Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bil'adama ka 169 TASKARNOVELS.COM.NG shigo lambu na babu sallama ka tsinki tuffata ka cinye. sa'adda hantaru yaji wannan sai kunya ta kamashi domin yasan baiyi da'a ba kuma bai nuna shi dane mai tarbiyya ba, cikin sanyin murya ya dubi budurwar yace yake wannan ma'abociyar kyau ki gafarceni hakika nayi kuskure amma ki sani kayan marmarin dake cikin lambun sunada daukan ido. budurwar ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace hakika kude bil'adama da rashin hakurh kuke to kasani cewa kaciwa kanka bala'i domin abune mawuyaci ka tsira da rayuwar ka ina yimaka albishir cewa ka fado cikin tarkon uwar mayu ta aljanu koda gama fadin hakan sai budurwar ta rikide ta dawo wata tsohumaw mummunar aljana mai matukar ban tsoro hantaru ya yunkuri da nufin ya kaimata sara sai yaji cikinsa ya murde ya fara ciwo kafin cikan dakika biu ya fara aman jini nan take fadi kasa sumamme. Koda shumailat taga abinda ya faru da hantaru sai itama ta fadi kasa sumammiya. lokacin da shumila ta farfado daga dogon suman datayi saita tsinci kanta acikin wanin irin gida an daureta da wata katuwar sarka shide wannan gida an gina shine da zallan duwatsun wuta kuma babu komai acikinsa face wata katuwar 170 TASKARNOVELS.COM.NG tukuba wacce aka hada guma guman itatuwa suna taci da wuta saman wutar an daura wani gado yayi jawur. kwatsam sai shamilat ta jiyo hayania daga can bangaren yammacin gidan sannu a hankali ya ringa karuwa yana cika dodon kunne daga can saiga dandazon wasu yayan aljanu sama dasu million 40 sun taho da gudu suna tsalle a tsakiyar su wannan mummunar aljanan ne dauke da hantaru su duka suka tunkaro inda tukubar wuta take koda ganin haka sai shamilat ta fahimci cewa cikin wannan gadon wuta aljanar nan zata daura hantaru shamilat ta kurma ihu tana kuka tana mai rokon aljanar kadata kona mata danta aljannar bata dubi shamilat ba saida suka iso dab da wutar sannan ta tsaya cak tana kyalkyala daria tace yake wannan bil'adama kiyi sani cewa idan ban gasa wannan danaki ba na baiwa yayana sunci duk mutuwa zasuyi ayau. kuma basu iya haura kwana 40 batareda sunci naman bil'adama ba kinga kuwa da bai fi ɗa ba. Kodajin haka sai shumilat ta fashe da kuka, aljanar ta sake bushewa da dariya a karo na biu tace ai gara kisha kukanki ki more kafin na dawo kanki domin idan na gasaki ni kadai zanyi walimanki domin yayana basa cin nama mace 171 TASKARNOVELS.COM.NG cikin tsananin fushi shamilat ta dubi aljanar tace tir dake wannan la'ananniar maiya inda dana acikin hayyacinsa yake dakin raina kanki domin baki isa kiyi masa komai ba sa'adda aljannar taji haka sai ta bushe da daria sannan ta dakawa shamilat tsawa tace ke bil'adama kiyi sani cewa agaban sarauniyar mayun aljanun duniya kike babu wani mahaluki daya isa ya hallakani sa'ar ki daya mijina baya nan ya tafi farautar bil'adama dayanzu kema mun gama dake dolene na hakura sai yadawo domin akwai yajin dazai tafo mana dashi wanda muke jin dadincin naman bil'adama dashi. ******************** Mazan Jiya Part 17 Labarin Sadauki Hantaru mai takobin saiful lujara na Mazan Jiya #Cigaba 172 TASKARNOVELS.COM.NG Gama fadin hakan keda wuya sai uwar mayu ta yunkara zata daura hantaru akan gadon wutan bazato ba tsammani sai sukaga hantaru ya mike zumbur ya daka tsalle sama daga kan tafin hannun ta kafin takai masa cafka cikin zafin nama ya gabza mata naushi a idon ta take hannun nasa ya burma cikin kwarmin idanun nata, koda ya zaro hannun nasa saiga kwayan idanun nata ya fado kasa nanfa jini ya kama feshi uwar mayu takama kururuwa tana katan tanwa saboda tsananin zafi da takeji a cikin idanun ta yayin da yayan uwar mayu sukaga abunda yafaru da mahaifiyarsu sai sukayi caa akan hantaru da nufin su yayyaga shi su cinye shi danye abinda basu saniba sun gamu da gamon su maimakon sadauki hantaru yayi amfani da takobin sa wajen yakar su sai yayi wurgi da takobin sa ya afka musu yadinga cafkar wuyan su yana gwara kawunan su nanfa kafun a jima hantaru ya hallaka sama da guda dubu dari a daidai wannan lokaci ne uwar mayu tadawo hayyacin ta koda taga mummunar barnar da hantaru yayi mata saita fusata ta runtuma sabon ihu da kukan bakin ciki shi kansa hantaru saida ya razana sakama kon jin sabon ihun datayi suko sauran yayan nata 173 TASKARNOVELS.COM.NG dasuka rage sai suka ruga izuwa bayanta suka tsaitsaya uwar mayu ta tunkari hantaru da mugun nufi shima sai ya tunkaro ta bada jin tsoron komai ba koda ya rage baifi taku goma su gamu sai hantaru ya ruga da gudu yayi tsalle sama yakai mata wawan naushi da nufin ya fasa daya idon cikin zafin nama uwar mayu ta kade shi da hannunta take hantaru ya maku da dirkar gini ya fado kasa a matukar galabaice koda uwar mayu taga hantaru a kasa ya kasa tashi saita rugo da gudu ta daga kafar ta sama ta kawo masa wawan taku da nufin ta mutsuke shi cikin zafin nama hantaru ya goce saboda karfin takun saida kafar uwar mayu ta nutse cikin kasa har gwuiwan ta uwar mayu ta zare kafar da sauri ta cigaba da kaiwa hantaru taku yana gocewa kafun ajima harabar gidan ya cika da ramuka ita kanta uwar mayu saida ta gaji ainun takama haki a sannan ne hantaru ya samu ya mike tsaye aiko sai suka kasa tsere ta dinga binsa tana kai masa cafka tana wangame baki domin ta hadiye kansa gabadaya aduk sa'adda ta karta mashi farata a jikin shi saidai taji kamar ana karta takobi akan dutse kuma ko korzanewa bayayi cikin dakika kadan gidan ya hautsine hankalin kowa ya dugunzuma domin gunguma 174 TASKARNOVELS.COM.NG gunguman duwatsu ne na wuta ke fadowa kasa su kansu yayan uwar mayu saida suka firgice suna neman mafaka itako shamilat tuni dirkar da'aka daure ta a jiki ta karye ta fadi sannan wani katon dutse ya fado akan dirkar lokacin da hantaru ya waigo yaga halin da shamilat ta shiga sai hankalin sa ya dugunzuma sabona yasan cewa idan ta dade a kasan wannan katon dutse na wuta kasa zata iya zaftarewa a wannan lokaci ne hantaru ya fusata don haka saiya daina gudun yama tsaya cakk awaje daya yana sauraron isowar uwar mayu gareshi koda uwar mayu taga hantaru ya tsaya cak ya daina guje guje sai murna ta kamata domin tasan cewa yanzu zata hallakashi bada bata lokaci ba kawai saita durfafe shi da dukkan karfinta cikin bakin zafin nama da isowar ta dabb dashi saita kawo masa wawan cafka da hannayen ta guda biyu cikin tsananin zafin nama hantaru ya sunkuya kasa ta kama iska kafun ta sake kai masa hari tuni daka tsalle ta cikin karkashin kafafun ta ya zagayo bayanta ya sake daka tsalle kafun ta waigo ya dira akan kafadar ta ya gabza mata naushi acikin kunnen ta aiko sai hannun nashi ya lume acikin kunnen ya futo ta cikin daya kunnen yana zare hannun jini yakama feshi take 175 TASKARNOVELS.COM.NG uwar mayu ta sulale kasa matacciya a matukar galabaice hantaru ya durshe kasa bisa gwuiwoyin sa saboda tsabar wahala a sannan ne ya lura cewa guma guman duwatsun wuta dasuka yita fadowa daga saman ginin sun hallaka gabadaya yayan uwar mayu dayan su bai tsiraba da rayuwarsa hantaru na durkushe yana haki sai kawai yajiyo ihun shamilat daga can kasan wannan katon dutsin daya danne dirkar ginin da'aka daure ta a jiki cikin zafin nama hantaru ya yunkura da saurin gaske ya ruga wajen ya kaimata dauki wani irin takun sawu mai karfi da hantaru ya jiyo a bayansa shine tsaida shi ya juya a firgice aiko sai yayi arba da wata jibgegiyar halitta mai tsananin kwarjini daban tsoro da muni bakomai ne wannan halitta ba sai mijin uwar mayu ya dubi yadda gidan sa ya rugurguje sannan ya hango gawar uwar mayu a can gefe daya can kuma saiga gawarwakin yayan sa kota ina kawai saiya takarkare ya kwarara ihu karar ihun tamkar ana ruwan kwaran kwatsa daga sama ak'amarin daya kara razana hantaru kenan musamman daya karewa mijin uwar mayu kallo sama da kasa ya tabbatar dacewa ruwa ba sa'an kwando bane a wannan lokacin ne kuma shamilat ta 176 TASKARNOVELS.COM.NG cigaba da kwala ihu ashe dutsen daya danne dirkar da take jiki ne yake kara dannawa kasa nan fa hankalin hantaru ya rabu gida biyu ya rasa abinda ya kamata yayi shin mijin uwar mayu zai fuskanta suyi yaki koko wajen mahaifiyar sa shamilat zaije ya ceto rayuwarta harya yunkura zai ruga wajen shamilat sai yaji an shako wuyan sa ta baya koda ya kama abun daya shake shi sai yaga ashe wata irin doguwar bulala ce mijin uwar mayu ya jefa mishi ta shake shi a wuya kuma ta shake shi ne ainun ya kasa cire ta mijin uwar mayu yafara janyo bulalar nan domin ya kawo hantaru gaban sa shiko hantaru saiya fara cijewa da dukkan karfin sa domin yasan cewa muddin ya kuskura yaje gaban sa ya damke shi saidai kuma mahaifiyar sa ta haifi wani amma shi tasa ta kare hantaru ya cigaba da cijewa amma saboda mijin uwar mayu yafi shi karfi nesa ba kusa ba saiya dinga jansa gabadaya al'amarin daya dugunzuma hankalin hantaru kenan ya saduda domin yasan cewa kwanan sa yazo karshe. ****************** Mazan Jiya Part 18 177 TASKARNOVELS.COM.NG #Cigaba A lokacin daya rage baifi saura taku biyar ba mijin uwar mayu ya cafi hantaru da hannun sa sai wata dabara ta fadowa hantaru ya tuno da wata wuka dake sakale a bayansa cikin hanzari ya zaro wukar ya yanke wannan bulala data shake shi ya fada baya koda mijin uwar mayu yaga bulalar sa ta yanke sai yayi jifa da ita ya zare wani katon sungumi dake sakale a cinyar sa ya ruga izuwa kan hantaru suka kacame da sabon azababben yaki mai ban tsaro da ban al'ajabi wohoho!! tashin hankali ba'a saka maka rana saida hantaru da mijin uwar mayu suka kwana suka tashi suna fafata yakin bala'i hatta kasa tasha azaba domin saida mijin uwar mayu ya ratattaka komai dake cikin gidan nan da wannan katon makamin dake hannun sa tunda hantaru yazo duniya bai taba shan bakar wahala ba irin ta wannan lokaci sau bakwai yana suma a wannan fafatawa dayayi da mijin uwar mayu amma kafun mijin uwar mayu ya zaro shi daga cikin karkashin kasa ya karisa kashe shi saiya 178 TASKARNOVELS.COM.NG farfado su cigaba da gumurzu saida yazamana cewa hantaru ya samu karaya tara a jikin sa amma bai fasa yaki ba. Itako shamilat tuntuni ta suma ta nutse a cikin karkashin kasa batama san abunda dake faruwa ba ana cikin wannan gumurzun ne mijin uwar mayu ya samu nasarar yiwa hantaru wani irin wawan naushi a fuska nan take numfashin hantaru ya dauke ya baje kasa ko motsi bai sake yiba mijin uwar mayu ya tsaya cakk yana haki kuma ya kurawa hantaru idanu domin yagani ko zai motsa a wannan lokaci shima mijin uwar mayu duk jikin sa raunuka ne jini na zuba har jiri na diban sa yana layi tsawon dakika dari shida da sittin hantaru bai motsa ba. don haka sai mijin uwar mayu ya tabbatar dacewa ya mutu amma duk da haka hankalin sa bai kwanta ba saboda bai taba ganin bil'adama hatsabibi mai tsananin jarumtaka da naci da taurin rai tamkar hantaru ba, nan take mijin uwar mayu ya nufi kan hantaru kai tsaye da nufin ya cizge kansa da karfin tsiya ya cinye, koda yazo dabb dashi ya raba kafafun sa akan hantaru kuma ya sunkuyo da nufin ya kama kansa sai kawai yaji hantaru gabza masa naushi a ido, take hannun hantaru ya burma ta kwarmin ido ya fito ta keya 179 TASKARNOVELS.COM.NG take mijin uwar mayu ya fadi ta baya tamkar giwa uku sun fadi a kasa, lokaci guda. Da kyar da jan jiki hantaru ya isa inda dutsen nan ya danne shamilat hantaru yayi amfani da dukkan karfin damtsen sa ya dago dutsen sannan kuma ya shiga zaro wannan dirkar gini wadda ta nutse cikin karkashin kasa kuma shamilat take daure a jiki saida yasake shan bakar wahala sannan yasamu ya dago dirkar yana gama zaro dirkar yaga shamilat a mimmike babu abinda ke motsi a jikin ta nan hantaru ya kurma ihu kuma ya fashe da kuka domin a zaton sa ta mutu, wani iko na Allah sai hadari ya gangamo adaidai wannan lokaci nan da nan aka kece da ruwa, koda ruwa ya daki shamilat saita farfado a wannan lokaci kan hantaru na sunkuye yanata rusa kuka, kwatsam sai yaji shamilat tayi tari cikin zafin nama yadago kai koda yaganta a raye ya matsa gareta ya rungumeta duk su biyun suka fashe da kukan farin ciki. Saida su hantaru suka kwana arba'in a cikin wannan busashen gida na uwar mayu suna jinyar cikin su sannan sukayi shiri suka cigaba da tafiya, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a 180 TASKARNOVELS.COM.NG dade ba je ba tunda su hantaru suka bar wannan daji dayayi mugun yaki dasu uwar mayu basu sake gamuwa da wani abu ba daya wahalar dasu har suka iso birnin darul habur da la'asar su shamilat suka shigo cikin birnin darul habur tundaga bakin kofar birnin shamilat ta cika da tsananin mamaki domin komai na garin yana nan kamar yadda tasan shi shamilat da hantaru suka yita kalle kalle suma suka zamo abun kallo a matsayin su na baki lokacin dasuka ratsa ta cikin kasuwa da makera sai hantaru yadinga ganin zaratan jarumai masu kirar karfi sunata kera makamai iri-iri wasu kuma sunata baiwa kansu horon kokuwa da gudu, daganin wadannan zaratan jarumai sai hantaru yasha jinin jikinsa yasan cewa lallai ya shigo nahiyar sadaukai inda sai yayi da gaske jarumtakar sa zata kwace shi, domin bai taba ganin samari masu girma da tarin kwanji irinsu ba abunda yafara fadowa hantaru a rai shine batun gasar nan na gudun kamo barewa nanfa ya shiga tunanin al'amarin a cikin zuciyar sa. Lokacin da hantaru yake ta wannan tunani itako shamilat farin ciki ne ya lullube ta sabona tsintar kanta a cikin mahaifarta in banda murmushi da kalle-kalle babu abunda shamilat 181 TASKARNOVELS.COM.NG takeyi hakadai suka cigaba da tafiya bisa dawakan su rakuman su na gaba, kwatsam sai daya daga cikin rakuman su hantaru yaje yana shinshina wata katuwar randa dake cike da ruwa yana kokarin ture marfin ta, dama rakuman na fama da kishirwa sunfi kwana talatin rabon su da shan ruwa domin sun dade a cikin sahara suna tafiya, ruwan dasu hantaru sukayi guzuri bashida yawa, a garin ture marfin randar ne rakumin ya bangaje randar gabadaya ta fashe karar fashewar randar ce tasa mai randar ya fito a fusace daga cikin rumfarsa rikeda takobi, koda yaga rakumin daya masa wannan barna sai yayi kansa zai sare shi cikin zafin nama hantaru ya zare takobin sa ya daka tsalle daga kan dokinsa ya dirka a gaban mai randar ya tare wannan sara takubban su suka hadu suka fitar da kara gami da tartsatsin wuta, nan fa aka tsaya ana kalon kallo tsakanin hantaru damai randar a iya rayuwar hantaru bai taba ganin saurayi mai tsawo da kauri da murdewar jiki kamar wannan saurayi ba, sannan yanada matukar kwarjini koda sauran jama'ar dake cikin kasuwa sukaga abinda ke shirin faruwa sai hankalin su ya dugunzuma kowa ya baro wajen sana'ar sa aka rugo inda su 182 TASKARNOVELS.COM.NG hantaru ke tsaye aka tsaitsaya ana kallo cikin tsananin fushi wannan saurayi ya dubi hantaru yace shin kazabi karasa rayuwar kane akan na rakumin ka hantaru yayi murmushi yace inason rayuwa ta, kuma inason rayuwar rakumi na idan saboda akan randar ka kakeso kadauki ran rakumi na toh gaskiya ka fadi kudin randar ka ko nawane zan biya kodajin haka sai saurayin yadakawa hantaru tsawa yace kai bako waye Kaine harda zaka nuna min gadara a cikin birnin mu lallai yau zakasan cewa ka tabo zaki uban dawa kuma dodon maza dakai da rakumin nakan duk yanzun nan takobi na zata sha jinin ku, kafun hantaru yace wani abu sai saurayin ya daga takobin sa cikin zafin nama ya kaiwa hantaru wawan sara a ciki da nufin ya tsarga shi biyu hantaru ya jada baya takobin ta sari iska nanfa suka kacame da azababben yaki, al'amarin dayayi matukar firgita shamilat kenan ta fara kuka tana rokon jama'ah dasu raba wannan fada amma babu wanda ya saurare ta face gudu da jama'ah suka ringayi domin wuri ya hautsine tsautsayi na neman afkawa kan kowa. Koda ganin haka sai Shamilat ta zaburi dokinta ta nufi gidan mahaifinta sarkin makera Shuraim 183 TASKARNOVELS.COM.NG ibn Alkasim domin tq sanar da shi abinda ke faruwa. Wohoho! Jarumtaka ta hadu da jarumtaka dole ne fafatawar ta zama abar tsoro, nan take Hantaru da saurayi suka hargitsa kowa da komai dake cikin kasuwar, suka rinka rushe rumfunan suna dagargaza dukiyar jama'a, nan fa jama''a suka dinga guje-guje da iface-iface, kafin a juma labari ya cika gari, Hantaru da wannan saurayi suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta ba kakkautawa, sai da suka shafe kusan rabin sa'a amman dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin dan uwansa ba, har takubbansu suka dakushe. Al'amarin daya fusatasu kenan suka zubar da makamansu suka sake ruguntsumewa da azabben gumurzu da bugun juna da hannu da kafa, nan take kuwa kowa ya hada wa kowa jini da majina. A daidai lokacin ne Shamilat da mahaifinta Shuraim tare da wasu jama'arsu suka iso wajen a guje bisa dawakansu, aikuwa sai ga wata jama'ar da ban bisa dawakai a sukwane, ba kowa bane yake jagorantar su ba face sarkin mafarauta na birnin wanda ake kira zaharu ibn 184 TASKARNOVELS.COM.NG Dauwal, nan fa rundunonin nan suka ja tunga suna masu fuskantar junansu ga dukkanin alamu so suke su yaki junansu, abinda ya hanasu shine kallon fafatawar da su Hantaru ke yi. Zaharu ibn Dauwar shine mahaifin wannan saurayi dake fafatawa da Hantaru, kuma tsakaninsa da Shuraim gaba ce mai tsanani tun iyaye da kakanni, kuma ba komai bane ya haddasa wannan gaba ba face wannan gasa da ake gudanarwa duk karshen shekara ta tseren gudun kamo barewa, domin auren budurwar da babu kamarta a birnin, duk shekara idan aka yi gasar zuri'ar mafarauta ce take cinye gasar, zuri'ar makera basu taba cinye gasar ba, saboda an fisu zakwakurarun jarumai masu sadaukartaka. Shuraim n da wani da guda daya mai suna Hurais, a duk fadin birnin babu kyakkyawan saurayi kamarsa, kuma ya kasance mai matukar kwarjini a cikin al'umma, Hurais kanin Shamilat ne, dan Lokacin da aka yi mata aure bai wuce shekaru bakwai ba. 185 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da Hurais ya girma ya zama saurayi sai soyayya mai zafi ta kulli tsakaninsa da wata kyakkyawar budurwa mai suna Marilat, wacce ta kasance kanwa ga wannan saurayi da ke yaki da Hantaru. Shi dai wannan saurayi ana kiransa da suna Rabbasu, ma'anar sunan shine mai karfin zaki. Bayan soyayya ta yi karfi tsakanin Hurais da Marilat sai iyayensu suka farga, nan fa iyayen kowanne daga cikinsu suka taka masu burki, aka hanasu ganin juna domin babu yadda za'a yi a bari suyi aure tunda akwai gabar asali a tsakanin dangin nasu. A asirce Hurais da Marilat ke haduwa a daji suna tattauna yadda zasu bullo wa wannan al'amari kan soyayyarsu, a karshe dai sai suka yanke shawarar cikin dare su sulale su gudu zuwa wani garin suyi aurensu. Aikuwa cikin tsakiyar dare suka sullae suka bar garin, koda gari ya waye sai aka nemi Hurais da Marilat aka rasa, nan fa rigima mai karfi ta kacame tsakanin dangin mafarauta da kuma dangin makera har ta kaisu ga yakar juna, wanda sai da takai cewa anyi asarar daruruwan rayuka, da kyar sarkin garin ya raba wannan rigima. 186 TASKARNOVELS.COM.NG A karon banza aka kamo Hurais da Marilat acan wani kauye waishi Gabril, a lokacin da suke daf da daura wa kansu aure. Daga wannan rana Hurais da Marilat basu sake ganin juna ba, a dalilin aka ne duk su biyun suka shiga mugun hali suka kwanta cuta, a karshe dai ciwo yakai ciwo rai yayi halinsa duk su biyun suka mutu a kuma rana guda. Marilat ce ta fara mutuwa, aikuwa Hurais na samun labarin mutuwarta sai shima ya hadiyi zuciya ya mutu. Bakin ciki a wurin dangin makera dana mafarauta ba sai an fada ba domin sai da kowannne bangare suka shafe kwanaki talatin suna kuka da bakin ciki na wannan abu daya afku, wannan shine sanadin daya kara zafafa kiyayya da gaba a tsakanin dangin guda biyu. Lokacin da rundunar biyun ta tsaya ana kallon ffaatawar da akeyi tsakanin Hantaru da Rabbasu sai kowa ya cika da tsananin mamaki, domin ba'a taba ganin jarumin da yayi gaba da gaba da Rabbasu ba har ya iya yakatsa ba sai yau, saboda tsananin jarumtakarsa da iya yakinsa. 187 TASKARNOVELS.COM.NG Koda yake shi kansa Hantaru ya raina jarumtakarsa domin bai taba haduwa da jarumi bil'adama kamar Rabbasu ba, kai ko yakinsa da mijin uwar mayu bai bashi tsoro ba kamar wannan gumurzu da yake yi da Rabbasu, domin ya tabbatar da cewa indai aka kara sa'a guda nan gaba sai dai cikin biyi ayi daya, kodai suyi ragas ko kuma daya ya kashe daya. Babban abinda ya tayar wa da Rabbasu hankali shine aduk sa'ar da ya sari jikin Hantaru sai dai yaji kara kal! Takobin nan bata tasiri a jikinsa sai dai wajen daya sara din ya dan kunbura. Shiko Hantaru abinda ya dugunzuma hankalinsa shine ko sau daya ya kasa samun nasarar yankar jikin Rabbasu. Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka hango wani mahayi bisa wani farin doki ya durfafo wajen, tun kafin ya karaso wata irin iska mai karfi ta dinga tarwatsa mutane ba shiri aka buda masa hanya domin an gane kowane ne. Da isowar mahayin wanda ke rike da wata farar sanda sai yayi nuni da sandarsa izuwa ga hantaru da kuma Rabbasu, nan take duk su biyu 188 TASKARNOVELS.COM.NG suka zube kasa sumammu, wato suka yi rabuwar dole ga barin yakar junansu. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part N Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey A sannan ne mahayin dokin ya tsaida dokinsa ya dubi rundunar su Zuhairu da kuma ta su Shuraim yace kowa ya dauki nasa ku tafi gida, na raba wannan rigima a yanzu amman fa bata kare ba, domin za'a yi babbar fafatawa ta karshe nan gaba tsakanin Rabbasu da wannan bakon jarumi a ranar gasar tseren gudu, ta neman auren Gimbiya Larziyya, to nan ne za a yi wannan fafatawar ta karshe. Ko da gama fadin hakan sai mahayin yayi girgiza ya bace bat! Shi da dokinsa, b wani bane 189 TASKARNOVELS.COM.NG wannan mahayin sai kakan Shamilat wato boka Sulbaini ibn Hukaish. Bacewar boka Sulbaini ke da wuya sai ko wanne bangare suka dauke nasu, wato su Shuraim suka dauki Hantaru suka tafi, su kuma Zuhairu suka dauki Rabbasu suka tafi da shi. Lokacin da hantaru ya farfado yana bude idanunsa sai ya tsinci kansa bisa cinyar Shamilat ta zuba mashi idanu tana zubar da hawaye, a gefe daya kuma sai yaga wani dattijo dogo siriri kuma kyakkya a tsaye a kusa da shi kuma wata dattijuwar mace ce sun kura masa idanu suna murmushi gami da zubar da hawaye. Hantaru ya dubi ko wacce kusurwa yaga a cikin wani kyakkyawan daki yake, cikin matukar mamaki ya mike zaune zumbur! Ya dubi Shamilat ya ce yaya aka yi nazo nan, sannan wadannna mutanen su waye? Koda jin wannan tambaya sai Shamilat ta share hawayenta ta ce ya kai dana kayi sani cewa kakana boka Sulbaini ibn Hukaish hine ya zo ya raba yakin da kuke yi da wannan sadaukin saurayin, nan dai Shamilat ta baiwa Hantaru labarin Rabbasu da mahaifinsa Zuhairu da kuma 190 TASKARNOVELS.COM.NG irin gabar dake tsakanin zuri'arsu da ta su Rabbasu. A karshe ta shaida masa cewa boka Sulbaini yayi bayanin cewa za a sake fafatawa da Rabbasu ta hanyar tseren gudun kamo barewa, bisa takarar neman auren Gimbiya Larziyya. Sa'adda da Shamilat ta zo nan a jawabinta sai hantaru ya kuma cika da mamaki ya ce wace kuma gimbiya Larziyya? Kafin Shamilat ta bude bakinta ta bashi amsa sai Shuraim ya riga da cewa ya kai jikana Hantaru ka yi sani cewa ba wata bace Gimbiya Larziyya face yar sarkin garin nan namu Uhairu ibn Sabus, kuma a halin yanzu a gaba daya nahiyar nan babu wata mace mai kyawunta, ya kai jikana kayi sani cewa mahaifiyarka Shamilat ta bamu labarin jarumtakarka data gani da idanunta a yayin tafiyarku tsakanin birnin sarki kusaidu zuwa nan. Hakika kayi gagarumar bajinta irin wacce wani bai taba yi ba, domin fiye da shekaru hamsin baya, babu mai iya ratsawa ta wadannan dazuzzuka ya fita lafiya face ayarin dakaru masu yawa kuma masu karfin sihiri, amman kai gashi kai baka da sihirin komai face na kariya irin wanda muka 191 TASKARNOVELS.COM.NG shayar da mahaifiyarka tun tana karama, shi wannan kariyar kawai kake da shi. Haka dai aka cigaba da fira tsakanin Shuraim da Hantaru suna cikin tsananin farin ciki, daga karshe sai Hantaru ya dubi Shuraim ya ce ya kai kakana yanzu ya ya za a yi naga gimbiya Larziyya? Shuraim yayi murmushi yace wai shin me kake ci ne na baka na zuba? Ka kwantar da hankalinka zaka ga gimbiya Larziyya da idanunka amman sai bayan mun dawo daga gidan mahaifina boka Sulbaini, domin yace da ni lallai mu kaika gidan shi gobe da safe. Koda jin haka sai murna ta kama Shamilat dan dama bata da burin daya wuce ta sadu da boka Sulbaini, ba tre da bata lokaci ba Shuraim da matarsa Shaulat suka shiga hidimar shirya walima ta musamman dan murnar dawowar Shamilat da jikansu Hantaru. Nan take aka yanka rakumi da raguna guda uku, Sannan Shuraim ya aika wasu kuyanginsa kasuwa, suka je suka yi cefane. Nan fa aka shiga dafe dafe da soye-soye, daman tuni an aika da sakon gayyata 192 TASKARNOVELS.COM.NG ga yan uwa da abokan arziki da kuma makwabta. Tun kafin a gama shirye-shiryen jama'a suka fara hallara a gidan Shuraim, nan da nan kuwa gidan ya cika da jama'a, wasu abokan ma na Shuraim rabonsu da zuwa gidan an fi shekara goma, sai da kowa ya zauna a inda aka tanada sai kuyangi suka fara fito da abinci da na sha aka fara walimar, bangaren maza da ban haka na mata da ban. Sai da aka fara walimar annan Shamilat, Shaulat, Shuraim da Hantaru suka fito daga cikin daki suka fara gaisawa da jama'a, Shuraim na gabatar da Shamilat da danta Hantaru ga wadanda basu sansu ba, kuma suma bakin ana gabatar d su ga su Hantaru, ana gaggaisawa. Ana cikin wannan gaggaisawar ne sai Hantaru ya hango wata mace can tsaye, wacce ta rufe fuskarta da mayafi, idanunta kadai ke iya gani, ita dai wannan macen ita kadai ce, bata ci kuma bata shan komai, kuma ya lura da ita cewa Shuraim take satar kallo. Yayi tunani a zuciyarsa ya ce to shin wace ce wannan? Kuma me ya 193 TASKARNOVELS.COM.NG kawota wannan taro, tunda bata damu da komai ba na walima? Hantaru ya tambayi kansa. Bayan gama gaisheshe ne sai Hantaru ya saki wuri shima ya zauna ya fara cin abincin, a lokacin ne sai gaba daya samarin dake wajen suk zo suka lullubeshi suna masu yi masa jinjina bisa gagarumar bajintar da yayi ayau, na fafatawa yaki da Rabbasu. Al'amarin da ya baiwa Hantaru mamaki kenan ya ce wai shin shi wannan Rabbasu har shayinsa ake yi a garin nan? Wani saurayi mai suna Kumais ya ce ai a tarihin jarumtakar Rabbasu a nan grin ba a taba samun gwarzon daya taba tararshi ba, balle har su fafata yaki ba sai kai kadai, kai a takaicema gabadaya nahiyar nan babu kamarsa a sadaukantaka, sannan kuma bashi da

Chapter 8 of 13