Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki,kuma nayi maka alkawari cewar zan taimaka maka da raina da jikina da dukiyata har izuwa lokacin da bukatarka zata biya.Ina so ka gama dukkan shirye shiryenka a yau din nan amma zan shiga nawa shirin kuma yanzu zamuje dakin da wannan Allon Sihiri yake na daukoshi in yaso gobe da sassafe a lokacin da alfijir ya keto zamu bar garin nan mu durfafi BIRNIN KIMRAS domin mu gana da SARKI DARMASU mu sanar dashi bukatarmu ta barin wannan Allon Sihiri dake hannunsa.Kayi sani cewa bana tunanin cewa Sarki Darmasu zai amince ya bamu wannan barin Allo dake hannunsa domin yau shekara kusan bakwai kenan muna yaki a tsakanin kasashenmu akan mallakar Allon Sihirin amma abun ya gagari kowanne bangare.Idan har kaga ya amince da fito da Allon Sihirin dake hannunsa saidai idan shima yana da wata bukatar dabam.Babban abinda yake bani tsoro shine kamar yadda nake da tsaro akan nawa Allon Sihirin haka shima Sarki Darmasu yake da tsaro akan nasa,kuma bazamu iya rabashi da Allon ba da karfin damtse kona yaki da tsafi.Sa'adda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ya rasa abinda yake masa dadi,kawai sai ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,nikam bani da wani zabi wanda yafi na jarrabata sa'ata kawai don haka babu gudu babu ja da baya a cikin wannan tafiya.Koda jin haka sai fuskar sarauniya Akisatul Sauwara ta fadada da murmushi tace biyoni muje.Tana gama fadin hakan ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuma saiya bita da sauri a baya. SHIN YARIMA LUBAINU ZAI SAMI NASARAR SAMO ABINDA YA FITO NEMA? A WANNE HALI YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA SUKE CIKI? INA LABARIN MATAR YARIMA LUBAINU (YAZARINA) DA MAHAIFINSA? ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI DARMASU NA BIRNIN KIMRAS DASU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ITA DA YARIMA LUBAINU YAYIN DA SUKA JE GARESHI DON KARBAR BARIN ALLON SIHIRIN HANNUNSA? SHIN ZAI AMINTA YA BASU WANNAN BARIN ALLON SIHIRIN? Mu hadu a ALLON SIHIRI 2 don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part A An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Sarauniya Akisatul Sauwara ta durfafi wani bangare daban na cikin gidan sarautar tayi ta kutsawa ta cikin wani surkuki mai lunguna da yawa har saida suka yi tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar wani gida.Koda masu gadin gidan suka hango Sarauniya Akisatul Sauwara tare da Yarima Lubainu sun tunkaro inda suke sai sukayi sauri suka bude kofar gidan tun kafin su iso.Suna isowa kuwa masu gadin suka risina suka gaida sarauniya.Ita kuwa ko kallonsu batayi ba ta kunna kai cikin gidan Lubainu na take mata baya.Babu komai a cikin wannan daki face kayna tarihi iri iri na kasar musamman abinda ya danganci kayan yaki kamar takubba,masu,Garkuwa da sauransu,kai harda kayan kyale kyale dana kawa kala kala.Nanfa Yarima Lubainu ya zama dan kauye ya kama kalle kalle da waige waige.Saida suka iso tsakiyar gidan suka iske kwalbar sihiri wacce aka dorata akan wani zagayayyen tubalin gini.A cikin wannan kwalba ne aka sanya Allon Sihiri.Nan take Lubainu yayi arba da wannan Allon Sihiri,ya dubi kwalbar da kyau yaga babu wata kofa ko huda a jikinta wacce za'a iya zura hannu a ciki a dauko Allon.Da isowarsu gaban kwalbar sihirin sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace,kayi iya kokarinka da duk abinda kake takama dashi wajen fasa wannan kwalba don dauko wannan Allon sihirin mu ga abinda zai faru.Ai kuwa kafin ta gama rufe bakinta tuni Yarima Lubainu ya dauko wani katon barandami ya sari wannan kwalbar sihirin da dukkan karfinsa.Maimakon kwalbar ta dare ko ta tarwatse sai shi barandamin ya karye bal,ya rabe gida biyu.In banda tarwatsin wuta daya tashi akan Gilashin babu abida ya sameshi.Al'amarin dayai mutukar girziza Yarima Lubainu kenan yaja da baya a dan tsorace.Ita kuwa sarauniya Akisatul sauwara sai ya bushe da dariya ta sake duban Yarima Lubainu tace to ai saika jarraba Karfin sihirin tsafinka mu gani.Lubainu bai karaya ba sai ya matsa dafda kwalbar sihirin ya shiga karanta wadansu dalasimai na tsafi yana shafar kwalbar da tafin hannunsa.Kwatsam sai yaji wata irin iska mai karfi ta sureshi ta baya ta gwarashi a jikin bangi ya fado kasa a galabaice. Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a karo na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya kai Lubainu kamar yadda na gaya maka da farko babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya isa ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan kwalba face ni.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta shafeta da hannunta na hagu.Take kwalbar ta rabe gida biyu kamar an yanke lemon bawo.Kawai sai ta sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace dashi,zo kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa Allon idanun.Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake gida biyu.Kuma bazai taba karantuwa ba a haka face an jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi ajiyar numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun karayar zuciya yace,Ai wannan Allon dake hannunki bashi da wani amfani idan ba'a samo daya Allon bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara tayi murmushi tace to ina tabbatar maka da cewa idan ma an samo Allon na biyu an hada da nawan rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an hada dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar da Allon cikin wannan kwalbar.Take kwalbar ta koma ta manne tamkar bata taba rabewa ba biyu.Akisatul Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga cikin wannan gida Lubainu yabita da sauri.Nan dai suka yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima Lubainu sai ya tsaya.Akisatul Sauwara ta juyo tana mai yi masa wani kallo mai dauke da murmushi da ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma izuwa masaukinka ka sake hutawa,amma ina gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na bayan turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in yaso gobe da safe muyi haramar tafiya.Tana gama fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin turakarta kuyangi na gyara mata hanya.Yarima Lubainu ya juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi masaukinsa zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi ko kuma KAUNA.Kamar yadda Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada haka al'amarin ya kasance wato da yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa jini dake bayan turakarta.Yana isowa wajen sai ya iske sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar yaki rike da takobi.Yana isowa sai shima aka miko masa sulke takobi da garkuwa.Ba tare da gardamar komai ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki karbar garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai shawartarka daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya baka mamaki.Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke baki rike garkuwa ba a matsayinki na 'ya mace nima ba zan rike ba.Akisatul Sauwara tace,shi ke nan muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura.Kafin Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka tsalle ta kawo masa wawan sara a kafada.In ba don Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin tsananin zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu.Nan fa suka kacame da azababben yaki ta rinka kai masa mugayen hare hare da wani irin azababben zafin nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi mamaki tun da yake haduwa da mazaje bai taba haduwa da mai kamar jarumtakarta ba.Bisa dole shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare haren nata amma sai yaga duk da haka tana neman kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi sakaki zata iya gamawa dashi.Nan fa shima ya fara maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama abin tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin azababben yakin dasu sarauniya ke yi.Saida suka dauki dogon lokaci a haka dayansu bai sami nasarar koda shafar jikin abokin gwaminsa ba.Al'amarin dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin shi kuwa ya fara haki.Koda ya fuskanci cewa lallai zaiji kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon fadan ya hada dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai ya shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa amma tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta guda tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi tsalle sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi wuf ya mike tsaye Zumbur.Yana mai gyara tsayuwa a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin tafiyar da zanyi tare dakai domin na gamsu cewar kai jarumi ne na kwarai.Koda jin wannan batu sai ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar jarumtakarsa.Amma sai ya boye fushin nasa bai nuna mata ba.A wannan lokaci duk sun jike Sharkaf da gumi don haka sai ta shawarce shi akan yaje yayi wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai gobe da safe yayin wannan tafiya.Nan take kuwa Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya bayar gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda itama ta fada cikin wasi wasi domin ta kasa tantance irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na gajiya?Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da zata kaita turakarta.Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin tafiya,kuma bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta ba.Su biyu rak suka fice daga birnin Rauhul Bagadar bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran gari. Prince Auwal Auwzab Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka sakarwa dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya basu yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin ko kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu wanda yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata mu yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu nake son na sanar dake hakan amma sai na kasa don kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai tun kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni da kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi kunnen doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a karo na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin sa'a kuwa sai suka hango wata fadama a can gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar akwai duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu suka kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance jakar guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin kafashi.Al'amarin dayai mutukar baiwa Yarima Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba? Ai mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a wannan fannin.Sa'adda Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar yadda nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya ta ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi 'yar guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba zai iya wulakantashi ya wuce abinsa.Ni yanzu na ajiye karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina daidai da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta biya mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba da bina har izuwa lokacin da burina zai cika?Ki tuna fa cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai zuwa goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin Allon Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi murmushi tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai zama gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi.Abida ya bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin bukatarsa ta biya?Abinda zuciyarsa keyi masa wasi wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan tafiya?A zahiri dai bai ga wani abu dazata amfana dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta ba.Nan dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya Akisatul Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya kwance jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka fara jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye masu shawagi a sama.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da sauri ta tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke shirin biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin mamaki Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma kin dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace naje na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara kokarin cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga cikin dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne yaji yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama ci.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji takun sawu a bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare takobinsa ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda ya tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye da wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce ta bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri da sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya taso a rayuwarsa bai taba ganin 'ya mace haka ba a rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya danne zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da cikakkiyar lafiyar da zaiji wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk da cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta a hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi cikin murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya ta? Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi yake sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka sai Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa suka zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin dumin tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai ya mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan ya dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna daf da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar taku uku a tsakaninsu.Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi ya dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki kwanta kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin bacci? Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin daji.Tabbas ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan dalili ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda nake so dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta cikin alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya bazan iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani cewa babu wani 'da namiji dazai ganki a cikin wannan yanayi bai rude ba ya kamu da sha'awarki da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba sanin 'ya mace ba kuma wanda yake nisantarku dole ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda baka taba sanin 'ya mace ba nima ban taba sanin wani 'da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina mai tuna maka cewa samun yin barcina yana gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin tantin taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa Yarima Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga cikin tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina Akisatul Sauwara ke kwance ya kwanta.Yana kwanciya sai zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin gwagwarmayar dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa barci ya saceshi har yana munshari bai sani ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa sai ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda ke kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba akan shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan shimfidar wato an cireshi daga cikin kwalbar data lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije ya dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da mahaifinka ya baka kafin ka baro gida.Cin amana ne idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu zaka sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama aiyana hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji motsin taba.Al'amarin d yayi matukar bashi mamaki kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi gangancin barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai Yarima Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya wanke fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan abu dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe a cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya da daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye jarrabar tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun siffarta kuma ya kamu da matukar sha'awarta.Bisa mamaki sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar Yarima Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi kokarin guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin sa'adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin ya rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma yaji bata amsa ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi nemanta kuma azo a sace wannan Allon Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon Sihirin zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin da Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta juya da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi farauta ta harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa haba ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da kin sanar daniba. Koda ya hangota sai ya mike zumbur!Da sauri ya tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaya zaki tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba?Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka bari mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a saukake.Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara kokarin fisge wannan tsunstu data harbo.Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta ki don haka sai ya zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna suka kama cin nama tsuntsun.Tsawon yandakiku suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin da dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar dake kadawa.Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,idan baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin dayasa kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin ban kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki? Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da daria sannan tace,tabbas kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana sami nutsuwa.Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba hakurinka shin zaka kasance mai tsare mutuncina bisa alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juma a cikin wannan tafiya?Tabbas ka kiyaye wannan jarrabawa ka hayeta.Dalili na biyu kuma wanda yasa na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine domin na jarraba amanarka na gani shin zaka sace Allon Sihiri na ne ka gudu?Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka sace Allon Sihirin ba alhalin kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo shi.Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da sannu zamu kai ga wannan matsayi.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata idanu.Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar guzurinsa.Itama Sarauniya Akisatul Sauwara sai mike tsaye ta bishi izuwa cikin tantin ta shiga kimtsa na ta kayan.Har suka gama kimtsa komai basuce da junansu kala ba.Nan take suka hau dawakansu suka nausa cikin daji suna masu cigaba da tafiya.Sai

Chapter 3 of 19