Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaisheta a mutunce ta amsa tana tambayarsu lafiyar iyayensu , anan suka qarasa yini  suna Hira daga wannan hirar zuwa wata hira sai dare suka kama gabansu ." ****** Bayan wata daya  aka wayi gari akaga gawar mubina agdan qanwar mahafiyarta zainba an kasheta ta hanyar tsoka mata wuka a daidai saitin zuciyarta Kuma aka bar wukar ajikinta ba'a cire ba hankalin family's din abdullahi ya tashi matuka mahaifiyarta kuwa kuka da sambatu take tana cewa daga ziyara shikenan an kashe min 'ya daga ziyara fa ,daga ziyara fa!!  haka ta dinga furtawa har abun yaso zame mata kmr ta zautu saboda ita kadai gareta mace sauran ya'yanta duk maza ne ,sauran yanuwanta sunyi kuka kamar zasu bita lahira maryam kamkame da hannun mubina tana wani irin kuka me ban tausayi saboda akwai sabo me tsanani a tsakaninsu "waye yayi mana haka ?waye ya kashe mana yar'uwa ?an kasheta batare da burinta ya cika na auren ya AD ba sai lokacin mutanen gidan suka San da batun soyayyar da mubina ke yiwa AD batare da bata lokaci ba jamian tsoro suka shiga lamarin suka shiga d'aukar gawarta hoto yayinda daya daga cikin police Ke rike da farar takarda yana rubuce rubuce akan gawar byn sun gama sannan aka cire wukar aka soma kokarin shiryata zuwa makwancinta Inda har lokacin jini bai daina tsiyayya ba." Mr ATA na gidansa dake banana estate yana kallon zanensa  dan wani lokacin idan yana son hutawa can yake zuwa yayi kwana biyu idan ya gaji ya dawo gida wurin mahaifiyarsa dan bazai iya yin nisa daita ba , Kiran sweetheart dinsa ya samesa inda cikin kuka take sheida masa halin daake ciki a zaune yake amman bai san sanda ya mike tsaye rike da zanensa gam yana furta kalmar innalillahi "yaushe kenan ? ya furta cikin tashin hankali " okay ganin nan zuwa nan da wasu yan mintuna  bai tsaya katse Kiran ba ya mike ya leko zuwa falonsa na uku Inda ya bawa masu tsaronsa umarnin fita  yana gama fadar haka ya koma ya shirya dan daman yyi wanka cikin kankanin lokaci ya fito ya karasa Inda motarsa  yake aka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna zuciayrsa na tsinkewa hankalinsa na sake tashe sai dai ba'a iya hango bacin ransa a fili sai dai daga ciki yake iya  bayyanashi ai kuwa da yana nunawa da duk ahlinsa sai sun fahimci yadda yaji mutuwar mubina .Kyawawan idanunshi wadan da suka wadatu da gashin idanu ya zubawa gawarta dake kwance a parlour dan har an fito daita domin tafiya daita makwancinta .duk da kasancewarsa mutumin da baya sakewa da 'yanuwansa amman yaji zafin mutuwar mubina sannan ya tausayawa iyayenta kasa furta komai yayi  duk da maganar yake son yi amman maganar taki fitowa hankalinsa sai sake tashi yake yana mamakin yadda aka kashe mubina yana wannan tunanin  aka fito da gawar mubina da jini duk ya bata likkafani aka nufi gidanta na gaskiya ." Bayan an dawo daga kaita duk yan'uwa suka yi tsuru tsuru kowa ka gani yana cikin tsananin tashin hankali me tsananin ,Sosai mr ATA yaji mutuwar yar'uwarsa duk da ba wani sabo ne a tsakaninsu ba, batun tana son shi kuwa sai lokacin yaji abun ya mugun tsaya masa rai duk da yasan babu digon sonta a zuciyarsa kawai dai tausayi ne da jimami , yan'uwa sun jajantawa juna "yarinyar da bata da hayaniya yaushe take fad'a bare a samu abokin gabarta da har zai yi sanadin mutuwarta ,bata shiga harkar mutane kullum cikin faraa take inji cewar hjy zulaiheart kowa mamakin da yake yi kenan a tsakaninsu .muryar mr ATA a sanyaye ya dube police officer din dake tsaye kusa da mahaifiyarta yana mata tambayoyi "kuyi iya bincike da zakuyi Ina son a gano wanda yayiwa mubina kissan gilla dan sam bazan barshi ba koda kuwa danuwana ne ," ya karasa maganar cikin tsananin fushi "karka damu ranka shi dade tabbas zamuji da komai bai ce komai ba ya k'arasa kusa da mahaifin mubina dake rike da wukar da'a aka kashe masa tilon diyarsa ya dafa kafad'arsa sannan ya karbi wukar daga hannunsa yana kallon wukar mai dauke da kan sarauniyya ya dinga kallon wukar da akayi kisan sabuwa ce fil da alamun ma akan mubina aka fara amfani dashi ya furzar da numfashi kana ya soma mgn "karka damu uncle jay dake haka yake kiransa inshallahu za'a gano ko waye yake da saka hannu gurin kashe mubina ka kwantar da hankalinka muddin Ina raye sai nasa an gano wannan mashekin ."ya karasa maganar jijiyo kansa na mikewa, hawaye ya zubo a idanun mahaifin mubina ya daura hannunsa daya akan hannun Mr ATA  dake kafadarsa "na gode ADTA dake shima hk yake kiransa  Allah ya jikan mahai ...."kasa karasawa yayi saboda kukan daya ci karfinsa dan sai lokacin ya samu damar zubar da hawaye mr ATA  ya rungumeshi ajikinsa tsam yana rarashinsa ." bincike sosai akayi akan mutuwar mubina sai dai har wannan lokacin da ta cika wata biyar da mutuwa ba'a samu nasarar gano hannun wanda yayi kisan ba a karshe mahaifinta yace abar case din ya barwa Allah komai amman mr ATA yace sam a cigaba da bincike da kyar uncle jay ya shawo Kansa ya hakura , maryam ta dade tana Jin mutuwar mubina a zuciyarta dan ko runtsawa bata yi duk sanda ta tuna maganarsu na karshe kafin akasheta sai ta rushe da kuka Mai tsanani "ki tayani da addua marsi ina Kara Jin qaunar ya ad a cikin zuciyarta gashi bani da yadda zanyi ya fahimceni tsoronsa ya hanani fuskantarshi da maganar amman zanyi qoqarin fad'a masa acikin satin nan Allah yasa idan na furta masa ya amince ya aurenni ,ni ko baya sona zan zauna dashi haka bare ma wuyarta mu kasance miji da mata tuni zan mantar dashi wani kiyyaya Allah sarki rayuwa kenan mubina Allah yayi Miki rahma .." ******* Bayan shekara daya Yana zaune akan gadon hjy Zulaihat sanye cikin kananan kaya wondo da riga ash colour idanunshi sanye da farin glass yana fama tura sakonni ta shigo dakin ta nufi inda beside dinta yake "sweetheart! ya kira sunan da yake kiranta dashi sabani Kowa dake kiranta da mami "Yaakayi my love ta amsa tare da kallonsa   "ko zan samu black tea ?yayi mgnr yana cigaba da aiki "me zai hana shalelena bari nasa maryam ta kawo maka nayi baki ne . "No abarshi kawai sweetheart idan itace zata kawo min yaran da babu abinda suka iya sai shirmen banza da wofi .tayi shiru shima yayi shiru ,shi dai bai san dalili ba amman baya son maryam a kusa dashi Kullum qara jin tsanarta yake wanda da zaa tsaresa da bindiga bazai ce ga dalili ba, shi dai hk kawai yake jin baya sonta a duk cikin family's dinsa na bangaren uwa da uba ." ta juya ta bude beside tana duba abinda ya shigo daita "yauwa ko zaki  bawa auta ta kawo min idan tana nan  "still bai dago ya kalli inda take ba ?dagowa tayi a natse tana sauke numfashi sannan ta d'an matso kusa dashi ta daura hannunta akan sumar kanshi tana lumshe ido  kana tace" ai duk abu daya ne da auta da maryam dukkaninsu shirmen banza da wofi suka iya zai fi kyau ka kawo wacce bazata dinga maka shirmen banza da wofi ba ta dinga maka abinda kake so " . "ta fad'a tana dauke hannunta akan sumar kanshi ."ya dan dago a hankali ya kalleta suka hada ido yaga yadda fuskarta ya canza sosai alamun bata ji dadin abinda ya fada ba, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yace  "am very very sorry ma "shikenan yanzu auta zata kawo maka ta dauki abinda ya shigo daita ta fice daga dakin ". Byn  minti  goma auta ta shigo a hankali tmkr kazar da Kwai ya fashewa aciki bakinta dauke da sallama hannunsa kawai ya mika mata tana mika masa cup din tea  ta fice da sauri ta bar dakin, yana cikin aiki ya samu kira daga danuwansa hisham  ya dauki wayar "hello hisham ! "Okay just give me ten minutes I will meet you there ya fad'a yana kokarin kashe system dinsa  byn ya kashe ya dauki system dinsa ya rungume a qirjinsa ya nufi kofar fita  ." yana qoqarin fita  maryam  na qoqarin shigowa dakin hannunta rike da akwatin sarkokin hjy Zulai da wayarta on exepecting taji tayi  karo da gangar jikin mutun nan take  system dinsa yayi tsalle daga qirjinsa yayi kasa ...,"da wani irin mugun sauri tayi watse da kayan hannunta har ma  da wayarta tayi kasa  ta tarô system din da hannuwanta duka tun bai kai kasa ba ta shiga uku ,shi kuwa ATA tsaye yayi batare da wata alamun damuwa a tattare dashi ba yana dubanta sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci ransa ya baci da abinda tayi ,shi bama system din yafi damunsa ba kamar haduwar da jikinsu yayi ." jikinta na rawa ta miko masa system tana cewa "am ... am very sorry kayi hakuri dan allah ban ....."ai batasan sanda tayi shiru ba sakamakon wani kwallo da yayi daita  da system din nasa gbdy kamar ball sai gata a waje bisa gwiwowinta  ta dunkule guri daya , bata bi ta kanta ba ta maida hankalinta ga system dinsa ,nan ta hango system ya wargaje a kasa kallo daya tayiwa  system din ya fahimci ya tashi aiki nan fa hankalinta ya sake tashi "stupid girl kawai ." ya furta da karfi yana qarasa fitowa daga cikin dakin sosai ya daga kafarsa daya zai daki gefen cikinta yaji sautin muryar hjy Zulai "karka soma adam ". Numfashi ya sauke yana waigowa zuwa inda take tsaye ranta a matukar bace tace  "me yayi zafi adam zaka kashe yar mutane ne ?laifin me tayi maka ?tayi masa tmbyr ajere ransa a matukar bace yace "ask this nonsense girl ." ya fad'a yana nuna maryam da dan yatsansa hjy zulai ta qaraso tana kokarin daga maryam "me kikayi masa yake kokarin kasheki "? ranta a matukar bace ta soma magana, ahankali ta zayyanewa hjy zulai komai tana sheshekan kuka tmkr ranta zai fita .."naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana dubansa " shine zaka mata irin wannan hukunci ko da gangan tayi bai dace ba bare babu daya "ya kada kai zai wuce "adam ! ta tsaidashi ta hanyar kira sunansa Ya juyo a matukar fusace yana dubanta " daga yau kar na kara ganin ka ta'ba lafiyar jikinta bama ita ba kowani yaro a gidan nan  ban amince ba ban lamunta ba kaji na fada maka........" iska ya shaka ta cikin bakinsa daman kuma duk sanda ransa ya baci baya fesar da iska a fili sai dai acikinsa juyawa yayi ya kama gabansa ."hjy Zulai ta kamo maryam suka shiga cikin dakinta tana bata hakuri "ki dinga kula kinji  maryam wannan yayan naki hakurinsa mai yawa ne ta zaunar da maryam   akan gado  itama ta zauna tare da daura kan maryam akan ciyarta ta daura hannunta akan sumar kanta tana shafawa"  ki tayani da yi masa addua allah ya yaye masa wannan nukufurcin da zafin rai da yake fama dashi ".Allah kiyaye  na rasa wanda zan wa addua sai mutumin daya tsaneni kamar ya kasheni ta fad'a acikin  ranta  mami tace  ,"zaki tayani yi masa addua maryam ?."cikin muryar  kuka ta gyada mata kai kawai ba dan zatai ba "Yauwa na gode Kwarai diyata allah yayi miki albarka ." Da daddare  ATA   na zaune akan makeken gadonsa yana operating  din wayarsa  hjy zulai  ta shigo bakinta dauke da sallama lumshe lumtsatsun  idanunsa yayi saboda ganinta duk halin damuwar da yake ciki da zarar ya ga mahaifiyarsa yake jin sanyi aranshi "fatan kina  Lfy sweetheart "?ya tambayeta yana riko yatsun hannunta daya cikin nashi "alhamdulillah ta fada fuskata babu yabo babu fallasa   ."ga coffe ta mika masa sannan ta zauna kusa dashi ya saki yatsun hannunta ya karbi cup din coffee ya kai bakinsa "me zakayi breakfast dashi da safe ? yayi shiru yana tunani can yace "komai sweetheart dina zata ci nima zanci ." Adam!!!  ta kira sunansa har sau uku ya sake rike hannunta gam cikin nashi yana kurban coffe yana lumshe ido har dimple dinsa na lotsawa ," ina son nayi wata magana mai mahimanci da kai,nan  take ya bar abinda yake ya tattara dukkanin natsuwarsa zuwa gareta "abinda kayi dazu sam banji dadi ba dan allah na roki arziki ba dan ni ba karka sake maimaitawa ."tai shiru tana jiran taji me zai ce "ya lumshe mata idanunshi "naji amman itama ki mata mgn ta daina shiga hanyata "wannan kuskure aka samu domin kuwa maryam na qoqarin gani bata shiga harkarka ba ". "kai  ba ita ba  kowa acikin family's din nan yana takatsntsan ba yara ba ,ba manya ba  sai kace wani azara ilu "yayi murmushin ciki wanda ita kadai take iya fahimtar haka ,"wallahi ka canza kai gaka nan kullum cikin bakin rai da miskilanci yanzu kai ko shaawa rayuwar gidan nan  bakayi kowa na son kowa kalli su hisham dasu tariq sweetie nah kenan ya dauko mai sunanshi tsab ,kai hatta muhd bello da ba dan gidan nan ba yana jan yaran gidan nan ajiki amman kai kowa tsoronka yake ji Kmr wani dodo wallahi ka dinga son mutane dan mutane rahma ne." "to ni nace bana son wani ne acikinsu ?ya fad'a a shagwabe yana daura kanshi saman cinyarta " girgiza kai kawai tayi  tana daura hannunta a sumar kanshi tana shafawa tana kallon kyakkyawar fuskarsa  mai cike da haiba ga kwantaccen gashin fuskarsa  dake  mugu mugun qara masa kyau  sosai ya kwanta luf luf  saboda gyaran da yake sha . "ni sweetheart kin kasa ganewa ne nifa raini ne banason su kuma yan renin sense ne kinga gara na dinga kama kaina "yyi mgnr Kmr bashi yayi mgnr ba ,girgiza kai ta sake yi kana ta cigaba  da mgn "sai abu na gaba "ya batun aure ko har yanzu baka samu true love din ba ? ."Yes of course ban samu ba sweetheart  ,"yanzu kai baka tausayawa wannan mamartaka da shekarunta  yaja ?  " "Adam at any time zan iya amsa kiran allah ko sai bayan mutuwata zakayi aure ? tayi mgnr tamkar zatai kuka nan fa hankalinsa yayi mugun tashi ya mike zaune tare da riko  hannuwanta gabadaya cikin nashi yana kallonta cike da matsanancin soyayyarta gbdy yanayinsa ya sauya kamar zai yi kuka dan baya qaunar abinda zai nisan tashi da mahaifiyarsa bare rabuwa ta har abada ,muryarsa a kasalance ya soma mgn "haba sweetheart me yasa zaki fadi haka ?" Me yasa bazan fadi haka ba ?ai  gaskiya na fad'a kaki kayi aure  kai dai  kullum aiki  kawai kasa gaba baka ma  duba lamarina  bare ka  tausaya min Adam , bana son na koma ga allah banga aurenka da ya'yan ka ba ta qarasa mgnr cikin raunanniyar murya wannan karon kam hawaye ne taf acikin kwayar idanunta "karki min hk sweetheart Kinsan illar zubar da hawayenki akaina, kuma Kinsan babu abinda na tsana kamar na ganki cikin damuwa "idan har da gaske  baka son ganina cikin damuwa to ka dan duba ko a cikin yammatan  estate din nan ai bazaka rasa masu sonka da aure  ba sai ka zabi biyu ko daya acikinsu  ". Ya ware mata lumtsatsun idanuwanshi sosai yana mamakin jin abinda tace  "har mata biyu sweetheart ina zan kai su ? "bansani ba ta fad'a tana zabga masa harara sannan ta cigaba da mgn "wallahi shine burina ka auri mata biyu kuma duk arana daya saboda kasancewarka  namiji kwaya daya tilo da allah ya mallamin "girgiza kai kawai yayi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa  batare da yayi yunkurin sake cewa wani abu ba ya sake jin sautin muryarta "zakayi abinda nace ko nasa araina sai bayan na mutu zakayi aure ?" ya shafa goshinsa yana cewa "okay  zanyi kokarin yin haka sweetheart." Ya fadi hk ne dan ya kawo karshen mgnrsu ."ko kai fa yaron albarka allah ya zaba maka mata na gari , runtse idanuwanshi yayi sosai tare da yin shiru yaki cewa komai dan har kanshi ya fara ciwo ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na  kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page2 ....Da misalin karfe goma na safiyar ranar asabar mr ATA ya sauko daga saman dakinsa jikinsa sanye da bakin riga da wondo baki yayinda kafafunsa ke sanye cikin wasu hadaddun silifas masu matukar kyau suma black kana gani kasan masu tsada ne haka idanunshi suna makale da farin glass wanda ya zame masa tamkar na gado, ko bacci wani lokacin dashi yake sai idan Mahaifiyarsa ta shigo ta gansa dashi ta cire masa ,yayi kyau sosai acikin shigar kasancewarsa fari ."ya qaraso ya dauki jarida daily trust da'aka ajiye masa ya samu wuri ya zauna akan doguwar kujera mai zaman mutun uku ya daura kafarsa daya a kan daya ya shiga duba jarida " yana zaune nana da maryam suka fito suna magana akan inda mai decoration zatai decorate din birthday din maryam dana hanan diyar Aunty zabiba kanwar mr ATA da zaa gabatar a ranar ." suna gama qarasowa parlour'n suka gansa zaune Kmr an dasashi a gurin ."suka bishi da kallo suna jin faduwar gaba babu yadda zaka ga mr ATA gabanka bai fadi ba ko kai waye kuwa saboda tsananin tsare gida , ya gansu amman yayi tamkar bai san da wasu halitta tsaye a wurin ba ,nan take kowacce ta shiga taitayinta jiki a sanyaye suka hada baki wurin gaishesa "good morning ya adam" ? sai daya dauki second goma batare daya amsa ba har sun cire rai da zai amsa suka jiyo sautin muryarsa daga can kasan makoshi "morning ! ya amsa batare daya dago ya dubesu ba ." Naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tasan darajar sister taci yasa har ya amsa gaisuwar dan da ita kadai ta gaisheshi bazai ta'ba amsawa ba Kai tsaye hanyar kitchen suka nufa domin bawa masu aiki umarnin abinda zasuyi na birthday duk da sauran abubuwa masu wuya tun jiya a kammala ,duk abinda suke hankalin maryam na kan mr ATA bini bini ta kallesa taja tsaki acikin ranta dan hakan nan kwanaki take jin matsanancin tsanarsa a ranta dan tasha alwashin tunda bai qaunarta itama bazata qaunacesa ba mai qaunarsa ma baso ." Sai dai duk da wannan tsanar da tayi masa ta kasa dauke kwayar danunta akanshi har sanda ya mike ya isa dining table ya dauki cup din coffee dinsa baki mai shegen kyau da gani daga wata kasar yazo dashi , a natse ya sake dawowa mazauninsa ya zauna fuskar nan tashi a hade tamkar wanda ake masa wahayi da bacin rai." "tunda aka haifeta ta bude idanunta akansa bata ta'ba ganin dariyarsa ba ,kuma haka kowa yake fad'a acikin family's ,komai zaayi na dariya sai dai ya bata rai yaja tsaki tare da cewa nonsense ko rubbish ga shegen miskilanci wani lokaci halinsa na dan burgeta Irin mijin da take so kenan mai matukar kamewa da sanin ciwon kai, dan gsky ita dai nmj mai yawon surutu ko shiga abinda bai shafesa ba yawon fara'a matsala ne agurinta bata so sai dai nashi yayi yawa ko dan murmushin nan ba yayi matukar kaga fuskarsa a d'an sake to yana tare da mami ne shima wani lokacin bata gane kansa kome zatayi bazai sakar mata fuska ba ." byn ya sha kad'an ya ajiye cup ya cigaba da abinda yake har sanda hjy Zulaihat ta fito itama ta shiga kitchen yana nan zaune ya tsurawa jarida idanunshi , al'ameen daya daga cikin securities na bakin get ya shigo bakinsa dauke da sallama sannan cike da girmamawa hannunsa rike da white lailon da box blue and white ,mr ATA ya amsa sallamar aciki yana mai d'ago kansa ahankali ya zubawa al'ameen lumtsatsun idanunshi "Alameen ya qaraso gabansa kad'an ya rusuna "barka da safiya yalla'bai "mr ATA ya gyada masa kai kawai batare daya amsa ba . " amm ga sako wai inji Ana's" mr ATA ya d'an kankace lumtsatsun idanushi yana bukatar qarin bayani daga bakin al'ameen,alameen yayi sauri yace "sakon hjy maryam ne ita yace abawa "shiru mr ATA yayi yana kallonsa da sakon hannunsa kamar bazai ce komai ba sai kuma ya nuna masa kan table din dake gabansa yana jan tsaki a fili al'ameen ya ajiye ya juya ya fice da sauri ya kama gabansa." Maryam dake kitchen wacce daman idanunta da hankalinta yana parlour ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, da sauri ta qarasa inda nana take tsaye "sister na shiga uku nah" ta fada tana riko hannun nana cikin nata "me kuma ya faru allah ya rabamu da shiga uku sister ?"kalli can ki gani sister ta nuna mata parlour'n "me ya faru ? "sakon Ana's ne daman ya turo min text message zai zo ya kawo min gift gsky al'ameen bai kyauta min ba maimakon ya kirani ya bani a hannuna tana magana idanunta na cikowa da ruwan hawaye hjy zulaiheart ta juyo a natse ta dubesu "ku kuma lafiya kuka tsaya kuka hade kai wa ya mutu ? a matukar firgice suka juyo suna dubanta maryam na 'kokarin dauke hawayenta a d'an rikice suka girgiza mata kai alamun "babu kowa " to meke faruwa daku ?babu komai suka sake hada baki "to allah yasa babu komai din amman ni dai na fahimce da komai tsayawa sukai suka qasa cigaba da aiki ." shi kuwa Mr ATA naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yana shan yaji kamar yadda ya saba sosai ya tsurawa box din dake dauke da sunan maryam da kallamar happy birthday yana lissafa abubuwa dayawa acikin ransa "wai gashi inji Ana's sakon hjy maryam "ya maimaita abinda al'ameen ya fad'a , kafin daga baya ya kwabe baki tare da kai hannu ya bude box din ,da wani hadadden freme idanunshi ya soma cin karo mai matukar kyau da d'aukar hankali an rubuta sunanta da larabci da kuma hausa ." "shiru yayi yana jin wani iri a gabadaya ilahirin jikinsa na tsantsar bakinciki ,a hankali ya dinga kallon abubuwan dake cikin box din mug, pray mate ,Casbaha alqurani da wani qaramin greating card na sokon taya murnar birthday sai kuma qaramin yellow takarda mai dauke da kalaman soyayya "ya dauka yana tabe baki kamar yaga wani mugun abu ya soma karantawa ." hjy Zulaihat ta fito daga kitchen tare da masu aiki mutun biyu zuwa dining maryam da auta suka biyo bayanta jikinsu duk a sanyaye dan basu san abinda zai faru ba "na shiga ukuna sister ki taimakeni karanta sakon fa yake " maryam ta sake fadan hk cikin tsananin tsoro "to sai me idan ya karanta ? " wallahi kin cika abun ban haushi kamarki dan an aiko miki da sako zai zama abun tashin hankali? Ke yarinya ce karki manta master's gareki kuma dole zakiyi aure "ni sister rabani da wani master's na yarda kowa ya karanta sakon amman ban dashi "bangane banda shi ba ? shi waye naki da zakice ban dashi ? tayi mata tmbyr tana kallonta "haba

Chapter 2 of 43