Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suka tsaya sunyi cirko-cirko suna kallon su Umma Kande da yaron sun ?i tafiya "To ya za'ayi da Mom Winsa,bacci take kuma ya kamata akaita Wakin hutu" "Kuma fa hakane,muje mu kaita Wakin hutu tunda gadon mai taya ne,abun yazo da sau?i" cewar wata nurse Haka suka koma cikin labour room Win tare da turo Maman Jummalo a gado mai taya zuwa Wakin hutu,still tana nan tana bacci batasan meke going ba.Su Iklima,Jummalo da Umma Kande na biye dasu zuwa Wakin,Wakin? mai zaman mutane biyu ne domin akwai empty gado wanda ba mutum akansa,haka suka shimfiWe Maman Jummalo a gado tare da sake leka yaron sannan suka wuce abinsu.(Oh ni Indo Nurses da shegen gulma,duk hotunan da kuka Wauka na jaririn bai isheku ba=??=??=??=?C?=?C?) Zama su Umma Kande suka yi sannan ta shimfide yaron a bisa gadon jarirai na Wakin sannan ita ma ta samu wuri kusa dasu Jummalo ta zauna,abin duniya ya addabi zukatan kowannansu,kowa ka gani yayi shiru yana karanta wasi?ar jaki(Au na manta ashe suna da Wa mai kan jaki=??=??=??) Maman Jummalo ta kwashe kusan hour biyu cur! Tana bacci sai can yaron ya fara kukan jaki alamun ya farka,itama kukan yaron ya tasheta cikin Sacin rai irin an hanata bacci Maman Jummalo ta ce "Wani irin hauka ne haka!!! Wa ya kawo jaki cikin asbiti ne!!! Duk ya ishemu da kuka babu daWin ji balle sauraro!!!? " Shiru sukayi dukkaninsu suna kallonta,tausayinta ne ya kama kowannansu musamman ?arta Jummalo wacca har yanzu sharan hawaye take,shirun nasu ?ara fusata Maman Jummalo yayi saboda kukan jakin a cikin Wakin take jinsa,cewa tayi "Wani irin abu ne haka,ina muku magana amma kun tsiramin na mujiya kunki amsani,kukan ma a Wakin nan nake jinsa" Umma Kande ce ta da ita "?awas don Allah ki rage fushin nan haka, duka-duka yaushe kika haihu,ki kwanta ki huta mana" "Inajin kukan jakin zan kwanta ?awas,ce nike kukan ne ya tasar dani daga bacci,wai ma ina Wana yake" Kallan-kallo kowa yake acikinsu an rasa mai bata amsa,katse musu tunani tayi da cewa "Magana nake muku fa" "To ai yaronki ne ke kukan jakin" cewar Iklima "Menehhh shike kukan jaki!!!.... " Tsandara wani sabon kukan jaki jaririn yayi jin an?i Waukarshi tare da katse maganar da Maman Jummalo tayi niyyar faWa,ji kake "Hiiiihiiiiih!!! Hiiiihiiiiih!!! Hiiiihiiiiih!!! " "Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un ni Hafsy naga ta kaina,ke kawoshi na dubashi nan" Iklima wacce take kusa da gadon da jaririn yake tayi saurin Waukoshi hadi da mi?a matashi still yana tsandara kukan jakin, ana mi?a mata ?irijinta ya bada wani sautin Ras! Ras! Rarass!!! A lokacin da tayi tozali da kansa irin na jariran jakuna sababbin haihuwa,kuka Maman Jummalo ta fara tare da ?ara duba yaron nata,innalillahi wannan wace sabuwar musiba ce haka yaro da kan jaki,tana kuka shima yaron na kukan jaki, Umma Kande ce ta ce "?awas nono yaron yake so fa" "Nono zan ba jaki Umma Kande, tayaya zan shayar da jaki ni Hafsatu wannan wace kalar musiba ce haka,daga wannan bala'in sai wannan duk a sanadiyar zuwa wurin boka,wayyo ni Hafsy,na bani na lalace" "A'a fa yanzu ba lokacin kuka bane ?awas ki bashi nono yasha tunda daga cikinki ya fito,albashi idan mun koma gida sai musan abunyi" Haka da jiro nononta tare da saka mishi a baki,kamar jira yake ai da ya wani zu?o nonon da sauri Maman Jummalo ta fizge nonon daga bakinsa jin wata azaba ta taso mata tun daga ?wa?walwarta zuwa kan nonanta wanda tunda take bata taba jin irin makamancin azabar ba,ko sanda ta haifi Jummalo bata ji zafi irin haka ba,Umma Kande ta kara cewa "Haba ?awas ki bashi yasha mana kuka fa yake fa,ko so kike ya tara mana jama'a a cikin Waki" "Wai wai waiii ina zan iya ?awas wannan azaba haka! Ai don ba nonanki yasha bane shiyasa zaki ce haka" ?ara tura mishi nonan tayi a baki,da sauri ya cafke ji kake Zut! Zut! Zut! Yana zu?ar ruwan nonan kasancewar Maman Jummalo akwai ruwan nono, yakai kusan mintuna ashirin yana shan nonan amma baida alamun ?oshi,ita kuma Maman Jummalo yunwa take ji sosai,tana bukatar tea mai kauri ko hanjin jikinta sa warware,fizge nonan tayi tare da cewa "Wallahi ko ka ?oshi ko baka ?oshi ba ya isa haka, wannan jaraba dame yayi kama haka,ni ku bani abinci yunwa nake ji" ?auko mata shayin da aka siyo mata a waje ne aka bata tare da soyayyan indomie da ?wai,ci ta fara yi wanda bata daWe ba saiga likita da nurses Win nan da suka amshi haihuwarta,tambayoyi ya mata tare da duba yaron, mamaki da al ajabi ya kama likita ganin yaron da kan jaki sak!,cewa yayi a yau za'a sallamesu tunda uwar da Wan lafiyarsu lau,fita yayi su Umma Kande sukaje wurin biyan kuWin sallama,kafin su dawo har su Jummalo sun tattara komai tare da goya yaron,fitowa sukayi zuwa wajen asibitin domin taran keke napep su wuce gida,sunci sa'a ko mintuna biyar basu yi ba saiga empty keke napep sun samu,shiga sukayi sai mai keke napep ya tada suka wuce,a akan hanya yaro da yaji wata sabuwar yunwa kawai ya fara kukan jaki babu ji babu gani,da sauri me keke napep Win ya tsayar ta kekensa,Allah ma ya tsaresu da sai sunyi accident saboda firgici hadi da ruWun da mai keke napep Win ya shiga jin kukan jaki a keke napep Winsa,bayan yayi parking ya ce "Malamai lafiya naji kukan jaki a kekena kuma banganku da jaki ba? " "Kayi ha?uri haka halittar yaron take,kukan jaki yake tunda aka haifesa" cewar Jummalo Wacca take a gaba tare da mai keke napep Win, mamaki ne ya cika shi,girgiza kai yayi tare da tada keken suka cigaba da tafiya har suka isa ?ofar gidansu,sauka sukayi sai Umma Kande ta biya mai keke napep Win kuWinsa sannan suka shiga cikin gidan. Nusaiba ce da Al Qur'ani izu 10 tana karantawa taji shigowarsu da sallama,amsa musu tayi da fa'arta tana ina yaronsu,su kuma fuskar nan tasu babu yabo babu fallasa,kwance goyan Maman Jummalo tayi lokacin har ya koma baccinsa ta mi?ama Nusaiba tare da nufar Wakinta don ta huta,da sauri Nusaiba ta amsa yaron tana dan murmushin,ai tana buWe gefen zanin daya rufe fuskar yaron ta tsandara ihu tana cewa "Na shiga aljanna ban fito ba,yaro da kan jaki!!!" "Ai saiki faWa kowa yaji harda ma?wafta!!! " cewar Umma Kande tana amsar yaron zuwa Wakin Maman Jummalo Mutuwar tsaye Nusaiba tayi,a zuciyarta tana ?ara tsakake sunan Allah tabbas Allah da girma yake, shike yadda yaso a lokacin da yazo,shike nuna ishara ga bayinsa a sanda yaso kuma a yanayin da yaso,tab! Zuwa wurin boka ko malamin duba baiyi ba,ga ?arshan zuwa wurin boka an haifo yaro mai kan jaki,Allah ya shiryamu shirin addinin musulunci,haka tayita zancen zuci still tana a tsayan kowa ya shige Wakin Maman Jummalo anbarta a wajen sai itama da shige Wakin. Koda Nusaiba ta shiga Wakin ta samu Maman Jummalo naba yaron nono,tsira ma yaron ido tayi ganin jariri dashi har ya iya ri?e nono abinsa ikon Allah, Wakin shiru yayi sai can Umma Kande ta ce "?awas yanzu ya za'ayi da wannan yaron ne" "To ya za'ayi dashi tunda Allah ya ?addara fitowarsa,ai sai ha?uri zamuyi" "Nifa wata shawara nazo da ita ko ince dubara" TaSe baki Maman Jummalo tayi don tasan maganar *gizo bata wuce da koWi* ce mata tayi tana saurare,saida Umma Kande ta gyara zama sannan ta ce "Tunda yaron ya fito duniya,mai zai hana mu sake komawa kun boka Sankeruuu........" "Dakata Umma Kande!!! Allah ya sittiri- bu?yi ni Hafsy na sake zuwa wurin wani don neman wata biyan bu?atata,da Allah na dora kuma shi zai biyamin bukatuna,wai ke Umma Kande baki ga isharar da take sauka akanmu bane duk saboda zuwa wurin bokan da muke ehhh,ce nike garin yawan zuwa wurin boka na kwaso ciki,sannan yanzu ga wata babbar ishara wacca Allah ya kara nuna mana duk don mu hankalta ,mu gane Allah ne ke biyama mutum bukatunsa ba wani ba,in ba ikon Allah ba tare da nufinsa taya mutum zai haifi yaro mai kan jaki,haba Umma Kande ki tuba mana,ce nike wacca kike zuwa wurin boka don ita tabar miki gidan keda yaranki,amma har yanzu? kin kasa gane Allah Waya ne" Huro guntayan hancinta Umma Kande tayi tare da taSe baki irin ko ajikinta Win nan, magana ta fara cike da ?asaita "Ke kikaga wani ishara bani ba,kuma zuwa wurin boka na faWa na ?ara yanzu na fara zuwa,babu gudu babu ja da baya,domin kuwa naga alfanu da daman a wurin zuwa wurin boka" "Haba Mama wai yaushe zaki tuba ki gane Allah Waya ne,Muhammad (S.A.W) manzonsa ne,kina cewa baki ga wata ishara ba,abubuwan da sukaita samun mu a gidan mazajenmu duk ba isharori bane Mama,yanzu ga yaro an haifa mai kan jaki shima din ba ishara bace a gareku masu zuwa wurin bokaye da malaman zaure,haba don Allah a gaskiya kam ki gyara domin ke kaWai ce bakiyi nadama ba" cewar Iklima "Oho dai ni kunga tafiya ta,bara nasa a nemo almajirai su siyomin itace da Wora ruwan wankanku" Mi?ewa tayi tare da barin Wakin,su kuma da kallo suka bita tare da yi mata adduar shiriya,haka suka cigaba da jegon wanda kafin ayi suna yaron yace ga garinku nan,daWi kamar ya kashesu ana damuwa da mutuwa amma su farin ciki suke domin kasancewar yaron a raye ba karamin matsala bane a garesu,saboda gulmursu za'a dinga yi ga Wan goka?an haifa musu. Haka suka cigaba da rayuwa hankalinsu kwance musamman Maman Jummalo jinta tare sakayau babu abinda ke damunta a yanzu,ibada ta koma yi ka'in da na'in babu wasa,ita ma haka Nusaiba ibadarta take yi ga jin wa'azuzzukan malamai da dama,su Iklima da Jummalo sun cigaba da zuwa Islamiyarsu sannan idan suka dawo sai su koyama Maman Jummalo da Nusaiba ita kuma uwa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r gayyar saidai ta taSe baki tare da hura guntayan hancinta sama irin ko ajikinta.Wannan kenan ? ? ? ? ?? @@@@@@@@@@@ A Sangaren zamantakewar *LOVE BIRDS*? =?J??=?J??wato Sauban da Maryam har yanzu zamansu babu daWi,kusan ince ita take da matsala bashi ba domin baka taSajin faWansu da Khairat saidai ita,kullum da ita suke faWa suyi su gaji wani lokacin harda doke-doke musamman idan a kamfani an Sata masa rai akan Maryam yake sauke fushinsa,ita ba hakuri kamar zawo haka take biye mishi shi kuma ya mata dukan tsiya.Har yanzu Maryam batasan me ake kira da aure ba,kuma iyayenta sun?i Worata a turbar gaskiya na bin mijinta da surikarta a kullum cikin zugata suke akan karta yarda a rainata ko? kuma karta sake a wula?anta ta,sun?i koya mata abubuwan da macen kirki ya dace ta sani a gidan auranta irin iya girki,tsafta,sanin darajar miji da hak?ok?insa,girmama uwar miji da danginsa,iya lafuzza masu daWi wurin yima miji magana da dai sauransu. A zamantakewarta da kishiyarta Khairat babu wani matsala domin Khairat tasan kan zaman duniya sosai,bata biye ma shirman faWanta,koda Maryam ta takaleta da faWa bata biye mata saidai ma ta? shige Waki abinta. Har yanzu babu wacca a cikinsu take da ciki ko kuma tayi Sari,hakan na damun Momin Sauban don ita a tunaninta ada baya kula Maryam shiyasa bata samu ciki ba,to yanzu fa ga Khairat ita shiru babu alamun ko Satan wata ta taSa yi. A Sangaren aikin Sauban a kamfani kamar jiya iyau ne domin duk wata hanyar da zasuyi cuta Sadam ya kulleta,komai akan tsari yake, babu muna-muna balle handama da babakere,wani lokacin idan Sauban ya zauna shi kaWai sai yayita karanta wasikar jaki(bafa Wan Maman Jummalo nake nufi ba ehehh=??=??=??=?C?=?C?) A zuciyarsa yana faWin 'Anya bada *farar ?afa* duka matana suka cigo gidana dashi ba,kullum babu cigaba sai baya,duk ?an uwana sun mallaki gidan kansu amma ni ko fili na gagari siya,Ya Salam a gaskiya akwai inda na samu matsala,gaskiya da sake wallahi,abin haushi saidai kowaccansu tashi tayi kashi amma ko Satan wata babu wacca tayi,da alama hauka zanyi musu wallahi dole su haihu don na gaji da ciyar dasu a banza babu haihuwa' haka yayita tunaninsa tare da sa?a-warwarar yadda zai fito musu mutum.Wannan kenan ? ? ? ? @@@@@@@@@@@@ *KEBBI* Sadam tunda ya isa Kebbi,yake ta tasa Mominsa da shagwaba wai shi aure yake so ayi mishi,dariya maganar Sadam tabama Mom da Daddynsa lokacin dukkaninsu suna falon Dad suna hira,ya samesu da maganar auran Sa'eeda kuma yanaso inda halin nan da ?an kwanaki haka, Mom ce cikin dariya tace "Ooohi nii Ru?ayya jikanyar Dikko Auta aure yake so haka da wuri,kaida ada nake binka da zancen aure kana guduna amma yanzu da kanka ba aike ba kake cewa ayi maka aure a nan kusa,O'o'oooo ni jikanyar Dikko,Alhaji kace wani abu" Dad dake dariyar shirman Sadam ya ce "A'aaah su Autan Momy aure akeso da wuri haka,a gaskiya ?ata ta ruWa Autan Mom dayawa" Dariya suka ?ara tintsirewa dashi ganin yadda yayi tu?u?u da fuska kamar mai shirin kuka kamar ba miskilin da kuka sani ba idan yana waje,amma a wurin iyayensa ji yake kamar yaron goye,cikin shagwaSa Sadam ya ce "Umm umm Dad dariya kukemin ko,Allah da gaske nake,a Waura mana auran ko nan da 2weeks coming ai yayi haka" "Eh lallai Sadam wato nan da 2weeks kamar an gaji da ita ne aka ce maka,to bari gaji saita kammala school Winta complete kafin a Waura muku aure tunda semester daya ya rage mata" cewar Mom Zaro idanu yayi waje jin ance sai ta kammala school Winta complete anya zai iya jira har wannan lokacin kuwa,a yadda yake tsananin sonta da ?aunarta wanda kullum wutar so da kaunarta ?ara ruruwa take a cikin zuciyarsa,tabb da sake wallahi. Tashi yayi tare dayi musu sallama yabar falon zuwa part Winsa, yana shiga ya kira wayar Sa'eeda don ya samu haWin kanta,bugu Waya-biyu a na ukun tayi picking tare da sallama cikin sassanyar muryarta mai daWin sauraro "Assalamu Alaika Ya Sadam" "Wa'ailikissalam my darling star" Rufe fuskarta tayi kamar yana kallonta ita nan taji kunya "Ya kike,ya kuma school Win hope everything is going normal" "Eh Alhamdulillah Ya Sadam" "Wai ba nace ki daina kirana da Ya Sadam ba" "Ka faWa,to ni bansan wani suna zan dinga kiranka dashi ba" "Nema yanzun nan ina jinki Sa'eedar Autan Momy" ?ara rufe fuskarta tayi,sai kuma tace "Na kiraka da my Happiness" "Ummm it sound very usual,nemo wani don wannan mutane sun sanshi,ki tuno Hajiyata" (Jama'ar Annabi Sadam da alama yasan sirrin lobayya=??=??=??) ?an tunani Sa'eeda tayi sai can ta ce "In kiraka da My Sadauki" "Woooow! Excellent! Great! Sunan yamin sosai haba ko kefa amma kullum Ya Sadam Ya Sadam" Dariya tayi jin yadda yake kwaikwayar maganarta,harda lakwasa murya,katse mata maganar yayi da cewa "My Darling Star kin mamaye ko'ina a jikina,jijiyoyina da gabSaina duk kin mamaye,ina matukar so da ?aunar Sa'eeda" "My Sadauki duk ni kaWai haka" "Eh mana Sa'eeda,saboda kefa na fara jin wa?okin hausa na soyayya musamman wa?o?in Umar.M.Sharif,kinsan yasan ilimin soyayya" "Laaaah!!? To rairomin naji My Lifeline" "Wayyo daWi wani sabon suna da Wimi-Wiminsa *My Lifeline* great my Sa'eedatyyy yanzu saiki shirya jin wa?ar" "Ina saurare" Saida yayi gyaran murya kafin ya fara rairo wa?ar kamar haka *"Kin sace zuciyata!!! Wayyo kin mallaketa!!! Kinsa inata sonta!!! Dubeni na jigata!!! Zanso kibanita ta!!! Inje in mallaketa!!! Inda za kijji abinda nake ji a cikin zuciya!!! Da ba ko shakka ni nasan da kin tausaya!!! Karda nayo jinya!!! Kibani soyayya!!! Sani akan hanya!!! Kiji daniiii!!! "* "Wooooow!!! A gaskiya kamafi Umar.M.shariff Win iya wa?a" "Da gaske Sa'eedatyyy" "Eh wallahi" "Naji dadi kuwa,yanzu mu buWe wata chapter my Darling Star" "To ina sauraranta? my Lifeline" "A gaskiya bazan Soye miki ba Sa'eeda, inason ayi auran mu da wuri,in yaso sai ki kammala school Winki a gidana,ko ya kika ce" Shiru ta Wanyi kamar baza tayi magana ba,har Sadam ya fara hello! Hello! sai can ta dawo cikin hankalinta tare da cewa "My Sadauki mai zai hana kabari bayan na kammala school sai a Waura mana auran inyaso sai nayi service a Wakinka,nagana hakan yafi ai" "Ohhhh kema bakinku Waya dasu Mom ko,Sa'eeda na ?agara naga na aureki,saboda kullum sonki da ?aunarki ?ara mamaye ko'ina na jikina yake,ni wallahi in don tani ne,a daura mana aure nan da 2weeks coming" "Ya Sadam in 2weeks coming tabb,to karatun fa" "Saiki kammala shi a gidana" "Kai my Lifeline kamar yarda Mom suka ce kabari after my school,i think is more better,kaji nima ai ina kaunarka sosai my Sadauki" Haka suka cigaba da hirarsu ta soyayya sai wurin 11:12pm suka yanke kira tare da kwanciya. A bangaren Umman Sa'eeda yanzu hankalinta a kwance yake, bata aikin komai sai kallon television da kwanciya,tayi Sul-Sul da ita,haskenta ya kara bayyana,gashi kullum sai sunyi waya da sanyin idaniyarta Sa'eeda,kullum Sa'eeda cikin ce mata take suna yin signout zatazo Kebbi hutu.Haka rayuwar? Umman Sa'eeda a Kebbi ta cigaba da tafiya cikin walwala da nishaWi,har mantawa take da rayuwar da tayi a baya,kuma koda Uncle Hassan ya tuntuSi maganar mijinta ya take gani,ce mishi tayi ya kyaleshi sai ya dawo cikin hayyacinshi domin yanzu an riga da an mallakeshi.Wannan Kenan ? ? ? ? @@@@@@@@@@@@@ *ABUJA* A Sangaren Haj. Zulfa'u lamari dai ?ara gaba yake domin ko abinci bata ci sai irin na karnuka,duka familin Haj. Zulfa'u suka tattaru a Abujan har dasu Fadila ma tazo Abujan,saboda rashin lafiyar Haj.Zulfa'u,an fito da ita daga wannan dakin zuwa can bedroom Winta tare da WadWaureta saboda kaima mutane cizo take tana haushi,sanda Fadila tazo ba karamin kuka tayi ba tare da tsoro saboda halin da ta same lovely grannynta mai sonta. Family doctor Winsu suka kira akan yazo ya dubata amma koda yazo ya dubata sai ya ce lafiyarta lau,shi baiga abinda ke damunta ba,hasalima tama fishi cikakkiyar lafiya inda za'a dubashi,saidai ya basu shawarar a aikata Psychiartry ko matsalar daga ?wa?walwa ne,haka suka bi shawararsa,nan take da nufa da ita wata babbabar asibitin kuWi na ?wa?walwa,nan ba basu dace ba saboda likitoci kusan uku ne ?wararru suka du?ufa akanta don ganin meke damunta amma ?wa?walwarta lafiya kalau take babu wata matsala,wani daga cikin likitocin ne ya ce su gwada maganin gargajiya ko zasu dace.haka suka fito daga asibitin da ita akan kujerar guragu wanda jikanta ne yake turata sai faman mutsu-mutsu take tanason ta ?wace gashi,an rufe bakinta saboda kukan karnukan da take kar ta tara musu jama'ah,suna cikin tafiyar har zun fito daga asibitin zuwa harabar asibitin sai da wani mutum da police dog Winsa gabjeje dashi yazo wucewa sai idanun karen dana Haj. Zulfa'u suka sar?afe dana junansu, ai tuni ta fizge daga daurin da aka mata tana rarrafe tare da haushi,shima karan mutumin fizge kacan da ake rike dashi yayi? tare da gudu zuwa inda Haj. Zulfa'u take yana haushi................. *Mu haWu a pages na gaba my Esteem Fans '? '? '?=?C?=?C?=?C?=?C?* *Ali yaga Ali,ga karan asali ga karya Haj. Zulfa'u koya zata Sarke???*..... *su Sadam wannan wa?a haka,shin iyayensa zasu yadda ayi auransu kafin Sa'eeda ta kammala makaranta ko kuwa???*...... *Wata Sabuwa inji ?an caca,Malam Sauban sai yanzu aka tuno da haihuwa,shin wani irin hauka zai Sallowa matansa???*..... *Umma Kande har yanzu baki tuba ba,da alama sai ishara ta saula akanki kenan,koya zata kaya a next pages???*.... *Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa=?C?=?C?=?C?,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai? ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions

Chapter 21 of 31