Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
satar jiki ya shiga daji yin farauta shi kadai b tare da ya dauki makami ba, sai dai aka ya kamo damisa ko bauna ya shigo da ita gari a mace bisa kafadarsa. Nan da nan jarumtakar Hantaru ya bazu a ko ina a nahiyar, har aka dinga zuwa kallonsa ana mamakin sa, wani abin mamaki a tattare da Hantaru shine ko kadan bai damu da harkar sarauta ba, babu yadda sarki Kusaidu bai yi da shi ba akan ya rinka zuwa fada sun zama tare amman sai ya sulale ya tafi farauta. Baya ga farauta abu abinda Hantaru ke so sama da koyon yaki, dan haka sai ya like wa Sarki yakin birnin Kisra ya zamana cewa kullum yana gidansa yana koyon yaki. Aiko a cikin shekaru bakwai Hantaru ya zama gagarumin mayaki har ma yafi sarkin yaki shahara. 145 TASKARNOVELS.COM.NG Tun sa'ar da Fazira da boka Ardusa suka fa cewar gaba daya hankalin Yarima Hantaru baya kan sarauta sai hankalinsu ya dugunzuma suka shiga kokarin asirce zuciyara domin yayi watsi da harkar farauta data koyon yakin nan. Amman sai suka sha ruwan mamaki domin asirin da suke masa yaki yayi tasiri akansa. Ganin haka ne yasa Boka Ardusa ya dukufa akan binciken gano dalilin faruwar hakan, a cikin binciken nasa ne ya gano cewa nonon da Hantaru ya sha na amarya shine yya janyo ashin tasirin tsafi a jikinsa, domin ita amarya Shamilat tana da wata kariya a jikinta wadda mahaifinta ya shayar da ita tun tana jaririya, kuma babu abinda za a iya yi dan lalata wannan kariya. Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya turnuke boka Ardusa, domin ya fahimci cewa har abada Hantaru bai yi sarautar birnin Kisra ba muddin baiyi watsi da harkokin farauta ba ya kama na fada ba. Al'amarin sarki Kusaidu kuwa da amarya Shamilat hankalinsu yafi na kowa dugunzuma bisa ganin yadda dansu yaki damu da komai face harkar farauta da kuma yaki, ko kadan Hantaru bai shaku da sarki ba sai dai 146 TASKARNOVELS.COM.NG mahaifiyarsa Shamilat, kuma yana bata mafi yawa daga lokitansa a gidan abokansa yayan mafarauta na birnin, sai da sarki Kusaidu ya gana da boka Ardusa sau 10 akan wannan matsala, amman ko yaushe sai dai boka Ardusa yace da sarki ai sai dai ayi hakuri amma babu abinda za a iya yi. Boka Ardusa bai fada wa Shamilat dalilin da yasa tsafi baya tasiri a jikin Yarima Hantaru ba, dalili kuwa shine idan tasan da hakan hankalinta zai dugunzuma ta bazama neman taimako a wajen wasu bokayen kuma a haka asirinsa na iya tonuwa har sarki Kusaidu ya gane cin amanar da suke masa. Wata rana amarya Shamilat na zaune tare da sarki Kusaidu suna fira sai ta ce da shi ya kai mijina ka sani cewa tunda ka aureni ka raboni da kasarmu ban taba kaiwa iyayena ziyara ba sai dai su sukawo mani, ina son kayinmani izinin zuwa a wannan karon, nayi kokari nayi shiri na je. Idan da hali ma zan so na tafi da yarima domin yaga dukkanin danginsa na can. Yayin da sarki Kusaidu yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya Ya ce yake mata ta kiyi sani 147 TASKARNOVELS.COM.NG cewa b laifina bane ki kai wannan ziyara, ina tsoron dazuzxukan dake kan wannan hanyar ne kafin a isa birninku, ni kaina sau daya nabi wannan hanyar lokacin da naje neman aurenki. Lokacin da zanje sai da akayi gagarumin shirin yaki na dakaru masu yawan gaske, kuma sai da Boka Ardusa yayi mani rakiya dan tabbatar da tsaro. Yayin da shamilat haka sai ta yi murmushi ta ce ya kai mijina indai dan tsautsayin hanya ne ka kwantar da hankalinka, ina mai tabbatar maka da cewa babu abinda zai samemu, domin tun ina yarinya karama iyayena suka bani tsari na musamman, bama ni ba hatta dana da ya sha nono na ya samu wannan tsari, kaima daka aureni ka samu wannan tsari, indai kana cikin hayyacinka to babu wani mahaluki daya isa ya cutar da kai. Ni nasan cewa baka son rabuwa da yarima daidai da rana daya shiyasa baka son nayi wannan tafiya Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubo wa sarki Kusaidu ya ce Tabbatas kin fadi gaskiya yake mata ta, amman ki sani a halin yanzu babu abinda ke damuna sama da rashin shakuwata da Yarima, ko kadan bai damu da ni ba tamkar 148 TASKARNOVELS.COM.NG ba ni na haifeshi ba, duk shawarar dana bashi baya amfani da ita, har gwara ma ke naga yana matukar kaunarki, kuma baya son yaga bacin ranki. Sa'adda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama Shamilat, ta dafa kafarsa ta ce kada ka damu ya kai mijina nayi maka alƙawari da zarar munje garinmu mun dawo zakaga sauyi a tare da Yarima zai kaunaceka kamar yadda ko wane da yake kaunar ubansa Hakazalika zai shaku da kai, sannan zai ajiye harkokin farauta ya rungumi na sarauta. Da jin haka sai sarki Kusaidu ya dubi Shamilat cikin tsananin mamaki ya ce Ta yaya hakan zata faru? Shamilat ta ce kakana shahararren boka ne wanda babu kamarsa a nahiyarmu, ina mai tabbatar maka da cewa ko Boka Ardusa aka sai dai suyi kunnen doki a karfin sihiri, kai ina da tabbacin kakana yafi Ardusa tarin ilimin tsafi, lallai nasan zai taimakemu ya juyo da hankalin yarima zuwa kan tafarkin da muke so. Yayin da sarki Kusaidu ya ji wannan batu sai ya cika da farin ciki kuma ya amince da batun 149 TASKARNOVELS.COM.NG tafiyar Shamilat. Tun kafin dare yayi Shamilat ta tura aka kira mata Yarima Hantaru tayi masa albishir da tafiyar da zasu yi a gobe ita da shi izuwa can mahaifarta ta darul maabur. Koda jin haka sai Hantaru ya cika da tsananin farin ciki domin a rayuwarsq bashi da wani buri da ya wuce yayi doguwar tafiya wacce zai ratsa ta cikin dazuka masu ababan hadari, kamar yan fashi da muggan dabbobin daji, ba dan komai ba sai don ya jaraba iyakar tsawagaron ku riyarsa da kuma shan wahalarsa, ya kuma ga iyakar karfin damtsensa, tunda ya ke sau daya ya taba halartar yaki a birnin Kisra kuma lokacin da yaje filin yakin ma saura kiris a gama da abokan gaba, a takaice dai Yarima Hantaru yana so yayi doguwar fafatawa da aboka gaba. Saboda tsananin dokin da yarima Hantaru yake saboda tafiyar da zasu yi tun a daren ya kimtsa kayansa sannan ya daura wa dokinsa sirdi sannan ya tanadi kayan yakinsa. Lokacin daya kwanta bacci sai idanunsa suka bushe ya kasa bacci saboda tunanin tafiyar ta gobe. Bisa wannan dalili ne yasa ya tafi dakin mahaifiyarsa Shamilat, da shigarsa cikin turakar sai ya isketa a zaune tayibshiru tana tunani sai faman murmushi take yi kamar wacce take magana da 150 TASKARNOVELS.COM.NG wani. Har Hantaru ya zauna kusa da ita amman bata san ya shigo ba, sai da ya dafa hannunta sannan tayi firgigit kamar wacce ta farka daga bacci, Hantaru ya dubi Shamilat cikin mamaki ya ce ya ke ummina tunanin me kike yi ne haka wanda har ya hanaki ki kwanta kiyi bacci. Sa'adda Shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta ce Ya kai dana kayi sani cewa tsananin murna ce ta hanani na kwanta nayi bacci, saboda ina murnar cewa zanje naga kakana wanda ya haifi ubana Boka Sulbaini Bn Ukash. Kayi sani cewa a hannun Sulbaini na girma har nayi wayo, daga baya da za a yi mani aure aka rabani da shi, a ranar da za'a rabamu da shi munsha kuka tamkar ranmu zai fita saboda sabo da juna, rabona da shi yau shekara 16 kenan, nasan cewa yanzu ya kara tsufa ainun babban burina shine na sake saduwa da shi kafin rai yayi halinsa. Koda Shamilat ta zo nan a zanjenta sai hawaye ya zubo mata, take Hantaru yaji tausayinta ya kamashi har shima kwalla ta zubo masa, Hantaru ya rungume Shamilat gana mai cewa ya ke ummina ki kwantar da hankalinki domin naji 151 TASKARNOVELS.COM.NG a jikina cewar wannan kaka naki na nan a raye kuma tabbas zamu je mu riskeshi. Tsawon yan dakiku duk su biyu suka yi shiru babu wabda ya ce kala, daga can sai yarima ya janye jikinsa daga jikin nata suka dubi juna sannan ya ce Ya ke ummina shin ba kya bani labarin yadda rayuwar mutanen birninku take ba? Lokacin da shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta gyara zamanta ta ce Mafi akasarin mutanen birninmu mafarauta ne da kuma makera, mahaifina shine sarkin makera kuma shine galadiman sarkinmu ana kiransa da suna Shuraim Bn Alkas. Tsakanin zuri'armu ta makera data mafarauta babu kyakkyawar fahimta ko zumunci mai karfi, kuma babu auratayya mai yawa. Babu abinda yafi burgeni a garinmu face wata al'ada da aka saba yi duk karshen shekara, al'adarvita ce za'a zabo budurwar data fi dukkanin yan matan garin kyau a sa gasar neman aurenta a tsakanin jaruman samari, masu ji da sadaukantaka. Yanayin gasar shine za a saki barewa a daji a kasa tsere duk saurayin da yafi kowa gudu ya kamonwannan barewa to shi zai auri wannan 152 TASKARNOVELS.COM.NG kyakkyawar budurwa. A lokacin da ake tseren gudun an yarda samarin su dinga bangaje juna duk wanda ya fadi kasa to ya fita daga cikin gasr kenan. Gabadaya mutanen garin banda al'karan gasar suna hawa kna wani dogon tsauni ne su tsitsaya dan su hango abinda ke faruwa, su kuwa alkalan gasar suna bin bayan mahayan ne, lokacin da shamilat ta zo nan a zancenta sai Yarima Hantaru yaji soyayyar darul maabur ta lullubeshi domin ya fahimci cewa can ne ya dace da yanayin rayuwarsa, dan haka sai ya sake cika da tsananin farin ciki. Yadda yarima yaga rana haka yaga dare, wato har gari ya waye bai runtsu ba, washegari da sassafe ya tashi tunma kafin alfijir ya keto yayi wanka ya kuma sanya tufafinsa, yana gama kimtsawa kuyanga ta kawo masa abincin kalaci, amman yana yin lokamar farko sai yaji ya koshi dan haka sai ya mike ya bar abincin ya tafi dakin Shamilat, yana zuwa ya iske ta, tuni itama ta gama shiryawa shi take jira kawai. Nan take kuyangi suka fito da kayayyakin Shamilat har da guzurin da zasu tafi da shi da 153 TASKARNOVELS.COM.NG kuma tsaraba, duk wannan abu da ke faruwa Zarifa bata sani ba sai a lokacin da sarki ya fito daga cikin turakarsa ya riski Shamilat da hantaru tsaye cikin turakarsa, kawai sai ta riske sarki Kusaidu yana bankwana da shamilat har yana rungume yarima Hantaru yana zubar da hawaye. A gigice zarifa ta taho da gudu ta karaso garesu ta kama hannu Yarima Hantaru ta rike tana mai cewa ya kai dana ina zaku tafi haka amman baku fada mani ba? Yarima ya dubi Zarifa a wulakance ya ce zamu tafi garin kakannina ni da mahaifiyata. Koda jin haka sai Zarifa ta ji zuciyarta ta buga da karfin gaske, har bata san sa'adda ta kama surutai ba tana cewa ai bai kamata ku tafi yanzu ba, zai fi kau ku bari ayi maku shiri na musamman. Yarima Hantaru yq ce ai babu abinda zai hana mu wannan tafiya a yau, sai dai fitar ruhi daga cikin gangar jiki. Gama fadin hakan keda wuya sai Hantaru ya kama hannun Shamilat ya ja ta suka tafi, barori ba biye da su da kaya niki-niki. 154 TASKARNOVELS.COM.NG Koda ganin haka sai Zarifa ta sulale tq fice daga cikin gidan sarautar ba tare da kowa ya sani ba. Cikin hanzari Zarifa ta haye bisa doki ta ruga izuwa gidan Boka Ardusa domin ta sanar da shi halin da ake ciki dan yasan matakin da zai dauka kada asirinsu ya tonu. Boka Ardusa na zaune shi kadai a cikin harabar gidansa ya zuba wasu alkaraman sihiri a gabansa yana nazari sai kawai yaga Zarifa ta shigo da gudu kuma a gigice har tana tuntube zata fadi kasa. Koda ta iso gabansa sai ta zube kasa tana mai faman haki, kuma ta bude baki zata yi magana sai kawai Boka Ardusa ya daga mata hannu yana mai yi mata nuni ta yi shiru. Bisa dole zarifa tayi shiru bata ce komai ba, kuma ta kura sama idanu har sai da ya gama yan tsubbace-tsubbacensa. Boka Ardusa ya juyo ya dubi Zarifa ya ce da ita ai nasan abinda ke tafe da ke, kuma tun a jiya nasan da batun tafiyar amarya Shamilat da danmu Yarima. Ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa domin babu abinda zai faru. Ina mai tabbatar maki da cewa muddin ina numfashi a doron kasa har abada asirinmu bazai tonu ba. Ki saki ranki kije kita bacci harda munshari, da sannu burinmu 155 TASKARNOVELS.COM.NG zai cika danmu ya zama sarkin birnin darul maabur. Koda jin wannan batu sai Zarifa ta kyalkkyale da dariya, can kuma sai ta hade fuska ta yi shiru kamar tana nazari. Boka Ardusa ya dubeta cikin damuwa ya ce tunanin me kuma kike yi, alhalin na fada maki cewar babu abinda zai faru? Zarifa ta yi ajiyar zuciya ta ce ni abinda nake tsoro shine kada yarima yayi zamansa acan birnin darul mahabur yaki dawowa nan gida, abu na biyu ni fa yanzu na shiga matsananciyar damuwa saboda dana yarima bai san cewa nice mahaifiyarsa ta gaske ba, shin kana tsammanin cewa nan gaba zai karbeni ne a matsayin uwa ? Boka Ardusa ya ce kwarai kuwa, kuma sai ya kaunace mu fiye da kowa a rayuwarsa nayi maki wannan alkawari, kedai ki ci gaba da hakuri al'amarine na lokaci, idan muka ce zamu yi wa lamarin gaggawa to fa lallai burinmu ba zai cika ba. 156 TASKARNOVELS.COM.NG Haka dai Boka Ardusa yayita lallamin Zarifa har hankalinta ya kwanta, suka aikata cin amanar da suka saba sannan ta tafi. Mazan Jiya Part 15 #Cigaba A lokacin da shumilat da yarima hantaru suka fita kofar gari sai suka kama hanya batareda fargabar komaiba su kwana nan su tashi chan saida suka bar birnin darul maabur da shiga su daji na fark6 wanda ake kira sujud sai shamilat taja linzamin dokinta ta tsaya shima sadauki hantaru saiya tsaida dokin nashin, shamilat ta kasa kunnenta bataji motsin komai ba sai tayiwa yarima hantaru magana cikin rada tace akwai muggan yan fashi a wannan daji kuma sun iya nada muggan tarkuna sai mun kula da kyau koda jin wannan magana sai hantaru yayi mata nuni data sauka daga kan dokinta batareda wata gardama b shamilat ta sauko 157 TASKARNOVELS.COM.NG shima saiya sauko daga kan nashi. kawai sai yasaki dokin nasa yayi gaba koda dokin nasa yayi tafiyar kamar taku talatin saiya zurma cikin wani wawakeken rami mai zurfin gaske saiga wadansu samudawan yan fashi suna mai rugowa daga cikin maboya suna zuwa bakin ramin suna tsayawa adadin yan fashin ya haura 300 dukkaninsu sun kasance majiya karfi kuma suna daukeda muggao makaman yaki sun shafe fuskokinsu da bakin shuni bayan yan fashin sun gama yiwa wawakeken ramin kawanya rai suka fuskanci cewa yaufa karensu bai kama zomo ba domin doki ne kawai ya fada cikin ramin babu mahayi akan dokin babu dukia cikin tsananin fushi shugaban yan fashi ya dubi sauran dakarun ya daka musu tsawa yace tsayuwar me kuke maza ku baxama neman mai wannan dokin kafin yagama rufe bakinshi sun tarwatse sun rarrabu acikin dajin, ashe dvk abin da akeyi hantaru da shamilat na labe acikin wani duhuwa suna hangowa koda hantaru yaga yan fashin nan sun rarrabu suna farautarsu sai ya cewa shamilat ta dada buya acikin wannan duhuwa shi kuma sai yakama wata doguwar bishia yakama hawa samanta hantaru yayi lamo acikin ganyen bishiyar duk dan fashin dayaxo 158 TASKARNOVELS.COM.NG inda shamilat ke boye sai hantaru ya diro ta bayansa ya masa mangara daya ya fadi sumamme sannan ya kwashe makanshi yayi sama dasu a haka saida ya sumarda sama da yan fashi 50 koda yaga zasu gano inda shamilat ke boye saiya sauko kasa ya dauke ta daga wajen ya ruga zuwa inda wawakeken ramin nan yake wanda dokinsa ya fada ciki!! wohohoh nan take hantaru ya shiga cikin ramin nan ya dauko dokinshi kafin hantaru ya juya ya daura shamilat akan dokinsa sai yaga yan fashin sun masu kawanya kimanin su 300 da doriya tuni shugaban yan fashin dora wata wuka mai tsananin kaifi akan wuyan shumilat cikin firgici hantaru ya dubeshi yana mai daka mishi tsawa yace ku kwashi duk abinda kuke so daga dukiya amma inamai gargadinku da kadaku kuskura ku tuba lafiyar mahaifiyata koda jin haka sai shugaban yan fashin yace aiko sai mun dauki fansar yan uwanmu daka sumar ka kwashe musu makamai yanxu xan kashe mahaifiyartaka sannan kaima nayi maka kisan gilla na kwashe dukiyar taku kafin hantaru ya budi baki yace wani abu tuni shugaban yan fashin nan ya dadara wukar nashin akan wuyan shumilat bisa mamaki sai yaji kamar akan dutse ya dadara 159 TASKARNOVELS.COM.NG cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikin shi Cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikinshi ya cillata ta cake a goshin shugaban yan fashin ya sulale kasa matacce koda ganin haka sai sauran yan fashin suka afkawa hantaru suna masu kai mishi sara da suka ta koina kaicoh! inda yan fashin nan sun san abinda zai biyo baya da dukkaninsu sun nemi gudu tsira. koda sukayiwa hantaru kawanya kawai sai yayi wuf yakama kafar daya acikinsu ya maidashi makaminshi da kuma garkuwanshi ya dinga tare sara dashi kuma yana maida martani dashh nan danan suka daddatsa dan uwan nasu duk wanda hantaru ya makawa dan uwan nasu sai kaga ya fadi sumamme koh matacce nan fah akarasa mutum daya daga cikinsu wanda zai iya koda lakutar jikin hantaru saboda tsananin zafin namanshi da karfin bugunshi kafin cikar sa'a dari biu duk ya bazar dasu akasa mattatu a sannane ne hantaru ya dubi shumilat cikin matukar mamaki yace yake ummina yaya akayi wuka ta kasa yanka ki? shamilat tayi murmushi tace shin kamanta cewa ubana sarkin makerane babu wani karfe dazai iya huda jikina koda kaima kanka karfe bazai 160 TASKARNOVELS.COM.NG cinkaba saboda kasha a nono shin kataba jarba karfe acikin ka? hantaru yace Aah amma barina jarraba yanxu nagani nan take hantaru ya zare takobinsa ya yanki dantsen hannunsa aiko sai yaga ko kortsanuwa bai yiba kawai sai ya cika da tsananin mamaki. batareda bata lokaci ba suka hau dawakansu suka cigaba da tafiya suna masu kada dawakan gaba suka bar yan fashin a zube a kasa matattu ru hantaru suka cigaba da tafia har tsawon kwana sha daya basu sake haduwa da wani mugun abuba da tsakar ranar kwana na shadayan ne suka shigo cikin wani bakin daji mai ban tsoro domin babu komai acikin shi tsaunuka masu tsawo da kwazazzabai da shigarsu cikin dajin hantaru ya aiyana a ranshi lallai baza'a rasa muggan halittu acikin shiba koda gama aina haka sai ya zare takobinshi yaceda shamilat ta dawo nashi dokin shamilat batayi wani gardama ba tayi yadda ya umarceta yin hakan keda wuya sai sukaga wadansu manyan gwaggon biri sunata fitowa daga cikin kogunan dutsen nan suka cigaba da bullowaa kamar bazasu kare ba koda ganin gwaggunan birin sai hankalin shumila da hantaru ya dugunxuma domin basu taba ganin birrai masu 161 TASKARNOVELS.COM.NG girma da muniba kuma koba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi hantaru yasake kankame takobinshi dakyau yana ainawa arranshi cewa yau komin rintsi da tsanani baxai bari a taba lfy mahaifiyarshi ba adaidai wannan lokacin ne shamilat taji nadama tazo mata abisa wannan tafia zuwa birnin iyayenta nan take ta tunoda zancenda mijinta a lokacin da yake fadamata hadarin dayake kan wannan hanya. sannu a hankali birurrukannan suka cigabada matsowa suna yiwa dawakansu hantaru kawanya sukansu dawakan saida suka kama ruri da haniniya bisa gani birurrukan,shiko hantaru koh gizo baiyiba yaci gaba da rike linzamin dokinshi da hannu daya dayan hannun kuma na rikeda takobi wannan birran dai sunfi shekara arba'in acikin wannan dajin idan maza suka kama take suke kashe su inko mata ne sai su tafi dasu cikin gidajensu suna lalata dasu koda birurrukan suka tasan ma hantaru sai shima yayi kansu yana mai saransu yana bangajesu da kafa suna zubewa kasa bisa mamaki sai hantaru yaga ai takobi bata tasiri acikinsu duk sa'adda ya sara sai yaji kamar dutse ya sara nan fah birran suka fara kokarin su hallakashi amma sai yazamo musu alakakai yayinda hantaru ya gano 162 TASKARNOVELS.COM.NG nufin birran nan kuma yasan takobinsa batada wani amfani sai zuciyarshi ta harxuka yayi jifa da takobinsa cikin zafin nama ya goya shamilat a bayansa sannan ya diro kan dokin aka cigabada gumurzu mai ban alajabi domin duk inda hantaru ya kai duka saidai kaga birurrukan sun zube a kasa duk yawan nasu sai yaxamo na banza domin sun kasa koda lagutar jikinshi da faratunsu babban abinda ya tayarwa hantaru hankali dazarar ya zubar da birurrukan a kasa sai sumike zunbur su sake afka mishi runa masu kai mishi cizo da yakushi suko birurrakan sunyi matukar mamaki domin basu taba haduwa da shaidanin mutum irin hantaru ba, haka dai aka cigabada wannan fafatawa har tsawon sa'a daya shibai nakasa suba kuma bai kashe koda daya daga cikinsu ba ka suma basu hallakashiba tuni shumilat ta acikada tsananin mamakin bisa ganin jarumtakar hantaru domin bata taba tsammanin yakai hakaba babu abinda ya bata mamaki kamar yadda birurrukan nan suka kasa kai shi kasa wani lokacin har dandaxo sukeyi waje guda su tafo da gudu domin su hallakashi amma sai kaga ya tokare su ya watsasu. lokacin da hantaru yaga cewa lallai idan kara sa'a daya ana wannan gumurxun zasu iya samun nasara 163 TASKARNOVELS.COM.NG akanshi saiya chanza salon fadan kawai sai ya dinga kama hannayensu da kafafunsu yana cisgewa saidai kaga jini na tsartuwa na feshi nan birurrukan suka dinga kururuwa suna zubewa kasa a mace.. wohohoho!! maza maganin maza hakika birurrukan nan sunga bala'i domin kafin su ankara hantaru ya kashe samada guda duba biyar daga cikinsu saida takai birurrukan sun fara jada baya kai da sukaga abin yafi kafinsu rugawa sukayi cikin kogunan koda ganin haka hantaru ya yunkura da nufin yabisu cikin kogon dutsen sai shamilat ta gargadeshi kada ya bisu cikin kogon dutsen nan domin kowa a gidashi sarki ne, ka kyalesu kawau mu cigaba da tafiyarmu ai nasan ba zasu sake biyomu ba domin sun tsaga basuga jini ba. Hantaru yayinkwafa sannan ya ce kash! Ummina naso ki kyaleni na cigaba da yaki da burirrikan nan har sai naga babu dayansu da ya rage mai numfashi. Shamilat ta yi murmushi ta ce na gaisheka dana, hakika ina farin ciki da samunka domin ayau ne nasan cewa ina da namijin duniya kuma jarumin jarumai. 164 TASKARNOVELS.COM.NG Hantaru ya ce ai dukkan godiya ta tabbata a gareki da kika zama uwata na sha nononki har ya zama garkuwa a gareni. Hakika dole ne nayi alfahari da zuri'arki domin ina ganin cewa sadaukarnan tawa a wajensu na gadota. Shamilat ta sake yin murmushi ta ce tabbas mahaifina gawurtaccen jarumi ne na gaske mai tarwatsa maza a filin daga ina ganin cewa shi ka gado kuma gashi har ma ka fishi yarinta. ********************** Mazan Jiya Part 16 Labarin Sadauki hantaru mai takobin #saiful lujara na mazan jiya #Cigaba 165 TASKARNOVELS.COM.NG Kafin shumilat ta rufe bakinta sai sukaji sautin taku daga cikin kogon dutseo nan tamkar sawun giwa koda hantaru da shamilat suka waiga nan take hantaru yayi arba da abinda yarazanashi yayi matukar firgitasu ba wani suka ganiba sai wani katoton gwaggon biri wanda girmarsa ya ninka na wadannan birurru kan sau biyar katon goggon birin nan ya dunfafo inda su hantaru ya yana tafe yana nishi da gurnani takun tafiyar tasa na haddasa karamar girgixar kasa koda ganin haka sai shamilat ta kara rudewa tana mai jan hantaru tana cewa zomu gudu yakai dana tabbas bazaka da wannan birin ba hantaru ya cije ya tsaya cak sannan ya dubi shamilat yace ai faduwar gaba asaran namiji ce kede kijada baya ki zuba ido kiga abinda zai faru a rude shamilat ta juya ta labe a bayan wata bishia tana leke sukuwa birurrukan sai suka haukan duwatsu suka zuba idanu domin suga abinda zai faru tsakanin hantaru da shugabansu asannan ne hantaru ya gane cewa wannan narkeken birin shine shugabansu kuma yaransane sukaje suka kirawo shi a fusace shugaba birurrukan yayi kan hantaru lokacin da sauran yaran nashi suka fara wani irin gurnani runa mai mishi kirari kawai sai hantaru ya dunkule yan yatsunsa ya 166 TASKARNOVELS.COM.NG gyara tsayuwa, cikin shammaci birin ya gabzawa hantaru naushi a fuskanshi saboda karfin daushin saida hantaru yayi sama ya fado kasa kuma jini yayi tartsuwa daga bakinshi har hakorinshi guda ya fadi akasa take hantaru ya tashi a fusace zuciyarshi ta fara tafarfasa koda ganin haka sai sauran birurrukan ruka fara ihu suna shewa saboda nasarar da shugabansu yasamu akan hantaru alamarin daya kara fusata hantaru kenan baxato ba tsammani hantaru ya daka tsalle ya gabza mishi naushi a kasan cibiya kawai sai akaga birin ya kame kamar an zare duka lakar jikinsa nan take kuwa ya sulale kasa ko shurawa bai sakeyi ba hantaru ya daga kai sama ya dubi birurrukan na ya kwarara uban ihu nan take suka tarwatse suna masu fantamawa cikin daji batareda sanin inda xasu tsayaba, Kaicon inbada wuyya ta kai wuya ya za ayi wadannan muggan burirrikan har su guje wa biladama guda daya jal. Bayan birurrukan sun gudu sai shamilat ta fito daga bayan bishiyarda take ta rugo da gudu cikin farin ciki tana mai cewa hakika yau kayi bajintar da bayantaba mancewa da itaba suka rungume juna daga can sai shamilat da dauki 167 TASKARNOVELS.COM.NG takobin Hantaru ta sare kan wannan birin ta cire a cikin wani icce. Koda ganin haka sai Hantaru ya dubi mahaifiyar ta shi ya ce da ita ya ke ummina me kuma zakiyi da kan wannan birin? Shamilat tayi murmushi ta cw da shi ai d shi zan tafi, kuma zanyita ajiyar kokon kan wannan birin har iya tsawon rayuwata, domin abun tarihi ne wanda har abada bai kamata a manta da shi ba, ya dana kayi sani cewa kayi gagarumar bajinta wajen kashe wannan buri. Nan de hantaru da shamilat suka yada zango suka kunna wuta suna jin dumi saboda sanyin dake kadawa. kashegari da safe suka kada rakumansu sukayi gaba su hantaru suka cigaba da ratsa dazuzzuka iri iri a ranar kwana na goma sha biyar ne suka shigo cikin daji mai girman gaske abinda ya fara daukan hankalin hantaru shine gaba daya harabar dajin komai tsab yake babu kazanta a ko ina, sannan ga kuma wata irin iska mai ni'imah na kadawa koda ganin wannan wuri sai murna ta kama hantaru ya yunkura zai sauko daga kan dokinsa ba caraf! sai shumailat ta rike hannunsa tace 168 TASKARNOVELS.COM.NG kadaka sauka yakai dana wannan daji baza'a rasa aljanu acikin saba hantaru yayi murmushi yace yake ummina inaso kisani cewa wahala ga da namiji ibada ce, haka kuma tsoro tsanani ne na hallaka da rashi. Koda gama fadan haka sai hantaru ya sauko daga dokinsa ya xare takobinsa ya rike linzamin dokin ita kuwa shamilat saita dinga binsa abaya a hankali tana wauge-wauge kwatsam sai hantaru yaga wani katon lambu a gabansa wanda ke cike da yayan itatuwa iri-iri kamar su tuffa, inibi, fasa dabur dadai sauransu, bazato ba tsammani sai yaga wata yarinya budurwa kwance akan wata shimfida tana cin tufa fuskan a cike da annuri a iya rayuwar hantaru bai taba ganin mace mai kyan taba amma abin takaici daya dubi kafarta sai yaga kofato koda kyakyawar ta kalli hantaru rai ya kauda kai yaje ya sai ya kaufa fuska yaje ya tsinki tufa guda daya ya fara ci, alamarin dayabawa budurwar mamaki kenan ta bishi da kallo cikin takaici ta kuma shumailat rai taki shiga cikin lambun alokacin da hantaru yagama cinye tafar kawai sai yaji an rike hannunsa bawata bace face wannar budurwar daya wuce kwance,budurwar ta dubeshi cikin fushi tace haba

Chapter 7 of 13