Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suka shafe sa'a hudu da rabi suna tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan Yarima Lubainu ya matso kusa da Sarauniya Akisatul Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta yace,waishin tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da muka nufa?Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa dadina dakai kenan ka cika zumudi da gaggawa.Ai idan kayi hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru bata kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa'a hudu suna tafiya.A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a bakin wani katon dutse.Anan suka kwana kashe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu riski wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu mugayen dabbobi ko kwaruka saidai kaga sun yi musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI TAYI NESA DA KASA!Kuma RUWA BA SA'AN KWANDO BANE.A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka Yarima Lubainu ya hango wani babban gari a gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu ya wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine ginen birnin cikin al'ajabi.Koda Sarauniya Akisatul sauwara ta lura da halin da yake ciki sai ta bushe da dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani kunya mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga cikin birnin tukunna.Koda jin wannan Batu sai Yarima Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin yanzu kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine Birnin Kimras inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara ta jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka sai abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi saboda Sarki Darmanu ba karamin shaidanin Mutum bane.A yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin wani abu domin ya cutar damu,don bani da tabbacin cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka zo masa da ita.Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da iya yaki KARE JINI BIRI JINI mukeyi.Sau tara muna fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki.Bisa sa'a ne kawai na samu na tsira daga sharrin tsafinsa sabodatsarin dana samu tun daga kakannina.Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta suna daf da shiga cikin birnin ne,Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a bayansa,shima zai shiga cikin birini.Cikin Ladabi Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu suka gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu kallo ya lura cewa baki ne don haka saiya dubesu yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne a garin nan ko?Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin yanayi mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da gani kun fito daga babban gida kuma kun sami tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don kada ku fada cikin tarkon maketacin sarkinmu.Ina mai sanar daku cewa bisa al'adar wannan mugun sarki namu duk bakon daya shigo garin nan kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a kaishi kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a duniya sannan zai tsira da rayuwarsa.Yanzu zan taimake ku ba bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda zai ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso indan gari ya waje sai ku saje da 'yan gari ku aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama fadin hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu yace,idan sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar 'yar uwar taka saiya rabaka da ita har abada.Koda jin haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai jinjina al'amarin ba tare da yace kala ba.Nan dai tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai bin wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin.Su kuma suka ci gaba da jan limzamin dawakansu a hankali suna yin tafiyar san'da suna waige waige cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin da suka yi 'yar doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin zai iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka turoshi ya yaudare mu ya cutar damu.Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da Yarima Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai ya tsaida nasa dokin suka kurawa tsohon idanu kawai yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace 'ya'yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka kuka daina tafiya?Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon banza!bakin mayaudari na gane ko kai waye.Maza ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu tattauna bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da tsohon yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara saiya bushe da mahaukaciyar dariya cikin karfin murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza na take ya rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar shigar yaki.Sarki Darmanu ya kasance katon mutum mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma gashi kakkaura mai murdadden jiki gami da tarin kwanji da jijiyoyi.KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA.Wadansu bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe.Rigar dai Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon wando da dogayen takalma duka na bakin karfe.A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa ce wadda akayi ta da zallan dutsen lu'u lu'u mai nauyin gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya rabata da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya rike.Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro birnin ki naga duk abinda ya faru tsakaninki da Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa sa'adda kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin Allon Sihirin dake hannuna.Tabbas dake dashi kuma sami tabin hankali har da kuke tunanin zan karbeku hannun bibbiyu na yarda da bukatarku.Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan rana wacce zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki taho har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na gano yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar dakika adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu daga sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan hallaku na dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na biya tawa bukatar dashi.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama kamar an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk su biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk su biyun suka kaucewa saran suk fado kasa daga kan dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar tuffa.Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai takubban nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu suka ruguntsume da azababben Yaki. (Shegen kaya Uban mayaudara) ,ya zama cewa yana kai musu sara da suka cikin bakin zafin nama da jarumtaka ta ban al'ajabi.Duk da tsananin jarumtaka irin ta Lubainu data Sarauniya Akisatul sai gashi sun raina kansu domin basa iya maida martani saidai kokarin kare kansu daga mugayen hare haren da yake kai musu.Al'amarin dayai matukar firgita Sarauniya Akisatul Sauwara ke nan,kuma ya bata matukar mamaki domin ada can ta san cewa karfin damtsenta da iya yakinta yazo iri daya sak dana Sarki Darmanu,amma sai gashi yanzu labari ya sha bambam.Koda Sarki Darmanu yaga ya fisu zafin nama da jarumtaka sai ya kara zage dantse a kansu ya ci gaba da kuntatasu yana mai sauya salon fada,wato ya hada da kai musu naushi da hannu da kafa.Faruwar hakan keda wuya sai ya fara samun lagonsu.Nan da nan ya hada musu jini da majina.Idan ya naushe su a ciki sai cikinsu ya kulle sunyi ihu sun kife kasa.Idan kuma a fuska ya naushe su sai kaga har sama sukeyi suna fadowa kasa a galabaice.Maimakon yasa takobinsa yayi musu kisan gilla sai ya rinka yankarsu a sassan jikinsu jini na tsartuwa da feshi suna ihu da kururuwa sakamakon tsananin zafi da zogin da suke ji har saida suka sami sama da raunika biyar a jikinsu.A sannan ne suka zube kasa wanwar suna numfashi sama sama kamar zasu mutu suka kasa koda mikewa tsaye.Koda Sarki Darmanu yaga ya sami wannan gagarumar nasara sai ya tsaya cak! a kansu yana mai kyalkyala dariyar mugunta da farinciki.Daga can kuma sai ya nufi kan Sarauniya Akisatul Sauwara da nufin ya lalube jikinta ya dauke wannan Allon Sihirin nata.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji Yarima Lubainu ya gabza masa mahaukacin naushi a fuska.Saboda karfin naushin saida yai tsalle sama da baya yaje ya gwaru da wata bishiya ya fado kasa a matukar galabaice a lokacin da hancinsa da bakinsa ke yoyon jini.Kafin Sarki Darmanu ya yunkura ya mike tsaye tuni Lubainu ya dako tsalle a sama ya doki cikinsa da guiwar kafarsa ta dama.Take wani gudan jini yai fitar burgu dagacikin bakin Darmanu kawai sai ya koma kasa ya baje sumamme.Da kyar da jan ciki Yarima Lubainu ya karasa inda Sarauniya Akisatul Sauwara ke kwance ya rinka yagar rigar jikinsa yana daure sassan jikinta inda ta sami raunika don tsaida zubar jini.In ba don yayi hakan ba cikin gaggawa da tabbas zata iya rasa rayuwarta.Bayan ya gama ceton rayuwarsa sai ya fara kokarin daddaure nasa raunikan sannan ya sake jan ciki ya koma inda Sarki Darmanu ke kwance ya cire dukkan gurayen tsafin dake jikinsa ya mai dasu nasa jikin,kuma ya dauke takobin sarki Darmanu ya koma can inda Akisatul Sauwara ke kwance ya taimaka mata ta mike zaune ya jingina bayanta a bayan wata bishiya.Faruwar hakan ke da wuya sai Sarki Darmanu ya farfado daga dogon suman da yayi.Koda ya bude idanunsa yaga babu takobinsa a kusa dashi kuma ya shafa jikinsa yaji duk babu guraye da layunsa na tsafi,sai ya takarkare ya kwarara uban ihu na bakin ciki da takaici,amma sai Yarima Lubainu ya tari numfashinsa yana ma daka masa tsawa yace,yakai wannan sarki kayi sani cewa a halin yanzu duk tasirin tsafinka yana hannuna tunda na mallaki takobinka da dukkan gurayenka na tsafi.Abinda nake so dakai shine ka bamu hadin kai yanzu mu tafi izuwa fadarka ka kirawo likitocinka suyi mana magani a raunikan dake jikinmu,sannan kuma ka bamu hadin kai bisa abinda muka zo nema.Idan kaki bin umarnina koka nemi ka shammace mu kayi mana wani tuggun zan fille maka kai da takobinka sannan mu shiga har cikin fadar taka mu bincike ko ina da ina har mu gani inda ka boye Allon Sihirin naka mu daukeshi mu kara gaba.Lokacin da Yarima yazo nan a zancensa sai kwallar bakin ciki ta ciko a idanun Sarki Darmanu.Bisa dole ba don son ransa ba ya mike tsaye ya wuce gaba,shi kuma Yarima Lubainu sai ya goya Sarauniya Akisatul Sauwara a bayansa saboda ba zata iya takawa ba da kafafunta suka bi bayan Sarki Darmanu don shiga cikin Birnin Kimrasa.Maimakon Sarki Darmanu yabi hanyar kwarai ta zuwa gidan sarautar tasa sai yabi wannan barauniyar hanya saboda kada asirinsa ya tonu jama'ar gari su gane cewa yau fa AN CI SHI DA SHI.'Yar gajeriyar tafiya sukayi sai gasu sun bullo a wata kofa dake can bayan gidan sarautar.In banda Sarki Darmanu babu wani mahaluki wanda yake bi ta cikin wannan kofa.Shima yana amfani da kofar ne kawai idan zai gabatar da al'amuransa na sirri.Tun daga nesa Sarki Darmanu yayi kamar dawo ne cikin nasarar samo abokan gabarsa,domin yana tafiya ne cikin tunkaho da izza kamar yadda ya saba a duk sa'adda ya dawo daga rangadi.Nan dai ya wuce kai tsaye ta cikin wannan koda ta gaban dakarun dake gadi.Duk da cewa dakarun sun fahimci abinda ke faruwa sai da suka yi mamakin abu daya.Ba wani abu suka yi mamaki ba face ganin takobin sarki Darmanu a hannun bakon dazo dashi.Ita dai wannan takobi ta Sarki Darmanu ta kasance sihirtacciya,kuma itace sirrin dukkan karfinsa na damtse dana sihiri.Ma'ana karfin damtsensa na zahiri bai kai wanda takobin ke kara masa ba.A duniya babu abinda Sarki Darmanu ke so sama da wannan takobi,kuma babu abinda daya dogara dashi sai ita ita.Ganin raunika a jikin Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara ne yasa hankalon masu gadin ya kwanta suka ratsa suka basu hanya suka wuce.Koda suka fara tafiya a cikin wannan gidan sarautar sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tsaida Lubainu tace,ya kai Lubainu ka sani cewa kowa Prince Auwal Auwzab Auwzab a gidansa sarki ne,baka tunanin cewa wannan mutumin bazai iya yaudararmu yanzu a cikin gidan nan nasa ya cutar da mu?Koda jin wannan batu sai Lubainu yayi murmushi yace ki kwantar da hankalinki yake Akisatul Sauwara ai mun gama dashi tunda kema kin tabbatar dacewar wannan takobi itace tasirinsa,ai babu abinda zai iya yi mana.Sarauniya Akisatul Sauwara tayi ajiyar numfashi tace hakane amma ka rike takobin hannu biyu komai rintsi kada ka bari ta subuce maka.ALLON SIHIRI Littafi na biyu(2) Part B Koda ganin abinda ya faru gareshi sai sarauniya Akisatul Sauwara ta sake bushewa da dariya a karo na biyu.Lokaci guda kuma ta hade fuska tace,ya kai Lubainu kamar yadda na gaya maka da farko babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya isa ya dauki wannan Allon Sihiri daga cikin wannan kwalba face ni. Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara taje gaban wannan kwalba ta shafeta da hannunta na hagu. Take kwalbar ta rabe gida biyu kamar an yanke lemon bawo. Kawai sai ta sa hannunta ta dauko Allon ta dorashi akan tafin hannunta ta yafito Lubainu da hannu tace dashi,zo kaga irin abinda aka rubuta a jikin Allo.Cikin sauri Lubainu yazo daf da iya ya tsaya ya kurawa Allon idanun. Ai kuwa sai yaga Rubutun a rabe yake gida biyu.Kuma bazai taba karantuwa ba a haka face an jona daya barin Allon na biyu.Kawai sai yayi ajiyar numfashin ya dubi Akisatul Sauwara cikin alamun karayar zuciya yace, Ai wannan Allon dake hannunki bashi da wani amfani idan ba'a samo daya Allon bana biyu.Koda jin haka Sai Akisatul Sauwara tayi murmushi tace to ina tabbatar maka da cewa idan ma an samo Allon na biyu an hada da nawan rubutun dake jikinsu ba zai karantu ba sai an hada dana ukun.Koda gama fadin hakan sai ta mayar da Allon cikin wannan kwalbar. Take kwalbar ta koma ta manne tamkar bata taba rabewa ba biyu.Akisatul Sauwara ta dauke kwalbar ta juya ta fice daga cikin wannan gida Lubainu yabita da sauri. Nan dai suka yita bin sako sako da lungu lungu har suka dawo inda turakarta take.Anan ne ta tsaye cak shima Lubainu sai ya tsaya. Akisatul Sauwara ta juyo tana mai yi masa wani kallo mai dauke da murmushi da ayar tambaya(?) tace,ai anan zamu rabu ka koma izuwa masaukinka ka sake hutawa, amma ina gayyatarka da yamma a can filin motsa jini na bayan turakata domin mu dan motsa gabban jikinmu in yaso gobe da safe muyi haramar tafiya. Tana gama fadin hakan ta kunna kai izuwa cikin turakarta kuyangi na gyara mata hanya. Yarima Lubainu ya juya ya nufi hanyar da zata mayar dashi masaukinsa zuciyarsa cike da tunanin wannan kallo wanda Sarauniya Akisatul Sauwara tayi masa wanda ya kasa gano ko na mene ne tsakanin SO da tausayi ko kuma KAUNA. Kamar yadda Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada haka al'amarin ya kasance wato da yammaci ta tura aka zo dashi izuwa filin motsa jini dake bayan turakarta. Yana isowa wajen sai ya iske sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye cikin shigar yaki rike da takobi. Yana isowa sai shima aka miko masa sulke takobi da garkuwa. Ba tare da gardamar komai ba ya karba ya sanya sulken amma sai yaki karbar garkuwar saboda yaga itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Lubainu tace ina mai shawartarka daka dauki garkuwar nan ka rike domin zan iya baka mamaki. Lubainu yayi murmushi yace,ai ni dai ke baki rike garkuwa ba a matsayinki na 'ya mace nima ba zan rike ba. Akisatul Sauwara tace,shi ke nan muje zuwa mu gani mahaukaci ya hau kura. Kafin Yarima Lubainu ya budi baki kara cewa wani abu tuni Akisatul Sauwara ta zare takobinta ta daka tsalle ta kawo masa wawan sara a kafada. In ba don Lubainu ya daka tsalle gefe daya ba cikin tsananin zafin nama da tuni ta tsargeshi gida biyu. Nan fa suka kacame da azababben yaki ta rinka kai masa mugayen hare hare da wani irin azababben zafin nama da karfin gaske wanda yai mutukar bashi mamaki tun da yake haduwa da mazaje bai taba haduwa da mai kamar jarumtakarta ba. Bisa dole shima ya zage damtse yaci gaba da kare hare haren nata amma sai yaga duk da haka tana neman kuntatashi,don ta fara turashi jikin bango tana hanashi yin kyakkyawan motsi yadda ko yay yayi sakaki zata iya gamawa dashi. Nan fa shima ya fara maida martani,ai kuwa sai yakin nasu ya zama abin tsoro abin tashin hankali,hatta kuyangi,borori da dakarun dake tsaitsaye a zagayen filin saida hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin irin azababben yakin dasu sarauniya ke yi. Saida suka dauki dogon lokaci a haka dayansu bai sami nasarar koda shafar jikin abokin gwaminsa ba. Al'amarin dayai mutukar girgiza Yarima Lubainu shine ko alamar gajiya babu a tare da sarauniya alhalin shi kuwa ya fara haki Koda ya fuskanci cewa lallai zaiji kunya idan baiyi da gaske ba,sai ya sauya salon fadan ya hada dakai naushi da bugu.Ai kuwa sai ya shammaci Akisatul Sauwara ya doki kafafunta da kafarsa guda tayi sama tana mai katantanwa amma tana fadowa kasa sai ta dafa kasa da hannunta guda tayi sama kamar sifirin ta doki kirjinsa da kafarta.Saboda karfin dukan saida Lubainu yayi tsalle sama da baya ya fado kasa,amma shima sai yayi wuf ya mike tsaye Zumbur. Yana mai gyara tsayuwa a lokacin da Akisatul Sauwara ta duro kasa bisa kafafuwanta.Kawai sai ta dubeshi tayi murmushi tace,tabbas yanzu bani da wata fargana a cikin tafiyar da zanyi tare dakai domin na gamsu cewar kai jarumi ne na kwarai. Koda jin wannan batu sai ran Lubainu ya baci daya fahimci cewar sunyi wannan gumurzu ne don kawai taga iyakar jarumtakarsa. Amma sai ya boye fushin nasa bai nuna mata ba. A wannan lokaci duk sun jike Sharkaf da gumi don haka sai ta shawarce shi akan yaje yayi wanka ya hutu,amma bazasu sake haduwa ba sai gobe da safe yayin wannan tafiya. Nan take kuwa Yarima Lubainu ya cire sulken dake jikinsa ya bayar gami da takobin hannunsa ya tafi yana waigen sarauniya yana yi mata wani irin kallo wanda itama ta fada cikin wasi wasi domin ta kasa tantance irinsa.Kallo ne mai kama dana jin haushi ko na gajiya? Nan dai itama ta juya ta nufi hanyar da zata kaita turakarta. Kafin Alfijir ya keto tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta gama yi musu shirin tafiya,kuma bata bukaci rakiyar dakarunta ko kuyanginta ba.Su biyu rak suka fice daga birnin Rauhul Bagadar bayan ta baiwa tsohuwa Dulaiba jiran gari.ALLON SIHIRI Littfina na biyu(2) Part C Nan fa Lubainu da Akisatul Sauwara suka sakarwa dawakansu linzami suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya basu yada zango ba,idan suka ji yunwa ko kishirwa sai dai su bude jakar guzurinsu su kama cin abincin ko kuma su daga battar ruwansu su sha.Tsawon wannan lokaci dayansu bai ce uffan ba,babu wanda yayiwa wani magana.Daf da faduwar rana ne dawakansu suka fara nuna alamar sarewa domin suna bukatar ruwan sha.A sannan ne Akisatul Sauwara ta dubu Yarima Lubainu tace,yakamata mu yada zango inba haka ba kuwa dawakanmu zasu sare.Lubainu yayi murmushi yace,ai tun dazu nake son na sanar dake hakan amma sai na kasa don kada kice na gaza.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya tace,ai tun kafin ma mu bari birnina ka sare tunda ka bari mukayi kunnen doki a gasar yakin da mukayi ni da kai.Lubainu ya girgiza kai yace aa bamuyi kunnen doki ba tunda nine na fara kai ki kasa kafin ke ki kaini.Akisatul Sauwara ta sake yin murmushi a karo na biyu tayi shiru bata kara cewa komai ba.Cikin sa'a kuwa sai suka hango wata fadama a can gabansu nesa kadan kuma a kusa da fadamar akwai duwatsu da dogayen bishiyoyi.Cikin murna suka karasa bakin koramar suka sauka.Dawakansu suka kama shan ruwa suna cin ciyawar dake bakin koramar.Kawai sai Akisatul Sauwara ta kwance jakar guzurinta ta dauko tanti ta shiga aikin kafashi. Al'amarin dayai mutukar baiwa Yarima Lubainu Mamaki kenan,ya mike da sauri ya kama ma ta aikin yana mai cewa,haba ranki ya dade saboda me bazaki umarceni dana kafa tantin ba? Ai mulki ba wasa bane dole ne na baki girmanki a wannan fannin.Sa'adda Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tai murmushi tace,kamar yadda nake mai mulki kaima ai mai mulki ne tunda ka kasance dan sarki.Lubainu yayi murmushi yace,ai dan sarki ba sarki bane,don haka yanzu kin bani tazara mai yawa.Darajarki da daukakarki a duniya ta ninka tawa sau goma.Akisatul Sauwara tayi 'yar guntuwar dariya tace,abinda ka fada gaskiya ne amma ai duk sarkin daya baro birninsa ba sarki bane tunda idan ya hadu da wanda bai sanshi ba zai iya wulakantashi ya wuce abinsa. Ni yanzu na ajiye karagar mulkina a gefe daya na dauki kaina daidai da kowanne talaka har sai bayan bukatarka ta biya mun koma kasata.Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Lubainu yayi sanyi yace,yake wannan sarauniya mai daraja,yanzu kina nufin kice bakya tsoron irin tsananin tashin hankalin dake cikin wannan tafiya tawa har kike tunanin zaki ci gaba da bina har izuwa lokacin da burina zai cika? Ki tuna fa cewa yanzu akan mataki na farko muke kawai.A kalla nan gaba akwai sauran matakai bakwai zuwa goma a gabanmu tunda sai mun nemo barin Allon Sihiri na biyu dana uku,sannan mu tafi neman abokan tafiyarmu mutum uku.Yayin da Sarauniya Akisatul Sauwara taji wannan batu sai tayi murmushi tace,ai rai ba abakin komai yake ba indai akwai biyan bukata,kuma matsoraci har abada bazai zama gwani ba.Yayin da Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya cika da mamaki gami da wasi wasi. Abinda ya bashi mamaki shine aka wane dalili sarauniya Akisatul Sauwara ta siyar da rayuwarta don ganin bukatarsa ta biya? Abinda zuciyarsa keyi masa wasi wasi kuwa shine,anya kuwa sarauniya Akisatul Sauwara bata da wata manufa ta binsa wannan tafiya?. A zahiri dai bai ga wani abu dazata amfana dashi ba kuma bata gaya masa da bakinta ba.Nan dai Yarima Lubainu ya taimakawa Sarauniya Akisatul Sauwara suka karasa kafa tantin kuma ya kwance jakartaya debo kayan shimfidarta ya gyara mata inda zata kwana.Bayan ya gama kintsa komai a daidai lokacin da magriba ta kunno kai sai suka fara jiyo kukan dabbobin daji dana manyan tsuntsaye masu shawagi a sama.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantin da sauri ta tofa wadansu dalasiman tsafi gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasa,sanna ta dawo cikin tantin ta dubi Yarima Lubainu wanda ke shirin biyota izuwa wajen tantin don tabbatar da cewar babu wani mugun kwaro ko raminsa.Cikin mamaki Lubainu ya dubi Akisatul Sauwara yace,mene ne naga kin fita da sauri daga cikin tantin nan kuma kin dawo da sauri?Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace naje na samar mana da tsaro ne a waje.Ko dabba ko mutum ko aljan bai isa yazo nan ba ya cutar da mu,don haka ka saki jikinka kayi barci mai dadi.Koda gama fadin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta nufi inda shimfidarta take ta fara kokarin cire tufafin jikinta domin tasa rigar bacci.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya juya ya fice daga cikin dakin.Da yake a wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ta fara kadawa,sai Yarima Lubainu yaje ya samo itatuwa ya kunna wuta ya zauna a gaban wutar yana jin dumi.A daidai wannan lokaci ne yaji yunwa ta kamashi.Don haka sai ya bude jakar guzurinsa ya fiddo da abinci ya kama ci.Kwatsam!ba zato ba tsammani sai yaji takun sawu a bayansa.Cikin zafin nama Lubainu ya zare takobinsa ya mike tsaye zumbur!Koda yai arba da abinda ya tunkaroshi sai yai sauri ya sunkui da kansa kas a lokacin da jikinsa ya kama tsuma.Ba wani abu ya gani ba face sarauniya Akisatul Sauwara sanye da wata doguwar Rigar fara mai shara shara wacce ta bayyana komai na surar jikinta.Ganin tsananin kyawun surar jikin nata ne yasa jikinsa ya kama kyarma kuma zuciyarsa ta kama bugawa da sauri da sauri kuma da karfi.Tunda Yarima Lubainu ya taso a rayuwarsa bai taba ganin 'ya mace haka ba a rayuwarsa sai wannan karon,don haka sai ya danne zuciyarsa da karfin tsiya,duk da cewa bashi da cikakkiyar lafiyar da zaiji wani abu sai zuciyarsa ta rinka harbawa.Ita kuwa sarauniya Akisatul Sauwara tazo masa ne a cikin wannan siffa don ta jarraba iyakar hakurinsa duk da cewar shine mutum na farko da ya taba ganinta a hakan.Kai tsaye ta matso daf dashi ta dubeshi cikin murmushi mai rikirkita kwakwalwa da hankali tace,shin na baka tsoro ne bisa jin sautin tafiya ta? Ba tare da ya dago kai ba ya dubeta sai yayi yake sannan yace,ai dole ne naji tsoro tunda ban taba zaton zanji wani motsi ba a baya.Koda jin haka sai Ta bushe da dariya sannan ta kama hannunsa suka zauna tare a gaban wutar suka ci gaba dajin dumin tare.Koda Lubainu yaga taki sakin hannunsa sai ya mike tsaye yace ina zuwa.Kawai sai ya zagaya bayan tantin yayi kamar yana bawali ne sannan ya dawo ya sake zama a kusa da ita suna fuskantar gabas,amma wannan lokaci bai yarda sun zauna daf da daf ba sai daya zamana cewa akwai tazarar taku uku a tsakaninsu.Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba sannan Lubainu yayi ajiyar numfashi ya dubeta yace,ranki ya dade ya kamata kije ki kwanta kiyi barci tunda dare ya soma kuma akwai gajiyar tafiya a tare dake.Wai shin ma mene ne dalilin dayasa kika fito ne alhalin gashi kinyi shirin bacci? Lokacin da Akisatul Sauwara taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,ya kai Lubainu kayi sani cewa a rayuwata tun daga kuruciyata har izuwa girmana ban taba kwanciya ba ni kadai a cikin turakata face tare da kuyangina.Yau gashi zan kwana ni kadai a cikin tanti kuma a cikin daji.Tabbas ko na kwanta barci ba zai zo min ba face ina jin numfashin dan Adam a kusa da ni.Bisa wannan dalili ne na kasa barci har na fito wajenKa.Abinda nake so dakai yanzu shine kazo mu koma cikin tantin nan mu kwana muyi barci.Koda jin wannan batu sai Idanun Yarima Lubainu suka zazzaro ya dubeta cikin alamun tsananin firgici da tsoro yace gaskiya bazan iya barci ba a kusa dake.Ranki ya dade kiyi sani cewa babu wani 'da namiji dazai ganki a cikin wannan yanayi bai rude ba ya kamu da sha'awarki da sonki.Ni a matsayina da saurayin da bai taba sanin 'ya mace ba kuma wanda yake nisantarku dole ne naji tsoron taraiya dake.Koda Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta kyalkyale da dariya sannan tace,kamar yadda baka taba sanin 'ya mace ba nima ban taba sanin wani 'da namiji ba,don haka na baka amanar kaina.Ina mai tuna maka cewa samun yin barcina yana gareka.Koda gama fadin hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye ta shige cikin tantin taje ta kwanta akan shimfidarta kanta na kallon saman tantin ta fada kogin tunani.Shi kuwa Yarima Lubainu dake a zaune a wajen gaban wuta sai ya mike tsaye ya kama kai kawo cikin tsananin damuwa da wasi wasi.Daga can sai ya shiga cikin tantin yayi shimfida a gefe daya nesa da ina Akisatul Sauwara ke kwance ya kwanta. Yana kwanciya sai zuciyarsa ta tafi izuwa tunanin irin gwagwarmayar dayayi a baya.Yana cikin wannan tunani ne kuwa barci ya saceshi har yana munshari bai sani ba,kuma bai sake farkawa ba saida gari ya waye rana ta kwalle.Yarima Lubainu na bude idanunsa sai ya hango shimfidar Sarauniya Akisatul Sauwara wayam babu kowa akai.Koda yayi arba da abinda ke kan shimfidar sai zuciyarsa ta buda da kafi ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani abu ya gani ba akan shimfidar face Allon Sihirin nan na Sarauniya Akisatul Sauwara.Allon ne tsurarsa akan shimfidar wato an cireshi daga cikin kwalbar data lullubeshi.Har Yarima Lubainu ya yunkura zaije ya dauki Allon Sihirin sai wata zuciyar ta daka masa tsawa tace,shin ka manta ne da guzurin da mahaifinka ya baka

Chapter 4 of 19