Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ LOKACIN da Yarima Lubainu ya gama aiyana haka a zuciyarsa sai ya daga kai ya dubi Aljana Badi'atul Sarira yace,yake wannan ma'abociyar kyau da siffa ta ban al'ajabi,kiyi sani cewa hakika kin zo mini da babban al'amaro wanda bazan iya yin saurin yanke hukunci a kansa ba,saboda haka ina so ki bani lokaci zuwa gobe da safe nayi tunani,sannan na yanke shawara bisa abinda nake ganin zai fissheni.Koda jin wannan batu sai Aljana Badi'atul Sarira taja dogon numfashi cikin alamun takaici ta dubi Yarima Lubainu tace,kaiconka ya kai wannan dan sarki,kayi sani cewa tabbas saikayi babbar nadama idan kaki amfani da wannan dama dana baka yanzu,domin kuwa har abada bukatarka bazata taba biya ba.Ina mai tabbatar maka da cewa Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu yaudararka zasuyi su gudu da wannan ALLON SIHIRI,Shi kuwa wannan Bakon Jarumi indai ka yi kuskuren karbar ADDININSA to har abada bazaka warke ba daga wannan lalura taka,saidai ka rungumi kaddara.Lokacin da Aljana Badia'atul Sarira tazo nan a zancenta sai hankalin Yarima Lubainu ya sake dugunzuma fiye da koyaushe.Nanfa ya kama duru duru ya rasa abinda zaiyi,kawai sai ya dubi Badi'atul Sarira yace,kiyi hakuri ni bana aiki da gaggawa,dole ne ki bari zuwa gobe da safe.Nayi miki alkawarin zan dawo gareki da duku dukun safiya kafin sauran abokan tafiya su fito domin na sanar dake hukuncin dana yanke.Yarima Lubainu na gama fadin hakan sai ya juya da nufin ya fice daga cikin lambun,amma sai Badi'atul Sarira ta kira sunansa ya waigo da sauri suka dubi juna a lokacin dayaga hawaye na cigaba da tsartuwa akan kumatunta.Badi'atul Sarira ta budi baki tace,shikke na tunda ka kasa yanke hukunci yanzu,ina son kayi min alkawarin cewa bazaka sanar da abokan tafiyarka labarina ba koda kuwa ka yanke hukuncin bazaka kwanceni ba daga cikin wannan dauri daka riskeni a ciki?Sa'adda Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya sake yin shiru yayi dan guntun tunani sannan yace shike nan babu matsala nayi alkawarin zan rufe sirrinki.Yana gama fadin hakan ya juya ya fice daga cikin lambun ya nufi wani dakin dabam ya fada cikinsa.Yana shiga yaga ashe falo ne guda daya,wato falle daya babu dakin barci a cikinsa,kuma babu komai a cikin falon face shimfida ta wani jan kilishi da kuma manyan dogayen kujeru masu taushi guda biyu.A tsakiyar kujerun kuma an ajiye wani farin tebur na azurfa.Koda ganin wannan tsari sai Yarima Lubainu ya aiyana a cikin ransa cewa"duk yadda akayi wannan daki ne inda Boka Darbusa ke Hutawa".Take Yarima Lubainu ya tafi izuwa kan daya daga cikin kujerun ya kwanta.Kwanciyarsa keda wuya sai barci mai karfi ya saceshi saboda tsananin gajiya da tsamin jiki sakamakon gumurzun da suka sha.Wannan shine abinda ya garu gasu Yarima Lubainu bayan sun sami nasarar dauko ALLON SIHIRI a gidan Boka Darbusa. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ AMMA abinda basu sani ba shine,karbar wannan ALLON SIHIRI na Boka Darbusa daidai yake da ALLURA TA TONO GARMA!Domin duk halin da suke ciki Boka Darbusa ya gani a cikin MADUBIN TSAFINSA a cikin wani kogon dutse dake wani bangare dabam na wannan daji da suke ciki.Shidai wannan kogon dutse babu yadda za'ayi a gane cewa akwai mutum a cikinsa,saboda dutse ne lailayayye kuma fafaffe mai siffar kwai,amma sai Boka Darbusa yasa Aljanu suka fafe cikinsa suka gina masa dakuna a ciki wadanda aka shiryawa kayan kawa a cikinsu tamkar aljannar duniya.A cikin wannan gida akwai hadima sama da guda dubu na jinsin mutane da aljanu,kuma suna rayuwa a cikinsa tamkar ba a cikin dutse suke ba saboda tsananin karfin sihirin tsafi irin na Boka Darbusa.Bayan Boka Darbusa yaga yadda Bakon Jarumi ya sami nasarar tarwatsa wannan bakaken aljanu daya turo su dauko ALLON SIHIRI sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta yayita kyakyatawa kamar bazai daina ba.Al'amarin dayai matukar baiwa babban wazirinsa mamaki kenan wanda ake kira da suna YAUHAN.Ya dubeshi a cikin alamun damuwa yace,haba ya shugabana yaya kake ta faman yin dariya haka alhalin makiyanmu ne suke samun galaba akanmu?Shin ka manta ne cewa sun koremu daga cikin ainihin fadarmu kuma sun rabamu da Allonmu na Sihiri? Koda jin wannan tambaya sai Boka Darbusa yayi murmushi mai nuna jin kai gami da izza yace,ai duk wannan nasara dasu Bakon Jarumi suka samu ta banza ce domin yanzu aka fara wannan mugun wasa.Ka sani cewa ina da tarkuna guda arba'in da zan dana musu a cikin hanyoyinsu wadanda basu isa su shallakesu ba har su iso KOGIN BAHAR IMFAL ba tare da sun hallaka ba gaba dayansu.Abinda ya bakanta mini rai a yanzu shine Yarima Lubainu ya san cewa shi dasu Akisatul Sauwara bazasu iya karanta dalasiman tsafin dake jikin Allon Sihirin ba,Badi'atul Sarira ce kawai zata iya.To amma abin tambaya game da Yarima Lubainu a yanzu shine,shin zai iya taimakon Badi'atul Sarira har ya kwanceta,kuma idan ya taimaketan itama zata taimakeshi ne bazata ci amanarsa ba?Koda jin wadannan tambayoyi sai hankalin Waziri Yauhan ya dugunzuma ainun ya dubi Boka Darbusa cikin alamun damuwa yace,ya shugabana yanzu yaya zamuyi kenan?Tabbas idan Yarima Lubainu da Badi'atul Sarira suka hada kai suka taimaki junansu bada yaudara ko cin amana ba tamu ta kare.Koda jin wannan batu sai Boka Darbusa ya kyalkyale da dariya sannan ya daga kafadar waziri Yauhan yace,ai abinda ba zai taba yiyuwa bane Badi'atul Sarira da Yarima Lubainu su hada kai ba tare da dayansu ya yaudari dayan ba.Shin ka manta cewa dukkan wani MATSAFI mayaudari ne,kuma makaryaci?Ka zuba ido kawai kasha kallo kawai,zakaga yadda zata wakana a tsakaninsu.Shi kansa wannan Bakon Jarumi sai yayi nadamar kulla alaka dasu Sarauniya Akisatul Sauwara domin yaudararsa zasuyi a karshe ba zasu taba karbar wannan bakon Addini nasa ba. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ A CAN BIRNIN ZAMRUL kuwa tun daga ranar da Yarima Lubainu ya bar kasar domin tafiya neman maganin lalurar da Yarima Mangul ya saka masa sai Amarya Yazarina ta kasance kullum cikin kuka da bakin ciki dare da rana,har ya zamana cewa ta fara shiga wani mugun hali na rashin lafiya sakamakon yawan tunani da rashin cin isasshen abinci.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalin Sarki Sailur kenan da kuma mahaifinta Attajiri Abu Yazarina suka rasa yadda zasu bullowa al'amarin saboda babu irin matakan da basu dauka ba wajen ganin ta daina kukan da bakin ciki gami da yawan tunani amma abun ya gagara.Lokacin da Tura takai Bango ya zamana cewa rashin lafiyar Yazarina tayi tsamarin da takai ga kwanciya sai likitan sarki Sailur ya bashi shawarar lallai a hanzarta yiwa Yazarina maganin abinda yake damunta,idan ba haka ba kuwa za'a iya rasa rayuwarta ma gaba daya.Koda jin wannan batu sai hankalin sarki sailur ya tashi,take ya tura aka kirawo Attajiri Abul Yazarina suka kadaita a cikin turakarsa.Sarki Sailur ya dubi Abul Yazarina cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abokina na sani cewa a duniya kaf babu abinda kakeso sama da wannan 'ya taka Yazarina wato matar 'dana Yarima Lubainu.Kuma nayi imamin kasan dukkan wani hali da yanayi da take ciki dangane da rashin lafiyarta,to ka sani cewa a yau abin yayi tsamari fiye da koyaushe wanda sanadin hakan ne ma yasaka likitana ya tabbatar mini da cewa idan har ba'a sadata da mijinta ba da gaggawa wannan ciwo nata zai iya zama sanadin ajalinta.Koda jin wannan batu sai nan take idanun attajiri Abul Yazarina suka ciko da kwallah.Sarki Sailur ya cigaba da cewa,nidai yanzu na kirawoka ne domin mu yanke shawara bisa abinda nake gani zai kawo karshen wannan matsala.Ka sani cewa ni kaina ina cikin mugun tashin hankali tun daga ranar da dana Yarima Lubainu yasa kafarsa yabar garin nan saboda bani da tabbacin cewa zai sami nasarar samo abinda ya fita nema ba tare daya rasa rayuwarsa ba.Sannan kuma idan har ya dawo ya iske Yazarina ta mutu zai iya kashe kansa koya susuce yadda bazai iya gadar karagata ba,yanzu menene abinda kake ganin ya kamata muyi domin ceton rayuwar wadannan 'ya'ya namu.Sa'adda sarki Sailur yazo nan a zancensa sai Attajiri Abu Yazarina ya kawo gwauron numfashi ya ajiye kuma yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubi sarki Sailur yace yakai abokina kayi sani cewa hanya daya ce damu wacce zamu iya bi mu magance wannan matsala.Dole ne mu hakura da zaman 'yata anan kasar mu hadata da amintattun dakarunmu su tafi neman Yarima Lubainu.Ina mai tabbatar maka da cewa ko a yanzu muka yiwa Yazarina bushara da hakan take zata sami lafiyar jikinta ta mike tsaye.Yayin da sarki Sailur yai wannan shawara sai ya gyada kai cikin alamun murna yana murmushi,sannan can kuma sai ya hade rai ya dubi Abu Yazarina cikin alamun matukar damuwa yace,na yarda da wannan shawara taka,amma fa kasani cewa akwai mugun hadari a cikinta.Hadari na farko shine zamu iya baiwa Yazarina cikakkiyar kariya ne kadai idan tana cikin wannan birni namu,amma idan har tasa kafarta ta fita koda mun hadata da dukkan dakarun yakin kasar nan ba zasu iya kareta daga harin mai son ta ba,wato YARIMA MANGUL.Saidai idan baisan cewa ta fito ba domin kuwa dole ya tura a satota a kaita gareshi.Hadari na biyu shine wannan tafiya da zatayi izuwa inda Yarima Lubainu ya nufa tafi komai hadari domin takadiran mutane da aljanu da matsafa suka kwallafa ransu akan wannan ALLONSIHIRI kuma suna da yawa,kuma zasu iya kawar da duk wanda ya shigo cikin al'amarin.Bisa wannan dalili da hujjoji kaga kenan 'yata zata iya rasa rayuwarta tun kafin ma ta sadu da masoyin nata Yarima Lubainu.Lokacin da attajiri Abul Yazarina yazo nan a zancensa sai Sarki Sailur yayi ajiyar numfashi yace,tabbas duk abinda ka fada gaskiya ne amma kuma akwai wani hanzari akan haka.Da farko dai inaso ka sani cewa zamu iya fitar da 'yarka daga cikin garin nan a sirrance ba tare da kowa ya sani ba bare har labarin hakan ya kai izuwa kunnen Yarima Mangul.Kuma koda ace ma yaji din kuma ya sami nasarar saceta ai garinsu zai kaita,kasan kuwa indai Sarki ALKAS na raye,bazai taba barin shi ya aureta ba bisa dole,kuma zai karbeta ne ya dawo da ita garemu.Dangane da batun hadarin dake cikin tafiyar zatayi kuwa,ina son na tambayeka.Shin da zamanta a gabanmu cikin mayuwacin halin rashin lafiyar da zata iya zama sanadin ajalinta a ko yaushe da kuma tafiyarta cikin koshin lafiya bisa burin saduwa da masoyinta wanne ne yafi mana sauki?Koda jin wanna batu sai Attajiri Abul Yazarina ya sunkui da kansa kas yayi shiru yana tunani sannan ya dago kai ya dubi sarki Sailur yace,hakika shawararka itace mafi kyau,don haka inason ka zabo BABBAN JARUMI daga cikin mayakanka wanda ka aminta dashi ainun ka hadashi da wadannan AMINTATTUN DAKARUNKA suyiwa 'yata rakiya a cikin wannan tafiya.Amma abinda danake so dakai shine,dasu da ita zasuyi bad-da- kama ne ma'ana suyi shiga kawai irin ta FATAKE su fice daga cikin garin nan a sirrance ba tare da wani ya shaidasu ba.Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullibe sarki Sailur yace,nima na karbi wannan shawara dakazo da ita,kuma na umarceka daka tafi izuwa bangaren da yarka take a cikin wannan gidan sarauta nawa kayi mata wannan kyakyawan ALBISHIR da duk wani abu da muka shirya yanzu.Kuma ka gaya mata cewa a yau dinnan zan kammala dukkan wani shirye shirye na wannan tafiya tasu,kuma a tsakiyar dare zasu fita daga cikin garin nan.Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube Attajiri Abu Yazarina ya zube lasa a gaba sarki Sailur ya kama godiya.Koda ganin haka sai Sarki Sailur yayi sauri ya sunkuya ya kama kafadunsa ya tasheshi tsaye,ya sallameshi ya tafi izuwa bangaren da turakar Yazarina take.Fitar Attajiri Abul Yazarina keda wuya daga cikin turarkar sarki Sailur ya nufi cikin gidan Sarautar bangaren 'yarsa Yazarina,sai sarki Sailur ya tura aka kirawo masa mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira da suna BARDE RUHAISU.Barde Ruhaisu ya kasance saurayi kyakyawa dan kimanin shekaru ashirin da takwas,amma kuma GWARZON JARUMI NE mai TARWATSA MAZA a FILIN DAGA.Sau bakwai Barde Ruhaisu yana jagorantar rundunar yaki a birnin Zamrul ana samin nasara na tare da anyi wata mummunar asara ba ta rayukan DAKARUN YAKI.Allah ya horewa Ruhaisu baiwar sanin YAKI da TUGGUNSA kuma yana da matukar TUNANI mai kyau gami da HANGEN NESA.Duk da cewa sarkin yakin kasar yafi barde Ruhaisu KARFIN DAMTSE da iya yaki da kuma kwarewa akan sanin tuggun yaki amma sarki sailur yafi aminta da Barde Ruhaisu dari bisa dari saboda ya jarraba amanarsa ya gani.Shi kuwa sarkin yaki mutum ne mai tsananin son abin duniya gami da MULKI,don haka sarki Sailur yana tsoron cewa wata rana zai iya cin amanarsa don cika burin rayuwarsa.Bisa wannan dalili ne sarki Sailur yake shirya komai nasa na sirri da Barde Ruhaisu,shi kuwa sarkin yaki sai ya bar masa abubuwan da basa bukatar sirri na cigaban kasa da kuma kare kasar daga yan hari ko ABOKAN GABA.Sarki Sailur yana zaune a cikin falon turakarsa yayi tagumi yana tunani da nazarin abinda ke gabansa,sai ga Barde Ruhaisu ya shigo.Tun daga nesa kadan Barde Ruhaisu ya cire takalminsa saboda biyayya,yana kara matsowa kusa da sarki Sailur sai ya zube kasa wanwar ya kwashi gaisuwa.Cikin hanzari sarki Sailur ya mike daga kan kujerar dayake zaune ya kama kafadunsa ya tasheshi tsaye kuma ya rike hannunsa yajashi izuwa kan kujerar da yake zaune suka zauna tare.Sarki Sailur ya gyara zama ya dubi Barde Ruhaisu cikin nutsuwa yace,yakai JARUMIN JARUMAI kuma BABBAR DIRKA ta birnin Zamrul,ka sani cewa ban kirawoka nan ba sai domin na baka wani gagarumin aiki mai mugun hadari wanda nakeson ka gabatar dashi a cikin sirri.Kafin na sanar dakai yanayin wannan aiki inason nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu.ALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part B Kafin na sanar dakai yanayin wannan aiki inason nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu.Tambaya ta farko itace shin zaka iya sadaukar da rayuwarka don ceton ta wanda nake kauna fiye da komai a duniya?Koda jin wannan tambaya sai nan take idanun Barde Ruhaisu suka ciko da kwalla ya dubi Sarki Sailur yace tayaya zan kasa fansar da raina ga wanda ya raineni ya rikeni tamkar dan cikinsa alhalin na kasance tsintaccen bawa da baisan iyayensa ba kuma bai san asalinsa ba?Koda jin wannan batu sai shima Sarki Sailur yaji hawaye ya subuto masa amma sai yai sauri ya sunkui da kansa kas yace,yakai Barde Ruhaisu shin zaka iya rabuwa da amaryarka wacce ke dauke da juna biyu na tsawon wata takwas tana shirin haife maka 'da ko 'ya don zuwa cika aikina alhalin ganin 'danka ko 'yarka a yanzu shine babban burinka a rayuwa?Da jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Barde Ruhaisu yace,ya shugabana kasani cewa dani da duk abinda na mallaka zan iya bayar dashi FANSA akan halaccin da kayi mini a rayuwa,kuma a kaso dari ban saka maka da kaso goma ba.Koda jin wannan batu sai sarki Sailur ya rungume Barde Ruhaisu duk su biyun suka fashe da kuka.Tsakanin Sarki Sailur da Barde Ruhaisu akwai tsananin kauna da shakuwa domin kafin Allah ya baiwa Matar Sarki Sailur haihuwar Yarima Lubainu saida suka shekara goma sha shida da aure ko batan wata bata bata yiba.A wannan lokaci babu irin kokarin da Sarki Sailur da matarsa basuyi ba akan su sami haihuwa har saida suka hakura suka rungumi kaddara.Wata rana sarki Sailur ya fita wani gagarumin yaki a wata kasa da ake kira DARNIS,wadanda tun iyaye da kakanni akeyin mummunar gaba a tsakanin kasashen biyu,sai Allah ya basu nasara suka kashe gaba dayan dakarun yakin birnin Darnis,kuma suka balle kofar birnin suka cigaba da kashe dukkan mazajen garin manya da kanana banda yan kasa da shekara goma saida ya zamana cewa sun gama da dukkan wani namiji mai karfi a jika wanda zai iya tabuka wani abin arziki.Ba komai ne yasa su sarki Sailur sukayi wannan rashin imani ba face akwai lokacin da gaba daya mazajen garin suka kai musu harin sumame suka kashe sama da mutane miliyan uku,da kyar da sidin goshi aka koresu daga cikin birnin Zamrul bayan sunyi mummunar barna sun kama bayi kuma sun kwashe dukiya mai yawan gaske sun kone kusan rabin birnin.Da gaiya Su Sarki Sailur su kayi ta ragargazarsu baji ba gani,kuma ba sassauci sannan suka yi ta kama matayensu a matsayin bayi,yara da tsofaffi ne kadai suka kai labari.Lokacin da Sarki Sailur ya shiga cikin gidan sarautar birnin Darnis ya sami nasarar kashe sarkinsu,ya kama matayensa a matsayin bayi da 'ya'yansa kanana saiya kunna kai izuwa cikin turakarsa.Yana shiga cikin turakar ne ya iske wani yaro dan kimanin shekaru goma kwance a kas an dora masa wani katon dutse a ciki yana ta numfarfashi kamar ransa zai fita.Koda ganin wannan yaro a cikin wannan halo sai Sarki Sailur ya ruga da gudu izuwa ga yaron yai sauri ya dauke dutsen daga kan cikin yaron sannan ya tasheshi zaune.Koda ya kalli fuskar yaron yaga yadda lebensa ya bushe saboda tsabar kishirwa da kuma yadda ya galabaita ainun sai ya kamu da tsananin tausayinsa.Nan take yai sauri yaje ya nemo ruwa ya baiwa yaron yasha.Saida yaron ya dawo cikin hayyacinsa sannan sarki Sailur ya dubeshi cikin nutsuwa yace,yakai wannan yaro waye yayi maka wannan muguwar azaba haka yake neman hallaka ka?Koda jin wannan tambaya sai yaron ya budi baki da kyar yace,sarki ne yayi mini wannan azaba saboda bani da lafiya na kasa aiwatar da aikin dana sabayi a kullum.Cikin mamaki sarki Sailur ya sake duban yaron yace,aikin ne kakeyi masa na bauta?Yaron yace nine mai wanke masa kwanukan abinci da kofuna.Sarki Sailur ya girgiza kai yace,shin kai haifaffen nan garin ne? Yaron ya girgiza kai yace NI BAWA ne bansan ASALINA ba,bansan IYAYENA ba,kawai na taso ne na tsinci kaina a cikin wannan gidan sarauta tun banyi wayo haka ba ina aikin bauta.Koda jin wannan batu sai sarki Sailur yaji ya kamu da tsananin tausayin yaron fiye da koyaushe ya dafa kafadarsa yace mene ne sunanka?Yaeon yace Sunana RUHAISU.Cikin murna da murmushi sarki Sailur ya dubi Ruhaisu kayi sani cewa daga yau ka zama dana,kuma nayi maka alkawarin cewar zan rikeka tamkar dan dana haifa a cikina,kuma zan duba abinda kafi cancanta dashi a rayuwa na doraka a kansa.Koda Yaron Ruhaisu yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushi ya kamu da tsananin farin ciki ya dubi Sailur yace,wane ne kai,kuma menene dalilin da yasa kukazo garin nan kuka afka mana da yaki?Shin kun kashe sarki ne ko kuwa kun kamashi a raye.Koda jin wannan tambaya sai sarki Sailur yayi murmushi yace Sunana SARKI SAILUR nai mulkin BIRNIN ZAMRUL.Ya kai Ruhaisu kayi sani cewa tsakanin kasata da wannan birni na azzalumin sarkinku akwai TSOHUWAR GABA tun iyaye da kakanni,kuma kimanin shekaru uku baya sarkinka da mayankansa sunje birnina sunyi mini mummunar barna shine mu ma yanzu mukazo mukayi RAMUWAR GAYYA.Tuni sarkinka ya dade da shekawa BARZAHU.Daga yau na yantaka kashi daga matsayin bawa ka zama cikakken da kuma dan sarki ba wai talakan gari ba.Koda gama fadin hakan sai sarki Sailur ya kama hannun yaro Ruhaisu yajashi suka fice daga cikin turakar.Ai kuwa suna fitowa kofar turakar ne yaro Ruhaisu yayi tuntube da gawar azzalumin sarkinsa.Kawai saiya tofawa gawar yawu yace,tur dakai azzalumi,azaba ninkin wadda ka yimini sau dubu ta tabbata a gareka a cikin kabarinka.Koda jin wannan batu sai sarki sailur ya fahimci cewar tabbas yaro Ruhaisu yasha bakar wahala ta gaske a hannun wannan sarki. Tun daga wannan rana kasar Darnis ta dawo karkashin mulkin birnin Zamrul,aka mayar da ita bbabar jaha kuma babbar cibiya ta kasuwanci. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ LOKACIN da Sarki Sailur yazo da yaro Ruhaisu gida sai ya tara gaba dayan yan majalisarsa da fadawansa ya gabatar da yaro Ruhaisu a garesu kuma yace dasu daga yau sunan wannan yaro Yarima Ruhaisu.Bawa ne amma na yantashi na maishe dashi tamkar dan cikina.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke kowa fadawa suka kama kace nace.Wasu suce yama za'ayi sarki ya dauko bawan da bashi da asali yace ya maishe dashi dansa,harma ya kirashi a matsayin yarima mai jiran gado!Au wannan abin kunyane abin gori a gareshi dama masarauatar birnin gaba daya!!!Wasu kuwa sai suka rinka cewa ai bazata sabi ba BINDIGA A RUWA a kawo bare wanda ba an kasa ba ace nan gaba shine zai mulkesu.Koda sarki Sailur yaji irin surutun da yan majalisarsu da fadawansa sukeyi sai ransa ya baci,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur daga kan KARAGAR MULKINsa ya daka kakkafar TSAWA wadda tasa hantar cikin kowa ta kada saboda tsananin tsoronsa da akeji.Nan ake fadar tayi tsit kowa ya sunkui da kansa kasa kamar ruwa yaci su.A sannan ne sarki Sailur yace,nine sarki a wannan birni na Zamrul,babu wani mai matsayin dayafini don haka idan har na gabatar da HUKUNCI babu wanda ya isa ya sauya mini shi.Wannan Yaro Ruhaisu shine Yarima na,wanda duk ya kara magana akan haka da hannuna zan cisge masa kansa!!!Koda jin wannan batu sai gaba dayan mutanen dake cikin fadar suka sake shiga taitayinsu aka rasa wanda ma zai iya daga kansa sama ya dubi sarki Sailur.Koda Yaro Ruhaisu yaga abinda ya faru tsakanin sarki Sailur da mutanensa sai ya fashe da kuka ya durkusa bisa gwiwoyinsa a gaban sarki saiur.Al'marin daya baiwa kowa mamaki kenan a fadar aka kurawa sarki Sailur da Yaro Ruhaisu idanu.Shi kuwa sarki sailur sai hankalinsa ya DUGUNZUMA shima ya durkusa a gaban Ruhaisu ya kama kafadarsa ya rike kuma ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da fargaba ya ce yakai dana ina dalilin wannan kuka naka? Yaro Ruhaisu ya dubi sarki Sailur cikin nutsuwa yace,yakai wannan sarki mai daraja,kayi sani cewa babu wani jin dadi ko kwanciyar hankali ga kowanne sarki komai arzikinsa da daukakarsa face ya sami soyayya da kaunarsa a cikin zukatan jama'arsa sannan ya cika sarki mai kima da daraja,domin a sannan ne jama'ar tasa zasu iya siyar da rayukansu domin tsare lafiyarsa da mutuncinsa.Ya kai wannan sarki mai daraja,mai adalci,bana son ka rasa wannan babbar dama saboda ni don haka na roke ka don darajar karagarka daka janye wannan matsayi daka bani na Yarimanka,ni kuma nayi alkawarin cewar zan cigaba da nuna maka SO da KAUNA kamar yadda kowanne da ke nunawa ubansa.Koda Yaro Ruhaisu yazo nan a zancensa sai gaba dayan jama'ar dake fadar suka cika da tsananin mamakin hankalinsa da basirarsa ta iya magana da sanin yakamata da kuma hangen nesa.Kawai sai jama'a suka kama yiwa yaro Ruhaisu tafi.Al'amarin daya aurewa sarki Sailur kai kenan,kuma yaji ya kara kamuwa da tsananin son yaro Ruhaisu fiye da koyaushe a rayuwarsa,don haka sai ya tashe shi tsaye ya rungumeshi yana mai cewa tabbas ka cika da na gari abin alfahari.Lallai na yarda da wanan shawara taka kuma zanyi aiki da ita.Koda jama'a suka ji haka sai suka rude da shewa,suka kama yiwa sarki Sailur jinjina da kirari suna masu nuna soyayyarsu a gareshi.Tun daga wannan rana Ruhaisu ya tunawa sarki Sailur cewa babu abinda yakeso a rayuwarsa sama da ya koyi YAKI.Ai kuwa ba tare da wata gardamar komai ba sarki Sailur ya shiga koya masa yaki da kansa,ya zamana cewa a kullum sarki sailur yana shafe kimanin sa'a guda yana koyawa Ruhaisu yaki.Da safe suyi sa'a biyu,haka ma da rana da kuma daddare.A cikin kwanaki goma sha hudu Kacal Ruhaisu ya iya sarrafa takobi ainun,kuma ya iya kare dukkan irin harin da sarki Sailur ke kawo masa.Koda aka shiga sati na uku kuwa sai gashi yana iya maidawa sarki sailur martanin kai hari,har ma akwai lokacin da saura kiris ya yiwa sarki Sailur rauni a lokacin daya kawo masa wani wawan sara aka,ya matsa baya cikin zafin nama,amma duk da haka sai da kaifin takobin tasa ta zabtare wani bangare kadan na rawaninsa.Shi kansa sarki sailur bai san sa'adda ya kama yiwa yiwa Yaro Ruhaisu tafi ba.Daga wannan rana ne sarki Sailur yakai Ruhaisu cikin manyan dakarun yakin kasar ya cigaba da daukar HORON YAKI a cikinsu.Abi dai kamar wasa sai gashi Ruhaisu yana iya jure duk irin wahalar da manya ke jurewa a matsayinsa na yaro karami dan shekara goma.Ashe wannan juriya tasa ta samo asalo ne tun daga azabar da sarkin birnin Darmis ya rinka yi amsa shi kuma yana shanyeta.Kai saida takai cewa barde Ruhaisu yana iya yin yaki da karti hudu yana yaro amma duk sai ya kaisu kasa.Lokacin daya cika shekara goma sha takwas a duniya kuwa sai gashi shi kadai yana iya tarwatsa mutum arba'in.A wannan shekarar ne aka jarraba iya yakin Ruhaisu inda aka shirya wata gagarumar GASA ta JARUMAI akan akarfin damtsensu da iya Yakinsu.Jaruman gasar su dari da goma sha hudu ne,amma RUHAISU ne ya karbi KAMBUN GASAR.Daga wannan lokaci ne sarki sarki ya sake jan barde Ruhaisu a jikinsa ainun ya zamana cewa duk wani abu da zaiyi na sirri tare dashi yakeyi.Al'amarin dayasa sarkin yaki ya fara kyashi da hassada dashi kenan,kuma ya tsaneshi ainun,amma sai Ruhaisu ya zame masa kadangaren bakin Tulu.Babu irin tuggu da makircin da sarkin yaki bai shiryawa Barde Ruhaisu ba amma sai sarki sailur ya rinka kareshi a boye ba tare da ya sani ba.Kai sau tari ma akwai mugayen tarkuna da Ruhaisu yake fadawa ya kasa fitar da kansa,amma sai yaga wani yazo tsulum ya ceceshi,kuma wanda ya ceceshin ya rufe fuskarsa da bakin rawani idanunsa kadai ake gani gaba dayan kayan jikinsa ma bakake ne.Saida akayi hakan kusan sau hudu.Abinda ya faru a karo na hudun shine. pls Like and comments 15 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part C A BINDA YA Faru a karo na hudun shine,wata rana da magriba Ruhaisu ya dawo daga FARAUTA a daji kawai sai yaga wadansu dakarun

Chapter 8 of 19