Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka sai Rabbasu yayi wurgi da takobinsa, ya dubi Hantaru har kwalla ta zubo masa, yayi shiru bai ce komai ba. Al'amarin daya sa Hantaru ya dubeshi ya ce da shi ya kai abokin tafiya ina dalilin zubar wannan hawaye naka? Rabbasu ya koma gefe daya ya zauna yana haki bai ce komai ba, daga can sai ya dago kai ya ce ya kai namijin duniya kayi sani cewa bayan ka baro ni a baya a inda muka fafata yaki nan,sai da 294 TASKARNOVELS.COM.NG na jima a kwance kamar gawa sananne n dawo cikin hayyacina. Ina farfadowa sai na nemeka na rasa, sai kawai gawar aljanin nan na gani ta rabe gida biyu. Nan take na raina jarumtakata, kuma naji zuciyata ta buga da karfi, tsoro ya shigeni kuma na fara tunanin cewa abu ne mawuyaci na tsira da rayuwata a wannan daji na hayatul Maut. Domin na samu nutsuwa sai na dauki madubin tsafina na shiga binceke, koda naga abinda binceken nawa ya nuna mani sai na fashe da kuka, ba komai na gani ba face bani da sa'a ko kadan a cikin wannan gasa, kaine da sa'a kuma tabbas kai zaka karbi kambun wannan gasa. Cikin bincekena na gano cewa ba zan tsira da rayuwata ba a cikin wannan daji, kuma a yanzu haka mahaifina sarkin mafarauta na can a kwance cikin ciwo, haka ma kakan Salimat duk su biyun ba zasu rayuwa ba mutuwa zasu yi nan da yan kwanaki kadan masu zuwa, kaga kenan ni yanzu babu abinda zan tsira da shi a rayuwata, na rasa ubana kuma na rasa masoyiyata Gimbiya Larziyya, wacce tun muna yara kanana na kamu da tsananin kaunarta, amman sai ya zamana cewa ta tsaneni kamar 295 TASKARNOVELS.COM.NG yadda ta tsani mutuwarta, akan haka ne na sha alwashin sai na aureta ta kowanne hali. Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa tun da kuruciyata nake ta shiryeyen wannan gasa, nayita baiwa kaina horon yaki, tseren gudu da shanye horon duka, har izuwa lokacin dana cika saurayi. Yau gashi na wayi gari duk wannan tanadi da nayi ta zamo a banza, soyayyata ta kaini izuwa ga halaka, tabbas yanzu na yarda cewa kaine zaka zamo mijin gimbiya Larziyya dan haka ina mai kara kara maka gwiywa akan ka dada jajircewa wajen karasawa cikin kogon Mazabatul Darshal ka dauko takobin Saiful Lujara, ni kam tafiyata ta kare anan domin nayi nadamar zurfafawa a soyayya gashi kuma soyayya ta kaini ta baroni. Ya kai abokin tafiya kaima ina mai baka shawara da ka taka a hankali domin su mata da kake ganinsu suna da matsari, da wannan furuci nawa nake maka sallamar karshe gami da fatan samun nasara bisa abinda ka sa a gabanka. Koda gama fadin haka sai Rabbasu ya yunkura cikin zafin nama, ya kama kansa da hannayensa biyu ya murde wuyansa, nan take kuwa ya fadi kasa matacce. 296 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin tsananin bakin ciki Hantaru ya ruga gareshi ya rungume gawarshi ya fashe da matsanancin kuka, duk da cewa Hantaru ya san cewa Rabbasu abokin gabarsa ne, amman sai yaji cewa kamar dan uwansa ne na jini ya mutu. Nan take hantaru yaji komai na duniya ya fice daga ransa, ya fara tunanin ya koma da baya ya hakura da dauko takobin Saiful Lujara. Sai da Hantaru ya shafe fiye da sa'a guda rungume da gawar Rabbasu yna ta shara kuka, sannan ya mike ya haka rami a wajen ya binne gawar Rabbasu, sannan ya rubuta sunansa da jinin dan yatsan sa a jikin duwatsun da ya rufe kabarin. Hantaru ya zauna a gaban kabarin ya shiga raira baitocin waka, da nuna jinjina da kirari ga sadauki Rabbasu, yana wakar yana zubar da hawaye har izuwa lokaci mai tsawo sannan ya mike tsaye ya tafi izuwa cikin wannan rijiya yana mai waigen kabarin Rabbasu yana cigaba da hawaye a haka har ya shige cikin rijiyar. Da shigar Hantaru cikin rijiyar sai kawai ya tsinci kansa a cikin wani makeken kogon dutse, wanda yafi wanda ya baro girma, tsawo da fadi sau uku, a cikin kogon akwai rijiyoyi guda dubu kowacce rijiya rufe take ruf da makulli, nan fa Hantaru ya kura wa rijiyoyin idanu yana 297 TASKARNOVELS.COM.NG ayyanawa a ransa cewa lallai takobin Saiful Lujara na cikin daya daga cikin wadannan rijiyoyi, abin tambaya anan shine a cikin wace rijiya takobin take? Kawai sai Hantaru ya yanke shawarar bude rijiyoyin daya bayan daya, nan take ya tunkari rijiyar farko gadan-gadan. Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu, hakika inda hantaru yasan abinda zai biyo baya da ya hakura da bude wannan rijiya ta farko. Lokacin da Hantaru yasa takobinsa ya sare kwadon dake jikin wannan rijiya ta farko sai kawai yaga wata mutukekiyar macijiya ta taso sama, macijiyar na da kawuna saba'in da daya, girman ko wane kai daya ya kai na katuwar bishiyar kuka. Kafin hantaru yayi wani yunkuri tuni kawunan macijiyar nan guda saba'in da daya sun fasa kai sun gabza masa sara a sassan jikinsa ko ina da ina. Nan take wani irin dafi ya shige shi, jikinsa ya kama kakkarwa, kafin a jima ya jike sharkaf da zufa tamkar an tsamoshi daga cikin kogi. Hantaru ya sulale kasa magashiyyan kuma jikinsa ya cigaba da kakkarwa kuma ya fara kakarin mutuwa lokacin da wata irin kumfa ta fara dalala daga cikin bakinsa. 298 TASKARNOVELS.COM.NG Duk wannan abu dake faruwa macijiyar na tsaye akansa, ta zubo dukkan kawunan nasa a kansa, tana kallonsa kawai kamar jira take ya mutu ta cinye shi. Daga can sai ya sandare ya daina motsi, sannan ne macijiyar ta kara sakkowa da kanta kas da niyyar ta hadiye Hantaru. Ba zato ba tsammani sai kawai macijiyar taga numfashin Hantaru ya dawo, nan take ya amayar da duk wani dafi data saka mashi, wanda ya kasance bakikkirin kamar an jika shuni. Cikin zafin nama macijiyar nan ta wangane bakinta gabadaya dan ta hadiye Hantaru, amman sai ya rikede ya zama katon dutse, duk da haka sai da macijiyar ta hadiye dutsen. Koda sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarin da yake baiwa yar uwarsa Gimbiya Hursiyya sai ya fuskanci cewar dare ya raba sosai, dan haka ya kamata su kwanta suyi bacci, amman bisa mamaki sai yaga idanun Hursiyya a kafe babu alamar jin bacci a cikinsu. Sarki Dujalu yayi shiru ya kafa mata idanu kawai yana murmushi. 299 TASKARNOVELS.COM.NG Gimbiya Hursiyya ta dubeshi cikin matukar damuwa ta ce haba ya kai dn uwana, sabida me zaka katse mani wannan labari, na rokeka dan girman iyayenmu daka karasa mani wannan labari domin naji yadda sadauki Hantaru yake dauko takobin Saiful Lujara, kuma naji yadda zai auri gimbiya Larziyya, sannan na ji yadda karshen rayuwarsa zata kasance a tafarkin soyayya. Haka kuma ina son jin yadda rayuwar sarki Kusaidu zata kasance da boka Ardusa, da Zarifa ma'abota cin amana. Lokacin da sarki Dujalu ya ji haka sai ya bushe da dariya ya ce yake yar uwata kiyi sani cewa a halin yanzu dare ya raba sosai, idan har zan cigaba da baki wannan labari har gari ya waye ba zai kare ba, zai fi kyau kiyi hakuri sai wani lokaci idan mun sake yada zango a wani wurin sai mu cigaba. Alkawarin da zan yi maki shine zanyi kokari na gama baki labarin sadauki Hantaru sannan mu shiga labarin Sadauki shaddar na birnin Kufa, wanda yama fi labarin Hantaru ban tausayi da ban al'ajabi. 300 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin mamaki Hursiyya ta ce haba ya dan uwana ya za ayi a samu labarin da ya fi na Sadauki Hantaru ban tausayi da ban al'ajabi, ka sani cewa tunda ka fara wannan labari nake zubar da hawaye har ka tsaya ban daina ba. Sarki Dujalu yayi murmushi yace aikuwa idan kika ji labarin Sadauki Shaddadu sai hawayen idanunki ya kare saboda zuba. Yanzu sai ki tashi ki tafi izuwa cikin tantinki na sallameki. Cikin sanyin jiki Hursiyya ta mike tsaye ta fita daga cikin tantin sarki Dujalu, shi kuwa sai ya kwanta bisa shimfida ya mike kafafunsa ya kama aikin rago. Me zai faru idan rundunar mayaka ta sarki Maharaz da ta sarki Dujalu suka hadu a bakin gabar tekun Bahar Suffiyya dan dauko takobin Saiful Lujara? Waye zai samu nasarar mallakar makaman yaki guda uku, na mazan jiya? 301 TASKARNOVELS.COM.NG Ta yaya Sadauki Hantaru zai dauko takobin daraja a kogon Mazabatul Darshal? Wadanne irin abubuwan al'ajabi dana ban tausayi, da kuma jarumtaka ne a cikin labarin Sadauki Shaddadu na birnin Kufa da Sadauki Hulkas na birnin Romaniya? Marubucin yace mu hadu a Littafin mazan jiya Littafi na biyu. 302 TASKARNOVELS.COM.NG 303 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 13 of 13