Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da makamai. Koda jaruma suhailat taga sun durfafota acikin wannan salon yakin sai nantake tagane nufinsu wato sosuke lalle suyimata kuri a tsakiya yadda bazata taba samun daman motsawa ba izuwa duk inda taga dama, saidai sutakure awaje daya har yazamana cewa tagaji sannan su samu lagonta. Koda yarage saura baifi taku biyarba samudawan maridan su cimmata sai tadaka tsalle sama ta tsallakesu, kafin ta dira Achan bayansu saita dako daya daga cikinsu. Take yarinjayi sauran suka kife kasa. Al'amarin dayi matukar baiwa maridan dasu sarauniya Akisatul sauwara mamaki kenan bisa ganin yadda jaruma suhailat tasami wannan gagarumin wannan karfin. Cikin tsananin fushi samudawan maridan suka miki zumbur! Suka juyo da baya a fusace. Maimakon susake rike hannun juna su rugo gareta sai suka tarwatse kuma kowannensu yadako tsalle daga inda yake, saigasu a sama tamkar tsuntsaye masu fuka_fukai. Asamanne ko wannensu yazaro makaminsa da nufin suyiwa jaruma suhailat rubdugun SARA DA SUKA. Kafin kowannesu yasamu daman Kai makaminsa jikinta tuni jaruma suhailat tayi Dan tsalle sama tayi wata irin katantanwa Sama tamkar An murza mazari ta tarwatsasuTana Mai naushin fuskokinsu da kafafunta dakuma hannayenta duk alokaci guda. Kawai saigani akayi samudawan maridan suna zuzzubewa kasa itakuma saitacigaba da katantanwa Asaman kaman Anmurza mazari ta tarwatsu Tana Mai naushin fuskokinsu da kafafunta dakuma hannayenta duk a lokaci guda.kawai saigani akayi suna zuzzubewa kasa, itakuma tacigaba da katantanwa Asama har izuwa 'yan wasu dakiku ba tare da tafado kasaba harsaida gaba daya samudawan maridan sukaje Kasa sannan taduro kasa da kafafunta. Saboda tsananin mamaki bisa ganin gagarumar wannan jarumta da jaruma suhailat tayi Akisatul sauwara, jarumi lubainu, sarki Darmaz da Dazyan basusan sa'adda suka wangame bakinsuba sukazama kamar gumaka domin ko giftawa basayi. Mutara kokuma Anjima idan nasamu time gobe Naku Khamis Idris Muhammad Allon sihiri littafi na 6 shida Part B Koda samudawan maridan sukaga abunda jaruma suhailat tayi musu yazamana cewa duk ta farfasamusu baki da hanci, sai suka fusata Ainun suka taso mata da nufin su tarwatsata. Koda ganin haka sai itama jaruma suhailat ta fusata ta maida takobinta cikin kufenta ta taresu Tana Mai karanta wasu Addu'a ta musamman acikin ranta. Aikuwa suna riskarta sai sukaci gaba da kaimata Sara da suka da manyan miyagun makamansu, ita kuwa sai tawanzu Tana Mai Kare duk hare harensu Tana Kama hannayensu da kafafunsu Tana kakkaryasu. Nanfa ihun samudawan maridan da kururuwarsu tacika dajin gaba daya. Karar karyewan kasusuwannasu kuwa tamkar karyewar bishiyoyine Manya ke faduwa Kasa. Kafin cikan dakika Dari bakwai da sittin gaba daya samudawan naridan sun zube kasa sunzama naka sassu sai koke-koke da ruri sukeyi sakamakon tsananin zafi da zogin da sukeji. A daidai wannan lokacin ne sarki Darmaz yadubi sarauniya Akisatul sauwara yace, Tabbas wannan jarumin ba mutum bane, Aljanine yazo garemu domin ya yaudaremu. Saboda idan ba Aljani ba banga wani mahaluki da zaizo yayi wannan gagarumin jarumtakar ba. Koda jin wannan Batu sai sarauniya Akisatul sauwara tayi murmushi tace, Tabbas mutum ne ba Aljan ba, domin inda Aljanine tun farkon haduwarsu za'agane, saboda dukkan matsafi yana gane Aljani adukkan shigar da yazomasa, kawai kace hatsabibine kuma takadarin BIL'adama Mai abubuwan Al'ajabi na gaban kwatance, Saidai Akwai wani Abu guda Dana kasa fahimta akansa, har yanzu nakasa ganewa shin namiji ne kokuma mace ne?? Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yadubi sarauniya Akisatul sauwara afusace yace, wannan wace irin maganan banza kikeyi yake wannan sarauniya? Ina Mai tabbatar miki da cewa maigidana namiji ne ba mace ba, saboda meye kike tantama akan haka? Koda jin haka sai itama sarauniya akisatul sauwara ta dubi wada Dazyan afusace ta dakamar tsawa tace, idan hard Mai gidan naka namiji ne meyasa yakejin kunyan ya rube agabana?? Tunda muka Fara wannan tafiyar babu Wanda ya taba ganin gashin kansa bare cinyarsa. Akan wane dalili yake boye komai na jikinsa? Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yayi tsaki yamiki daga cikinsu yatafi inda jaruma suhailat take. Shukuwa yarima Lubainu daman yana gefe daya yana ganin ikon Allah. Lokacin da Dan wada Dazyan yace wajen jaruma suhailat sai ya sanar mata da duk abunda suke fada akanta, sai hankalinta ya dugun zuma ainun, tayi mamakin yadda har sarauniya akisatul sauwara take kokarin gano haka. Kawai sai ta dubi Dan wada Dazyan acikin YAREN KURAME. Karka damu da ita akan Hakan zargi takeyi batada yakini akan hakan. Gama fadin haka keda wuya sai jauma suhailat ta juya gefen inda yarima lubainu yake tsaye. Awannan lokaci samu dawan maridan da jaruma suhailat ta bazar akasa sun Fara Jan jikinsu akasa dakyar tamkar macijiyar da tayi babban hadiya. Kwatsam bazato ba tsammani sai sukaji wata gagarumar iska a samansu. Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri tun An mammakesu. Saboda karfin bugun da akayiwa kowannensu a fuska, take suka zube kasa sumammu. Lokacin da jaruma suhailat da yarima lubainu suka farfado daga suman da sukayi sai suka tsinci kansu a daddaure da wata murtukekiyar sarka ajikin wata bishiya kuma duk gabobin jikinsu a sanyaye suke ta yadda ko daga hannunsu bazasu iyaba saboda rashin karfi da kuzahari. Acan gefe guda kuma sarauniya akisatul sauwara, sarki Darmaz, Dan wada Dazyan ne suma acikin mummunan Hali suyi darsham akasa kamar yadda su jaruma suhailat suke na dauri. Har izuwa wannan lokaci wannan iska bata daina ba ta gabar da yamma kudu da Arewa. Nanfa jaruma suhailat da Dan wada dazyan suke kokarin bude bakinsu suyi Addu'oi Amma abun ya gagara. Al'amarin dayayi matukar dugun zuma hankalinsu kenan suka rasa abunda keyimusu dadi, sabida tamkar sunayin yakine da abunda basa ganinsa! Kawai sai sukaji An bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce sautinta yacika dajin gava daya karfinta yasa tantuna sukafara jijjiga kamar zasu tumfuke sufadi Kasa. Bazato ba tsammani sai halittar ta baiyana tsulum! Agaban yarima lubainu ta yadda har sunajin nunfashin junansu. Bakowa bace wannan halittar face Aljana badi'atul sauwara. Cikin razana da mamaki yarima lubainu yaja da baya yadubeta yace, Kekuma waye ya kunceki acikin daurin Dana baroki? Koda jin haka sai Aljana badi'atul sauwara tasake bushewa da dariya a Karo na biyu sannan ta tsuke bakinta Tana Mai turfune fuska tace, Kai a iya tunaninka ka dauren kana tunanin vazan taba kubuta ba ko? To kayi babban kuskure da kayi zaton haka, saboda Mai RAI baya fidda tsammanin RABO face yaba nunfashi a doron Kasa. ALLON SIHIRI LITTAFI NA SHIDA 6 PARTC Tabbas yanzu ne zakayi babban nadama akan rashin bani hadin Kai domin mugudu tare mu tsira tare da Kai. Aljana Badi'atul sauwara takauda kanta wajen jaruma suhailat race, Angaisheki BABBAR JARUMA! Hakika kin yaimakeni kin gajarcemun duk wahalan da zansha ta hada wannan ALLON SIHIRI guda uku, tunda gashi yanzu gaba dayansu a Hannunki. Kisani cewa wadanchan samudawan maridan da kika yakesu bakowa bane ya turosu face Boka darbusa, kuma har ynz baituromuku kaso goma ba daga cikin dubun irin mugayen abubuwan da yayi tanadi domin ku Akan wannan ALLON SIHIRI''. Lokacin da Aljana badi'atul sauwara tazo daidai nan a zancenta sai Sarauniya Akisatul sauwara ta wunkura cikin karfin Hali ta bushe da dariyar farinciki sannan tace, yake wannan Aljana Mai tsananin SA'A da RABO! Ina Mai godia a gareki da kika fitar damu faga cikin duhun daya baibayemu game da Abokanan tafiyarmu. Tun a farkon tafiyar mu da wannan bakuwar jarumar idanuna suka nunamin cewa wannan MACE ce ita Name MIJI ba kamar yadda take ikirari. Shin yanzu ke mecece ribarki idan kika tafi kika barmu awannan mawuyacin halin makiya sukazo suka hallakamu tunda dai kinsami abunda kike nema? Sa'adda Aljana badi'atul sauwara taji wannan Batu saita bushe da dariya tace, Ai shi makiyi ba'a bashi dama komai kankantarta. Ni banida makiyin da yawuce boka Darbusa a duniya, shikuma awajensa kune manyan makiyansa tunda kunzo har gidansa kurrabashi da abunda yashafe shekara da shekaru yana gadinsa Dan yacika burinsa na duniya. Kusani cewa bayan na dauke Allunan sihiri da suke wajenku yanzu, ina tafiya da tsawon dakiku sarkokin Dana daureku zasu bace bat! Daga cikin jikinku, kuma kuzaharinku zai dawo kamar yadda kuke a da, Amma fa kusani boka darbusa bazai taba barin kokarin hallakakuba tunda shi azatonsa kuna tare da ALLON SIHIRI. Nikuma daman zanyi Amfani da wannan ALLON SIHIRIN Wanda daman asalinsa nawane tunda mahaifinane yakerashi, kafin ku fita daga cikin masifun da kuke ciki tuni nagama dukkanin shirye shiryena na zama SARAUNIYAR DUNIYA acikin kwanciyar hankali batare da na fuskanci wata matsalaba. Gama fadin haka keda wuya sai tajuwo ta dubi yarima lubainu tadubeshi cikin wani irin murmushi na mugunta tace, tabbas kasaki reshe ka Kama ganye! Yanzu inda ace ka taimakeni ka kunceni acikin daurin da boka darbusa yamin da yanzu take Zan daukeka na doraka akan gadon bayana natafi dakai Chan fadata. Achanne zan karanta wannan ALLON SIHIRI nagano inda KOGIN IMFAL yake nakaika Chan kaciro saiwar da bishiyar da ake bukata wacce zakasha ka warke daga lalurar da yarima mangul ya sakamaka. Yanzu gashi kayi biyu babu, domin bazaka warke ba, kuma bazaka sake saduwa da matarkaba GIMBIYA YAZIRINA har Abada, dimin a halin yanzu suna Chan wani waje Mai mugun Nisa acikin daji acikin mugun yanayi na rashin sanin inda suke dama inda zasu dosa. Kuma yarima mangul bazai daina farautarsuba har saiya riskesu ya kashe SADAUKI RUHAISU sannan ya dauke gimbiya yazarina''. koda Aljana Badi'atul sauwara tazo nan a zancenta saitakara Bushewa da dariya akaro na biyu sannan tadubi yarima lubainu tace, shin kanada wata wasiyya ne ga mahaifinka!? tabbas zanyi maka wannan Alfarmar nakai wannan wasiyyarka tunda nima Kayimin Alfarma guda daya ta rufamin Asari baka sanar da wannan BAKUWAR JARUMA Mai Rufe fuskarta da jikinta labarina sa'adda ka ganni acikin gidan boka darbusa da bansamu wannan damar yanzu ba Dana shammaceku Dana sumar daku, kuma nasanya muku wannan tsananin mutuwar jikin. koda jin haka sai Aljana Bari'atul sauwara tasake tuntsurewa da dariyar mugunta taita kyalkyalewa kamar bazata dainaba ba. daga can kuma saita tsuke bakinta tace, Ai shi kenan nida Kai zanga Wanda zancensa zai tabbata. Tana Gama fadin haka sai ta bude fuka fukanta saiga ALLON SIHIRI guda uku amakale a hammatarta. harta yunkura zata tashi sai yarima lubainu yace yake wannan Aljana, waishin wanene ya kunceki daga wannan daurin da boka darbusa yamiki? Koda jin wannan tambaya sai Aljana badi'atul sauwara tayi murmushi tace, babu Wanda ya kunceni face ni kaina. Kasan Ance Mai rai baya kasa motsi! Bayan kaki kunceni katafi kabarni acikin wannan mawuyacin Hali ina zubar da hawaye sainarinka buga kaina ajikin bango saboda bakin ciki kuma narinka buga kafafuwana a kasa. Adalilin hakanne kafafuwan nawa suka rinka fasa malalen kasan har suka haddasa rami Mai zurfi, Ashe acikin kasan dakin danake aciki yake ajiye Littatafai dayawa na sirrikan tsafin boka darbusa. Dayake sarkar dayake daure Dani Mai tsawo ce sosai, take nakarasa Burma ramin da kafafuna sukayi nafada kasan dakin nashiga karanta littatafan. Acikin littatafanne naga sirrin yadda zan kwance kaina daga sarkokin da boka darbusa ya daureni. Nantake nakamu da tsananin farinciki dakuma takaici ganin cewa sai a sannan ne nasan da wannan damar bayan na shafe shekaru da dama acikin kurkukun bakin ciki. Da wannan furuci nakeyi muku bankwana na karshe. Koda Gama fadin haka sai Aljana badi'atul sauwara tasake bude fukafukanta ta tashi sama. kafin giftawar ido ta luluka acikin gajimare ta bace bat!! Tamkar bata taba wanzuwa ba awajen. Bayan shudewan wasu 'yan dakiku ne su jaruma suhailat sukaga sarkokin da aka dauresu dashi sun bace bat!! Tamkar basu taba wanzuwa ba Sannan sukaji karfin jikinsu yadawo dakuma kuzaharinsu yadawo tamkar wani Abu bai taba samunsuba. Cikin hanzari jaruma suhailat mike tsaye zumbur! Tacire rawanin dayake kanta tayi jifa dashi. Alokacinne dogon gashin kanta ya zubu izuwa gadon bayanta yana sheki da walwali. Jaruma suhailat ta cire babban rigan da ke jikinta doguwa ta tsargeta da hannayenta biyu tayi jifa da ita saiga gaba daya surorin jikinta sun fito. Koda sarauniya Akisatul sauwara da sarki darmaz sukayi Arba da wannan baiwa ta kyau wacce Allah yayiwa jaruma suhailat saisuka dimauce suka fita a haiyacinsu alokacin idanuwansu suka kafe, jikinsu ya Kame suka kuramata idanu kawai. Ita kuwa sai ta durfafosu saida tazo dafda su sannan ta tsaya fusakrta a murtuke. Susana SUHAILAT BINTU AFUWAN, kuma nafitone daga wata nahiya Mai Nisa, daban da taku ba, Acikin wata kasa da ake Kira DARUL ILMUN. Bakokai ne yakawoni nayiyarku ba face jaddada ADDINiNA Wanda shine Addinin gaskia a bautawa Allah shikadai Wanda bashida Abokin tarayya, wato ADDININ MUSULUNCI! Lallai saina tabbatarwa da sarakunanku da kuma Bokayenku cewa bautar gumaka da tsafin da kukeyi duk karyace, kuma hanyace ta bata mabaiyani. idan har na'isa login bahar imfal da taimakon ubangijina nayi nutso acikinsa na tsunto Dan itatuwar da yarima lubainu zaisha ya warke daga asirin da yarima mangul Yamar dolene su yarda da Addinin tunda sun tabbar babu Wanda yataba yin hakan, kuma babu Wanda zai iya. Kosani cewa koda Allon sihiri na wajenmu ko bayanan zamu isa kogin bahar imfal nabiyawa yarima Lubainu bukatarsa Da izinin ubangijin musulunci. Sa'adda jaruma suhailat tazo nan azancenta sai sarauniya akisatul sauwara da sarki darmaz suka dawo haiyacinsu sunamasuyin doguwar ajiyan nunfashi, sannan sai sarki darmaz yadubi jaruma suhailat cikin fushi yace, to mu meye Amfanin mu cigaba da binku acikin wannan tafiyan tunda Arrabaki da Allunan na sihiri? tayaya zaki iya dauko wannan makarun maganin da akayiwa trains lubainu Alhalin babu ALLON SIHIRI awajenki? koda jin wannan Batu sai jaruma suhailat tace, tunda imaninku ya karkata akan sai da ALLON SIHIRI?! Za'a aiwatar dashi, to shiekenan zan karbo muku ALLON SIHIRIN daga hannun wannan Aljana da tazo tasaceshi. ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part D Kusani cewa sakaci ne yasa har tasamu dama ta shammaceni kuma bansan da batuntaba, Amma a yanzu Dana Dani duk inda take saina bita na karbo ALLON SIHIRIN naku da iznin ubangijina. Kusani cewa wannan buri na banza da kuke son MALLAKAN DUNIYA da abun cikinta shirme ne kuma nadaukeshi tamkar tatsuniya, wato Abunda bazai taba faruwa ba, Saboda shi tsafi karyane kuma batane. Da idanunku kunga dai Abubuwa da dama danayi na Al'ajabi cikin jarumtaka cikin taimakon ubangijin gaskiya kokuwa har yanzu zukatanku suna yaudarar ku?? Sa'adda jaruma suhailat tazo daidai nan a zancenta sai dadin muryanta yasake dimauta Sarki darmaz, yadubi sarauniya Akisatul sauwara sai sukakamayin in'ina suka kasacewa komai. Koda ganin haka sai jaruma suhailat ta yafito yarima lubainu da hannunta tajashi can gefe daya inda baza'aji abunda suke tattaunawa ba, suka kamayin maganganu. Koda ganin haka sai KISHI yakama Sarki darmaz da Dan wada dazyan, domin kowannensu jiyayi inama shine yakadaita da jaruma sulailat haka yana kallon kyakkyawar fuskarta kuma Yana ka sauraron naganarta Mai zaki wacce ita kadai zatasa mutum yayi bacci kokuma ta kwantar masa da hankali a lokacin da yasamu kansa cikin bakin ciki ko damuwa. Ita kuwa Akisatul sauwara wani tunanine yafado mata nan take Wanda ya dugunzuma hankalinta tarasa Abinda yake mata dadi. Dafarko dai sa'adda taga yarima lubainu da jaruma suhailat sun koma gefe sun tsaya dabda juna suna magana saita kuramusu idanu Tana Lura da irin kallon da sujeyiwa junansu, kawai so take ta gano shin Akwai soyayyane a tsakaninsu? To idanma Akwai soyayya ai saidai idan ayanzu take aka farata tunda dai shi baitaba ganin fuskartaba sai a yanzu. Tun a ranan da Sarauniya akisatul sauwara tafara ganin yarima lubainu taji ya kwanta mata aria domin yanada duk abunda takeso ga namijin da zaizamo abokin rayuwarta. Abu nafarko dai shine, yanada tsananin kyau, kuma gashi basarake ne, sannan jarumin maza. Wadannan abubuwa uku sune samarin da suke nemanta suka kasa hadawa duk, kuma shine dalilin dayasa itama taki karbar soyayyarsu. Daga ranan da tahadu da yarima lubainu taga Ashe Allah yakawo mata karshen laluben da takeyi. A yanzu kuma dataga jaruma suhailat tare da yarima lubainu, saitaji wani irin BAKIN KISHI ya turnuketa, saboda.... KUYI HAKURI BABU PAGE DAYA missing 27 page. Sarauniya akisatul sauwara sai taji kamar Tasa kafarta tayi tamaula dashi, tunda tsawonsa gaba daya baiyuce tsayin guiwartaba. Dan wada dazyan yayi shiru ga barin yin dariyan sannan yadubi sarauniya akisatul sauwara yace, dafarko dai kisani cewa ban isa na fadi komai akan shugabata face sai da izninta saboda bin umarninta. Abu na biyu danakeso na tunamiki shine, yarima lubainu yanada mata wacce tunima Andaura musu Aureda ita, kuma saboda itane yafito neman maganin lalurarsa. Shin tayaya kike tsammanin zaibada soyayyarta take tsawon shekaru izuwa wata macen daya hadu da ita acikin kankanin lokaci? Idan kema kinji kinfara kamuwane da soyyar yarima lubainu inamai shawartarki da ki gaggauta ki shafeshi acikin Kundin rayuwarki don kada yabada miki kasa..... Kafin Dan wada dazyan yagama fadin abunda ke bakinsa tuni sarauniya akisatul sauwara ta daka masa tsawa. Al'amarin dayasa yarazanane har hantar cikinsa ta kada yadan ja da baya a firgice. Sarauniya Akisatul sauwara ta dubeshi a fusace tace, waccer Shugaba taka babu wani Abu da da namiji bazata iya saye zuciyarshiba saboda kyawunta, koda kuwa shine Wanda ya kirkiri soyayya a duniya. Ni kaina danake 'ya mace kuma kyakkyawa abar kwatance ayanzu Dana ganta saida na Raya a Raina cewa imani ni namiji ne Dana mallaketa Amatsayin Matata. Kasani shi SO ba karya bane gaskiyane kuma nasani cewa yarima lubainu yanada matar da yakeso, Amma shin mainene tabbacin zaisake saduwa da ita Alhalin rayuwarta nacan acikin mugun hadari? Kai! Ni tuni ma nayi bincike acikin tsafina nagano cewa gimbiya yazirina da yarima lubainu baza su tabayin zaman mata da miji ba, Dan haka babu abunda zaisa nadaina sonsa. kuma kasani cewa nice nafara haduwa da yarima lubainu har nabaro kasata, mulkina da jama'ata domin na taimakeshi. kaikanka kasan cewa idan babu SO da KAUNA babu yadda za'ayi Nabaro wadannan Abubuwa uku, na sallama rayuwata kawai Dan biyan bukatarsa. Caraf! Sai dazyan yatari mumfashin Akisatul sauwara yace Ai badon bukatarsa kadai kema kika fitoba sai domin kema ki samu daman hada Allunan sihiri guda uku. sarauniya Akisatul sauwara tayi murmushi tace, maiyasa tuntuni banyi wukurin Nemo wadannan Allunan sihiri ba guda biyu tunda nasan A inda suke sai ayanzu da yarima lubainu yazo gareni? Kai! Dakata nagaya maka gaskia, karfin soyayya yafi dukkan karfi, domin so yana iya sakawa mutum yadaina tsoron abunda yake tsoro, Saboda soyayya ta mantar dashi baya ganinsa. SO yana sakawa mutum ya fansar da rayuwarsa, kuma duk Wanda yayi yunkurin rabani da Abunda nake kauna shima zarrabashi da rayuwarsa!!! Ko ka sanar da shugabarka wannan ko baka sanar ba wannan ba matsalata bace, Amma zaifi kyau kagaya mata, domin ta nisanta kanta da yarima lubainu domin nawane ni kadai."" koda fadin haka sai Sarauniya akisatul sauwara tajuya da nufin ta koma inda tabaro sarki darmas,Amma sai Dan wada dazyan yayi saurin kiran sunanta sai tajuyo ta dubeshi sannan yace, Babu yadda za'ayi ta nisanta da yarima lubaino saboda ahalin yanzu yazama tamkar Dan uwanta najini tunda yakarbi Addininta, wato Addinin musulunci. koda jin haka sai habkalin sarauniya Akisatul sauwara ya dugunzuma fiye da ko yaushe, tayi shiru Tana Mai sunkuyadda kanta kasa, inda tafada cikin kogin tunani Mai zurfi. Tana cikin tunanin ne taga yarima lubainu ya baru inda jaruna suhailat take ya durfafo inda suke, Dan haka saita kura masa idanu Tana Mai murmushi.. da isawarsa inda suke yadubeta sannan yadubi sarki darmaz yace, jagorar tafiyarmu tace nasanar daku cewa anan zamu kwana tunda Rana ta fadi sai gobe mucigaba da tafiya. Kodajin wannan Batu sai Sarauniya Akisatul sauwara tadubi yarima lubainu cikin fushi tace, waishin akan wane dalili zamucigaba da bin jagorancinta Alhalin tanaji Tana gani akazo aka kwace mana ababan dogaranmu aka tafi dasu?? Ai wannan alamune na gazawa, waishin yanzu tasan inda zamuga Aljana badi'atul sauwara ne bare har muje mu risketa a fafata KAZAMIN YAKI Don kwato kayanmu. to kasani Aljana badi'atul sauwara bakamar hatsabibiya bace, Sarkin wannan Birni na Istanbul saurayine kyakkyawan gaske, kuma sadauki Mai TARWATSA MAZA a FILIN DAGA!! A duniya kaf! Awannan lokaci babu Wanda yafishi tarun dukiya, girman sarauta da kwarjini. wannan daliline kowace kasa ke shakkarsa, domin yatara mayaka 'yan gaban gani kasheni masu tsananin karfi da horon yaki na ban Al'ajabi. Ana kiran wannan sarki na Birnin Istanbul da suna SHA'AFARAN IBN AUHID. Khamis Idris Muhammad ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part E Babu wani jindadi Wanda Allah baibawa sarki Lubainu ba face Abu guda daya jal!! Bakomai bane face Rashin lafiyar maza kuta!!! Tundaga balagar sarki lubainu har yacika shekara talatin da uku baisan wani Abu waishi Sha'awa ba akan 'ya mace, baitaba yin wata mu'amala dawata mace ba hasalima ko kuyangi basa masa yidima saboda sanin baya bukatarsu a rayuwarsa. Duk wata hidima tasa maza ne ke masa, dafarko boye matsalarsa yayi Sai akafara zargin ko yana harkan banzane da maza Amma da'aka gano baya wannan harkan Sai akagano bashida lapia ne, saboda tunda yake arayuwarsa baitaba yin soyayya ba, kuma baitaba tunanin koda yin Aure ba. Akaf duniya babu abunda Allah yajarrabi sarki lubainu yakeso sama da kananan yara 'yan shekara hudu zuwa kasa. A kullim yanasa adebomasa kananan da yammaci acikin lambunsa azauna acikinsu yaita wasa dasu har magariba tayi sannan za'araba musu kayan wasanni iri iri da kayan zaki sannan ya sallamesu. Duk sa'ilin da sarki lubainu ya kurawa wa'yannan yaran idanu ASA ilin da suke wannan wasa Sai yafara zubda kwalla saboda takaicin sanin bashida haiwuwa bare yasamu magaji na har Abada! Babban abun bakinciki ma agareshi shine, shine zuri'a na karshe a wannan gidan sarauta, dazarar ya mutu shikenan sarautar tabar Ahalin gidansu takoma kan wata zuri'a sannu ahankali za'amanta da zuri'arsu ma gaba daya a doron kasa. Bisa wannan daliline yabaza yaransa afadin duniya suna ziyartar bokaye da manyan likitoci har tsawon shekara uku domin asamo masa magani Amma ba'adaceba,kuma Duk wajen bokan da akaje saiyace indai sarki Lubainu yanso yasamu lafiya irinta da namiji toko saidai yaje birnin Hindu yayi tsirata a gaban sarauniya Mauzuratul shardila ya fadi bukatarsa bayan yayimata yanka sannan ne bukatarsa zata biya shikuwa sarki Lubainu yace bazai taba kaskantar da Kansa irin haka ba ace har mutane suga tsiraicinsa don kawai biyan bukata Lallai daya Aikata haka gwara yamutu babu haihuwa. Dukkanin samoyan sarki Lubainu da makusantanshi da Aminansa babu Wanda baibashi shawari akan yaje gaban sarauniya mauzuratul shardila baya Aikata abunda aka uwarceshi domin yasamu Haihuwa, Amma Sai yaki. Duk Wanda yamatsamar akan yaje karshenta batawa sukeyi da shi yadaina kulashi, dukkuwa kusancin dake tsakaninsu dashi. Haka dai sarki Lubainu yaci gaba da tayuwa haryacika shekara sha biyar akan mulki bayatare dayasamu da ba bare jika. Kwatsam! Sarki Lubainu wata rana yayi sha'awar yafita daji yayi farauta, don haka saiyadibi dakarunsa mutum shida kacal! Domin suyi masa rakiya, sukayi shiri irin na mafarauta suka shiga daji.s A farkon yammaci sarki Lubainu yafito wannan farutan, alokacin da rana tayi sanyi launin garin sunyi shudi, alokacin anayin wata iska mai sanyi atakaice dai yanayin da akeciki yanayine mai dadi, uanayin da yakesa mutum nishadi da farinciki. Duk da sarki Lubainu ya kasance sadauki, kuma GORZON MAYAKI mai TATWATSA MAZA a FILIN DAGA Amma Sau uku kacal yataba fita farauta a rayuwarsa, don haka baisan sirrin dajiba sosai, kuma baisan sirrin dabbobin daji ba. Sai da sarki Lubainu suka shafe kusan sa'a biyu da rabi a daji suna yawon farauta Amma ko zomo basu kamoba. Hatta ysuntsayen da suke Yawo asararin samaniya sunkasa hatbo ko guda daya. Al'amarin da ya fusata sarki Lubainu kenan yadubi wa'yannan dakaru guda shida a fusace ya daka musu tsawa sannan yace, Amma tur! Da Ku! Tabbas kunji kunya!! Nazaboku ne saboda dukkanku kunkasance 'ya'yan manyan mafarauta, Amma kunkasa farauto koda Kwaro ballantana dabbar daji ko tsuntsayen da suke giftawa ta saman knmu. Towai shin sokuke mukoma gida cikin Abun kunya agammu babu komai a hannunmu ko yaya ?? Koda jin haka Sai babban cikinsu Wanda shine Dan sarkin mafarauta na garin yarisina Ga sarki Lubainu yace, agaskia Akwai matsalar da tafaru akan wannan lamarin. Yau kusan sati uku kenan dazuzzukan dake yankin birnnan namu sun zama wayam! Duk dabbobin dake cikinsa sun face bat! Tamkar Anyi ruwan sama Andauke. Amma mahaifina yace yanaganin wasu bakin mafarautane suka gifta ta wannan dajin kuma suna da yawan gaske, Ayari ne guda, yana zaton sune suka kwashe mana komai."" Kodajij wannan batu Sai ran sarki Lubainu ya baci, zuciyarsa tayi bakikkirin sayake dakawa Dan sarki mafarauta tsawa har said a hantarsa ta kada yace, yanzu daman Ansan da wannan matsalar ba'azo an sanar daniba?? Dan sarki mafarautan yasake risinawa yace, ya shigabana mahaifina ya sanar da waziri, kuma waziri yasa Ana bincike akan lamarin, nayi tsammanin Sai abun yafi karfinsa ne zai sanar dakai"". Koda sarki Lubainu yaji haka Sai yayi kwafa yacije lebe sannan yace, aikuwa idan nakama wa'yannan bakin mafarauta Sai sun biya duk abunda akarasa acikin dazuzzukanmu kokuma su fanshi laifin su da rayukansu,,,,,"" Kafin sarki Lubainu yagama rufe bakinsa Sai sukaga giftawar wani mutum cikin wani azabebben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya ya wuce fit! Tagabansu ya bausa cikin daji , kafin giftawar ido yabace bat! Aikuwa Sai sarki Lubainu ya sakatwa dokinsa linzami yabi wannan mutum, cikin hanzari suma dakarun suka rufa masa baya. Sarki Lubainu uacigaba da baiwa dokinsa kaimi yanamai irin wani azabebben gudu tamkar zai tashi sama, Amma Dakar ya iya hango mutumin daya gotasu a can gaba nesa dashi. Ashe ma macece acikin shigar kayan fatar damisa. Koda sarki Lubainu ya hango wannan mace tana faman wannan azabebben gudu na ban Al'ajabi kuma yaga Ashe dawata damisa suke tsere. Damisar gudu take iya karfinta domin ta ceci ranta Amma tazarar dake tsakaninsu da wannan macen baiwuce taku biyar ba, Ako yaushe za'aiya cimma damisar, Nan take sarki Lubainu yacika da tsananin mamaki kuma ya dimauce sakamokon dalilai biyu. Dalili na farko shine, Duk da cewa bayan wannan macen yake hangowa mai kyan kira da siffa kamar ta ba. Gashin kanta kadai ya isa mutum yasa ya dimauce saboda ya zubo harkan kasan kugunta saboda tsawonsa. Duk da cewa an tartare gashinne a gadon bayanta Sai tarwatsewa yakeyi acikin iska saboda yawansa ya kasance yanada tsananin baki gami da kyalkyali da hasken da mutum zai iya gamin fuskarsa akansa tamkar madubi. Dalili na biyu kuwa shine, sarki Lubainu baitaba ganin bil'adama ba mai karfin gudun wannan mace ba wacce take kokarin kurewa damisa gudu. Nan da nan zuciyarsa ta Aiyyana masa tambayoyi. KUMA WAI SHIN ITA WANNAN JARUMA MACE WACE IRIN SHAIDANIYACE ITA HAR DA WANNAN KATUWAR DAMISAR ZATA GUJE MATA. KOKUWA TA KASANCE ALJANA BA MUTUM BA.?? Sarki Lubainu yabaiwa kansa Amsar da yayiwa kansa wannan tambaya kawai saiyaga wannan mace ma'abociyar kyau tayi sufa tafadi cahn gefe ta chapo wuyan namisar suka kama kokawa a kasa. Kawai Sai jarumar ta miki tsaye ta rike makoshin damisar da hannu daya tayiwa damisar hajijiya Asama say uku ta fyadata da kasa ta takemata wuya da kafarta guda. Nan fa damisar tafara kakakin Mutuwa inbanda jelarta da kafarta babu abunda take iya motsawa kafin sarki shahran ya iso garesu tuni damisar tazama gawa. Koda wannan jarumar taji sukuwar dawakai abayanta sai tajuyo saita kurawa sarki Lubainu idanu batare da tayi wani motsiba ko taji wani tsoro ba. Sarki Lubainu yadira a gabanta yajuyo yana mai yimata nuni da tabashi wannan damisar. Jarumar ta wunkura kamar zata mikamasa wannan damisar. Amma Sai itama ta daka tsalle sama cikin shammata takaimasa duka da kafarta a girjinsa. Duk da tsananin karfi irin na sarki Lubainu said a yayi baya taga taga kamar zai fadi, yzamana suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa acikin tsananin zafin nama. Juriya da bajinta. Ai kuwa Anafara wannan gumurzu ne Sai sarki Lubainu yacika da tsananin mamaki domin a iya rayuwar gwagwarmayarsa baitaba haduwa da jarumin da karfinsu na damtse yazo daya ba irin wannan jaruma. Komai karfin kato da iya fadansa akaron farko yake gamawa da shi Amma gashi wai 'ya mace ya shafe 'yan dakiku da ita. PAGE 46 IS MISSING. Wannan bakuwar jaruma kasa, kuma ya kwace wannan damisa dake hannunta ta kowane hali, Idan ba hakaba kuwa ta karya Alkadarin jarumtakarsa kuma ta bashi kunya agaban dakarunsa. TUNDA DAI TA'IYA FADA DA HANNU GASHI HARMUNYI KUNNEN DOKI , BARIN GWADA IYA YAKINTA DA MAKAMI NAGANI. Koda Aiyana hakan acikin ransa Sai sarki Lubainu yadubi jarumar a fusace yace, yake wannan budurwa INA gargadinki da ki mika wuya agareni na kamaki amatsayin mai laifi, kuma ki bani wannan damisar dake hannunki inbahaka ba kuwa zaki tilastani nayi Amfani da takobina akanki, kuma banaso naragewa wannan kyakkyawar sura naki kyawu. Koda jin wannan batu Sai jarumar tayi wani dan guntun murmushi Ga

Chapter 13 of 19