fara kama
wannan barewa da ta rabe biyu a hannunsu.
Cikin hadin baki alkalan gasar suka ce a tare
kuma lokaci guda suka kama barewar.
Koda jin haka sai wuri ya yamutse da shewa
murane suka hau fadin anyi ragas, anyi ragas...
Nan fa dajin ya rude da hayaniya, sai da aka
busa kaho sannan aka yi tsit tamkar mutuwa ta
gifta, sarki ya dubi sauran jama'a ya ce
sakamakon wannan gasa shine anyi ragas
tsakanin Sadauki Rabbasu mai wakiltar zuri'ar
mafarauta da Sadauki Hantaru mai wakiltar
zuri'ar makera, saboda haka za a sake yin
wannan gasa a shekara mai zuwa.
Da jin haka sai jama'a suka barke da shewa gami
da murna.
Al'amarin Sadauki Rabbasu da zuri'arsa kuwa
sai suka cika da tsananin bakin cika, Rabbasu
245
TASKARNOVELS.COM.NG
bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba
saboda tsananin takaici ya durkushe kasa ya
kafa kansa a kasa.
Shi kuwa Hantaru dama yasan cewa babu
wanda zai samu nasara a wannan gasa tsakanin
shi da Rabbasu, domin boka Sulbaini ya fada
masa cewa sai sunyi wannan gasa sau uku babu
mai nasara, wanda a karshe dole ne a tura su
neman takobin Saiful Lujara dan kawo karshen
gasar gabadaya a birnin na Darul Habur.
Nan take Hantaru ya yanke jiki ya fadi kasa
saboda tsananin galabaita, cikin gaggawa aka zo
aka dauek shi aka sanya shi cikin kekn doki aka
tafi da shi, saboda kumburin jiki da duruwar jini
sai da aka kwana uku ana jinyar Hantaru sai a
sannan jinin daya taru a fuskarsa da kuma
jikinsa ya bace.
Salimat ce tayita gasa masa jiki da ruwan dumi,
kuma tana dafa masa magani yana sha, kafin
jikin Hantaru ya dawo daidai a kullum idan ta
dubw shi sai ta fashe da kuka saboda ganin irin
tsananin wahalar da ya sha, hakan ne ma yasa ta
tubure akan ba zata yarda a sake yin wannan
gasa da Hantaru ba, sai dai su tattara yanasu-ya
246
TASKARNOVELS.COM.NG
nasu su koma can birnin Kisra gidan mijinta. Da
kyar d sidin goshi su Shuraim suka lallabata ta
yard zata sake zama a garin har shekara ta
zagayo.
Wannan shine abinda ya faru a can birnin Darul
Habur bayan anyi gasar tseren gudun barewa ta
neman aure da aka saba yi duk shekara.
MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part R
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
*******
Acan birnin Kisra kuwa tun daga ranar da
Shamilat da Hantaru suka bar gari sai sarki
kusaidu ya shiga cikin wani mugun hali da bakin
247
TASKARNOVELS.COM.NG
ciki, sannan yana yawan kuka bisa yawan begen
yarima Hantaru da yake yi, abu kamar wasa sai
sarki kusaidu ya kwanta ciwo kuma aka rasa
abinda ke damunsa, domin sam bai fada wa
kowa abinda ke damunsa ba.
Lokacin da ya fahimci cewa idn ya kara jimawa
a wannan hali to tabbas rayuwarsa zata
salwanta, sai ya kira wadansu amintattun
bayinsa su uku ya basu wasika yace suyi shiri su
tafi can birnin darul Habur su kai wa matarshi
wannan wasika.
Nan da nan kuwa suk yi shiri suka kama hanya a
sirrance ba tare da kowa ya sani ba, dalilin da
yasa sarki Kusaidu bai yi shawara da boka
Ardusa ba wannan karon shine yaga wani abu
da yayi matukar daure masa kai, har yaji cewar
ba zai kara yarda da shi ba har sai ya tabbatar
da abinda yake zargi.
Masu iya magana sunce shi laifi kuikuyo ne har
abada yana bin mai shi, duk abinda mutum ke yi
a boye komai daren dadewa sai asirinsa ya tonu,
musamman abinda ya shafi cin amana da danne
hakkin wani.
248
TASKARNOVELS.COM.NG
Wata rana da tsakar dare sarki kusaidu na
kwance a dakin uwar gidansa suna bacci, sai
kawai wani dan mitsitsin tsuntsu ya shigo
turakar ya tsaya a saman taga daidai saitin
Zarifa yayi wani irin kuka tamkar yana raira
waka. Koda jin wannan tsutsun sai Zarifa ta
farka daga baccin da take yi kamar dama can
idonta biyu ba baccin take yi ba, da mikewarta
zaune sai ta dubi sarki Kusaidu ta tabbatar dda
cewa bacci yake tunda gashi har yana sharar
munshari, a hankali cikin sanda ta sakko daga
saman gadon ta cire rigar baccin dake jikinta
sannan ta saka tufafinta masu kyau ta nufi bakin
kofa.
Ashe sarki Kusaidu ba bacci yake ba, domin tun
daga ranar da su Hantaru suka tafi birnin Darul
Habur bai sake samun damar yin bacci daddare
ba, sai dai kawai ya kwanta yayi lamo kamar
mai yin baccin amman ba baccin yake iya wa ba,
zuciyarsa cike da tunanin gami da begen dansa
yarima Hantaru da kuma matarsa Salimat. Duk
motsin da Zarifa ta ke yi yana jinta, kuma wani
lokaci har bude idonsa yake yi kadan ya kalleta,
da zarar yaga ta juyo sai yayi maza ya rufe idon
nasa.
249
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Zarifa ta isa bakin kofar turakar, sai
ta tsaya cak, ta juyo ta kura wa fuskar sarki
Kusaidu idanu ta sake tabbatar da cewa bacci
yake yi, sai da ta bata dakika sama da dari shida
a kofr sannan daga bisani ta bude kofar a
hankali ta fice daga cikin turakar gabadaya.
A lokacin ne shima wannan mitsitsin tsuntsun
da ya shigo wannan turakar ya fice da sauri,
koda jin ficewar tsuntsun sai sarki kusaidu ya
leka waje ta cikin taga, duk da cewa dare ne gari
yayi duhu amman duk da haka sarki kusaidu ya
samu damar hango wannan mitsitsin tsuntsun
ta cikin ragowar hasken farin wata, lokacin da
mitsitsin tsuntsun ya rikide ya zama wani aljani,
bisa ga mamakinsa kuma sai yaga matarsa
Zarifa ta haye bayan aljanin ya bude fuka
fukansa ya tashi da ita sama, kafin kifta ido sun
kule a sararin samaniya sun bace bat!
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu
ya cika da tsananin mamaki, kuma hankalinsa
ya dugunzuma ainun ya tambayi kansa a cikin
zuciyarsa ya ce ina matata Zarifa ta tafi a cikin
wannan dare, sannan wane ne ya turo wannan
aljanin daya dauketa? Sarki Kusaidu ya kasa
baiwa kansa amsar wadannan tambayoyi dan
250
TASKARNOVELS.COM.NG
haka sai yayi shiru ya shiga sabon tunani, daga
can sai yayi ajiyar zuciya ce hakika duk yadda
aka yo matata Zarifa tana cin amanata ne,
alhalin ni ina zaune da ita da zuciya daya, kuma
ina kaunarta bilhakki, amman babu komai,
koma mene ne take aikatawa a boye da sannu
zan sani.
Haka dai sarki Kusaidu ya koma ya kwanta ya ci
gaba da tunanin su Hantaru da Salimat, bayan
kamar rabin sa'a da kwnaciyarsa sai yaji an
bude kofar an shigo, bai bude idanunsa ba,
kuma bai yi wani motsi ba sai kawai ya ci gaba
da kwarara munshari. A lokacin ne yaji an hawo
gadon an kwanta, kamshin turaren data saba
sakawa a jikinta ne ya sa ya gane matarsa ce
Zarifa ta dawo.
Nan take sarki Kusaidu yaji wani azabben bakin
ciki ya shigeshi tamkar ya hadiyi zuciya ya
mutu, amman sai ya danne zuciyar tasa ya
hakura.
Kashegari da safe sarki kusaidu bai nuna wa
Zarifa wata damuwa ba, sai ma ya tashi da farin
ciki yana mai cewa zarifa shi fa yau ya tashi da
sha'awar fita rangadi.
251
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Zarifa ta yi caraf ta ce aiko
nima ina sha'awar fita rangadi sai mu fita tare
kenan?
Sarki Kusaidu ya dubeta cikin damuwa ya ce a'a
gwara dai kiyi zamanki a gida domin wannan
rangadin da zan fita ni kadai zan fita ba tare da
dakaru ba, kuma zan iya yin nisan zango, kinga
Kenan bani da tabbacin zan iya kare lafiyarki
idan kika biyo ni.
Cikin matukar mamaki Zarifa ta ce kai kuwa
saboda me zaka fita rangadi kao kadai, shin ka
mnta ne cewa kai sarki ne? Baka tsoron
magauta su kawo maka hari?
Sarki Kusaidu yayi dariya ya ce ai ni bana tsoron
harin magauta domin na tabbatar da cewa ina
tare da tsarin boka Ardusa, ke nake ji saboda
baki da tsari irin nawa.
Koda jin wannan batu sai Zarifa ta yi shiru bata
kara tankawa ba.
Ba tare da bata wani lokaci ba, sarki Kusaidu ayi
shiri shi kadai, cikin batar da kammani ya fice
daga cikin birnin Kisra. Sarki Kusaidu ya durfafi
wata hanya da zata sadashi da wani kauye da
252
TASKARNOVELS.COM.NG
ake kira da Raufal, daga cikin birnin Kisra zuwa
kauyen Raufal tafiya ce ta rabin sa'a kacal,
amman sai sarki ya zaburi dokinsa da sauri
domin yana son ya isa kauyen cikin kakanin
lokaci. Da isarsa kauyen kai tsaye ya wuce zuwa
wajen wani bakon boka wanda bai wuce kwana
uku da sauka a kauyen ana kiransa da suna
Hulubul Auzar.
Yau kwana biyu kenan rak da sarki Kusaidu ya
samu labarin saukar boka Hulubul auzar, kuma
ya samu labarin bokan ne a wajen wani
amintaccen yaronsa da yake masa fatauci mai
suna Ramzal.
Ramzal ya tabbatar wa da sarki kusaidu cewa
yaga bokan da ya fi boka Ardusa karfin sihiri,
domin a gabansa boka Hulubul auzar ya warkr
da wani mara lafiyya wanda ya shekara ashirin
a kwance sakamakon wani asiri da aka yi masa,
wanda yasa ya makance kuma ya kuturce, babu
irin kokarin da boka Ardusa bai yi ba akan yaga
cewa ya warkar da wannan mara lafiya amman
ya kasa, sai ga shi a dare daya boka Hulubul
auzar ya zo ya warkar da shi
253
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da sarki Kusaidu ya iso kofar gidan da
aka sauki boka Hulubul auzar sai ya iske bakan
a tsaye ya zubo masa idanu fuskarsa cike da
annuri.
Tun kafin sarki Kusaidu ya karasa gareshi sai
boka Hulubul auzar ya rugo da gudu izuwa ga
sarki Kusaidu yana mai yi masa lale marhabun,
kuma ya kama mashi dokin ya sauko, nan take
suka shiga cikin gida suka kadaita a cikin wani
daki.
Har sarki Kusaidu ya bude baki zai ce wani abu
sai boka Kusaidu ya tari numfashinsa ybace ya
kai wannan sarki kada ka bata yawun bakinka
wajen yi mani bayanin abinda ke tafe da kai,
nasan kazo wajena ne domin nayi maka bincike
bisa zargin da kake yi akan matarka Zarifa ko ba
haka bane?
Cikin tsananin mamaki sarki Kusaidu yace
zancen ka dutse ya kai wannan boka mai daraja.
Hulubul auzar ya dubi Sarki Kusaidu yace ya kai
wannan arki mai daraja kayi sani cewa sau tari
wadanda muka dauka a matsayin masoyanmu,
kuma abokan shawararmu sune manyan
abokan gabarmu masu son ganin bayanmu, mafi
254
TASKARNOVELS.COM.NG
akasarin mutanen da muaka yi wa rana su kuma
sai suyi mana dare, in mai bakin cikin sanar da
kai cewa fiye da shekaru ashirin baya, boka
Ardusa da matarka Zarifa suna cin amanarka ta
hanyar lalata da junansu, kuma dan da matarka
Salimat ta haifa Hantaru ba danka bane dan
boka Ardusa ne da Zarifa.
Ko da jin wannan batu sai sarki kusaidu ya dubi
bokan cikin tsananin mamaki da rsahin gasgata
zancen shi yace to amman ta yaya aka yi
wannan abu ya faru haka?
Maimakon boka Hulubul auzar ya bashi amsa
sai kawai yayi nuni da hannunsa izuwa jikin
bango, nan take hoton dukkan abunda ya faru
tsakanin boka Ardusa da Zarifa ya bayyana akai,
tun daga ranar da suka fara cin amanar shi
kawo izuwa ranar da zarifa ta haifi Hantaru ta
ajiye wa Salimat, yayin da Salimat ke nakudar
sihiri wanda boka Ardusa ya sanya mata ba tare
da ta sani ba.
Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu
ya fashe da kukan bakin ciki, yaji duniyar gaba
daya ta yi masa zafi, kawai sai ya zabura ya zare
wuka daga jikinsa ya daga sama zai burma a
255
TASKARNOVELS.COM.NG
cikinsa, cikin hanzari boka Hulubul auzar ya
rike hannunsa ya fisge wukar ya ce haba ya
shugabana, ai idan ka kashe kanka makiyanka
sun samu nasara akanka cikin ruwan sanyi,
inason ka dauki dangana ka koma gida ka kuma
cigaba da rayuwarka kamar yadda ka saba yi a
kullum, sannan kada ka nuna wa zarifa sauyin
komai, kada ka raba shimfida da ita, daga nan
har izuwa ranar da amaryarka da kuma danka
Hantaru zasu dawo gida, a sannan ne ido zai
raina fata ayi maka ramuwar gayya, wacce tafi
ta gayya ciwo.
Kada kace zaia dauki wani mataki a yanzu akan
Zarifa da Ardusa, domin ba zaka iya ganin
bayansu ba, kuma idan ka matsa zasu kawar da
kai ne su gaje mulkinka da dukiyarka a banza.
Ko ni dinnan ban isa na kareka daga sharrin su
ba. Ina mai tabbatar maka da cewa boka Ardusa
ba karamin hatsabibi bane ni kaina ba zan iya
da shi ba duk da cewa na fishi karfin sihiri.
Alkawarin da zan maka shine zan cigaba da kare
lafiyarka da kuma rufe sirrinka bazai taba sanin
cewa ka san sirrin abinda yayi maka ba a yanzu
har sai lokacin da Hantaru zai dawo gida.
Tabbas Hantaru ne zai yi masu hukunci daidai
256
TASKARNOVELS.COM.NG
da abinda suka aikata, domin har abada bazai
taba karbar ba a matsayin iyaye, kuma ya
tsanesu tamkar yadda ya tsani mutuwarsa.
Daga wannan rana sarki Kusaidu ya cigaba da
rayuwa mara dadi, ciwo kuma ya kara tsananta
a jikinsa, kullum sai dai a kwantar a kuma tayar
baya iya yiwa kansa komai, a duk sa'ad da boka
ardusa yazo duba shi inya dubi fuskarsa sai yga
kamar kura yake gani, ita kuwa Zarifa a duk
sa'ad da tazo kusa da shi sai yaga kamar bakar
macijiya ce take fasa kai zata sareshi, baban
qbnida ya kara susuta sarki shine aminttatun
bayinsa da ya tura zuwa birnin Darul Habur dan
kai wasika ga matarsa Salimat tunda suka tafi
basu dawowa ba har tsawon wata shida babu su
babu duriyarsu.
Al'amarin da ya kara jefa matsanancin ciwo
kenan ga sarki Kusaidu, ya zamana cewar
kullum fadawansa ma jira suke kawai ace rai
yayi halinsa su san wanda zasu dora akan
karagarsa.
Babu abin takaici face kullum boka ardusa a
turakar Sarki yake yini, shine mai nuna wa sarki
kauna fiye da kowa, hatta masu baiwa sarki
257
TASKARNOVELS.COM.NG
magani bai yarda da su ba, sai ya tabbatar da
ingancin maganin sannan yake yarda a baiwa
sarki maganin ya sha.
Wannan hali da sarki Kusaidu ya shiga sai ya
zamo tamkar samun dama a wajen Ardusa da
Zarifa suka shagala da more rayuwarsu wajen
cin amanarsa.
A duk sa'ad da Zarifa ta bukaci boka Ardusa yayi
bincike akan halin da Yarima Hantaru ke ciki sai
ya kwantar mata da hankali yace ai yarima
Hantaru yana nan lafiya lau, kuma zai dawo
birnin Kisra a lokacin da sarki kusaidu zai mutu
ya haye karagar mulkinsa.
Lallai a wannan lokaci ne zamu sanar da yarima
cewar mune iyayensa na gaskiya, kuma babu
yadda zai yi dole ne ya karbemu a matsayin
iyayen nasa, kuma ya girmamamu. Wannan
kalamai na boka Ardusa ba karamin faranta wa
Zarifa rai yake yi ba, sai kawai ta rungume boka
Ardusa su ci gaba da sharholiyarsu.
A zahirin gaskiya boka Ardusa yayi iyakar
kokarinsa wajen gano halin da Hantaru yake
ciki a cikin hallarar tsafi da mahaifiyarsa acan
birnin darul habur amman abu ya gagara, duk
258
TASKARNOVELS.COM.NG
sa'ad da ya matsa akan bincike sai madubin
tsafinsa yayi bindiga ya tarwatse. Al'amarin
daya dugunzuma hankalinsa kenan ya gane
cewa lallai akwai wani babban bokan dake boye
sirrin yarima acan birnin Darul Habur, abinda
bai sani ba shine ba wani boka bnae face
malaminsa a harkar bokanci wanda tuni ya dade
d yin gaba har ma ya baiwa yan bayansa sirrinsa
wato boka Sulbaini.
Abinda boka Ardusa ya gano a cikin bincikensa
kawai shine nan da shekaru uku masu zuwa
yarina Hantaru zai dawo gida, wannan shine
abinda yasa hankalinsa ya kwanta, ya amince da
cewar zai cigaba da jiran dawowar yarima
Hantaru.
Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin
inda boka Ardusa yasan abinda zai biyo baya
idan yarima hantaru ya dawo gida da ya kashe
kansa saboda munin abin takaicin da zai samesu
shi da farkarsa Zarifa.
259
TASKARNOVELS.COM.NG
Acan kuwa birnin Darul Habur bayan kimanin
wata daya da yin gasar neman auren gimbiya
Larziyya, sai bangarorin biyu suka shiga shirye
shirye gasar da za a yi nan da watanni goma sha
daya masu zuwa, ya zamana cewa sun dage
ainun dan ganin cewa idan lokaci yayi su samu
nasara. Dare da rana kuma kullum Hantaru da
Rabbasu cikin basu horo ake na kara wa jikinsu
juriya da zafin nama gami da tsananin gudu, sai
da takai cewa kowannensu na iya yin azabben
gudu wanda a cikin rabin sa'a zai shafe tafiyar
yini guda.
Haka suka cigaba da baiwa jikinsu horo har
tsawon wata goma sha daya, a tsawon wannan
watanni tsakanin Hantaru da Rabbasu Babu
wanda ya kara ganin fuskar gimbiya Larziyya
saboda sarki ya sa an tsareta a gidan sarauta,
babu wani mahalukin da ya isa yaje inda take,
kuma itama bata isa taje ko ina ba.
Da kyar da sidin goshi kuma a sirrance Gimbiya
Larziyya ta samu damar aika wa da Sadauki
Hantaru wasikar soayayya a cikin kwana talatin,
duk sa'ad da wasikar ta riski Hantaru baya
ganin komai a cikin takardar face kalaman kuka
da bakin ciki bisa dalilin rashin saduwarsu,
260
TASKARNOVELS.COM.NG
gami da baitocin waka na kara kaimi da kuma
shawara kan lallai ya kara kaimi wajen ganin
cewa ya samu nasara lashe wannan gasa da za'a
yi ta neman aurenta a karo na biyu.
Baya ga haka kuma a koyaushe tana yi masa
tuni bisa alkawarin daya daukar mata guda uku,
alkawari na farko;
Shine komai rintsi ba zai janye ba, alƙawari na
biyu kuwa shine duk alfarmar data nema a
wajensa zai yi mata, alkawari na karshe wanda
shine cikon na uku kuwa shine a duk halin da
suka cintsi kansu a ciki ba zasu guji juna ba.
Ko sau daya Hantaru bai taba saba wa aika wa
da Gimbiya Larziyya amsar wasikarta ba, kuma
a koyaushe yana kara tabbatar mata da cewa
alkawarinsu yana nan babu abind zai tashe shi
har abada.
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a
je ba, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da
suka ce rana bata karya sai dai uwar diya ta ji
kunya, a kwana a tashi sai ranar gasa karo na
biyu ta dawo.
261
TASKARNOVELS.COM.NG
Ai kuwa a wannan rana sai da hankalin
gabadaya mutanen birnin Darul Habur ya
dugunzuma saboda tsananin yawan al'ummar
da suka cika wannan gari, tamkar mutane
duniya ne suka hallara.
A wannan rana anyi muguwar bakar gasa ta
tashin hankali, wacce ta zamo sanadiyyar ajalin
gaba daya dakarun gasar face na mutum biyu
rak wato Hantaru da Rabbasu, suma din sai da
kowannensu ya suma sau uku, kuma a karshe
suka sake yin ragas kamar yadda al'amarin ya
faru a gasar farko, wato a lokaci guda suka kama
barewar gasa kuma suka tsinkata gida biyu. A
wannan rana Sadauki Rabbasu kwana yayi yana
kukan bakin ciki, haka dai ya rungumi kaddara
bisa dole ya cigaba da hankoro zuwan Shekarar
gaba.
A takaice dai sai da aka yi gasa sau uku ba
zakara sai ragas ake yi tsakanin Hantaru da
Rabbasu, a ranar da akayi gasar ta uku ne
shugaban alkalan gasar wato sarkin birnin
Darul Habur wato mahaifin Gimbiya Larziyya ya
yi bayanin cewa tunda dai wadannan zaratan
jarumai sunyi ragas har sau uku akan gasar
neman auren yarsa, to yanzu za suyi gasa ta
262
TASKARNOVELS.COM.NG
karshe mai tsananin wahalar da ko dayansu
yayi nasara ko kuma duk su biyun su hallaka,
idan kuma suna ganin cewa b zasu iya yin gasar
ba to sai dai duk su biyun su hakura da neman
auren Gimbiya.
Sarki yayi gyaran murya sannan ya cigaba da
cewa ita dai wannan gasa ta karshe bata komai
bace sai ta tafiya izuwa kogon mazabatul
hirsham dake can karshen dajin hayatul Maut
dan dauko takobin Saiful Lujara.
Koda sarki ya zo nan a jawabinsa sai filin gasar
ya rude da hayaniya da ka-ce-na-ce saboda
sanin masifun dake dajin hayatul Maut.
Dajin hayatul Maut yayi kaurin suna a ko ina a
wannan zamani, domin dajine fiye da shekaru
dubu da suka gabata babu wata halitta da ta
taba shigarsa ta fito, duk abinda ya shiga cikinsa
ya shiga kenan, har abada b za a sake jin
263
TASKARNOVELS.COM.NG
duriyarsa ba, walau mutum ko aljan ko dabba
ko tsuntsu, kai bama cikin dajin hayatul Maut
ba, hatta gefen dajin ba a bi.
Lokacin da filin gasar ya rudu da ka-ce-na-ce sai
sarki yasa aka busa kaho kowa yayi tsit tamkar
mutuwa ce ta gifta. A sannan ne sarki ya dubi
Hantaru da Rabbasu wadanda ke duke a
gabansa cikin mugun yanayi na galabaita mai
kama da suma y ce Ya ku wadannan manyan
zakuna ababan kwatance, kuyi sani d cewa daga
yau har duniya ta nade ba za a manta da
jaruntakarku ba, to amman fa ba zaku cika
mazan jiya ba sai idan kunyi wannan gasa ta
karshe, dayanku ya samu nasarar dauko takobin
Saiful Lujara, shin kun amince zaku siyar da
rayuwarku domin neman suna da neman auren
yata?
Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Rabbasu
yayi farat ya ce ya shugabana kayi sani cewa
rayuwata bata da wani amfani muddin ban
mallaki gimbiya Larziyya ba, kuma ban kare
martabar zuri'ata ba ta mafarautan wannan
Birni, saboda haka na amince na siyar da raina
domin cikar burina da burin zuri'ata.
264
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai jama'a suka sake
barkewa da sowa, aka hau buga tambura da
ganguna ana yiwa Rabbasu kirari da jinjina, sai
da sarki yasa aka sake busa kaho sannan jama'a
suka yi tsit a karo na biyu.
Sarki ya dubi Sadauki Hantaru ya ce ya kai
wannan namijin duniya ka ji abinda abokin
gasarka ya fada, kai kuma me zaka iya cewa?
Hnataru yayi ajiyar zuciya ya ce ya kai wannan
sarki mai daraja, ka yi sani cewa a duniya babu
wani abu mai daraja wanda yakai faranta rab
masoyi, lallaı bani da masoyi wanda ya kai
mahaifiyata da kuma abar begena Gimbiya
Larziyya, mahaifinta bata da wani buri face ace
yau kambun gasa ya dawo hannun zuri'arsu ta
makeran wannan birnin, haka kuma masoyiyata
bata da wani buri da ya fi ace yau nine zakaran
gasar neman aurenta, bisa wannan dalilai dana
wassafa na amince na sallama rayuwata domin
faranta ran zuciyoyin wannan masoya nawa
guda biyu.
Koda jin haka sai jama'a suka sake barkewa da
shewa gami da ihu, masu buga ganga nayi, masu
busa algaita da tambura ma nayi. Sai da aka dan
265
TASKARNOVELS.COM.NG
jima ana cashewa sannna aka busa kaho kow
yayi shiru, saannan sarki yayi gyaran murya ya
ce to jama'a kunji abinda zaratan jarumanmu
suka fada, saboda haka kofa a bude take ga
dukkanin jarumi wadanda suka ga zasu iya
shiga wannan gasa wato su bi su Rabbasu izuwa
dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul
Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Ko da
mutum bai yi nasara ba, zai yi suna, idan kuma
suna bai samu ba rayuwa zata salwanta, wanda
duk yake ganin zai iya bin wadannan Sadaukai
ya bayyana kansa yanzu.
Koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru ya
kama kalle kalle yana mai duban gabas da
yamma kuma kudu da arewa ko zaiga wani
jarumin da zai fito ya kawo kansa, tsawon lokaci
ba asamu mutum daya da ya fito ba.
Ko da ganin haka sai sarki yace na sallami kowa
da kowa, domin ta tabbata cewa wadannan
zaratan jaruman guda biyu sune kadai zasu yi
wannan tafiya, da wannan furuci nake sallamar
kowa, sai kuma bayan kwana talatin zamu yi
sallama da jarumanmu biyu domin su tafi dajin
hayatul Maut, zamu ba jaruman mu adadin
kwanaki arba'in wanda duk ya dawo daga dajin
266
TASKARNOVELS.COM.NG
hayatul Maut dauke da takobin Saiful Lujara a
cikin kwanaki arba'in din a cikinsu to shine zai
zamo mijin ya ta gimbiya Larziyya, kuma ya cika
namijin duniya Sarkin Sadaukai wanda har
abada tarihin jarumtakarsa ba zata taba
gushewa ba, kuma idan yaso zai iya mulkar
duniya gabadayanta saboda sihirin dake jikin
wannan takobi da ya mallaka ta Saiful Lujara.
Koda jin wannan batu sai jama'a suka cika da
tsananin al'ajabi kowa ma yaji inama zai iya
saida rayuwarsa ya tafi neman wannan takobi.
Nan dai mutane suka yita fadar albarkacin
bakinsu, aka kwashi Hantaru da Rabbasu a
matukar galabaice tamkar wadanda suka
shekara suna jinyar cuta aka tafi da su gida,
haka yasa taro ya watse kowa ya kama gabansa.
A wannan karon ma Samilat ce ta yi jinyar
Hantaru har tsawon kwanaki ashirin, sannan
jikinsa y dawo daidai ya samu lafiya. A kullum
dan Salimat ta dubi Hantaru ta tuna saura
kwanaki kadan su rabu, Rabuwar da babu
tabbacin su sake saduwa sai ta fashe da
matsanancin kuka. Da kyar da sidin goshi
Hantaru yake rarrashinta ya kuma bata baki
sannan take daina kukan. A koyaushe Hantaru
267
TASKARNOVELS.COM.NG
yana kara kara mata gwarin guiwa da cewa ya
ke ummina kiyi sani cewa da zarar na dawo ne
zamu koma can birnin Kisra tare da amarayata
Gimbiya Larziyya ki sadu da mijinki, mu cigaba
da sabuwar rayuwa, kuma a sannan ne zanyi wa
boka Ardusa da mahaifiyata larifa hukunci da ya
dace dasu bisa cin amanar mijinki da suka yi.
A duk sa'ad da Hantaru yayi wannan furuci a
gareta sai ta sake fashewa da kuka ta ce ya kai
dana ka yi sani cewa har abada komi lalacewar
iyaye, iyaye ne. Kada ka kuskura kace zaka
hallaka Ardusa da Larifa bisa cin amanar d suka
yi wa mijina, kai dai kawai ka tona masu asiri
domin su zamo abin kwatance ga al'umma
kuma darasi ga al'umma, ni dai bukatata a
gareka ita ce, duk matsayin da ka kai a duniya
kada ka gujeni, domin bani da wani face kai, duk
da cewa banice na haifeka ba, ina jin a raina
cewa ko a nan gaba bazan so dan da zan haifa
kamar yadda na so ka ba. Ya kai Hantaru ka rike
ni a matsayin uwa mahaifiya, kuma ka sani
kamar yadda kowanne da ke son uwarsa, burina
shine koda mai rabawa zata rabamu mu rabu da
soyayyar juna.
268
TASKARNOVELS.COM.NG
Yayin da Hantaru ya ji wannan batu sai ya
rungumeta kuma ya fashe da kuka yana mai
cewa har abada bazan gujeki ba yake ummina,
kece uwata a zahiri, kuma kece uwata a badini.
Kaico! Hakika kowa ya rasa masoyi yayi kuka, a
duniya kaf babu abinda yafi farin ciki kamar
samun masoyi, inda ace mutum na nan a lokacin
da wadannan masoya suka rungume junansu
sun kuka dan alhinin rabuwar da zasu yi nan
bada daddewa ba, dole ne tausayinsu ya kmashi
har ya zubar da hawaye, domin shakuwar dake
tsakaninsu da sabo da juna ya wuce ayi misali
face abinda zuciya ta kintata.
A ranar da kwanaki talatin suka cika ne Hantaru
ya gama shirya kayansa domin tafiya izuwa
dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful
Lujara, lokacin da yazo yin bankawana da
Salimat da kuma iyayenta, sai zuciyarsa ta
karaya ya fashe da kuka ya kasa cewa komai a
garesu, koda ganin haka sai duk su ukun suka
fashe da kuka suma suka rungumeshi suna
masu kankame shi a jikinsu tamkar ba zasu
barshi yayi wannan tafiya ba.
269
TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam sai suka ji alamar motsin tafiya ana
shigowa cikin gidan, cikin hanzari suka wauga
suka yi arba da wanda ya shigo, ba kowa bane
sai boka Sulbaini mahaifin Shuraim.
Sulbaini ya tsaya cak yana kallon Hantaru shi
kadai, a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla
sannan sai ya dubi Salimat ya fara zubar da
hawaye.
Koda ganin haka sai Salimat da Hantaru suka
ruga gareshi suka rungumeshi shi tare da
fashewa da matsanancin kuka har zuwa lokaci
mai dan tsawo, daga can sai Salimat ta janye
jikinta daga nasa, suka fuskanci juna sosai
sannan ta ce ya kai kakana mene ne dalilin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 13