daga cikin gidansu "Ina muka nufa ma kika ce ? ita Kuma wannan ina zaki daita nifa bana son kwashe kwashe a motata? asibiti ta bashi amsa duk da tasan yaji abinda tace , bai sake cewa komai ba har suka iso asibiti ,yaki fitowa Yana jiran aunty shahida ta karasa fitowa dan maryam tuni ta fito "adam muje akwai sakon da zan baka yayi shiru yana maimata maganarta yaji Kmr yace ta bawa mrym ta kawo masa Amman Kuma baya son abinda zai hadashi da yarinyar "a hankali ya fito ransa a bace Kai tsaye office dinta suka nufa aunty shahida ta bude office dinta dukkaninsu suka shiga Yayinda mr ATA ya tsaya daga bakin kofa yana jiran ta bashi sakon da tace aunty shahida tace "bismilla mana ranka shi dade mr ATA shigo ka zauna ga guri nan yayi mata wani irin kallo yana bukatar qarin bayani akan abinda ta keyi "ta gyada masa kai "shigo mana ." da kyar mr ATA ya shigo office din ya zauna yana hura hanci sannan itama maryam ta samu guri ta zauna tana satar kallon fuskarsa kwata kwata babu digon annuri ,"
" Maryam tashi ki bude fridge ki dauko masa ruwa dan nasan bai fiyye shan lemo ba ,ta mike a hankali ta karasa ta dauko masa ta ajiye a gabansa ta koma ta zauna gabanta na faduwa "ka bani minti goma kawai zan duba wani fayal ne yanzu zan gama sannan ta soma aiki tsaki yaja a ransa dan dai tana da matsayin aunty shi ce if not bai ga dalilin da zai yita batawa kanshi lokaci ba akaron banza ba ."baka sha ruwan ba ?ta dago ta tambayesa cike da kulawa "no need !ya bata amsa ataikaice
byn kmr minti biyu ta mike ta fita tace "kanina ina zuwa "zuciya ta sake kawo masa wuya sakamakon barinsa da zatai yi shi da wannan guntuwar yarinyar mai siffar aljanu yaja tsaki yana dafe goshinsa da hannunsa ."
Zamansu daga ita sai shi acikin office din baqaramin tashin hankali maryam ta shiga ba ,gbdy duk ta rude sai zufa take fitarwa da zarar tayi kamar zata dago ta kalleshi sai ta kasa dan gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga allah allah take Aunty shahida ta shigo domin bazata iya cigaba da irin wannan zaman ba ,minti biyar kawai Aunty shahida tayi da fita amman ganin take Kmr awa biyar tayi da barin office din ,shi kuwa mr ATA banda tsaki babu abinda yake yana qarawa domin ya fara gajiya da zamansa tare da abinda yafi tsana arayuwarsa ."
Aunty shahida na fita ko cikakken minti goma batai yi ba sai ga nuzla ta shigo office din bakinta dauke da sunan Aunty shahida,turus tayi sakamakon ganin maryam zaune gefe guda kuma mr ATA ne zaune kallon tsoro tayi masa ta dauke kanta tana gaishesa bai amsa mata ba kamar sauran lukuta ta qarasa ta dafa maryam "marsi ina Aunty shahida ."?
"ta dan fita amman tace bazata jima ba ki jirata ,
"okay da ido tayi mata tmby me ya Adam yake yi ? itama da kwayar idanunta ta bata amsa da bata sani ba dan babu damar ayi magana mai sauti kasamcewar sun san baya son hayaniyar komai saurin ciro wayarta tayi ta maida silet ."
sadiya wacce ta kasance me koyon aiki ce a asibiti ta shigo bakinta dauke da sallama "Assalamu alai...... kasa karasa sallamar tayi sakamakon gani mr ATA zaune idanunshi na kallon screen din wayarsa sanye cikin kanan kaya ,gbdy ta rikice akansa madadin ta karasa ta ajiye file din dake hannunta ta kasa ko daga dan yatsan kafarta garin kallonsa ma har file din hannunta ya subuce daga hannunta ya fadi kasa da sauri ta tsugunna ta dauka jikinta na rawa ta karasa ta ajiye fayal din akan table ,tana faman kallonsa sai lokacin ta lura da maryam dake zaune tana kallon yatsun hannunta yayinda nuzla ke tsaye a gefenta "sannuku da hutawa ta furta a hankali ."
maryam ta dago tana murnushi tace "yauwa ya kokari ? alhamdulillah sadear ta bata amsa tana kallon nuzla sannan ta fita tana waiwayen Mr ATA tana yaba kyawunsa acikin ranta shi kuwa Mr ATA ko ajikinsa dan iskar ma data debota bai gani ba idan da sabo ya rigada ya saba da irin kallon da suke masa haka ma kallon da mrym da nuzla Ke masa bai sa ya dago daga duban wayarsa da yake ba .
Nurse sadiya na fita daga office suka ci Karo da husaina itama maakaciya ce "ke lafiyarki kika fito a hargitse Kmr wacce aka koro ?"uhm ke dai bari husseina wani matashi na gani a office din doctor shahida mutumin yayi min kyau matuka ya dauki hankalina wallahi irin mijin da nake nema kenan mijin duniya Mijin novel ya hadu sosai da gani yana da kudi yana da tarin ilimin boko da Arabic uwa Uba kyau "ke sadear raba kanki da wahala, kina diyar talaka dake naci ma da kyar kuke samu kullum Kuna yawo a gidan haya , yayanki ma da kyar yake daukar dawiniyarki Amman kin kashe kanki da mugun buri , ki roki Allah idan yaga dama zai Baki ki Daina zafafa burin akan auren me kudi ."
sadear ta Dan turo mata karamin Bakinta tana yatsina fuskar ,jikin Sadia yayi sanyi sosai husaina taja tsaki ta wuce ta barta Nan tsaye tana maganar a fili ."
Wayar hannunsa da yake ta faman daddanawa ce ta dauki qara ya manna a kunnensa tare da zamowa kad'an daga Kan kujerar da yake zaune yana lumshe idanunshi "na barota a gida ne ,okay suna bukatar new design's da kaya ?shikenan ki bawa kwararrun wadan da suka iya domin bana son a samu matsalar komai aikinsu dan last time sunyi complain okay may be tomorrow yana magana yana lumshe idanuwa yana lasar lip's dinsa na kasa ."
uzla,maryam duk suka zuba masa idanunsu suna kallonsa kowacce da abinda zuciyarta take saqawa jikinsa ya bashi kallonsa suke dan haka ya tsaida lumtsatsun idanunshi akansu yana masu wani irin kaskantacce kallo sannan ya dauke kansa ya cigaba da waya a daidai lokacin da husseina da sadiya suka shigo tare ita kanta husseina ta jinjinawa kyawunsa dan sai da tabawa idanunta abinci suka dauki abinda ya shigo dasu suka juya ."
Ya sake tsaida idanunshi akansu ganin still shi din suke kallo har lokacin Kmr basu san shi ba wani irin taikaci ya kamashi dan baya son yawon kallo arayuwarsa wani abu ya hadiye mai daci a makoshinsa kafin ahankali yaja tsaki yana cigaba da kallonsu yayinda su kuwa a matukar firgice suke kallonsa cikin tsananin tsoro da firgici sam basuyi tsamanin zai sake kamasu suna kallonsa ba irin kallon da yake masu yasa suka sake shiga rudani dan basu san abinda zai biyo bayan kallon da yake masu ba sannan basu abinda zasu fad'a dan kare kansu ba nuzla ta kalli maryam itama ta kalleta gabadaya jikinsu ya kama rawa nuzla tayi saurin durkushewa kasa bisa gwiwowinta dan tasan na lahira zai fisu jin dadi idan bata hanzarta bashi hakuri ba dan taga maryam bata da alamar bada hakuri "ka..! kayi hakuri ya Adam magana yake son yi amma ina jin isa acikin ransa yasa ya gagara furta komai illa kafarsa daya daya shiga jijigawa yana takaici ."
ganin har kusan minti talatin aunty shahida bata dawo ba yasa mr ATA ya Mike a fusace ya tura hannunsa daya cikin aljihunsa ya bar office din dan jikinsa ya fara bashi so take ta hadasu da Maryam ta fayyace mata komai a gabansa,yana fita nuzla ta nufi kofa cikin sand'a itama mrym ta biyo bayanta, nuzla na gama bude kofar turus sukai yi sakamakon ganin sadiya da husseina tsaye rungume da file suna kallon byn mrs ATA suna magana can kasa kasa sakamakon mutanen dake kai kawo " ai wannan ba bakon fuska bane sadiya matashin dan kasuwan nan ne da duniya Ke ji dashi sannan kani ne ga sister shahida yana zuwa lokaci zuwa lokaci ke baki ga kamarsu ba "?lallai kam sai yanzu na ganesa ko dan na rikice ne amman yafi kyau a fili km suna matukar kama sosai da Sister shahida sai dai har ya fita kyau ,wallahi husseina mutumin nan ya shiga raina sosai ban ta'ba ganin halittar daya dauki hankalina ba kamarsa komai nashi irin mafarkina "uhm uhm sadiya na sha gaya miki ki daina irin wannan hange ki tsaya matsayinki kin kasa fahimtata ."kisani babu abinda allah bayayi bansan dalili ba gani daya nayi masa amman na kamu da matsanancin soyayyarsa " wallahi wannan yafi karfinki Ke ko yaronsa yafi karfinki bareshi idan zaki dawo haiyacinki ki dawo taja hannunta sukai wuce sadiya na juya bayanta ."
Naunayen ajiyar zuciya nuzla da maryam suka sauke atare suna dafe qirji "marsi wallahi ba qaramin tsorata nayi ba ,koni kusan nafiki tsorata wallahi kadan ya rage ban saki fitsari ajiki ba qaramin saa muka ci ba da yau mun sha maruka suka kwashe da dariya "kinga bari na wuce bazan iya jiran Aunty shahida ba daman nazo karban test din hjyrmu ne nace nazo mu gaisa kinga wucewata sai mun hadu a gida ta zame hannunta dake cikin na maryam ta wuce tana daga mata hannu , maryam ta koma cikin office zaman jiran Aunty shahida ."
Bai Dade da wucewa ba doctor shahida ta dawo ta ga wayam bashi Babu alamunsa "sarkin zuciya halan ya gaji ya wuce "eh Maryam ta fada muryarta a sanyaye "okay ta shiga tattara kayayyankinta muje kou daman akwai maganar dana so muyi mu uku Amman zanzo gobe inshallahu idan na tashi daga aiki muyi a gida "magana kuma aunty.?"ta tmbyeta a tsaro ce .
"Eh!
" wacce magana ce haka Kuma har da ya adam zaayi ?aunty shahida tace ",magana ce me mahimmam ci , dan girman Allah aunty shahida wallahi bana son duk abinda zai hadani dashi nifa tsoro yake bani culmdown my sister ki cire wannan tsoro ba wani Abu bane face alkhairi shiru mrym tayi tana nazarin maganar aunty da tunanin wacce magana ce wannan da har sai anyita da ya Adam Kuma tace alkhairi ne ...?
suna fitowa haraban asibinti suga direbansa na jiransu "a ruwa Ina mai gidanka ? sai daya rusuna mata sannan yace "ya kira anzo an daukesa da wata motar aunty shahida ta girgiza Kai ta shiga mota ita da maryam inda take fad'a mata zuwan nuzla "Ayya kanwata ai kuwa na gode sosai itama kuwa ina son ganinta nan hankalin maryam ya dan kwanta jin har da nuzla sai dai har sanda a ruwa ya sauke aunty shahida a kofar gidanta zuciyar mrym bata bar Saka da warwara ba Allah Allah take gobe tayi taji ko meye .."
washegari da misalin karfe goma na safe sakon mutuwar sadiya ne ya riski doctor shahida, tayi matukar firgita da Jin wannan mummunar labari saboda cewar da akayi yankar rago akayi mata ta zabura ta mike daga zaunen da take jikinta na rawa ......."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page4
"Wani irin gumi ke tsatsafowa ajikin aunty shahida yayinda zuciyarta ta dinga bugawa da karfi fiyye da kaida ,nan take ta mike tsaye ta shiga zariya a office ta kasa zaune ta kasa tsaye tana sake jin wani sabon tashin hankali tana cikin wannan halin sai ga doctor sa'a ta shigo a rud'e ta tsaya suna kallon juna yanayin doctor shahida ya tabbatar mata taji abinda ya shigo daita office din dan duk ta fita haiyacinta ,a matukar tsorace aunty shahida take kallonta qirjinta na dokawa "nasan kinji abinda ya shigo dani ? wai an yiwa sadear yankan rago a gidansu."
har lokacin fargaba da tashin hankali bai bar gangar jikin aunty shahida ba ,da kyar ta iya motsa labbanta "yanzu doctor zinnira ta kirani take fad'a min wannan mummunar tashin
hankali alamarin nan ya d'aure min Kai matuka ,
hakika mutuwar sadear ya gigitani jiya fa iwar haka muna tare daita har tana cewa zatayi magana mai mahimmanci dani yau idan mun
had'u ko me zata fada min ? ta k'arasa maganar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "gbdy mutuwar mubina ce ta dawo min , Allah sarki rayuwa , Allah ya jikansu ya tona asirin duk wanda yayi sanadiyyar barinsu duniya , "duniyar nan ma guda nawa take da zaka kashe dan'uwanka ?cewar doctor sa'a "ya kamata muje gidansu yanzu ko ? "Eh ! wannan gaskiya ne ya kamata muje " da sauri aunty shahida ta tattara abubuwanta dan bata Jin zata dawo asibiti daga can gidan hajiya zata wuce doctor sa'a ta nufi kofar fita itama aunty shahida ta biyo bayanta da s auri ta rufa mata baya suka jera tana kokarin neman number doctor zinnira suje tare ."
"Kai tsaye gidansu sadear dake ijora olopa
suka nufa a kofar gidan suka iske 'yansanda suna tambayar aminu yayan sadear yadda abun ya kasance "to ni dai bazan qarar da komai ba , kawai dai na tashi da asuba na shiga d'akinta Inda take kwana tare da yarana guda biyu domin suyi sallah kawai naga gawarta cikin jini amman babban yarona sadi yace yaga bayan matar Kuma ya ganeta duk da jikinta lullube yake da bakin kaya ba'a iya ganin komai nata ".ya qarasa maganar Idanunshi na sauya kala." yauwa haka muke so yanzu Ina yaron yake ? police officer ya tambayi aminu yana gyara tsayuwarsa " kan aminu na kasa hawaye na tsiyaya daga idanunshi cikin rawar murya yace "yana ciki gida " girgiza Kai aunty shahida tayi cike da tausayawa masa ,."
a tsanake suka gaisa sannan gbdy suka had'a baki da doctor sa'a da dr zinnira sukai masa gaisuwa "aminu ya qarin hakurinmu Allah ya jikan sadear Allah yayi mata rahma halinta na gari ya bita "Ameen ya Allah , na gode Allah ya bada lada "Allah ya tona asiri duk wanda keda sa hannu a kisan sadear ya sake amsawa da" amen
na gode Kwarai da gaske yana kukan an cucesa an rabashi da yar'uwarsa tilo , a lisafinsa yanzu tayi awa hud'u a kabarinta shiru yayi yana juya girman alamrin zuciyarsa na zafin da bai san ranar dainawa ba ."
"Nan su aunty shahida suka barsu tsaye suka shiga cikin gidan suka nufi bangaren yayan sadear Inda suka tadda tsirarun mutane zaune
a cikin d'akin ana karba gaisuwa ,a natse suka gaisa da mutane tare da yi musu gaisuwa suka zauna Inda ake ta jimamin mutuwar kowa na fad'ar albarkacin bakinsa ,wasu na cewa ai hadiza ce ta kasheta tunda daman ta furta cewar itace zataga bayanta a bayyanan nasi ,yayinda wasu na cewa ba lallai bane ya kasance itace ta kasheta ."
Suna zaune police officers suka shigo tare da
aminu da yaronsa sadi dan kimani shekaru goma shabiyu yana musu bayanin wacce ya gani ."
'yansanda na sauraron yaron daki daki gefe guda kuma suna dudduba gidan a karshe suka tsaya a kofar d'akinsu hadiza tare da tambayar wacce ake zargi da aikata kisan ."
batare da 'bata lokaci ba akayi sallama a bakin kofar d'akinsu, hadiza kam tunda taji sallama police cikinta ya duri ruwa ta soma juya Kai zuciyarta na tsinkewa dan tunda akayi mutuwar take cikin tsoro da matsanacin firgici mara iyaka gabadaya komai nata ya tsaya cak ."mahaifiyarta ce ta amsa sallamar tana fitowa daga cikin d'akin "muna son ganin hadiza ko tana ciki ?"."eh ! tana ciki ta fad'a muryarta na d'an rawa "hadiza ki fito ana son ganinki da kyar hadiza ta fito kamar wacce kwai ya fashewa aciki ta tsaya a bakin kofar d'akinsu , kana kallonta zaka fahimci a tsorace take , sai da suka mata duban tsanake sannan daya daga cikin police din yace "kece hadiza ko ? ta gyada masa Kai alamun "eh! gabanta na faduwa da sauri da sauri suka ce "muje akwai wasu tambayoyi da zamu miki a office dinmu ."
"akan wani laifi kenan? mahaifiyarta tayi
karfin halin tambayarsu". idan muje office
dinmu kwaji akan wani laifi ne " suka tasa keyarta gaba mahaifiyarta ta biyosu da sauri
tana cewa "bazan bari ku tafi min da yarinya ba ku zubar mata da mutunci ba ." jin maganar mahaifiyarta yasa hadiza ta tsaya cak taki cigaba da tafiya police suka ce "muje ko!" "shiru tayi jikinta na rawa taki motsawa daga Inda take aiko daya daga cikin yar sanda mace ta rike tsintsiyar hannunta "zaki da girma da arziki ko kuwa mu tafi dake ta karfin tsiya ? "cike da tashin hankali hadiza ta fixge hannunta daga hannun yarsanda tare da marairaice fuska kamar zatayi kuka "ni bazani koina ba har sai na san dalilin da yasa zaku tafi dani office dinku ". zata sake magana suka daura bakin bindiga keyarta "idan kika sake furta wata Kalma zamu sakar miki wuta mu tasheki aiki," oya muje "tsimi tsimi hadiza ta soma tafiya mutane gidan na kallonta cikin tsananin farinciki dan daman taadabi kowa acikin gidan kowa tsoronta yake ."
"wani mummunar tashin hankali ya shigi mahaifiyar hadiza da hadizan karon kanta, ana k'okarin turata cikin motar 'yansanda su aunty shahida suka fito suka kama gabansu zuciyoyinsu cike da tsoro da fargaba ,direban aunty shahida ya sauketa a kofar gidansu sannan ta bashi umarnin ya kai doctor sa'a da zinnira ya dawo, suka yi sallama da abokan aikinta da zumar sai sun had'u gobe , Jiki a sanyaye aunty shahida ta shiga cikin tangamemen falon mahaifiyarta parlour'n shiru babu alamun akwai wani bil adama acikinsa hatta 'yan aikin gidan bata ji motsinsu ba ."
Ta samu guri ta zauna jagwab akan d'aya daga cikin kujerun Parlour'n tana sauke ajiyar zuciya har lokacin wani iri take ji ajikinta , shiru parlour'n baka Jin motsin komai sai na AC dake aiki a falon .
ko cikakken minti biyar batayi ba ta fara Jin motsin mutane , ta d'ago a hankali masu aiki ta gani cikin shigarsu ta kullum dukkaninsu rike da farantin silver suka rusuna tare da had'a baki "barka da zuwa hajiya "barka sannuku ya aiki ?"
"alhamdulillah ! suka amsa tare da ajiye tire suna tambayar abinda za'a kawo mata " me za'a kawo miki hjy akwai rice and stew akwai tuwon shekafa akwai dabmu shimkafa akwai ......? "duk babu wanda zanci aciki ta fada tana runtse idanunta dan kanta wani irin sarawa yake kmr ana buga mata guduma ,tana nan zaune hajiya zulaiheart ta shigo cikin shigar alfarma doguwar rigar lace har kasa wanda kimanin kudinsa ya Kai 500k ta zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya tayi shiru tana duban fuskar babbar diyarta "lafiya shahida duk na ganki haka ?a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu akan hajiya zulaiheart "wallahi mami wata mutuwa akayi mana agurin aiki mai shiga jiki ko ince an kashe yarinyar ......"
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun oh ni zulai me mutane suka d'auki rayukan mutane ne yanzu
kashe mutun bai musu wahala ?"wallahi mami sai ma Kinga yayan yarinyar abun tausayi marayu ne babu uwa babu uba sai Allah abun daya fi d'aga min hankali yankar rago akawa yarinyar abun tausayi sam babu Imani a zukatan wasu mutane taya zan iya kashe mutun da hannuna ?ta karasa maganar hawaye na zubo mata."uhm duniya kenan Allah dai ya tona asiri ko suwaye suke bin ya'yan mutane har gida suna kashesu to Kalli mutuwar mubina kigani abu kamar wasa har an kusan shekara biyu amman har yanzu babu labarin wanda yayi kisan."
Allah dai ya kyauta sam kasar nan babu tsaro shiyasa nasa aka qara tsaro mai karfi a gidan nan."
"hajiya ai ita sadear ana zargin makwafciyarsu ce tabi dare ta kasheta yanzu haka maganar da nake miki tana hannu jami'an tsaro zasu fara bincike akanta "alhamdulillah ai gara kam ita kuwa me yayi zafi haka ko akan me zata kasheta ?mutumin duniya hjy ai ba'a iya mutumin duniya sai Allah daya haliccesa, Allah dai ya sawaka kawai zamuce ."
"Ameen inji cewar hjy "wai Ina maryam da auta suka shige ne ? sunje gidan zabiba amman dai
nasan zuwa la'asar idan anci sa'a babu traffic zaki gansu sun dawo " Anya kuwa zan jira har wannan lokacin ? bari kawai nazo na wuce gida ."
"kin kuwa fada ma maryam batun wannan sarkin zuciya ?"wallahi a'a jiya dai nayi kokarin had'asu gbdy a office dina sai Kuma hakan bai yiwu ba ga yau ma ,Ina ganin sai dai weekend zanzo dan gbdy jina nake wani iri, wallahi mutuwar nan ta shigeni yarinya mai kirki da biyyaya da sanin ya kamata sam sadear bata da matsala a rayuwarta sannan bata da abokin fada kowa nata ne agurin aiki ga wasa da dariya ga ..."kira ne ya shigo wayar aunty shahida wanda yayi sanadiyyar katse mata magana ta d'auka tana duba screen din wayar direbanta ne mlm garba dan haka ta mike ta d'auki jakarta tayi wa hjy zulaiheart sallama ko a gidanta ma kasa tabuka komai tayi babbar yarinyarta madina duk ta damu sai faman tambayarta take ta fada abinda ke damunta bata ,boye mata komai ba ta fada mata mutuwar , mutuwar tsaye madina tayi dafe da qirji dan tasan sadear sosai tana janta ajiki idan taje gurin mamanta ,addua tayi mata hawaye na zubawa aunty shahida lokacin da take tuna moment dinsu da yarinya babu abinda yafi daga mata hankali kamar maganar da tace zasuyi a yau din gashi ta mutu batare da san ko akan me zata mata magana ba kwarai taso tasan ko akan meye , Allah sarki rayuwa kenan ta dade zaune tana jimamin mutuwar sadear kafin daga baya ta mike ta shiga dakinta ta kwanta zuciya da gangar jikinta na mata ciwo .."
Har yansanda suka karasa office dinsu kuka hadiza take , aka nufi d'akin bincike daita aka nuna mata gurin zama sannan bayan kamar awa daya wasu qararrun 'yan sanda suka shigo nan suka fara Aiko mata da tambayoyi d'aya daga cikinsu tace "ko zamu iya sanin dalilin da yasa kika kashe makwafciyarki sadear ? hadiza taji tambayar tamkar saukar aradu
take idanun sukayo waje tare da dafe qirjinta "wallahi bani na kasheta ba nima tashi nayi naji labarin mutuwarta ,"karki wahalar da hukuma zai fiyye miki sauki ki fito ki fada mana gskiya kunyi fad'a da sadear ko ba haka ? cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya tattare da tsoro ta gyada Kai alamun "Eh!"can km ta girgiza musu Kai alamun "a'a! police ta gyada Kai sannan ta cigaba "kenan kina nufin babu wata matsala ko fada wacce tasa kukayi sa'insa daita ? nan ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 43