Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kafin ka baro gida.Cin amana ne idan ka dauki wannan Allon Sihiri,Amana,cika alkawari da fadin gaskiya sune guzurin da mahaifinka ya baka,kuma idan har ka koyayesu zaka sami nasarar abinda ka fito nema.Koda gama aiyana hakan sai ya juya ya fice daga cikin tantin.Yana fitowa ya dubi gabasa da yamma,kudu da arewa amma bai hango Akisatul Sauwara na kuma baiji motsin taba.Al'amarin d yayi matukar bashi mamaki kenan domin baiga dalilin dazai sa tayi gangancin barin Allon Sihirin ta ba a fili haka.Nan dai Yarima Lubainu ya nufi gabar wannan korama yaje ya wanke fuskarsa ya kuskure bakinsa.Ashe duk wannan abu dake faruwa Sarauniya Akisatul Sauwara na labe a cikin wata duhuwa kuma tana kallon duk abinda Yarima Lubainu keyi.Ta buya ne domin ta jarraba amanarsa ta gani shin zai iya rike amanar.A jiya da daddare ta jarraba hakurinsa kuma ya haye jarrabar tunda har gari ya waye bai kusanceta ba duk da cewa ya dimauce da ganin tsananin kyawun siffarta kuma ya kamu da matukar sha'awarta.Bisa mamaki sai sarauniya Akisatul Sauwara taga cewar Yarima Lubainu bai dauke Allonta na sihiri ba yayi kokarin guduwa.Maimakon hakan ma sai taga cewar hankalinsa ya tashi bisa rashin ganinta domin sa'adda ya wanke fuskarsa da bakinsa a cikin wannan korama sai ya kasa komawa cikin tantin ya rinka kai kawo a harabar wajen yana leke leke a kowacce kusurwa yana kwalla mata kira amma yaji bata amsa ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsa kenan domin yana tsoro kada ya tafi nemanta kuma azo a sace wannan Allon Sihirin.Kuma yana tsoron kada ya dauki Allon Sihirin zargi ya shiga tsakaninsa da Sarauniya Akisatul Sauwara.Lokacin da Akisatul Sauwara taga halin da Yarima Lubainu ya shiga sai tayi murmushi ta juya da baya ta nausa cikin daji.Sai da taje tayi farauta ta harbo wani tsuntsu sannan ta dawo.Tana isowa bakin tantin ta iske shi a zaune yayi tagumi cikin alamun tsananin damuwa.Koda ya hangota saiya mike zumbur!da sauri ya tareta yana mai cewa haba ranki ya dade yaya zaki tafii cikin daji batare da kin sanar daniba.ALLON SIHIRI Littafi na daya(2) Part D Koda ya hangota sai ya mike zumbur! Da sauri ya tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaa zaki tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba? Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka bari mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a saukake. Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara kokarin fisge wannan tsunstu data harbo. Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta ki don haka sai ya zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna suka kama cin nama tsuntsun. Tsawon yandakiku suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin da dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar dake kadawa. Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,idan baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin dayasa kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin ban kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki? Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da daria sannan tace,tabbas kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana sami nutsuwa. Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba hakurinka shin zaka kasance mai tsare mutuncina bisa alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juna a cikin wannan tafiya? Tabbas ka kiyaye wannan jarrabawa ka hayeta. Dalili na biyu kuma wanda yasa na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine domin na jarraba amanarka na gani shin zaka sace Allon Sihiri na ne ka gudu? Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka sace Allon Sihirin ba alhalin kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo shi. Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da sannu zamu kai ga wannan matsayi. Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata idanu. Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar guzurinsa. Itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta bishi izuwa cikin tantin ta shiga kimtsa na ta kayan. Har suka gama kimtsa komai basuce da junansu kala ba. Nan take suka hau dawakansu suka nausa cikin daji suna masu cigaba da tafiya.Sai da suka shafe sa'a hudu da rabi suna tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan Yarima Lubainu ya matso kusa da Sarauniya Akisatul Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta yace,waishin tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da muka nufa? Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa dadina dakai kenan ka cika zumudi da gaggawa. Ai idan kayi hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru bata kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa'a hudu suna tafiya. A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a bakin wani katon dutse. Anan suka kwana washe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu riski wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu mugayen dabbobi ko kwaruka saidai kaga sun yi musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA! Kuma RUWA BA SA'AN KWANDO BANE. A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka Yarima Lubainu ya hango wani babban gari a gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu ya wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine ginen birnin cikin al'ajabi.Koda Sarauniya Akisatul sauwara ta lura da halin da yake ciki sai ta bushe da dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani kunya mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga cikin birnin tukunna. Koda jin wannan Batu sai Yarima Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin yanzu kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine Birnin Kimras inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara ta jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka sai abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi saboda Sarki Darmanu ba karamin 2shaidanin Mutum bane.A yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin wani abu domin ya cutar damu,don bani da tabbacin cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka zo masa da ita. Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da iya yaki KARE JINI BIRI JINI mukeyi. Sau tara muna fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki. Bisa sa'a ne kawai na samu na tsira daga sharrin tsafinsa saboda tsarin dana samu tun daga kakannina. Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta suna daf da shiga cikin birnin ne, Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a bayansa,shima zai shiga cikin birnin.Cikin Ladabi Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu kallo ya lura cewa baki ne don haka saiya dubesu yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne a garin nan ko? Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin yanayi mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da gani kun fito daga babban gida kuma kun sami tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don kada ku fada cikin tarkon maketacin sarkinmu.Ina mai sanar daku cewa bisa al'adar wannan mugun sarki namu duk bakon daya shigo garin nan kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a kaishi kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a duniya sannan zai tsira da rayuwarsa. Yanzu zan taimake ku zna bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda zai ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso indan gari ya waje sai ku saje da 'yan gari ku aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama fadin hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu yace,idan sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar 'yar uwar taka saiya rabaka da ita har abada. Koda jin haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai jinjina al'amarin ba tare da yace kala ba. Nan dai tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai bin wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin. Su kuma suka ci gaba da jan limzamin dawakansu a hankali suna yin tafiyar san'da suna waige waige cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin da suka yi 'yar doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin zai iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka turoshi ya yaudare mu ya cutar damu. Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da Yarima Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai ya tsaida nasa dokin suka kurawa tsohon idanu kawai yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace 'ya'yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka kuka daina tafiya? Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon banza!bakin mayaudari na gane ko kai waye.Maza ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu tattauna bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da tsohon yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara saiya bushe da mahaukaciyar dariya cikin karfin murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza nan take ya rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar shigar yaki. Sarki Darmanu ya kasance katon mutum mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma gashi kakkaura mai murdadden jiki gami da tarin kwanji da jijiyoyi. KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA. Wadansu bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe. Rigar dai Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon wando da dogayen takalma duka na bakin karfe. A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa ce wadda akayi ta da zallan dutsen lu'u lu'u mai nauyin gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya rabata da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya rike. Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro birnin ki naga duk abinda ya faru tsakaninki da Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa sa'adda kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin Allon Sihirin dake hannuna. Tabbas dake dashi kuma sami tabin hankali har da kuke tunanin zan karbeku hannun bibbiyu na yarda da bukatarku. Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan rana wacce zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki taho har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na gano yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar dakika adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu daga sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan hallaku na dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na biya tawa bukatar dashi. Koda gama fadin hakan sai Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama kamar an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk su biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk su biyun suka kaucewa saran suka fado kasa daga kan dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar tuffa. Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai takubban nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu suka runtsume da azababben Yaki. Shegen kaya Uban mayaudara Sarki Darmanu. 6 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part E Sannan su dauke mu mu ci gaba da tunkarar gidan Boka Darbusa.Yanzu ga dawakai nan guda biyu dana tanadar muku sai ku hau mu kara gaba.Ba tare da gardamar komai ba kuwa Lubainu da sarauniya Akisatul Sauwara suka hau wadannan dawakai suka bi bayan Sarki Darmanu suka fice daga cikin birnin gaba daya.Nan dai suka nausa cikin daji suka yi ta tafiya ba sassauci har suka shafe sa'a goma sha biyu ba tare da sun hadu da wani mugun abu ba.Duk wata muguwar dabba idan ta hangosu daga nesa sak kaga ta ratsa ta sauya hanya,haka ma mugayen aljanu.Yan fashi kuwa da zarar sun hango Sarki Darmanu tare dasu Lubainu sai kaga sunyi ta kansu saboda sun san cewa Bakin Rijiya ba wajen wasan yaro bane.Adaidai wannan lokaci ne magriba ta riskesu kuma a sannan ne suka shigo farkon dajin da wadannan tsuntsaye na sarki Darmanu suke.Da shigarsu cikin dajin sai Sarki Darmanu ya daga kansa sama yana mai karanta wadansu dalasimai na tsafi.Faruwar hakan keda wuya sai Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka ji wata irin iska mai karfin daga sama ta fara kadawa.Kwatsam sai ga wadansu jibga jibgan tsuntsaye guda uku sun bayyana suna masu saukowa kasa.Duk su ukun a gaban sarki Darmanu suka sauka suna masu dukar da kawunansu alamar cewa sun kwashi gaisuwa.Nan take sarki Darmanu ya shafa kawunan wadannan tsuntsaye yayi magana dasu a cikin yaren tsafi.Faruwar hakan ke da wuya sai tsuntsayen suka bude fukafukansu suka sake tashi sama suka luluka a cikin gajimare har suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba.A sannan ne Sarki Darmanu ya dubi Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara yace,anan zamu yada zango mu dan huta nan da cikar kamar sa'a uku wadannan tsuntsaye zasu dawo su daukemu mu ci gaba da tafiya.Nan take suka kafa tanti suka fidda abincinsu na guzuri suka kama ci suna hira.kafin Yarima Lubainu yayi wani abu da hannunsa tuni Sarauniya Akisatul Sauwara ta miko masa,ya zamana cewa tana kyautata masa,bata son taga ya yi wani abu na wahala da kansa face ta taimaka masa.Bayan sun gama cin abincin ne Akisatul Sauwara ya mike tsaye ta dubesu tace,tana son ta zagaya bayan wata katuwar bishiya dake can gabansu tayi bawali.Tana gama fadin hakan sai ta juya ta nufi inda wannan bishiyar take.Tana isa kuwa ta zagaya bayan bishiyar ta bace musu da gani.A wannan lokaci ne Sarki Darmanu ya dubi Lubainu cikin murmushi yace,na fuskanci cewar Akisatul Sauwara ta kamu da matukar sonka.Koda jin haka sai mamaki ya kama Lubainu ya dubeshi yace,wacce irin magana kake yi haka?Ai wannan bayani naka daidai yake da tatsuniya a cikin kunne na,domin babu yadda za'a yi sarauniya Akisatul Sauwara ta so ni saboda kwararan dalilai guda uku.Dalili na farko shine a rayuwarta bata tabayin soyayya ba don babu wani 'da namiji daya taba burgeta.Dalili na biyu shine ta san cewa ni ba cikakken namiji bane,kaga kuwa bazata so ta auri wanda baya haihuwa ba tazo ta rasa magaji.Dalili na uku shine ta fini kyau,ta fini mulki,kuma kasan su mata sun fi son su auri wanda yafi su komai.Koda Yarima yazo nan a zancensa sai Sarki Darmanu ya bushe da dariya sannan dubi Lubainu cikin nustuwa yace,Lubainu kai saurayi ne matashi wanda har yanzu yake daukar darasi a cikin karatun duniya,sabanin magidancin mutum kamata wanda yake da matan aure ashirin da hudu.Babu irin soyayyar daban yi ba a rayuwata,dukkanin alamomin SO da KAUNA sun bayyana akan fuskar Sarauniya Akisatul Sauwara a gareka da kuma alamomin kauna a zahiri.Idan ma baka yarda da abinda nake gaya maka ba yanzu nan gaba zaka gani a lokacin da Kura takai bango.Ka bar ganin cewar tasan kana da mata a gida mai jiran ka koma gareta.Hakan ba zai hana taso ka ba saboda shi SO bashi da hijabi kuma babu abinda yake iya tareshi idan har ya yunkuro.Har Lubainu ya bude baki zaice wani abu sai ga Sarauniya Akisatul Sauwara ta dawo,don haka sai yai shiru baice komai ba yana ta nazarin abinda Sarki Darmanu ya gaya masa.Haka dai Akisatul Sauwara tazo ta zauna tare dasu aka ci gaba da hira,inda Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu tace,yanzu kai a ganinka ta yaya zamu jewa boka Darbusa?Shin zamuje masa ne cikin lumana da nasiha ko kuwa zamuje masa ne ta tsiya tsiya? Koda jin wannan tambaya sai Sarki Darmanu yayi murmushi cikin ajiyar zuciya sannan yace,ni ta yaya kuka zo mini keda Lubainu?Sarauniya Akisatul Sauwara tace ai kai baka bari mun iso fadarka ba tun a daji ka taremu kana mai badda kama kazo mana a siffar tsoho don ka yaudaremu ka cutar damu.Dajin haka sai Sarki Darmanu yayi dariya kuma ya hade fuska yace,to kiyi zaton yaudara da tarkon tuggu ninki wanda nayi muku daga Boka Darbusa tunda kin san cewa ya ninka ni sau dari A komai.Koda jin wannan batu sai hankalin Sarauniya Akisatul Sauwara dana Yarima Lubainu ya tashi domin sun fuskanci cewar hadarin dake gabansu na fuskantar Boka Darbusa ba kadan bane.Kodai su sha wahala ko kuma su rasa rayuwarsu gaba daya.Haka dai suka ci gaba da hira har lokaci ya cika sai ga wadannan manyan tsuntsaye guda uku na Sarki Darmanu sun dawo suna masu saukowa kasa daga can kololuwar sama.Cikin gaggawa su ukun suka mike tsaye suka hada nasu i nasu su,kowannensu ya hau kan tsuntsu guda.Sarki Darmanu ne akan gaba,Sarauniya Akisatul Sauwara a tsakiya sannan Yarima Lubainu.Lokaci guda tsuntsayen uku suka bude fuka fukansu suka tashi sama suka luluka izuwa can sama suna masu giftwa ta gaban Rana wacce ke shirin faduwa ta zama ja jawur.Abin gwanin ban sha'awa ga dukkan halittar da take kallo daga kasan Turba.Kamar yadda Sarki Darmanu ya fada haka al'amarin ya kasance wato saida suka shafe kwana hudu da yini daya suna tafiya a sararin samaniya bisa wadannan manyan tsuntsaye sannan suka hango gidan boka Darbusa a nesa kadan dasu.ALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part F Sannan suka hango Gidan Boka Darbusa a nesa kadan dasu.Babban abinda ya baiwa Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara a cikin wannan tafiya shine a tsawon duk kwanakin da akayi ko sau daya tsuntsayen dake dauke dasu basu gajiya ba,kuma ba a sauko kasa an yada zango ba.Haka kuma duk su ukun babu wanda wata bukata ta kamashi ta bawali ko bayan gari saidai kawai idan sun gaji da zama akan tsuntsayen su kwanta suyita sharar barci abinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba.Da yammaci ne sakaliya suka hango wannan gida na Boka Darbusa wanda saidai a kirashi da aljannar duniya saboda ginuwarsa da kawatuwarsa.Tunda Yarima Lubainu yazo duniya ko a bakin masana tarihi bai taba jin labarin gida mai kyan na Boka Darbusa ba.Saidai babban abin takaice shine a tsakiyar dokar daji aka zo aka gina wannan gida wanda aka bata miliyoyin dinare wajen ginashi.Kai da gani kasan cewa in ba rikakken Boka ba wanda ya cika hatsabibin gaske babu wanda zai iya gina irin wannan gida a dokar daji haka ya zauna a cikinsa.Da saukar tsuntsayen uku kusa da kofar gidan da tazarar kamar taku ashirin sai kawai suka ga an bude kofar gidan wacce ta kasance katuwar gaske.Kofar na budewa sai sukaga wadansu kyawawan kuyangi su goma sha biyu sun fito daga cikin gidan a jere a layi.Shida a hannun dama ragowar shidan a hannun hagu.Dukkaninsu suna dauke da wani dan karamin kwando wanda akayi shi da karfen jauhar.Kowanne gwando an cikashi da wani irin jan fure mai tsananin kamshi.Gaba dayan wadannan kuyangin suna sanye ne da dogayen riguna masu launin kore wadanda akayi su da Miski.Babbar cikin kuyangin ce kadai take da riga kala dabam mai ruwan kwai wacce akayi mata dinki mai siffar dawisu.Tsananin kyawun wannan kuyanga gami da kyawun shigar datayi dole ne ya rudi kowanne lafiyayyen 'da namiji.Cikin tafiyar kasaita da karairaya tamkar macijin gona haka wannan kuyanga da sauran yan uwanta suka iso daf da su sarki Darmanu suka risina sukayi gaisuwa gami da yimusu barkda da zuwa.A sannan ne shugabar kuyangin ta dago kai ta dubi su Lubainu tace lale marhaban da manyan baki na musamma,lallai mai girma Darbusa yana farin ciki da zuwanku kuma yace nayi muku jagora izuwa cikin fadarsa.Koda jin wannan batu sai Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka sauki daha kan wadannan tsuntsayen.Suna sauka sai tsuntsayen suka sake bude fuka fukansu suka tashi sama.Kafin kiftwar ido sun kule a cikin sararin samaniya.Koda ganin haka sai mamaki ya kama Lubainu da Akisatul Sauwara suke a cikin zuciyarsu,Wai shin su wadannan tsuntsaue wane iri nesu?Gashi sunyi tafiyar kwanda hudu da yini daya basu yada zango ba,kuma da saukarsu yanzun nan sun sake tashi sama ko hutawa basuyi ba bare su nemi ruwan sha ko abinci.Anya kuwa wadannan tsuntsaye ba sihirtattu bane?.Amsar da suka kasa baiwa kansu kenan.Ba tare da fargabar komai ba kuwa su Sarki Darmanu suka bi wannan shugabar kuyangin a baya suka nufi cikin gidan.Su kuwa sauran kuyangin tuni suna kan gaba suna zubar da wannan Jan fure mai kamshi a kasa su Lubainu na bi ta kansa.Da shigarsu cikin gidan sai duk su ukun suka kama kalle kalle da waige waige domin sun zama cikakkun yan kauye duk da cewar dukkaninsu sarakai ne masu tarin abin duniya.Ba komai ne yasa suka zama yan kauye ba face ganin kayan kawar da idanunsu basu taba gani ba da abubuwan al'ajibi wanda ko a mafarki da hasashe basu taba zaton wanzuwarsu ba.A cikin wannan gida ne suka ga wani katon Lambu wanda girmansa yafi na wani dan karamin garin kuma kyawawan bishiyoyin dake cikinsa da furanni tamkar halittarsu akayi a ciki ba shukasu akayi ba sai kayi zaton idan kayi musu magana zasu amsa.Barewa,tsuntsaye da kwaron nan mai suna malan buda mana littafi kuwa gasu nan birjik a cikin Lambun kala kala,launi launi bazasu kirgu ba.Kai idan mutum yana kallon wadannan Lambu da abubuwan dake cikinsa sai ya manta da duk wani bakin cikin duniya kuma sai yaji kamar shine sarkin duniyar gaba daya saboda farin ciki.Saida akayi tafiya dasu kusan ta rabin sa'a sannan aka iso dasu fadar Boka Darbusa.Wangamemiyar fada ce wadda girmanta yakai a sanya gidan sarautar Sarauniya Akisatul Sauwara guda uku a ciki.Wannan karon sai da su Lubainu suka rinka yin tuntube suna faduwa kasa saboda kalle kalle da waige waige bisa ganin kayan kawar da yafi wanda suka gani a baya,amma kuma duk wannan kawa sai ta zama ta banza domin kuwa ba karamar razana da firgita sukayi ba sakamakon ganin irin fadawan da suke cikin fadar.Babu bil'adama ko guda daya a cikin dubbun fadawan Boka Darbusa face wadansu irin halittu wadanda mutum bazai iya tantancewa ba yace Aljanu ne ko Dodonni.Wasun su rabin jikinsu na mutum ne rabi na Aljan,wasu rabi dabbobi,rabi dodanni,wasu kuwa rabinsu na Aljan ne da wuta.Sun ksance manya manya,girda girda saidai a kwatanta girmansu da siffofin maridai ko mutanen farko.Dukkaninsu suna da matukar muni,kwarjini da ban tsoro,kuma suna dauke da mugayen makaman yaki iri iri barkatai.Wani kalar makamin ma ko a tarihi mutum bai taba kin irinsa ba.Wadannan dakaru sun cika fadar gaba dayanta sai yar siririyar hanua suka bari a tsakiyar fadar wacce fadinta bai wuce kamu uku ba,kuma itace hanyar dazata kai mutum har izuwa inda karagar mulkin Boka Darbusa take.Koda Boka Darbusa ya kyallara ido yaga kuyanginsa sun shigo cikin fadar tare dasu Sarki Darmanu sai ya mike tsaye daga kan karagar cikin tsananin farin ciki ya bushe da mahaukaciyar dariya yayita dariyar kamar wanda aka bashi komai na duniya.Al'amarin daya kara razana su Yarima Lubainu kenan sukaji a jikinsu cewar lallai Boka Darbusa yaudarsu yayi daya turo aka karbesu hannu biyu,lallai yunkurin cutar dasu zaiyi yanzu.Bayan Boka Darbusa yayi dariyar mugunta har ta ishe shi sai ya murtuke fuskarsa a lokacin da wadannan kyawawan kuyangi goma sha biyu suka rikide suka zama aljanun haske rike da zabga zabgan takubba kuma suka yiwa su Yarima Lubainu kawanya.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu ma suka zare takubbansu suka jingina da bayansu su ukun suna jiran suga ta inda za a kawo musu hari.Koda gani haka sai Boka Darbusa ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi su Yarima Lubainu yace,kunyi hauka kuma kunyi babban kuskure harda kuke yin tunanin cewa zakuzi wajena neman Allon Sihiri na kuma na baku alhalin yau sama da shekara bakwai kenan ina son ku kawo kanku nan fadata kun ki.Ai abinda kuka fada gaskiya ne cewar kowa a gidansa sarki ne.Ina mai tabbatar muku da cewa tunda har kuka shigo nan cikin fadata to tabbas babu dayanku dazai fita daga nan a raye,kuma shi kun shigo dauke da Allunan Sihiri guda biyu.Ku sani cewa tuni nayi bincike na gano hanyar dazan iya cire Allunan Sihirinku daga cikin kwalaben Sihirin da kuka sasu.Ina cirosu zan hada su da nawa.Hakan na faruwa shike na na zama SARKIN DUNIYAr nan gaba daya.Duk wata halitta dake bisa doron kasa walau mutum ko aljan,dabba,tsunstu ko kwaro sai ya dawo karkashin mulkina da ikona.Yanzu zan barku da wadannan Aljanun haske da suka yi muku kawanya na ga iyakar shirin ku dakuke dashi don karbar Allon Sihirina.Koda gama fadin haka sai Boka Darbusa ya yiwa Aljanun izinin su hallaka su Darmanu.Nan take kuwa Aljanun suka afka musu aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa Aljanun suna kai musu sara da suka cikin tsananin zafin nama dabasu taba gani ba.Duk sa'adda takobin Aljanun ta hadu da tasu saidai kaga tarwatsin wuta na tashi kuma takobin Lubainu data Akisatul Sauwara suka rinka dakushewa,ta Sarki Darmanu ce kawai batayi komai ba.Haka kuma duk sa'adda su Lubainu suka sami nasarar sara ko sukar jikin Aljanun saidai suji kamar iska suka soka.Bugu da kari da kyar su Lubainu suke iya tare harin Aljanun saboda karfin saransu,jinsa suke kamar katon dutse ake bugawa a kan takubbansu wanda sai kato arba"in sun tare zasu iya daukarsa.A duk sa'adda takobin Aljanun ta shafi jikinsu Lubainu koda kuwa dan lakatarsu tayi saidai kaji sun kwalla ihi saboda tsananin zafi da zogon da suka ji,a lokacin da jini je tsartuwa gami da feshi daga jikin nasu.Koda Boka Darbusa yaga yana samun wannan gagarumar nasara saiya cigaba da kyalkyalewa da dariyar mugunta saboda ya tabbatar da cewar hakansa ya kusa cimma ruwa.Al'amarin su Yarima Lubainu kuwa suna wannan yaki ne cikin nadama da takaici domin sun gane cewa lallau tsautsayi ne yasa suka biyo Boka Darbusa har gidansa domin karbar Allon Sihiri.Banda Tsautsayi kuma zasu iya cewa Ajali ne ya kirasu,domin sun san cewa babu wata dabara dazasu iya yi a yanzu su ceci rayuwarsu daga hannun wadannan Aljanu na haske. SHIN SU YARIMA LUBAINU ZASU KUBUTA DAGA HANNUN WADANNAN MUGAYEN ALJANU NA BOKA DARBUSA HAR SU KARFI ALLON SIHIRIN HANNUNSA? IDAN HAR HAKAN TA KASANCE YAUSHE NE ZASU ISA KOGON BAHAR IMFAL YARIMA LUBAINU YA SAMO MAGANIN DA YA FITO NEMA? YAYA SOYAYYAR SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DA YARIMA LUBAINU ZATA KASANCE?SHIN ZATA BAYYANA MASA SIRRIN ZUCIYARTA NE KUMA YAYA ZAI KARBI TAYIN NATA? A WANE HALI YAZARINA TAKE YANZU A CAN BIRNIN ZAMRAL BISA BAKIN CIKIN RABUWA DA MASOYINTA YARIMA LUBAINU? INA LABARIN YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA SARKI ALKAS WADANDA SUKA KOMA CAN BIRNINSU A CIKIN BAKIN CIKI NA SABANI? SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIRE SON YAZARINA DAGA CIKIN ZUCIYARSA GABA DAYA A MATSAYINSA NA WANDA YA ZAMO MASAKI MAI HANNU DAYA? WANE MATAKI ZAI DAUKA AKAN MAHAIFINSA SARKI ALKASA WANDA YACE YA CIRESHI DAGA SAHUN 'YA'YANSA?SHIN YANA TUNANIN DAUKAR FANSA NE AKAN YARIMA LUBAINU KO KUWA YA RUNGUMI KADDARA? YAUSHE NE YARIMA LUBAINU ZAI DAWO BIRNIN ZAMRAL HAR YA SAKE SADUWA DA MASOYIYARSA YAZARINA 'YAR BABBAN ATTAJIRI NA NAHIYAR? Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI 3(kashi Na Uku) don jin ci gaban wannan kayataccen Kasaitaccen Labari. An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku

Chapter 5 of 19