Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
imani ko kadan shiyasa kowa ke shakkarsa, babu mutum daya isa ya fada masa magana yaji face boka Sulbaini, shima dan babu yadda zai yi d shi ne, domin kura ta san gidan mai babbar sanda. Hantaru ya jinjina kai sannan ya ce wai shin Rabbasu yana shiga gasar gudun tseren barew da ake yi duk shekara ne kuwa? 194 TASKARNOVELS.COM.NG Kumais yabce ai Rabbasu bai taba shiga gasar ba, saboda baya son ya auri kowacce budurwa face gimbiya Larziyya. Ita kuwa Larziyya mahaifinta sarki yace ba zai aurar da ita ba, sai bayan shekarar da za'a yi gasa ta arba'in sannan zai aurar da ita. Wannan shekara da muke ciki itace shekara ta arba'in din, a yanzu haka saura kwanaki ashirin aidai ayi wannan gasa. A daidai wannan lokacin ne su Hantaru suka ga wannan macen mai satar kallonsu ta baro inda take tsaye ta durfafo inda suke tsaye. Koda ta zo daf da Hantaru sai ta mika masa wata takarda. Hantaru na karbar takardar sai kawai budurwar ta juya da sauri ta fice daga cikin gidan. Hantaru ya mike d sauri da nufin yabi bayanta, amman sai Kumais ya rikota yace da shi kafa ka bita, kuma kada ka duba takardar sai bayan ka kadaita a cikin dakinka kai kadai, cikin mamaki Hantaru ya dubi Kumais ya ce shi shin kasan wannan matar data kawo mani wannan takardar ne? 195 TASKARNOVELS.COM.NG Kumais yace eh nasan kowace ce, amman bazan fada maka ba, domin nasan ba zatayi bayanin kanta ba a cikin takardar fata baka. Koda jin haka sai Hantaru yayi shiru bai sake cewa komai ba, kuma ya sanya wannan ta karfa a cikin minti goma, kuma ya saki jikinsa aka cigaba da walima kamar babu abinda ya faru. Ita dai wannan walima tunda hantsi aka farata amman sai bayan magrib sannan kowa ya watse suka tafi suna son barka. Hantaru na zaune shi kadai a harabar gidan bayan kowa ya tafi aka barshi shi kadai a zaune yana tunani, ba tunanin komai yake ba face irin rayuwar daya baro acan birnin Kisra da kuma irin wacce ya tarar a birnin darul Habur, abinda Hantaru ya fara ayyanawa a ransa shine ina ma ace ba sarki Usaidu bane mahaifinsa, gwara ace mahaufina dan usulun wannan birni ne na darul Habur, domin rayuwata ta fi dacewa anan, da tuntuni na share hawayen kakannina na takaicin rasjin cin gasar d suke yi. Amman dai tunda yanzu na zo nan to komai ya zo karshe, ta kowanne hali a wannan shekarar nine zan zama zakaran wannan gasa. 196 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da Hantaru ya gama ayyana haka a cikin zuciyarsa, sai yaji alamun ya soma jin bacci dan haka sai ya mike tsaye ya shiga cikin dakinsa, har Hantaru ya kwanta akan shimfida dmin yayi bacci sau ya tuno da batun wasikar nan da mace mai rufaffiyar fuska ta bashi. Hantaru ya mike zumbur ya zaro wasikar daga cikin aljihun rigarsa ya warwareta sannan ya fara karatu kamar haka: Takarda daga Gimbiya Larziyya zuwa ga bakon jarumi mai ban mamaki, ya kai taurarn shekara kayi sani cewa nayi matukar farin ciki da zuwanka wannan birni, kuma dama can na dade ina sauraron wannan rana ta zuwanka. Hakika wannan rana ta fiye mani komai a duniyar nan, ba komai bane yasa nake farin cikk da zukanka ba, face sanin cewa kai kadaine zaka iya yaye bakin cikin da ya addabi zuciyata tsawon shekara da shekaru. Ina mai tabbatar maka da cewa Sadauki Rabbasu ya dade yana sona, tun muna yara kanana, amman daidai da dakika ban taba jin ina kaunarsa ba, a kaidar wannan birni namu babu wanda zai auri wata mace kyakkyawa dole sai ya shiga gasar gudun barewa. Tunda sadauki 197 TASKARNOVELS.COM.NG Rabbasu ya zama saurayi bai taba shiga wannan gasa ba domin a kaina kadai yayi tanadinta, wato ya kudurce a ransa cewa ba zai shiga gasar ba sai idan akaina ake yinta. Tabbas bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa duk sa'adda gasar aurena ta zo, indai Rabbasu ya shiga gasar babu wanda zai samu nasara akansa. Ni kam dadai na auri Rabbasu gwara ace na rasa rayuwata ma gaba daya. Ya kai Gwarzon jarumi ina mai rokonka saboda mahaifiyarka Shamilat da kuma kakanka sarkin makera Shuraim da ka taimakeni ka ceci rayuwata ka shiga wannan gasa, koda kuwa ba zaka samu damar aurena ba, ni dai babban burina shine ace Rabbasu ya rasani, idan har ka amince zaka yi mani wannan taimako, to mu hadu a dutsen kufainu dake can bayan gari a gobe da yammaci daidai lokacin faduwar rana domin naji amsata a bakinka, daga karshe ina mai kira a gareka daka rungumi kaddara bisa wani mummunan labari da zaka ji daga bakin kakan mahaifiyarka wato boka Sulbaini, domin labari ne mara dadi kuma zai yi matukar jefaka a cikin bakin ciki da damuwa. 198 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da Hantaru yazo daidai nan a karatun wsikarsa sai hankalinsa ya dugunzuma ya shiga sabon tunani, har ya zamana cewar dare ya raba amman ya kasa bacci, abinda ke wa Hantaru zarya a cikin zuciyarsa shine wai shin wane irin mummunan labarine boka Sulbaini zai labarta masa wanda zai kefashi cikin bakin ciki. Abu na biyu kuma shine, ta yaya zai samu nasarar lashe gasar tseren kamo barewa na karshen shekara domin kubutar da rayuwar Gimbiya Larziyya. Haka dai Hantaru ya cigaba da wannan tunani a cikin zuciyarsa, bai gushe ba yana tunani har alfijir ya keto bai anakara ba. Bayan anyi kalacin safe kowa ya gama kimtsawa sai Salimat, Shuraim da Hantaru suka yi hawa suka tafi izuwa gidan boka Sulbaini, da yake akwai yar tazara tsakanin gidan Shuraim da gidan Boka Sulbaini basu isa can dinba har sai da hantsi ta yi. Gidan boka Sulbaini a bayan gari yake a saman wani katon dutse wanda ana iya hangoshi daga kowanne sashi, wato bangaren gabas da yamma, da kuma kudu da arewa. Daga nesa mutum zai iya hangoshi dan mitsitsi amman da zarar ya gabato sai ya fuskanci cewar yana da girma ainun. 199 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da su Shuraim suka iso bakin kofar gidan boka Sulbaini sai suka sauka daga kan dawakansu suka dauresu a jikin bishiyoyi, sannan suka haye saman dutsen suka durfafi gidan boka Sulbaini. Shuraim ne akan gaba sannan Shamilat sai kuma Hantaru, da isarsu kofar gidan wanda hantaru ya kura wa idanu yana mashi kallon mamaki saboda ganin yadda aka gina shi da zallar dutse na murjani, sai Shuraim ya kunna kai, Shamilat ta bishi a baya. Koda Hantaru ya mika kafarsa zai sa a cikin gidan, sai yaji a daka masa tsawa wacce tasa tsigar jikinsa mikewa, bai san sa'adda ya janye kafar tasa ba kuma ya koma da baya, Shuraim da Shamilat ma sai suka razana suka koma da baya, kawai sai sukaga kofar gidan ta rufe da kanta. A sannan ne kuma boka Sulbaini ya bayyana tsulum a gabansu kamar walkiya, idanunsa cike da kwalla ya kurawa Hantaru idanu. Al'amarin daya daure wa Shuraim, Shamilat da Hantaru kai kenan, Shamilat ta dubi Sulbaini cikin matukar mamaki da damuwa ta ce Haba ya kai kakana, shin baka shaida ni bane? Ka tuna fa yau kusan shekara ashirin da doriya kenan rabon da muga juna, ina ta dokin nazo naganka 200 TASKARNOVELS.COM.NG domin na nuna maka dana, amman sai ka tarbemu da tsawa, Kaicona! Inda nasan haka zaka karbeni da bazamu zo gareka ba. Sa'ad da Shamilat ta zo nan a zancenta sai hawaye ya sake zubowa Boka Sulbaini ya dubeta cikin takaici da damuwa sannan ya nuna Hantaru da hannu ya ce Yake jikata abar kaunata, kiyi sani cewa wannan yaro ba jininmu bane, ina nufin ba kece kika haifeshi ba, kiyi sani cewa duk wanda ya kasance ba jinina ba idan ya shiga cikin gidan nan hallaka zai yi, wannan ne yasa na yi muku tsawa domin bana son ya hallaka. Koda jin wannan batu sai Hantaru, Shuraim da Shamilat suka zazzaro idanu, hankalinsu ya dugunzuma ainun. Nan take idanun Hantaru suka ciko da kwalla ya dubi boka Sulbaini yace wace shaida ce da kai wacce zata gamsar damu cewa ni ba jininku bane? Koda jin wannan tambaya sai tausayin Hantaru ya kama Boka Sulbaini har hawaye ya zubo masa, sannan ya ce tabbas kuwa nike da babbar shaida, na umarceku da kuyi duba izuwa 201 TASKARNOVELS.COM.NG wannan bangon gidan nawa domin ku ga yadda al'amarin ya kasance. Ba tare da gardamar komai ba su Hantaru suka dubi bangon gidan, shi kuwa boka Sulbaini sai yayi nuni da hannunsa izuwa bangon, take hoton birnin Kisra ya bayyana a kai, aka fara nuno wasu ababuwa da suka gabata tsawon shekara da shekaru, da farko a nuno lokacin da matar sarki Kusaidu wato Zarifa ta kadaita da Boka Ardusa ta ce da shi lallai ya baiwa sarki shawarar kara aure domin su cimma burinsu, wato suyi shirin da zasu baiwa sarki dan da suka samu ta hanyar lalata ta cin amanar sarki a matsayin dan cikinsa ba tare da ya sani ba. Daga nan aka nuno lokacin da sarki Kusaidu ya zo birnin darul Habur har ya shiga gasar neman aure kuma ya samu nasara a tseren gudun barewa, sanadin Salimat ta zamo matarsa aka daura aure ya tafi da ita birnin Kisra. Ina yi maku barka da wannan lokaci sannan ina baku hakuri na shiru da kuka ji hakan ya faru ne 202 TASKARNOVELS.COM.NG saboda rashin lafiya da na kwanta tun bayan sallah, amman yanzu AlhamduLillahi Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta Ko Kuma Complete Document zasu iya mani magana ta whatsapp 08138873799 MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part O Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Sannu a hankali aka nuno yadda boka Ardusa ya saka wa Salimat juna biyu na sihiri da kuma yadda ya boye cikin zarifa na gaskiya har izuwa lokacin haihuwarta ba tare da kowa ya sani ba. Daga nan aka nuno ranar da Shamilat ta kamu da ciwon nakuda, ta kwana ta yini a ciwon 203 TASKARNOVELS.COM.NG nakuda, har sai da zarifa ta shiga dakin haihuwar ta kori matan dake yi wa Shamilat unguwar zoma, ya zamana cewa su biyu ne rak a cikin dakin. Nan take ta sumar da Shamilat ta kama tata nakudar, ta haifi santalelen jariri, ta ajiye wa samilat nata jaririn ta fice daga dakin haihuwar, daga nan ne fa sai jama'ar gari suka rude da farin ciki Salimat ta haifi da, daga nan aka ci gaba da rainonsa har ya zama Hantaru. Koda hoton duk wannan al'amari yazo daidai nan sai boka Sulbaini ya sake yin nuni da hannunsa izuwa ga bangon, take hoton komai ya bace. Nan take Hantaru ya kwarara uban ihu cikin takaici da bakin ciki, kuma ya fashe da matsanancin kuka. Itama samilat sai kawai taji jiri ya kwasheta, kafin su ankara ta sulale kasa sumammmiya. Cikin hanzari boka Sulbaini yayi tsafi ruwa ya zubo daga cikin yan yatsunsa ya yayyafa mata, sannan ta farfado ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. Sulbaini da Shuraim suka kamu da tsananin tausayin samilat har basu san sa'ad da suka 204 TASKARNOVELS.COM.NG kama kuka ba duk su hudun, haka suka yita wannan kukan. Sai daga can Hantaru ya zo gaba samilat ya durkusa bisa gwiywoyinsa ya kama kafadunta itama sai ta kama kafadunsa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunsu yace ya ke Ummina hakika yanzu na gamsu cewa ba kece kika haifeni ba, amman kiyi sani cewa har abada kece uwata domin nononki nasha na rayu har na girma, dan haka bazan taba daukar waccan ba da boka Ardusa a matsayin iyayena, kuma a halin yanzu ina jin cewa bani da makiya a duniya sama da su, kuma bani da wani buri a duniya da ya wuce na zare masu ruhin numfashinsu, domin sunci amanar mijinki sun cuci rayuwata sun kuma yi mani babbar barna da har abada bazata gyaru ba. Lallai bayan naci gasar tseren gudu sai na koma Birnin Kisra na kasheta ita da Ardusa sannan na fada wa sarki Kusaidu gaskiyar al'amari na ce masa ni ba dansa bane ga yadda akayi aka same ni. Bayan d Hantaru yazo nan a zancensa sai samilat ta rungumeshi, sannan ta fashe da sabon matsanancin kuka, shima sai zuciyarsa ta karaya ya cigaba da kukan, daga can sai samilat 205 TASKARNOVELS.COM.NG ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna sosai ta ce ya kai dana ina son k tuno da tsantsar kaunar dake tsakaninka da sarki Kusaidu, ka tuna cewa ba a son ransa na taho da kai nan garin ba, saboda baya son rabuwa da kai daidai da na kwana daya, yanzu idan kaje ka sanar da shi gaskiyar al'amari yaya zai ji, kuma wane irin hali kake tunani zai shiga? Ina mai tabbatar maka idan yaji wannan labari zai iya hadiyar zuciya ya mutu, domin gabadaya zai ga rayuwarsa bata da wani amfani a duniya, tunda mutumin daya amincewa fiye da kowa a duniya wato boka Ardusa ya ci amanarsa. Sannan babban burinsa na duniya ya wargaje, tunda bai samu haihuwa ba, matarsa d suka yi auren saurayi da budurwa wacce yake kauna fiye da kansa, kuma ya bata amanar kansa tsawon shekaru yau itama ta ci amanarsa, ya kau dana ina mai rokonka da komai rokonka komai rintsi da tsanani kada ka bari sarki kusaidu yasan wannan sirri, idan har ka dauke ni a matsayin uwa ina so ka sani cewa ina kaunar mijina fiye d duk yadd kake tsammani, saboda haka lallai ina so na koma birnin Kisra na cigaba da rayuwa da shi cikin farin ciki, ban 206 TASKARNOVELS.COM.NG hanaka yiwa boka Ardusa da waccan mata hukunci ba, amman kayi sani cewa tana lafiyarta dai-dai yake da taba lafiyar mijina, idan kuwa kayi haka to babu ni babu kai sai dai ka sauya uwa. Sa'ad da Samilat ta zo nan a zancenta sai Hantaru ya rungumeta a karo na biyu ya fashe da kuka saboda bakin ciki da takaici domin yasan cewa ba xai iya ketare wannan doka ba data kafa masa. Bayan Samilat da Hantaru sun dade suna kuka na bakin ciki sai boka Sulbaini ya janyeshi daga jikin Salimat, sannan ya jashi gefe daya inda su Salimat ba zasu ji abinda zasu tattauna ba. Sulbaini ya dubi Hantaru cikin natsuwa sannan yace ya kai wannan Gwarzon jarumi, namijin Duniya, kayi sani cewa na hango maka mugun hadari a cikin rayuwarka da kuma mummunan karshe amman fa sai idan kayi sakaki soyayya ta rudi zuciyarka, na sani cewa Gimbiya Larziyya ta baka wasika a jiya sa'ar da aka yi walima a gidan Shuraim, kuma ta gayyaceka zuwa bayan gari tana son ku hadu a dutsen kufainu, ko ba haka bane ? 207 TASKARNOVELS.COM.NG Hantaru ya gyada kai cikin mamaki yace haka al'amarin yake. Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce yakai wannan jarumi ka sani cewa Gimbiya Larziyya kyakkyawar mace ce ta gaban keatance dan haka da zarar ka yi arba da ita zaka ji ka tsunduma a cikin kogin soyayyarta, kuma zaka iya salwantar da rayuwarka kai data kowa ma dan kawai ka mallaketa, gargadin da zan yi maka shine, kada ka yarda ta umarceka da yin abinda zai sa ka rushe alakar dake tsakaninka da jikata Salimat anan gaba bayan kaci gasar tseren gudun barewa, idan kuwa ka kuskura ka aikata haka to kaima halaka zaka yi, kuma daukakarka zata tafi a banza, sai dai kawai a dunga tuno da kai a tarihi. Lokacin da boka Sulbaini ya zo nan jawabinsa sai hankalin Hantaru ya dugunzuma fiye da koyaushe, yayi shiru yana tunani har izuwa lokaci mai tsawo, daga can sai ya dago ya dubi boka Sulbaini yace lallai zan kiyaye bisa dukkan wannan shawara daka bani. Cikin farin ciki boka Sulbaini ya rungume Hantaru yana mai cewa madalla da da mai 208 TASKARNOVELS.COM.NG halacci ga jikata, wanda naso ace ya zamo jinin jikata. Koda jin haka sai Salimat ta taso da gudu daga inda take tsugunne ta rungume Sulbaini da Hantaru suka kankame juna su uku suka fashe da sabon kuka. Shuraim dake tsaye yana kallonsu shima sai ya fashe da kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu. Shuraim, Salimat da Hantaru basu yi sallama da boka Sulbaini ba sai da la'asar ta yi, lokacin da suka zo yin sallamar ne sai Sulbaini ya dubi Hantaru ya ce da shi ya kai Gwarzon namiji ina son kayi sani cewa zaka sha bakar wahala a wannan gasar tseren da zaka yi, kuma kai da Sadauki Rabbasu kunnen doki zaku yi a cikin gasar, saboda haka sai kunyi gasar sau uku, kaga kenan dole ne ka zauna a wannan garin tsawon shekara uku, idan ma har zaka lashe wannan gasa to sai bayan kaje ka samo wata sihirtacciyar takobi wacce babu kamarta q fadin duniya. Tabbas kai da Sadauki Rabbasu zaku tafi neman wannan takobi, duk wanda ya riga dan uwansa mallakar wannan takobi to shine zai auri gimbiya Larziyya. Tabbas sai ka jajirce ainun sannan zaka iya samo wannan takobi da ake yiwa lakabi da Saiful Lujara. 209 TASKARNOVELS.COM.NG Asalin takobin Saiful Lujara wani hatsabibin boka ne ya kareta da ruhin wasu babaken aljanu guda dubu casa'in, a rabar da bokan ya kammala takobin ne ya mutu, sakamakon tsananin wahalar daya sha a kokarin kerata, saboda sai da ya kwana hudu ba ci ba sha, tsananin yunwa da kishin ruwa ne suka kasheshi, yanzu haka takobin na nan a cikin wannan kogon da bokan ya mutu, kuma babu wanda ke iya zuwa inda wannan takobi take saboda tsananin masifun dake cikin dazuzzukan kafin a ketare a isa kogon, da kuma shi kanshi bala'in dake cikin kogon face sadaukin da ya yarda da Sadaukantakarsa, kuma ya zamana cewa yana da matukar karfin sihiri. Daga lokacin da makerin takobin Saiful Lujara yya mutu kawo izuwa yanzu shekara dubu uku kenan, kuma a kalla sadaukai sama da guda dubu sun tafi dauko wannan takobi amman har yau har gobe dayansu bai dawo ba. Ya kai Hantaru ni kam nayi alƙawarin cewa zan taimaka maka da dukkan karfin sihirina, kamar yadda sarkin mafarauta zai taimaka wa dansa Rabbasu da dukkanin karfin sihirinsa domin yaje ya samu damar dauko takobin daraja ta Saiful Lujara. 210 TASKARNOVELS.COM.NG Ka sani cewa bani da wani buri da ya fi naga kambun gasar tsere ya dawo zuri'armu ta makera. Sa'ad da boka Sulbaini ya zo nan a zancensa sai jikin Hantaru yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma domin ya fuskanci cewar duk wahalar da ya sha a baya kamar somin tabice akan wacce zai sha a nan gaba, saboda samun nasarar sa akan sadauki Rabbasu a wannan gasa da kuma dauko takobin Saiful Lujara wannan abu ba karamin jidali bane. Nan dai boka Sulbaini yayi wa Hantaru sallama a matsayin ba zasu sake saduwa ba sai nan da kwanaki goma sha takwas wanda ya rage saura kwana daya ayi gasar tseren gudun barewa. Ba tare da bata lokaci ba Shuraim da Salimat suka yi wa Sulbaini sallama gami da godiya sannan suka sakko daga kan dutsen suka kwance dawakansu duk su ukun suka hau sannan suka nufi hanyar gida. Salimat na waigen gidan boka Sulbaini wanda ke saman dutse, ta tuno da rayuwarta a gidan tun tana yarinya karama kafin rasuwar matar boka Sulbaini, abinda salimat ba zata taba 211 TASKARNOVELS.COM.NG mantawa ba shine kullum sai sunyi wasan yar boyo ita da matar boka Sulbaini, wani lokacin ma har wasan doki suke yi, ta hau gadon bayan Sulbaini tana sukuwa. A daidai wannan lokacin ne hawaye ya zubo wa salimat taji ace inama zata iya dawo da abinda ya wuce amman ina ai babu dama. A lokacin da su Hantaru suka iso mararrabar hanya ne, inda ta rabu gida uku; daya zata kaisu izuwa cikin gari, daya izuwa dajin kufainu, dayar kuma izuwa inda suka baro. Sai Shuraim ya nuna wa Hantaru hanyar da zata sadashi izuwa dajin kufairu. Yace ya kai Gwarzon Sadaukai wannan hanyar ita zaka bi kaje inda gimbiya Larziyya ta ke, maza kaje ku hadu, sannan ka tabbatar ka dawo gida da wuri kafin dare yayi sosai. Koda jin haka sai Hantaru yayi murmushi sannan ya dubu salimat ya ce zan tafi izuwa ga Gimbiya idan har kinyi izini a gareni ya ummina. Salimat ta mayar masa da martanin murmushi sannan ta ce jeka abinka ya kai dana, ina goyon baya dari bisa dari. 212 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin haka sai Hantaru ya zaburi dokinsa cikin farin ciki ya sukwaneshi izuwa cikin dajin kufairu. Yar gajeriyar tafiya hnataru yayi ya iso inda dutsen yake, tun daga nesa Hantaru ya hango gimbiya Larziyya a bisa dutsen a zaune tana sanye da wasu kurayen tufafi, masu tsananin kyau da ban sha'awa ta lullube kanta gaba daya da mayafin kayan. Koda Larziyya ta hango Hantaru ya durfafo inda take, sai ta mike tsaye, mikewarta keda wuya sai iska ta dauke mayafin data rufe kanta da shi ta yi kasa da shi, a wannan lokacin ne hantaru yayi arba da fuskar Gimbiya Larziyya, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya daidaita gabban jikin gimbiya Larziyya, a iya sanin Hantaru ko a bakin ma'abota labarin duniya, bai taba jin wanda ya wassafa mace mai kyau na Gimbiya Larziyya ba, saboda tsananin kyawun fuskarta dana kirar jiki. Idan mutum yayi arba da ita sai yayi tsammanin cewa ba mutum bace aljana ce. Hantaru dai bai san sa'ad da ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak ba, daga kasan dutsen suka kura wa juna idanu suna sun murmushi. Nan take yaji kibiyar so ta sokeshi a kahon zuci kuma yaji cewa a haukansa ko mutuwa bata isa hanashi mallakar gimbiya Larziyya ba. 213 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin natsuwa da tafiyyar kasaita Larziyya ta sakko daga saman dutsen kufairu, tazo daf da Hantaru ta tsaya sannan ta ce lale marhabun da Sadauki uban sadaukai, tauraron zamani mai haska duniya. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa yauce ranar da tafi kowacce rana farin ciki a rayuwata, domin a yau nayi arba da masoyin zuciyata wanda na dade ina begensa tun gabanin naga fuskarsa, ina godiya daka amsa gayyata ta bisa muhimmiyar wannan rana ta saduwarmu. Shin daka ganni a yanzu kaji kana sona, kamar yadda na dade da kamuwa da kaunarka? Lokacin da Hantaru yaji wannan tambaya sai yaji dariya ta kubuce masa, itama sai ta kama dariyar kamar su duka biyun sun zautu. Lokaci guda suka daina dariyar kuma suka kura wa juna idanu, Hantaru yq ce yake wannan mafifiyar ma'abociyar kyawun, kiyi sani cewa babu wani mahaluki walau a mutane ko a aljanu da zai ganki bai kamu da tsananin kaunarki ba. Tabbas a yanzu ina ji a jikin cewa zan iya salwantar da rayuwata domin farin cikinki ko domin na mallakeki. 214 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin wannan batu sai Gimbiya Larziyya ta cika da tsananin farin ciki, nn take rungume hantaru suka kankame juna har izuwa wani lokaci mai dan tsayi, daga can sai ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna ta ce ya kai masoyina kayi sani cewa yau saura kwana goma sha tara ayi gasar neman aurena, kaine kadai mutumin da zai iya share mani hawayena, ya hana Sadauki Rabbasu samun nasara a wannan gasa, idan har kaunar da kake mani ta gaskiya ce ina so ka daukar mani alkawarika guda uku a yanzu, alkawari na farko shine; duk wuya duk rintsi ba zaka janye takarar neman aure na ba, alƙawari na biyu duk alfarmar da na nema a wajenka zaka yi mani ita, alkawarina na uku kuwa shine a duk halin da muka tsinci kanmu ba zamu guji juna ba, idan har ka amince da wadannan alkawaruka to nima na yi maka alkawari cewa zan sallamar da rayuwata domin ka, kuma har abada babu wani da namiji da zai sanni ya mace face kai, haka kuma duk irin bala'in da zaka shiga zan bika mu shiga tare koda kuwa zan hallaka. Sa'ad da Gimbiya Larziyya ta zo nan a bayaninta sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfin gaske, abinda ya fara fado masa a rai ne shine 215 TASKARNOVELS.COM.NG batun alkawarin daya daukar wa mahaifiyarsa, Hantaru ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa anya kuwa alkawarin dana daukar wa ummina ba zai zamo kishiyar wanda Gimbiya Larziyya ta ke so na daukar mata a halin yanzu ba kuwa? Nan fa ya rasa irin hukuncin da ya kamata ya yanke. Lokacin da Larziyya taga Hantaru yayi shiru bai bata amsa ba, kuma ya sunkuyar da kansa kasa yana tunani, sai ta dafa kafadarsa ta ce kai nake sauraro ya masoyina, wane hukunci ka yanke game da alkawarin da muka daukar wa junanmu. Hantaru ya dago kai cikin murmushi yace yake abar kaunata kiyi sani cewa kinzo mani da babban alƙawari, wanda yafi gaban na yanke hukunci yanzu take, saboda haka ina neman alfarmar ki bani lokaci nayi tunani. Koda jin haka sai Larziyya tayi murmushi sannan ta ce na baka lokaci, daga nan har izuwa ranar da za'a fara gasar neman aurena, amman sai kayi alkawarin cewa ba zaka yi shawara da kowa ba, sai da zuciyarka kadai. 216 TASKARNOVELS.COM.NG Hantaru ya maida mata da martanin murmushi sannan ya ce nayi alkawarin ba xan yi shawara da kowa ba face da xuciyata, cikin tsananin farin ciki Larziyya ta sake rungume Hantaru a karo na biyu sannan ta sumbaci goshinsa. Kawai sai ta tafa hannayenta biyu take wani bawan sarki ya fito daga cikin duhuwa janye da keken doki. Larziyya ta dubi Hantaru cikin wani irin murmushi mai dagula tunanin da namiji ta ce daga yau ba zamu sake saduwa ba sai ranar gasa, lallai a ranar ne zaka bani amsoshin tambayoyina, da wannan kalami nake maka sallama ya madubin zuciyata, sai lokaci yayi. Koda gama fadin haka sai Gimbiya Larziyya ta juya ta nufi inda keken dokinta yake tana mai waigen Hantaru, shi kuwa sai ya biya da kallo kawai ya kasa cewa komai har ta shiga cikin keken dokin ta zauna. Ina yi maku barka da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin lafiya 217 TASKARNOVELS.COM.NG Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta Ko Kuma Complete Document zasu iya mani magana ta whatsapp 08138873799 Bawan ya kafa linzaman dawakan dake jan keken dokin suka nufi hanyar cikin gari. Tun Hantaru na hango keken dokin har ya bace wa ganinsa, sai da Hantaru ya dade a tsaye yana mai nazari da tunani sannan shima jaye ya hau dokinsa ya nufi cikin gari. Da isar Hantaru gida sai ya iske tuni Salimat ta shirya masa abinci a ajiye a dakinsa. Bayan Hantaru ya zauna ne ya huta kuma ya ci abinci sai ya fada cikin kogin tunani, ya kasa yi wa kansa zabi bisa amsar da ya kamata ya baiwa Gimbiya Larziyya a ranar da za a yi gasa. Yana cikin wannan hali ne Salimat ta shigo cikin dakin ta riskeshi a cikin halin tunani. Cikin matukar damuwa Salimat ta zauna daf da shi sannan ta ce ya kai dana na sani cewa ka kamu da kaunar Gimbiya Larziyya domin babu 218 TASKARNOVELS.COM.NG wani da namiji da zai yi arba da ita ba tare d ya fada tarkon begenta ba. Ya kai dana ka fada mani dukkanin abinda kuka tattauna kai da ita, ni kuma zan baka shawara wacce zata fissheka a rayuwa. Koda jin haka sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ainun, kuma ta gargadeshi akan kada ya fada wa Salimat gaskiyar maganar da yayi da Gimbiya Larziyya. Hantaru ya dubi Salimat cikin murmushi yace yake ummina kiyi sani cewa babu abinda muka tattauna face kalmomin kauna gami da alkawarin zamu so juna da gaskiya. Koda jin haka sai murna ta kama Salimat ta sa masa albarka sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin. Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda Hantaru yasan abinda zai biyo baya bisa boyewa Salimat gaskiyar al'amari da bai boye mata ba. Tabbas

Chapter 9 of 13