Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya bata da kashi, kuma itace abar dake jefa mutum ga halaka dare daya. Daga wannan rana Shuraim da Hantaru suka rinka motsa jiki, yana nuna masa yadda ake yin 219 TASKARNOVELS.COM.NG wannan gasa ta tseren gudun kamo barewa a daji, a kullum sai su wuni suna gudu a daji, kuma suna gudun ne a bisa dawakai suna yakar juna domin daya ya jefo daya daga bisa dokinsa. A wannan lokacin ne Hantaru ya tabbar da cewa lallai Shuraim ya cika Sadauki domin yayi mamaki matuka da yaga irin juriyarsa gami da jarumtakarsa wajen shanye duka da kuma zafin namansa na kare sara da suka yayin da suke gudu a kan dokin, duk da cewa girma ya fara kamashi. Duk irin kokarin da Hantaru ke yi a wannan motsa jiki da suke yi, kullum.sai yaga Shuraim baya yaba masa, domin a kullum ce masa yake ya kai jikana ka kara kwazo domin har yanzu baka yi rabin kwazon da Sadauki Rabbasu zai iya yi ba yayin gasar, nasan yanayin gasar nan kuma nasan sirrinta ciki da bai, sannan nasan iyakar jarumtakar Rabbasu, bugu da kari duk shekara idan za a yi wannan gasa sai Rabbasu ya fito filin gasar ya zuba idanu yana nazarinta. Tabbas ya fika sanin sirrinta shiyasa nake da yakinin sai ya fika kokari dan har baka kara jajircewa ba, gobe zan gayyato samarin zuri'armu mu fita daji tare domin mu gwada 220 TASKARNOVELS.COM.NG wannan gasa tare da kai, a sannan ne zanga iyakar kokarin da zaka iya yi. Kashegari kuwa da sassafe samarin zuriar makera suka taru a gidan Shuraim sannan suka dunguma suk tafi daji domin jarraba gasar tseren barewa tare da Sadauki Hantaru. Ai kuwa ana fra wannan gasar sai Hantaru ya raina kansa, domin kuwa kafin ya farga tuni anyi masa fintinkau. Sabida samarin sun kware ainun wajen sarrafa doki, kuma kowannensu ya dade yana hora dokinsa saboda zuwan wannan rana. Sai da Hantaru ya zamo shine a can baya na karshe, koda ganin haka sai hankalin Hantaru ya dugunzuma, zuciyarsa ta harzuka ya tuno da gwagwarmayar da yayi a baya, ya kuma tuna cewa shifa sadaukine na kwarai, lallai idan bai dage ba ya ci wannan gasa ba, to kamar ya rasa Gimbiya Larziyya ne, kuma ya kasa karbo kambun gasa daga zuri'ar mafarauta wanda shine burin mahaifiyarsa Salimat. Hantaru yace da kansa a cikin zuciyarsa, me zanyi na saka wa da Salimat a rayuwa bisa shayar dani da tayi a matsayin dan cikinta? Kuma ta rikeni amana ba tare da tasan cewa ba dan cikinta bane ni. 221 TASKARNOVELS.COM.NG Abinda zanyi shine ya wanke bakin cikin zuri'arsu gabadaya wanda ya addabi zuciyarsu tsawon shekara da shekaru. Koda hantaru ya gama ayyana haka a cikin zuciyarsa sai ya kara zaburar dokinsa yayi masa kaimi ya kutsa cikin jaruman gasar nan yana bangaje wasunsu, bisa mamaki sa sai yaga yana matsawa gaba-gaba, sannu a hankali sai da riski wadanda ke kan gaba wasu zakwakuran samari jaruman gaske su uku, wadanda ya kasa wucesu, Hantaru ya dage iya karfinsa yana kai masu sara da suka da mangari, suma suna mayar masa da martani, amman saboda nacinsu sai ya kasa zubar da su a kasa, sai da suka yi doguwar tafiya a haka har suka fara hango barewar da aka saki tana ta tsula gudu ana so su cimmata. A karshe dai da hantaru da wadannan zakwakuran samarin jarumai uku ragas akayi, wato duk sun banke junansu sun fado kasa daga kan dawakansu, dayansu bai samu nasarar kamo barewar ba. Al'amarin daya dugunzuma hankalin Hantaru kenan, ransa ya baci kuma gwiywarsa tayi sanyi 222 TASKARNOVELS.COM.NG akan wannan gasa. Amman sai Shuraim ya karfafeshi akan cewar ya kara kwazo nan gaba akwai alamar cewa zai zamo zakara. Haka dai aka cigaba da wannan gasa ta baiwa kai horo dan tanadin ranar babbar gasa ta ainahi, ya zamana cewa a kullum sau biyu ake yin gasar safe da yamma, sai da ya rage saura kwana daya jal ranar gasar ta ainahi ta zo, a wannan rana ne Jarumi Hantaru ya samu nasarar banke wadannan zaratan jaruman guda uku ya zubar da su kasa, sannan ya cimma barewar da keso a kamo ya cafketa. Nan fa jama'ar zuri'ar makera suka cika da tsananin farin ciki, domin sun san cewa yanzu kam sun samu Gwarzon da zai karbo masu kambun gasa daga hannun zuri'ar mafarauta. A wannan rana kwana akayi suna walima, kadede-kadede gami da raye-raye, babu wanda yafi Shuraim da Salimat farin ciki a wannan rana, domin kuwa basu san iyakar dukiyar da suka raba wa jama'a ba. Wannan shine abinda ya faru a bangaren makera na birnin Darul Habur. 223 TASKARNOVELS.COM.NG ******************* Acan bngaren zuri'ar mafarauta kuwa lokacin da sarkin mafarauta Zaharu Ibn Dauwar ya isa gida tare da dansa Rabbasu a sume, tare da dukkanin jama'arsu, sai suka taru a cikn fadar Zaharu aka shimfide Rabbasu a bisa wata doguwar kujera, nan take Zaharu ya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa masa, nan take rabbasu yayi atishawa ya farfado, a dimauce ya mike tsaye zumbur yana mai kokarin kai duka, domin shi a zatonsa har yanzu yana fafatawa ne da Hantaru. Bisa ga mamaki sai yaga mahaufinsa tre da jama'arsu a tsaitsaye suna kallonsa kawai. A sannan ne ya dubi inda yake ya gane gida yake ba kasuwa ba. Cikin tsananin fusata Rabbasu ya dubi mahaifinsa ya ce ya abbana ina abokin fadana yake ne? Yaya akayi nazo nan gida? Koda jin wannan tambaya sai Zaharu ya bushe da dariya sannan lokacin guda ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, 224 TASKARNOVELS.COM.NG nan take kuma kwallar takaici ta zubo masa ya ce ya kai dana kayi sani cewa ba wani bane ya zo ya raba fadanku da wannan bakon saurayin ba face babban abokin adawata boka Sulbaini, wannan bakon jarumi ya kasance babban barazana ga zuri'armu gabadaya, domin yazo ne domin ya rabamu da kanbun gasar gudun tseren barewa, kuma shi gimbiya Larziyya ke son ta aura. Koda jin wannan batu sai Rabbasu ya kwarara uban ihu, wanda ya firgita kowa dake wajen, fuskarsa ta kama kakkarwa kamar zata zazzago ta fado kasa, cikin tsananin fushi ya dubi Zaharu ya ce ya kai abbana ka sani cewa yau shekaru sittin kenan ina tanadin neman auren Gimbiya Larziyya, ka sani cewa ina matukar kaunar Larziyya irin kaunar da in har na rasata to lashakka sai na rasa rayuwata, yaya kake tsammanin cewa zan bari wani yazo ya mallaketa. Zaharu ya dafa kafadar Rabbasu ya ce ka kwantar da hankalinka ya kai dana, kaima ka sani cewa babu yadda za a yi ina raye a doron kasa hakan ta faru, ina tabbatar maka da cewa yanzu lokaci yayi da zan baka gabadaya 225 TASKARNOVELS.COM.NG sirrinkan tsafina sabanin da dana baka rabi kawai, ka sani cewa abinda yasa ban baka sirrikan tsafina ba, shine kana da tsananin fushi da bakar zuciya, idan ka mallaki sirrin tsafina duka cewa zaka yi zaka yaki boka Sulbaini, duk ranar daka yaki boka Sulbaini kuwa a ranar wannan birni namu sai ya baje kowa ya hallaka. A halin yanzu bani da wani zabi face na baka sirrikan tsafinnawa tunda ni bani da ikon shiga wannan gasa, domin kare martabar zuri'armu da kuma mallakar gimbiya Larziyya. Abu na biyu dole ne mu baka sabon horo akan wannan gasa, domin ka samu karfi ninkin na da da kake da shi, dan kada abokin gabarka ya samu nasara akan ka, ka sani cewa da mutum dubu uku ake wannan gasa ta tsere, to amma daga yanzu kullum zaka rinka jarraba wannan gasa da mutane dubu shida, lallai indai ka samu nasara akan mutum dubu shida to ba makawa sai ka samu nasara akan abokin gabarka, wato wannan bakon jarumin daya zo. Koda jin haka sai Rabbasu ya cika da farin ciki. Daga wannan rana aka soma baiwa Rabbasu horo da mutum dubu shida, kuma kullum sau uku ake yin gasar, safe, yamma da dare. 226 TASKARNOVELS.COM.NG Tun a ranar farko Rabbasu ya rinka banke zaratan dakaru, duk inda ya ratsa ta cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa, wani lokacin ma har dawakan nasu yake bankewa kasa, saboda tsananin karfin Rabbasu sai da ya lashe gasar nan. Daga ranar farko da aka fara wannan gasar zuwa ranar karshe kullum Rabbasu ne yake lashe gasar, kuma ko dau daya ba a taba kaishi kasa ba. Tabbas Rabbasu ya cika sadaukin Sadaukai domin yafi hantaru karfin damtse, a ranar karshe ana gobe za a yi gasar ainihi ta neman auren Gimbiya Larziyya boka Zaharu ya sanya dukkanin sirrikan ttsafinsa a jikin Rabbasu. Nan take Rabbasu yaji wani gagarumin karfi ya shige shi, tamkar zai iya nada gammo a ka a dora masa duniyar gabadayanta. Nan take ya cika da farin ciki, ya ji a zuciyarshi cewa dole ne ko ta halin kakama yaci wannan gasa da za'a yi. Acan cikin gidan Shuraim kuwa har dare ya raba amman boka Sulbaini bai zo ba kamar yadda yayi alkawari, al'amari daya dugunzuma hankalin Shuraim, Samilat da mahaifiyar 227 TASKARNOVELS.COM.NG Samilat kenan, domin sun san cewa muddin Hantaru bai samu taimako daga boka Sulbaini ba, babu yadda za a yi ya ci wannan gasa akan Rabbasu, saboda sanin cewa dole ne Zaharu mahaifin rabbasu yayi masa gagarumin shiri irin wanda bai taba yi masa ba. Haka dai aka kwanta cikin ta tarrabi da jimami. Al'amarin Sadauki Hantaru kuwa ko kadan baiji wata damuwa ta shigeshi ba, saboda koda yaushe yana da yakinin cewa indai yana cikin hayyacinsa babu wani tsautsayi da zai taba lafiyarsa. Hantaru na kwanciya sai bacci ya dauke shi, tamkar babu wani gagarumin abu dake gabansa a gobe, daf da ketowar alfijir ne Hantaru ya farka daga bacci, kawai sai yaga boka Sulbaini a zaune daf da shi idanunsa a rufe yana jan wani abu. Abinda ya daure wa Hantaru kai shine kofar dakin da tagar dakin a rufe suke ruf, to wai shin ta ina Sulbaini ya shigo cikin wannan dakin ba tare da ya sani ba, kuma ta ina ya shigo din? Koda ya tuna cewa iki ne na tsafi sai hankalinsa ya kwanta, hantaru ya yunkura da nufin mikewa zaune, amman sai Sulbaini ya nuna kirjinsa da tafin hannunsa, take Hantaru ya ji an danne shi da wani irin karfi na musamman wanda b zak iya dagowa ba. Bisa 228 TASKARNOVELS.COM.NG dole ya koma ya kwanta, faruwar hakan ke da wuya sai Sulbaini ya kammala wuridin tsafin da yake yi, kuma yayi tofi akan kirjin Hantaru, har a sannan Sulbaini bai bude idanunsa ba, koda ya tofa sai Hantaru yaji wani irin radadi da zugi na shigarsa, nan take gabadaya jikinsa ya kama kakkarwa, sannan wata irin zufa mai yawa ta rinka kwaranyowa daga jikinsa tana zubowa a kasa tamkar ana kwarara ruwa a wajen. Jim kadan sai zufar ta bace bat daga jikinsa, wanda ta zube a kasa ma ta bace. Nan take Hantaru yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi, irin wanda bai taba jin kamarsa ba a rayuwarsa, domin ji yayi kamar shi kadai zai iya tunkarar gabadaya dakarun duniya, yayi yaki da su tsawon kwanaki arba'in ba tare da ya gaji ba. A daidai wannan lokaci ne boka Sulbaini ya bude idanunsa cikin murmushi yace bude idanunka ya kai sadaukin Sadaukai. Hantaru ya mike zaune daga kan gadon suka fuskanci juna, boka Sulbaini yayi gyaran murya ya ce Yanzu na gama nawa, na gama baka iyakar taimakon da zan iya baka, ya kai sadaukin Sadaukai ka yi sani cewa na baka dukkanin 229 TASKARNOVELS.COM.NG sirrikan ttsafinsa, ni yanzu babu abinda zan iya yi na tsafi, domin duk karfina ya koma jikinka, kamar yadda na boka Zaharu ya koma jikin dansa, idan har baka ci nasarar wannan gasa da za'a yi ba mutuwa zan yi, haka ma idan Rabbasu bai ci nasarar wannan gasa ba, boka Zaharu mutuwa zai yi, mu haka ka'idar tsafinmu ta ke. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa dukkan burinmu mu jama'ar makera a kanka ya ke, dan haka ya zama dole ka zage damtse ta kowanne hali ka ci wannan gasa. Koda Hantaru yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ya dubi boka Sulbaini cikin tsananin damuwa ya ce Ya shugabana, sabida me zaka salwantar da rayuwarka akan wannan bukata, kayi sani cewa mahaifiyata na tsananin kaunar ka, yau idan aka ce babu kai zata iya shiga cikin wani hali, ina rokonka bisa darajar zuri'arku da soyayyarka ga kakana Shuraim ka cire wannan shiri na tsafi da ka bani, k barni da tsagwaran karfin damtsena, ina mai tabbatar maka da cewa t kowanne hali sai na lashe wannan gasa. 230 TASKARNOVELS.COM.NG Sa'ad da Hantaru ya zo nan a jawabinsa, sai kawai yaga hawaye ya zubo wa da boka Sulbaini daga cikin idanunsa, abinda yayi matukar bashi mamaki da tsoro kenan. Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce yakai jikana ina so kasani cewa ni nasan abinda kai baka sani ba, akwai wani sirri babba wanda bazan iya fada maka shi a halin yanzu ba, kuma shine dalilin da yasa na sallamar da rayuwata dan samun nasararka, zaka iya sanin wannan dalili amman sai bayan mutuwata idan ka shiga dakin tsafina. Yace alfarmar da nake nema a wajenka ita ce kada ka kuskura ka fada wa mahaifiyarka Salimat cewa na baka sirrikan tsafina duka, domin idan ka yi haka zata iya shiga mugun hali ta rasa sukuni daga yanzu har izuwa ranar da za a kammala wannan gasa. Da wannan furuci nake maka sallamar karshe idan da rabon mu sake saduwa zamu sadu bayan ka lashe gasa. Koda kammala wannan jawabi sai Hantaru ya ji ya kamu da tsananin tausayin boka Sulbaini, dan haka sai ya rungumeshi ya fashe da kuka, kuma yana mai cewa da iznin abin dogaronka 231 TASKARNOVELS.COM.NG sai mun sake saduwa, da yardar su su ummana ba zasu zubar da hawaye ba. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part Q Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni boka Sulbaini ya ce bat daga cikin dakin, nan fa Hantaru ya nemeshi sama ko kasa ya rasa. Kashegari kuwa tunda duku-dukun safiya jama'ar birnin Darul Habur suka fara tafiya wani daji da ake kira Furja'al Maut, daga cikin birnin Darul Habur zuwa dajin tafiya ce ta rabin sa'a kacal, al'amarin daga daure wa jama'ar birnin kai shine shigowar baki daga kauyuka da birane da dama dan kallon wannan gasa, kai harma daga wasu nahiyoyi haka jama'a suka 232 TASKARNOVELS.COM.NG yita zuwa birnin Darul Habur tun ma saura kwana goma a fara wannan gasa. Al'amarin da ya janyo cunkoso a cikin birnin kenan na fatake dama yan kasuwa. Nan fa kasuwa ta bude, bisa tarihin birnin ba'a taba samun arki mai yawa a kasar ba irin na wannan shekarar ba, kuma ba a taba ganin yawan jama'a irin na wannan shekarar ba, sai da takaicewa babu masaukai inda baki zasu zauna, hakan yasa har a wajen gari kafa tantuna ake yi, kai ko ruwa mutum yake saidawa a wannan lokaci cikin kwana uku yake zama attajiri. Ba komai bane duk ya haddasa wannan al'amari ba face labari ya bazu cewa Sadauki Rabbasu ya shiga wannan gasa, wanda labarin jarumtakarsa ya bazu ko ina a nahiyar kuma an samu labarin cewa an samu wani bakon jarumi da ya iya fafatawa da shi har tsawon rabin sa'a b tare da dayansu ya samu nasarar komai akan dan uwnsu ba. Sannu a hankali jama'a suka rinka turueuwa a cikin dajin Furja'al Maut suna hawa saman manyan Duwatsu da tsaunuka suna masu tsayawa dan kallon wannan gagarumar gasa da za a fara a yau din. Shidai wannan daji na 233 TASKARNOVELS.COM.NG Furja'al Maut daji ne mai girma da fadin gaske, kuma duwatsu dake ciki sun kasance masu tsananin yawan gaske, wasu tsaunukan ma idan mutum ya hau shi sai a hangoshi dan mitsitsi tamkar dantsako. Kafin gari ya waye dajin ya cika ya batse da jama'a babu masaka tsinke, face wacce take a tsakiya wadda aka barwa dakarun gasa. Bayan jama'a sun shafe kusan sa'a uku a tsaitsaye suna jira, sai ga dakarun gasa sun tunkaro dajin daga can nesa, tawagar farko mutum dubu daya da dari biyar ne, sunyi shigar jajayen tufafi, dukkaninsu suna bisa fararen dawakai abin gwanin ban sha'awa, sannan suna rike da kulake na duka babu dayansu dake rike da takobi ko wani makami na karfe. Wannan zuga ita ce ta zuri'ar makera na birnin Darul Habur. A cikinsu gabadaya babu mai kwarjini da daukar hankali sama da Sadauki Hantaru, su kansu gabadaya dakarun wato yan uwansa sun sallama masa, kai da gani kasan cewa wannan karon sun fito gasar ne da matukar karfin gwiywa, kasancewar suna tare da shi, sai yi masa kirari da jinjina suke yi. 234 TASKARNOVELS.COM.NG Jim kadan da shigewar wannan tawaga sai kuma ga tawaga ta biyu wanda suma sun kasance su dubu daya da dari biyar, gaba dayansu suna sanye da bakaken tufafi haye bisa bakaken dawakai, babu wani mai haske a tare da su, saboda tsananin kwarjinin wannan tawaga sai da yan kallo suka razana, wasuma buya suka kamayi, saboda gani suke kamar zasu iya afka wa yan kallo a kowanne lokaci, suyi masu tamore, saboda ko kadan babu alamar tausayi ko digon imani a bisa fuskokinsu. A tsakiyar wannan tafiya Sadauki Rabbasu ne bisa wani jibgegen doki da yafi na sauran girma. Rabbasu ya shafe dukkanin jikinsa da bakin shuni, in banda jajayen idanunsa da ake gani babu abinda mutum ke iya gani a fuskarsa, sai faman huci da gurnani yake kamar tsohon mayunwacin zaki. Wani ayari daban na zuri'ar mafarauta na biye da su a baya, sunata buga tambura da ganguna kuma suna raira wakoki na jinjina da kirari ga sadauki Rabbasu. Duk mahalukin da yazo wannan daji na Furja'al Maut sai da hantar cikinsa ta kada a lokacin da 235 TASKARNOVELS.COM.NG Rabbasu ya kurma wani uban ihu, mai tsananin razanarwa face jarumi Hantaru wanda ya saba da kuruwar manyan aljanu da dodanni, shine kawai bai razana ba. Suma wannan tawaga ta biyi babu makamin karfe a hannunsu sai kulake, domin yanayin gasar kenan, ba a yarda a xo da makamin karfe ba. Bayan tawagar biyun ta cakude ne sai aka fara kallon kallo gami da harar juna. Wohoho! Yayin da manyan mazaje suka hada ido kuwa sai da zuciyar kowa a wajen ta buga da karfin gaske dan kada su kacame da azabben fada su tashi hankalin duwatsu da bishiyu dake wajen. Rabbasu da Hantaru suka kura wa juna idanu ko kiftawa basa yi, kowannensu fuskarsa ta kama gyatsine kuma jikinsu ya kama tsuma ji suke kamar su rufe juna da duka tun gabanin a fara wannan gasar. Wani akasi kuma da aka samu shine Rabbasu na daga hannun hagu shi kuma Hantaru na daga hannun dama, har ma wani lokacin idan aka yi 236 TASKARNOVELS.COM.NG turmutsutsu kafadunsu na gogar na juna. Jim kadan da cakudewar tawagar biyu sai alkalan gasar suka shigo cikin tawagar suna masu binsu daya bayan daya suka cajesu, aka tabbatar da cewa babu dayansu daya boye makamin karfe a jikinsa, ya zamana cewa in banda guraye da layu babu komai a jikinsu, to kuma sai kulkin duka. Gama hakan keda wuya sai alkalan gasar suka fice daga cikin tawagar biyi su hau kan duwatsu suka tsaitsaya kafin a busa kahon fara gasar. A daidai wannan lokacin ne kuma Hantaru ya hango gimbiya Larziyya a cikin taron yan mata can saman wani tsauni, tana danye da jajayen tufafi masu ratsin fari, wato dai tayi shiga irin dakarun zuri'ar makera, al'amarin daya baiwa kowa dake wajen mamaki kenan, aka shiga zunde da surutu ana cewa Me yasa gimbiya Larziyya zata yi irin wannan shiga, alhalin tana matsayin yar sarki, ai bai kamata ta nuna bangaren da take so ba daga cikin zuri'ar nan guda biyu ba. Duk da cewa kowa yasan cewa bata son Sadauki Rabbasu, dan ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta. 237 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Gimbiya Larziyya ta hada idanu da jarumi Hantaru, sai ta cire amawalin data rufe bakinta da shi ta yi masa murmushi. Koda Hantaru ya maida mata da martanin murmushin sai ta daga hannunta ta yi masa jinjina, sannan ta rufe fuskarta kuma ta sake daure fuska tamau ta ki yarda ta kalli fuskar Sadauki Rabbasu. Wannan abu da gimbiya ta yi ba karamin bakin ciki ta dasa wa Sadauki Rabbasu a cikin zuciyarsa ba, nan take jikinsa ya kama kakkarwa kuma zuyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Acan gefe daya kuma sarki ne da yan majalisarsa tsaitsaye bisa dawakai bisa wani dogon tsauni sun zuba idanu kasa dan ganin yadda wannan gasa zata kasance. Dama musamman aka sassabe dogayen bishiyoyi na dajin domin a samu cikakken samun damar kallon gasar yadda ya kamata. Nan take wani dogon mutum ya hau kan wani dogon tsauni da babu kowa a kansa, koda ya kafa kahon a bakinsa ya busa, sai karar sautin kahon ta cika dajin gabadaya. 238 TASKARNOVELS.COM.NG Aikuwa sai gaba daya dakarun gasa suka zaburi dawakansu a lokaci guda aka zuba tseren gudu. Wohoho! Idan da ace mutum yana nan yaga yadda dakarun nan suka rankaya da gudu kura na binsu a baya sai yayi tunanin yakin duniya ne za a yi. Nan fa aka fara bugun jama'a da kulake, daman tuni an saki wata barewa a sanda aka fara gudun ta fice da gudu ta gaban dakarun nan, haka ko wanne badakaren gasa ya ci buri sai ya kamo wannan barewar. Kaicon maza! Lokacin da aka fara bugegebiya a tsakanin tawagar nan biyu, sai al'amura suka zamo abin tsoro kuma abin tausayi, domin sai dai aga an mako mutum.ya fado kasa, dawakai sun tattakeshi yayi raga-raga, wani lokacin ma har dawakan ake makewa su fadi kasa, wasu zaratan jaruman masu naci da tsananin juriya ko an maka masu kulki a kasa basa yarda su fado kasa, sai dai kaga jini na tsartuwa a fuskokinsu suma suna mayar da martanin duka. Al'amarin Sadauki Rabbasu da Hantaru kuwa, tun daga lokacin da suka fara gidun ne suka shiga bugun junansu, wato suna gudu suna gudu 239 TASKARNOVELS.COM.NG suna bugun junansu da kulake ga kuma duka ta ko ina, ta fuska, ta kai ta jiki, dukan da suke yi wa junan nasu wawan duka ne, wanda babu mai iya shanyeshi a gaba daya dakarun gasar, tunda suka fara bugun junnasu babu wanda fatar jikinsa ta tsage ko ta kwaile, sai dai kaji kara na tashi kamar ana bugun bugun dawa da tabarya, tim! Tim! Duk wanda aka zabga wa kulki sai dai kaga ya girgije ya mayar da martani. Kafin a samu tsawon dakika dari uku da sittin da fara wannan tsere an zubar da fiye da rabin dakarun a kasa, wasu sun kakkarya wuya sun mutu, wasu kuma sun kakkarye a gabban jikinsu, wasu kuma jikinsu yayi fatafata ba kyan gani, ga dukkanin alamu ba zasu yi rai ba. Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda mutane ke ragargajewa cikin wannan gasa dole ne zuciyarsa ta raunana. Sannu a hankali dakarun gasa suka rinka zubewa kasa har ya zamana cewa saura bai fi su dari uku ba, daga cikin su dubu uku. A wannan lokacin ne dokin Hantaru dana Rabbasu suka baiwa sauran dakarun rtaa mai 240 TASKARNOVELS.COM.NG yawan gaske, har ya zamana cewa suna iya hango barewar da akeso su cimmawa. Nan fa suka kara karfin gudu kum suka cigaba da kaiwa junansu cikin tsananin karfin hali da jarumta fiye da farko, aiko nantake kalaken naku suka kakkarye saboda tsabar bugun juna da suke yi, duk fuskokinsu sun kumbura, haka jikinsu ma duk ya kumbura, idanunsu ta kumbura hatta fatar idanunsu neman rufe idon take yi saboda itama ta kumbura abun ba kyan gani. Lokacin da Hantaru da Rabbasu sukaga kulakensu sun kakkarye sai suka ci gaba da naushin juna da hannu, a duk lokacin da Rabbasu ya naushi Hantaru a fuska sai yaga taurarin wuya, idan tsananin zafi da zugi ya shigeshi ya dimauce sai kaga yana layi kamar zai fado daga kan dokinsa, amman sai kaga ya makalkale dokinnasa shima ya takarkare ya ganza wa Rabbasu wawan naushi a fuska, saboda kasancewar Rabbasu ya fi Hantaru tsananin karfin damtse da juriya, ko Hantaru ya naushe shi baya yin layi sai dai ya shanye naushi kuma ya mayar da martani sau uku a jere kuma a lokaci guda. 241 TASKARNOVELS.COM.NG Kafin cikar dakiki dari uku Rabbasu yayi lagalaga da Hantaru, amman saboda tsananin naci da juriya Hantaru yaki yarda ya fado kasa, shi kuwa Rabbasu yayi mtukar mamaki yadda aka yi Hantaru bai fado kasa ba, duk d cewa ya galabaita ainun har ma kamar numfashinsa yana neman daukewa. Adaidai wannan lokacin ne gaba daya sauran dakarun suka ci kasa suda dawakan nasu, ya rage saura dokin Hantaru da na Rabbasu kadai dauke da mahayansu sunata tsala gudu. Mahayan na cigaba da gumurzu ga barewa a gabansu sun kusa cimmata. Duk wannan abu dake faruwa akwai wasu zaratan alkalan gasa su hudu suna bin dakarun gasa a baya cikin tsananin gudu, su dai wadannan alkalai dama can kwararrun mahaya dawakai ne wadanda babu kamarsu a gasar tseren doki a birnin kaf, kuma aminttatun sarki ne, suna aiki ne ba tare da son wani bangare ba daga cikin zuri'ar guda biyu. Lokacin da Sadauki Rabbasu ya waiga baya yaga gaba daya dakarun gasar sun zube saura su biyu tak, wato daga shi sai Hantaru. Sai ya harzuka ya kara kaimi wajen naushin Hantaru. Da dai yaga 242 TASKARNOVELS.COM.NG ya kasa kada Hantaru sai ya dage ya zabga wa dokinsa naushi a ciki, take dokin ya sulale ya fadi kasa tare da Hantaru. Dokin nan ku shurawa bai yi ba haka ya zama gawa, a wannan lokacin tuni Rabbasu ya fara kyalkkyala dariyar farin ciki, yana ganin cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya kai Hantaru kasa, kuma tsakaninsa da barewar nan bai wuce kamu biyar ba. Ba zato ba tsammani sai kawai sadauki Rabbasu ya ji ana binsa a baya Daf! Daf! Ko da ya waiga baya sai yaga ashe hantaru ne ya biyoshi cikin wani irin azabben gudu na gaban kwatance, wanda ko dokin ma sai haka, har saura kiris ma ya riske shi. Cikin tsananin fushi da mugun nufi Rabbasu ya shiga kaiwa Hantaru duka ta bayan da mugun nufi, amman sai Hantaru ya rinka sunkuyawa yana kauce wa dukan, cikin matukar zafin nama Hantaru ya daka tsalle ya haye saman dokin Rabbasu ya rukunkumoshi ta baya suka fado daga kan dokin tare, kafin Rabbasu ya mike saboda tsananin nauyinsa ya ninka na Hantaru, tuni Hantaru ya mike ya gabza wa dokin 243 TASKARNOVELS.COM.NG Rabbasu naushi a fuska, nan take idon dokin ya fashe ya sulale kasa matacce. Nan fa hantaru da Rabbasu suka kasa tsere kowannensu na kokarin ya kamo wannan barewa, har a sannan alkalan gasa na biye da su kuma duk sunga abinda ya faru, bisa ga mamaki sai gudun Hantaru dana Rabbasu ya zo daya, ya zamana cewa suna hada kafada da juna an kuma rasa wanda zai wuce wani, kuma a hakan ne suka ci gaba d naushin juna amman a haka kowannensu ya ki yarda ya kai kasa. Yayin daya rage taku biyu kacal tsakanin su Hantaru da wannan barewa, sai suka daga tsalle sama a lokaci guda suka kai wa wannan barewar cafka, bisa rashin sa'a sai Rabbasu ya kamo kan barewar, shi kuma hantaru sai ya kama kafafunta, koda Rabbasu ya ja shima Hantaru ya ja sai barewar ta rabe gida biyu, a dai-dai wannan lokacin ne alkalan gasar suka karaso gabansu a guje bisa dawakai suka yi turjiya. Cikin zafin nama alkalan uka sakko daga kan dawakansu, mutum biyu suka rike Rabbasu, sauran biyun suka rike Hantaru kowannensu yana rike da rabin barewa a hannunsa. 244 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan lokacin ne shima sarki da fadawansa suka iso wajen, sannan sai ga sauran jama'a yan kallo suma suna karasowa wajen. Sarki ya dubi alkalan gasar ya ce tsakanin Hantaru da Rabbasu yace wane ya

Chapter 10 of 13