Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shekara ashirin kenan ina maka wahala amma shi danka baisan wahalan 98 TASKARNOVELS.COM.NG kaba ko guda tabbas ka cuceni kuma kaci amanata sbd haka nima dole naci amanarka yanzu take zan kashe ka kuma komai daren dadewa saina kashe wannan dan naka na cire kambun nasa, nasa a hanuna na hagu. Kodajin wannan batu sai mahaifina ya yunkura da sauri domin ya bude wannan tsohuwar akwatin nasa amma kafin hannunsa yakai kan akwatin tuni dumbazu ya zare takobinsa ya fille mishi kai nan take mahaifina ya sulale kasa matacce. Batareda bata lokaci ba dumbazu ya dauki wannan tsohuwar akwatin sihirin mahaifina ya tafi ya bazama gari nema na amma duk inda yaje sai ace dashi yanzun nan nabar wajen wato mukayita sabani kenan lokacin dana koma gida na iske gawar mahaifina saina sulale kasa sumamme nan take daya daga cikin almajiran mahaifina mai suna Kusad ya zuba min ruwa na farfado kodana bude idanu na nayi arba da Kusad saina tambaye shi a fusace nace wanene yayiwa uban nan nawa kisan gilla? nan take Kusad ya gayamin cewa shide yaga sa'adda mahaifina ya kira dumbazu cikin turakarsa suka kadaita kuma daga karshe ya jiyo dumbazu na daga murya cikin fushi daga can kuma sai yaji sautin sarar takobi kodajin haka sai kusad ya 99 TASKARNOVELS.COM.NG la6e a bayan kofar turakar kawai sai yaga dumbazu ya fito daga cikin turakar da sauri rikeda akwatin sihirin mahaifina dakuma takobin sa jini na diga a jikin ta. ********************* Mazan Jiya Part 14 #Cigaba Koda gama jin wannan batu saina rushe da matsanacin kuka domin nasamu tabbacin cewa dumbazu ne ya kashe min mahaifina babban abun bakin cikina shine nasan cewa har abada bazan iya daukar fansa ba akan dumbazu domin akwai ranar da mahaifina yace dani yakai dana ko a bayan raina kada ka kuskura kace zakayi kokarin ganin bayan dumbazu domin bazaka taba samun nasara a kansa ba saboda yafika karfin sihiri, kai baka samu komai ba daga cikin ilmina amma zan baka wata kariya wadda babu wani mahaluki dazai iya cutar dakai. 100 TASKARNOVELS.COM.NG Koda naji haka saina dubi mahaifina nace yakai abbana wai shin meyesa kaki ka koyamin ilmin ka na tsafi koda mahaifina yaji wannan tambaya sai idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye suka zubo masa sannan yace kafin mahaifiyarka ta rasu ta rokeni alfarmar kadana koya maka tsafi, domin bincike yanuna cewa idan ka mallaki irin sirrukan tsafina bazaka taba haihuwa ba a duniya niko saina daukar mata wannan alkawari kuma na tabbatar dashi najin haka saina rungume mahaifina muka fashe da kuka har izuwa lokaci mai tsawo tun daga ranar da dumbazu ya kashe mahaifina bamu sake haduwa dashi ba, amma a kullum acikin farautar nema na yake har yagaji da neman ya tafi can wata nahiyar inda yadinga amfani da karfin sihiri yana yakar sarakuna yana mallake dukiyar su da mulkin su a hakane ya mallaki kasashe dayawa duk zamo a karkashin kasa guda mai suna kailus daidai da rana daya sarki dumbazu bai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba saboda kawai rashin samun daman hallakani, a kullum a cikin aiko aljanu da sadaukan bil'adama yake domin suzo su hallakani yakai hibru kayi sani duk lokacin dakaga kana samun nasara wajen kare 101 TASKARNOVELS.COM.NG rayuwata aduk sa'adda aka kawo farmaki ba takobin ka bane take baka sa'a face kambun tsafin dake jikin ka na hagu wannan shine asalin yadda gaba ta kullu tsakani na da sarki dumbazu ina mai tabbatar muku da cewa babu yadda za'ayi kuje birnin kailus kuci dumbazu da yaki face nayi abu guda wannan abu kuwa bakomai bane saidai nacire kambun tsafina nabaka kai hibru kasa a hannun ka sannan kaje ka tari dumbazu tabbas zaka samu nasara akan sa saidai ni daku munyi bankwana bazaku dawo ku sameni a raye ba domin ka'idar wannan kambu shine duk wanda yadaura shi a hannunsa to duk ranar daya cire shi bazai kara kwana uku a duniyar nan ba. Koda Sarki hubru yazo nan a zancen sai hankalin mu ya dugunzuma na dubi sarki hubru nace ya shugabana ina dalilin salwantar da rayuwar ka akan yarka. Kodajin haka sai Sarki hubaru ya zubarda hawaye sannan yace yakai sadauki dan sadaukai kayi sani cewa nifa sarki nayi arziki kuma na haihu duk abinda ake nema a duniya 102 TASKARNOVELS.COM.NG na same shi haka kuma shekaruna sun tafi yata fa yanzu ne take ganiyar kuruciyar ta SBD meye zan bari rayuwarta ta salwanta alhali kadai gareni idan na mutu itama ta mutu babu wani wanda za'a kalla a tuna damu idan bakuje kun ceto rayuwarta ba za ayi biyu babu domin bakin cikin rashin tane zai kashe ni anan ita kuma sarki dumbazu ne zai kasheta a can yanzu yanzu bada bata lokaci ba nakeso kuyi shiri kutafi izuwa ga bokana domin ya sadaku da hadimin dazai kaiku fadar sarki dumbazu domin ku yake shi amma kafun sannan ina mai dada jaddada muku alkwarin dake tsakanin ku kai hibru amanar yata na wajen ka domin kaine zaka aure ta kai kuma maharaz na damka amanar kasata da jama'ah ta a gurin ka domin kai zaka gaji sarauta ta gama fadin hakan keda wuya sai sarki hubru ya cire kambun dake hannunsa na hagu ya miko min hanuna na karkarwa na karbi kambun nasa a hanuna ina karba saina saka shi a hanuna wannan shine babban kuskure danayi a rayuwa ta domin na manta cewa duk wanda yadaura wannan kambu toh duk ranar daya cire shi bazai haura kwanaki hudu ba a duniya nan take mukayi bankwana da sarki hubaru yana kuka muna kuka domin munsan cewa mun 103 TASKARNOVELS.COM.NG rabu har abada bazamu sake ganin juna ba kaico babu ranar bakin ciki wacce tafi ranar rabuwa da masoyi tabbas mun shaku da sarki hubru koma munyi imani cewa yana matukar kaunar mu kamar yadda muke kaunarsa amma gashi munaji muna gani zai rasa rayuwar sa bamuda yadda zamuyi mu kareshi lokocin damuka baro fadar sarki hubaru muka nufi kofar gidan shaburus Ibn mukaibar rana ta fadi magariba ta doso kai muna isa kofar gidan muka iske boka shabarus a tsaye yana jiran isowar mu koda mukazo dab dashi sai mukaga idanunsa cike da hawaye yana kallon mu kawai alamarin daya karya mana zuciya kenan jikin mu ya karayin sanyi boka shabarus ya dube mu cikin sanyin murya yace lale da manyan gobe hakika kun baro masoyina a cikin mugun hali inda nasan wannan rana zatazo ta riske ni daban kawo iyanzu ba kuyi sani cewa a duniya banida masoyi tamkar sarki hubaru amma gashi an wayi gari inaji ina gani rayuwarsa zata salwanta babu abinda zan iyayi don kareshi yanzu bada bata lokaci ba zan hadaku da babban hadimi na wadda zai kaiku fadar sarki dumbazu acikin kwana goma sha daya maimakon tafiyar kwanaki saba'in da bakwai bisa rakumi ko doki 104 TASKARNOVELS.COM.NG batare da an yada zango ba koda gama fadin haka sai boka shabarus ya hade tafin hannunsa waje guda ya kama karanta wadansu kalmomin tsafi yana tofawa akan tafin hannun daga can sai yayi nuni izuwa kan kasa nan take kasa ta dare saiga wani narkeken aljani ya ratso ta cikin kasar ya bayyana a samanta aljanin nada suffa irinta tsuntsaye saidai kansa da wuyansa irin na biladama ne kuma fukafukansa guda goma sha takwas ne cikin rusunawa aljanin ya dukar da kai kasa ga boka shubarus ya kwashi gaisuwa shabarus ya dube shi yace angaishe ka mara'il labarus yakai mara'il labarus kasani cewa yaune ranar karshen aikin ka dani domin abune mawuyaci kudawo ku riskeni a raye. Koda jin wannan sai hankali aljani mara'il labarus ya dugunzuma ya dubi boka shabarus cikin damuwa yace ya shugabana ina dalilin ka na fadan haka boka shabarus yace yakai babban hadimi na kayi sani cewa zaka dauki sadauki hibru tare da boka maharaz ka tafida su izuwa fadar sarki dumbazu domin su yakeshi su kawar dashi, kodajin haka sai aljani Mara'il labarus yayi tsalle ya tumu da kasa ya kama kuka yana mai cewa haba ya shugabana laifin maina maka kakeso ka hallakani inani ina zuwa fadar 105 TASKARNOVELS.COM.NG shugaban bokayen duniya domin a yake shi, na roke ka daka yafemin wannan aikin kanemi wani yayi shi amma bani ba. Kodajin haka sai boka shabarus ya dakawa aljani mara'il labarus tsawa yace dolene kai zakayi wannan aikin domin kai kadai ne zaka iya idan kuma kace bazaka yiba yanzu take anan zan hallakaka kayi sani cewa sadauki hibru na tareda kambun tsafin sarki hubaru don haka babu wani tsautsayi dazai sa ku halaka saidai zaku iya shan bakar wahala, maza ka kwashe su ku tafi kuma ka tabbatar dacewa kun isa can a kwanakin dasuka gaza ashirin tabbas bazaku dawo ku riske niba domin a ranar da masoyina zai mutu nima zan mutu, koda gama fadin haka sai boka shabarus ya juya ya shige gidansa, koda faruwar haka sai aljani mara'il labarus ya suremu nida maharaz sannan ya bude fukafukansa yayi sama sannan ya fara tsala gudu nagaban kwatance muna gifta giza gizai tambar wucewar tauraruwa mai wutsiya saida muka shafe kwanaki tamkar wucewar tauraruwa mai wutsiya, sai da muka kwashe kwana goma sha takwas muna tafiya bisa aljani mara'il labarus a sararin samaniya batareda yasauko kasa ba don ya huta nikam a rayuwata 106 TASKARNOVELS.COM.NG bantaba ganin aljani mai juriyar wahala ba tamkar aljani mara'il labarus baisan yunwa ba baisan ishirwa ba balle lalaci a yammacin kwana na goma sha takwas dinne muka hango fadar birnin kailus daga can nesa kadan a gaban mu. Wohoho!! tabbas fadar ta isa da akirawota da matsayin aljannar duniya domin gavadaya ginin ta da gilashin lu'u-lu'u akayi shi babu abinda zaibawa mutum mamaki face ganin yadda aka gina gabadaya birnin na kailus a tsakiyar wani kogi abinda bamu saniba shine aljanu ne suka zuba tubalin ginin harya fito saman kogin nan duk inda zaka taka jauhar ne da zabar amma indaga sama ka taho kana iya ganin yadda ruwan kogin ya zagaye birnin gabadaya, aljani mara'il labarus bai sauko kasa ba saida muka iso dabda birnin sannan ya dira a bakin kofar garin babu kowa a bakin kofar balle muyi artabu damasu gadi kuma sai muka iske kofar a bude wanwar sannan mukaji garin yayi tsit tamkar babu wani abu mai rai acikin sa, alamarin dayayi matukar bamu mamaki kenan batareda fargabar komai ba muka sauko kasa daga kan aljani mara'il labarus na wuce gaba ina mai yafuo maharaz da aljani mara'il labarus da 107 TASKARNOVELS.COM.NG hanuna ina mai cewa kubiyo ni a baya, a lokacin ne na zare takobi na, na cigaba da tafiya ina mai duba kowace kusurwa kuma ina kasa kunne kozanji motsin wani abu daka iya kawo mana farmaki sumame saida muka shafe sa'a shida muna tafiya a cikin birnin kailus ko bera bamu ganiba rayayye duk mutanen garin da dabbobin su sun kame sun zamo gumaka babu abunda ke motsi hatta kasuwa damuka ratsa ta cikin ta mukaga mutane sunata harkoki amma kowa a kame yake yazamo gunki, wasu suna musayar kudi da kaya wasu kuma bakunan su a bude alamar cewa magana sukeyi hakadai muka cigaba da tafiya har muka iso kofar fadar birnin anan bamuga komai ba ko gunkin dakaru babu ma balle muji tsoron cewa zasu iya tashi akoda yaushe su farmana, kai tsaye muka kunna kai izuwa fadar har muka isa inda karagar sarki take amma bamuga kowa ba bamuga wani abu mai rai ba, kuma duk kofofin fadar nan a bude suke bamu riski guda daya a kulle ba dazuwan mu gaban karagar mulki sai muka dubi junan mu mukayi ajiyar zuciya a tare na dubi maharaz da aljani mara'il labarus nace yaku abokan tafiya kuyi sani cewa ruwa baya tsami banza duk yadda akayi an sanda zuwan mu kuma an yi 108 TASKARNOVELS.COM.NG mana tanadi, nikam ina ganin cewa wani tuggun aka shirya mana shiyasa bamuga komai da kowa ba kafun nagama rufe bakina sai kawai mukaji kofofin fadar na rufe kansu daya bayan daya sannan sai mukaji an bushe da mahaukaciyar dariya amma bama iya ganin mai dariyar nan nan fa maharaz yafara amfani da karfin sihirin sa domin yaga mai yin dariyar amma sai abu ya gagara nan take cikin mu ya duri ruwa duk da na tuna cewa ina tareda kambun tsafi wanda sarki hubru yabani amman sai naji banida nutsuwa da yadda dakai kwatsam sai mukaga wadansu dakarun aljanu ma'abota kwarjini daban tsoro sun bayyana dayawa ba adadi sunyi mana kawanya suna rikeda muggan makamai wadanda ko a labari bamu tabajin irinsu ba sbd razanar damukayi bamu san sa'adda muka kankame juna ba mu ukun, abin mamakin ma shine aljani mara'il labarus yafimu firgicewa domin duk ilahirin gabban jikinsa karkarwa sukeyi kamar wadda ake zukar jinin jikinsa, bazato ba tsammani sai mukaga sarki dumbazu ya bayyana tsulum akan karagar mulkin sa yana kyakyata dariyar mugunta sannan saiga sauran dakaru na bil'adama da duk fadawan sa sun bayyana suma 109 TASKARNOVELS.COM.NG sunayi mana dariya, al'amarin kashe mana jiki kenan mukaji nadama tazo mana bisa kawo kanmu izuwa wannan birni domin mun san cewa mun sayi ajalin mune da kudinmu, lokaci guda sarki dumbazu ya tsuke bakinsa yabar dariyar fadar tasa keyin tsit sarki dumbazu ya dube mu, mu ukun yace yanzu ku uku kacal aka turo ku yakeni wani haukane yasa kuke tunanin zaku iya karawa dani hakika yaro baisan wuta ba, yakai hibru kayi sannin cewa nayi nisa a halwar tsafi sanina ya wuce na maigidana mahaifin sarki hubru don haka wannan kambun tsafi daya baka ka daura a hannun ka bazai maka tasirin komai ba domin ka gamsu da bayani na a yanxu zan nuna maka wani abu, koda gama fadin haka sai sarki dumbazu ya bude damtsen sa na dama saiga irin wannan kambun tsafi wadda sarki hubru yabaiwa hibru nan take sarki dumbazu ya cire kambun ya jefa shi a cikin wani kasko take kambun nan ya kone kurmus, sarki dumbazu yasake kyalkyalewa da dariyar mugunta a karo sannan yace to kaga yadda nayi da irin kambun nan na hannunka ko dan haka wannan kambun darajar su daya da takarda banza a wajena amma idan baka yadda ba zakaga zahiri a yanzu, kafin na bude baki 110 TASKARNOVELS.COM.NG nace wani abu tuni sarki dumbazu ya dubi waddan nan zakakuran aljanu nasa yace ku afka musu naga iyakar jarumtakar su, nan take aljanun nan sukayi mana rubdugu nan fa aljanun nan suka haumu da sara da suka maharaz ya tare su da karfin sihirinsa yana kare harin su shima aljani mara'il labarus niko da karfin damtsena na taresu amma sai akayi min kwab daya na zube a kasa sumamme ko dakika arba'in ba'ayi ba aljanun sarki dumbazu sukayi fatafata da jikin aljani mara'il labaru, aljani mara'il labarus ya fadi kasa magashiyam ko ina a jikinsa yazamo kofar fitar da jini kawai maharaz ne yadan tabuka wani abu domin yasamu dakika kusan dari uku da tamanin yana fafatawa da aljanun nan sannan suka karya karfin sihirin sa sukayi masa sara tamanin ya baje a kasa ko shurawa bayayi. Lokacin dana farfado idanuna suka bude saina tsinci kaina a wata fadar a daure a jikin dirkar gini wata irin sarkar tsafice ta daureni koyaya na motsa sai naji sarkar ta kara matseni bisa dole na hakura na daina motsi bisa mamaki sai naga abokina maharaz a daure kusa dani yana numfashi sama sama kaida gani kasan cewa akan gangarar mutuwa yake, raunukan jikinsa 111 TASKARNOVELS.COM.NG guda tamanin na digar da jini shiko aljani mara'il labarus babu shima a wajen alamarin daya tabbatar min da cewa aljani mara'il labarus ya mutu kenan, bazato ba tsammani sai naga sarki dumbazu ya riko hannun gimbiya sahira yar sarky hubru sun tafo gareni sunata hira da dariya cikin nishadi nan fa na cika da tsananin mamaki nace a zuciyata saboda me sahira zata saki jiki da babban makiyin ubanta wadda a halin yanzu ya rabata da ubanta kuma yazamo sanadin ajalin sa sarki dumbazu yakai gimbiya sahira izuwa kan wata kujera ta alfarma ya zaunar da ita sannan ya tafo gareni saida yazo dab dani yadda muna iya jin numfashin juna sannan yace dani ga masoyiyar ka can tazamo tawa a yau zan sadaku da ita sannan na cika alkawari na wato na kasheta a gaban idanun ka tunda mahaifinta ya saba ka'ida ta bai baku kansa kun kawomun ba, bisa mamaki sarki dumbazu yaga na dubeshi nayi murmushi sannan nace matukar bil'adama na numfashi a doron kasa ako yaushe to baya yanke kauna da kubuta daga kowani irin bala'i, ya kai wannan azzalumin sarki maci amana kayi sani cewa lallai karshen lalacewa kuma har abada burinka bazai cika ba idan har amana da 112 TASKARNOVELS.COM.NG soyayya sun kasance ababen gaskiya lallai bazaka samu nasara akan gimbiya sahira ba. Kodajin wannan batu sai sarki dumbazu ya kyalkyale da dariyar mugunta yace yanzu kai a tunanin ka har akwai wani tsautsayi dazai sa nakasa samun nasaran abinda nasa a gaba duk duniya fa babu sadauki mai karfin damtse na babu matsafi mai karfin sihiri na wanene ya isa yaja dani nan take dumbazu ya shiga yiwa kansa kirari yana ihu da kururuwa a gabana yana cikin yin hakan ne na lura da wani guru dake kugunsa wadda ke dauke da layun tsafi akalla guda dubu, alkyabbar dake jikin sane ta rufe gurun amma saboda yana juyi da daga hannaye a gaban idona sai idanuna suka hango wannan gurun, cikin shammaci da zafin nama na sunkuya na kaiwa gurun nan chafka da bakina aiko sai nayi sa'a na chafke laya guda da hakorana na gatsa layar ta fashe take gurun nan ya bace bat itama sarkar tsafin da aka daure mu ta bace bat itama. Cikin zafin nama na zare takobina, haka kuma sai aba daya dakarun aljanun nan sarku Dumbazu sai naga suna narkewa kamar ana narka man shanu a kasko, kafin kiftawar ido duk sun zama ruwa a kasa. Su kuwa fadawan 113 TASKARNOVELS.COM.NG sarki Dumbazu sai duk suka firgice suka mimmike tsaye jiki na kyarma. Sarki Dumbazu ya tsaya kyam a waje daya ko motsi bai yi ba. Kawai sai ya suddar da kansa kasa yana mai zubar da hawaye, ni dai har wannan lokacin ina rike da takobina banyi yunkurin yin komai ba, daga can sai Sarki Dumbazu ya dago da kai ya dubeni cikin tsananin fushi fuskar nan tasa a murtuke, a wannan lokacin ne naga gimbiya Sahira ta mike tsaye zumbur tana kalle kalle a cikin fadar kuma tana kallon jikinta, ga dukkan alamu ta dawo cikin hayyacinta na ce a cikin zuciyata. Wato a da an juyar mata da tunaninta ta manta da kanta da kuma komai nata. Sarki Dumbazu ya kura mata idanu har wannan lokacin hawaye bai daina zub daga cikin idanunsa ba, kawai sai ya bude baki da kyar ya ce "Ya kai yaro hakika ka cuceni, ka ruguza Mani tsafin dana kwashe sjekaru da dama ina shirya shi, yanzu bani da suran sirrin tsafi a tare da ni, lallai sai na yi maka kisan gilla irin wanda ba'a taba yi ma wani a wannan duniyar ba, kayi sani cewa ko bani da sirrin tsafi ai in da na karfin damtse wanda babu kmaarsa a kaf nahiyar nan, dan haka maza bisa kanka yi kokari ka cice rayuwarka na gani. Cikin wani irin azababben 114 TASKARNOVELS.COM.NG zafin nama sarki Dumbazu ya zare takobinsa, takubbanma guda biyu ne ya kawo mani wasu tagwayen mugayen sara, duk da nayi sauri na kauce amman sai da takubban nan suka zarge rigar dake jikina, kuma suk yi mani dogon yanka akan kirjina har jini yana tsartuwa. Kawai sai na tafi da baya taga-taga zan fadi kasa ana layi. Koda Dumbazu yaga ya samu wannan gagarumar nasara sai ya sake dako tsalle domin ya dura a kaina da nufin ya gididdiba sassan jikina, amman sai na yunkura cikin karfin hali da matukar juriya na yi tsalle can gefe guda yayinda takubban nasa suka sari wata kujera take ta ragargaje. Nan fa muka ci gaba da azababben yaki yayi ta kokarin ya gididdibani ni kuma na himmatu ina mai kare hare-harensa, ina zuluyewa gami da kaucewa amman ko kadan na saka mayar da martani ko da sau daya ne kuwa. Domin zafin namansa da karfin saransa sun wuce misalin ta yadda bazan iya taresu ba har na mayar masa da martani. Sai da muka shafe sa'a tara muna wannan bakin Artabu Dumbazu ya kasa samun nasara a kain 115 TASKARNOVELS.COM.NG ni ma na kasa maida mashi da martani koda sau daya ne kuwa, hakika duk wanda ya fika jarumta to fa ya fika har abada, domin baka isa ka kamoshi ba. Koda sa'a tara ta cika muna wannan gumurzu sai gajiya ta riskeni har ya zamana cewa da kyar nake iya daga takobina na kare saran da Dumbazu yake kawo mani, shikuwa ko kadan bai gajiba domin kmar ma a sannan ne ya fara gumurzun. Yayi da yaga na fara sarewa sai ya cika da murna ya ci gaba da kawo mani hari a sannu yana murmushin mugunta, sai da ya kaini jikin bango ya tareni sannan ya buge takobina ta fadi kasa sannan ya labta mani wawan sara a cinya, ban san sa'ar da na kwarara uban ihu ba tare da durkushewa a kasa ba cinyata na zubar da jini. Dumbazu ya sake dankara mani wani saran a dayar cinyar tawa na zube kasa wanwar a matukar galabaice nan fa idanuna suka fara gani dishi-dishi. Dumbazu ya sake dag takobinsa da nufin ya fille mani kai, amman kawai sai naga hannun nashi ya sandare ya kasa labta mani saran, da kyar da sidin goshi na juya baya kawai sai naga wuka ta nutse a tsakiyar gdon bayansa 116 TASKARNOVELS.COM.NG jini na burbulowa ta tsakiyar girjinsa, tsaye a gaban Dumbazu gimbiya Sahira ce jikinta na karkarwa, a sannna ne na gane cewa ita ce tayi ta maza ta rugo ta caka wa Dumbazu uka a gadon bayansa. Nan take Dumbazu ya sullae kasa matacce ko shurawa bai yi ba, a sannan ne nima idanuna suka rufe na sume a wajen. Lokacin dana farfaɗo sai nayi arba da gimbiya Sahira tsugunne a gabana ta rusar kuka, raunikan dake jikin cinyoyina an saka masu magani, a gefe daya kusa da ni kuma Maharaz ne a kwance har wannan lokaci yana numfashi da yar duk da cewa an sa masa magank a jikin raunikan nasa. Koda na daga kina na dubi gabas da yamma, kudu da arewa sai naga ashe gaba daya mutanen birnin Karlus ne suka rufemu sun tsura mana idanu suna kallonmu kawai, a gefe daya kuma fadawan Sarki Dumbazu ne a tsaitsaye sunyi tsuru-tsuru kamar ace kyet su fice da gudu. Ashe duk mamakinmu suke yi yadda akayi har muka iya ffaatawa da sarkinsu, har ma kuma muka samu nasarar hallaka shi. 117 TASKARNOVELS.COM.NG Saida muka yi kwana arba'in muna jiyyar raunikan mu a birnin Karlus ni da Maharaz sannan muka warware, amman duk da haka bamu warke sumul ba, sai a sannan hankulanmu suka dawo jikinmu har na samu damar baiwa gimbiya Sahira llabarin dukkan abinda ya faru tsaninmu da mahaifinta gami da wasiyar da ya bamu mu shaida mata. Koda gimbiya Sahira ta gama jin bayanina sai ta fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni tana mai ci gana da kuka. Da kyar na lallasheta daga can sai ta dubeni ta ce da ni tana so tayi wata magana ta sirri da Maharaz. Cikin matukar mamaki na dubeta nace da ita "Ke kuwa wace irin magana ce wannan da zaki yi da abokina wacce bakya so na ji? Koda taji wannan tambaya ai hawaye ya zubo mata ta ce ka yi hakuri ya kai mijina na gobe, wannan magana da zanyi da maharaz sakone daga mahaifina zuwa gareshi, kuma ya gargadeni da cewa komai rintsi da tsanani kada na kuskura na sanar d kai. Koda gama fadin haka sai gimbiya Sahira ta tafi wajen maharaz tayi masa rada a kunnensa, 118 TASKARNOVELS.COM.NG gabadaya jama'ar dake wajen babu wanda yaji abinda ta ce masa, faruwar hakan keda wuya sai kawai muka ga Aljani Mara'il Labarus ya sakko daga sama tare da tsirga a gabanmu, al'amarin da yayi matukar bamu mamaki kenan domin mu a zatonmu ya dade da mutuwa, hakan yasa ko neman inda gawarsa take ba muyi ba. Yayin da Aljani mara'il labarus yaga muna mamaki da ganinsa a raye sai ya bmau labarin cewar ai dama dogon suma yayi, lokacin daya farfado sai yaga babu kowa a wannan fada ta farko da muka fara shiga, dan haka sai ya tashi da yar ya tafi can bayan birnin Karlus ya boye knsa a cikin daji yayita jinya har saida ya warke. Koda jin wannan labari sai muka cika da farin ciki, a daidai wannan lokaci ne wazirin sarki Dumbazu ya zo gaba ya tsaya tare da cewa ya kai wannan sadauki mai abun mamaki, tunda har ka samu nasarar kashe sarkinmu, yanzu abinda ya kamata kayi shine ka maye mana girbinsa. Da jin wannan batu sai nayi murmushi n ce ai ni bnai da bukatar mulki ko dukiya, abinda nazo nema na samu, kuma ba komai bane face masoyiyata kawai, sai nayi nuni izuwa ga gimbiya Sahira, ita kuwa sai ta rugo gareni 119 TASKARNOVELS.COM.NG cikin farin ciki gami da murna ta rungume ni. Daga nan sai na dubi wazirin Dumbazu nace da shi mukam yanzu mun kammala aikin da aka turomu yi a birninku, saboda haka muna yi maku sallama sai ku zabi shugabanku a tsakaninku. Gama fadin hakan keda wuya sai Aljani mara'il labarus ya rankwafa bayansa muka hau mu uku muka zauna, sannan ya bude fuka fukansa guda 18 yayi sama da mu, kafin kiftawar idanu mun bace bat a cikin gajimare. Tun daga wannan rana sai naga abokina Maharaz ya daina sakin jiki da ni, ya daina yin hira da ni, hatta abinci baya yarda muci tare, al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na rasa binda ke mani dadi a duniya, a duk sa'ar dana tambayeshi shin ko nayi masa wani laifi ne? Sai yayi murmushi ya ce sam banyi masa laifin komai ba. Tsawon kwanaki 17 da muka shafe muna tafiya a sararin samaniya daga birnin Karlus zuwa birninmu na darul mahabur bamu yi hirar rabin sa'a ba nida Maharaz. Muna isa birnin darul mahabur muka iske sarki Hubaru da boka karlus sun mutu an binne su, muna kuka muka 120 TASKARNOVELS.COM.NG isa inda kabarinsu yake, sai da muka shafe sa'a uku cur muna a gaban karin muna kuka sannan da kyar aka kawar damu daga bakin kabarin aka tafi da mu izuwa fada. Kashegari da safe aka dora Maharaz akan karagar sarki Hubaru kuma aka daura aurensa da Husuna yar sarki Hubaru, bayan an gama bikin nadin Sarki Maharaz ne aka daura aurena da gimbiya Sahira sannan ya bani sarautar sarkin yakinsa, na cigaba da yin bauta gami da biyayya ga sarki Maharaz tsawon shekaru, kuma duk bukatar da ya zo mani da ita ina binta ga dukkan iyakar karfina ban taba nuna masa cewa na gajiya ba, na sha bakar wahala akan biyan bukatunsa musamman a lokacin da suka rasa haihuwa shida matarsa Husuna, domin sai da na kusa rasa rayuwata a kakarina na nemo masu maganin haihuwa. Duk wannan iyayya da bauta da nake yiwa sarki Maharaz bai taba yi mnai godiya ko sau daya ba, kuma gabadaya abotarmu da kusancinmu sai ya yanke su, ko magana bana samun damar yi da shi face in mun zauna dakin gani tare da sauran fadawa idan bukatar hakan ta taso. Har yau har gobe ban san dalilin da yasa sarki Maharaz ya nisanta da ni ba. Yake gimbiya Mulaifa wannan shine 121 TASKARNOVELS.COM.NG tarihin rayuwata data mahaifinki da kuma dangantakar dake tsakanina da shi. Masu iya magana suna cewa ranar wanka ba'a boyon cibi, yanzu dai gani ga shi kuma yace zai fada mani wani sirri wanda

Chapter 5 of 13