ta dawo daidai, acikin satin tasan yadda tayi suka hadu da ussein maganar gsky ussein na sonta shima bazai iya rayuwa babu ita ba ,sai dai wulakancin da mahaifiyar bilkisu tayi masa da kiransa matsiyaci da tayi shi yafi komai tunzurashi ,domin duk gargadinta a banza ya daukesu babu abinda yasa aransa kamar cima burin sake kwace mata yarinya ta kowani hali sannan bai boye ma mahaifiyarsa komai da irin wulakanci daakayi masa itama kwarin gwiwa ta bashi tunda yarinyar tana son shi a matsiyaninsa talaka kar ya kuskura ya rabu daita ai su suke da mace sune a wahala , ina son nayi mgn alokacin amman babu halin yi a gabanta domin ussein shine auta km soyayyarsa dabam ce acikin yayanta amman dana fad'a masa gsky ya janye kudinrinsa ya rabunmusu da yarinya "
"nasan duk wannan ne sbd ni abokiyar hirarsa ce
dan duk gidan nan da yan'uwansa mata bai yarda
da kowa ba sai ni domin yace ina da sirri wasu abubuwan ma a gabana suka faru ,ussein ya sha kawo min bilkisu bangarena ta yini anan bilkisu na da matukar kirki da son mutane sannan bata da rowa idan zata zo wajena tana kawo min abubuwan amfani ga aiki da take min sam bazakice diyar mai kudi bace bata da son jikinta tana son aiki sosai da son mutane sadam kam ya sha gata a wajenta dan komai ta gani na yara zata siyo ta kawo masa wanda hakan yasa naji ina matukar qaunarta har cikin raina nake jin tausayinta domin tana sakewa ta fada min damuwarta da duk halin da take ciki a gidansu da yawon mgnr aurenta da mubarak da mahaifiyarta ke mata tana nuna mata mubarak yafi ussein sam bata dace da ussein ba ."
"ni kaina nazo na gano bata dace da ussein ba a wani zuwa datai na zaunar daita nace ina son nayi magana daita a matsayinta na kanwata da muka fito ciki daya baa matsayin matar da kanin mijina keso ba ta bani hankalinta ni kuma na fara magana bilkisu ko kinsan ussein yana shaye shaye ? ."tace min "eh !tasani km tayi masa mgn yace da zarar ya auret zai daina ,na numfasa nace "ke kin yarda zai daina ?tace min "eh ! Ko kinsan yana da yammata byn ke ?ta sake ce min eh ai ya rabu dasu Ina son na bata shawara ta auri mubarak ta bar ussein amman ina jin tsoro kar taje ta kwashe ta fada masa tunda idanunta sun rufe shi kuma ya fadawa mahaifiyarsa na samu matsala na kama bakina amman duk wanda ya kalli bilkisu km yasan family's dinta gsky yasan basu dace da juna ba ."
Soyayya ta sake yin karfi a tsakanin ussein da bilkisu dan babu abinda barinsa gidansu bilkisu ya janyo sai tabarbarewar rayuwar bilkisu dan a tunanina ussein ya fara saduwa da bilkisu batare da aure ba ni kaina alokacin naso ace iyayenta sun barta ta aureshi tunda ita taji kuma tagani amman mutanen nan suka ki saboda kyamar talaka , dan da irin rayuwar da suke gara ace aure sukayi, bazan ta'ba mantawa ba wata rana bilkisu ta sameni tana kuka na tmbyeta bata boye min ba ta fada min ciki gareta nan take na shiga damuwa mai tsanani nace "haba bilkisu me yasa zaki sakewa nmj jiki haka ?bakya jin tausayin iyayenki da yan'uwanki bakya gudun ranar da ussein zai juya miki baya ?ina ta mata fad'a Kmr kanwata ta jini ita km tana kuka tace ."na taimaketa acire mata cikin nace babu ruwana bazan saka hannu a kashe rai ba ,muna cikin wannan halin hjy ta shigo ashe taji duk mgnr mu itama cewa tayi abarshi kar acire taje gida zata samu iyayenta sai ayi mgnr aure kawai abu ya bani mamaki kamar wasu yoroba tunda sune ake irin wannan rayuwar dasu sai kayi ciki zaa yi aure km su yin ciki ba wani aibu bane a wajensu murna ma zaayi da samunsa tun daga nan na fahimci duk abinda ussein yake da saka hannun hjy ciki ."
Tô tun daga ranar ban sake saka bilkisu acikin idanuna ba a she byn ta bar wajena ussein ya bata maganin zubar da ciki ta sha koda ta koma gida sai ciwon ciki kwana tayi tana murkususu ciwo har garin allah ya waye ,cikin yaki fita ga ciki yaki daina ciwo iyayenta dai suka gaji suka kira doctor ya dubata byn ya gama dubata ya rubuta mata scan tô a wajen scan ne likita yaga ciki a mahaifarta tunda likita ya soma bayani mahaifiyarta ta rikice ta dimauce ta kasa gane takamaiman abinda yake fada ganin ta rude yace mata wani abu ya gani me kama da gas a mahaifarta amman ta kira wani daga gida yazo nan ta kira Aisha yayar bilkisu hankalinta a tashe tazo ta samu hjy rahma a reception zaune tayi tagumi bilkisu zaune a gefenta cikin tsoro da fargaba scan taso cikin ya fita cikin sauki batare da kowa yasani ba hjy rahma tace Aisha tashiga taji me doctor yake nufi da gas din da ya gani a mahaifar bilkisu ta shiga nan likita ya fad'a mata komai itama tashin hankali tashiga mai tsanani amman sai ta boye ta fito tana cewa uwar ulcer ke damunta nan hankalin mahaifiyarsu ya dan kwanta suka koma gida ."
Aisha ta kira bilkisu zuwa gidanta tana qarasowa bata tsaya wata wata ba ta rufeta da duka sai datayi mata mai isarta kamar zata kasheta sannan ta barta byn ta gama dukanta ta kira kaf yan dakinsu ta sheida masu sannan tasa akayi mata wankin ciki aka cire cikin lokacin da hjytr ussein taji babu cikin Kmr ta mutu dan bakinciki har da kuka tayi an cire mata jikanta dan karfin halin irin nata har da tmbyr bilkisu tayi wa ya cire mata jikanta ita km kuruciya ta fad'a mata tun daga lokacin hjy ta tsani Aisha da yan gidansu bilkisu amman km tana son bilkisu ace warta bazata tsaneta ba dan tana son danta."
Hajiya rahma ta lura tun da bilkisu ta dawo daga gidan Aisha ta warke sumul babu kwana ciwon ciki ta cigaba da abubuwanta sai dai Aisha ta kira hjy rahma tace kar a sake barin bilkisu fito koina har sanda mubarak zai dawo a daura masu aure abinda bilkisu ta tsani ji kenan dan ta tsani mubarak tsana mai girma bata ma son ana yi mata maganarsa karki ce shima mubarak din mummuna ne dogo ne sosai Kmr ussein sai dai shi baki ne kyakkyawan gaske dan sai dana sa ta nuna min hotonsa a istagram
an kafa wa bilkisu takunkunmi rashin fita koina hatta islamiyya ta daina zuwa alokacin sai datayi wata uku babu shiga babu fita kawai tana gida zaune km babu waya a hannunta an kwace da wayar hjy rahma take mgn da mubarak ."
Ganin Kmr ta kwantar da kai suna soyayya da mubarak Kmr gske yasa mahaifiyarta ta dauka ta cire komai aranta kuma taji dadin hk kulawa da soyayyarta ya qaru ta zaunar daita tayita nuna mata illar ussein tana qawata mata mubarak zataji dadin rayuwa agidan mubarak alokacin ta tmbayeta ta yarda zata auri mubarak tace eh ta amince wanda ba haka bane acikin ranta wata rana yan'uwanta gbdy suka zo gidan suna zaune a falon mahaifiyarsu yayanta abubakar wanda ya kasance first born a dakinsu yace a barta ta cigaba da rayuwata ta koma islamiyya Kmr kowa dan lokacin saukar alqurninsu ya kusa duk da bata zuwa baa cire sunanta acikin yan walima ba ba dan me ma zaa hanata rayuwa sbd wani matsiyacin banza Aisha da sauran yanuwata mata sukace a'a basu yarda da fitarta koina ba shi km yace abashi dalili gbdy suka kasa sheida masa dalili su dan haka yace dole ta koma islamiyya nasan kuna tunani ko zata hadu da wannan yaron ne yace su barta dashi idan ta isa tayi Kuskuren haduwa da ussein nan take uwar tace "ai bilkisunta ta canza bama zata kunyatata ba yanzu mubarak ne agabanta ."
Cikin satin aka dinka mata sabon uniform ta fara zuwa islamiyya Kmr abun arziki sai dai aranar ta samu waya ta kirasa bai shiga ba sai ta kirani nan na tmbyeta kwana biyu da halin da take ciki ,bata boye min komai ba a karshe tace na fadawa ussein ya kunna wayarsa nace mata "to! na qara da yi mata fad'a kar ta sake yarda dashi tace taji nan fa suka sake din kewa da ussein soyayya ta sake karfi har tafi nada da zara ta fito daga gida suke haduwa dashi km ni na tabbatarwa kaina bazasu ga junansu su bar junansu hk ba tunda sun dandani juna dole sai sunyi wani abu duk da shiedar zina tana da wahala "to ! bazan manta ba ranar wata asabar da safe ta fito daga gidansu da nufin zuwa islamiyya kai tsaye dakin ussein ta zarto ashe ana biye daita abaya batasani ba har ta shiga dakinsa tana shiga suka fara abinda suka saba suna cikin wannan halin sai shigowar mutanen gidansu sukaji tana rungume ajikinsa aiko ranar munga tashin hankalin da bamu ta'ba gani ba ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 18
"wato afa akan dai yarinyar nan ce da nazo akanta yar kanin mijina daya mutu ya barmana amatsayin riko to malam kamar yadda kasani banason yarinyar nan na tsani na ganta dan ina ji ajikina akwai nasarori da anan gaba zata iya samu domin soyayyar da mutane suke nuna mata kamar ma aikinka na farko bai ci ba, yanzu haka samari sunfi biyar da suka nuna suna sonta sai dai dadin abun da zarar sun zo lokaci kad'an sai su gudu ."
"to ga aikin nan yaci zaki ce kamar aiki bai ci ba , ai haka zasu dinga zuwa suna 'bata mata lokaci suna wucewa batare da tasamu wanda zai aureta ba babu fa wanda zai like mata acikinsu sai matsiyaci da zarar masu arziki sunzo zasu gudu ."
"Ai ni ba abinda nake só kenan ba ,ai bana son ko matsiyaci ma yazo wajenta nafi son ta qare rayuwarta a kaskance a bauta da wahala , sai tawa yar saurayin da yake sonta mutun d'aya ne kuma ba wani mai abun kirki bane gashi kace yarinyata zata samu farinjin samari masu kyau da kudi sai gashi sa'banin haka nake gani madadin maryama tayi bakin jini acikin mutane da samari duk banga haka ba ."
"kullum farinjinta sake qaruwa yake jamaa suna matukar qaunarta basa son kula ya'yana koina akaje sai dai ace a gaishe da maryama amman banda ya'yana , wani abun bakinciki afa har yaran nawa suma kullum maryama , suna matukar sonta sunki su gane ita din matsalarsu ce, ko wani abu nayi mata sai dai kaji suna min fad'a suna nuna min rashin daidai nan ta tsaya ta sauke numfashi da ajiyar zuciya ,afa yace "to yanzu ki takaita matsalarki me kike son ayi ?
Aunty salma ta gyara zama tace "ina son a fara rabata da ya'yana ina son naji sun tsaneta fiyye da yadda nake jin tsanarta acikin raina wannan shine kawai muradina kafin nazo neman wani bukatar ."afa yayi murmushi yace "ai wannan shi yafi komai sauki ki tafi gida kawai zaki ga aiki da cikawa cikin sati biyu masu zuwa , amman ina son ki dawo kafin kwanakin su cika akwai abinda zan baki indai har na baki ki kai amfani dashi magana ta qare amman yanzu zan fara jaraba 'yan abinda bazaa rasa ba ."
aunty salma tayi godiya ta ajiye masa kudi ta fice tana faman zuba godiya tana cigaba da zagi da maseefar kiyayyarta da maryama har ta fice daga gidan afa ta dawo gida tana saka da warwara dan ita ko kashe maryama afa zai yi tana só saboda tsanar datai mata yarinya sai kace lu'u lu'u ai muddin tana cikin gidan sai ya'yanta sun rigata samun gidan aure kafin tayi ,idan kuma har zata yi auren zata sa afa yayi mata aikin da zata auri matsiyacin daya fi ubanta talauci ."
*****
Bayan kwana biyu da faruwar wannan alamarin maryama tana tafiya cikin kayan islamiyya ta Ardus-salam yayinda hannunta ke rungume alqurani , yammaci ne duk mazan unguwarsu sun dawo daga aiki duk inda ta wulga sai an kalleta da shaawar tafiyarta tmkr bata son taka qasa tana cikin tafiya taji tafiya abayanta bata juya ba dan hakan baya daga cikin d'abiarta , sai ma qara saurin da tayi ta cigaba da tafiyarta saboda tasan kowaye ita yake bi zarginta ma cikin samarin unguwarsu ne dan akwai masu nuna suna sonta acikinsu ."
"maryama wannan uban sauri haka da kike zabgawa ko dan gudun kar na biyoki ne ?ta tsaya cak lokacin data fahimci muryar malamin islamiyyarsu ne na Ardus-salam mlm yahuza ta juyo a natse ta dubeshi cikin nikaf dinta tare da girmamawa ta gaishesa ."ya gyara tsayuwarsa yana kallonta , kunyarta ita tafi komai tsoratashi ,duk iya takun saurayi in har ya had'u da mace mai kunya yana samun karaya matuka a zuciyarsa ."
yayi dan murmushi irin nasu na ustaz "maryama har kullum zuciyata bata da sukuni jiddan wala khairan ,na kasa mantawa dake ,bani da wani sukuni face na samu amsarki game da bukatata dana kawo miki ."yayi shiru tare da tsayawa yana sauraron yaji me zatace nan take tayi kicin kicin tamkar wacce aka tsare da wuka zaa yankata sai da ta dauki second goma sannan tace "uhm !sai kuma tayi shiru ta qasa qarasa abinda zata fad'a maganar ta makale acikin zuciyarta shi kanshi ganin motsa lip's dinta bai sawa ranshi cewar zatace uffan ba bayan abinda ta furta ba ."
ba yau bane farko haka zalika yasan ba yau bane zai zama karshe ya saba tareta a hanya ta kasa ko ambaton sunan shi bama shi kadai ba kusan mutane suna yawon fad'ar haka akanta bata da yawon surutu da saurin sabo da mutun duk wanda ka ganta dashi tana d'ar d'ar alamun tsoro shima dan matsayin da yake dashi na malaminta ne yasa har ta tsaya akan hanya babu wanda ya kai ta tsaya dashi akan hanya ".
"Maryama idan na lura da yanayin fuskarki ba soyayyata bace baki amsa ba amman kuma bazan tabbatar akan cewar kin amsa ba ,tunda a kwayar idanunki kawai nake iya karantawa shine kunya ce ta hanaki ki fad'ar abinda Ke cikin zuciyarki maryama ki daure ki sanar dani menenê acikin zuciyarki akaina ko zuciyata zata samu sukuni da natsuwa ?".
shirun dai da baya só shi tayi dan bata da abinda zatace masa ,bazata iya wata soyayya ba da'ace ta d'aurawa kanta soyayyar samari da lokacin da suke guduwa suna barinta da ba qaramin tashin hankali zata shiga ba gara ta qarasa rayuwarta haka tunda soyayya ba dole bane arayuwar mutun haka ma aure sunah ne matukar mutun zai iya rike kanshi domin acikin
Sahbbai ma akwai wad'an da suka mutu basuyi aure ba dan haka mutun zai iya zamansa haka kuma aure da haihuwa bashi bane karshen duniya a ganinta ko babu shi mutun zai iya rayuwarsa ."
"hakika maryama duk cikin unguwar nan kai garin nan ma gbdy har cikin islamiyyarmu banga diya macen da take burgeni kuma zuciyata take dawainiya da tarin soyayyata kamar ki ba ki samar da amsar soyayyata a cikin zuciyarki ko zan samu farinciki da sukuni koda ta wata sigace da zan fahimta ."sosai hankalinta ya kai kololuwar tashi tama qasa tsayuwa bisa kafafunta , kafafunta suka shiga karkarwa ,yana son ya bata dama ta wuce gida saboda halin daya karanta atattare daita amman kuma bai gaji da kallonta ba kuma shi yasani ko zai kwana tsaye atare daita bazai gaji ba , sakina da kanwata ne suka zo zasu giftasu malam yahuza yayi sauri yace "sakina ku tsaya ga maryama tsaye ku wuce gida tare ."
Shukura ta kallesa tana jin wani irin tuttukin bakinciki acikin zuciyarta abun yayi matukar bata mamaki maryama tare da mlm yahuza malamin da take matukar só amman tsoro da shakkansa ya hanata fito da soyayyarsa
"malam ! kawai tace tayi gaba tana jan tsaki acikin ranta dan tasan muddin tayi a fili ta kad'e har ganyenta dan mlm yahuza babu wasa wajen disfila d'alibai da iya karatu da d'aukar wanka ga tsantsar kyau shiyasa kowani d'alibi ke matukar jin tsoronsa a kaf ardus-salam babu malamin da'ake shakka da só kamarsa da yawa yammata na qaunarsa ."sakina kam jikinta a matukar sanyaye ta wuce batare datayi mgn ba maryama ta bita da idanuwanta wani abu ya soki zuciyarta domin tun safiyar yau ta lura sakina ta canza mata abun ya matukar d'aure mata kai amman tayi mata uzuri da cewa yanayin rayuwa ne ."
Mlm yahuza bai sake magana ba sai tunanin kunyar shi da sakina taji dan ganinsa da maryama yasa ta kasa tsayawa dan haka yace "maryama sai gobe idan mun had'u a makaranta amman fa kisani bazan ta'ba daina tsaidake anan ba har sai ranar dana samu na cire kunyar nan kika amince min "Kanta kawai ta gyada masa muryata a matukar sanyaye tace "sai da safe ta juya ta cigaba da tafiya a natse bai bar wajen ba sai da tayi nisa sosai ta 'bacewa ganinsa ."
yana juyawa sukai ido biyu da mlm umar mai hausa atare sukai murmushi "wato kai har kullum bazaka daina wahalar da kanka akan maryama ba ko ?"Mlm yahuza ya qarasa inda mlm umar yake ya tsaya yana cewa "ya zanyi umar allah ya jarabeni da soyayyar maryama bazan iya hakura daita ba "kai kuma allah ya jarabi mata dayawa da sonka ba ?"wannan kuma damuwarsu ce ,ai dama haka zaka fad'a duk kuna son maso wani ,kai ma ka tausayawa masu sonka sai allah ya duba lamarinka ".
"Allah ma ya sani babu wacce nasan tana sona bare na tausayawa ya fad'a yana wani sham kamshi "Uhm uhm mutumina banda fad'ar son rai duk wanda ka fadawa haka zai d'auka bakasan abinda kakeyi ba ,"kaga umar rabani da wannan zance mu barta matsawar bata sarauniyar mata zaka min ba "karka duba yanayin gidansu maryama amman dai kai kanka kasan tafi karfin aurenka , maryama macece daya kamata wani hamshakin mai kudi yayi wuf daita ."
dan murmushi mlm yahuza yayi yace "haka ne amman ai duk mace bata fi karfin auren nmj ba kuma kowani mutun yana da nashi matsayin da zai iya burge mace , kuma ina dashi ina da quality da mace zata soni koda kuwa bani da kosisi bugu da qari ita mace ba kudi take bukata a soyayya da kulawa take so ni nan kuma zan kula da maryama ."
"da me zaka kula daita ?karka manta ita din cikakkiyar 'yar boko ce , yarinyar da idan ta fara aiki yanzu sai ta d'auki nauyin ciyar da mutanen gidanku gbdy dan haka banga abinda zai sa ka dinga wahalar da kanka kana 'batawa kanka lokaci akanta ba , kayi hakuri ka rabu daita domin dai babban goro sai magogin karfe ."
Mlm yahuza ya dan ji zafin maganar malam umar dan haka ya rage farar fuskashi "wai me kake nufi ? kana nufin dan ita din yar boko ce tana da kyau na bugawa a jarida kana tunanin zata samu aiki nan gaba zai sa ta iya fin karfin halittar ubangiji "? yahuza abinda nake son ka fahimta duk wad'an nan abubuwa da kake gani fifiko ne a tsakaninka da maryama kawai abinda nake so kaji aranka tafi karfinka tafi karfin aurenka ."
"kaga dan allah mlm ka barni ka zuba min ido ba wahalar banza nake yi ba ina cikin zuciyarta kunyar da take yawon nunawa akaina ta wadatar dani cewar nayi mata , nan gaba kad'an zata fahimtar dani ."Ka dai bi a sannu kar wata rana kana zaune wani hamshakin mai kudi ya shigo har cikin unguwar nan ya aureta .".
"bari kaji babu wani mai kudin da zai aureta domin suma masu kudin sunfi son ya'yan masu kudi yanuwansu , ita maryamar da ba galihu ne daita ba ,ai ba uban da zai shigo cikin wannan rubabbiyar unguwar ya kwashta ai duk wannan kyawun nata akan irinmu zai qare "yana gama fadar haka ya juya dan baya son ya sake 'bata masa rai ."
Tafiya kawai maryama take zuciyarta cike da kunci da tunani barkatai ba kuma akan mlm yahuza ba sai sabon sauyin data gani akan fuskar sakina dan na shukura mai sauki ne idan da sabo ta saba ita da yaran aunty hassana haka suke mata amman sakina fa basu saba haka ba suna matukar qaunar junansu tun suna yara su din masoya ne na hakika ."
da wannan tunani ta qarasa cikin gidansu kai tsaye ta nufi bangaren su sakina domin tambayarta dalilin sauyawarta ashe wahala ce ta shigo daita tana sallama aunty salma tace " Yauwa maryama d'auki tsintsiyar ki share min d'akuna tas shine amsar sallamar da aunty salma tayi mata kamar tace bazatai ba amman ta kasa ta ajiye alquranin dake hannunta ta d'auko tsintsiya ta fara shara batare da wata damuwa ba ."
tana shara aunty salma na zaginta ita da shukura amman sakina na zaune batace komai ba sa'banin da da bata yarda a zageta ko sakata aiki akan idanunta ,tana shara wani gurin da simiti wani gurin babu ga kuma sakina na zaune ta d'ago idanunta a natse ta kalleta taga kurar sharar na zuwa inda take muryata a sanyaye tace "sakinata ina ganin sai kin d'an tashi kinga kurar tana zuwa inda kike ta wani watso mata harara "ai gudun ruwanki nake kallo naga zaki shareni ko kuwa ."?
maryama tayi shiru tsaye tana karantarta akwai wulakanci acikin maganarta "ke kika kyaleta aunty sakina amman banda jakanta irin nata tana kallon mutane suna zaune zatace su matsa , banza shasha kawai mai siffar mayu ." inji cewar shukara dake zaune kusa da aunty salma abun bai yiwa aunty salma dadi sosai ba domin kuwa sakina taso ta furta ma maryama haka ba shukura ba ,sakina kam tun maganar farko datai bata qara ba ta tashi cikin bacin rai ta shige daki tana jin wani zazzafan kiyayyar maryama ."
Maryama tayi shiru kawai tana bin shukura da kallo "me kuma hakan yake nufi dani ? me na yiwa sakina ni kuwa daga jiya zuwa yau take fushi daita hk ."tayi wa kanta tambayar da bata da mai bata amsa sai sakina ita zagin shukura bai dameta ba kamar sauyawar sakina ta gyada kanta ta cigaba da shara tana tunanin laifin da taiwa sakina har ta qarasa ta wanke hannunta da kafafunta ta d'auki quraninta ta shiga d'aki inda sakina take zaune akan gado tana cika tana batsewa tana ganin maryama ta sake had'e rai Kmr taga mugun abu maryama bata damu ba ta zauna kusa daita ta soma janta da mgn taso tmbyrta laifin da tayi mata amman ganin yadda take barsarwa yasa tayi shiru daga karshe ta wuce zuciyarta cike da matsanancin damuwa ."
*******
Da misalin karfe d'aya na ranar laraba wanda yayi daidai da sauran kwana uku jirgin mr ata ya tashi zuwa france amman har lokacin jikinsa sai a hankali daga matsanancin ciwon kai ya dawo masa ciwon gabobin jiki dan ko miyo baya iya had'eyewa sosai mami ta sauko daga saman d'akin mr ata tare da likitansa byn mami ta sallame doctor rafeeq ta dubi maryam da nana hauwa'u tace "yayanku fa yau tsawon kwana biyu bashi da lafiya ku
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 43