Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bai taba fada mani ba a yanzu, wanda shine sanadin da yasa ya nisanta abotarmu. Lokacin da Hibru ya zo nan a labarinsa sai hawaye ya zubowa sarki Maharaz ya matso daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan ya ce ya kai abokina hakika abinda kake zargi tabbas haka yake, idan baka manta ba a ranar da gimbiya Sahira ta kashe sarki Dumbazu acan birnin Karlus ta fada mnai wani sako a cikin kunne na cikin rada ko ba haka ba? To wannan sako ba wani abu bane face wasiyya daga mahaifinta wacce ya sanar da ita tun kafin sarki Dumbazu ya zo ya saceta, abinda ya fada mata shine, lallai ta sanar da ni cewar dole ne na nisnta da kai tun daga ranar da n zama Sarki birninmu na darul mahabur, idan kuwa naki to tabbas mulkina zai rushe, kaima kuma burinka bazai cika ba, domin ba zaka zama Sarkin yaki ba, kuma duk mu biyun ba zamu samu haihuwa ba har abada, bisa wannan alilai ne yasa na yanke abotarmu kuma na nisanta kaina daga 122 TASKARNOVELS.COM.NG gareka, amman a kullum sai na shiga turakata na kulle kaina nayi ta kukan bakin ciki ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai abokina ka gafarceni inaso ka fahimta cewa dole ce tasa na aikata hakan a gareka bawai a son raina bane kuma dama ance kada na sanar da kai gaskiyar al'amarin sai a lokacin da naga gagarumin yaki ya taso wanda bamu da tabbacin samun nasara akan shi. Sa'adda Sarki Maharaz ya zo daidai nan a jawabinsa sai Hibru ya rungumeshi, take duk su biyun suka rushe da matsanancin kuka suna masu daɗa kwakumar juna. Mulaifa dake tsaye tana kallonsu sai ta kamu da tsananin tausayinsu, itama sai ta fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu. Bayan sun jima a cikin wannan hali sai Sarki Maharaz ya janye jikinsa daga na Hibru suka sake kallon juna a karo na biyu sannan ya ce ya kai abokina kayi sani cewa abotarmu ta zama samu kamar yau muka fara ta, kuma ina neman alfarma guda daya a wajenka. Cikin murmushi Hibru ya ce fadi duk abinda kake so zanyi maka shi, sarki Maharaz ya ce ina so kabar yata Mulaifa tayi jinyar Sadauki Imnal a cikin wannan tafiya da zamu yi, lallai tare da 123 TASKARNOVELS.COM.NG ita za a yi wannan tafiya. N sani cewa Imnal yana matukar kaunar Mulaifa idan har tana tare d shi sai ya fi saurin warkewa, samun kafiyarsa da wuri shine samun kwanciyar hankalinmu, domin bincike ya tabbatar da cewa rawar da Imnal zai taka a wannan yaki ko ni da kai ba zamuyi rabinta ba. Da jin haka sai Hibru ya yi murmushi tare da cewa na amince da haka. Nan take farin ciki ya lullube Mulaifa da sarki Maharaz, har suka rungume juna tare. Sadauki Imnal na kwance a cikin dandazon mayakan da zasu fita yaki izuwa tekun Bahar Suffiyya, sai kawai akaga kuyangi da dakarun sarki Maharaz sun rako gimbiya Mulaifa suna masu ratsowa ta sansanin dakarun yakin, nan fa aka zuba ido aga wajen wa kuma gimbiya ta zo, kunyangin dake yi wa gimbiya Mulaifa su 12 ne, 6 na dauke da faratin abinci da abinsha iri-iri, ragowar 6 kuwa suna dauke da magunguna, shimfidu da kuma tanti. Kai tsaye gimbiya Mulaifa ta durfafi inda Sadauki Imnal yyake kwance, al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a wajen, da isowar Mulaifa gaban Imnal sai ta durkusa daf da shi, ta dubeshi tare da 124 TASKARNOVELS.COM.NG sakar masa wani tattausan murmushi ta ce da shi nice baiwar daka bukaci mahaifinka ya samo domin yin jinyarka. Koda jin haka sai Imnal ya yunkura da nufin ya mike tsaye, amman sai Mulaifa tayi sauri ta danne kafadarsa ta maida shi kwance, Imnal ya ce wane ni na kalleki a matsayin baiwa, ai nine bawanki, haba ya shugabata ki kula fa domin kina gaban talakawanki kike kada kije kiyi abin kunya. Koda jin haka sai Mulaifa ta bushe da dariya tare da cewa ya kai masoyina, kayi sni cewa shi so makahone kuma kurma ne, wanda duk yayi zurfi a cikin kogin so to baya ji kuma baya gani, nayi nisa a cikin kogin kaunarka dan haka babu abinda zai sa naji kunyar wani mahaluki yayi kyautata maka. Ina son k saki jikinka ka daina dari-dari da shakkar komai, domin mahaifina ne ya turoni gareka da kansa kuma ya umarceni da nayi jinyar ka a yayin wannan gagarumar tafiya da zamu yi har izuwa lokacin da zaka samu lafiya ka warke sumul. Ina mai dada yi maka albishir da cewa a halin yanzu abotar mahaifinka da abbana ta dawo sabuwa kamar da. Nan take Mulaifa ta baiwa Imnal labarin duk 125 TASKARNOVELS.COM.NG abinda ya faru a dakin gani tsakaninta da sarki Maharaz da kuma sarkin yaki Hibru. Koda ta gama bashi labarin sai nan take yaji wani irin farin ciki ya lullube shi irin wanda bai taba jin kamarsa ba, kwatsam! Sai suka ji an fara busa algaita gami da kida tambura alamar cewa sarki ya fito daga cikin gida domin a fara wannan gagarumar tafiyar. Nan take kowa ya nutsu aka mimmike tsaye, masu dibar kya na diba, masu hawa dawakai suna hawa, wasu kuma ana tattara dukiya da guzuri ana laftawa rakuma, dawakai da kuma keken doki. Koda sarki Maharaz ya fito daga gidan sarauta sai aka ganshi tare da abokinsa sarkin yaki Hibru bisa kan fararen dawakai biyu, duk sunyi gagarumar shigar yaki kala daya suna tafe suna fira cikin nishadi abin gwanin ban sha'awa. Gabadaya jama'ar dake filin fadar sai suka cika da matuƙar mamaki, domin rabon da aga Maharaz da Hibru a haka tun kafin su samu sarauta, maimakon sarki Maharaz da Hibru su tsaya gaban jama'a suyi bayanin karshe na wannan tafiya, sai suka wuce kai tsaye wata 126 TASKARNOVELS.COM.NG hanya da zata kaisu zuwa dakin gunki darzuba. Da isarsu kofar dakin bautar sai suka sakko daga bisa dawaknsu, bayin dake biye da su sukayi sauri suka kama dawakan suka rike. Maharaz da Hibru suka shige cikin dakin bautar rike da hannun juna, a haka har saida suka isa inda gunki darzuba yake, isarsu keda wuya sai suka durkusa bisa gwiywoyinsu sannan suka suddar da kawunansu kas, kuma suka rufe idanunsu. Bayan sun dan jima a haka kawai sai suka yunkura da nufin su fece daga cikin dakin bautar, ba zato sai suk ji muryar darzuba yana mai cewa "Ku dakata mana tukunna yaku abokan asali, kuma masoyan gaskiya, sannan aminan zahiri. Cikin hanzari suka koma suka durkusa kamar yadd suka yi a farko. Darbuza ya ce hakika a yau ina mai matukar farin ciki da dawowar abotarku, domin kuwa kunyi hakuri da dukkanin kunci gami da takaicin da muka jarabceku da shi, domin inganta rayuwarku da nuna amincewarmu bisa karbar bautarmu da kuke yi ba dare ba rana. Nayi maku alkawari zan tsare rayukanku daga dukkanin irin masifun da zaku shiga a cikin 127 TASKARNOVELS.COM.NG wannan gagarumar tafiyar, kuma lallaı duk irin wahalar da zaku sha karshe kune zaku yi nasara, abinda bni da tabbacin yi maku alkawarinsa shine kare lafiyarku, dalili kuwa shine wanda kuke bautawa da wanda su sarki duzalu ke bautawa ya kasance mai karfi kamata kuma shine babban makiyina a duniya, tabbatas muna yi gaba mai tsanani kwatankwacin irin wadda sarki huburu da sarki darzuba suka yi kafin mutuwarsu. Ina mai sanar da ku cewa nima ina nan ina gagarumin shirin yaki domin tunkarar abokan gaba acan tekun bahar Suffiyya, wanda kokarinsa shine ya kare sarki dujalu kuma ya bashi ikon da nasarar dauko takobin saiful lujara, kmar yadda nima zan kareku kuma na baku nasara, wannan yaki da za a yi a bakin kogin bahar Suffiyya ba a taba yin kamarsa ba a tarihin duniya ba, domin sai anyi asarar dubun nan rayukan miliyoyin aljanu da biladama da kuma dukiya mara adadi. Dole ne cikin biyu ayi daya, kodai su halakamu ko kuma mu mu halakasu, amman ina da yakinin cewa mune da nasara domin nayi bincike har sau dubu dari amman banga komai ba sai nasara a garemu, da wannan kalami ne nake sallamarku sai mun hadu a bakin kogin bahar Suffiyya, lallai 128 TASKARNOVELS.COM.NG zamu gajarce maku tafiyar daga kwanaki masu yawa zuwa kwanaki kadan. Sa'adda darzuba yazo nan a jawabinsa sai Sarki Maharaz ya bude baki yayi godiya, shiko Hibru sai yayi shiru bai ce komai ba, tun sa'ar da darzuba yayi nisa a cikin jawabinsa sai zuciyar Hibru tta cika da wasiwasi ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa ya ce wai shin wannan wane irin abune muke bautawa, wane ne haka muke bautawa wanda basji da cikekken yakini, ai bai kamata ace abinda ake bautawa yana shakkar wani abu ba, kai ni a ganina ma kamar akwai wani guda daya wanda yafi dukkaninsu karfi da iko, inya so sai ya yake su ya kawar da su dukkaninsu ya zamana cewa shi kadai ake bautawa. Nikam dama can zuciyata ta dade tana rawa akan wannan abin bautar na mu, domin sau tari yana barinmu muna shan bakar wahala, da kyar muke tsira da rayuwarmu, to yanzu kuma gashi shi da bakinshi yake cewa yana da kishiya gami da abokin gaba amman muje zuwa sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba. Nan dai Maharaz da Hibru suka mike tsaye suka fice daga cikin dakin bautar, kai tsaye suk koma bakin kofar fada suka sake tsayawa, bayan sun 129 TASKARNOVELS.COM.NG sauka daga kan dawakai sai sarki Maharaz ya wuce zuwa kan mimbari yayin da Hibru ke take masa baya, bayan sun hau kan mimbarin ne sun tsaya sun masu fuskantar jama'a sai Sarki Maharaz ya bayanin godiya ga jama'a uma yayi gaisuwa ga baki wadanda suka zo daga sauran makwabtan kasashe domin kawo agajin yaki bisa kare mutuncin nahiyar gabadaya. Daga nan sai yayi bayani ga jama'a inda ya kara masu kwarin gwiywa da karfafesu bisa mahimmancin wannan yaki da za'a fita. Yana gama wannan jawabi ne jama'a suka barke da shewa aka hau yi masa kirari. Nan take sarki Maharaz da sarkin yaki Hibru suka yi wa gabadaya jama'ar jagora, wato suka wuce gaba aka bisu duw a baya. Inda ace mutum na nan tsaye a wajen yaga wannan rundunar ke fitowa daga cikin birnin darul mahabur sahu sahu bisa rakuma, dawakai da alfadarai sai yayi tsammanin cewa gaba daya mutanen duniya ne suka fitowa saboda yawansu. Wannan shine abinda ya faru a birnin darul mahabur bayan kasashen dake nahiyar gaba daya sun hada kai sun fita gagarumin yaki dan kare buranensu daga sharrin sarki dujalu. 130 TASKARNOVELS.COM.NG ********************** Al'amarin Sarki Dujalu kuwa lokacin daya durfafi hanyar kofin bahar Suffiyya tare da dandazon dakarunsa na yaki mutum miliyan dubu daya da suke tafiya bisa wasu zaratan dakarun aljanu suma miliyan dubu daya. Wohoho! Hakika tashin hankali ba a samasa rana zuwa yake ba sallama, idan mutum yayi arba da wannan zuga ta rundunar sarki Dujalu zai iya haukacewa koma zuciyarsa ta buga fat daya, saboda tsananin kwarjininsu gami da bna tsoro, idan aka ce zasu iya tashin duniyar nan kaf a cikin sa'a daya su baje kaf biranen to ba za ayi mamaki ba, idan suna tafiya a kasa bisa turba aka hangosu daga nesa kamar zango dari sai mutum ya jiyo takun sawayensu wnda ke haddasa girgizar kasa, idan kuwa a sama suke tafiya sai kaga sun haddasa gagarumar guguwa wadda ke haddasa bishiyoyi su kama rangaji suna karyewa da zubewa kasa, koguna kuwa su kuma tambal-tambal suna zubewa kasa. 131 TASKARNOVELS.COM.NG Sarki Dujalu na da matan aure guda dari da goma sha daya, amman bai taba samun haihuwa ba, bashi da iyaye kuma bashi da sauran dangi face wata kanwarsa guda daya wacce ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance wacce suke uwa daya uba daya ana kiranta da suna Hursiyya. A duniya babu abinda sarki Dujalu ke tsantseni sama da kanwarsa Hursiyya, domin ko kadan baya kaunar abinda zai sosa zuciyarta ko kuma ya taba lafiyarta, duk inda kaga sarki Dujalu to fa sai kaga Hursiyya a damansa sam basa rabuwa da juna dare da rana sai dai kwanciyar bacci, kai wani lokaci ma akan cinyar sarki Dujalu Hursiyya ke bacci yana shafa gashin knta gami da raira mata wakoki masu dadin sauraro ko kuma yana bata 'abarai masu dadi da debe kewa, ko kadan Hursiyya bata da sadaukantaka kuma sarki Dujalu bai bata sihirin tsafin sa ba ko guda daya, wani babban abin mamaki a tare da ita shine gabadaya halayenta da ra'ayainta ya sha banban dana dan uwanta sarki Dujalu domin bata son zalunci sannan tana da yawon tausayi. A fagen kyautavkuwa tamkar indararo dan ko yaushe hannunta a bude ya ke, bisa wannan halayya tata ne yasa ta samu daukaka da farin jini a wajen talakawan kasar, 132 TASKARNOVELS.COM.NG har addu'a suke a boye suna fatan Sarki Dujalu ya mutu ta haye kan karagarsa saboda sun san cewa zasu samu yancin kansu. A rayuwar Hursiyya babu abinda ta fi so sama sauraron dadadan labarai, jarumtaka da kuma na abubuwan al'ajabi. Bisa halayen Hursiyya na jin kai da tausayi ne yasa sarki Dujalu ya tsani yin tafiya tare da ita, domin ita ce kadai mahalukiyar da take take masa burki wajen tafiyar da zalunci a harkokin mulkinsa. Kai sau tari ma ko zaman fada baya son yi tare da ita saboda tana yawan katse masa hanzari, kasancewar baya son ganin bacin ransa duk alfarmar data nema baya fasa yi mata, sau tari idan sarki Dujalu ya fusata saboda irin katse masa hanzari da take yi, ko yayi yunkurin dukanta sai ya kasa saboda alkawari daya daukar wa mahaifiyarsu kafin ta mutu, alkawarin kuwa shine ya rike mata Hursiyya bisa amana, kuma komai ta yi bazai hukunta ta ba, sannan zai kula da lafiyarta fiye da yadda zai kula da tasa lafiyar. A duk sa'adda Dujalu ya tuno da wannan alkawari sai ya cizi yatsa kwallar takaici ta zubo masa. A ranar da su sarki Dujalu suka shafe kwanaki goma sha takwas suna tafiya ne izuwa tekun 133 TASKARNOVELS.COM.NG bahar Suffiyya, sai suka yada xango a cikin wani kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, Kasancewar yana dauke da koramai, bishiyoyi da kuma kananun dabbobin daji masu saukin farauta gami da kyawawan tsuntsaye, duk irin masifar dake cikin daji da zarar rundunar su sarki Dujalu ta ratso cikin daji sai masifar ta nemi mabuya saboda taga sa gudu maganin ki gudu. Bayan an kafa tantuna a cikin wannan daji mai ni'ima an ci abinci an huta sai Hursiyya taga sarki Dujalu ya kwanta yayi shiru ya shiga zurfin tunani, al'amari daya sosa Zuciyarta kenan ta dube shi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin wannan tunanin naka haka mai zurfi, shin kana wasi-wasi ne akan samun nasarar mu ne akan wannan yaki da muka fito ko kuma kana tunanin yadda zuwa nan gaba zaka mulki duniya ne? Yayin da sarki Dujalu yaji wadannan tambayoyi daga bakin yar uwarsa Hursiyya ai yayi murmushi sannan ya sake gyara kwanciyarsa a saman lallausar shinfidarsa irin tasu ta sarakai, ya dubi Hursiyya cikin natsuwa yace da ita ya ke yar uwata kiyi sani cewa duk abinda ika fada ba shi nake tunani ba, ina naxari ne akan yadda 134 TASKARNOVELS.COM.NG soyayya takai Mazan Jiya zuwa ga halaka, har suka rasa komai na duniya, bisa wannan dalili ne nayi alƙawarin cewa bazan taba yarda naso mace fiye da kima ba, domin ita soyayya siradin mutuwa ce, duk wanda ya taka siradin ba makawa sau ya hallaka, haka nan kaidin mace yafi tsinin allura tsini kuma yafi kaifin zabira kaifi, komai jarumtakar mutum kuma komai karfin mulkinsa da karfin arzikinsa mace na iya maida shi rago, fakiri kuma bawa kamar yadda ta faru ga Mazan Jiya irin su Sadauki Hantaru. Koda jin wannan batu sai Hursiyya ta gyara zama sannan ta ce ya kai dan uwana na rokeka bisa darajar mahaifiyarmu ka bani labarin Mazan Jiya da yadda aka yi soyayya ta jefa su ga halaka. Dujalu ya gyada kai tare d cewa ai kin tambayeni labari mai tsawo, wanda in muka farashi ban san ranar gamawa ba, sai dai yana dauke da darasi mai yawa a cikinsa domin zaki samu ilimin zaman duniya, za kuma kiji yadda ake yaudara ta rashin mutunci gami da mummunan cin amana, sannan kuma zaki ji abin tausayi wanda nasan dole ne ki zubar da hawaye, ke idan kika ji wannan labari kin daina 135 TASKARNOVELS.COM.NG yarda da kowa a duniya koda kuwa iyayen da suka haifeki ne. Hursiyya ta sake gyara zama ta ce dan darajar tsafinka da darajar mulkinka ka gaggauta far banu wannan kasaitaccen labarin, ina mai tabbatar maka da cewa ko ina mai tabbatar maka da cewa koda zamu kwana kana jawabi bazan gaji ba, kuma bazan ji bacci ba. Sa'adda da sarki Dujalu yaji haka sai ya bushe da dariya sannan ya ce to shikenan bari na jarabaki na gani idan har zaki iya jurewa, Dujalu yayi gyaran murya sannan ya fara bada labarin da cewa: Kimanin shekara tamanin da suka shude, anyi wani adalin sarki mai suna Kusaidu a birnin Kisra, Sarki Kusaidu ya mallaki dukiya mai tsananin yawa, sannan yana da tarin mayaka Hakazalika akwai manya manyan birane a karkashinsa kimanin guda 40, sarkin Kusaidu nada matar aure guda daya jal wadda suka yi auren saurayi da budurwa ana kiranta Bazira, har bayan shekaru oma da aurensu amman nasu taba samun haihuwa ba, ko kadan wannan matsala bata damu Bazira ba. Amman shi sarki 136 TASKARNOVELS.COM.NG Kusaidu duk sa'adda ya kalli yawan dukiyarsa d kuma karfin mulkinsa ya kuma tuna cewa bashi da magaji sai yayi ta kuka, babu irin neman maganin da sarki Kusaidu baiyi ba amman abu ya gagara, domin saida ya ziyarci ko wanne bangare na duniya dan ganawa da manyan bokaye amman abu ya cutura. Lokacin da Fazira taga hankalin sarki ya ki kwanciya bisa ga matsalar rashin haihuwa, sai ta kadaita da shi ta ce ya kai mijina ka yi sani cewa a duniya bani da farin ciki sai naka, kuma bakin cikinka nawa ne, ni a tawa shawarar tunda dai ni ban haihu da kai ba me zai hana ka kara aure, ko a dace a samu biyan bukata? Koda jin wannan batu sai Sarki Kusaidu ya cika da tsananin mamaki ya ce da ita Kaicon ki ya ke mata ta, tun kafin muyi aure kika kafa mani dokar cewa daga kanki bazan kara ba, kuma na amince da haka ko kin manta ne? Da jin haka sai hawaye ya zubo wa Fazira ta ce ai wata larurar tana kawar da wata, nidai a halin yanzu na janye wannan sharadin in har soyayyata da taka ka tabbata gaskiya ce to ka yi aiki d wannan shawara tawa. 137 TASKARNOVELS.COM.NG Yayin da Sarki Kusaidu ya ji hkaa sai yayi shiru yana tunani ba tare da yace da ita komai ba har izuwa lokaci mai tsawo, daga can kum sia ya dago kai ya dubi Fazira ya ce ki dan bani kwanaki uku zan yi shawara tukunna. Koda jin haka sai Fazira ta cika da farin ciki kuma ta rungume sarki Kusaidu tare da sumbatar goshinsa kna daga bisani ta fice daga cikin turakar tana tsalle gami da murna, ba kaomai ne yasa Fazira farin ciki ba, sai sanin cewa sarki Kusaidu bashi da wani abokin shawara wanda ya wuce bokansa mai suna Boka Ardusa Bn Zabbar. Fiye da shekaru talatin sarki Kusaidu ake harka da boka Ardusa kuma ya yard da shi dari bisa dari, babu wani sirri nasa wanda bai sni ba. Sai dai abin bakin ciki da takaici shine duk tsawon wadannna shekaru boka Ardusa na cin amanar sarki Kusaidu ba tare da ya sani ba. Domin Ardusa ya mayar da Fazira matarsa ta sirri, wannan cin amana ya samo asaline tun daga lokacin Fazira ta so ta auri Sarki Kusaidu, kasancewarta yar wazirin mahaifinsa amma sai sarki Kusaidu ya nuna ko kadan baya sonta da aure, domin ya dauketa kamar kanwarsa ta jini, dalili kuwa shine a gidan su Fazira sarki Kusaidu yayi wasan kasa 138 TASKARNOVELS.COM.NG saboda akwai yayan Fazira sa'ansa ne, kuma abokinsa wanda suka shaku ainun har ya zamana cewa basa rabuwa dare da rana sunansa Asharab. Tun Fazira na karama jininta ya hadu dana Sarki Kusaidu take matukar kaunarsa, lokacin da Fazira ta cika budurwa sai masoyanta suka yi mata ca! Sabida ta kasance kyakkyawar gaske, ita kuwa sai ta tubure ta ce babu wanda take so face yarima Kusaidu. A wannan lokaci mahaifin sarki Kusaidu ne yake mulkin birnin Kisra, kwatsam! Sai aka wayi gari Asharab ya kamu da rashin lafiya har ta kaishi ga kwanciya, al'amarin daya dugunzuma hankalin Yarima kusaidu kenan ya koma gidan su Asharab ana jinyarsa kenan dare da rana ya zamana cewar yayi wa gidan sarki kaura gabadaya, a ranar da Asharab ya kwana tara yana jinya ne sai rai yayi halinsa, bakin ciki a wajen Kusaidu bazai fadu ba, domin sai da ya kwana uku bai ci abinci ba, kuka kuwa dare da rana haka ya dinga yi babu sassauci, nan da nan ya rame ya kuma lalace da kyar aka samu ya dawo daidai ya ci gaba da rayuwa kamar yadda ya saba, tun daga lokacin da Asharab ya rasu sai Kusaidu ya dauke kafarsa daga gidansu Fazira gabadaya ya daina zuwa, hakan ne ya tada 139 TASKARNOVELS.COM.NG hankalin Fazira ta dinga biyoshi har gida tana nuna masa soyayya, shiko ya dinga nuna mata cewa shifa kanwa ya dauketa ba masoyiya ba, har Fazira ta girma ta cika ya mace nan fa ta cigaba da kokarin janye hankalin Yarima Kusaidu amman ya ki amincewa da ita. Sai bayan da mahaifin Kusaidu ya rasune ya gaji sarauta sannan ta soma samun yardarsa albarkacin boka Ardusa. Shidai boka Ardusa hadimin mahaufin sarki Kusaidu ne, ganin haka ne yasa shima Kusaidu ya aminta da shi. A ranar farko da Fazira ta je wajen boka Ardusa da bukatarta ta son auren satki kusaidu, sai ya nuna mata bukatarta mai sauki ce amman fa sai idan ta yarda ta bashi kanta. Sai da Fazira ta shafe wata uku tana nazarin wannan sharadi a karshe dai taga cewa in har bata amince da sharadin boka Ardusa ba, to fa bazata taba samun damar auren sarki Kusaidu ba. Kawai sai ta abince d shi din, a ranar da abin ya faru ne Sarki Kusaidu ya amince da batun aurenta, da mako ya dawo aka daura auren amman duk da cewa Fazira ta auri sarki bata daina zuwa wajen Ardusa ba sun lalatrsu a sirrance, ita kanta Fazira ta yi mamakin yadda ak yi ta cigaba da 140 TASKARNOVELS.COM.NG yarda da boka Ardusa, abinda bata sani ba shine, ya asirceta ne babu yadda za'a yi ya bukaceta ta ki yarda. Haka dai Fazira da Ardusa suka cigaba da cin amanar sarki Kusaidu har tsawon shekaru sirinsu bai taba tonuwa ba. Bayan Fazira taji cewar sarki Kusaidu zai yi shawara sai ta saci jiki ta wuce zuwa gidan boka Ardusa nan ta sanar d shi abinda ya faru da sarki, ta kuma ce lallai ya baiwa sarki shawarar ya kara aure. Boka Ardusa ya kyalkkyale da dare tare da cewa amman ke meye hikimarki akan bashi wannan shawara? Fazira ta dubi boka Ardusa cikin nutsuwa ta ce da shi ka yi sani cewa har abada sarkk ba zai taba haihuwa ba, tunda matsalar rashin haihuwar daga gareshi ta ke, ni kuwa zan iya haihuwa, idan ya auro wata matar ina so kayi aikinka na bokaye kaga ta samu juna biyu, inyaso cikinka da nake dauke da shi a yanzu in na haifeshi sai ya tashi a matsayin dan amaryar sarki, kaga kenan danmu ne zai gaji sarautar, nasan tabbas zaka iya boye nawa cikin har na haihu ba tare da mutane sun sani ba. 141 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da Fazira tazo daidai nan a batunta sai boka Ardusa ayi shiru, ya fada dogon tunani gami da nazari, daga can sai ya bushe da dariya harda buga kafa a kasa yana mai cewa Hakika ku mata ababan tsorone, ta yaya kika iya kulla wannan dogon makircin acikin dakiku kadan? Nikam tunda nazo duniya ban taba ji ko ganin yaudara da makirci irin wannan ba. Fazira ta bushe da dariyar murna tare da cewa ai bakaga komai ba sai nan gaba tukunna sannan ne zaka gane mu mata mune muke sarrafa duniya da duk abinda ke cikinta, muke haddasa zaman lafiya da rashinsa, kai ko yaki idan kaga ya barke ba zato ba tsammani idan ka yi bincike zakaga snadinsa mune. Koda gama fadin haka sai Fazira ta mike da sauri, tayi wa boka Ardusa sallama domin a wannan lokacin yamma ta yi likis, ta tashi tayi tafiyarta, kuma a wannan lokaci an kusa tashi daga fada, tana tsoron kada sarki ya nemeta bata nan. Kamar yadda Fazira ta shirya makircinta haka al'amuran suka kasance, wato sarki Kusaidu ya auro wata kyakkyawar budurwa jinin sarauta 142 TASKARNOVELS.COM.NG mai suna Shamilat acan wata kasa dake makwabtaka da birnin Kisra mai suna Darul Maabur. Wata uku da tarewar amarya Shamilat sai ga ciki ya bayyana, amman abin mamaki shine ko kadan amarya bata ji wani sauyi a jikinta ba, kuma bata yin wata lalura irin ta masu ciki. Sannu a hankali ciki ya rika girma har ya cika wata tara rana daya sai nakuda tazo wa Shamilat, mata suka taru akanta amman saida Shamilat ta kwana ta wuni tana nakudar bata haihuba. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin sarki kenan ya kasa zaune ko tsaye. A lokacin da shamilat ta samu juna biyu irin farin cikin da sarki Kusaidu yayi ya wuce gaba tunani, domin sai da ya kusa zaucewa saboda tsananin farin ciki, ya rika kyautar dukiyarsa dare da rana, kai sai da takai hatta suturar dake jikinsa yana cirewa gami da baiwa barorin dake gidan sarautar, har sai da aka kulleshi a daki kuma aka hanashi fita. Yayin da nakudar amarya Fazira ta ki cinyewa sai ga uwargida Shamilat ta zo dakin haihuwa, da zuwanta sai ta kuri duk matan dake baiwa 143 TASKARNOVELS.COM.NG Shamilat agaji ta ce duk basu san aikinsu ba ma, kawai sai ta kulle kofar dakin ya zama cewa daga ita sai mai nakudar a cikin dakin, nan take ta shafa cikin amarya Shamilat ai kuwa sai hankalinta ya gushe ta suma, Fazira ta shafi nata cikin kawai sai ga tsohon cikinta ya bayyana kuma nan take nakuda ta zo mata, bayan kamar rabin sa'a Fazira ta haifo santalelen yaro kyakkyawan gaske, cikin hanzari ta gyara jikinta sannan ta gyara jaririn ta ajiyeshi daf da amarya, daga nan ta sake shafar cikin anarya a karo na biyu sai ga jinin haihuwa na zubo wa daga jikinta. Jim kadan amarya ta farfaɗo aiko sai ta ji jariri na tsala kuka a kusa da ita. Koda sauran mutanen gida suka jiyo kukan jariri sai suka rugo izuwa dakin haihuwar suna shewa gami da murna, cikin matukar mamaki. Ai kuwa labari na riskar sarki sai kuwa ya fito daga cikin turakarsa tare da fadawa dakin haihuwar ya dauki jaririn ya rungumeshi yana kukan farin ciki. Sai da aka kwana talatin ana bukukuwa da walimar farin ciki a birnin Kisra saboda murnar wannan haihuwa da akayi wa sarki Kusaidu. 144 TASKARNOVELS.COM.NG A kwana a tashi dan da amarya ta haifa mai suna Hantaru ya fara girma ya cikq shekaru biyar, Hantaru ya taso yaro kyakkyawa mai jarumtaka tq ban al'ajabi, domin tun yana da shekaru iyar yake iya daukar abubuwa masu nauyin gaske, idan kuwa yana wasan kokawa a cikin sa'anninsa babu mai iya kada shi. Kai sai da takai cewa yaran da suka girmeshi ma kada su yake yi. Lokacin da Hantaru ya cika shekaru tara sai ya zama cewa yana

Chapter 6 of 13