Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sarki Lubainu kuma tasake murtuke fuskarta tace. Ai ba'a sanin maci tuwo Sai miya takare! Idan har kana ganin zaka iya samun nasara akaina da karfin takobinta saika jarraba!!. A India babu kasa Anan ake gardamar kokawa!!! GA FILI GA MAI DOKI Mu zuba mugani!!! Tana gama fadin haka tasa hannu ta zare takobinta, Al'amarin dayayi matukar girgiza dakarun sarki Lubainu kenan suka kamu da tsananin mamaki kuma suka tausayawa wannan jarumar domin inda tsan tsananin iya yakin sarki Lubainu da batayi wannan ganaganciba duk da cewa sums basusan iya NATA yakinba. Koda yake makaho bayacewa ayi wasan jifa saiyaga hoge, Amma kuma ai bakin rijiya bawajen wasan makaho bane!!! Koda sarki Lubainu yaga irin dakewar wannan jarumar budurwa harms ta rigashi zare takobi Sai ya sake cika da mamakinta, kuma yaji ta Dada burgeshi Ainun,domin yanason mace mai zuciyar maza wacce yakeganin itace kadai zata iya dacewa da shi , Nan take sarki Lubainu ya sake ja da baya kamar taku biyar sannan yatsaya tsaf yazare tasa takobin yanamai bude hannayensa suka kurawa juna idanu shida ita har izuwa wani Dan lokaci. Kamar hadin Baku Sai duk su biyun suka Togo da gudu izuwa kan junansu sunamasu kartan kasa da takubbansu kaida gani kasan cewa idanu akayiwa wannan haduwar komai zai iya faruwa. Muhadu gobe in Allah yakaim . ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part F Koda yarage saura taku uku su hadu Sai suka daka tsalle sama suka kaiwa jujansu mugun hari. Shidai sarki Lubainu a wuya ya kaimata saran da nufin ya tsizge mata kai, ita kuma Sai takaimasa Sara a kafada da nufin ta zaftaremasa hannunsa na hagu. Cikin zafin nama kowannensu yakaucewa harin da aka kawomasa Amma Sai wani abun Al'ajabi yafaru a lokacin da suka duro a kasa a bayan junansu a tare. Abunda ya faru shine, sakaomakon da saran da sarki Lubainu yakaiwa jarumar wuya ko shafar jikinta baiyiba Amma Sai kaifin takofinsa ya tumke wani Jan kyalle da ta daure gashin kanta da shi, ya tsargeshi gida biyu ya fado kasa. Ita kuwa kwalar rigar da ke jikinsa ta yanke ta yanke tafadi kasa. Ita dai wannan rigar ta sarki Lubainu mai muguwar tsada domin ta zallar rigar Alhariri akayita gami da zaren danyen zinare, musamman yasa akaje birnin farisa aka dinkota. Koda sarki Lubainu yaga An lalata masa wannan Riga mai Daraja Sai ranshi ya baci Ainun. Itama jarumar dataga An yanke mata wannan Jan kyalle nata Sai tajuyo a fusace Ainun. Ashe wannan kyalle shine matsayinta na sarauniyar mafarauta a cikin gabilarsu. Cikin tsananin bakin zafin nama sarki Lubainu da wannan jarumar suka juyo a cikin fushi Sai suka juyo izuwa kan junansu suka ruguntsume da sabon masifeffen yaki yazamana cewa suna kaiwa junansu mugayen harehare. Nan fa karar haduwar takubbansu yacika dajin gaba daya, motsinsu da hare harensu ya haifar da tashin kura, kuma ya dugunzuma hankalin duk wani Abu dayake kusa. Domin hatta yaran sarki Lubainu Sai suka rinka ja da baya, wani lokacimma har buya sukeyi a bayan bishiyoyi kar tsautsayi ya hausu,Dan wata 'Yar karamar bishiya ma sarki Lubainu da jarumar Sara daya sukeyi mata ta fadi kasa,a lokacin da suke kaucewa harin junansu. Nanfa dajin gaba daya ya hautsine, tsuntsaye ma dake kan bishiyoyi babu shiri suka farayin yijira dole suna sauya sheka. Wannan tashin hankalin ne gami da karafkakiyar yakuba na sarki Lubainu da jarumar ne yakai izuwa kunnen 'yan uwan jarumar dake can gefe nesa kadan awani bangare a dajin, inda suke yada sansani. Adadin wadannan Ayari yakai na mutum dubu uku da sittin da biyu, kuma dukkajinsu suna karkashin wani mutum ne ma'abocin kwarjini da kamala gami da kira Da SADAUKANTAKA Amma girma yafara kamashi, domin ya haura shekara sittin a duniya, Ana kiransa da suna ZAHAR BIN AUDASI. Sadauki zahar shine mahaifin waccer yarinyar da take fafatawa da sarki Lubainu. Koda sadauki zahar yajuyo karar takuban 'yarsa saiya zabura yafito ya fito da sauri daga cikin tantinsa ya dubi gaba dayan dakarunsa wadanda suka kasance maza da mata, kuma dukkaninsu acikin shigar yaki suke irinta mafarauta yace, Ga Sarauniyarmu can tana gunurzu, kuzo muje mukai mata dauki tunda bamusan Adadin mutanen da take yaki dasuba, kunsani cewa 'yata daga nesa da sarki Lubainu yaga wannan gagarumar jarumtaka da jarumar tayi kuma ya kare mata kallo yaga irin tsananin kyawun da Allah yayi mata Sai yasake dimaucewa kuma nan take akaron farko a rayuwarsa yaji yakamu da tsananin son 'YA MACE!! Lokacin da wannan jarumar taga sarki Lubainu ya kura mata idanu kuma ta kare masa kallo taga yanayin shigarsa Sai tagane cewa mai mulki ne Dom haka Sai ta turbine fuska tacigaba da kallonsa kawai har ya iso daf da ita. Dazuwansa Sai ya dubeta a fusace ya daka mata tsawa yace, yake wannan bakuwar mafarauciya wacece ke har da zaki shigu jejin kasata kiyi farauta ba tare da izininaba? Ina sauran 'yan uwanki suke wadan sukamin mummunar barna haka kuka kwashe mana duk Amfanin cikin dazuzzukanmu?? Kisani cewa tunda na kamaki dolene Ku dawomana da dukkanin abunda kuka kwashe kokuma Ku biya da rayukanku tunda kun karya doka. Hatta wannan damisa da kika kashe yanzu dolene ki bani ita. Koda sarki Lubainu yazo nan a zancensa Sai kyakkyawar jarumar ta kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ta turbune fuskarta tace, Ai isace takesawa akarya dokar sarki! Munan daka gammu babu bangaren da bamuje ba a duniya munyi FARAUTA, Kuma kasa ko birni ko Alkaryar da muka zuwa muka nemi izinin wani Wanda mukashiga yankinsa"". Koda gama fadin haka Sai jarumar ta sunkuya tadau wannan damisar ta saba ta kafadarta taruga inda 'yan uwanta suke, kawai Sai sarki Lubainu ya daka tsalle sama dagakan dokinsa ya shallaketa, sarki Lubainu yana gana Ayyana hakan a ransa saiyaja da baya yadaina yakar jarumar kamar zaiyi saran da Amma saiya shammaci jarumar yaruga da gudu izuwa inda damisar take. Koda ganin haka Sai ita jarumar ta falfala da wannan azabebben gudu nata tabi bayansa, saigashi har tashi sama takeyi saboda tsananin gudun, Amma duk da hakan dakyar ta riski sarki Lubainu sukayi kafada da kafada, ahaka sukaci gaba da kaiwa junansu naushi domin akai daya kasa Amma abun yaki yiwuwa. Koda sukaga saura baifi taku biyarba su isa inda damisar take.Sai duk su biyun suka daka tsalle suka kaiwa damisar cafka da Hannu daya. Bisa rashin sa'a Sai sarki Lubainu ya damki wuyan damisar, ita kuma Sai ta cafko kafadar damisar. Koda kowannensu ya yaja iya karfinsa Sai damisar ta rabe gida biyu duk su biyun suka fadi rike da tsagin damisar. Kawai Sai yaran sarki Lubainu suka farayimusu tafi sakamakon ganin gagarumar jarumtakar da sukayi. A daidai wannan lokaci ne zugar su sadauki zahar ta karaso wajen a guje bisa dawakai sukayiwa su sarki Lubainu KAWANYA. Koda jarumar taga mahaifinta shima yaganta kwance a kas rike da tsagin damisa kuma Ga jini a hancinta da bakinta kuma yana diga Sai ya dubi dakarunsa yamusu inkiya. Take tadarun suka zaro kibiyoyi suka tana suka ta6e zasu sakarwa sarki Lubainu da yaransa harbi, Amma Sai jarumar tayi sauri yace ae ba'abokin gaba bane, wannan shine sarkin wannan birni da muke ciki"". Koda jin haka Sai sadauki zahar ya dubeta a fusace yace, idan ba abikin gaba ba to menene yasa ya yakeki harya lalata naman farautarki?"" Koda jin wannan tambaya Sai tayi murmushi tace, "' saboda munyi masa babbar barna mun kore duk dabbobi da tsuntsayen dake cikin dazuzzukan birninsa.. Yanada gaskia akan wannan Al'amari duk da cewa shi daji na Allah ne bana kowa ba..yakai Abbana abunda nakeso dakai shine, mu biya wannan sarki duk abunda ya bukata dangane da wannan barnan da muka masa, Amma ayau dinnan nakeso mubar yankin kasar nan tasa mu kara gaba. Banason muyi yaki da wannan sarkin domin shine jarumi na farko dana taba ganin iyada jarumtaka irin taka"".. Koda jin wannan batu Sai mamaki Yakama sadauki zahar da sauran jama'arsa. Shi kuwa sarki Lubainu Sai hankalinsa ya dugun Zuma Ainun bisa jin ayau su jarumar sukeson subar kasarsa Alhalin ayanzu ma jiyake kamar bazai iyayin rayuwa ba in baya ganin wannan kyakkyawar sura tata. Nan take sarki Lubainu yashiga tunanin dabarar da zaiyi ya hana wadannan mafarauta barin kasarsa. Ita kanta jarumar ta gano abinda ke cikin ran sarki Lubainu domin ta lura da irin kallon da yakeyimata run farkon haduwarsu kuma itama jarumtakarsa ya burgeta. To Amma Sai ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace, MEYASA WANNAN SARKI YA YAKENI DA DUKKANIN KARFINSA DA NUFIN YA HALLAKANI IDAN HAR WANNAN KALLO DAYAKE YININI NA KAUNANE? WATA KILA DARAJARSA DA KIMARSA AWAJEN YARANSA KOKUMA DOMIN YA JARRABI JARUMTAKARSA AKAN TAWA"".. Shi kuwa sadauki zahar Sai ya sake doban 'Yar tasa yace, yake SUHAILAT, Nawa ne adadin kudin da wannan sarki yakeso mu biyashi bisa wannan barna da mukayimasa? Koda jin wannan magana Sai jaruma suhailat ta dubi sarki Lubainu tace, Ai waka abakin mai ita tafi dadi, don haka Sai yayi mana bayani da bakinsa muji. Koda jin wannan batu Sai sarki Lubainu ya kara fadawa kogin tunani. Abu na farko dayayi shine,ya karewa wadannan mafarauta kallo domin yaga ya Arzikinsu saboda yasamusu kudi mai yawa wadda baza su iya biya ba. Amma Sai wata zuciyar tace dashi, Aisu kudi basuda kama, kuma bisbisa ganin yadda wadannan mutane sukeyin wannan gagarumar farauta, Akwai alamun zasu iya Tara makudan kudaden da ba'a zato"". Koda jaruma suhaikat taga sarki Lubainu yayi shiru Sai ta matso kusa da shi ta katsenmar tunani tace Malam kana bata mana lokaci mu mata fiyane ba mazauna ba! Bamu gaba zama akowane gariba sama da tsawon kwana bakwai ba Sai a wannan gari naka"". Koda jin wannan tambaya Sai sarki Lubainu yayi murmushi yace, Ai wannan babbar barns da kukayimin baza Ku iya biyanta da kudi ba domin ni mawadacine na kudi, harma sunyi mini yawan da babu abunda zanyi dasu. Idan kunaso Ku biyani saidai mu shirya wata Gasa ta jarumta tsakanin zakurkuran mayakanku mutum Ashirin da nawa, kuma kullum mutum biyu ne kacal zasuyi wannan gasar. Abunda ake bukata a gasar kawai shine, akai mutum kasa ba tare ta an illatashiba, idan jama'atane suka lashe wannan gasa to dole Ku zauna a birnina tsawon wadansu kwanaki Ashirin din kunayimin Aikin bauta a cikin gidan sarautata. Idan kuma kune muka lashe gasar a cikin kwana ashirin din to shikenan kun biyani barnar da kukayinin saikuyi tafiyarku"". Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar da jaruma suhailat Sai suka dubi junansu kawai Sai sukayi shiru suna tunani. Suma jama'ar tasu Sai suka kama kus kus suna tattauna Al'amarin a cikin fargaba da damuwa. Muhadu gobe in Allah yakaimu muji yadda wannan Al'amari zai kasance ALLON SIHIRI Littafi na shida 6 Part G Koda ganin haka Sai sadauki zahar Yakama hanjun jaruma suhailat ya jata gefe daya ya dubeta yace, ni Abunda na lura dashi shine, wannan sarki bayason tafiyar mu kuma laifin da muka masa mashine a gabansaba kece matsalarsa. Ga dukkan Alamu yafada irin tarkon da sauran sarakai dayawa suka fada akanki"". Sa'adda jaruma suhailat taji wannan batu Sai tayi ajiyar zuciya cikin alamun damuwa tace, yakai Abbana indai hakane kuwa bamuda wani zabi Wanda yafi muyi wannan gasa, domin idanma mukace zamu gudu nida kai ne kadai zamu iya gudun da barlza acimmana ba, yazamuyi da sauran jama'armu zamu barsu ne akamasu Amatsayin bayi? Duk da cewar bamusan irin jarumtakar dakarunsaba dolene muma a bangarenmu muma mu ware namu jaruman wadanda muka yarda dasu kuma dole ne muma mushiga cikin gasar domin karawa namu jaruman karfin gwuiwa"". Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar ya jinjina kai yace, "" tabbas bamuda wata mafita da tahuce wannan"". Koda gama fadin haka Sai sadauki zahar ya matsa kusa da sarki Lubainu yadubeshi yace, "" mun yadda zamuyi wannan gasa ta kwana Ashirin a birninka, Amma bisa shatadi guda!! Sharadin kuwa shine, cimmu da shammu da masaukinmu yana hannunka Atsawon wannan kwanaki dakuma tsaron lafiyarmu dakuma rayukanmu tunda mu munfi kwarewa rayuwar daji yanzu kuma kai kanaso muzauna a birninka tare da jama'arka. Idan rayuwar daya daga cikinmu ta tabu ko lafiyarsa to zaka biya diyya mai darajar gaske, shin ka Amince da wannan sharadin??"". Lokacin da sarki Lubainu yaji wannan batu Sai zuciyarsa takamu da farin ciki tayi fari kal, kawai Sai yadubi sadauki zahar yace, "" Nima na Amince da duk wannan sharadin naku "". Batare da wani bata lokaci ba sarki Lubainu da dakarunsa shida suka wuce gaba da dakarun su wannan tawagar su sadauki zahar suka rufa masa baya aka nufi cikin BIRNIN ISTAMBUL. Duk bayan kamar dakika goma Sai sarki Lubainu ya dubi jaruma suhailat. Koda taga kallon yayi yawa Sai ta dauko wani shudin rawani ta rufawa kanta yazamana cewa idanuntane kadai ake gani. Koda ganin haka Sai sadauki zahar ya bushe da dariya yace, dakyau 'yata kinyi maganin ido domin shi ido gubane! Ina mai shawartarki da kija ajinki awajen wannan sarki da dukkan jama'arsa, kuma ki kula da kanki don inatsaron wadannan mutane suyi wani Abu Wanda zai cutar da mu"", Koda jin wannan batu Sai jaruma suhailat tayi murmushi tace, " kwantar da hankalinka yakai Abbana, kayi sani Babu abunda zai samu dayanmu a wannan gari, lafiya lau zamu gama abummu acikinsu mutafi".. Lokacin da sarki Lubainu ya iso gidan sarautar akaganshi da wannan bakin mafarauta Sai aka cika da tsananin mamaki, Dafarko Sai dakarun suka taso danufin su tsare bakin masarautar domin su azatonsu kama sarkinsu Akayi, Amma Sai sarki ya musu inkiya suka koma suka tsaitsaya a inda suke. Nana take aka bude kofar masarautan take suka kunnakai ciki. Da zuwansu Sai akaga sarki Lubainu duk ya rude yanata haba haba da wadannan bakin mafarauta, domin da kansa yayi musu jagora izuwa masaukinsu, kuma masauki mai Daraja yakaisu inda ba'a saukar kananan mutane, daga manyan sarakai Sai shahararrun Attajirai. Nan take sarki Lubainu yabada umarnin Ashiryawa bakinsa abinci mai Daraja. Nana da nan kuwa akacika babban falon da aka kaisu da kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri birjik! Wadanda ma sunyi musu yawa, baza su iya karar da su ba, duk da cewa adadinsu yahaura dubu uku. Dakin barcin da aka baiwa jaruma suhailat kuwa, koda matar sarki ce iya abunda za'a shirya mata Keenan acikin dakin, Dakin yana hade da makewayi acikinsa. Shikansa makewayin katone kuma bahon wankansama na zallan lu'u lu'u ne. Gadon da ke dakin kuwa Lumsheshene mai tarin shimfidu masu taushin gaske. Abinka da wadanda basusan komai ba Sai rayuwar daji, kuma basu da dakujan kwana Sai bukkoki da kogunan duwatsu da tanti, duk Sai suka zama cikakkun 'YAN KAUYE, don haka Sai suka kasa Amfani da kayan kyale kyalen cikin dakinnasu dole aka kawo kuyangi suka koyar dasu. Bayan jaruma suhailat taci abinci ta koshi Sai kuyangi uku su ka kamata suka shigar da ita kewaye domin suyi mata wanka. Koda suka kwabe mata kayan jikinta suka yi mata tum6ur! Sai suka rude suka dimauce sakamakon kyawun da dirin da Allah yabata dakuma kyawun da Allah yayiwa fatar jikinta dakuma laushi, domin ko a TARIHI basu tabajin An wassafa mace mai irin kyawun jikintaba. Hakadai kuyangin suka shigar da jaruma suhailat cikin bahon wankan suka shiga yi mata wanka hannunsu na kyarma, jikinsu nata makyarkyata saboda tsananin Al'ajabi. Bayan Angama yiwa jaruma suhailat wankan aka shafeta da mai dakuma turare Sai aka je Aka kwantar da ita bisa wannan lumsheshshen gadon. Koda taji laushin gadon kuma ta duba kayan kawan dake cikin dakin Sai fuskarta ta fadada da murmushi da Annuri gami da kurawa rufin dakin idanu tana mai cewa acikin ranta. WAI SHIN YAUSHENE NIDA MAHAIFINA DA JAMA'ARMU ZAMUSAMU NUTSUWA DA DAULA IRIN WANNAN? A IYA RAYUWAR DA NA TASO NA RAYU ACIKIN DAJI, YAKA MATA ACE YANZU NE ZAN HUTA NASAMU MIJIN DA ZAN AURA UBAN 'YA'YANA. BANIDA BURIN DAYAWUCE IDAN NAYI AURE NASAMU DA KO 'YA WACCE ZATA GADONI A JARUMTAKA DA KYAU, KUMA TACI GABA DA SHUGABANTAR KABILARMU!"" Koda jaruma suhailat tazo nan a zancen zucinta Sai hawaye ya zubo mata, saboda bataga ranar da wannan buri nata zaizo ba saboda amatsayinta na shugabar kabilarsu kafin abaya tashugabancin saida tayi rantsuwa akan har abada bazata taba nisantar jama'arsuba kuma zata ci gaba da shugabantarsu izuwa tafiye tafiye donyin farauta akowane bangare na duniya har izuwa karshen rayuwarta.haka Sai suhailat taci gaba dayin wannan tunani har bacci yasaceta bata sani ba. AL'AMARIN Sarki Lubainu kuwa, tunda yaga Anbaiwa su suhailat masauki da abinci mai kyau Sai yatafi izuwa turakarsa cikin tsananin farinciki. A wannan ranadai saida gaba dayan fadawansa da hafiman gidan sarautar sukasan cewa lallai yana cikin farinciki, domin saida halayensa suka sauya nan take, Kawai Sai Yakama yiwa mutane kyauta taban mamaki da bazato, sannan ya 'yanta bayi tamkar yasamu waraka daga lalurar da ta addabi rayuwarsa. Kai awannan ranadai sarki Lubainu kasa bacci yayi domin duk sa'inda ya runtse idanunsa domin yayi baccin saidai yaga fuskar jaruma suhailat na yi nasa murmushi. Atakaice Sai yadda sarki Lubainu yaga rana haka yaga dare a wannan ranar. Ita kuwa jaruma suhailat baccinta tayi ta more hadda munshari. Koda ta farka da safe saitaji zuciyarta na faman bugawa alamar cewa Akwai wani Abu dake shirin faruwa marar dadi agareta kokuma Ga jama'arta. Koda gama aiyana hakan acikin zuciyarta Sai hankalinta ya zugunzuma ainun. Bisa wannan daliline ta dauko madubin tsafinta ta shafashi da hannun hagu tashiga bincike. Nan take taga duk abunda yafaru Ga sarki Lubainu agaba dayan rayuwarsa da matsalar da ta Addabi rayuwar harda baccin da yakasayi sakamokon kamuwa da sonta da begenta. Koda ganin wannan Abu Sai nan take taji takamu da tsananin tausayin sarki Lubainu akaron farko dataji sonsa yadan digu cikin zuciyarta. Jaruma suhailat taci gaba da bincike akan rayuwarta da sarki Lubainu, Aikuwa Sai taga wani babban abin tashin hankali Wanda indai tana Raye da sarki Lubainu Sai ya faru. Ba komai ne wadannan abunba face mugayen yake yake Wanda za'ayi miliyoyin rayuka da dukiya dakuma tsananin wahala ta gaban kwatance. Koda ganin haka Sai jaruma suhailat ta Aiyana aranta cewa bazata taba baiwa sarki Lubainu fuskar da zasuyi soyayya ba. Abunda zatayi kokarin yi shine, ta tabbatar da cewa itada jarumansu sun sami nasara acikin wannan gasa da sarki Lubainu ya shirya. Bayan jaruma suhailat ta gama yanke wannan hukunci ne Sai ta mike da sauri taje tayi wanka da kanta domin wannan karon kuyangin basuzoba tunda sun koya mata yadda akeyin wankan. Koda tafito daga kewayenta tashiga dakin barcin domin tasanya tufafinta na fita farauta Sai tayi Arba da wasu tufafi masu kyawun gaske irin nasu na mata visa kan gadon nata wata kuyangan sarki na tsaye agefe daya. Koda kuyangar taga jaruma suhailat tashigo dakin saita zube kasa gabanta tayi gaisuwa sannan ta dago kanta ta dubeta tace, ya shugabata sarki ne ya turoni nasa miki wannan tufafi saboda ya gaiyaceku izuwa fadarsa keda mahaifinki, koma Akwai manyan bakin sarakuna da sukazo halattan wani biki da akasabayi a wannan gari namu arana irinta yau"". Koda jin wannan batu Sai jaruma tadubi wannan kuyanga da'alamun mamaki tace, Wane irin biki ne wannan haka?" Kuyangar tace, gasa ne na Raye Raye da kade kade gami da wake wake. Wanda duk yalashe gasar sarakuna nabashi kyaututtuka wani ma Sai yasamu sarkin dazai bashi kwangila ta daukemasa kewa har izuwa karshen rayuwarsa yana biyanshi Albashi mai tsoka." Koda jin wannan batu Sai suhailat takamu da murna saboda a rayuwarta tanson kallon abubuwan nishadi irin haka. Batare da wata matsalaba ta Amince akasanya mata wannan Riga mai Daraja akayimata kwalliya ta gani afada. Koda kuyangar takaita gaban madubi suka tsaya takalli kanta Sai tacika da tsananin mamaki, da farko razana tadanyi taja da baga don zato tayi wata Al'jana ce me kamarta a jikin madubin. Saida ta shafa hannunta ajikin madubin sannan ta tabbatar hotonta ne ajikin madubin ba Al'jana ba. Cikin murmushi suhailat tadubi kuyangar tace, "Kaini masaukin mahaifina", Nan take kuyangar tahuce gaba jaruma suhailat na biye da ita. MUHADU A LITTAFI NA GABA WATO NA BAKWAI (7) DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN KASAITACCEN LABARI. DAGA MAI DEBE MUKE KEWA A KULLUM A KO YAUSHE. KING OF ADVENTURE STORY. ABDUL'AZEZ SANI MADAKIN GINI. NI NAKU HAR KULLUM KHAMIS IDRIS MUHAMMAD NAKE CEWA MUGANA A GABA NAN BADA JIMAWABA INSHA ALLAHAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ [1/23, 00:53] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi na bakwai 7 Part A Duk Inda Suka Wuce Dakaru, Bayi, Barori Da Kuyangi Kamar Babu Mai Rai Acikinsu Sbd DuksuYazaunaKamar Gunki Suna Masu Quramusu Idanu, Bakomaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Tsananin Kyawun Jaruma Suhailat, Gashi Kuma Wannan Riga Datasaka Ba Qaramin Kyawu Tayi Mataba, Da Shigarsu Cikin Dakin Sai Suhailat Tasake Cika Da Mamaki, Ba Komaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Mahaifinta Sadauki Zahar Zaune Akan Kujera Cikin Tufafi Na Alfarma Tamkar Wani BASARAKE, Koda Sadauki Zahar Ya Hango Suhailat Acikin Wannan Kyakyawan Shiga Wace Taqara Fito Da Tsananin Kyawunta Da Kwarjininta Sai Ya Miqe Tsaye Cikin Matuqar Farin Ciki Ya Tareta Suka Rungume Juna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata Ya Dubeta Cikin Alamu Matuqar Damuwa Yace, Yake 'yata Shin Kinada Lbrn Cewa Inda Zamuje Yanzu Taro Ne Na Sarakai Da Manyan Masu Fada"aji, Jaruma Suhailat Ta Gyada Kai Tace Nasani Ya Abbana, Kuma Ka Kwantar Da Hankalinka Babu Wani Sarki Ko Attajiri Wanda Ya Isa Ya Mallakeni Da Qarfin Arziqinsa, Na San Wannan Ce Damuwarka, Kodajin Hak Sai Sadauki Zahar Yayi Murmushi Yace Wannan Gsky Ne Yake 'yata, To Amma Wane Mataki Zaki Dauka Don Kaucewa Hakan? Kisani Cewa Dazarar Sarakan Sun Ganki Zasu Dimauce Kuma Sufara Tunanin Hanyoyin Dazasubi Su Mallakeki Ta Kowanni Hali, Jaruma Suhailat Tasake Yin Murmushi Akaro Na2 Tace Kada Kadamu Yakai Abbana Domin Tuni Nadauki Mataki Akan Hakan, Kai Dai Kawai Kazuba Ido Kaga Abinda Zaifaru, Gama Fadin Hakan Keda Wuya Saiga Wani Hadimi Ya Shigo Cikin Turakar Da Sauri Ya Dubesu Yace, Sarkine Yaturoni Nayi Muku Jagora Izuwa Fada, Batare Da Bata Lkc Ba Jarumu Suhailat Da Sadauki Zahar Sukabi Bayan Wannan Hadimi Suka Nufi Fadar, Filin Fadar Yacika Ya Batse Da Bil'adama Duk Inda Mutum Yahanga Babu Abinda Zaigani Face Kawunan Mutane Rututu! An Kange Tsakiyar Filin Dawata Katangar Qarfe, Makada, Mawaqa Da 'yan Rawa Sunjeru A Gefe Sahu Sahu Acan Sama Bisa Wani Gini Mai Tsawo Wanda Ke Dauke Da Matattakala Sarakai Ne A Zazzaune An Shirya Kayan Ciye Ciye Da Shaye Shaye Agabansu, Tuni A Wannan Lkc Anfara Gabatarda Sauran Jama'a Kuwa Sai Idanunsu Sakakafe Bakunansu Suka Wangame Sbd Kallon Kyakkyawar Surar Dake Wucewa Ta Cikin Tsakiyar Fadar Wato JARUMA SUHAILAT Tarada Muqarrabanta Nan Take Sarki Lubainu Da Dakkannin Sarakuna Dake Kewaye Dashi Suka Mimmiqe Tsaye Dao Tarbar Jaruma Suhailat Da Tawagarta, Sudai Sarakan Sunyi Zaton Cewa Suhailat Wata Shahararriyar Sarauniyace Daga Wani Bangare Na Duniya, Donhaka Basusan Sa'adda Sukakama Risinawa Ba A Gareta Suna Gaisheta, Shikansa Sadauki Zahar Anzata Cewa Sarkine Sbd Kwarjininsa Da Yanayin Shigar Dayayi Irinta Manyan Sarakai Ce, Cikin Hanzari Sarki Lubainu Yatarbi Jaruma Suhailat Da Mahaifin Sadauki Zahar Yarakasu Harzuwa Inda Aka Tanadarmusu Suka Zauna Sannan Shima Yakoma Gaban Karagarsa Yatsaya Ya Fuskanci Jama'a, Nanfa Fadar Tayi Tsit! Kamar Mutuwa Tagifta Aka Zubawa Sarki Lubainu Idanu Ana Sauraronsa Aji Bayanin Dazaiyi, Sarki Lubainu Yayi Gyaran Murya Sannan Yace Yaku Manyan Baqi Da Dukkanin Jama'a Dake Wannan Wurin, Ina Yimuku Barka Daxuwa Wannan Babban Taro Wanda Mukasabayi Aduk Shekara Awannan Birninamu Mai Albarka Na Istambul, Bayan Haka Inamaiyiwa Jama'a Busharada Cewa Wannan Tarona Banatarone Nadabam,kumanamusamman Wandabamutabayin Kamarsaba Sabodawannankaron Munada Wadansu Bakinamusamman Masu Dumbinbaiwada Darajakamar Yaddakukaga Shigowarsu Akarshe Izuwacikinwannantaro.Wannanmanyanbaki Sunzoda Zakwakuran Sadaukai Kuma Jarumaihar Gudaashirin Wadandazasu Yigasar Karfindantseda Dakarunbirnina,inamaiyiwa Jama,a Albishirdacewa Nimainacikin Jarumandazasuyi Wannan Gasarjarumtaka;kodasarki Lubainuyazo Nan Azancensa,saimutanesukarude.Dashewa,gami-datafi.Sabodasun,san.Irin Tsananin JARUMTAKARSA Da Sadaukantakarsa Don Hakasuna Son Kallon GUMUZUR, Al'amarin Jaruma Sahailat Da Mahaifinta Sadauki Zahar Kuwa Koda Sukaji Cewar Sarki Lubainu Mazai Shiga Wannan GASAR JARUMTAKA, Daza Ayi Sai Sukakamu Datsananin Mamaki Kuma Tsoro Yadarsu Acikin Zukatansu Domin Basu Taba Zaton Cewa Hakan Zatafaruba, Cikin Kaduwa Jaruma Suhailat Tadubi Zahar Cikin Qaramar Murya A Daidai Kunnensa Tace Yakai Abbana Yanzu Meye Abinyi? Idan Harmuka Bari Saski Lubainu Yashiga Wannan Gasa Muza A Cinye, Sadauki Zahar Yanumfasa Yace Maganarki Dutsece Donhaka Ina Ganin Cewa Nima Zanshiga Gasar Sbd Natareshi, Jaruma Suhailat Ta Girgiza Kai Tace A'a Bazaka Tareshiba Nice Dai Dai Dashi Domin KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA Yadda Yake Taqama Da Quruciya Daqarfi Nima Haka Nake Taqamadasu Kaikuwa Shekarunka Sunfara Nisa, Zai Iya Amfani Da Wannan Dama Yayi Saurin Galabaitar Dakai Donhaka Kawai Kabarni Dashi, Sarki Lubainu Yaci Gabada Bayani Yana Mecewa Yaku Jama'a Yanzu Batare Da Bata Lkb Ba Ina Kira Ga Wadannan Manyan Baqi Namu Dasu Fitoda Jaruman Gasarsu Guda Ashirin Su Gabatardasu A Tsakiyar Filh Sannan Muma Mu Gabatar Da Namu, Bayan Nan Za'ayi GASAR JARUMTAKA Guda Daya Jal! Awannan Rana Sannan A Cigaba Da GASAR NISHADI Koda Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yakoma Kan KARAGAR MULKINSA Yazauna. Muhadu gobe in Allah yakaimu. Naku khamis idris Muhammad [1/23, 00:53] +234 808 677 7945: e ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part B A Sannan Ne Sadauki Zahar Da Jaruma Suhailat Sukamiqe Tsaye Suka Kira Jama'arsu Suka Koma Gefe Daya Acikin Filin Fadar Sunaware Sadaukan Dazasuyi Wannan Gasa, Bayan Sungama Ware JARUMAI Goma Sha

Chapter 14 of 19