super tana kwallawa auta da maryam kira atare suka fito daga dakinsu suna amsawa mami ta dan yi taku zuwa dining area taja kujera ta  zauna tana cewa "maryam zuba mana abinci jikinta a sanyaye ta bude kular farko tana tmbayarta "mami me zan zuba miki  ?" " bani rice  ma ya isa amman kadan zaki zuba min ta zuba mata ta ajiye agabanta sannna ta zuba abinda tasan ATA yake so rice and stew da miyar kayan ciki da cowslow ,ta zuba shinkafar a plet dabam haka ma miyar daban tayi  masa  ta ajiye a gabansa sannan ta zuba nasu ita da nana hauwa'u ta dauka ta wuce." Ahankali mami take cin abinci amman ATA ko kallon abincin gabansa bai yi ba saboda haushin mami  taki kallonsa ballatana yaga faraarta taki furta komai garesa idan zasu hada ido sai ta dauke kanta sosai ya shiga damuwa hankalinsa ya tashi "to me yayi mata da zafi haka ?shi kam bazai ta'ba boye felling dinsa akan maryam ba yadda zuciyarsa bata sonta haka bakinsa bazai qasa furtawa ba sai dai tayi hakuri dashi ." Ganin yaki ci yasa mami taji babu dadi aranta ta dauki spoon ta sanya cikin abincinsa ta sake tura masa tana tsaresa da idanunta jiki a sanyaye ya sauke numfashi zuciyrasa na sake  karyewa allah sarki sweetheart yasan bazata iya dogon fushi dashi ba ,haka ya dinga cusawa cikinsa abinci tana tsiyaya masa ruwan lemu sai data ga ya koshi sannnan ta mike ta soma tafiya ya dago kanshi yana kallon bayanta zuciyarsa cike da tausayinta ya sani  cewar tana matukar son maryama ,da wani ne yayi abinda yayi mata koda kuwa acikin ya'yanta ne sai ya hadu da fushinta fiyye da yadda ta dauka dashi amman shi allah ya saka mata hakuri dashi komai zai mata tana shanyewa har ma ta kasa daukar dogon fushi dashi." tashi yayi ya haye saman d'akinsa babu laifi   zuciyarsa ta d'an samu  natsuwa." Da misalin karfe hudu na ranar baki  suka fara sauka a gidan mami murna a wajen mami ba'a  magana  ranar a kasalance maryam  tayi komai daga karshe ta shige daki ta kwanta ta huta dan ta samu zuciyarta da gangar jikinta su samu natsuwa da suka rasa tun da taga jama'ar sun fara sauka hankalinta ya tashi jikinta yayi sanyi ."washegari aka fara shirye shirye biki , zaune suke  a falon aunty shahida masu gyara  jiki nata faman shafa masu dilka ajiki  yayinda yanuwa suka zagayesu ana hira daga maryam har nuzla kana kallonsu zaka fahimci suna cikin damuwa da rashin son auren dan fuskarsu kamar zasuyi kuka gidan mami ya sake cika da yan'uwanta  har yau friday da zaayi kamu mutane suna cikin zuwa ." a wani hadadden hall akayi  kamu amare sunyi kyau sosai sai dai ango ATA  bai je koina ba yana kwance a gida ,bangaren maryam ita kadai ce zaune akan kujerar daaka tanada dominsu dan juyin duniya  aunty khadija tayi dashi  amman yaki zuwa aranshi yace "ko bikin da yake so ne zaayi bazai je wani kamu ba bare wanda zaa masa na dole ."mrym kuwa juya  kai kawai take   zuciyarta a jagule bare idan ta kalli hisham da nuzla yadda hisham Ke jefa mata kallon soyayya  da kaffa kaffa daita sai taji kamar ta daura hannuwanta duka  aka ta saka ihu  ko taji saukin zafin da zuciyarta take mata ta sake kallon  hisham taga ya  makale  nuzla sai d'aukarsu hoto ake amman ita nata ango ya wulakantata." aunty shahida tayi  mata duban tsanake nan da nan ta fahimci halin da take ciki ta qaraso inda take zaune tana cewa   "Ki kwantar da hankalinki mrym da rashin zuwan adam kema Kinsan halinsa gara rashin zuwansa daya zo ya kunyata mu ta hanyar wulakanta mu amman muddin muna raye bazakiyi bakinciki a gidansa ba."maryam  tayi narai narai da idanu zatai kuka "qul karki  daga hankalinki bare Kiyi asarar hawayenki da zarar an daura shikenna ya zama naki na har abada  a hankali ta dinga rarrashinta har ta dan samu natsuwar zuciya sai dai taji haushi da bakinciki rashin zuwansa domin  dai so yake lallai sai duniya tasan irin auren da zasuyi ." bayan an gama kamu amarya maryam ita kadai a bayan mota direba yajata suka dauki hanyar zuwa gida  yayinda hisham da nuzla suke zaune abayan tasu motar direbansu na qoqarin kunna mota hisham ya kafeta da ido sosai Kmr zai cinyeta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta  cikin nashi yana  kallo yace "Woow my nuzla gsky lallen yayi kyau my wife waya miki shi ? hade rai tayi sosai  tamkar bata ta'ba yin dariya ba a tsawon rayuwarta tana zame hannunta cikin nashi tace "ka tsaya iya matsayinka karka sake ta'ba min jiki dan wannan jikin ba naka bane "na waye "? ya tambayeta yana matsota sosai Kmr zai shige jikinta "tambayarki nake "jikin waye ?"stil dai shiru tayi  masa " jibi iwar haka kina cikin gidana watakilla ma muna kwance acikin bargo daya makale da juna "wani kuka ta fashe da shi tana qara matsawa ". " to to!!  shikenan na bari  Kiyi hakuri amman dai Kinsan dole zamu kasance tare? tsaki taja ta kawar da fuskarta gefe a haka suka qaraso   gida ."mota bata tsaya a koina sai a kofar gidansu bayan motar ta tsaya   ta fito hisham ya biyota suka jira yana yi mata magana amman taki kulashi tana  qoqarin shiga  gida ya riko hannunta daya cikin nashi ta juyo a matukar fusace tana kallonsa shima kallonta yake with a broad smile a fuskarsa sai itace ta  dauke kanta tana lissafi yadda zata gudu ta bar shi da wahalarsa  ". "anya kuwa zata iya gudu ta bar iyayenta  bayan a yanzu bata iya zuwa koina ta kwana batare dasu ba ?ta tambayi kanta nan take zuciyarta ta bata amsa da" wannan shine mafuta a gareki  idan komai ya natsa sai ki dawo wanda zuwa lokacin dole kowa ya hakura ." ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo yana murmushi wanda bata san ko na meye ba ."cike da jin haushi ta  fix hannuta tana mai bakinciki dan  komai ya faru da rayuwarta shine sila shekara da shekaru bata ta'ba tunanin barin iyayenta ba sai a dalilinsa ita kam tsakaninta dashi sai dai allah ya isa  da wannan bakinciki ta shige gida  ta barshi tsaye  yana kallon bayanta ". Sai bayan data shiga  gida sannan ya juya ya wuce  kai tsaye wajen ATA ya wuce koda ya shiga parlour'nsa yana tsaye akan dadduma yana sallar magrib bai zauna ba shima bathroom ya shiga ya dauro alwala ya fito ya bisa sallah ,bayan sun idar ya fara tsokanar ATA "ango ango !!amman gsky kai dai anyi dan iskan ango ,wallahi baka kyautawa maryam ba, ka barta ita kadai allah sarki wallahi na tausaya mata, wallahi abokina kabi a hankali ina guje maka ranar da zaka rufta "wani dogon tsaki yaja yana  watsa masa harara tare da cewa "ka maida hankalinka jikinka da wannan shirmen da kake yi  karka sake min maganar auren nan" hisham  yayi murmushi  yana cewa "ai hankalina yana jikina nan dai yayita jan ATA." Nuzla tsaye a dakinta hawaye na zubo daga kwarnin idanunta alokacin da take daukar abubuwan amfanita masu mahimanci tana tuna rayuwar kuncin da iyayenta zasuyi idan suka laluba basu ganta ba ,bayan kamar awa daya nuzla  ta fito zuwa babban parlour'nsu koina  ta kalla mutane a parlour'n yan'uwan mahaifiyarta gbdy  zaune kai tsaye ta shiga dakin hjy salema bata dade ba ta fito ta rasa yadda zaayi ta sake fita dan haka  ta koma ciki d'akinta  tana tunani hanyar da zata bi ta  kubta  daga wannan wahallen auren ." byn Kmr mintuna goma ta sake fitowa har ta kai bakin kofa aunty maijidda tace "ina zaki kuma adaidai wannan lokacin ? Ta fad'a tana kallon agogon dake manne a falon ,nuzla ta dan diririce sannan tace "yaya hisham ne ya kirani yana waje" tana gama jin abinda ta fad'a  ta juya tayi d'akin da baki suke  ita kuma nuzla  ta samu damar fice wa daga gidan gabadaya ." yan'uwan hjy salema suna ta kikiniyar da hadahadar abincin  gobe diner sam babu wanda ya fahimci nuzla bata gidan  har karfe goma sha biyu na dare ."Hjy salema dake zaune a bakin gadonta haka   nan jikin ta   ya dinga mata wani iri ,ta fito ta shiga dakin nuzla bata ganta ba dan haka ta juya ta fito daga dakin  tana  tmbayr   aunty rabi wacce ta kasance diya kanwarta  ce "umma  bansa inda take ba amman bari na dubata a dakinta "ai  daga dakin nata nike bangata ba shiyasa ma na tambayeki ." to bari naje na tmbyi aunty maijidda ko tasan inda taje da sauri ta wuce hjy salema." A bakin kofar fita daga parlour'n suka hadu  da aunty maijidda "Yauwa aunty maijidda ina nuzla ko ta fad'a miki inda zata "eh d'azu tace min zata wajen hisham amman bari na kirata nan  ta soma qoqarin kiran layin nuzla sai dai numberta na shiga bata dauka  dan haka ta kira layin hisham tana tmyrsa nuzla amsar daya bata yasa ta  shigo d'akin hjy salema da mugun sauri  ta isketa tsaye cikin faduwar gaba ." Aunty maijidda batayi magana ba  ta cigaba da kallon hjy salema "maijidda ko nuzla ta fad'a miki inda zata ?ta bude bakinta kenan zata bata amsa idanunta suka ci karo  da envelop asaman dress mirrow din hjy salema  an rubuta wannan sakon na umma da abba ne kallon da takewa envelop din yasa hankalin hjy salema ya kai kanshi " gabadayansu gabansu ne ya shiga dokawa dan basusan me Ke kunshe a cikinsa ba  tun baa kai ga budewa ba hjy salema ta soma furta kalmar "innalilahi inna ilahi rajiun  azuci  da fili dan ta gama shiga rudani "hannun aunty maijidda na rawa ta dauka  ta bude  envelop ta soma karantawa  a fili hannunta da jikinta na wani irin wara ." _Assalamu alaikum iyayena nasan aloakcin da zaku nemi ni ku rasa zaku ji babu dadi acikin ranku amman ina mai baku hakuri da neman afuwarku akan halin damuwar da zaku shiga a dalilina na tafe ne adalilin bana son aurena da yaya hisham  na fito  maku da manufata  amman kun kasa fahimtata dan haka na yanke shawarar barinku ba dan raina yaso ba ina sonki ummanah ina sonki fiyyr da komai haka kai ma abbanah ina sonka zanyi kewarku sosai_ rabi ta nike takadar ta mayar cikin envelop din tana kallo  hjy salema data zube kasa  jinta ne ya dauke dip  sakamakon abinda wasikar Ke dauke dashi  duk wani kuzari da karfin jiki babu atattare da ita baya ga tashin hankali "ji  take kmr ba ita bace anya nuzlarta ce  kuwa ta ajiye mata wannna sakon  ? Aunty rabbi duk ta rude sai zufa take fitarwa  nan da nan aka kira baba babba da yayyen nuzla maza har ma da hisham da ATA aunty rabi tace baba "kaji wani sabon  tashin hankali  nuzla ta gudu ta mika wa yaya Ibrahim wasikar  ya duba ,hannu  hjy salema  ya kama dan ta kasa motsin kirki binshi takeyi kmr rakumi da akala har  uwar dakanta ya kamota yana qoqarin zauna daita taki zama tana fashewa da wani gigitaccen kuka tana furta sunan "nuzla! "ku nemo yarinyata dan allah ku nemo yarinyata abinda kawai take

Chapter 38 of 43