Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi,an saisaye eyar kan ambar tsakiyar kai da mirWe-mirWen gashi sai kace kan zakara,ga kayan da ya saka wanda zakayi tunanin cikakken inyamuri ne ba Bahaushe ba kuma Wan musulmi,wannan duk bashi ne matsalar ba kuma bashi ne abin mamakin ba yanayin maganarsa duk ta canja takoma kamar na Wan daudu.

Cike da barikanci Musa ya fara magana kamar mace"Hi Maman Jummalo ar uwa, ya jin nice,kwana da yawa,ashe zamu aurar da yara"

Sai wani lanwasa da karairaya yake kamar wata mace,macan ma karuwa.Haba gida ba sai ya kaure da salati da sallalami ba,ma gulman layi an samu sabon rahoto.Matan gida na cikin wannan yanayi sai ga Umma Kande ta shigo gidan,dama bata nan ya dawo ba,taje siyayyar wasu kayan biki a kasuwa,saukanta kenan daga keke napep aka ce mata Musa ya zama Wan daudu sai zance yakeyi a gidan da matan aure,bata Sata lokaci ba ta shiga gidan cike da tashin hankali.

"Musa!,Musa!!,Musa!!!,kai ne haka!!!"

Waro idanu tayi waje tare da dafa irjinta hannu bibbiyu sai kuma ta fashe da kuka har da shasshea don tayi mamakin a ce wai yau Wan da ta haifa da cikinta ya zama Wan daudu,to ya hakan ta faru ne,mai ya maida shi haka,tana kukan ne ya zo kusa da ita tare da cewa

" Oh My God,haba mommy na,why cry naaaa,keda zaki ji daWin ganin an matanki amma sai kuka,no no no,stop mommy na"

"an matana fa kace Musa,da hankalinka kuwa,kai macace da kake kiran kanka da an mata,mai ya shiga wawalwarka Musa,wayyo ni Saratu jikar sarkin ruwa,naga ta kaina!!! "

"To miye a ciki don na zama mace,ai normal ne wallahi chass Mommy na,kinga nazo miki da tsaraba harda kayan mata ma wallahi sai kiba su Zaliha su gyara jikinsu kinsa ina harka da kayan mata kuma ina saidasu,naga annena zasuyi aure shiyasa nace bara na kawo musu suma"

Ai ba shiri da tsagaita kukanta,jin Wanta na wa'inan kalamai,yau mai ke faruwa da ita ne.

"Musa anya wawalwarka a daidai take aiki kuwa,kodai maiyana suka ma asiri ne,na shiga uku ni Saratu,wayyo ni wayyo ni shikenan sun mai damin Wa Wan daudu!!!

Kowa a gidan na mujiya ya zuba musu,jin wannan sabon salo sharri wai asiri a aka ma Musa,habawa tuni Umma Kande ta katse ma kowa tunani da kururuwanta wanda ya karaWe gidan gaba Waya,har wasu an waje sun fara shigowa cikin gidan don kashe kwarkwan idanunsu saboda har an fara kai rahoton Musa ya zama Wan daudu.

" Wallahi bazata saSuba,wannan aikin asiri ne! Wallahi bazan yarda ba,asiri akama yarona don anga arzii ya fara samun mu,to wallahi an bain ciki sai dai su mutu,wallahi bazan yarda ba,sai na Wau mataki wallahi kawai a maida min Wa mace, wayyo ni Saratu,wayyo ni sarere jikan sarkin ruwa,yau naga ta kaina,yiiiiiiiiii,yiiiiii,wayyo niiiiiiii!!!"

Da sauri Maman Jummalo tayi cikin Waki da ita saboda ta fara sakin layi,kar an layi suji sirrinsu,da yar ta shigar da ita Waki,ta ce kowa ya wuce gidansa.

an uwan Umma Kande ne da dangin Maman Jummalo d'a Wakinta tare da ita kanta Maman Jummalo suna bama Umma Kande baki akan tayi hauri,ta kwantar da hankalinta bayan biki sai a bi lamarin na Musa a hankali.

Haka dai suka lallaSata har da rage kukan sai dai shasshea wanda lokaci bayan lokaci take ajiyar zuciya.

Shiko Musa ko a jikinsa hasalima fita daga gidan yayi,daman baida niyyar kwana gidan,hotel na garin yaje ya kama na kwana huWu har a gama biki ya koma Calabar abinsa.

arin Haske

*****Abinda bata sani ba game da Musa shi ne,tun farkon tafiyarsa Calabar halayansa suka fara canjawa,duk da lokacin akai-akai suna waya da Umma Kande, zuwanshi gida wanda daga shi bai ara zuwa ba sai wannan zuwa duk halayansa sun canja,kasancewarsa mai sanyin murya,gashi ba mai hayaniya ba yasa a lokacin da yaje Calabar abubuwa suka mishi wuya,tunda baida zafin nama da karsashi a komai nasa kamar wata mace haka yake ji da kansa.Farko ya fara dako sai daga baya yaga babu ci ya daina,sai wani abokinsa da suke kwana a Waki Waya yaji tausayinsa yayi mishi hanyar aiki gidan abinci wanda yawancin an aikin hausawa ne amma fa cikakkun an bariki mai gidan abincin ma bahaushiya ce,haka ya fara aiki gidan abinci wanda daga arshe an daudun gidan abinci suka fara bashi sha'awa ganin suna samun kuWi sosai,manya-manyan matan garin suna zuwa Waukarsu fita cikin manyan motoci,shima kawai ya tsunWuma cikin wannan harkar,abinda yafi arfafa mishi son shiga harkar shi ne Mamansa Umma Kande,a duk sanda sukayi waya da ita sai ta mishi orafin rashin turo kuWi akai-akai da ba yayi,wai ya cika son jiki kamar mace,shi yasa bai samun komai a acan, ga abokanansa wasu har da gidaje da mata amma shi ko sisi bai turowa balle tunanin yin aure,shi kuma a gaskiya maganganunta suna ona mai rai sosai,shi yasa ya bama kanshi shawaran zai naima kuWi kota y'halin aa ne in har Mamansa zata daina ce mishi rago ne.Wannan ne asalin dalilin da yasa Musa shiga cikin harkar an daudu a Calabar har shi ma yanzu yayi suna a can ana kiransa da Pretty Mussy,don ba laifi tana kai mai yanda ya kamata.Daman wannan zuwan da yayi bayan biki yake son ya siya gida sannan ya siya shagugguna a kasuwa wanda kuWi zai dinga shigo masa akai-akai har Mamansa tayi alfahari da shi kamar yadda take alfahari da Nusaiba wai tafishi samun kuWi kuma tana tallafa musu a gidan****.

@@@@@@@@@@@@@@

Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta Allah yasa basama gidan a lokacin da Musa ya dawo,balle suga abin mamaki da al'ajab,kuma koda suka dawo Waki suka shige abinsu,daman ba shiga harkar bikin suke ba tunda ba'a sakasu ciki ba,Sa'eeda da take budurwa ma babu wacca a cikin an uwan nata ya gayyace ta balle taje an matanci a bikin.

Dangin Abbansu Sa'eeda tun fil-azal ba son Umma Kande suke ba shi yasa koda wannan lamari ya afku suna Waki basu fito ba sai dai Allah ya kyauta suka iya cewa, dayake mata uku ne sai namiji Waya sukazo bikin.annan Abbansu Sa'eeda mata da yayarsa Waya sai kuma aninsa namiji sukazo bikin.

Dayake suna shiri sosai da Umman Sa'eeda haka sukai ta janta da Sa'eeda a jiki.Hakan yama Sa'eeda daWi a rai,ganin yanda suke janta a jikinsu da hira har da Ummanta.

Daman auran Umman Sa'eeda su ne suka arfafa gwiwar sai ya ara aure saboda halin Umma Kande,bata girmama iyayansu tun suna raye,gashi da tsani wani daga daginsu ya raSa Abbansu Sa'eeda saidai ita da yaranta kaWai,wannan dalilin ne yasa aka aura masa Umman Sa'eeda saboda tanada hankali da girmama na gaba da ita ba kamar Umma Kande ba.

@@@@@@@@@@@@

Umma Kande dai ta dangana,tayi hauri sai bayan biki kamar yanda Maman Jummalo ta ce da ita saboda bikin,ta haura ta cigaba da shirya shiryan biki sosai,tun ana saura kwana uku amare suka fara shagalin biki har yau da ya kasance gobe Waurin aure suna shagali kala-kala.

Day 1 sunyi auye day, sai day 2 sunyi fulani day sai yau kuma ana kamun amare,anyi kashe kashen kuWi,ba laifi angwaye sunyi Sarnar kuda don Naira tayi kuka=.Nusaiba tayi Sarin Naira sosai dan yanxu ta zama wata himmm da ita sai kace wata babbar mace ,tayi iba sosai ga bleaching Win da take yanxu na allura ne, tayi haske sosai sosai.

Duk wannan bidirin da ake yi a gidan bai hana Sa'eeda zuwa makaranta ba,sannan Ummanta ma haka kullun sai ta fita shara abinta,a tare suke fita da safe abinsu.

@ @@@@@@@@@@@@

Ranar Waurin aure

Yau take asabar kuma ranar Waurin auran yara uku a gidan Malam Sulaiman Sani,a Masallaci aka Waura auran na aan uku akan sadaki Naira dubu #100,000 lakadan ba ajalan ba ga kowaccansu,sannan aka shafa fatiha aure ya Wauru(Su Umma Kande sai a zuba ruwa a asa a sha====).

Angwaye babu wanda yazo gaisuwan iyayen amare kamar yanda ake a al'adan ce,nan ma akaita surutai musamman an layi( an layi akwai gulma,kunsama su Umma kande da Maman Jummalo ido,kun hanasu rawar gaban hantsi haba====C>) ,wurin arfe 8:00pm aka zo Waukan Jummalo, sai kuma Zaliha,ita kuma Iklima sai 11:00pm aka Wauke ta,wannan abu ya janyo surutun mutane da dama, su Umma Kande hakan bai dame su ba tunda an Waura mai ya rage can tamatse musu da gulmar,duk lokacin da suka zo Waukar amare suna mara ba dasu tunda dai an Waura auran arshen tika-tiki-tik.

Haka aka kai kowacce Wakinta,babu laifi angwaye sunyi bajinta sosai,sai dai bamusan ya yanayin zaman auran nasu zai kasance ba.

@ @@@@@@@@@@@

Bayan kwana biyu da biki,dangi na kusa da na nesa kowa ya koma gidansa da abin arzii daga wurin su Umma Kande da Maman Jummalo banda dangin Abbansu Sa'eeda tai basu abin biki wai tunda dama ba sonta suke ba kuma wannan zuwa biki wurin su Umman Sa'eeda suka tare to wallahi babu abin biki da zata basu,har Abbansu Sa'eeda saida ya roa amma tai,haka suka wuce garinsu daman su can basu sa rai a abin bikin ba balle hakan ya damesu.

A ranar bayan tafiyar an uwan Abbansu Sa'eeda daman su kaWai suka rage, Musa ya shigo gidan,tun sanda yazo gidan ta fara kuka bai sake zuwa ba kuma koda yaje Waurin auran bai zo nan gida ba.

Lokacin arfe 12:00pm na rana,shiga Wakin Umma Kande ya yi da sallama kamar mutumin arzii amma muryar nan a lanwashe take kamar mace,ya samu wuri akan kujera ya zauna.

Maman Jummalo ce ta amsa masa sallamar amma Umma Kande ko kallan inda yake batayi ba.

akin shiru ya Wauka na Wan wani lokaci kowa na zancen zuci kafin Musa ya atse shirun da gaishe dasu.

"Mommy na barka da rana,na same ku lafiya,ya gajiyan biki"

Yana maganar yana yanga sai kace mace,su Umma Kande dai ido suka zuba mai babu Waya a cikin wanda ya iya amsa mai,tsabaragyen mamaki da ya cika su musamman Umma Kande wanda har yanzu ta kasa yarda Wanta ne Musa,shi Musa Wanta ya zama Wan daudu.

"Yanxu Musa wannan wani irin Wabi'a ne ka Wauko,kaga kuwa yanda ka koma yanzu sai kace mace wallahi abinda kakeyi ko wata macan baza tayi ba,haba Musa ya kamata ka dawo cikin hayyacinka don Allah" cewar Maman Jummalo

"Nahiiiiii Maman Jummalo inji an india kinsa nayi yaransu , wannan ra'ayina ne,babu ruwanki koma mai zanyi,haka nake da ra'ayin zama,kuma ina alfahari da zama na haka,chass wallahi"

Miewa yayi duk suna binsa da kallo yayi wani juyi a Wakin tare da girgiza Wan aramin kafaWunsa sannan ya ce

"Yanzu ki kallo dubeni kyakkyawa dani san kowa in wanda ya rasa,ke a Calabar ma har bukin Wina akai manya manya Mata suna ji dani,zaki wani ce in dawo hayyacina,to da ba a hayyacina nake ba"

"Shikenan ni Saratu, ta faru ta are Musa,yanzu a gabana ni mahaifiyarka kake girgiza kafaWunsa haWe da rangwaWa,wayyo ni Sarere jikar sarkin ruwa!!!,na shiga uku!!! "

Kuka take yi mararan,da sauri Musa yazo wurinta haWe da dafa kafaWunta tare da cewa" Sorry mommy mi,kibar kukan nan don Allah babyn ki da kika sani a da bana yanzu bane,don nayi kuWi sosai sosai "

Tsagaita kukan Umma Kande tayi tana dubansa tare da cewa"Da gaske kake Musa na Wan albarka"

aga mata kai ya yi alamun eh,haba sai Umma Kande ta haWe ido da Maman Jummalo nan suka kwace da dariya.

"Haba sai yanzu naji sanyi a raina,mai yasa tunda kazo baka faWamin ba,kabarni ina kuka akan yanayin da ka koma,ai babu laifi tunda akwai samu"

"Wallahi mommy naso faWa miki amma sai naga duk kin rikice kawai sai na bar gidan na tafi hotel abuna,daman na bari sai bayan biki nazo muyi maganar dake"

"Toh yanzu dai fadamin maganar ina jinka kace kayi kuWi,ni kuma banga komai ba"

Dariya Musa yayi yana wani lanwasa afa Waya kan Waya sannan ya ce"Suna account Mommy,daman nazo ne da niyyar siyan gida,tare da shaguna koda biyar ne a kasuwa,sai nasa haya,kinga zaki dinga samun kuWi akai-akai ko Mommy na? "

"Da kyau Wan albarka,naji daWin wannan batu wallahi, Allah yama albarka,amma gaskiya idan zakazo garin nan,inaso ka koma yanda kake a da,bayan ka tafi sai ka juya saboda an gulmar layi kaji Wana"

"Bakida case Mommy mi, yanzu sai ku fara cigitamin gidan haWe da shagunan ko"

Da "Eh" dukkaninsu suka ce suna murmushi ,sai ya ciro bandri Win dubu kuda uku ya mia ma Umma Kande da Maman Jummalo, haba wannan karon harda kuWa tare da rungumeshi su duka(Allah ya kabamu wadatar zuci da arin imani).Wannan kenan.

@@@@@@@@@@@@@

A bangaren karatun Sa'eeda sai dai muce maa shaa Allah,tana maida hankali sosai da sosai dan yanzu har sun kammala first semester suna a second semester a lokacin first semester result Winsu har ya fito.Sa'eeda ce ta samu highest score a class Win nasu wanda baima da yawa daga cikin an ajin daWi ba.

Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi a school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department Winsu ita da Maryam zasu nufo wajen gate Win makarantarsu don su samu mai keke napep ya kaisu gida,sukaji horn Win mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta zuyo suka cigaba da taifiyarsu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba,yayi saurin parking a gefen titi sannan ya fito daga motar.............



****waye wannan mai yima su Sa'eeda horn kuma mai yazo dashi wurinsu?.......


****Gashi dai burinsu Umma kande ya cika an aurar da aa,koya zaman nasu zai kasance da mazajensu?.........


<9<9<9Shin ya kuke ganin mugun son kuWin Umma Kande wanda ko kallon yanda Wanta ya koma batayi ba,mai zakuce akai........


Sai mun haWu da pages na gaba in
shaa Allah=C=C=C


Ina matuar alfahari daku My Esteem Fans=؝=؝=؝<9<9<9<9


I love y'll lodi lodi domin da bazarku nake taka rawata=؝=؝=؝=؝=C=C=C=C>>>>



Daga alalamin
=؍=Narrnarhh Bukar ==؍

Comments and share =O=O=OFisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
< NACINA YAJAWOMIN<


Narrnarhh Bukar
'

<9Perfect Essential Writer's
Association<9
(' P. E. W. A('


Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002




My Esteem Fans ina matuar alfahari daku, i love y'll all Lodi Lodi>>><<<<<<<<<<9<9<9=C






1 9 ---2 0


Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi daga school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department Winsu ita da Maryam zasu nufo gida,sukaji horn Win mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta juyo suka cigaba da taifiyansu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba, sai yayi saurin parking a gefen titi kana ya fito daga motar.

Wani handsome and classy guy ne ya fito daga motar,yana sanye da shadda mai kalar sararin samaniya,sanye yake da hula mai ube wacca ta saje da kalar kayan.Yana da tsayi sosai,bai ne amma ba cancan ba,sannan fuskarsa zagaye take da gemu wanda kana gani kasan yana shan gyara,his face look very innocent,babu laifi guy Win ya haWu sosai,da murmushi a fuskarsa ya nufo wurinsu da Wan sauri kasancewar tafiya suke.

"Assalamu Alaikum Malamai"

Maryam ce ta amsa mishi da fa'arta,ita ko Sa'eeda ko kallansa batayi ba,idonsa na kan Sa'eeda yana murmushi,don mace mai aji tana burgeshi sosai.

"Naga akwai rana sosai yau,gashi kuna tafiya babu mai keke napep suka balle ku hau,mai zai hana na rage muku hanya koda ban kaiku gida ba,kar kusha wahala"

A lokacin ne Sa'eeda ta bashi amsa da cewa"Kaga munyi ma kana da musu son a rage musu hanya ne,to karka damu,mun gode da kulawarka amma......."

Bata arasa zancen da tayi niyya ba Maryam tayi saurin cewa"Babu komai muje Sa'eeda, kinsan uzirin da ya bari ya ce zai rage mana hanya ne? "

Sunan ya sake maimaitawa a zuciyarsa ' Sa'eeda suna mai daWi'

Babu yadda Sa'eeda ta iya tunda abokiyar tafiyarta tana son a rage musu hanya amma a ranta baso take ba tuno da nasihar Ummanta akan kula samari,haka dai ta shiga motar.

Maryam ce ta zauna a front seat,ita kuma Sa'eeda ta shiga baya,tada motar yayi suka fara tafiya.

Motar shiru babu mai magana sai can ya katse shirun da cewa"Wani department kuke? "

"Department of Business Administration muke,100level" cewar Maryam

" Woow,ashe fresh students ne ku"

"Eh wallahi amma yanzu muna a second semester ne"

"Allah ya taimaka,ya bada sa'a"

"Ameen ya Rabbi" cewar Maryam

"Wai awarki kurma ce,bata magana ne? "

Dariya Maryam tayi sannan ta ce"Magana kuwa sosai,saidai da alama an surutun basa nan yau"

"Oh really ai naga alama kuwa"

Maryam ce take nuna mishi hanya,har ya kai daidai inda take so a sauke su wato hanyar da zata sadasu da layinsu,sannan yayi parking gefen titi,ya juyo yana duban Maryam yace.

"Sunana Sauban Muhammad  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~araye,ina aiki a wani kamfinin sarafa shinkafa a matsayin Manager nice meeting you friend"

"Nice meeting you too"cewar Maryam

Dukkansu fitowa sukayi,a tare har shima don yana son magana da Sa'eeda amma ta mishi kwarjini a fuska.Har zasu wuce yayi saurin cewa

"Friend ko zaki aramun wannan awarta taki mara son magana,zsmuyi magana ne just for 2 minutes"

Yana maganar da zolaya duk don Sa'eeda da tanka amma shiru,hasalima ara murtuke fuska tayi.

an jimmm Maryam tayi sannan ta ce "Haba bara na matsa,sai ku tattauna da ita"

Matsawa tayi Wan gaba dasu,shi kuma ya matso kusa da Sa'eeda da murmushi a fuskarsa,sai da yayi gyaran murya sannan ya fara magana da cewa.

"Nasan ba a jinki bane magana a hanya amma taimako nake nema wurinki,don Allah ba dan ni ba ki taimaka min da number wayanki,Don girman Allah"

Hannu biyu ya haWa alamar roo,fuskar nan ta shi tayi kalar tausayi,Sa'eeda a da bata da niyyar ba shi numbarta amma haWata da Allah da yayi yasata aminta saboda ta tuno nasihar Ummanta da ta ce ' Sa'eeda duk wanda ya nemi abu wurinki kuma ya roeki da Allah koda cutarki zaiyi ki basa,sannan ki barshi da Allah' tuno da wannan nasihar yasata amsar wayarsa tasa numbarta sannan ta mia mai wayar tare da wuce wurin Maryam suka nufo gida.

@ @@@@@@@@@@

arfe 11:53am ta iso gida,lokacin Ummanta ta dawo daga aikin sharanta tana Waki.

Da sallama ta shiga gidan kasancewar yanxu babu an mata a gidan daga ita sai Nusaiba,ita kuma Nusaiba ba zaman gidan take ba, yanxu ma kamar kodayaushe shiru gidan saika ce babu mutane ko a da can da akwai mutane a gidan ba amsa sallamarta da Ummanta suke ba.

Direct ta wuce Wakinsu,haWe da sake Sallama, Umman Sa'eeda dake a tabarmarta ta amsa mata tare da cewa.

"Da wuri haka"

"Eh Ummina,kinsa ranar jumma'a bamu cika lectures da yawa ba,yau kuma lecturer Waya ne ya cigo ajin namu"

"Ai gwara,zaku Wan dinga hutawa,ba ace kullun sai wurin biyar zaku dinga ta shi ba,wahalar yawa zata muku"

"Nima Ummina nafi son duk ranar Friday mu dinga tashi kamar haka wallahi"

Buta Sa'eeda ta Wauka ta zagaya bayan gida,bayan ta dawo ne taji wayarta na ringing,sai ta nufa jakarta ta Wauko wayar.Sabuwar numbar ta gani,Wan jimmmm kaWan tayi har saida Ummanta ta ce

"Kina ji ana kiranki amma kin wani tsaya kamar hoto kina kallon wayar"

Picking call Win tayi haWe da karawa a kunnanta sai tayi shiru,acan bangaren aka fara magana.

"Tsira da amincin Allah su ara tabbata a gareki Sa'eeda"

"Wa'alaikumussalam"

A gajar ce ta amsa haWe da tsuke fuska kamar mai shirin kuka Ummanta dai na binta kawai da kallon mamaki ganin yadda take amsa wayar,a can a ka cigaba da Magana.

"Nasan kin gane mai maganar don koda jin kamar kina Waure fuska nasan yes kinsan mai maganar"

A zuciyarta ta ce 'Sai ka ce maye,to taya yasan na tsuke fuska na,ohon masa' katsa mata tunani yayi da cewa

"Sa'eeda ganinki na farko da nayi a Wazo,lokaci guda kika shiga raina,kuma a gaskiya bazan Soye miki ba ina sonki da aure ne ba da yaudara ba,zuciya ta gama yarda da ke ce wacca take adduarka samu a kullum haWe da burin kasancewa tare da ita a matsayin miji da mata,please Sa'eeda ba nazo dan na yaudareki bane ko ko wata manufa tawa don in cimma,a'a ko kaWan nazo ne a gareki saboda aunarki da nake yi wanda lokaci kuda ya shigeni,don Allah ki aminta dani please,in ma kina tunanin karatunki ne ni a shirye nake tare da goyon bayan karatunki Wari bida Wari,inaso kiyi tunani akai don girman Allah Sa'eeda bada wasa nazo gareki ba"

Duk wannan surutan da yake wayar na a kunnanta kuma tana ji amma ta kasayi mishi magana,hasalima shiga kogin tunani tayi 'Wai yana sonta da aure huhh',ita da a tsarin rayuwarta bata kawo aure nan kusa ba,amma shi yanzu yana mata maganar aure.

"Hello,baki jina ne Sa'eeda"

Firgigit ta dawo hayyacinta tare da fara magana cikin murya mai sanyi da dadi ta fara magans"Ina jinka,but can you please give me some days to think about it?

"Quite sure dear"

"Alright Nagode da kulawa"

Bata jira mai zai ce ba ta katse kiran,sai da dubi Ummanta da tun Wazu da zuba mata na mujiya.

"Naga sai wani taSe baki kike haWe da ya mutsa fuska tunda kika Wau wayan lafiya? 

" Wallahi Ummina wani ne mai suna Sauban Wazu ya takuramin haWe da haWa ni da Allah in taimaka mishi da number na,lokacin mun taso daga school ni da Maryam kuma yanzu da ya kirani sai sai..."

"Uhmmm ina jikin sai kuma me"

Kwashe duk abinda ya ce mata tayi ta sanar da Ummanta har aikin da ya ce yakeyi duk ta sanar mata, shiru Ummanta tayi tana kallonta sannan ta ce

"To ke kuma me kika ce masa"

"Nace ne ya bani lokaci zanyi tunani a kai"

"To ai shikenan,amma dai ki kula da kanki Sa'eeda,don mazan yanzu wasunsu ba abin yarda bane,sun iya kalamai masu daWi ga an mata duk don suja hankulansu,ina ara fadamiki ki kula da kanki sosai,ban hanaki kula samari ba amma ki duba wanda yasan ya kamata sannan kuma mai addini da halaye masu kyau a cikinsu sai ki kulashi,amma ba kowani kala ba,ko kuma kita tara samari,kin jini ko"

"Toh Ummina,zan kula sosai in shaa Allah"

"Allah yasa"

"Aameen"

Sai kuma suka cigaba da wata hirar .

@@@@@@@@@@@@@

Bayan an wasu kwanaki

Sa'eeda dai ta aminta da soyayyar Sauban,dan yanzu yakan zo har ofar gidansu,duk da a wata baifi sau Waya yake zuwa ba kasancewar Sa'eeda bata cika son hira ba hasalima shi yake matsa mata akan yanason yazo koda sau Waya ne a wata.

Sunyi exams Win second semester wanda azumi baifi saura kwana shida a Wauka ba suka gama,duk wannan lokacin suna tare da Sauban wanda yanzu soyayyarsa ta riga da ta gama mamaye ilahirin jikinta da gaSoSinta gaba Waya.

Sauban ya iya kashe mace da salon soyayyarsa,don zance professor ne a ta wannan fannin,ya kama zuciyar mace taji duk duniya babu wanda take so sai shi,haika ya rikita Sa'eeda da kalaman soyayya masu saka mutum shaui,sannan yana kula da lamarinta sosai duk da idan ya bata kuWi bata amsa sai in ya mata jan ido kana take amsa haWe da yi masa godiya.

Haka sanda aka fara azumi ya kawo mata ramadan basket da yar ta amsa saboda Ummanta ta hanata yawan amsar kaya wurin samari,haka zalika lokacin sallah kaya kala biyar ya mata haWe da jaka da takalmi masu tsada,shima da yar ta amsa sannan ta masa godiya sosai.

Duk wannan abubuwan da Sauban yake ma Sa'eeda sai ta faWama Maryam tun daga kalaman soyayya da yake mata,kyaututtuka da dai sauransu,duk da wani lokacin ba Sa'eeda take fara bata labari ba,ita Maryam da kanta take tambayar ta ya friend Winta,to a nan ne sai ita kuma Sa'eeda tai ta zubo mata zancansa.

Haia wannan sallar su Sa'eeda sunyi shi cikin farin ciki da annashuwa ba kamar saura shekarun da suka gabata ba kasancewar yanzu babu laifi Umman Sa'eeda na oarin ganin sunyi cima mai kyau.

Bayan sallah da sati Waya suka koma 200 level,soyayyar Sauban bai hana Sa'eeda karatu ba hasalima yanzu karatun nata ya ara bada wuta saboda tana so taga a kowanni result ta fito da flat A,shi yasa kullun zaka ganta da littafi a hannu tana karatu.

Akwai specific time da taba ma Sauban zai dinga kiranta ba koda yaushe ba,kuma hakan ta faru sai lokacin yake kiranta don baya son matsa mata da yawa.

@ @@@@@@@@

Waje guda kuma,rayuwarsu Umma Kande da Maman Jummalo ta cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment