Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yasa kake kuka a yanzu, alhalin kaine ya kamata ka karfafi zukatanmu bisa wannan tafiya da dana zai yi. Sa'ad da Sulbaini ya ji wannan tambaya sai ya kama hannu Salimat ya jaya gefe guda inda babu wanda zai ji abinda zasu tattauna da ita, ya shiga yo mata wadansu bayanai, tunda ya fara bayanan Salimat ta fara kuka, aiko yana gamawa sai ta rushe da matsanancin kuka, kuma ta rungumeshi tana mai kankameshi a jikinta 270 TASKARNOVELS.COM.NG kamar wani zai kwace mata shi, da kyar Sulbaini ya cire jikinsa daga nata sannan ya taho gaba hantaru ya tsaya daf da shi har suna iya jin numfashin juna, Sulbaini yayi murmushi mai taushi ga Hantaru sannan ya ce ya kai namijin duniya kayi sani cewa nazo ne domin muyi bankwana, kuma nayi maka tuni bisa abinda na fada maka a baya idan baka manta ba, a ranar da kuka je gidana nayi maka gargadi akan kada ka kuskura Gimbiya Larziyya ta umarceka da yin abinda zai lalata alakar ka da jikita wata Salimat, bayan ka samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, idan ka kuskura ka aikata hakan tabbas zaka yi biyu babu a rayuwa, domin zaka rasa masoyanka kuma ka rasa daukakarka, har ya zamana cewa ka gwammace mutuwa da rayuwa, saboda haka ka kiyaye kuma kayi matukar nazari a duk lokacin da Gimbiya Larziyya ta zo maka da bukatarta. Lokacin da Hantaru ya ji wannan batu sai yayi murmushi yace kada ka damu ya shugabana, lallai zaka samenk mai kiyayewa bisa wannan shawara daka bani. Gama fadin haka keda wuya sai ga wani manzo yazo daga gidan sarki. Da zuwansa sai ya fadi 271 TASKARNOVELS.COM.NG gaban Shuraim ya ce ya shugabana sarki ne ya aikoni yace na sanar da kai cewa ana juran Hantaru a fada domin a sallamesu shida abokin tafiyarsa Rabbasu. Koda jin wannan batu sai Hantaru ayi wa mutanen gidan sallama karshe, ya kama doki ya hau ya tafi izuwa fada yana waugen su Salimat yana zubar da hawaye, suna zub da hawayen suma, masu daga masa hannu nayi haka dai har ya mace masu da gani. Lokacin da Hantaru ya isa fadar Sarki sai ya iske tuni Rabbasu na zaune a gefe daya cikin gagarumar shigar yaki yana muzurai tamkar zai ci babu, da zuwa sai Hantaru ya wuce gaban Sarki ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya koma gefe daya ya zauna shima, inda suka fuskanci juna shida Rabbasu. Koda suka hada ido sai Rabbasu ya daka wa Hantaru harara, wacce inda karamin jarumi yayi wa ita zai iya tsurewa ya kama gudawa, shi kuwa Hantaru sai yayi murmushi kawai ya kawar da kansa ga barin kallon Rabbasu. Ashe duk abinda ya faru sarki ya lura dan haka shima sai yayi murmushi ba tare da yace komai 272 TASKARNOVELS.COM.NG ba. Nan take sarki ya tura aka kira Gimbiya Larziyya ta zo ta zauna daf da sarki, a wannan lokaci fada ta cika taf da jama'a babu masaka tsinke face inda sarki da jam'arsa ke zaune. A wannan rana dai Gimbiya Larziyya ta ci ado na gaban kwatance irin wanda ba a taba ganinta da shi ba, kuma ta bar fuskarta a bude sabanin rufeta da take yiko gaishe. Wohoho! Lokacin da Gimbiya ta fito ta nufu inda karagar sarki ta ke tana yin tafiyar kasaita, sai ganadaya jama'ar dake fadar suka zuba mata idanu, kuma take suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta, da yawan jama'a basu san sa'adda yawu ya ka dalala da cikin bakinsu ba tamkar basu taba ganin gimbiya ba. Hatta Hantaru da Rabbasu ai da suka firgice suka bita da kallo, ko kifta ido basa yi, domin basu san cewa kyawunta ya wuce yadda duk suke zammani ba sai yau. Kai shi kanshi mahaifin nata binta yayi da kallo ya kama wasiwasi a zuciyarsa yana mai cewa anya kuwa wannan Larziyyata ce, yaya aka yi naga kyawunta ya zarce na kullum a yau? 273 TASKARNOVELS.COM.NG Abinda sarki bai sani ba shine tsananin kwalliyar data yi ne gami da tsaba adon da ta yi, suka kara mata kyau na ban al'ajabi, domin idan kyau ya hadu da kyau sai idanuwa su kasa banbance wanda yafi wani. Bayan Gimbiya Larziyya ta zauna kan wata kujera ta alfarma wacce ke kusa da karagar sarki, sai sarki yasa hannu a cikin aljihunsa ya dauko wani dan karamin madubi na tsafi ya ajiyeshi a tskiyar fadar, sannan yayi gyaran murya ya ce ya ku jama'ar birnin Darul Habur, kuyi sani cewa ayau ne masoyan yata Gimbiya Larziyya wato masu neman aurenta, zasu yi gagarumar tafiya dan tabbar da gasa ta karshe a tsakaninsu, domin fitar da zakaran da zai zama mijin Gimbiya, kowa ya sani wannan gasa b komai bace face tafiya zuwa dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Duk wanda ya dauko wannan takobi ya zo da ita tsakanin Hantaru da Rabbasu shine mijin ya ta. Koda sarki yazo nan a zancensa sai fada ta rude da shewa, sai da sarki ya daga hannu aka yi tsit sannan ya dubi Hantaru da Rabbasu ya ce kunga wancan madubin tsafin dana ajiye a tsakiyar 274 TASKARNOVELS.COM.NG fada? Shine alkalin wannan gasa da xaku tafi, duk abinda zai faru a cikin wannan tafiya zamu gani a cikin wancan madubin saboda akwai dokoki da zamu shimfida maku a yayin wannan tafiya. Duk wanda ya karya doka daya daga cikin dokokin koda ya dauko takobin Saiful Lujara to ba zai auri Gimbiya ba, doka ta farko ita ce; Babu yaki a tsakaninku, wato ba a yarda dayanku ya cutar da dan uwansa ba. Doka ta biyu ba a yarda dayanku ya taimaki abokin tafiyarsa ba, abinda ake so shine kowa karfin damtsensa dana sihirinsa ya cece shi. Doka ta uku wacce ita ce ta karshe wanda duk ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, to kada ya tsaya ko ina face anan fadarmu. Da fatan zaku kiyaye wannan dokoki domin tabbatar da burinku, da wannan furuci nake maku bankwana da fatan samun nasara ga dukkan mai sa'a a cikinku. Koda gama wannan jawabi sai sarkk yasa aka kosassun dawakai kuma ingarmu guda biyu baki da fari, kowanne da guzuri akansa, ya dubi Hantaru da Rabbasu yace kowanne ya zabi wanda yake so. 275 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin hanzari Rabbasu ya tashi tsaye yaje ya kama bakin dokin ya haye, shi kuwa Hantaru sai ya kama farin dokin ya haye. Nan take suka jera suna tafiya tamkar abokai suka nufi hanyar fita gari, jama'a na biye da su duu... Kamar kiyasai. Sai da aka raka su Hantaru har izuwa iyakar gari sannan aka tsaitsaya ana kallonsu suka kutsa kai cikin daji. Tun ana kallonsu har sai da suka kule suka bace bat! Hantaru da Rabbasu suka cigaba da tafiyya a jere suna ketawa ta cikin kwazazzabai da duwatsu, sai da suka yi tafiyyar sa'a shida cur dayansu bai ce d dan uwansa kala ba, sannan suka iso bakin wata korama. Anan ne fa dawakansu suka yi turjiya suka kama shan ruwa, saboda daman sun debo rana kuma sun gaji, su kansu su hantarun sun gaji kuma suna jin yunwa da kishin ruwa, amman saboda dakakkiyar zuciya irin ta mazan kwarai sai suka basar saboda kada suka cewa dayansu ya gaza. Lokacin da dawakan nasu suka tsaya a bakin gabar koramar suka kama shan ruwa, sai Hantaru da Rabbasu suka dubi juna, bisa ga 276 TASKARNOVELS.COM.NG mamaki sai suka yi wa juna murmushi. Rabbasu yayi gyaran murya ya ce ya kai abokin gaba ina ganin cewa ya kamata mu yada zango anan, domin mu huta kuma dawakanmu ma su huta, dan na lura cewa akwai gajiya a tare da mu. Hantaru yace kwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau. Nan take duk su biyun sauka kayan su dake bisa dawakansu kowa ya kafa tantinsa, kuma suka bude jakar guzirinsu suka ci kuma suka sha. Bayan sun gama kimtsa cikin nasu ne sai kuma hira ta barke a tsakaninsu, inda Rabbasu ya dubi Hantaru yace ya kai bakon garinmu, kayi sani cewa ina da wata tambaya a gareka, wacce zan so ka bani amsarta bilhakki. Koda jin wannan batu sai Hantaru yayi murmushi sannan ya ce fadi duk irin tambayar dake bakinka ni kuma nayi alƙawarin zan baka amsa iyakar gaskiyata. Rabbasu yayi gyaran murya sannan ya ce ina son ka fada mani alakar dake tsakaninka da Salimat yar sarkin makera Shuraim, shin ita ce ta haifeka ko ba ita bace? 277 TASKARNOVELS.COM.NG Yayin da Hantaru yaji wannan tambaya sai ya cika da mamaki kuma yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai ya ce alakata da Salimat itace ta shayar d ni, amman ba ita ce ta haifeni ba. Koda jin Wannan batu sai idanun Rabbasu suka zazzaro, kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki, ihun nasa ne ya firgita kananun dabbobin dake cikin dajin da tsuntsaye suka kama tashi da guje-guje wasu suna sauya ramuka, nan take kwallar takaici ta cika idanun Rabbasu ya dubi Hantaru yace hakika nayi babban kuskure da banyi cikakken bincike akanka ba, tun a farkon zuwanka garin nan, inda nasan cewa kai ba jinin zuri'ar makera bane da bazanyi wannan gasa d kai ba, da tuni na kashe kaina na da huta da takaici. Cikin tsakanin mamaki Hantaru ya dubi Rabbasu yace kai kuwa sabida me yasa ka fadi haka? Rabbasu yace saboda bincike ya tabbatar da cewa babu wani dan zuri'ar makera da ya isa ya samu nasara a kaina, duk da cewa har a yanzu baka samu nasara a kaina ba, in tsoron faruwar 278 TASKARNOVELS.COM.NG hakan a nan gaba, tunda kai ba zuri'ar jinin makera bane. Koda jin haka sai Hantaru ya bushe da dariya sannan ya ce ai kuwa babu makawa sai abinda kake tsoron faruwarsa ya faru, ina mai tabbatar maka da cewa nine zan karbi kambun wannan gasa ta neman auren Gimbiya Larziyya. Rabbasu shima ya bushe da dariya yana mai cewa ai Shikenan, muje zuwa mahaukaci ya hau kura, zanga ta yadda zaka lashe wannan gasa. Koda gama fadar haka sai Rabbasu yayi shiru bai sake cewa komai ba, shim Hantaru haka har dai suka gama hutawarsu suka cigaba da tafiya. Daman tun kafin su baro birnin Darul Habur an baiwa kowannensu zanen taswirar hanyar da zata kaisu zuwa kogon nan na Mazabatul Darshal, dan haka suna tafe suna duba wannan taswirar, haka dai su Hantaru suka wanzu suna masu keta dazuzzuka dare da rana wani lokacin ma basa kakkauta tafiya sai dai su kunna wutar icce su haska wa kansu hanya, wani lokacin kuma idan duhu ya kai duhu sai su hakura su yada zango. 279 TASKARNOVELS.COM.NG Duk inda tsautsayi yasa suka hadu da yan fashi ko muggan dabbobin daji, tofa komai yawansu cikin dakiku kadan suke ratattakasu su bi ta kansu, su kuma wuce tamkar anyi sassabe a gona, kai bama mutane da dabbobi ba, komai shedancin aljani da taurin kansa, da zarar ya hango Hantaru da Rabbasu sai kawai kaga ya ratse ya nemi maboya, domin yasan karo da shiryayyun maza irin su babu sa'a. Sai da su Hantaru suka shafe kwana goma sha tara suna ratsa dazuzzuka iri-iri sannan suka iso dajin hayatul Maut. Shi dai wannan daji na hayatul Maut ya fita da ban da kowanne irin dazuzzuka da suka saba gani. Tun a farkon dajin suka sha jinin jikinsu suka gane cewa sun shigo cikin bala'i da masifa wacce basu da tabbacin fita daga cikinta sai abinda hali yayi. Komai na cikin dajin ba irin wanda ido ya saba gani bane, gaba daya bishiyoyin dajin siffar dodanni garesu, su kuwa duwatsu suffar muggan dabbobi garesu, a cikin koramai kuwa sai suka rinka ganin aljani nata nukkaya da nutso, kai hatta ciyayin dake dajin hira suke da junansu, har ma suna yi wa junansu rada da zarar sunga su Hantaru sun matso daf da su. 280 TASKARNOVELS.COM.NG Koda ganin waɗannan abubuwa na ban tsoro, sai Hantaru da Rabbasu suka zare takubbansu suka ci gabada tafiya suna masu kallon gabas da yamma, kudu da arewa cikin nutsuwa domin suka ta inda za a fara kawo masu hari. Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga wani aljani mai siffar guguwa ya taho a sama yanata kyakyata masu mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu, hakika komai taurin kan mutum idan yaji wannan dariya dole ne ya razana, balle kuma idan yayi arba da aljanin wanda saboda matukar muninsa idan ka kalleshi zaka iya kama kumallo. Aljanin ya tsaya a cikin iska yana jale-jale kamar idan aka hureshi da iskar baki zai iya tarwatsewa, kawai sai ya dubi su Hantaru ya daka masu tsawa ya ce ku kanana kwari, wane tsautsayi ne yasa kuka siyar da rayukanku ku ka shigo wannan daji na hayatul Maut, shin baku da tarihin wannan daji ne? To ku sani cewa fiye da shekaru dubu duk halitar data shigo wannan daji ta ratso ta nan sunanta gawa, saboda mu tabbatar da tsaro ga takobin daraja ta Saiful Lujara. 281 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da aljanin ya zo nan a zancensa sai Hantaru ya tari numfashinsa ya ce da shi Kai tsohon maketaci la'ananne, yau masu karya tasirinku sun zo, mukam mun shigo cikin wannan daji a raye cikin koshin lafiya, kuma sai mun fita a raye bayan mun dauke abinda kuka dade kuna gadi, wato takobin Saiful Lujara. Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni Aljanin ya gabza masa wawan naushi a fuska, nan take hantaru ya sulale kasa sumamme, ya fado daga bisa dokinsa wata irin farar kumfa na fita daga bakinsa. Koda faruwar haka sai aljanin ya dubi Rabbasu ya daka masa tsawa ya ce Kai kuma maza ka kashe kanka ko kuma nayi maka abinda nayi wa dan uwanka. Rabbasu ya maida wa aljanin nan martanin tsawa ya ce karyarka ta sha karya dan haka ga maza nan bisa kanka, kawai sai Rabbasu ya tashi sama kamar tsuntsu ya bar bisa dokinsa ya afka wa aljanin yana mai kai mashi sara da suka cikin matukar zafin nama. Shikuwa aljanin sai yayi amfani da dan yatsansa guda daya jal a matsayin tasa takobin yana mai kare saran gami da mayar da martani, idan 282 TASKARNOVELS.COM.NG takobin Rabbasu ta hadu da dan yatsan aljanin nan sai kaga tartsatsin wuta na tashi, wata irin walkiya ta cika dajin baki daya, sai da suka jima a sama cikin iska suna wannan gumurzu dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin daya ba, al'amarin daya fusata aljanin kenan ya harzuka ainun, kawai sai aljanin ya rikide ya koma dan siriri kamar zare ya nannade jikin Rabbasu tun daga kafafunsa har zuwa kansa kawai sai ya shiga matseshi. Nan fa Rabbasu ya ji kamar za a rugurguza kasusuwan jikinsa gabadaya har bai san sa'ad da ya kurma uban ihu ba, sannan ya kama kumbura tamkar iska ake hura masa, nan fa shima aljanin ya fara rusa ihu domin shima ji yayi kamar Rabbasu zai tsinkashi gida biyu. Ba shiri aljanin ya rabu da jikin Rabbasu ya cilla izuwa can kololuwar sama tamkar daga cikin baka aka harba shi. Rabbasu ya daga kansa sama take ya zama haske ya bi aljanin da gudun tsiya, amman sai yaga ya kasa cimma wannan aljani domin karfin gudun aljanin yafi na tauraruwa mai jela. 283 TASKARNOVELS.COM.NG Ba zato ba tsammani sai aljanin ya sake rikidewa ya zamo wata irin masifaffiyar wuta mai tsananin zafi, ya juyo da baya suka kasa tsere da wannan haske, nan fa Rabbasu ya ji kamar daga cikin tafasasshen mai aka tsunduma shi, duk da cewa kuwa wutar ba ta taba jikinsa ba. Ba shiri Rabbasu shima ya rikide ya zama kankara, koda wutar da kankarar suka hadu sai duk su biyun suka rinka kururuwa wani irin sauti mara dadin ji ya dinga tashi, tamkar ana diga ruwa a cikin tafasasshen mai. Ba shiri duk su biyun suka rikito kasa kowa ya juye izuwa ainihin siffarsa. A daidai wannan lokaci ne aljanin ya shammaci Rabbasu ya narka masa dundu a gadon baya, take Rabbasu yaji tamkar kashin bayansa ya karye, kawai sai jiyayi yana kumallon wahala, shi kansa kumallon ji yayi kamar yan hanjin cikinsa zasu fito ta baki. Nan take ya baje a kasa sumamme, shi kuwa aljanin sai ya sauko kasa ya dira bisa turba yana mai kyakyata dariyar murna. Ba zato ba tsammani sai kawai yaji takobi ta tsargeshi gida biyu, tamkar yadda ake sa zabira a keta takarda, sai ga gangar jikin aljanin nan ta rabe gida biyu, ko wanne bangare ya fadi gefe daya. Ba wani bane yayi wannan aiki sai sadauki 284 TASKARNOVELS.COM.NG Hantaru, shi kansa sai kawai ya tsaya yana kallon takobin tasa yana mamakin yadda aka yi tayi wannan namijin aikin. Aljanin nan dai ko shurawa bai kara yi ba, Hantaru ya dubi Rabbasu wanda ke kwance magashiyan ko motsawa baya yi sai kawai ya kawar da kansa ya kama dokinsa ya haye ya cigaba da tafiya, yana mai tunanin cewa shikenan ya rabu da abokin tafiyarsa har abada, domin bai ga alamun zai iya rayuwa ba. Sai da Hantaru yayi tafiyar sa'a uku cur a cikin dajin hayatul Maut bai kara haduwa da wani mugun abu ba, kuma yana tafe yana duba taswirar hanya izuwa kogon Mazabatul Darshal. Kawai sai Hantaru yaga hanya ta bi dashi ta cikin kogon dutse mai tsananin tsawo da ba a iya hango karshensa, sannan da ya leka cikin kogon sai yaga mugun duhu ne da shi baya iya ganin komai, bisa dole hantaru ya sakko daga bisa dokinsa ya nemi icce ya kunna masa wuta, sannan ya sake hawa dokin nasa ya kunna kai cikin wannan kogo ba tare da fargabar komai ba tamkar yana shiga cikin gidansa. Shigarsa cikin kogon keda wuya sai yaga babu komai a ciki face kasusuwan bil'adama rututu a 285 TASKARNOVELS.COM.NG ko'ina, ta kai dokinsa yake bi yana takawa suna ruburbushewa, abinda ya daure wa Hantaru kai shine wanne irin mugun abu ne a cikin wannan kogo wanda ya hallaka miliyoyin rayukan bil'adama haka, ga dukkan alamu abun ya dade yana barna a cikin wannan kogo tsawon shekara guda shekaru, domin kasusuwan bil'adama dake wajen da yawansu sun gama bushewa, dan da zarar an takeau sai dai kaga suna ruburbushewa suna zama gari. Lokacin da Hantaru ya iso karshen kogon dutsen sai yaga a rufe yake ruf babu wata hanya ta fita, nan take ya fito da taswirarsa ya duba, kawai sai yaga hoton wata ƙatuwar rijiya a cikin kogon, kuma anyi nuni da cewa rijiyarce kan hanyar fita daga kogon, nan fa hantaru ya sakko daga kan dokiksa ya cigaba da haske haske da wutar iccen dake hannunsa, ai kuwa sai ya hango katuwar rijiya acan gefe daya koda ya hangota sai ya ruga da gudu izuwa inda rijiyar take, da zuwa wajen sai ya maida takobinsa a cikin kufenta kuma ya sakare wutar iccen a jikin bango, sannan yasa hannayensa biyu a bisa rijiyar da nufin budeta, nan fa Hantaru yaji kamar katon dutse yake son dauka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya kara 286 TASKARNOVELS.COM.NG hade gabadaya karfinsa waje guda ya cigaba da kokarin daga marfin rijiyar amman sai abu ya gagara, domin ko motsawa ma marfin ma baiyi ba. Nan da nan Hantaru ya hada gumi yay sharkaf bisa dole ya yi tagumi ya koma waje daya ya shiga tunanin dabarar da ya kamata ya yi, yana cikin wannan hali ne yaji takun sawu ana shigowa cikin kogon, Hantaru ya mike tsaye zumbur yana mai zare takobinsa, sannan kuma ya dauko iccen wuta domin yaga mai shigowa. Ba zato ba tsammani sai kawai yaga ashe abokin tafiyarsa ne Sadauki Rabbasu, nan take Hantaru yaji farin ciki ya shige shi duk da cewa Rabbasu babban abokin gabarsa ne, amman ai ko ba komai tafiyarsa cikin wannan daji mai ban tsoro bata da dadi, gwara dai ace su biyun ne, dan haka sai ya ji yana murna da Rabbasu ya tsira da rayuwarsa. Yayin da Rabbasu yayi arba d Hantaru sai ya murtuke fuska tamkar yaga bakin kumurci kawai sai ya wuce cikin kogon ya kama haske haske yana mai duba taswirar hannunsa. Nan take ya gane wannan rijiya yake nema wato hanyar fita dag kogon, yace koda na fuskanci 287 TASKARNOVELS.COM.NG haka sai na koma gefe guda na zauna na zura masa idanu. Lokacin da Rabbasu yaga rijiyar sai ya sagale iccen wutar a jikin garu kamar yadda nayi sannan ya mayar da takobinsa cikin kube. Rabbasu ya tsaya akan rijiyar sannan yasa hannayensa biyu yayi amfani da dukkan karfinsa domin ya dauke murfin rijiyar, nan fa jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi birdin burdin, kwanjinsa suka kumbura, da kyar da sidin goshi ya daga murfin rijiyar kadan, amman sai murfin rijiyar ya rinjayeshi kasa dan haka dole ya sake shi. A wannan lokacin ne na tabbar da cewa indai batun tsagwaron karfin damtse ne to Rabbasu ya fini, tunda ni na kasa daga murfin rijiyar. Abinda kawai nake gani zan iya fin Rabbasu shine juriyar wahala, naci da kuma Sa'a. Rabbasu ya jaraba janye murfin daga bisa rijiyar amman sai abu ya gagara domin har saida ya jike sharkaf da zufa kamar yadda na yi a dazu, bisa dole Rabbasu ya hakura ya koma gefe shima ya zauna, duk su biyun sai suka zuba wa rijiyar idanu suna tunanin abinda zai ficcesu. 288 TASKARNOVELS.COM.NG Kwatsam sai muka ji wani irin gurnani na fitowa daga cikin rijiyar, tunda Hantaru yazo duniya bai taba jin gurnani irin wannan ba mai matukar ban tsoro, sannu a hankali gurnanin ya rinka karuwa ba shiri suka mike tsaye cikin razani suka ji kamar su ruga wajen kogon amman sai suka yi ta maza suka tsaya dan suka ko mene ne wannan abu dake cikin rijiyar. Kawai sai sukaga an naushi murfin rijiyar daga cikinta, take marfin yayi sama kamar anyi wurgi da faifai, ya fada can gefe daya, wani shirgegen dodo ne ya fito daga cikin rijiyar ya dira a gabansu. Koda kafafunsa suka taka kasa, sai gaba daya kogon ya kamar girgiza kamar zai ruguje, ni da Rabbasu sai muka zama yan mini-mini a gaban dodon nan kamar an ajiye yan tsaki a gaba muzuru, Hantaru da Rabbasu suka daga kawunansu sama suna kallon dodon nan cikin tsananin kaduwa da tsantsar al'ajabi jikinsu na kyarma. Gabadaya jikin dodon a murde yake kuma gashi da taurin gaske kamar dutse, yana da wani dogon kaho guda daya a tsakiyar kansa tamkar na dabbar karakanda, jelarsa kuwa murtukekeya ce mai tsawon gaske kamar ta 289 TASKARNOVELS.COM.NG kada, faratan yan yatsunsa kuwa zako-zako masu tsini da kaifin tsiya, koda Hantaru ya dubi dodon nan da kyau sai ya jinjina kai ya ce wannan zai iya halaka dakaru Miliyan dubu a lokaci guda, hakika yau mun gamu da gamonmu, dan abune mawuyaci mu fita daga nan. Koda dodon yayi arba da su Hantaru sai ya daga kafarsa ya shallakesu ya koma bangaren kofar da suka shigo ya tare hanya. Nan fa hantaru da Rabbasu suka dubi juna gami da yin ajiyar zuciya, duk da cewar a dokar wannan tafiya tasu, babu taimako juna amman yanzu ya zama masu dole su hada hannu domin yakar wannan dodo. Bayan anyi kallon kallo tsakanin dodon da su hantaru sai kawai dodon ya wangame bakinsa mai kama da rijiya ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce ta kara furgitasu sannan yace ya ku wandannan kananan halittu, kuyi sani cewa yau kimanin shekara dubu kenan ina gadin wannan rijiya wacce ita ce hanyar da zaku bi domin ku shiga kogon Mazabatul Darshal, inda takobin daraja ta ke, duk mahalukin daya shigo wannan kogo walau mutum, aljan ko dabba to sai na zare masa ruhin numfashi, komai yawan 290 TASKARNOVELS.COM.NG ayarin dakaru muddin suka shigo to sunansu gawa, ku kuwa wanne tsautsayine ya shigo daku wannan daji, ko kuwa kuma kunzo ne domin daukar takobin daraja? Sa'ad da suka ji wannan tambaya sai Rabbasu yayi tsuru-tsuru ya kasa cewa komai, shi kuwa Hantaru sai yayi farat ya ce Ya kai wannan babbar halitta kayi sani cewa komai na duniya lokacine, tabbas ka yi sharafinka har tsawon shekaru dubu, to kayi sani cewa yanzu lokaci namu sharafin ne, a yau kuma a yanzu zamu halaka ka, sannan mu shiga cikin rijiyar nan mu wuce zuwa kogon Mazabatul Darshal mu dauko takobin Saiful Lujara. Koda Hantaru yazo nan a zancensa sai dodon ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, wacce ta haddasa girgizar kogon gabadaya ya kama tambal-tambal, daga can sai ya tsuke bakinsa ya dubi Hantaru da kyau yace ai sai na gwada akan san na kwarai, mu zuba ni da ku asan gwani. Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri, tuni dodon ya kai masu wani wawan mangari, cikin zafin namq suka sunkuya hannun dodon ya bugin kogon, sai dutsen ya fara zubowa kasa, 291 TASKARNOVELS.COM.NG al'amarin daya firgita su hantaru kenan suka fara amfani da karfin sihiri, domin su hallaka dodon amman si sihirin nasu ya ki aiki, nan fa suka kasa tsere da dodon yana kai masu duka, mangari da kuma taku da hannu da kafa, duk inda kafar dodon ya taka sai ya haifar da rami zururu wanda zurfinsa ya kai kamu arba'in, fadinsa kuwa yana kai kamu ashirin, nan fa Hantaru da Rabbasu suka kama tsalle-tsalle a haka dai suka samu daman naushin fuskar dodo, amman duk sa'adda suka naushe shi sai suji kamar dutse suka nausa domin hannunsu ma sagewa yake, kafin a jima Hantaru da Rabbasu sun fara gajiya da galabaita, shiko dodon ko alamar fara gajiya bai yi ba tamkar ma kara masu kuzari ake. Ana cikin haka ne dodon ya samu nasarar damkar wuyan Rabbasu da yan yatsunsa biyu, nan fa Rabbasu ya hau reto da wutsil-wutsil, nan fa idanun Rabbasu suka zazzaro suka yi bulu-bulu ya fara kokarin cire yan yatsun dodon daga wuyansa amman sai ya kasa. A wannan lokacin Hantaru ya ruga izuwa can saman dodon ya hau kan kafadarsa ya dinga gabza masa sara da takobi a fuska, amman shi 292 TASKARNOVELS.COM.NG dodon ko kulashi bai yi ba domin ji yake tamkar susa yake mashi. Lokacin da Rabbasu yaji zahiri numfashinsa ya fara daukewa, ya tabbatar da cewa mutuwa zai yi, sai ya tattaro dukkan karfinsa ya kama dan yatsa daya na dodon ya finciko shi, nan take dan yatsan ya fice fit daga jikin hannun, aikuwa sai jini ya fara bulbula. Dodon ya kurma uban ihu ba shiri Rabbasu ya fado kasa. Hakika idan mutum yaga mutuwa babu abinda ba zai iya ba, Hantaru bai taba tsammanin cewa Rabbasu zai iya ceton rayuwarsu ba daga hannun wannan dodon, a wannan lokacin ne Hantaru ya dada sallamawa Rabbasu, ya tabbar da cewa ya cika Sadauki uban sadaukai. Yayin da dodon ya dubi dan yatsansa ya ga jini na shatata a jikin hannun nasa, sai ya haukace ya cigaba da kai masu duka da mangari ta ko ina, haka ya rika makesu suna gwaruwa da jikin bangon kogon, cikin kankanin lokaci Hantaru da Rabbasu suka galabaita ainun suka fita daga cikin hayyacinsu, har ya zamana cewa babu mai sauran kuzari a jikinsu, sai da dodon ya tabbatar da cewa yayi masu laga-laga sai ya sunkuya ya 293 TASKARNOVELS.COM.NG suri Hantaru yayi sama da shi da nufin ya soka kanshi a cikin bakinsa, cikin matukar zafin nama Rabbasu ya dauki takobinsa ya dagata sama tamkar an cillashi daga sama, kafin dodon ya soka Hantaru a cikin bakinsa tuni Rabbasu ya fada cikin bakin nasa, cikin tsananin zafin nama ya zarce zuwa cikinsa yasa wukarsa ya fara daddatsa hanjin cikinsa. A karshe sai ga shi ya faso ta duburarsa, kawai sai Hantaru yaga dodon ya kame wuyansa ya kame ya sake shi ya fadi kasa, yan dakiku kadan dodon yayi kasa tim! Hantaru dai bai san sa'ad da yayi wa Rabbasu jinjina ba, yace tabbas ka cika Sadauki uban sadaukai na sallama maka. Koda jin

Chapter 12 of 13