Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tulun ganyaye a sama da suka cika gami gami da duhuwa mai yawan gaske, ga kuma tarin manyan duwatsu masu siffofin ababan tsoro da kuma jibga-jiggan tsaunika. Muggan dabbobin daji kuwa adadinsu ya wuce kima sai dai ka gansu suna ta gilmawa, in ba don a sama muke tafiya ba, da sai mu yita yaki da su sai da muka yi tafiyar sa'a hudu a sama cikin iska a dajin na shajaril maurud, sannan muka jiyo wani irin gagarumin gurnani na dodo gurmazu, koda jin gurnanin wanda ya cika djin gaba daya sai hantar cikina ta kada, duk da jarumtaka da dakakkiyar zuciya irin tawa. Shi kuwa aljani barzila gaba dayan jikinsa ne ya dume da zafi, tamkar an tsomasi a ruwan dumi mai tiriri, ya kama karkarwa bai san sa'adda ya saki fitsarin firgita ba. Duk da cewa a tsorace nake, sai da dariya ta kwace mini, na ce, "Haba namijin duniya, ai ka karya alkadarin jarumtakarka wadda kayi a baya, domin bai kamata ba ace tsoro har yasa ka saki fitsari saboda kawai ka ji gurnanin dodo gurmazu ba". Cikin karfin hali, da rawar murya barzila yace, "Haba ya shugabana, ai bama fitsari ba, ko kashi na saki bai kamata kayi mamaki ba, Katuna fa cewa shi fa dodo gurmazun nan a halin yanzu duk duniya babu wata halitta mai karfin damtsensa da karfin sihirinsa. An ce komai kaurin bishiya, idan ya nausheta da hannu daya, saita ratattake, ta fadi kasa idan kuwa ya kwarara ihu, girgizar kasa ake yi, tsawa da walkiya na amo daga cikin bakinsa. Komai yawan maza a cikin dakika biyar yake tarwatsasu, walau rundunar bil'adama ko ta aljanu". Kawai sai nayi ajiyar zuciya, nace "Lallai kuwa baka yi laifi ba, domin tsoro wajibine, amma fani bana tsoron bala'I dan babu Wanda banganiba, sai dai na firgita da shi. Ai kawai muci gaba da tafiya, ina so ka durfafi inda kake jiyo sautin wannan gurnani". Cikin matukar tsoro aljani barzila yace, "Banki tatakaba ya shugabana, amma dai katuna cewa, "Riga kafi yafi magani. Bai kamata mu tari dodo gurmazu gaba da gaba ba, zai fi kyau mu dunga yin sanda da labiya har mu isa inda yake, ai shi yaki dan zamba ne a duk sa'adda abokin gaba ya fara ankara da abokin gabarsa, to yana iya samun hikimar da zai iya samun nasara akansa da wurwuri". Batare da wata gardama ba, na amince da wannan shawara, saboda haka sai aljani barzila ya sauko kasa ya dira bisa turba, nima na sauko daga kansa muka fara tafiya sanda muna leke-leke, wani lokacin ma har kwanciya muke a kas muna tafiya da ruf da ciki. Kaico! Rashin sani yafi dare duhu, ashe duk wannan tafiyar dudduke da mukeyi dodo gurmazu ya hangomu tun daga can nesa, saboda kwarin idanunsa yana iya hango abin dake tafiyar sa'a shida a bayansa ko gabansa, sannan duk irin abin da ya jingina ajikinsa sai kalar jikinsa ta koma irin launin abin sak komai hasken da ke wajen, ido bazai iya shaidashi ba. A wannan lokaci da muke tafiyar ruf da ciki, dodo gurmazu na can sama bisa wata gabjejiyar bishiya mai tsananin girma da tsawo. Ni kam na tabbatar da cewa, wannan bishiya babu ta biyunta a duniya, domin ko a tarishi ban taba jin labarin bishiya irintaba. Haka dai muka ci gaba da tafiyar ruf da ciki har muka iso gaban wannan narkekiyar bishiya, amma bamu ga komai ba, kuma bamu sake jin gurnanin dodo gurmazu ba. Mun dade a kwance muna kasa kunne ko zamu ji wani motsi, amma ba muji ba. Daga can sai muka mike tsaye na dubi aljani barzila nace, "Abin da zamu yi kawai mu hau can saman wannan bishiya mu tsaya in dai muka yi haka zamu iya hango dodo gurmazu a duk inda yake domin zaton da nake ba a nan kusa yake ba. Yana nesa da mu ne". Koda jin wannan shawara tawa, sai barzila ya cika da murna, yace, "kwarai kuwa kayi tunani mai kyau, haka za a yi" nan take na sake hawa bayan barzila yai sama dani, sai da muka kure tsawon bishiyar sannan muka sauka a kan wani katon reshenta guda. Cikin hanzari aljani barzila ya zaro kwari ya dana akan wannan katuwar baka tashi ya tabe bakan ya shiga kalle-kalle ko zai hango dodo gurmazu ya sakar masa harbi. Ni da Nake bayan barzila sai na daga wani gatari nawa sama na tsaya cak! A waje daya ina kallon gabas da yamma, kudu da arewa, kuma ina leko kasan bishiyar. A binda bamu saniba shine, munyi aikin banza domin kuwa mun kulle kofar gida da barawo a ciki, domin kuwa tsakaninmu da dodo gurmazu bai wuce taku uku ba. Ashe shi ma yana kan bishiyar amma da yake kalar jikinsa ta saje da kalar jikin bishiyar ko kadan bamu ganshi ba. Kwatsam! Ba zato kuma ba tsammani, sai dodo gurmazu ya sauya kalar jikinsa izuwa ainashin tasa ta gaskiya, ya baiyana daf da aljani barzila. Koda barzila yai arba da dodo gurmazu yaga irin kwar jininsa da muninsa sai ya firgita kuma ya dimauce, bai san sa'adda ya saki kwari da bakan dake hannunsaba ya juya da nufin ya bude fuka- fukansa ya tashi sama, amma sai dodo gurmazu ya cabo jelarsa cikin zafin nama, sai ga barzila na reto a sama, tamkar dan biri na wasa. A dai-dai wannan lokaci ne na dako tsalle daga inda nake tsaye na taho a sama zan kirbawa gurmazu sara a tsakiyar kansa, amma sai gurmazu ya mangareni da daya hannun nasa, na rikito kasa, tun asama na fita daga haiyacina, naji kamar anyi mini kanshin mutuwa. Ai kuwa ina fadowa kasa na sume. Nidai ban san abin daya faruba daga sannan sai farkawa nayi na ganni a cikin katon keji tare da aljani barzila, da kuma wadansu aljanu kimanin su dubu biyu, duk suna ta faman rusa kuka shi ma aljani barzila sai ya tayasu kukan. Koda barzila yaga na farfado, sai ya dubeni a fusace, yace, "Kaga irinta ko, ai dama na gayamaka bamu isa mukawar da dodo gurmazu ba, ga shi yanzu ya kamamu. Wadannan aljanu duk fursunoninsa ne, kuma sun gaya mini cewa, sudubu arba'in ne ya kamosu, kullum yana diban biyar yana cinyewa, yanzu saura su dubu biyu kacal, kaga kenan muma mun zama abincin sa. Haka kuma sun tabbatar mini da cewa babu wani makami ko sihiri da zai iya karya wannan keji, har mu sami damar fita daga cikinsa. Abin da zance da kai kawai shine, ince koka bar wasiyya a gida kafin muyi wannan tafiya?". Yayinda naji wannan tambaya, sai na bushe da dariya, al'amarin daya baiwa dukkanin fursunonin aljanun mamaki kenan, domin gashi su a matsayinsu na aljanu, suna kuka saboda sun shiga bala'In da babu fita, amma ni a matsayina na bil'adama ina dariya. Ti me nake takama dashi? Shin ina zaton zan iya fita ne daga cikin wannan masifa? Amsar da basu sani ba kenan, amma dai ai tunda suna tare dani zasu zuba ido su ga iyakar gudun ruwana. sHIN HASANUL MAUZUR DA ALJANI BARZILA ZASU KUBUTA DAGA HANNUN DODO GURMAZU, HAR HASANUL MAUZUR YA KASHE WANNAN GIWA TA DODO GURMAZU, YA YANKO HARSHENTA? WADANNE SAMARI Ne ZASU SHIGA GASAR NEMAN AUREN GIMBIYA SHULAIRA, KUMA DAGA CIKINSU WAYE ZAI CI GASAR YA ZAMO MIJINTA. Muhadu a TARWATSA MAZA littafina biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Daga mai debe maku kewa Khamis Idris yawan comment dinku shizai sa acigaba Dana biyu anjima if not sai jibi lolx An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ALLON - SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part A LAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __OKACIN DA Yarima Mangul da Barde Ruhaisu suka ruguntsume da azabbaben yaki mai tsananin muni,sai wani abin mamaki ya afku domin kuwa gashi a zahiri Yarima Mangul yafi barde Ruhaisu karfin damtse da iya yaki,domin da kyar ma barde Ruhaisun ke iya kare saransa saboda nauyin saran,amma da yake Barde Ruhaisu nada matukar zafin nama gami da juriya da mugun naci sai Yarima Mangul ya kasa cutar dashi.Saida suka shafe sa'a guda cur suna wannan mugun artabu amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin dayan ba.Al'amarin daya fusata su kenan kowa yaja da baya suka tsaya suna kallon kallo suna haki kamar zakaru.Koda Yarima Mangul ya karewa Barde Ruhaisu kallo ya fahimci cewar ba sa'ansa bane a kallah Barde Ruhaisu zai iya girmarsa da tazarar shekaru kusan goma sai takaici ya kamashi yaga cewa ai yakamata yayi ace tuni ya gama da wannan JARUMI tunda yafishi kuruciya,idan kuwa kafi mutum kuruciya zaka iya finsa kuzari,saidai kawai ya nuna maka tsohon kashi.Gama aiyana hakan keda wuya sai Yarima Mangul ya daga hannunsa sama yana mai baiwa dakarunsa inkiyar su afkawa su barde Ruhaisu.Ai kuwa shima Barde Ruhaisu sai ya baiwa nasa dakarun umarnin su taresu.Nan fa kowacce RUNDUNA ta ruga da rugu izuwa kan dayar ana haduwa a tsakiya aka ruguntsume da azababben yaki.Karar karafa gami da ihun mazaje ya cika dajin gaba daya.Jini ya rinka fallatsi da fantsama sai gashi al'amarin ya rinciba a tsakanin dakaru dubu da guda dari.Kodaga nesa ne mutum ya zuba ido yana ganin abinda ke faruwa bazai iya gane bangaren mutum zai zuba ido da kyai a cikin lura zai gane cewa anfi ragargazar dakarun Yarima Mangul.Lokacin da aka fara wannan gumurzun ne Yarima Mangul ya sami damar matsawa kusa da inda Yazarina ke tsugunne saboda duk Badakaren Barde Ruhaisu da yazo gabansa kwaf daya yakeyi masa.A lokacin Barde Ruhaisu ya shiga cikin tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana ta ragargazarsu yana yi musu sarki ya hana dawa tsayuwa.Hakan ne yasa ya sha'afa ya bar daidai wajen da Yazarina ke tsaye.A wannan lokaci da yakin yai tsamari ne Yazarina ta dimauce kuma ta firgice saboda wannan ne karon farko a rayuwarta da akayi yaki a gabanta.Koda taga an sare wani Badakaren ya fado a gabanta jininsa yai feshi akan fuskarta bata san sa'adda ta kurma uban ihu ba ta daka tsalle sama.Faruwar hakan keda wuya sai rawanin fuskarta ya subuce ya fadi kasa.Kyakkyawan dogon gashin kanta ya tarwatse a sama ya zubo kasan kafadunta.Koda Yarima Mangul yayi arba da fuskar Yazarina yaga itace sai ya kamu da tsananin mamaki ya daka tsalle sama ya dira a bayanta yasa takobinsa a wuyanta ya ritsata kuma ya daka tsawa.Take aka daina yakin kowa ya juya ya dubeshi.Take aka daina yakin kowa ya juya ya dubeshi.A sannan ne Barde Ruhaisu ya hango abindake faruwa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun.Yarima Mangul ya bushe da dariyar farinciki a lokacin daya dora yankakken hannunsa akan kafadar Yazarina ya sumbaci wuyanta yace,marhaban da ganinki ya abar kaunata.Tabbas nayi matukar farin cikin sake saduwa dake a wannan lokaci da ban taba zata ba.A tsammani sai na karbi karagar mulkin ubana sannan zan sami damar sake ganinki na kashe mijinki Lubainu koda yana raye domin na mallakeki amma sai gashi yanzu na sameki a banza ba tare da wata matsala ba.Ki sani cewa yanzu ina gama kashe wadannan abokan tafiya naki zan tafi dake can sansani na a daura mana aure bisa dole..Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa tuni Yazarina ta tofa masa yawu a fuska sannan tace karyarka tasha karya saidai ka auri gawata amma bani ba.Yaza'a yi na auri azzalumin daya lalata rayuwar wani saboda son zuciyarsa?Ka sani cewa ni yanzu bana tsoron mutuwa tunda kasa mijina ya tafi izuwa inda zai iya rasa rayuwarsa gaba daya.Idan kuwa har Lubainu ya mutu to nima banga amfanin tawa rayuwar ba saidai na bishi.Koda Yazarina tazo nan a zancenta a lokacin da jikin su Barde Ruhaisu duk yayi sanyi sun sauke makamansu kawai suna kallon abin da ke faruwa tsakanin Yarima Mangul da Yazarina cikin alamun tsananin tsoro da fargaba.Har izuwa wannan lokaci Yarima Mangul bai cire kaifin takobinsa daga kan wuyan Yazarina ba don haka sai ya sake bushewa da dariya,kuma yayi amfani da dan yatsansa guda daya ya lakuci yawun bakin Yazarina data tofa masa akan fuskarsa ya lashe a bakinsa yace,ban taba jin abu mai zakin yawun bakinki ba yake MASOYIYATA.Yana gama fadin hakan sai ya dubi Barde Ruhaisu ya daka masa tsawa yace maza ku bude fuskokinku kaida yaranka kuma ku zubar da makamanku ko yanzu nan na shaftare makogwaron yazarina.Har su Barde Ruhaisu zasubi wannan umarni sai Yazarina ta daka musu tsawa tace,kada ku yarda ku aikata hakan domin bazai kasheni ba saboda bashi da burin dayafi ya mallakeni a rayuwarsa.So yaje kawai ya yaudareku ku zubar da makamanku yasa a kasheku a banza.Koda ma ya kasheni din bani da asara ko nadama,domin babban bakin cikina shine ya mallakeni din.Ku ci gaba da yaki har sai idan karfinku ya kare,domin ku zamto masubin umarnin sarki.Zaku iya bude fuskokinku domin ko baku bude ba su ba yanzu yasan cewa ku dakarun sarki Sailur ne.Koda Yazarina tazo nan a jawabinta sai Barde Ruhaisu da dukkan sauran yaransa kimanin mutum saba'in suka bude fuskokinsu kuma suka daga takubbansu sama suna masu niyyar cigaba da yaki.Koda Yarima Mangul yayi arba da fuskar Barde Ruhaisu sai ya jinjin kai yace,tabbas babu mamaki domin banda sarki yakin garinku da Yarima Lubainu babu wanda zai iya tarata muyi GUMURZU na tsawon wannan lokaci ba tare dana sami nasarar hallakashi ba face kai.Ai kuwa dayanmu bazai bar wannan wuri ba a raye saidai a dauki gawarsa!Yarima Mangul na gama fadin hakan sai ya wurga Yazarina izuwa hannun sarkin yakinsa ya cafketa ya dubeshi yace,mazaka ka tafi da ita izuwa sansaninmu a tsareta kuma ka dawo nan tare da dakari dubu goma.Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu ya falfalo da azababben gudu izuwa inda Yazarina take ya kutsa ta tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana karkadesu da karfin sara da suka domin ya isa inda sarkin yakin Yarima Mangul yake a lokacin daya ja Yazarina da karfin tsiya izuwa kan wani doki.Koda ganin haka sai shima Yarima Mangul ya falfalo da gudun tsiya da nufin yasha gaban Barde Ruhaisu ya hanashi isa inda su Yazarina suke.Koda ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin Barde Ruhaisu da Yarima Mangul sai Ruhaisu ya daka wawan tsalle a sama ya tsallake Yarima Mangul ya doki gadon bayan sarkin yakin nasa.Ba shiri sarkin yakin ya saki Yazarina ya fadi can gefe daya.Kafin Yarima Mangul ya juyo baya da gudu yazo ya riskesu tuni Barde Ruhaisu ya daka tsalle sama ya haye dokin dake gabansa.Kawai sai ya mikawa Yazarina hannunsa ta kama ya dagota sama cak ya dorata a bayan dokin kuma ya zaburi dokin da gudu izuwa cikin daji.Koda ganin haka sai shima Yarima Mangul ya ruga izuwa inda nasa dokin yake ya daneshi kuma ya zabureshi da gudu yana mai bin bayan dokin su Ruhaisu.Nanfa filin yakin ya watse kowacce runduna hankalinta ya tafi izuwa tafiya neman shugabanta tamkar ma an manta mummunan yaki da ake fafatawa.Lokacin da Barde Ruhaisu ya sami nasarar gudu da Yazarina akan doki suna tsala gudu a cikin daji ba tare da sanin inda suka dosa ba sai suka jiyo sukuwar doki a bayansa.Cikin firgici Yazarina ta waigo baya kawai sai taga ashe Yarima Mangul ne ya biyosu kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin da biyar ba,kuma dokin nasa gudun bala'i yake yi yana rike da linzaminsa da lafiyayyen hannin nasa sai dada zungurar dokin yake da kafafunsa yana kara masa kaimi ga zabgegiyar takobinsa rataye a bayansa.Cikin tsananin firgici Yazarina ta juya tace,yakai Ruhaisu kayi sani cewa wannan azzalumin makiyi makiyin namu yana daf da riskarmu.Koda jin haka sai shima Barde Ruhaisu ya karawa nasa dokin kaimi.Nanfa dawakan suka cigaba da kasa mugun gudu,tseren gudu na ban al'ajabi.Koda karfin gudun dokin Ruhaisu ya karu sai Yazarina taji tana neman fadowa kasa don haka ba shiri tasa hannayenta biyu a zagayen cikin barde Ruhaisu ta rukeshi gam gam da kyau ta kwantar da kanta akan gadon bayansa.Haka dai aka cigaba da wannan tseren gudu na tashin hankali har izuwa tsawon sa'a guda.Kwatsam sai dokin Barde Ruhaisu dana Yarima Mangul din suka iso wani wuri mai tudu wanda basu ankara dashi sukayi tuntube suka zube kasa gaba dayansu har su Barde Ruhaisu.Cikin gaggawa Barde Ruhaisu ya mike tsaye zumbur ya kama hannun Yazarina ya tasheta tsaye suka sake ruguntsumawa da gudu izuwa cikin daji.Shima Yarima Mangul a dimauce ya mike tsayen da sauri yabi su a guje suka kasa sabon tseren gudu kafafunsu tamkar zasu tashi sama saboda karfin gudu.Faruwar hakan keda wuya sai Yazarina ta sare ta fadi kasa kuma a lokacin tazarar dake tsakaninsu da Yarima Mangul bata wuce taku ashirin ba.Koda Yarima Mangul yaga Yazarina ta fadi kuma gashi babu makami a jikin Barde Ruhaisu sai yayi wuf ya zaro sharbebiyar takobinsa yayi kansu da nufin ya riskesu kafin Barde Ruhaisu ya tasheta tsaye ya sare masa kai.Amma sai yaga Barde Ruhaisu yayi wuf cikin wani bakin zafin nama da bajinta ya suri Yazarina tamkar sillan karah ya daga ya goyata a bayansa.Ita kuma ta rukunkumeshi ya cigaba da falfala azababben gudu.Sai gashi sun ci gaba da tseren gudun nasu tamkar mai kaya ya biyo barawo.Yarima Mangul ya dage iya karfinsa domin ya cimmusu amma sai abu ya gagara.Al'amarin daya daurewa Yarima Mangul kai kenan ya cika da tsananin mamakin yadda akayi ya kasa cimma Barde Ruhaisu duk da cewa yana fama da nauyin Yazarina wacce ke goye a bayansa.Barde Ruhaisu na cikin wannan gudu ne ya riski wani katon tsauni mai fadi,girma da tsawon tsiya a gabansa,kuma babu wata hanya da zai iya ratsewa tsaunin dole ne yabi ta kansa in ba haka ba kuwa saida ya tsaya ya jira isowar Yarima Mangul ayi wacce za'ayi.Ta yaya zan fuskanci Yarima Mangul alhalin babu makami a hannuna?Tabbas bani da wani zabi wanda yafi na hau kan wannan tsauni.Ya bawa kansa amsa a cikin zuciyarsa.Yaba gama aiyana hakan sai ya hau kan tsaunin goye da Yazarina a bayansa yana cigaba da gudun.Shima Yarima Mangul yana isowa bai tsaya jiran komai ba sai yabi shi izuwa kan tsaunin a guje yana ruri da kururuwa mai ban tsoro,cikin murna domin gani yake kamar ma ya gama samun nasarar kashe Barde Ruhaisu gami da mallakar Yazarina.Nanfa duka cigaba da gudu akan tsaunin tun sunayi da karfinsu da guzarinsu har saida suka sare suka fara faduwa kasa suna mikewa da kyar suna haki.Saida suka shafe sa'a daya da rabi suna gudu gudu,tafiya tafiya akan tsaunin sannan suka iso can kokoluwar karshensa.Koda Yazarina Da Barde Ruhaisu suka leko kasan tsaunin wanda saboda tsananin nisan zurfinsa mutum baya iya hangi abinda ke xan kasan nasa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,a lokacin da suke ta fama haki saboda tsananin gajiya tamkar ransu zai fita.A daidai wannan lokaci ne shima Yarima Mangul ya iso kusa dasu da kyar yana haki da layi rike da takobinsa.Koda yaga cewa ai sun iso karsshen tsaunin sai ta dubesu ya bushe da dariyar farin ciki duk da cewa makogwaronsa a bushe yake saboda muguwar kishirwa gashi babu ruwa a kusa.Suma su Yazarina haka suke jin tsananin kishirwa tamkar zata kashesu domin yawun bakinsu ma daukewa yake kamar babu shi.Yarima Mangul ya gyara tsayuwarsa irin ta wadanda suka sami nasara ya dora zabgegiyar takobin tasa kan kafadarsa ya dubesu cikin izaa yace,yanzu kuma ta yaya zaku iya guje mini tunda gashi kunzo makura?Tabbas yanzu zan kasheka yakai Barde Ruhaisu,amma fa ka burgeni domin kayi jarumtakar da ban taba zaton kana da ita ba,kuma dole ne na rubutaka a cikin KUNDIN TARIHIN rayuwata,saidai kash,jarumtakarka taka ta zama ta banza tunda baka cika aikin sarki Sailur ya baka na kare Yazarina kuma gashi zaka mutu a banza.Koda Yarima Mangul yazo yazo nan a zancensa sai Barde Ruhaisu ya tari numfashinsa yace,kaicinka yakai wannan azzalumin dan sarki wanda rayuwarsa ta gama tarwatsewa.Ka tuna cewa ka rasa masoyiyarka yazarina kuma ka rasa abokinka amininka YARIMA LUBAINU,Kuma ka cutar dashi bisa son zuciyarka don kawai ka rabashi da wacce ya riga ka SO da KAUNA kun zama ABOKAN GABA!Yanzu gashi ka rabu da mahaifinka ka rabu da matsayinka na Yarima tunda Mahaifin ya zama abokin gabarka,kana hada runduna ta YAN TAWAYE domin kaje ka kashe shi,kaga kenan kai yanzu abin tausayi ne tunda baka ga tsuntsu ba bakaga tarko ba.Baka da komai bakada kowa sai mafarkin zuciya wanda ina tabbatar maka da cewa har abanda ba zai taba tabbata gaskiya ba.Da wannan furuci nake yi maka bankwana domin ko zaka sami nasarar mallakar Yazarina saidai ka mallaki gawarta.Nima saidai ka tusa gawata amma ba dai ka kasheni da hannunka ba!!!Barde Ruhaisu na gama fadin haka sai ya juya da sauri ya daka tsalle ya fado kasan wannan tsauni mai zurfi shi da Yazarina suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu ce tazo. Just now · PublicALLON-SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part B Suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu tazo.Shi kuwa Yarima Mangul sai bakin ciki ya turnukeshi ya durkuse kasa bisa guiwoyinsa sannan ya wangame baki shima ya kwarara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin kuka saboda yasan cewa shike nan har abada bazai sake ganin Yazarina a raye ba.Kafin Yazarina da Barde Ruhaisu su kai rabin nisan tsaunin tuni sun sume saboda karfin iskar dake kadasu da kuma jirin daya kwashesu don haka sa'adda suka iso can karshen tsaunin sun zama tamkar gawarwaki sai ji kake tunjum...!sun fado cikin kogi.Lokaci guda suka nutse kasa amma sai suka taso sama igiyar ruwa ta rinka kadasu cikin tsananin sa'a da rabon sauran rayuwa ta kaisu can gefe kogin ta watsar.Saida suka shafe kusan rabin sa'aa kwance a gefen kogin a sume basu farfado ba,iska mai sanyi ce ta rinka kadawa a wajen ta yadda utace ta zamo sanadin farfadowarsu daga dogon suman da sukayi.Koda suka bude idanunsu suka kalli juna suka tabbatar da cewa suna raye basu mutu ba sai suka kamu da tsananin mamaki suka kama kyalkyala dariya.Saboda tsananin farin ciki Yazarina batasan lokacin data rungume Barde Ruhaisu ba.Faruwar hakan keda wuya ta tuna cewa ita fa matar Yarima Lubainu ce,kawai sai tayi saurin janye jikinta daga cikin na Barde Ruhaisu ta sunkui da kanta kasa ta budi baki cikin rawar murya da kunya tace ka gafarceni.Take shima Barde Ruhaisu yaji kunya ta lullubeshi yama rasa abinda zaice da ita.Kawai saiya juya mata baya ya fada kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi yana mamakin al'amarin da ya kasance hakan.Wannan shine abinda ya faru tsakanin Barde Ruhaisu Da Yazarina a lokacin da suka baro Birnin Zamrul domin neman Yarima Lubainu. 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 AL'AMARIN SU Bakon Jarumi kuwa lafiya sumul suka kwana a cikin fadar Boka Darbusa kuma dukkaninsu suka wayi gari cikin koshin lafiya ba tare da fuskantar wata matsala ba.Da sassafe bakon jarumi da bawansa Dazyan suka shiga daji suka farauto wani katon tsuntsu suka zo suka fisgeshi sannan suka gasashi.Da naman wannan tsuntsun kowa yayi kalaci.Bayan an gama kalacin ne bakon jarumi ya dubi Dazyan yayi masa inkiya shi kuwa sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki Darmanu yace,yaku abokan tafiya,maigidana yace na gaya muku cewa zamu cigaba da tafiya gaba dayanmu izuwa kogin BAHAR IMFALkamar yadda akayi alkawari da farko domin ya nuna muku karfi da iko na ubangijin musulunci amma badon ya yarda da tsafinku ba.Zai baku dama ku tsirar da rayuwarku da karfin ababan bautarku da karfin sihirigami da karfin damtsen ku har sai yaga kun kasa kare kan naku sannan zai taimakeku da taimakon ubangijinsa.Yace na dada jaddada muku cewa idan fa har aka isa can kogon Bahar Imfal aka samo abinda akaje nema da taimakonsa to dole ne ku karbi addininsa ko kuna so ko bakwa so,in ba haka na kuwa zaku zamo abokan gabarsa babu abinda zai rabaku face

Chapter 10 of 19