Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TASKARNOVELS.COM.NG 1 TASKARNOVELS.COM.NG MAZAN JIYA 1 MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part A Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa anyi wata kasaitacciyar kasa mai suna DARUL MAHABUR. Kasar Darul Mahabur na da matuqar girma da fadi kuma ta qunshi manyan birane a karkashin mulkin sarki guda daya mai sun MAHARAZ IBN SULEDENI. Birnin darul mahabur ya bunqasa da karfin arziki, yawan alumma da kuma kasuwanci har 2 TASKARNOVELS.COM.NG ya zama abin kwatance a ko ina cikin duniya. Sarki Maharaz ya kasance mutum mai tausayi, taimako da jin kan al'umar sa, Allah ya hore masa arziki mai dunbin yawa gami da kaifin hankali da kuma hasashen gaba yana da matar aure guda daya kacal mai suna SHALIFAT kuma basu sami haihuwa ba sai bayan shekara 11 da yin aure don haka a yanzu 'yar su qaramar yarinya ce 'yar shekara 8 a duniya wadda ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance ana kiranta da suna MULAIFA. Tun daga lokacin da Allah ya baiwa Maharaz da Shalifata Mulaifa sai suka dauki soyaiyar duniya suka dora akanta ya zamana ko quda basa son suga ya sauka a kanta.tun da mulaifa ta taso ake tsantseni da ita kuma komai sai dai ayi mata koda ruwa zata sha sai dai a bata a baki batun jin dadi dai da hutu masana sunyi bincike sun tabbatar da cewa a wannan zamani babu 'yar gata kamar mulaifa ko kadan sarki maharaz bai kasance Sadauki ba hasalima bai ta6a yin yaqi ba, amma yana da Sarki yakk wanda ake kira HIBRU IBN IMLAS. 3 TASKARNOVELS.COM.NG Hibru ya kasance babban masoyin sarki maharaz wanda a koyaushe a shirye yake da ya sadaukar da rayuwar sa don kare ta sarki da mutuncin sarki. Sai dai wani abin mamaki shi ne duk irin wannan kauna da Hibru ke nunawa sarki tazama a banza don sarki yaqi yaja shi a jikinsa.Sharifa matar sarki maharaz ta sha yi masa fadan akan sabo da me yaki yaja hibru a jikinsa amma bai ta6a gaya mata dalili ba.sun sha samun sa6ani akan hakan har ma rai ya 6aci, akwai ranar da ta harzuqa sarki baisan sa.adda ya mare ta ba. Cikin tsananin mamaki sharifat ta ruqe kuncinta ta dubeshi a lokacin da qwalla ya cika idanunta tace "Ya kai mijina kayi sani cewa 2n da ka aureni baka ta6a gayamin baqar magana ba bare zagi,amma yau gashi ka mareni lallai dalilin da yasa ka mareni shine yasa baka son kowa yasan sirrin dake tsakaninka da saduki hibru, ni kuwa nayi maka alkawari komai daren dadewa sai na bincika wannan sirri na san shi" Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Maharaz ya dugunzuma ya risina a gaban sharifat tamkar qaramin yaro sannan ya ce "Ya ke matata ki yafe min bisa dora tafin hannuna a 4 TASKARNOVELS.COM.NG kuma a lokacin bana cikin haiyacina hakan ta faru ki ina cewa tunda muka hadu ni da ke ban ta6a rokon ki alfarma ba hakane? Cikin sanyin jiki sharifat tace "Kwarai kuwa" Sarki ya durkusa bisa guiwoyinsa a gabanta ya rike hannayenta a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace "Na roke ki don darajar iyayenki da soyaiya dake tsakanin mu da 'yar mu kada ki binciki wannan sirri domin ubangiji darbuza ya hanani yin hakan." sa.adda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai jikin sharifat ya qara yin sanyi ainun kuma ta cika da tsananin mamaki daga wannan rana bata qara yiwa sarki maganar hibru ba. Shima sarkin yaqi sau daya ya ta6a yin aure a rayuwar sa kuma matar tasa ta sami shekara 7 da mutuwa amma ta bar masa da guda daya kyakkyawan matashi dan shekara 12 ana kiransa IMNAL. Ya gado mahaifinsa a fagen sadaukanta har ma ana ganin cewa nan gaba idan ya girma sosai sai yafi mahaifinsa jarumtaka domin 2n yana da shekara 7 yake dakawa maza gumba a 5 TASKARNOVELS.COM.NG hannu.duk sa,adda za.a fita yaqi dashi ake fita kuma yana taka muhimmiyar rawa irin wacce manyan mayaqan hibru ya raina abokan gaba sai yayi zamansa ya 2ra imnal ya wakilceshi wajen dakarunsa. Hakika duniya tana da fadi take haka kuma abin cikinta yawa gareshi a can wata nahiyar daban kuma akwai wani gawurtaccem sarki mai suna Dujalu Ibn Shardud wanda ke mulkin birnin hawaruldin. Sarki dujalu ya kasance mashahurin mayaki, sadaukin sadaukai yana iya yakar mutanen gari guda ya kashe su ya kama matansu a matsayin bayi, ya kuma kwashe dukiyar su a matsayin ganima ta wannan hanya ce ya mallaki garuruwa da yawa a qarqashin mulkinsa kuma yana tara dukiya mai qazamin yawa. Bugu da kari sarki dujalu ya kasance qasurgumin matsafi wanda babu kamar sa a nahiyar. A lokacin da sarki dujalu ya ga ya qasaita sai yai bincike a cikin halwar tsafinsa don yasan matsayinsa a akan sauran sarakan duniya. Sai da ya kwana arba'in sannan ya kammala binciken inda hankalinsa yai ma2qar tashi ya rasa abin da ke masa dadi a duniya. Ba komai ya gani ba illa sarki maharaz shine yayi dai dai 6 TASKARNOVELS.COM.NG dashi komai da komai. Koda sarki dujalu yaga wadannan al.amura sai ya kamu da baqinciki ya aiyana a ransa dole ne yayi 2nanin hanyar da zai bi ya rushe daular sarki maharaz ya zamana ya kawar dashi daga doron qasa kuma ya gaje dukiyarsa da mulkinsa ya hada da nasa domin ya zama babu kamarsa a duniya. Bisa wannan dalili ne ya sake shiga halwa ta kwana saba'in don ya sami mafita. Mafitar itace dole ne ya mallaki wandansu makaman yaqi na # mazanjiya wadanda zamaninsu ya shude shekarun baya, wadanda ba a ta6a yin mayaqa tamkarsu ba,kuma ba.a ta6a samun makaman yaqi masu qarfin sihirin nas ba. Makami na farko shine wata sihirtacciyar takobi mai suna Saiful Lujara mallakar Sadauki Hantaru na Birnin Kisra sai mashi mai suna Galilil Haras mallakar Sadauki Shaddadu na birni kufa. Sai wata hular tsafi mai suna lamsara mallakin sadauki hulkas na birnin romaniya . ☼☼☼☼☼☼☼☼☼ 7 TASKARNOVELS.COM.NG Ita dai takobin saiful lujara duk abin da aka sara da ita sai ya tsage gida 2 koda dutse ne ko qarfe, kuma koda shafar jikin mu2m akayi da ita sai ya mu2 saboda mugun dafin da ya ke jikinta. A yanzu haka takobin ta na can ajiye a qarqashin tsakiyar tekun Bahar dufiya a ƙarƙashin tsaron dakarun aljanu dubu 90. Tun bayan mutuwar Sadauki Hantaru wadannan aljanu suka dauko takobin daga gidan hantaru suka kawota tekun bahar sufiya suka ci gaba da tsaronta. Ba za su gushe akan wannan aiki ba face izuwa qarshen rayuwar su don aduniya ba su da abin bauta face wannan takobi. Tun a lokacin da bokan ya qerata mutum uku kacal za suyi amfani da ita. Yanzu mutum daya yayi amfani da ita ya bar duniya ba a san sauran mutum biyun da suka rage ba. Duk wanda ya mallaki wannan takobi har abada ba za.a cishi da yaqi ba koda zai shekara miliyan a duniya. Su kuwa wadannan aljanu guda dubu 90 an gutsuri ruhin kowannen su an sa a cikin sinadarin qarfen da akayi wannan takobi, shi ya sa suka mallaka rayuwar su a kan babu wanda 8 TASKARNOVELS.COM.NG ya isa ya iya rabasu da ita face yana cikin mutane 3 da ke da damar anfani da ita. ☼☼☼☼☼☼☼☼ Mashin Galilil haras mallakin Sadauki Shaddadu na Birnin Kufa, a halin yanzu yana ajiye a can wani kogon sihiri dake birnin kufa, fiye da shekara dubu tun da aka ajiye mashin ba wani mahaluki da ya sake shiga kogon. Shi dai kogon a cikin ƙarƙashin kasa yake mutum bai isa ya ga inda kofar kogon take ba face ya zo da takobin saiful lujara wajen ita ce zata sa shi a kan hanya ta shigar da shi har cikin kogon ta bude masa kofofi 99 ya isa inda aka ajiye mashin galilil haras. Haka kuma mashin na iya rikida ya zama abin hawan mu2m doki ko rakumi wanda ba zai gaji da tafiya ko yunwa ko kishin ruwa har kwana 40. 9 TASKARNOVELS.COM.NG ☼☼☼☼☼☼☼☼ Ita kuwa hular lamsara shu'umar hula ce wadda idan mutum ya sanyata yana iya ganin abin da ke gaban sa nisan tafiyar kwana 40 tamkar abin a gabansa yake, haka duk irin guguwar da akeyi ko tsananin ruwan sama ba zasu kusance shi ba. Sai dai ka ga yana tafiya amma babu su a inda yake. Hular lamsara na ajiye a cikin wani gida na kayan tarihi da ke birnin romaniya, in da aka ajiye kayan tarihin dukkanin sarakunan birnin wadanda suka shude, babu wani tsaro akan hular amma komai hatsabibancin mutum bai isa ya dauke ta ba face ya shigo dakin dauke da mashin galilil haras. Bayan sarki dujalu ya gama nazarin wadannan kayan yaqi na # mazanjiya sai ya cika da tsananin farin ciki yayi ta kyalkyata dariyar murna. Kashe gari kuwa da sassafe yasa a ka shirya dakaru miliyan dubu suka kama hanya suka nufi nahiyar da tekun bahar sufiya take domin dauko 10 TASKARNOVELS.COM.NG takobin saiful lujara, sannan su wuce birnin kufa da birnin romaniya don dauko mashin galilil haras da hular lamsara. ***************** A can birnin darul mahabur kuwa yau ne a ke bikin qarshen sheka na bautar gunkin darbuza. Tunda duku-dukun safiya dakin bautar ya cika da jama.a maza da mata duk inda mutum ya hanga sai dai yaga kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke, shi dai wannan dakin bauta yana da ma2qar girma da fadi.domin ya kai girman wani garin.A duk shekara mutane na zuwa daga dukkan sauran qasashen dake nahiyar domin neman tubarraki. Saboda haka duk shekara akwai wakilan wadan nan manyan sarakuna tara dake zuwa wadan nan dakin bauta. A wannan rannan rana sadauki hibru da dansa imnal sunzo bautar da wuri-wuri. Ba komai ne yasa hakan ba face imnal ne ya sa matsawa 11 TASKARNOVELS.COM.NG hibru akan lallai su zo da wuri don su kusanci gunkin darbuza. Maganar gaskiya ita ce ba don su kusanci darbuza bane sai don kawai yaje kusa da gimbiya mulaifa ta ganshi ya ganta. 2ni imnal ya sha alwashin cewa llai a yau ne zai furtawa mulaifa cutar da take addabar zuciyar sa tsawon shekara bakwai kuma a shirye yake ya dauki duk irin horon da za.ayi masa. Cikin sa.a kuwa su hibru suka kusanci inda gunkin darbuza yake ya zamana tazarar da ke tsakaninsu da inda su maharaz ke zaune ba ta wuce taku biyar ba. Gaba dayan dakin bautar tayi tsit,kuma kowa ya rufe idanunsa ya sunkuyar da kansa qas. Dama haka qa'idar dokar bautar take kuma sai an shafe a qalla sa'a guda a haka,sannan sarki maharaz zai miqe yayi bayanin jawabin da gunkin darbuza yayi masa, ma.ana ya isar da saqon darbuza ga jama.a. Dama duk shekara gunki darbuza yana bayani ne akan abubuwan da sa su faru a nahir na alheri ko na tsiya. Kua duk abin da ya fada suna faruwa ne ba a ta6a samun akasi ba. Game da abubuwan tsiyan da 12 TASKARNOVELS.COM.NG za su faru sai ya fadi abin da za ayi domin neman tsari ko sauqi. A wannan lokaci da kowa ya sunkui da kansa qas kuma ya rufe ido akayi tsit ne, imnal ya dago kansa ya bude idanunsa wato ya karya dokar bauta. Kawai sai ya miqe tsaye ya tafi cikin sand'a yana tsallake mutane har isa inda gimbiya mulaifa ke zaune su biyu rak. Kawai sai imnal ya zauna daf da mulaifa ya dauki hannunsa guda ya d'ora akan nata cikin firgici mulaifa ta d'ago kai don taga wanda ya ta6a ta, koda tayi arba da imnal sai ta qura masa idanu ta qame tamkar ba ta da rai . Nan take taji ta kamu da tsananin qaunar sa bata san sa.adda ta dafa hannun sa da nata d'ayan tayi masa murmushi sannan tasa bakinta akan kunnensa tayi masa magana a cikin rad'a "tabbas kaine imnal d'an sarkin yaqi hibru" ko da jin wannan ba2 sai mamaki ya kamashi don haka sai shima ya kara bakinsa a kunnenta yace "tabbas maganarki gaskiya ce amma ya akayi kika sanni alhalin nayi imani cewa baki ta6a ganina ba?". 13 TASKARNOVELS.COM.NG Mulaifa ta ce ansha bani labarinka a siffanta mini kamanninka. Na dade ina kwatantaka a cikin zuciyata.kamannin da nake gani a mafarkina su na gani a yanzu. Kai kuwa menene dalilin da yasa ka karya dokar bauta kazo har wajena? Shin baka tsoron sarki ya sa ayi maka horo mai tsanani? Imnal yayi murmushi ya ce ya ke ma.abociyar kyau da kwarjini ki sani cewa zuciyar da ta kamu da begen masoyi makauniya ce kuma kurma ce. Haka zalika ba ta tsoron komai a duniya muddin za ta sadu da abin begenta. Lallai na dad'e ina begenki a zuciya ta tsawon shekaru bakwai kuma a yaune nayi alqawarin sai na furta miki ciwon zuciya ta ko da kuwa bayan nai hakan za.a tsireni nan gaban miliyoyin wannan jama.a. Da taji wannan zance sai idanunta suka ciko da qwalla ta ce "godiya ta tabbata ga ubangiji darbuza wanda ya cusa min qaunar ka a zuciyata 2n kafin na ganka da ido na." ya kai masoyina ka sani daga ranar da na fara jin labarinka ni ma naji na kamu da tsananin qaunar ka kuma nima yau shekara bakwai 14 TASKARNOVELS.COM.NG kenan ina fama da begenka a zuciyata,bani da burin da ya kai na ganka da idanuna amma damar hakan bata samu ba sai yau. Da yaji wannan ba2 sai ya kamu da tsananin farin ciki kuma yaji sonta ya qaru a ransa d'ari bisa d'ari, kawai sai suka rungume juna.' a dai dai Wannan lokaci ne sarki maharaz ya d'ago kansa sama ya bud'e idanunsa sharkaf da hawaye.' ba zatao ba tsammani sai ya ga Mulaifa da Imnal a kankame da juna. A dai dai wannan lokaci ne sarki maharaz ya dago da kansa sama ya bude idanunsa domin ya yiwa jama'a bayanin sakon darbuza, idanunsa sharkaf da hawaye. Nima ganin yadda sarki Maharaz ya dago da jajayen idanunsa yayi matukar bani tsoro yasa na tsaya cak da typing, sai Allah Ya kaimu gobe mu cigaba. Zan ci gaba. 15 TASKARNOVELS.COM.NG Da fatan anyi sallah lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part B Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Ba zato ba tsammani sai ya ga mulaifa da imnal a rugume da juna daf da shi al.amarin da ya matukar firgitashi kenan,kuma ya cika da tsananin mamaki, ya tambayi kansa, "ya ya akayi imnal ya tsallako yazo har nan inda muke? Kuma ya akayi mulaifa ta yarda dashi har 16 TASKARNOVELS.COM.NG ta rungumeshi alhalin ta kasance mai ji da kanta da kare martabarta"? Gama aiyana hakan ke da wuya sai mulaifa ta dago kai tayi arba da sarki yana kallonsu cikin razana ta janye jikinta daga na imnal. Al'amarin da ya sa shima ya juya kenan ya yi arba da sarki maharaz ya daka masa harara ba tare da ya ce da shi uffan ba. Imnal ya juya da sauri ya koma can wajen mahaifin sa ya zauna ya kara sunkui da kansa kas, ita ma gimbiya Mulaifa sai ta sunkui da kansa qas ta rufe idanunta zuciyarta na ta daka. A sannan ne sarki Maharaz yai ajiyar zuciya gami da gyara murya. Koda jin gyaran muryar tasa sai kowa ya dago da kai aka qura masa ido. Da aka ga hawaye na zuba a idanun sarki sai hankalin kowa ya dugunzuma,sabo da ba a ta6a ganinsa a cikin irin wannan hali ba. Sarki Maharaz ya qara yin gyaran murya a qaro na biyu sannan ya dubi jama.a cikin tsananin tashin hankali, domin mai girma darbuza ya gaya min cewa rayuwar dukkanin jama.ar dake wannan nahiya na cikin mugun hadari, sa6o da akwai wani gawurtaccen sarki mai suna dujalu 17 TASKARNOVELS.COM.NG wanda ke mulkin birnin hawarul din. Bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu da ni da sarki dujalu mun yi kunnen doki a qarfin mulki, arziki da girman kasa. Bisa wannan dalili ne kishi ya kama sarki dujalu ya sha alwashin cewa sai ya rushe daulata ya mallake mulkina da arziqina sannan sai ya mamaye duk kasashen da ke wannan nahiya tamu. Ba ma nahiyar mu kadai ba gaba daya duniyar yake son ya mallaka sabo da biyan wannan buqata ne sarki dujalu ya shiga halwar kwana saba'in ya samo mafita bita bisa samun biyan buqata. Mafitar kuwa ita ce dole ne yaje ya samo wadansu sihirtattun makaman yaqi guda wadan su zaqaquran sadaukai uku MAZAN_JIYA wadanda a zamaninsu ba a sami kamar ba. Wadannan mutane su ne, kaura Shaddadu na birnin kufa, sadauki Hantaru na birnin kisra, da kuma Hulkas na birnin romaniya. Wadannan barade sun cika MAZAN JIYA domin har yau har gobe ba a sami jarumai ba kamar su kuma har i zuwa qarshen duniya ba za a ta6a mancewa da tarihin su ba. Shi sadauki 18 TASKARNOVELS.COM.NG 1... Hantaru yana amfani da wata sihirtacciyar takobi ce mai laqanin Saiful Lujara, kome aka sara da ita sai ya dare gida biyu tamkar a sa wuqa a yanka lemon 6awo koda kuwa a takobi sai ya mutu saboda kaifin dafin da ke jikinta. 2...Shaddadu yana amfani da wani sihirtaccen mashi ne mai laqanin Galilil Haras, duk mahalukin da ya mallaki wannan mashi komai yawan abokan gaba shi kadai zai iya hallakasu da mashin, domin a duk sa'add ya cillashi cikinsu sai ya burma cikin mu2m dubu arba'in a cikin dakiku kadan, sannan zai dawo hannun sa. Mashin galilil haras yana da tsananin haske don haka komai duhun waje in dai aka shiga da shi sai anga komai ko da kuwa allura ce ta fadi qasa.bugu da qari mashin na iya rikidewa ya zama abin hawan mamallakin sa walau doki ko raqumi kuma ba zai gaji da tafiya ba, ba zai buqaci abinci ko ruwa ba har kwana arba'ing. 3... Hulkas shine mamallakin hular qarfe mai suna Lamsara. Ita lamsara ta kasance shu'umar hula ce in dai mutum yana sanye da ita yana iya ganin abin da ke gabansa, haka kuma duk irin 19 TASKARNOVELS.COM.NG guguwar da akeyi da tsananin ruwan sama ba za su kusanci inda yake ba. Wannan kadan ne daga cikin sihirin wadannan makamai na Mazanjiya. Akwai sauran sirrikan wadanda babu wanda ya san da su face masu su. Wato mazanjiya. A halin yanzu tuni sarki dujalu ya baro kasar sa tare da dakarun sa na yaqi ya nufi tekun bahar sufiya don dauko takobin saiful lujara. Daga birnin hawaruldin zuwa tekun bahar sufiya tafiyar shekara uku bisa doki ko raqumi ba tare da ya da zango ba." ko da sarki dujalu zai yi anfani da qarfin sihiri wajen yin wannan tafiya kuma koda akan aljanu za su tafi dole su shafe sama da shekara guda kafin su isa tsakiyar tekun bahar sufiya. Neman takobin saiful lujara a cikin kogin kuwa dai_dai yake da neman jaki mai qaho, wato dai mace ce da ciki zata iya haihuwa lafiya kuma zata iya rasa rayuwarta. A taqaice al'amari ne na sa'a da rabo, amma dai sai babbar sa'a sannan za'a dace. Idan har aka sami nasarar dauko takobin saiful lujara to lallai sauran makaman biyu ba za suyi wahalar samu ba sosai. Duk mutumin da ya 20 TASKARNOVELS.COM.NG hada wadannan makamai a jikinsa shi kadai tabbas ya cika GAGARABADAU kuma sai ya mulki duniyar na n gaba dayanta. Ba wai mutane kadai zai mulka ba hatta aljanu, dabbobi da dukkanin halittu sai ya iya sarrafa su har tsuntsaye kuma babu halittar da ba zai iya yin magana da ita ba, kuma ya bata umarni ta bi dole. Ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa ba mu ga ta zama ba, dole ne mu mike tsaye mu zage damtse don ganin mun riga sarki dujalu samo wadannan makamai guda uku. Idan kuwa mukayi sakaki ya riga mu samunsu to muna ji muna gani zai zo ya baje qasarmu ya kashe mazajen mu sannan ya gaje matan mu da 'ya'yan mu da dukiyoyin mu. Ya zama wajibi mu aika da wannan sako ga sauran kasashen da ke karkashin wannan nahiya tamu domin mu sanar da su halin da ake ciki kuma mu nemi gudunmawar su bisa wannan gagarumar tafiya". Sa'adda sarki maharaz yazo nan a zancen sa sai dakin yayi tsit tamkar babu kowa a cikin sa. 21 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take dakin bautar ya watse jama'a suka tafi suna tattauna wannan lamari a cikin firgici da matukar damuwa. A wannan rana dai mutane ba su da hirar da tafi ba2n shirin sarki dujalu. Nan da nan labarin al'amarin ya fara bazuwa sauran garuruwa birane da qauyuka da kuma sauran qasashen maqofta. Duk jama'ar da ta ji wannan labari sa ta rude ta shiga shirye shiryen kare kai da bayar da dakarun gudunmawa izuwa birnin darul mahabur. Tun a wannan rana ne sarki maharaz ya aiki wasu zakwakuran hadiman sa na jinsin aljanu suka kai wasika zuwa dukkanin sarakunan da ke muli a nahiyar. A cikin sa'o'i kadan labarin ya riski ko in da ina sarakai suka firgice ainun kuma suka miqe tsaye wajen fara shirye shiryen tafiya. Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki maharaz bayan ya sanar da jama'ar sa jawabin gunkin darbuza wanda aka saba yi a duk qarshen shekara a lokacin bauta. ☼☼☼ ☼☼☼ ☼ 22 TASKARNOVELS.COM.NG Al'amarin imnal da mahafin sa sarkin yaki hibru kuwa, tun da suka baro dakin bauta suka nufi hanyar gida sai duk suka yi shiru suna tunani a cikin zukatan su ba tare da sun ce kala ba. Shi dai sarkin yaki hibru ba komai ya ke tunani ba face kiyasta rayukan da za'a yi asara yayin wannan tafiyar gami da irin dukiyar da za'a 6arnatar. Haka kuma yana jimamin tafiyar da za.ayi abar mata yara da tsofaffi kawai a birnin ba tare da an bar musu dakarun tsaro ba wanda hakan na iya janyo komai ya faru, duk da cewar sadauki hibru ya san cewa bashi da mata, kuma bashi da sauran dangi a fadin kasar gaba daya sai yaji takaici da baqin ciki suka mamaye zuciyar sa saboda ya san cewa wannan gagarumin yaki da za'a fita ba karamar masiba bace da koma bayan ci gaban nahiyar gaba daya domin zai janyo karyewar tattalin arziqi kuma masoya za su rasa masoyan su, iyaye za su rasa 'ya'yansu 'yan uwa zasu rasa 'yan uwansu. Koda hibru yazo nan a zancen sa sai idanunsa suka ciko da qwalla saboda tausayin halin da jama.a za su shiga. 23 TASKARNOVELS.COM.NG Shi kuwa sadauki imnal ko kadan tunaninsa ba irin na mahaifin sa bane. Abin da yafara fado masa a rai shine wai shin ya za.ayi ya mallaki wadannan kayan yaki guda 3 na MAZAN JIYA? Koda ya gama aiyana hakan a zuciyarsa sai ya yiwa kansa dariya ya ce Amma fa bani da hankali akan wane dalili ne ma zan nemi abin da ya gagari manyan sarakunan duniya masu taqama da komai. Gama aiyana hakan ke da wuya sai gimbiya mulaifa ta fado masa a rai ya ce to wai shin yanzu za'ayi tafiyar nan tare da gimbiya mulaifa kuwa? Lallai zan kasance mai tsananin baqin ciki idan ba a tafi da ita ba. Idan kuwa aka tafi da ita sai na fi kowa farin ciki a fadin duniya. Haka dai imnal yayi ta saqe saqe a zuciyar sa har suka isa qofar gida. Dama imnal ne akan gaba har ya sanya qafar sa a cikin qofar gidan sai ya dakata ya waigo ya dubi hibru fuskar sa cikda alamun damuwa koda ganin haka sai hibru ya tsaya cak ya kura masa idanu sannan ya ce mene ne ya faru? Imnal ya ce ka gafarceni ya abba na nayi babbar mantawa dazu a dakin bauta sarki ya ce min na 24 TASKARNOVELS.COM.NG fada maka muzo ni da kai yana neman mu a fada da yammacin gobe. Ko da jin wannan batu sai hankalin hibru ya tashi yai shiru ya sunkui da kansa qas .daga can kuma sai ya dubi imnal ya ce ka gaya min gaskiya shin kayi wani laifi dazu a dakin bauta??? Jin wannan tambaya sai imnal ya sunkui da kanasa alamun rashin gaskiya ya ce qwarai kuwa nayi laifi. Domin na tashi daga inda nake zaune naje wajen gimbiya Mulaifa.... Koda jin haka sai hibru ya dafe kai yana mai ajiyar numfashi, sa'annan ya ce tabbas na san cewa ruwa baya tsami banza. Ni dai a sani na sarki bai ta6a neman shawarata ba sai dai kawai a gaya min cewa za'a fita domin naya shiri. Tabbas ka aikata babban laifi don haka dole ne ka fuskanci mai tsanani saboda wannan laifi don haka ni babu ruwana, tsuntsun da yaja ruwa shi yake duka. Koda jin wannan magana

Chapter 1 of 13