Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai imnal yayi murmushi ya ce indai akana soyaiya ta ga gimbiya Mulaifa ne a shirye na ke don na kar6i horo koda kuwa na mutuwa ne, cikin tsananin takaici hibri ya dube shi a fusace, kawai sai ya 25 TASKARNOVELS.COM.NG wuce zuwa turakar sa ya bar imnal tsaye a kofar gida. Da yammaci kuwa fadar sarki maharaz ta cika makil da jama.a masu amsa gaiyatar tafiya yaki, duk da cewa adadin jama.ar da suka taru bai kai daya bisa goman masu tafiya yaqin ba sai da fadar ta cika ta batse sai da ya zamana duk inda ka duba kawunan bil'adama ne rututu. Tun a farkon yammacin ne sarkin yaqi tare da dansa suka amsa kiran sarki suka hallara a fadar, shi kuwa sarki maharaz bai fito ba sai da kowa ya gama zuwa. Da fitowar sarki kowa ya miqe tsaye don girmamawa a gare shi har sai da ya zauna sannan kowa ya zauna. Sarki ya dubi dubun mutane da suka amsa kiran sa sai ya cika da farin ciki, da ya duba 6angaren da su imnal suke tsaye sai ya murtuke fuska ya 6ata rai. Bayan fadawa sun zube sun kwashi gaisuwa ya rage sauran sarkin yaki hibru da dansa Imnal, kawai sarki yayi nuni da hannun sa izuwa ga wani badakare yana maiyi masa nuni da yazo da imnal gabansa, nan take badakare ya tasa keyar sa yazo da imnal gaban sarki. 26 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan lokaci gimbiya Mulaifa na zaune daf da sarki. Koda taga an tasa keyar Imnal anzo dashi gaban sarki sai hankalinta ya tashi domin ta tabbatar da cewa lallai hukunci za'ayi masa. Gaba daya jama'ar dake fadar kuwa sai suka cika da mamaki suka zuba ido don su ga irin hukuncin da za'a yiwa Imnal yaron da ba.a ta6a ganin yayi wani laifa ba. A kullum shi da mahaifin sa ba su da wani abin da ya wuce biyaiya ga sarki, Sarki maharaz ya mike tsaye daga kan karagar mulkin sa ya dubi jama'a ya ce ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa wannan yaro Imnal d'a ga sarkin yakin mu hibru ya kasance mai ladabi da biyayya a garemu kamar yadda mahaifin sa ya kasance, kuma bamu ta6a kamashi da wani laifi ba, amma sai gashi a jiya ya aikata wani babban laifi wanda bamu ta6a zaton zai aikata shi ba. Laifin kuwa shine a jiya sa'adda kowa ya sunkui da kansa kas a dakin bauta sai shi ya miqe yaje inda nake zaune ya zauna kusa damu. Wannan shine karo na farko da wani mahaluki ya karya dokar maigirma darbuza a cikin kasar nan, don haka dole ne ayi masa hukunci gwargwadon laifin sa. 27 TASKARNOVELS.COM.NG Mai girma darbuza ya ce a daure imnal a sama jikin katako kuma a cikin rana tun daga hudowar ta har zuwa faduwar ta ba tare da an bashi ruwa koda makwarwa daya ba har tsawon kwana uku. Idan kuma ya sake aikata irin wannan laifi hukuncinsa zai zamo kisa ne. Koda sarki maharaz ya zo nan a zancensa sai idanun Mulaifa suka ciko da qwalla suka fara zubar da hawaye. Hibru da imnal kuwa ko a jikin su maimakon ma hankalinsu ya tashi sai suka kama murmushi domin sun san cewa wannan horo ba komai bane akan irin horon da hibru ya bashi tun yana dan karami. Sarki Maharaz yaci gaba da bayani .. Sai gobe za'a fara wannan horo ga Imnal, kuma washe garin ranar da aka gama horon ne zamu dunguma gaba dayan mu mu tafi izuwa gagarumin yaki da ke gaban mu. Domin mu riga sarki dujalu dauko takobin saiful lujara. Ina mai kira ga dukkanin jama'ar mu da a ci gaba da shirye-shirye babu sassauci domin tuni dakarun gudunmawa sunzo da yawan su mu kawai suke jira a tafi... Ko da gama wannan jawabi sai sarki Maharaz da Mulaifa suka shiga gida sannan jama'a kowa ya kama gabansa. 28 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da imnal da hibru suka isa gida sai hibru ya aika imnal kasuwa don ya sayo masa zugazugi na wutar Qira sabo da nasa ya lalace. Imnal ya hau doki ya tafi kasuwa tun kafin ya isa kasuwar sai yaga duk inda ya ratsa jama'a na kallonsa suna magana akan hukuncin da sarki zai yimasa. Kafin ya isa kasuwar ne ya hadu da wadansu kuyangin gidan sarki suna tafe suna hira. Koda suka ganshi sai suka sha gabansa suka shiga yi masa kirari suna kodashi. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan ya dubesu ya ce ya ku wadannan kuyangi ku kuwa mai yasa kuke kodani haka alhali kuwa banyi wani abin al'ajabi ba? Suka ce ai kuwa kai ne kayi babban abin al'ajabi tunda har ka siye zuciyar gimbiya Mulaifa a halin bata ta6a nuna tana son wani da namiji ba face kai. A yanzu haka tana can gida tana kuka sabo da jin za'ayi maka horo na kwana uku bisa laifin da ka aikata. Babu irin rokon da gimbiya ba tayi wa sarki ba akan ya janye wannan horo amma yaki, saboda bakin ciki ne shi yasa ta kasa ci ta kasa sha kuma ga dukkan alamu haka zata kwana a wannan hali yau. 29 TASKARNOVELS.COM.NG Sa'adda kuyanga ta zo nan a zancenta sai hankalin Imnal ya dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya, sai kawai ya dubi kuyangin ya ce da su idan kun koma gida ku shaidawa gimbiya cewa wanda take kuka dominsa yana bakin ciki bisa zubar hawayenta da kuma rashin ci da shanta.. Lallai shi ma ba zai ci kuma ba zai sha ba a yau har sai yazo ya ganta ta kowane hali... Jin wannan batu sai kuyangin suka zazzaro idanu cikin tsananin mamaki wacce tayi magana dashi tace taya zaka iya shiga gidan sarauta har ka ganta ahalin akwai tsananin doka da tsaro? Imnal yai murmushi ya ce ko mutuwa ke tsaro a yau sai na ga gimbiya Mulaifa kuje ku gaya mata cewa komai dare ina nan tafe a yau. Koda gama fadin haka sai imnal ya kada linzamin dokin sa ya wuce izuwa kasuwa ya siyo zugazugin ya koma gida sannan ya ci gaba da taya hibru kera wasu sababbin makaman yaki tamkar babu wani abu da ke sosa zuciyarsa. Nima zan so ganin yadda Jarumi Imnal zai iya ratsawa ta cikin wannan tsaro na gidan sarautar 30 TASKARNOVELS.COM.NG birnin darul mahabur har yaje ya sadu da Gimbiya Mulaifa, masu karatu ko zan samu dan rakiya kuwa? Da fatan kuna hutun karshen mako lafiya, sannan duk wanda yake son complete na Littattafan yaki harma da na soyayya zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 whatsapp kadai pls banda kira MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part C Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Da tsakar dare lokacin da gari yayi tsit ba kajin komai face kukan gyare. Da daidaikun sautin 31 TASKARNOVELS.COM.NG tsuntsaye, imnal ya miqe tsaye dama ko runtse ido bai yi ba bare yayi barci. Cikin sanda ya debo wadansu bakaken kaya ya sanya sannan ya rufe fuskar sa da bakin rawani, takalmin da ya sa kuwa na fata ne kasansa gashi ne yadda duk abin da ya taka ba za.aji sautin komai ba. Ko allura bai dauka ba a matsayin makami, ya bude kofar dakin sa ya fita ba tare da hibru ya ji motsin sa ba, maimakon ya bude kofar gidan sai kawai ya daka tsalle kamar dan biri ya dira akan katangar gidan, duk da cewa tsawon katangar ya kai kamu sittin. Kafin ya tafi ya tanadi kayam da ya cire daga jikinsa a cikin 'yar qaramar jaka kuma shifidar da ya kwanta sai yatara tsummokarara yai musu siffar mutum ya lullu6esu tamkar mutum ne a kwance. Dama tuni ya daure dokinsa a kofar gida bai shiga da shi ciki ba saboda dama yasan cewa zai yi amfani da shi yayin da dare ya raba. Koda imnal ya dirgo daka kasa daga kan katangar sai yaje ya kwance dokin ya haye kansa ya zabureshi ya nufi hanyar da zata kai shi gidan sarki tuni ya aiyana a ransa ba zai wuce rabin sa.a ba zaije ya dawo. 32 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin matsanancin gudu imnal ya ci gaba da tunkarar gidan sarautar sai ya sauya hanya domin ya 6ullo ta bayan katangar gidan, cikin kakanin lokaci ya hango katangar gidan da sauri ya sauko daga kan dokinsa ya daureshi a cikin bishiyoyi masu duhuwa sannan ya 6uya a cikin duhuwar, ya kurawa katangar idanu yana kallon dakaru kuma yana nazarin hanyar da zai bi ya shiga gidan ba tare da wani ya ganshi ba. Al'amarin da ya qara tayar da hankalinsa kenan domin bai ga ta yadda hakan zata iya faruwa ba. Sai imnal ya dan jima yana nazari sannan dabara ta fado masa. Nan take ya hau kan bishiya ya karyo itatuwa sannan ya sauko ya daddaure itatuwan da 6awon bishiya yayi siffar mutum mutumi ya dora shi kan dokin sa ya kora shi, dokin ya fita da gudu ya wuce ta gaban wadannan dakaru dake tsaitsaye a bayan katangar. Ko da suka ga mutum a sukwane ya wuce ta gaban su sai suka bi shi gaba daya da gudu domin su kure masa gudu, damar da imnal ya samu kenan ya fito da gudu daga cikin duhuwar da ya 6uya.. Ko da ya rage saura taku uku ya 33 TASKARNOVELS.COM.NG riski katangar sai ya daga tsalle yai sama tamkar tsuntsu ya kama karshen katangar, yana kama katangar sai ya ji ta da tsananin santsi har hannun sa ya su6uce zai fado sai ya sake jefa daya hannun nasa ya kamo katangar ya dafa kafafun sa sama ya dirga akan katangar, koda ya leqa qasan katangar izuwa cikin gidan sai ya ga akwai tsawo sosai in yace zai fada zai iya karyewa. A dai dai wannan lokacin ne ya jiyo dawowar dakarun da suka bi dokin sa sun dawo da gudun tsiya. Nan fa zuciyar imnal ta buga da karfi domin ya san cewa babu mamaki sun bi dokin ba su ga kowa a kan sa ba sai itatuwa, sai baban su ya ce lallai ma ko waye mai dokin nan ya raina mana wayo, sai ya daka ma sauran dakarun tsawa ya ce kowa ya koma malafar sa ya ci gaba da aiki don akwai alamar zuwan baki gidan nan. Imnal ya ringa bin katangar har ya hango wani tafki a jikin katangar daga cikin gidan sai yayi sauri zuwa wajen keda wuya sai yaga bakin tafkin 12dakaru ne suke kaiwa da komowa, amma sai yayi ta maza ya daka wawan tsalle sai ya fada cikin tafkin nan ji kake Zundum.. 34 TASKARNOVELS.COM.NG Al'amarin da ya juyo da hankalin kwamandan dakarun nan sai ya umarce su da su shiga cikin tafkin su lalubo abin da ya fada su fito da shi. Nan take suka bi umarninsa suka shiga tafkin nan.. Koda imnal ya ji dakarun nan sun shigo cikin ruwan, cikin zafin nama ya samu guda daga cikin dakarun nan ya suburbudeshi ya bishi da mazga, nan take ya suma sai ya cire kayan jikin sa ya sanya masa shi kuma ya sanya nasa, sakamakon dakarun duk kayan su iri daya ne. Can sai gaba daya suka yo sama su shaida ma sugaban ba su ga kowa ba, sai ya ce kowa ya koma ma6uyar sa imnal ne na karshe ya fito daga cikin tafkin ya ruga izuwa cikin wani sashen gidan sarautar. A lokacin da imnal ya fito daga ruwan ne ya ruga akayi akasi shugaban dakarun ya waigo kawai sai ya hango imnal ya ganshi dan karami kamar wada. Al'amarin da ya ba shi mamaki kenan domin ya san cewa duk cikin yaran sa babu gajere ko wada. To ya ya akayi aka samu wannan? . A gigice shugaban dakarun ya ruga izuwa bakin tafkin kawai sai yaga nasa badakaren a saman 35 TASKARNOVELS.COM.NG ruwa a sume.Shugaban dakarun yayi sauri ya kwala wa yaransa kira suka firfito daga malafar su a guje suka taru a gaban tafkin. Ya dubesu yace lallai muna da baqo a cikin gidan nan ku bazama neman sa. Nan take dakarun suka bazu izuwa kowanne sashe na gidan sunan dube dube. Lokacin da imnal ya ruga cikin gidan sarautar yana la6e la6e sai ya rasa hanyar da ya kamata ya bi saboda bai san 6angaren turakar gimbiya mulaifa ba. Kawai sai ya bi kan wata matattakalar bene da gudu. Da zuwa ya ga dakaru za su gan shi sai ya nemi wuri ya 6uya. A haka ne yayi ta wuce dakuna barkatar yane leke leke ta cikin tagoginsu. Wani lokacin sai kaga saura kiris a ganshi sai kuma ya duka kasa ko ya shige cikin wani lokon ya 6uya. Yana cikin haka ne ya hango wani daki kofar sa a bude kuma fitila a kunne. Koda ya leqa tagar dakin sai ya hango kuyangin nan guda biyu a zaune cikin tararrabi idanun su a bushe babu alamar sunyi barci ko suna jin sa, cikin zafin nama imnal ya fada dakin ya rufo kofa. Koda kuyangin nan biyu suka ganshi sai sukayi sauri 36 TASKARNOVELS.COM.NG su kashe fitilar dakin, cikin rada daya daga cikin su ta matso dab da shi ta ce hakika ka cika mai sa.a yaya akayi ka shigo cikin gidan nan ka tsallake duk tsaron waje da na ciki? Imnal yayi ajiyar zuciya ya ce ni dai yanzu bani da lokacin amsa tambaya ,abin da nakeso da ku kawai kuyi mini jagora izuwa inda turakar gimbiya take. Cikin hadin baki suka ce"ta6dijan ka rufa mana asiri indai ba so kake a hallakamu ba shin ba ka jin guje gujen dakarun tsaro ne? Nan din nan ma da kake ciki hadari ne ga rayuwar mu idan aka shigo aka ganka. Abin da zamu iya yi maka kawai shine mu baka zanen taswirar gidan nan mai dauke da nunin inda gimbiya take" Imnal ya ce na gode da hakan ma maza ku bani. Cikin rawar jiki daya daga cikin kuyangin ta dauko taswirar wadda ke zane akan wata busasshiyar fata ta miqa masa ta ce "Wannan ita ce gudummawar mu a cikin soyaiyarku kai da gimbiya" Koda jin haka sai murna ta kama imnal yace "Ni kuwa nayi muku alqawari duk ranar da burin mu ya cika ni da gimbiya sai na 'yantaku na ba 37 TASKARNOVELS.COM.NG ku kyautar dukiya irin wacce ba.a ta6a baiwa wani ba" Gama fadin hakan keda wuya sai suka ji ana kwankwasa kofar dakin da qarfi ana yi musu tsawar su bude. Kafin kuyangin suyi wani yi wani yunkuri sai suka ga imnal ya daka tsalle sama kamar dan biri ya naushi saman rufin dakin wanda akayi shi da katako mai kaurin gaske. Take saman ya 6urma ya fice fit ta cikin sa. Koda imnal ya tsinci kan sa a saman rufi sai ya ci gaba da gudu akan dakuna. Ba zato sai yaji ana harbo masa kibiyoyi cul cul cul ! In ba don karfin gudun sa ba da tuni an sameshi, sai da yayi tafiya mai tsayi a sama sannan ya hango wani tafkeken tafkin wanka mai dauke da ruwa garai garai gunin ban sha.awa.kwatsam sai ya hango gimbiya Mulaifa a tsaye a gaban tafkinkwatsam sai ya hango gimbiya mulaifa a tsaye a gaban tafkin ta daga kai sama tana duba madubi. Koda imnal yaga babu kowa a kusada ita sai ya yadako tsalle ya fado cikin tafkin kafin ya fito daga tafkin tuni itama ta daka tsalle ta biyoshi ciki kawai saita danna shi izuwa kasan tafkin 38 TASKARNOVELS.COM.NG sukayi nutso ta wuce gaba yana biye da ita sai gasu sun biyo wani kwararo sun fito saman wani sabon tafkin wadda yake tsakiyar cikin turakarta babu kowa awajen face kuyangi fitowar keda wuya daga cikin tafkin sai kuyangi 2 suka rugo suka yafa musu mayafan goge jiki har izuwa wannan lokaci mulaifa bata dubi fuskar imnal ba balle tace dashi wani abu kuma fuskarta a murtuke take tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa. Al'amarin daya jefa imnal cikin mamaki kenan amma sai yayi shiru baice komai ba bayan an gama tsame lemar dake cikinsu sai Mulaifa ta sake kama hannun imnal zuwa dakin baccinta da zuwa sai dukkanin kuyangin da suke ciki suka fito waje suka rufo kofa nan take Mulaifa ta sharawa imnal mari ta fashe da kuka ta rungumeshi tana mai cewa saboda mai zaka saida rayuwarka kace sai kazo ka ganni a wannan dare, shin mun rabune har abada baxamu sake saduwa ba inda tsautsayi yasa ka hallaka da tuni nima na kashe kaina. Sa'adda imnal yaji wannan batu na mulaifa sai gabadaya jikin shi yayi sanyi nan take yaji kaunar mulaifa ta kara mamaye zuciyarsa kawai 39 TASKARNOVELS.COM.NG saiya janye jikinsa suna masu fuskantar juna yace yake abin begena kiyi sani cewa sa'adda na samu labarin halin da kika shiga sbd hukuncin da aka yanke min sai hankalina ya dugunzuma, naji bazan iya yin komai ba sai nazo na ganki burina na ganki da idanuna koda kibiyoyi dubu zasu nutse a cikin gangar jikina, sa'adda imnal yazo nan a zancen sai mulaifa ta sake rungumeshi cikin tsananin farin ciki tana mai cewa tabbas kaine zaka zamo abokin rayuwata gama fadin hakan keda wuya sai sukaji Sarki Maharaz na kwankwasa kofa yana cewa a bude alamarin daya dugunzuma hankalin imnal da kuyangun ita kuwa mulaifa ko a jikin ta kawai saita dafa imnal da dan yatsanta guda na hagu take imnal ya rikide yazamo kofin zinare irin wadda ake saka furanyi aciki faruwar hakan keda wuya sai mulaifa ta umarci kuyangin nata su bude kofar. Sarki maharaz ya shigo a fusace yana haki nan take ya kama kalle-kalle yana nazarin ko wace kusurwa batareda yace komai ba. daga can sai Mulaifa ta duci sarki tace babu wani bako daya shigo wajena koda jin haka sai sarki maharaz yayi murmushi ya matsa dab da Mulaifa ya dafa kafadunta yace yake yata a iya sanina baki taba min karya ba ashe za'a wayi 40 TASKARNOVELS.COM.NG garin ranar da zaki min karya saboda soyayya inaso kisani cewa na fahimci akwai soyayya tsakanin ki da imnal dan sarkin yaki tabbas shina nake zargi da shigowa gidan nan ahalin yanzu na tura dakaru zuwa gidan sarkin yaki idan sukaje suka iske baya nan tabbas toh shine yazo... hukuncin kisane zai tabbata akan shi maimakon horo. Koda mulaifa taji haka sai hankalinta ya dugunzuma amma saita dubi sarki maharaz batare da nuna wani damuwa ba tace ina mai tabbatarka imnal na gida a kwance, sarki maharaz yayi murmushi har ya juya zai fita sai idanunsa suka kai kan wannan kofin zinaren sarki maharaz ya kura kofin kurawa kofin idanu yana nazarinsa, a lokaci ne zuciyar Mulaifa ta fara bugawa. Lokacin da sarki maharaz ya kurawa kofin zinaren nan idanu yana nazarin sa a lokacin zuciyar Mulaifa ta fara bugawa da karfi bayan sarki maharaz ya gama nazarin wannan kofin saiya juyo ya dubi mulaifa yace yaushe kika samu wannan kofin? Nide asanina bantaba sayo irinsa ba mulaifa tayi murmushi tace ai musamman na aika birnin shamrun aka kera 41 TASKARNOVELS.COM.NG mini shi koda jin haka sai sarki maharaz ya karisa inda kofin yake ya daukeshi yana mai jujjuya shi a hanun shi yace amma fah ya bani sha'awa sosai shin zaki iya bani kyautarsa mulaifa tayi murmushi tace ya abbana ai komai kake so daga gareni basai ka tambaya ba dauka yakamata kayi kawai amma akwai wanda zaifi dacewa dakai nasa akera maka shi zaizo nan da kwana Bakwai, yayin da sarki maharaz yaji wannan magana sai jikinsa yayi sanyi kuma ya kasayin gardama kawai saiya ajiye kofin sannan ya sumbaci goshin gimbiya mulaifa ya fice daga cikin turakar. Fitarsa keda wuya sai kuyangi suka rufe kofar turakar. ita kuma mulaifa saita ruga ta dauko wannan kofin zinare nan take ta karanta wadansu dalamisan tsafi ta tofa akan kofin faruwar hakan keda wuya sai kofin ya tarwatse kamar an watsa hoda, sannu a hankali hodar ta dinga disashewa ta bace bat kawai sai gimbia mulaifa ta tafi izuwa kan gadonta ta kwanta domin sai a sannan ne hankalinta ya kwanta. Al'amarin imnal kuwa shide kawai ya tsinci kansa ne kan gadon cikin dakinsa kawai sai yaji ana magana da mahaifinsa hibru a kofar dakin ga dukkan alamu ran hibru a bace yake domin 42 TASKARNOVELS.COM.NG yana magana ne cikin daga murya da fushi maganar da imnal ya fara ji daga mahaifinsa itace, yanzu niza ayiwa haka to kusani cewa tun safe ina tareda dana kuma yanxu haka yana cikin dakinsa yana barci wata kakkausar murya tace "Ya shugabana kayi hakuri mu yan aiken sarki ne dan haka bai kamata kaga laifin mu ba saboda bin umarni ne, yanzu dolene ka bude mana mugani idan yana ciki musan amsar daza muje mugayawa sarki, idan kuma bazaka bude ba dolene mu bude da kanmu". Koda jin haka sai hibru yayi ajiyar zuciya yace ai bama sai takai haka ba. Nan take ya bude kofar dakin aiko saiga imnal yanata sharar barci abunsa kamar ma baisan abinda akeyiba sai jikin dakarun sarki yayi sanyi babban cikinsu mai kakkausar murya ya dubi hibru yace ka huta lafiya ya shugabana kawai saiya juya ya fita daga cikin dakin sauran dakarun kuma suka rufa masa baya, cikin hanzari hibru yaje ya kullo kofar gidan sannan yadawo cikin dakin imnal ya dubi imnal yace yakai dana tashi muyi magana nasan idanunka biu kuma tabbas ka fita daga cikin gidan nan cikin dare. 43 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin haka sai imnal ya mike zumbur ya kurawa hibru idanu cikin mamaki sannan ya sunkuyar da kanshi kasa cikin alamun kunya da rashin gaskiya. Koda ganin haka sai hibru yace yakai dana kayi sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dolene ya rigaka tashi a ka'idar rayuwata duk tsakar dare nakan farka na duba ko'ina na gidan nan kuma na fita kofar gida na kwanta, tun kafin a haifeka nake wannan al'ada kuma mahaifiyar ka batasan inayi ba, yauma kamar kullum hakan tafaru kuma dana duba cikin dakinka sai naga baka nan kuma dana duba waje sai naga babu dokinka, hakan ya tabbatar min dacewa ka fita cikin daren nan abinda bansani ba ina katafi? yanzu na samu amsar inda kaje tunda dakarun sarki sunzo don su tabbatar da cewa ko kaine kaje gidan sarki yakai dana mai yasa kake jefa kanka cikin rigima da tashin hankali mai kajeyi gidan sarki shin kamanta ne cewa kanada babban kaifi kuma a gobene za'ayi maka hukuncinsa. Sa'adda hibru yazo nan a zancensa sai jikin imnal yayi sanyi, daga can sai yadago kai cikin alamun nadama yace yakai abbana ka gafarceni 44 TASKARNOVELS.COM.NG kayi sani wannan kuskuren danayi bayin kaina bane zuciya ce ta ribance ni ina mai tabbatar maka ayanzu nida gimbiya mulaifa bazamu iya rayuwa ba idan bama tare da juna. Koda jin wannan batu sai hankalin hibru ya dugunzuma ya mike tsaye ya juyawa imnal baya lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla, imnal ya mike tsaye ya zagayo gaban hibru ya tsaya kawai saiya durkusa bisa gwuiwoyinsa ya kama tuba da neman gafara hibru kuma kama kafadan imnal yayi suka fuskanci juna a lokacin da hawaye ke zuba da idanunsu hibru yace yakai dana bakayi min laifin komai ba kayi sani cewa in bah soyayya ba da nine sarkin wannan birni namu, amma saboda na zabi soyayya nayi watsi da mulki in badan soyayya ba da maxan jiya guda uku wato jarumi hulkas mai hular Lamsara, Kaura Shaddadu na birnin Kufa mai mashin galilul haras da sadauki Hantaru mai takobin Saiful Lujara da basu mutu a banza ba tabbas soyayya tushen wahala ce sai mai sa'a da rabo ke tsallake shaukin cikinta ina tsoron kada rayuwar ka ta kare irin yadda tawa takare da kuma yadda ta mazan jiya takare, ya kai dana kayi sani cewa na ziyarci bokaye da dama kuma sun tabbatar min dacewa zaka samu daukaka 45 TASKARNOVELS.COM.NG anan gaba. Da wannan furuci nake maka sallama sai ka je ka kwanta ka rintsa muga abinda zai faru dakai gobe, gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaja kofar dakin ya rufe Imnal ya koma kan gadonsa ya kwanta. Tab! Gaskiya nima fa na fara tsorata da sha'anin soyayya dan haka zan ajiye dukkan wasu kalamaina na soyayya a wajen guda tunda ga jarumai ma masu dakakkiyar zuciya sun mutu a banza saboda tafarkin soyayya ballantana mu , amman dai wace irin shawara zaku bani shin na cigaba da soyayya ko kuma na hakura da ita gudun kada abinda ya faru da mazan jiya ya faru da ni. Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799. Zan ci gaba. 46 TASKARNOVELS.COM.NG MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part D Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Al'amarin sarki hibru kuwa tunda duku dukun safiya ya shirya abincin kalaci ya shiga dakin imnal sai ya iske shi acikin mafarki har yana surutai a fili, ba komai yake ambato ba face sunan gimbiya Mulaifa yana fadan kalamomin soyayya. Hibru ya daki kafar imnal yana mai daka mishi tsawa yace mai kakeyi har yanzu baka tashi ba, to kasani saura kiris mu makara zuwa fada, kashirya ka sameni a falo muyi kalaci, gama fadin hakan keda wuya sai hibru ya juya ya fita, shiko imnal sai yayi sauri ya kimtsa ya riski hibru a falo sukayi kalace sannan suka fita kofar gida domin su tafi izuwa fada. Da fitowarsu sai hibru ya shiga cikin bsuma ya kamo dokinsa da nufin su hau tunda na imnal baya nan, har sun yunkara zasu hau sai imnal ya 47 TASKARNOVELS.COM.NG hango nashi dokin ya tafo da gudu shi kadai, cikin gaggawa imnal ya rugo ya riske shi kawai sai yaga wasika a karkashin siddin dokin cikin zafin nama ya zare wasikar ya boyeta acikin rigar sa saboda kar hibru ya gani, nan take imnal ya hau kan dokin shi shima hibru hau kan nashi suka tafi fada. Fada ta cika makil babu abunda mutum zai gani sai kawunan bil'adama lokacin da hibru da imnal suka shigo cikin fadan kowa ya gama halatta har sarki kuwa sai da yazo, kuma a wannnan lokaci shi ake jira a hankali suka cigaba da tafiya bisa kafafunsu suka durfafi inda sarki yake. Sarki maharaz da gimbiya Mulaifa na zanne sun zubawa su hibru idanu shi dai sarki maharaz fuskar sa acike takeda murmushi amma na mugunta ita kuwa gimbiya Mulaifa fuskarta acike take da tsananin damuwa kamar zata fashe da kuka. Koda hibru da imnal suka zo dab da karagar sarki sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa. Sarki maharaz ya amsa gaisuwan cikin murmushi yana mai kauda kai ga kallon su kawai saiya dubi wadansu karti biyu majiya karfi da suke tsaye a gefe daya yayi musu inkiyar su cika aikin su, nan take kartin biyu suka kama imnal suka daure shi ajikin 48 TASKARNOVELS.COM.NG wani murtukeken ice mai gwafa dake kasa sannan sai suka yayyage rigar jikin imnal da karfin tsiya suka daga murtukeken icen sama suka soke shi acikin rami mai zurfi saiga imnal a sama. Koda kammala haka sai sarki maharaz ya miki ya fiskanci gabadayan jama'ar da suke fadan yace yaku jama'ar darul mahabur, kamar yadda kuka sani fiye da shekaru talatin da suka gabata muna bautan mai girma darbuza a kasar nan, ba ataba samun wanda ya karya doka ba, sai a wannan karon da imnal dan hibru ya aikata wannan laifi kusani mai girma darbuza shiya yanke hukunci dakansa hukuncin kuwa shine za ayita shara masa bulala har sai fatar jikinsa da kwoilewa kuma ana zuba mishi gishiri acikin shi har sai ya suma. Ba za'a kunce shiba sai ya kwana, kuma babu ci babu sha har na tsawon kwana uku. Koda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai gimbiya Mulaifa ta fashe

Chapter 2 of 13