Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kuka ta kama rokon sarki maharaz da ayi wa imnal afuwa, sarki maharaz ya dakawa mulaifa tsawa yace kinaso nima nayi laifi ne ga mai girma darbuza, lallai ni mai biyayyane ga mai girma darbuza idan 49 TASKARNOVELS.COM.NG kikaga ba ayiwai imnal wannan hukuncin ba to tabbas bana nunfashi ne, nan take sarki maharaz ya sake duban karti guda biyu kawai sai suka daiki bulala da gishiri acikin wani katon kasko suka hau kan wani dogon munbari mai matattakala, Wanda yake dab da inda aka daure imnal suka fara cika aikinsu, yazama cewa daya ya fara zabgawa imnal bulala shi kuma dayan yana manna mishi gishiri a fatar jikinshi, maimakon jama'ah suji imnal na ihu da kuka sai sukaga ya kurawa gimbiya mulaifa idanu yana mai murmushi, ita kuma mulaifa in banda kuka babu abunda takeyi awannan lokaci a sannan jamma'ar dake wajen suka tabbatar da cewa akwai soyaya tsakanin imnal da gimbiya Mulaifa. Kafin ajima bayan imnal yayi kaca kaca da jini, komin rashin imanin mutum idan yaga yadda akewa imnal dolene ya tausaya mishi, lokacin da Mulaifa taga azabar da akewa imnal ta wuce ta hankali sai ta mike zumbur ta ruga izuwa gidan sarauta kash!! inda gimbiya Mulaifa tasan muhimmancin zamanta awajen da bazata tashiba domin kallon fuskarta da imnal keyi shi ya hana shi jin zafin azaban da akeyi mishi, aiko tana shigewa gidan sarauta imnal yaji tamkar 50 TASKARNOVELS.COM.NG numfashinsa zai dauke sbd azaba amma saboda juriya da jarumtaka saida imnal ya shafe sa'a uku acikin wannan hali sannan ya suma, duk abinda ke faruwa sarki yaki hibru na tsaye a gefe yana kallo yana murmushi tamkar zuciyar sa bata sosuwa akan abinda ke faruwa, a badine zuciyar hibru a tafasa take kamar zata kone saboda takaicin da bakin cikin ganin yadda sarki ya rufe Ido yake horar da dansa, babban takaicin dake damunshi shine yasha bakar wahala awajen taimakon sarki maharaz harma ya kusa rasa ranshi a lokacin da sarki maharaz yake neman haihuwa ruwa ajallo yau gashi sarki bai damu danashi danba. hibru ya tambayi kanshi wai menene amfanin biyayyar dana kewa sarki, akan wani dalili zan cigaba dayin bauta ga Wanda baisan halacci ba, na kubutar da rayuwar yar shi amma shi gashi yana so ya salwantar da dana hakika lokaci yayi dazan daina wannan bauta a yayin da muka bar gida don tafiya wannan gagarumin yakin, adaidai wannan lokacin da sadauki hibru yazo nan azancensa imnal ya suma saboda azabar da'ake masa. Koda kartin biyu sukaga ya suma sai suka daina masa azaban suka sauko daga mumbarin a 51 TASKARNOVELS.COM.NG sannan ne sarki maharaz ya sake mikewa cikin farin ciki yace yanzu mun cika umarnin mai girma darbuza hankali ya kwanta dan haka da sallami kowa, shiko mai laifi za'a bar dakaru masu tsaronsa don karwani yakawo masa dauki lallai ahaka zai kwana uku batare daci ko shaba koda gama sai sarki ya juya da nufin ya shiga gidan sarauta kawai saiya hada idanu da sarki yaki hibru nan take maharaz yaji zuciyar shi ta buga da karfi, bakomai ne haddasa haka ban face tunda sarki maharaz suke tare da hibru bai taba ganin ya harare shiba sai ayau bayan shigar sarki maharaz cikin gidan sarauta fada ta watse babu kowa face and wadansu dakaru 300 wadda suke tsaron imnal. Shiko hibru saiya tafi can nesa kadan da filin fadan yayi sumfuda ya zauna inda yana iya hango imnal, nan fah hibru ya shiga sakar zuci wata zuciyar tace dashi ya afkawa wayennan dakarun dake tsaron imnal ya kashe su sannan ya kunce imnal ya tafi dashi in yaso subar kasar gabadayan su, wata zuciyar kuma sai tace dashi ai bai kamata yayi hakan ba tunda shima yayi imani da darbuza zaifi kyau ya bari sai antafi yaki sannan sukama gabansu haka dai hibru ya cigabada zancen zuci ya kulla wannan ya kunce 52 TASKARNOVELS.COM.NG wancan har yamma tayi likis bai gusa daga inda yake zaune ba kuma bai nemi abinci koh abin sha ba har dare ya raba hibru nanan zaune a inda yake bai gusa ba cikin halin damuwa da bakin ciki kuma koh alamar bacci a idanunsa babu a lokacin ne hibru yaji tsani sarki maharaz da darbuza domin baiga amfanin biyayyar dayake mishi ba. Adaidai wannan lokacin ne iska mai sanyi ta soma kadawa wadda ta zoma sanadin farfadowar imnal daga doguwar suman da yayi, imnal ya bude idanunsa da kyar yana gani dishi-dishi sai kawai yaji wata irin izababbiyar ishirwa nan fah ya fara kiran ruwa! ruwa!! tun yana fadi a hankali harya bude makokoron sa yana fadi da karfi koda hibru ya jiyo sautin muryar imnal yana kiran ruwa saiya mike zumbur a firgice ya lalubi sulkar sa ya yunkura da sauri da nufin ya ruga zuwa inda imnal yake kawai sai yaga matarsa wato marigayiya mahaifiyar imnal ta bayyana a gabansa cikin tsananin tsoro hibru ya fadi kasa ya kama ja da baya yana mai nunata da dan yatsa yana karkarwa. Koda ganin haka sai marigayiyar ta dube shi cikin murmushi tace kwantar da hankalin ka yakai sadaukin zamani kayi sani cewa niba matarka bace na kasance 53 TASKARNOVELS.COM.NG cikin jinsin aljanu sunana luzaira yar salbas, nazone gareka acikin suffar matarka domin nasamu damar hanaka abinda kake son yi domin idan ka kaiwa imnal agaji wannan lokaci tamkar ka ruguza cigaban rayuwar sane, cikin rashin yadda hibru ya dubi luzaira yace ta yaya zan yarda dake kuma akan wani dalili zaki min wannan taimako shin bakya ganin halin da dana yake ciki ne sakamon kishirwar dake addabarsa. Koda aljani luzaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace duk irin wahalar da imnal zaisha bazai mutu ba bincike ya tabbatar da cewa danka zai girma ya shahara a duniya nan gaba lallai ya zamo wajibi ka yarda Dani idan har kana son ka cika burinka na rayuwa inko kaki acikin bautar sarki maharaz zaka mutu, ina sanar dakai cewa a duniya darbuza bashida wani makiya wadda yawuce ubana sarki salbas mai mulkin birnin Shulai a kullum suna farautar juna Kuma wannen so yake ya kama dayan su a raye domin samun sinadarin da zasu cika burinsu, nazone sbd mu taimaki juna zan taimake ku kusamu yancin kanku daga sarki maharaz da aljani darbuza, ni kuma da taimakon kadai zan iya taimakawa mahaifina domin mu kama darbuza a raye sa'adda aljana 54 TASKARNOVELS.COM.NG luzaira taxo nan a zancen ta sai hibru ya sake rudewa kuma ya cika da mamaki yace yanzu kina nufin darbuzan da muke bautawa aljani ne kamarki? Luzaira tace ko shakka babu tace ai dayawan ku bil'adama mu kuke bautawa sbd kuna ganin munayin abunda ku bazaku iyaba hibru yayi ajiyar zuciya yace to yanxu tayaya zan iya taimakonki ke kuma tayaya zaki iya taimakona? Aljana luzaira tayi murmushi tace har abada bazaka taba kubuta daga cikin bautawa sarki maharaz ba sai an karya wani asiri daya maka shidai wannan asiri anyi shine silin gashin kirjinka guda daya kuma an bunne shine a cikin wata tsohuwa rijiya gaba-dubu (1000) dake can karkashin wani kogi dake birnin sin, itadai wannan rijiya duk duniya babu mahalukin dazai iya shigarta sai ni da abbana mu kadai, tabbas zanje na tono wannan asiri amma sai idan kayi alkwarin cewa zaka hada karfi da karfe dakai da danka imnal ku dauko takobin saiful lujara da mashin galilul haras da kuma hular lamsara kun bani su a hanuna, ina tabbatar maka dacewa bincikena ya nuna min cewa sarki dujalu da sarki maharaz bazasu iya dauko wayennan 55 TASKARNOVELS.COM.NG makaman ba amma kaida imnal zaku iya, lokacin da aljana luzaira tazo nan a zancen ta sai hankalin hibru ya dugunzuma daga can saiya dago kai ya dubi luzaira yace wato de yanxu bangare ukune suke son mallakar wayan nan kayan yaki na #mazan jiya bangare na farko shine sarki dujalu sai sarki maharaz sai na uku kuma keda abban ki, abinda na fahimta shine idan muka samu nasarar dauko wadannan makamai nida dana muka damka miki zaki rikesu ne amfanin kanki ke kadai koko zaki kaiwa abban ki? Kuma tambaya ta biyu agareki itane shin kina nufin mai girma darbuza bai san da zuwanki ba, kuma baisan duk abun dake faruwa tsakanin mu? yayin da aljana luzaira taji wadannan tambayoyi saita bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace yakai sadaukin zamani kayi sani cewa duk wani boka da amsa sunan sa bashida wani burin da yuce ya mallaki wadannan makamai na Mazan JIYA, karshe kuma batun aljani darbuza shin yana gani koh yana jin mu bai tasoba sbd idan yanada ikon ganina da banxo ba domin bazai taba bari nayi hulda dakuba. Sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai sadauki hibru yayi shiru yana tinani kansa a 56 TASKARNOVELS.COM.NG sunkuwe sannan ya dubi can inda ke daure a sama yaga ya sake suma na biyu, sai takaici da bakin ciki yasake mamaye zuciyar sa cikin karfin hali ya dubi aljana luzaira yace ki tafi sai bayan mun fito daga wannan yaki ki dawo izuwa gareni kiji amsar dazan baki idan zakizo kijo min acikin tsakar dare, koda fadin haka sai ya mike tsaye ya kwashe shimfidar sa ya nufi hanyar dazata kaishi gidan shi ko sau daya bai sake waiwayowaba balle yaga halin da imnal ke ciki. Bayan tafiyan hibru sai aljana luzaira ta tashi sama taje daidan fuskar imnal ta hura mishi iska a bakin ta wadda tasa gashin kansa ya tarwatse yana kadawa acikin iska tamkar ana guguwa mai karfi take imnal ya farfado yana mai ajiyar numfashi aiko yana bude idanun shi sai yayi arba da luzaira ta kura masa idanu tana murmushi babban abun mamaki shine duk ciwon dayakeji ajikinsa ya gushe haka yunwa da ishirwa ma duk sun gushe batare da fargabar komai ba imnal ya dubi aljana luzaira yace wacece ke? kuma menene ya kawoki wajena? ina mai rokonki da kadakiyi kokarin fitar dani daga cikin wannan halin danake ciki. Koda jin haka sai aljana luzaira ta bushe da dariya ta tankwashe kafafunta tamkar tana 57 TASKARNOVELS.COM.NG zaune a kasa bisa buzu ta fiskanci imnal sosai sannan tace yakai jarumin gobe kayi sani cewa lbrn yana tsawo amma idan kanaso kasan ni wacece ka tambayi abbanka bayan ka kubuta ka tambayeshi lallai ni mai amfani ne ga cigabar rayuwar Ku ina mai yimaka sallama yakai jarumin gobe sai gani na biyu in mun sake saduwa, gama fadin hakan keda wuya sai aljana luzaira ta bace bat kaman bata wanzuwaba awajen. Bayan Kwanaki uku fadar sarki maharaz ta cika ta batse bakomai ne ya haddasa haka ba face ayau ne za'a dugunzuma bakidaya dakarun birnin dana sauran kasashe makwabta wadanda aka gayyato saboda yin gagarumar tafiya izuwa kogin bahar sufiya don dauko takobin Saiful lujara saboda yawan jama'ah da kyar sadauki hibru ya kutsa ta cikin jama'ah ya isa inda aka daure imnal da zuwa sai ya iske imnal lafiya kalau acikin hayyacin sa, kuma babu yunwa ko ishi atare dashi cikin hanzari hibru ya hau kan wannan dogon mumbari ya kunce igiyar data daure hannayen imnal sannan ya sabo shi a kafada ya sauko kasa, gabadaya dandazon jama'ar dake wajen suka zubawa hibru idanu duk inda yabi sai kaga ana darewa ana bashi 58 TASKARNOVELS.COM.NG hanya ana masa jinjina da kirari domin ansan yaune rana irin tasa wato ranan dazai jogaranci rundunar mayaka izuwa yaki, dayawa daga cikin mutanen garin sunyi bakin cikin hukuncin da aka yankewa imnal dan hibru kuma sun san cewa imnal gwarzon mayaki ne wanda ake takama dashi yanzu gashi raunata shi a lokacinkirari daza tafi yaki a lokacin da akewa hibru da dansa kirari ne sarki maharaz da yar sa suka fito daga gidan sarauta, nan fah kallo ya koma kansu kowa ya zuba musu ido cikin matukar mamaki bakomai ne ya haddasa mamakin ba sai ganin irin shigar da sarki maharaz yayi dakuma irin wacce mulaifa tayi dukansu sun sanya jajayen sulke sun rataye takuba a bayansu komai na jikin su jane hatta dawakansu kowa yasan sarki da mulaifa basu kasance mayaka ba amma ansan cewa sarki maharaz kasurgumin matsafi ne, lokacin da hibru ya isa inda dokin sa yake saiya zaunar da imnal a kasa ya jingina bayansa a jikin gini ya bude wata jaka ya fiddo da garin magani ya mika masa sannan yace karbi wannan ka shanye ya kai dana domin raunukan sudaina maka zogi, imnal ya dubi hibru cikin murmushi yace ya abbana ai babu inda yake min ciwo a jikina 59 TASKARNOVELS.COM.NG kuma ko kadan bana jin kishirwa da yunwa koda jin haka sai hibru ya dubi imnal cikin mamaki yace menene ya kawo maka agaji a tsakanin dare uku zuwa wayewar gari? Imnal yace wata aljana ce mai suffa wadda kasha kwatantamin data mahaifiyata kuma tazomin a cikin suffar mutane ba aljanu ba tace a wajen ka zan samu labarin ta wacece wannar aljana ya abbana? Hibru yayi ajiyar zuciya yace kabar wannan magana tukunna har sai bayan kasamu lafiya gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaji an busa algeta alamar sarki ya tsaya a gaban jama'ah zaiyi bayani da hanzari hibru ya mike tsaye imnal ya riko hannun hibru yace shin gimbiya mulaifa ma tafito kodajin wannan sai hibru ya dubi imnal a fusace yace na rabaka da gimbiya mulaifa amma ka ki to kasani cewa idan ka kara min maganar ta ko kuma kanuna min kana kaunar ta zamu raba hanya yayin imnal yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla ya dubi hibru yace ka gafarceni yakai abbana naimaka alkawari daga yau bazan sake maka magar gimbiya ba kuma bazan sake nuna kauna agareta ba. 60 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin farin ciki hibru ya sumbaci goshin imnal yace ubangijin daya halicci darbuza ya albarkace ka gama fadin haka keda wuya ya nufi inda karagar sarki take har saida yaje dab da sarki ya tsaya sarki ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa a lokacin da filin fadar yayi tsit tamkar babu mai rai a wurin sannan yayi gyaran murya yace yaku jama'ar birnin darul mahabur tare da jama'ar sauran kasashe makwabta a wannan nahiya tamu ina mai yiwa kowa barka dazuwa fadata kuma ina gdy dakuka amsa gaiyatata domin nuna kishin kasar Ku dakuma dukiyar ku data jama'ar ku Kamar yadda kuka sani cewa gagarumar masifa da bala'i na tunkarar mu idan bamu fita wannan yaki ba ina mai kira agaremu damu jajirce iya karfin mu dan ganin munje mun riski babban abokin gabar mu a can tekun bahar sufiya domin hanashi dauko takobin saiful lujara a can ne zamu yake shi don tserar da rayuwar mu da jama'ar mu kafin yasami nasarar mallakan kayan yakin mazan jiya kamar yadda kuke gani a yanzu nida yata munyi gagarumar shigar yaki alhali bamu kasance mayaka ba ko sadaukai kuyi sani cewa ayau munfito ne da dukkan karfin sihirin mu don tunkarar masafi dujalu a 61 TASKARNOVELS.COM.NG halin yanzu na baiwa yata mulaifa dukkan sihirina na tsafi guda dari tara da casa'in da Tara(999) na cikon dubun ne ban bata ba SBD wani dalili mai karfi na bata wadannan sirruka ne sbd ta taimaka min awannan yakin domin abokan gabanmu yawansu ya wuce misali ina mai sanar daku cewa yanzu haka sarki dujalu tareda miliyoyin dakarunsa sunyi nisa a tafiyar su ta zuwa tekun bahar sufiya kuma suna amfani da alkaluman tsafi wajen gajarce nisan tafiya muma zamuyi amfani da namu sihirin don gajarce nisan tafiyan yanzu nabaiwa dukkan ninku sa'a daya daku gama kimtsawa domin sa'a dayar na cika hadiman zasu iso daga karshe ina mai kira ga sarki yaki na hibru bn imlas dayazo yanzu ya sameni a cikin dakin gani domin muyi tattaunawa na musamma akan yadda yaka mata mu bullo wa wannan yaki koda sarki maharaz maharaz yazo nan a zancen sa sai filin fadar nan ya rude da sowa. Nan de sarki maharaz ya kama hannun gimbiya mulaifa suka wuce izuwa cikin dakin gani shiko sadauki hibru saida ya koma wajen imnal ya sanar dashi cewa zaije wajen sarki su gana.. 62 TASKARNOVELS.COM.NG Kuyi haƙuri kwana biyu kun jini shiru ko, wallaahi laifin Hadejawa ne dan kawai munje bakunta garinsu sai bari dai nayi shiru da bakina Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part E Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey 63 TASKARNOVELS.COM.NG Lokaci da hibru ya shiga dakin gani sai ya cika da tsananin mamaki domin sarki Maharaz kawai ya gani da gimbiya Mulaifa babu sauran yan majalisa, kuma maimakon yaga sarki akan kujerar daya saba zama akai sai yaganshi a kasa bama akan kujara ba, ita Mulaifa a dab dashi, koda hibru ya hada idanu da sarki sai yaga idanunsa acike suke da kwalla, al'amarin da yayi matukar girgiza hibru kenan, ya karasa gurin su sarki Maharaz jikinsa a sanyaye shima saiya zauna a kasa suka fuskanci juna, maganar farko da ta fito daga bakin sarki Maharaz itace yaya jikin Dana imnal? Kodajin wannan tambaya sai ran hibru ya baci bai san sa'adda ya dubi sarki a fusace ba yace ya shugabana kayi magana akan abun dayake gaban mu amma ba batun imnal ba, Yace domin ina ganin bashida wani amfani a wannan yakin da zamu je, mu barshi anan gida saboda yayi jinyar jikinsa. Koda gama fadan haka sai Hibru yaga hawaye ya zubo daga cikin idanun sarki Maharaz cikin razani Hibru yace ka gafarceni yakai shugabana idan har wannan furuci nawa ya kona maka rai. 64 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin haka sai sarki Maharaz ya tsam daga inda gimbiya Mulaifa ke zaune sannan ya dawo dab da Hibru ya dafa kafadunsa suka kurawa juna ido sannan yace yakai babban aminina kuma abokina, ayau ina mai neman gafara agareka duk abin dakaga nayi maka ko nayi ma danka ba'a kan kiyayya bane sai domin soyayya da kuma bin umarnin mai girma darbuza dana marigayi sarki hubaru, a halin yanzu baka kaunata acikin zuciyar ka, yakai abokina kayi tinani zuwa shekarun baya da suka gabata tun sa'adda muna yara kanana kawo izuwa girman mu da yadda akayi nazamo sarkin birnin nan da kuma yadda akayi kazamo sarkin yakina, lallai ayau ne zan fada maka wani sirri daban taba gaya maka shiba, amma sai bayan ka bawa Mulaifa labarin rayuwar mu ta baya da yadda akayi na auri mahaifiyarta, da kuma yadda na shiga tashin hankali bisa rashin samun haihuwa. Lokacin da sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai idanun Hibru suka cika sharkaf da hawaye ya dubi Mulaifa cikin tsananin tausayi yace yake 'yarmu ki saurara da kyau kiji wannan labari mai dauke da dimbin abun tausayi da ban alajabi, kuma kisan irin dangartakar dake tsakani na da mahaifinki. 65 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin haka sai Mulaifa ta tattara hankalinta waje daya ta kurawa Hibru idanu. Shi kuma saiya shiga bata labari kamar haka "A wasu shekarun baya da suka gabata zamanin da sarki Ruzba ke mulki a wannan birni Darul Mahabur, nida mahaifinki mun kasance fadawan sarki ruzba wadanda aikin mu kawai tsaron lafiyar sarki, duk inda sarki zaije muna tare dashi kuma ko kuda bama bari ya sauka a jikinsa, mahaifin sarki ya kasance kasurgumin matsafi dan haka ya gaji tsafi kuma ya shahara, bisa wannan dama daya samune sarki ya zabe shi acikin dakaru masu tsaron lafiyar sa, niko mahaifina shine sarkin yaki birnin Darul Mahabur, a wannan lokaci tsufa ya riske shi har yakai baya iya fita yaƙi, awannan lokaci ban wuce shekaru sha biyar ba don haka ni nake wakiltar mahaifina a yakuna, sau uku muna tseratar da rayuwar sarki ruzba a lokacin da wani babban abokin gabarsa yake kawo masa hari don ya halaka shi, hari na farko a wani yammaci ne da sarki ruzba ya fita rangadi izuwa bayan gari inda muka shiga wani daji da ake kira Furuz, a rayuwar sarki ruzba babu abunda yake sha'awa kamar yin suu acikin kogi kuma dakan shi yakan shiga kogi yayi kamun kifi. 66 TASKARNOVELS.COM.NG Acikin dajin Furuz akwai wani babban kogi da ake kira bahar zur, shidai wannan kogi yana da girman gaske da muggan halittun ruwa a cikin sa, lokacin da mukazo zamu gifta ta gaban kogin tare da tawagar mu, sai sarki ruzba yace a tsaya a bakin kogin. Kodajin haka sai hankalin dakarun mu ya dugunzuma domin sun san halin sarki zai iya cewa sai an shiga cikin kogin yayi suuu. Nida maharaz ne kawai hankulanmu basu tashiba domin mun yarda da kanmu, kawai sai sarki ya dubeni ya dubi maharaz yace inaso na shiga cikin kogin nan nayi suuu. Don haka sai Ku biyoni ciki domin nasan cewa Ku kadai ne zaku iya biyoni. Nan take sarki ya sauko daga kan dokin sa ya dauki fatsarsa ya fada cikin kogi, cikin sauri nida maharaz muka bishi. A duk dakika biyar sai Maharaz ya dubi hannunsa domin ajiki yake ganin abinda ke karkashin kogin, da zarar yaga wani mugun abu ya tafo inda sarki yake saiya sanar dani sai nayi nitso a kasa na tarar da abun komai hazarinsa na kashe shi, acikin abinda bai kai rabin sa'a ba na kashe manyan kadodi biyar saida sarki ruzba ya shafe sa'a guda amma ko 67 TASKARNOVELS.COM.NG kifi daya bai kama ba, har ya hakuri da nufin ya daina ya fita da cikin kogin sai yaji fatsar sa tayi nauyi matuka ta yadda bazai iya dago taba, cikin mamaki ya dubi Maharaz yace yakai boka dan boka wai shin wani irin kifine na kamo mai girma da nauyi da har na kasa dago shi sama? Maharaz ya dubi tafin hanunsa yaga babu komai acikin fatsar cikin kaduwa da zaro idanu maharaz ya dubi sarki yace nikam banga komai acikin fatsar nan ba, tabbas muna cikin tashin hankali, duk yadda akayi wani abune mai mugun sihiri ya shiga fatsar ka, kafin ni koh sarki ruzba muce wani abu sai mukaga an fisgi sarki ruzba anyi kasa dashi izuwa karkashin kogin, ba shiri muma mukayi nitso izuwa karshin kogin, kawai sai mukayi arba dawani wani katon mutum ya shake sarki ruzba da hannu biyu har sarki ya fara kakarin mutuwa, cikin zafin nama na kafa hannayen wannan maridi na fara kokarin banbaresu daga wuyan sarki, nan kwanjin maridin ya kumbura idanun sarki ruzba sun kumbura ga kuma rashin numfashi shima Maharaz yana kokarin kashe maridin da karfin tsafi, amma duk abinda ya watsa mishi basa tasiri, kawai sai maridin ya juya baya ya gabzawa Maharaz naushi a fuska 68 TASKARNOVELS.COM.NG take Maharaz ya sulela sumamme ya tafi izuwa karkashin ruwa. Al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na tattara karfina gabadaya na gabzawa maridin naushi a kunnensa na hagu, sbd karfin naushin saida jini yayi tsartuwa ta kunnensa na hagu, ba shiri ya saki wuyan sarki ya kwarara ihu cikin zafin nama na kamo sarki ruzba sannan nayi kasa na kamo Maharaz sannan nayiyo sama, kafin maridin ya dawo hayyacinsa tuni na fito dasu bakin kogin muka zube wanwar a gabar kogin duk mu ukun muna cikin mugun hali, ni ina numfashi sama sama Sarki da Maharaz kuwa duk a sume suke, cikin gaggawa aka shiga yi musu fifita. Koda na mike tsaye sai naga wannan basamuden katon yayi fitar burgu tamkar an chillo shi daga cikin baka, take ya dira akan turba ya tsaya kyam kawai yana murmushi, har asannan jini na diga daga kunnensa, koda sauran dakaru sukayi arba dashi sai suka razana suka dinga fantamawa cikin daji, mutumin ya dubeni ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda amsa kuwarta ya cika dajin, daga can sai murtuke fuska cikin kakkausar murya yace kai 69 TASKARNOVELS.COM.NG yaro kayi kuskure da kake zaton cewa zaka kare sarki ruzba, tabbas sai nayiwa sarki ruzba kisan wulakanci a gabanka kuma kaima sai nayi filla filla da sassan jikinka.. Kodajin wannan batu sai zuciyata ta kekashe gabarin tsoro na dubeshi a fusace nace karyarka tasha karya yakai wannan azzalumi, kai waye dakake tinanin zakayi mana kisan gilla. Maridin ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan yace sunana Gilzam sadaukin sadaukai na maridan duniya, musamman sarki darbuza na birnin kailus ya dauko hayata domin na kashe sarki Hubru ayau, bisa yarjejeniya aduk kwanaki bakwai zai dinga bamu mutum dari nida iyalina muna cinyewa, domin naman mutane ne abincin mu, babu wani bala'i dazai hanani kashe sarki hubru ayanzu, idan kuma kuna gani zaku iya toh ku jaraba. Kafin na bude baki nace wani abu tuni gilzam ya zare wadansu zabga zabgan takubba guda biyu ya durfafo mu, girman kowace takobi ya wuce misali, nauyin ta kuwa saidai karti ashirin su dauka, dama tuni jikin sarki hubru dana Maharaz ya fara karkarwa sbd tsananin razanar 70 TASKARNOVELS.COM.NG da sukayi bisa ganin gilzam da kalamansa, amma sbd tsabar tsoro sun kasa mikewa ma su gudu. Cikin matukar karfin hali na zare tawa takobin na tunkari gilzam duk dayake ni kaina nasani gilzam yafi karfina nesa ba kusaba amma saina tari aradu daka... Gilzam ya nufo kaina gadam gadam nima na nufeshi acikin dakewar zuciya, takun sawun gilzam tamkar na toron giwa ne amma hakan batasa na razana ba, koda muka hadu ya kawo min wawan sara da takuba biyu da nufin ya fille min kai da kafafu saina goce da dukkan zafin nama na, takobin farko saita samu wata bishiyar dibino mai tsawo take bishiyar ta rabe gida biyu ta ratattake akasa, takobi ta biyu kuwa sai ta karci kasa, nan take ta haifar da girgizar kasa da zabtarewar ta, koda ganin faruwa wannan alamari sai hankalina ya dugunzuma na tabbatar dacewa yaufa na gamu da gamona. Sarki Hubaru da Maharaz kuwa sai suka sake tsurewa domin sun gama saduda sun san mutuwa tazo, niko danaga haka ban karaya ba sai na dada durfafan gilzam, shi kansa gilzam yayi mamaki dan bai taba haduwa da mutumin dabai taba razana akan shiba sai ni, abinda yafi 71 TASKARNOVELS.COM.NG daure mashi kaima shine na kasance yaro mai kuruciwa dan shekaru goma sha, cikin matukar fusata gilzam ya tasomin da dukkan karfin sa yana mai kawomin sara da suka da muggan makaman sa, nikuma ina gocewa amma ko kadan na gagara maida martani saboda karfin harinsa da zafin namansa ya ninka nawa, kaini kaina nayi mamakin yadda ma nake gocewa harinsa nan gilzam ya tashi hankalin dajin gabadaya ya haddasa kamawar wuta da girgixar kasa. Sai da muka shafe sa'a guda cif nida gilzam muna fafatawa shi baisami nasarar hallakani ba balle ya koma Kansu sarki hubru. Bayan ansamu sa'a gudan ne naji na fara gajiya, shiko Gilzam kamar a lokacin nema ya fara gumurzun, alamarin daya dugunzuma hankalina kenan na tabbatar dacewa saura kiris tawa ta kare. kwatsam! sai muka jiyo kururuwan mazaje daga bayan mu cikin sauri muka waiga sai naga ashe dakarun da muka fito rangadi dasune sukaje suna neman daukin sauran dakarun darul mahabur, sama da mutum miliyan biyu ne suka durfafo mu suna ihu da karaji, karar sukuwar dawakan suma kawai ta isa ta razana mutum ya dauka yakin duniya akeyi. 72 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Gilzam ya hango wannan runduna ta durfafo shi sai yayi murmushi ya ruga garesu, tun gabanin su riske shi. Kaico!! yayin da Gilzam ya ratsa ta cikin dakarun saiya dinga zubar dasu tamkar yana shara, sai dai kaga takobinsa na datsa mutane tana raba dawakansu gida biyu, nanfa ya bude kasuwar daukar rai sai hangowa nayi jini na tsartuwa yana malala akasa, kafin na ankara tini gilzam ya kashe sama da dakaru miliyan daya da rabi da dawakansu. Ko da na hango wannan barna saina fusata ainun na falfala da matsanacin gudu Irin wadda bantaba yin irinsa ba, domin har ji nake kamar zantashi sama, na nufi inda gilzam yake wannan barna, yayin daya rage saura taku uku na isa gareshi sai na daka tsalle sama na sauka akan wuyansa, kafin yasa takobinsa ya kadoni tuni na soka masa wuka a kunnensa na hagu take wukar ta lume acikin kunnensa ya bullo ta daya kunnen. Gilzam ya

Chapter 3 of 13