Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sumame kimanin su arba'in sanye da jajayen tufafi sun dako tsalle a sama sun kewayeshi.Su duka sai suka zare takubbansu suka ja tunga cikin shirin afka masa.Tunda Barde Ruhaisu yazo duniya bai taba ganin ZARATAN DAKARU masu kwarjini da kirar SADAUKAI ba irin wadannan.Nan take jikinsa ya bashi cewa yau fa ya gamu da gamonsa,amma da yake shima jarumi ne mai DAKAKKIYAR ZUCIYA ko kadan baiji tsoron yayi kokarin ceton kansa ba.Abinda ya aiyana aransa shine ko ba komai sai yayi iya bakin kokarinsa yaga cewa bai mutu shi kadai ba.A kalla yana son ya sami nasarar kashe koda mutum goma ne daga cikin wadannan zaratan jarumai da suka kawo masa MAMAYAR BAZATO.Lokacin da dakarun suka ga Ruhaisu ya gyara tsayuwarsa yana dafe kufen takobinsa ba tare daya nuna alamun tsoro ba ko tunanin guduwa,sai su ma suka sha jinin jikinsu,suka fahimci cewa lallai shima JAN IDO ne,kuma zai iya yin barna kafin a gama dashi.Hakan ne yasa dakarun basuyi saurin afka masa ba suka tsaya daga baya baya suna nazarinsa tukunna.Shi dai wannan wuri inda DAKARUN SUMAMEN suka ritsa Ruhaisu wajen gari ne sosai a tsakiyar daji inda babu gida gaba ko baya,kuma babu wani mahaluki dazai tsaya a wajen tsawon dakika goma batare daya firgita ba saboda waje ne mai yanayi na ban tsoro.Akwai dogayen bishiyoyi masu duhuwoyi gami da manyan tsaunika wanda dole ne baza a rasa mugayen dabbobin daji ba akansu.Ko yaushe wajen tsit yake tamkar babu wata halitta mai rai a wajen,kai da gani kasan cewa ba za'a rasa mugayen MUTANEN BOYE ba a wajen.Ana cikin wannan hali ne sai tsulum dakarun sumamen sukaga wani Badakaren a cikin shigar bakaken kaya rike da takobi ya duro tsakiyarsu daga can sama daga kan wata doguwar bishiya ya tsaya daf da Ruhaisu suka hada baya alamar ce Ruhaisu ya kawowa dauki.Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen yabaiwa sauran yan uwansa inkiya suka afkawa su Ruhaisu.Nanfa aka ruguntsume da azababben masifaffen yaki mai matukar tayar da hankali da muni.Ana fara yin wannan gumurzu ne kowa ya san cewa KARO DA KARO sai RAGO!Kamar yadda dakarun sumamen suke da KARFIN DAMTSE da iya yaki,zafin nama da bakin naci,haka Ruhaisu ma da mai bakaken kayan nan suke dashi,don haka saida aka shafe sa'a biyu da rabi ana dauki ba dadi,in banda karar haduwar takubba gami da sautin naushin jiki babu abinda kunne yakeji.Gashi dai an kasa koda lakutar jikin mutum daya a GUMURZUN bare a fitar masa da JINI mai yawa,amma kuma ana naushin juna yadda yakamata kuma ana shanye naushin sai kace jikin kowa bana jini da tsoka bane.Duk wanda ka duba saidai kaga hancinsa da bakinsa na yoyon jini.Koda shugaban sakarun sumamen yaga an bata wannan lokaci mai tsawo haka ba tare da sun sami wata nasara ba saiya fusata ainun ya bayar da wata inkiya.Take dakarun sumamen suka ja da baya su duka alokaci guda suka zaro wadansu adduna guda dai dai wato ya zamana cewa kowannasu na rike da makamai biyu a jikinsa ga TAKOBI ga kuma ADDA.Koda ganin haka sai wannan badakare mai bakaken tufafi yai wuf ya zaro wadansu Wukake guda biyu a cikin jikinsa ya mikawa Ruhaisu guda ya karba,suma suka dubi juna sukayi wata inkiya iri daya.Koda Ruhaisu yaga sunyi inkiya iri daya shi da wannan badakare mai bakaken kaya sai zuciyarsa ta buga da karfi kuma tsoro ya shigeshi.Ba komai ne yasa masa wannan tsoro ba face ya gane cewa ba wani bane wannan badakare mai bakaken kaya face SARKI SAILUR.Take Ruhaisu ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,saboda ne sarki yake siyar da rayuwarsa don ceton tawa rayuwar?Ai wannan ba karamin ganganci bane a matsayinsa na sarki yayi haka kuma idan wani abu ya sameshi nima na shiga wani bala'in.Yana cikin wannan tunani ne dakarun sumamen suka sake afko musu aka sake ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki a karo na biyu wanda yafi na farko tashin hankali da bala'i domin wannan karon wani irin sabon salon yaki dakarun sukazo dashi ya zamana cewa sun hada da tsalle tsalle da kwance kwance suna yawo a saman su Ruhaisu da kasansu suna kai musu hari ta ko ina.Faruwar hakan keda wuya kuwa sai suka fara ruda sarki Sailur da Ruhaisu nan take suka sami nasarar yankar kowannansu sau uku uku,jini yai tsartuwa daga jikinsu suka kurma ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da suka ji.Nan take jiri ya kwashi Ruhaisu ya durkushe kasa yana mai cake takobinsa cikin kasa don kare kansa daga faduwa.Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen ya dako tsalle sama cikin shammace da zafin nama ya daga makaman nasa biyu sama da nufin ya fille masa kai.Koda Sarki Sailur yaga abinda ke shirin afkuwa gashi yana yaki da sauran dakarun sumamen shi kadai ya hanasu kusantar Ruhaisu sai ya daka tsalle sama yayi wata irin katantanwa da kafafunsa a tsakiya dakarun sumamen ya tarwatsa su kuma ya kare saran da shugaban dakarun sumamen ya kawowa Ruhaisu a gadon bayansa.Taka takobin da Addar suka datsa bayan sarki Sailur jini yai feshi a lokacin da sarki sailur ya kurma uban ihu kuma ya fadi kasa tim a sume.Koda Ruhaisu yaga abinda ya faru ga Sarki sai ya kurma ihun daya ninka na sarki Sailur sau goma kamar MAHAUKACIN ZAKI ya faso gari.Take gaba dayan dakarun sumamen suka firgita suka ja da baya.Shi kuwa Ruhaisu zuciyarsa ce ta kekashe ga barin jin dukkan tsoro da kasala saboda tafarfasa data kamayi kamar zata kone saboda fishi bisa ganin halin da sarki ya shiga,kawai sai gani akayi Ruhaisu ya daka tsalle sama tamkar daga cikin BAKA aka harboshi ya sare kan shugaban na su kuma ya soka masa wuka a tsakiyar kirjinsa ta fullo ta gadon bayansa.Take gangar jikin shugaban dakarun sumamen ta sulale kasa matacciya.Shi kansa Jarumi Ruhaisu yayi matukar mamakin yadda akayiyayi wannan gagarumar BAJINTA da JARUMTAKA.Koda sauran dakarun sumamen suka ga yadda Ruhaisu yayi da abin dogaronsu,wato shugaban nasu sai suka firgice suka zubar da makamansu suka cika wandunansu da iska.Kafin kace wani abu babu dayansu a kusa.A sannan ne Ruhaisu ya fashe da kuka ya fara dinke raunikan dake gadon bayansarki sailur cikin razana da dimauta yana ta fama rusa kuka domin a lokacin ma gani yake kamar tuni sarki ya dade da mutuwa.Bayan ya gama dinke masa raunikan ne yaga har a sannan jini bai daina zuba daga cikin raunikan,al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya ruga da gudu izuwa cikin daji ya samo wadansu saiwoyin bishiyoyi yazo ya dakesu ya shafe raunin dasu.A sannan ne jinin ya daina zuba,har izuwa wannan lokaci Ruhaisu bai daina kuka ba saboda ko kadan babu alamar numfashi akan kirjin sarki Sailur,kuma babu inda yake motsi a jikinsa.A daidai wannan lokaci ne Ruhaisu ya fara sakar zuci wata zuciyar tace dashi menene amfanin rayuwarka a duniya tunda ka rasa wannan BABBAN MASOYI wanda baka da kamarsa a duniya.Ai gwara kaima ka kashe kanka tunda idan ma ka dauki gawarsa ka kaita cikin gari babu yadda za'ayi ka tsira daga zargin cewa kaine ka kasheshi.Koda gama aiyana hakan sai Ruhaisu ya sake fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki har izuwa lokaci mai dan tsawo.Daga can kuma saiya daga takobinsa sama da nufin ya cakata a cikinsa ya kashe kansa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga sarki sailur yayi wuf ya taso zaune ya rike hannunsa kuma ya budi baki da kyar cikin matukar karfin hali yace,dakai ka mutu gwara ni na mutu kai ka rayu saboda indai ban samu haihuwa ba kai nakeso ka gajeni.Har yau har gobe wannan shine babban BURIN ZUCIYATA.Koda sarki Sailur yazo nan a zancensa sai Ruhaisu ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki bisa ganin cewa bai mutu ba.Kafin sarki Sailur ya sake budar baki yace da Ruhaisu wani abu sai Ruhaisu yayi wuf ya goyashi a bayansa ya falfala da azababben gudu izuwa hanyar dazata kaisu cikin gari.Nanfa ya rinka yin wani irin gudu na ban al'ajabi yana gifta bishiyoyi tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.Cikin kankanin lokaci suka iso cikin gari suka karasa fada,tun a kofar gidan sarautar Ruhaisu ya kwallawa likitan sarki Sailur kira don haka kafin su karasa turakar sarki sailur tuni anje an kirawo likitan ya karaso da gudu izuwa cikin turakar.Nandai Likitan ya shiga aikinsa ya baiwa sarki sailur wadansu magunguna wajen kala uku yasha kuma ya shafa wani maganin akan rauninsa.Faruwar hakan keda wuya sai barci ya sace sarki.Saida sarki Sailur ya shafe sati uku a kwance yana jinyar wannan rauni na gadon bayansa sannan ya warke sumul,tamkar bai taba samun wani rauni ba ma.Sa'ar dayayi itace saran da akayi masa bai taba kashi ba,tsokar nama ce kawai ta dare.Wannan shine takaitaccen tarihin Barde Ruhaisu. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ BAYAN SARKI SAILUR da Barde Ruhaisu sun dan jima a tsaye rungume da junansu suna kuka sai sarki sailur ya janye jikinsa daga cikin na Ruhaisu ya dubeshi a nutse yace,yakai dana kayi sani cewa ba komai nake so kayi mini ba face ka yiwa surukata Yazarina rakiya izuwa tafiya neman mijinta dan'uwanka Yarima Lubainu.Ka sani cewa tuni mun gama shirya komai ni da mahaifinta Abu Yazarina saboda haka a cikin wannan dare nake so kayi wannan tafiya kuma zan hada ka da wadansu amintattun zakwakuran dakaru nawa kamar mutum dari kacal wadanda zasu taimaka maka.Ina son kuyi bad-da-kama a cikin daren yau zaku bar garin nan domin a samu cikakken sirri.Koda Sarki Sailur yazo nan a zancensa sai farinciki ya lullube barde Ruhaisu ya dubi sarki sailur fuskarsa cike da annuri yace,yakai Abbana kayi sani cewa a iya tsawon rayuwata ban taba jin farin ciki ba a raina irin na yau saboda yaune ranar farko daka taba neman wata alfarma a wajena.Tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana bantaba saka maka ba da abin alherin daka ke yi mini tsawon shekaru,amma yau gashi ka bani damar dazan iya kwatantawa.Na rantse da darajar kauna da soyayyar dake tsakaninmu dakai zan sallama rayuwata don kare ta surukarka,kuma duk inda dan'uwa na Yarima Lubainu yake a cikin duniya sai na damka Yazarina a hannunsa cikin koshin lafiya kuma a raye.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake baibaye sarki sailur ya rungume barde Ruhaisu a karo na biyu yace,ina alfahari dakai yakai yayan Lubainu,kuma nasan cewa saika cika wannan aiki dana baka bisa amana.Ni yanzu babbar masifar dazan fuskanta itace ta kewarka a yayin daka yi wannan tafiya.Ka tuna cewa tun daga ranar dana daukoka a gidan sarautar Birnin Darnis kawo izuwa yau bamu taba rabuwa daidai da rana daya ba,yanzu gashi zakayi wannan tafiya mai mugun hadari wacce bansan ranar dawowarka ba.Koda sarki sailur yazo nan a zancensa sai ya sake kankame barde Ruhaisu a kirjinsa ya fashe da matsanancin kuka.Al'amarin daya karya zuciyar barde Ruhaisu kenan,shima ya fara yin sabon kukan.Tabbas irin son da sarki Sailur yake yiwa Barde Ruhaisu har yafi wanda yake yiwa Yarima Lubainu duk da ya san cewa barde Ruhaisu ba dansa bane na cikinsa,'da ne na TSUNTUWA wanda ma baisan asalinsa ba.Tsananun tausayin barde Ruhaisu da yakeyi be yasa yake kaunarsa fiye da Yarima Lubainu.Sarki Sailur bai taba fifitashi ba kan Ruhaisu,kuma kowanne taro sarki zai tura wakilci bai taba tura Yarima Lubainu ba saidai ya tura barde Ruhaisu.Kai saida takai cewa Yarima Lubainu ya fara nuna kishinsa a fili akan Barde Ruhaisu saboda ganin yadda sarki ke fifitashi akansa.Daga ranar da sarki sailur ya baiwa Yarima Lubainu labarin haduwarsu tun yana dan shekara goma kawo izuwa girmansa shike nan sai Yarima Lubainu ya kaunaci barde Ruhaisu fiye da yadda ma sarki ke sonsa,kuma suka zamo manyan abokai yan'uwa kuma aminan da basa son rabuwa.A ranar da Yarima Lubainu zaiyi wannan tafiya saida suka shafe rabin sa'a cif a tsaye rungume da junansu suna kuka na bakin cikin rabuwa,da kyar suka saki juna Yarima Lubainu ya tafi,domin a cikin zukatansu ji suke kamar dama can sun kasance yan'uwan juna na jini.Bayan bardw Ruhaisu da sarki Sailur sun dan sake jimawa a kankame da juna sai Ruhaisu ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna yana mai share hawayensa yace,yakai Abbana kayi sani cewa akwai bukatar naje na kammala dukkan shirye shiryena yanzu tunda bani da isasshen lokaci kuma nayi bankwana da matata.Sarki sailur ya gyada kai a lokacin da hawaye ya subuto masa yace wannan gaskiya ne,kuma ka nema mini gafara a wajen surukata matar taka tunda na rabata dakai a lokacin datafi koyaushe kewarka.Na sani cewa bata da burin dayafi ta haihu kana nan ku raini abinda kuka haifa tare domin babu takaicin dayafi na rabuwa da IYAYE tun mutum yana karami.Gashi kai ka rabu da iyayenka a lokacin ma baka sansu ba,amma na sani kuma naji a jikina cewa tarihi bazai maimaita kansa akanka ba,lallai kai zaka dawo gida a raye cikin koshin lafiya tun kafin 'danka ko 'yarka tayi wayo.Koda jin haka sai fuskar Barde Ruhaisu ta fadada da murmushi ya yiwa sarki Sailur godiya sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar ba tare daya yarda ya sake waigowa ba.Take Barde Ruhaisu ya nufi izuwa gidansa. 2 mins · PublicALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part D DA ISAR BARDE RUHAISU gidansa sai ya iske matarsa ZASMIN tsaye a falo dauke da tsohon juna biyu tana kai kawo cikin alamun damuwa.koda ta hango shigowar Barde Ruhaisu sai ta taho gareshi fuskarsa cike da annuri suka rungume,amma yayin data janye jikinta daga nasa taga idanunsa sunyi jajir alamar cewa yasha kuka sai zuciyarta ta buga da karfi ta dubeshi cikin alamun tsananin tashi hankali tace,gaya min gaskiya yakai mijina yau kuma menene ya faru a fada?Lallai ba ka taba dawowa gida a cikin irin wannan yanayin ba.Shin wani makusancinka ne ya mutu ko kuwa wani abu ne ya sami sarki?Tabbas yadda na sanka da DAKAKKIYAR ZUCIYA in ba wadannan abubuwa ba babu abinda zai saka kuka.Koda jin wannan tambaya sai Barde Ruhaisu ya suri Zasmin ya dagata sama yana mai rungumeta a kirjinsa yayi juyi da ita don haka bata san sa'adda ta kama kyalkyala dariya ba.A hankali Ruhaisu yaje ya shimfide Zasmin akan gado ya kama wasa da gashin kanta suna kallon juna cikin murmushi.A sannan ne ya kwashe labarin dukkan abinda ya faru tsakaninsa da sarki Sailur ya zayyane mata.Koda gama bata wannan labari sai yaga ta kyalkyale da dariya,amma kuma hawaye na zuba a cikin idanunta.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan kuma ya kadu,cikin mamaki yace,yake matata ina dalilin wannan dariya taki gami da kuka a lokaci guda.?Sa'adda Zasmin taji wannan tambaya sai ta nutsu ta dubeshi da kyau tace,ya kai mijina abin begena dare da rana,kayi sani cewa ba komai ne ya sakani wannan kuka ba face yau ne ranar farko da zan fara rabuwa dakai tun daga lokacin aurenmu.Alhinin rabuwar tamu ne kawai ya sakani kuka,amma ina ji a jikina cewa tabbas zaka dawo gareni.Abinda ya sani nake yin wannan dariya kuwa ba komai bane face tsananin tayaka farincikin samun damar dazaka iya sakawa sarki kadan daga cikin irin abubuwan alherin dayayi maka.Kash!In badon ina dauke da wannan TSOHON CIKI ba da lallai tare dani za'ayi wannan tafiya,sabida inason na haife maka danka a lokacin da kake cikin GWAGWARMAYA ko shima dan naka ya sami tabarraki irin naka.Koda Zasmin tazo nan a jawabinta sai farin ciki ya lullube Ruhaisu ya rungumeta ya kama sumbatarta yana sa mata albarka.Nan take Zasmin ta mike tsaye da kanta ta fara debo kayan Ruhaisu tana zuba su cikin jakar guzuri don kammala shirye shiryen tafiya.Al'amarin daya kara bashi mamaki kenan,kuma yaji ya kamu da tsananin sonta fiye da koyaushe.Cikin kankanin lokaci ta gama shirya masa dukkan kayansa sannan suka yi bankwana ya saba jakarsa a kafadarsa bayan yayi shigar bad-da-kama irin ta fatake sannan ya koma can kofar gidan sarautar.A wannan lokaco tuni Sarki Sailur ya gama shirya komai,domin a samu cikakken shiri dangane da wannan tafiya Tasu Ruhaisu saida aka sauya masu gadin kafor gidan sarautar gaba daya a cikin daren aka zuba wadanda ya tabbatar da cewa masoyansa ne na gani kasheni,kuma ya gargadesu akan cewa duk abinda suka gani ko sukaji a wannan dare su barshi a cikin zukatansu kada su kuskura su sanar da wani.D isowar Barde Ruhaisu bakin kofar gidan sarautar sai ya iske sarki Sailur tsaye a gaban wadansu dakaru guda dari suna bisa kan dawakai dauke da hajoji da makaman yaki alamar cewa su fatake ne.Tun daga nesa Barde Ruhaisu ya fara nazarin fuskokin wadannan dakaru,koda ya shaidasu sai ya kamu da tsananin farinciki da mamaki.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin cewa gaba daya sa'anninsa ne kuma manyan abokansa wadanda ya aminta dasu a cikin dakarun yakin kasar.Koda sarki Sailur ya hango tahowar Barde Ruhaisu sai ya tafi gareshi cikin murna yace,yakai dana an gama shirin komai dama kai kadai ake jira saboda haka sai kayi haramar tafiya.Koda jin haka sai Ruhaisu ya kama hannayen sarki guda biyu ya sumbacesu kawai sai ya sake rungume junansu suka dan jima a kankame da juna.Al'amarin daya karya zukatan sauran dakarin kenan suka kamu da tausayinsu saboda sunsan irin shakuwar dake tsakaninsu.Nandai Barde Ruhaisu da Sarki Sailur suka rabu bisa dole sunayin kwallah badon suna so ba,aka kawowa Barde Ruhaisu wani farin INGARMAN DOKI wanda ya fita dabam da dukkan dawakan abokan nasa ya kama ya hau.Take ya kada linzamin dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ba tare daya yarda ya sake waigowa ba.Ai kuwa sai sauran dakarun guda dari suka rufa masa baya da sauri shi kuwa sarki Sailur sai ya bisu da kallo kawai,bai bar wajen ba har saida suka kule ya zamana cewa ko kurarsu baya iya hangowa,sannan ya juya ya koma izuwa cikin gidan sarautar yana mai zubar da hawaye. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ A CAN BIRNIN Sarki Alkasu kuwa tun da aka gama wannan gasa ta neman Auren YAZARINA tsakanin YARIMA LUBAINU da YARIMA MANGUL suka dawo gida sai sarki Alkas ya sanya hijabi tsakaninsa da Yarima Mangul.Suna dawowa gida yayi masa korar kare daga fada kuma ya gaya masa cewa idan ya sake sa kafarsa a cikin harabar gidan sarautarsa zai yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku.Koda jin wannan batu sai mamaki da bakin ciki ya turnuke Yarima Mangul ya dubi dungulmin hannunsa a lokacin da hawaye yake zubo masa sannan ya dubi Sarki Alkas yace saboda mezaka kyamaceni alokacin dana fi bukatarka?Ka dubi yadda na zamo musaki ka tuna cewa nine fa kadai danka guda wanda zai gaji karagarka?Ka tuno da irin tsananin son daka keyi min saboda me yau zaka bari zuciyarka ta rinjayi soyayyar danka?Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa tuni sarki Alkas ya daka masa tsawa a lokacin da shima hawaye ya zubo masa ya dubeshi yace,karka sake kirana da matsayin ubanka domin tuni nasaka TAKOBI na datse wannan alaka dake tsakaninmu kamar yadda ka datse wacce ke tsakanina da Abokaina kuma manyan masoyana sarki Sailur da Attajiri Abu Yazarina.Ka sani cewa ka jefa wadannan masoya nawa a cikin bakin cikin da har abada babu abinda zai gusar dashi tunda ka rana Yarima Lubainu da lafiyarsa ka sanya masa cutar da bata da magani kuma a sanadiyyar hakan yayi rabuwar doke da masoyiyar tasa rabuwar da ba lallai bane su sake saduwa ba.Kaga keknan ka raba iyaye da 'ya'yansu kuma ka raba MASOYA.Ka sain cewa a yau idan na rasaka a gobe daya daga cikin matana zata iya sake haifa mini wani dan,amma aminaina daka rabamu dasu bazan taba samu kamarsu ba.Yarima ka cuceni cutar da har abada ba zan iya yafe maka ba.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya zube kasa a gaban sarki Alkas ya fashe da kuka kuma ya kama tuba yana rokon gafara.Maimakon sarki Alkas yaji tausayinsa sai ya dubi wadansu dakarunsa su shida dake tsaye a gefe daya yace dasu su kama Yarima Mangul su fitar dashi daga cikin gidan sarautar kuma a kulle kofar gidan.Nan take kuwa dakarun suka kama Yarima Mangul Suka fitar dashi daga cikin gidan Sarautar da karfin tsiya yana kuka da ihu gami da turjewa kuma yana kwallawa sarki Alkas kira mma sarki Alkas ko waigowa baiyi ba bare ya dubesi ya tausaya masa.Ana fitowa da Yarima Mangul daga cikin gidan sarautar sai akayi wurgi dashi a wulakance tamkar bai kasance dan sarki ba,aka janyo kofar gidan sarautar aka kulleta bam,aka zuba mata sakatu.Cikin tsananin bakin ciki da takaici Yarima Mangul ya mike tsaye yana kuma.Nan taje yaji ya tsani sarki Alkas yadda ya tsani mutuwarsa.Kawai sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta iska ta dauki sautin dariyarsa takai har izuwa kunnen sarki Alkas gami da muryarsa yana mai cewa yakai Abbana ka saurari ranar da zan dawo gidan nan nine zan zama sanadin AJALINKA kuma saina hau kan KARAGARKA.Koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke sarki Alkas zuciyarsa ta kama tafarfasa.Har ya zare takobinsa da nufin ya juya da baya da gudu yaje ya kashe Yarima Mangul sai zuciyarsa ta daka masa tsawa tace dashi so kake kabarwa kanka abin gori a wannan masarauta?Ka kyale Yarima da Halinsa ai duniya makarantace zata koya masa darasi.Daga wannan rana Yarima Mangul ya bar cikin birninsu gaba daya ya koma daji da zama saboda bakin ciki.A sanadinyyar haka ne ya hada kai da 'yan TAWAYE gami da 'YAN FASHI suka fara shirye shiryen yadda zasu kawar da mulkin sarki Alkas ya dane KARAGAR MULKINSA,amma kullum idan ya dubi iya yawansu da iyakar makaman dasuka tanada sai takaici ya kamashi saboda yasan cewa ko kasa daya cikin kaso goma na shirin sarki Alkas basu kai ba don haka dole ne ya cigaba da hakurin jiran lokaci.A haka dai Yarima Mangul ya cigaba da jagorantar wannan runduna ta yan fashi da tawaye suka rinka kai harin SUMAME izuwa kauyukan dake sauran kasashen ketare suna kwaso mata,dukiya da kudi suna kamo bayi da karfin tsiya suna basu horon yaki domin kara yawan dakarunsu kuma suna siyan mugayen makaman yaki suna tarasu.Ana cikin wannan hali ne wata rana Yarima Mangul na zaune a cikin sansaninsu yana shan giya ga mata a gabansa suna ta fama tika rawa anayi musu kida saiga wani DAN LEKEN ASIRINSA ya rugo da gudu bisa kan doki.Da isowarsa kusa da Yarima Mangul sai ya tsaida dokinsa ya sauko kasa ya fadi a gaban Yarima Mangul yace ya shugabana ga wani AYARI can na BAKIN FATAKE kimanin su dari da doriya dauke da HAJAH mai tarin yawan gaske sun nufi hanyar dazata kaisu Birnin SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul yayi jifa da kwalbar giyar dake hannunsa ya mike tsaye zumbur cikin tsananin farin ciki yace,tabbas yau zamuyi babbar farauta mai inganci.Maza a kawo mini dokina da kayan yakina.Dakaru dubu daya kacal nakeson suyi min rakiya.Nan take kuwa cikin gaggawa aka kawowa Yarima Mangul kayan yakinsa ya sanya sannan ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu dakaru dubu suka rufa masa baya."Ashe wannan AYARI na fatake ba wasu bane face su Barde Ruhaisu wadanda suka fito neman Yarima Lubainu a cikin shiga ta bad- da- kama domin a sada Yazarina da Mijinta Yarima Lubainu. kuyi hakuri yau Ansamu delay din post hakan yafarune sbd bansamu time bahALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part E TUNDA WANNAN Ayari nasu Barde Ruhaisu suka baro birnin Zamrul sukayi ta ratsa dazuzzuka,kauyaka da kananan Birane basu fuskanci matsalar komai ba har tsawon kwana tara.Kuma a duk tsawon wadannnan kwanaki Barde Ruhaisu bai taba yarda ya gusa ba daga kusa da Yazarina ba wacce koyaushe fukskarta a rufe take cikin mayafi idanunta kadai ake gani,kuma shigar datayi mutum bazai iya gane cewa ba macece ko namiji.Ko dare ne yayi har tayi bacci Barde Ruhaisu yana tsaye a kusa da ita kuma ya saka Dakaru sun kewaye yankin wajen da take.Kai ko wani kyakkyawan motsi yaji a kusa da wajen da suke sai ya duba ya tabbatar da cewar babu abu wanda zai kawo mata barazana.A tsawon wadannan kwanaki da suka shafe suna tafiya ko sannu babu wanda ya yiwa wania tsakanin Barde Ruhaisu da Yazarina ma'ana basuyi magana da junansu ba.A ranar kwana na taran ne da yammaci sakaliya suka yada zango a bakin wata korama domin su dan huta kuma dawakansu su sha ruwa.Bayan an tsaya kowa ya sauka daga kan Dokinsa,dakaru sun kewaye wajen don tabbatar da tsaro,Yazarina ta zauna a gefe daya ta bude jakar guzurinta ta dauko nama yana ci,shi kuma barde Ruhaisu yana tsaye a bayanta ya zare takobinsa yana wasata akan dutse sai kawai suka jiyo sukuwar dawakaia daga yamma,gabas,kudu da Arewa.Sannan kuma sai suka jiyo kururuwar mazaje mai ban tsoro amma saboda su Ruhaisu sun kasance ZARATAN JARUMAI masu dakakkiyar zuciya ko gezau basuyi ba,kawai sai sukayi sauri suka zaro wadansu manyan garkuwoyi daga kan dawakansu saboda tsoron kada a fara kawo musu hari da harbin kibiya.Take kowannen badakare yacake garkuwarsa a gabansa sannan ya zare takobinsa,kowa ya tsaya a inda yake ba tare da wata razana ba.Yazarina ce kadai ta firgita a lokacin data hango wadansu dakarun sumame su da yawa sun durfafosu a guje bisa dawakai rike da makamai tsirara suna ihu da kururuwa.Har ta yunkura zata mike tsaye a dimauce sai Barde Ruhaisu yayi wuf ya kamo hannunta ya zaunar da ita kasa.A karon farko ya dubeta yace,ki gafarceni ya shugabata idan kika matsa daga nan koda taku daya ne halaka zakiyi.Abinda nakeso dake shine komai RINTSI DA TSANANI kada ki gusa daga kusa dani,koda kuwa kinga an karar da dukkan dakaruna saura ni kadai jal na rage a raye!Lallai ki kiyaye wannan umarni dana baki muuddin kina son ki sake saduwa da masoyinki dan'uwana Yarima Lubainu.Koda Yazarina taji wannan batu sai ta gyada kai tana nuna masa alamun cewa lallai zata kiyaye wannan umarni nasa.Koda jin haka sai Ruhaisu yai sauri ya rufe fuskarsa da rawani suma sauan dakarun nasa sai sukayi koyi dashi.Abinda ya daurewa Ruhaisu kai shine har dakarun sumamen suka iso daf dasu ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba amma basu harbo musu kibiyoyi ba.Da isowar dakarun sumamen sai sukayiwa su Ruhaisu KAWANYA suka yi cirko cirko bisa dawakansu.A sannan ne shugaban dakarun sumamen wanda dashi da dukkan yaran nasa sun rufe fuskokinsu sai ya sauko daga kan dokin sa ya karewa fataken kallo tsaf,sannan ya bushe da dariyar mugunta,lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubesu yace,ni da yarana mu dubu daya ne da daya,ku kuwa bakufi ku dari ba,abin kunya ne mu yakeku ta hanyar farar harbo muku kibiyoyi.To waishin kuma menene amfanin rufe fuskokinmu damu daku mukayi?Ai kawai kowa ya bude fuskarsa muyi GABA DA GABA fada da buya ai tsoro ne.Koda gama fadin hakan sai shugaban dakarun sumamen ya kwaye rawanin dake kan fuskarsa su Barde Ruhaisu sukayi arba dashi.Ba wani bane face Yarima Mangul dan sarki Alkas!!! Hannunsa na dama na rike da zabgegiyar takobi,ya saki daya dungumin hannun nasa.Koda Barde Ruhaisu yayi arba da Yarima Mangul sai shida dukkan dakarunsa suka kamu da tsananin mamaki gami da tsananin tsoro.Koda ganin haka sai barde Ruhaisu ya kwaye fuskarsa shima ya mike ya matso gaba kadan ya dubi Yarima Mangul yace,sau tari Jarumi yakan rufe fuskarsa saboda wata BABBAR HUJJA da manufa saboda haka mu bazamu bude fuskokinmu ba saidai mu gwabza daku a hakan.Kafin sannan kuma muna son mu san dalilin dayasa kuka kawo mana wannan hari na MAMAYAR BAZATO.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta sannan yace,ai shi dan fashi bashi da wata hujja takai hari face don ya kashe rayuka kuma ya kwashe dukiya.Koda yake nasan ka san ko ni waye tunda ni fitacce ne a wannan nahiya kuma ada ni ba dan fashi bane,amma a yanzu ni UNGULU ne dakan ZABO!Har yanzu ina nan akan matsayina na Yarima Mangul dan Sarki Alkas mai jiran Gado.Yakai wannan jarumi ka sani cewa zan iya yi muku adalci guda daya kai da dukkan jama'arka naki kasheku na karbe dukiyarku,amma sai idan zaku bude fuskokinku naga ko ku su waye?Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu ya tari numfashin Yarima Mangul yana mai daka masa tsawa yace,ba zamu taba bude fuskokinmu ba don cika umarninka kuma kaidin nan baka isa ka iya kashemu ba ko ka karbe dukiyarmu.Ina mai shawartarka daka janye jama'arka ku bar wannan wuri idan ba haka ba kuwa sai kayi nadamar kawo mana wannan hari.Idan ka kuskura ma sai na sake guntule maka daya lafiyayyan hannun naka!!Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya fusata ainun ya zare takobinsa kuma ya daka tsalle daga inda yake ya dira a gaban Barde Ruhaisu ya kawo masa wawan sara aka.Cikin bakin zafin nama barde Ruhaisu ya kare saran.Nanfa suka ruguntsume da azababben yaki,ya zamana cewa suna kaiwa Junansu SARA DA SUKA cikin tsananin bakin zafin nama,juriya da bajinta,sauran dakarun kuwa na kowanne bangare sai suka zuba ido suka zama yan kallo tunda ba'a basu umarnin suyi yaki ba. WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNAN AZABABBEN YAKI DA AKE KWABSAWA TSAKANIN YARIMA MANGUL DA BARDE RUHAISU? INA LABARIN YARIMA LUBAINU DA BAKON JARUMI DASU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DAKE CIKIN GIDAN BOKA DARBUSA? SHIN YARIMA LUBAINU ZAI CIKAWA ALJANA BADI'ATUL SARIRA ALKAWARIN DAYA DAUKAR MATA NA KWANCETA DAGA DAURIN DA BOKA DARBUSA YAYI MATA ITA KUMA TA TAIMAKA MASA? WANE NE BAKON JARUMI DA TARIHINSA? YAUSHE BAKON JARUMIN ZAI SAMU NASARAR YADA ADDININSA NA MUSULUNCI A NAHIYAR? SHIN YARIMA LUBAINU YANA SAMU LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI? YAUSHE YAZARINA ZATA SADU DA MASOYINTA YARIMA LUBAINU? WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI A TSAKANIN DUMBIN JAMA'AR DA SUKE NEMANSA? WANE IRIN MUGUN TANADI SU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ZASU YIWA BAKON JARUMI?. Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI littafi na Biyar (ALLON SIHIRI-5)don jin cigaban wannan kayataccen,kasaitaccen labari. 1 hr · PublicTARWATSA MAZA-1 TYPE E »«« Nidai a iya yawon da nayi bantaba shiga daji mai kwarjini da ban tsoro ba, tamkar dajin shajaril maurud. Ba komai ne yabawa dajin kwarjiniba, face wasu irin dogayen bishi yoyi gami da

Chapter 9 of 19