Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah bisa shimfida ya lulluba da bargo.Kawai sai tasa hannunta guda ta yaye bargon,take Dazyan ya farka yai firgigit.Koda yaga itace sai ya dukar da kansa kasa ya gaisheta cikin girmamawa.Kawai sai Jaruma Suhailat ta sunkuyo tayi masa rada a kunne sannan ta ruga izuwa cikin jeji domin farauto naman daza'ayi kalacin safe.Tafiyarta keda wuya sai Dazyan ya zaga bayan tantin Yarima Lubainu yayi kamar bawali zaije yayi domin a lokacin tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantinta ta tsaya tana mika da kallon yanayin dajin,kuma taga sa'adda Suhailat ta dashi Dazyan daga barci.Koda Dazyan ya zagaya bayan Tantin Yarima Lubainu sai ya kira sunansa a cikin karamar murya mai kama da rada.Yarima Lubainu ya amsa kiran,shi kuma yace dashi shugabata tace kayi sauri ka sameta a daji bangaren gabas domin ku tattauna ta tafi farauta.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya mike tsaye zumbur,dama a tube yake ko riga babu a jikinsa sai wani gajeren wando.ALLON-SIHIRI, Littafi na Biyar (5) Part D Dama a tube yake ko riga babu a jikinsa sai wani gajeren wando.Cikin hanzari ya sanya kayansa ya dauki KWARI DA BAKA sannan ya leko da kansa waje kadan sai ya gano Sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye a bakin tantinta tana yin asuwaki.Cikin hanzari ya maida kansa cikin tantin don kada ta hangoshi a lokacin da zuciyarsa ta cika da damuwa saboda yasan cewa indai ta ganshi zai tafi daji farauta cewa zatayi saita bishi.Jim kadan sai Yarima Lubainu ya sake lekowa waje,saiya hango Sarauniya Akisatul Sauwara ta bar kofar tantin nata ta nufi inda tanti sarki Darmanu yake.Cikin hanzari yayi amfani da wannan dama ya fice daga cikin tantin nasa yana sanda da labiya ya nausa cikin daji ba tare da an ganshi ba.Da shigar Yarima Lubainu cikin daji ya nausa gabas yana duban sawun Jaruma Suhailat.Ai kuwa bai dade da fara duba sawun Suhailat ba ya ganshi don haka sai ya cigaba da binsa da sauri har dayayi tafiya mai dan tsawo.Kwatsam sai ya hango Jaruma Suhailat daga nesa kadan ta ratayo wata matacciyar barewa a kafadarta ta tunkaro inda yake.Tun daga nesa suka kurawa juna idanu suna murmushi har ta iso daf dashi.Kawai sai ta dubeshi tace,zo mu cigaba da tafiya muna hirar mu don kada abokan tafiya su ga mun dade bamu koma ba suyi zargin wani abu.Ba tare da wata gardama ba Yarima Lubainu ya jera da ita suka cigaba da tafiya don komawa can masaukin nasu.Suna cikin tafiyar ne ta dubeshi tace,yakai Yarima Lubainu,kamar yadda na yimaka alkawari jiya nayi istahara kafin na kwanta barci kuma ubangijina ya nuna mini halin da matarka ke ciki tun kafin ma ta baro kasarku Zamrul.Shin kasan wani mayakinku mai suna BARDE RUHAISU?Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu ya dubi Jaruma Suhailat cikin tsananin mamaki yace,kwarai kuwa na sanshi,abokina ne na amana,kuma na daukeshi tamkar dan uwa na jini,domin a hannun mahaifina ya girma.Ko na takaice miki labarin ma mahaifina yana kaunarsa fiye da yadda yake kaunata ni da ya haifa a cikinsa.Koda jin haka sai Suhailat ta jinjina kai sannan tace,hakika Barde Ruhaisu dan halak ne kuma ya cancanci mahaifinka ya so shi fiye da kai,saboda mutum ne mai karfin amana kuma yana kaunarku kai da mahaifinka fiye da yadda yake son kansa.In badin Barde Ruhaisu bada tuni yanzu makiyinka kuma abokinka Yarima Mangul ya mallaki Yazarina.Nan take Suhailat ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakanin Yazarina da Barde Ruhaisu tun daga lokacin da suka baro Birnin Zamrul tare da dakaru dari kawo izuwa sa'adda Yarima Mangul ya kawo musu harin bazato suka fafata kazamin yaki dashi,inda a karshe suka ruga izuwa cikin daji suka hau kan wannan dogon tsauni mai mugun nisa,Yarima Mangul ya bisu har izuwa karshensa suka fado kasan tsaunin don su tsira daga sharrin Mangul.Koda Suhailat tazo nan a labarinta sai ta dubi Yarima Lubainu tace,wannan shine iyakar abinda ubangijina ya nuna mini a mafarkina don haka daga lokacin da Yazarina da Barde Ruhaisu suka fado kasan wannan tsauni bansan abinda ya samesu ba.Wata kila sun hallaka wata kila kuma suna nan a raye,amma dai kayi hakuri izuwa wani daren zan sake yin istahara domin naga halin da suke ciki.Koda Suhailat tazo nan a zancenta sai Hawaye ya zubowa Yarima Lubainu yace,yanzu ni dame zan sakawa barde Ruhaisu bisa wannan gagarumin taimako dayayi mini?Ki dubi yadda ya sallama rayuwarsa don kare ta matata.Koda jin wannan tambaya sai Suhailat tayi murmushi tace,tabbas akwai abinda zaka iya saka masa dashi anan gaba,amma fa sai ka danne zuciyarka,domin wani abu ne mai daraja a wajenka zai bukaci ka sallama masa shi..Koda yake amma a wannan lokacin kaima ka sami wanda ya ninka wancan din daraja.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya dimauce ya kasa fahimtar abinda Suhailat take nufi,don haka sai ya dubeta cikin alamun matukar mamaki yace,wane abu ne haka mai daraja a wajena wanda Ruhaisu zai bukaceshi kuma nima zan sami wanda yafishi daraja?Sa'adda Suhailat taji wannan tambaya sai ta hade fuska tace kasan komai yana da lokacinsa to ka yi hakuri lokacinka na sanin wannan al'amari baiyi ba.Idan kuwa ka matsa har ka sani din to tabbas zakayi nadamar sanin!!!Tana gama fadin hakan ne suka jiyo sautin haduwar takubba daga bangaren wajen da suka yada zango.Cikin firgici suka dubi junansu sannan suka falfala da azababben gudu suka nufi wajen.Ai kuwa suna isowa inda suka yada sansani sai suka hango sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da dan wada Dazyan a tsakiyar wasu narka narkan SAMUDAWAN MARIDAI kimanin su saba'in suna yaki dasu.Kowanne maridi guda tsawonsa yakai kamu ashirin da biyar kuma fadin kirjinsa ya kai kamu ashirin.Suna rike da manyan sungumai guda bibbiyu.Sungumin dake hannunsu na dama da dutse akayi shi,don dunkulalle ne mai kauri da nauyi,duk abinda suka rotsawa shi sai ya dagargaje.Daya sungumin dake hannunsu na hagu da zallan kashin wata katuwar dabbar daji akayi shi mai KAIFI DA TSININ TSIYA!Komai kaurin bishiya idan suka caketa dashi sai ya hudata ya bullo ta karshenta.Su dai wadannan maridai sun kasance suna da tarin kwanji mai girman gaske gami da jijiyoyi tamkar jikin nasu ma na dutse ne bana tsoka ba.Ita kanta Jaruma Suhailta da ta jango wadannan samudawan maridai daga nesa saida ta firgita ta tabbatar da cewa karo dasu ba wasa bane,dole ne a sha BAKIN GUMURZU da wahalar gaske,don haka tun kafin ma su iso wajen su kawowa su Sarauniya Akisatul Sauwara dauki tuni maridan sun galabaitar dasu,sun kaisu kasa sun kasa koda mikewa tsaye saboda kowannensu ya sami rauni a jikinsa sama da guda uka sai zubar da jini suke,jiri na dibarsu. Koda ganin haka sai Suhailat ta dubi Yarima Lubainu ta gargadeshi da kada ya kuskura yace zai tayata yakar wadannan samudawan maridaiTana gama fadin hakan sai ta kara kardin gudun nata tana mai neman taimakon Allah a cikin zuciyarta.Ai kuwa sai karfin gudun nata ya zama tamkar na TAURARUWA MAI WUTSIYA!!!Nan da nan ta baiwa Yarima Lubainu tazara mai yawan gaske.Saura kiris samudawan maridansu hallakasu Sarauniya Akisatul Sauwara a lokacin da suka daga sungumayen hannayensu zasu mammaka musu sai kawai Suhailat ta daka tsalle sama tamkar an harbota daga cikin BAKA ta dira a tsakiyar samudawan maridan ta tarwatsasu da karfin naushin kafafunta biyu,sannan suka sake taso mata aka ruguntsume da sabon masifaffen yaki.. WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN YAKI TSAKANIN JARUMA SUHAILAT DA WADANNAN SAMUDAWAN MARIDAI? A WANE HALI YAZARINA DA BARDE RUHAISU SUKE? SHIN YARIMA MANGUK ZAI SAKE TARFA SU BARDE RUHAIUS HAR YA MALLAKI YAZARINA? SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIKA BURINSA NA KASHE MAHAIFINSA DON HAWA KARAGAR MULKIN BIRNINSU? WANE ABU NE MAI DARAJA WANDA BARDE RUHAISU ZAI NEMA NAN GABA A WAJEN YARIMA LUBAINU? YAUSHE NE YARIMA LUBAINU DA YAZARINA ZASU SAKE SADUWA KUMA YAUSHE NE ZA'A ISA KOGIN BAHAR IMFAL? Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI(ALLON-SI HIRI-6)don jin cigaban wannan kayataccen labari. Alhamdulillah!!!Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)daya bani ikon gama rubuta wannan littafi.Sai muyi jira littafi na shida(6).Allon-Sihiri 6 ya fito.Insha Allah yana nan tafe bada jimawa ba. Kafin yafito inaga zamufara muku # TASKAR_AJALI # TARWATSA_MAZA An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part A. An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __. Marubucin littafin :- Abdul aziz sani madakin gini typing by :- Al amin Ahmed Misau nickanme ; Guyson sunana kenan call:- 08064594218 For more doka ;- Itace ban yarje ba a yi edit na post dina ba tare da sani na ba ehem . Labari ya isowa guyson cewa. JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN KARAGAR MULKIN, ta tako kafafunta tazo har daf da alkasim ta tsugunna fuskarrta na kallon tasa yadda har suna iya jin numfashin juna sannan ta dubeshi fuskarta a daure tace wnene kai kuma me kake takama dashi har da zakayi kokarin zaluntata ka rabani da abinda na farauto a daji alhalin hannuna ya riga naka kaiwa kan dabbar? Sa adda yarima alkasim yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace bazan baki amsar wannan tambaya ba sai kin fara gabatar da kanki tukunna nasan ko ke wacece. Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta mike tsaye zumbur ta koma da sauri zuwa kan karagarta ta zauna zamanta keda wuya sai ta yi nuni da hannunta zuwa kan alkasim take wannan murtukekiyar macijiya data kanannadeshi ta sauka daga jikinsa amma sai wadansu sarkokin karfe suka fito daka cikin bango kimanin guda dubu suka kanannadeshi har kansa suka janyeshi zuwa jikin bangon suka shiga matseshi yarima alkasim bai san sa adda ya fara kurma ihu da kururuwa ba sakamakon tsananin zafi da zugin da yake ji koda ganin haka sai jarumar ta fara kyalkyala dariyar mugunta tana cikin yin dariyar ne kwatsam taji alkasim ya daina yin ihu da kururuwan kuma nan take sarkokin suka karkatse suka zube kasa gutsungutsun sai gani tayi Alkasim ya baro jikin bangon ya durfafota yana tafiya da karfinsa tamkar wani abu bai taba samunsa ba Manya gatan wasa kenan sarki Alkasim. Cikin tsananin kaduwa da mamaki jarumar ta mike tsaye tana kallonsa kawai alkasim ya iso har daf da ita yadda suna iya jin numfashin juna kamar yadda tayi masa dazu ya dubeta cikin murmushi yace duk abinda kike takama dashi nima ina da irinsa ko ma wanda ya fishi akan wane dalili zaki dauki girman kai a gareni alhalin nine yakamata na zamo mai girman kai a gareki tun da na kasance da ga sarkin dake mulkin wannan kasa da kike cikinta. Koda jin wannan batu sai jarumar tayi murmushi sannan tace dama saboda kai nazo wannan kasa abinda yasa banje fada kai tsaye ba shine ina son na gabatar da abinda nazo yi a sirrance ya kasance a tsakaninmu ne kawai mu biyu sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN MAFARAUTA NA BIRNIN TEHERAN tun ban fi shekara takwas ba a duniya mahaifina ya bani horon yaki wanda ina iya fuskantar zaratan mayaka guda dubu sannan ya bani horon gumurzu da manyan dabbobin daji baya ga hakan ya bani horon rayuwa a cikin daji gami da yin gudu na tsawon kwanaki tara ba tare da tsayawa ba sama da dakika arba in ba bugu da kari mahaifina ya tsumani a cikin tsumin tsafi irin wanda samun mai irinsa sai an tona lokacinda na samu shekaru goma sha takwas ina samun wannan horo ya zamana cewa na zama budurwa cikakkiya sai na kawai da dukkan yan fashin dake cikin dazuzzukan kasarmu ni kadai hakanne yasa yan fashin suka fusata suka nemo taimakon yan uwansu dake cikin kasashen ketare amma duk da hakan sai na zame musu alakakai na zamo tamkar shaidaniya a cikin bil adama akwai wata ranar da wadannnan yan fashi suka ritsani a daji adadinsu yakai miliyan shida amma ni kadai na kashe mutum miliyan uku da rabi daga cikinsu sauran suka tsere daga wannan rana ne na dinga jin kamar babu wani mayaki ko sadaukin da yafi ni jarumtaka amma sai mahaifina ya dubeni yace yake yata kada ki kuskura ki dorawa kanki girman kai bisa wannan jarumtaka da kika ga kin samu a halin yanzu ina mai tabbatar miki da cewa akwai wani dan sarki wanda karfinsa da jarumtakarsa har da karfin sihirinsa zasu iya zuwa dai dai da naki koma yafiki koda jin wannan batu saina kamu da tsananin mamaki na tuna irin karfiin da nake dashi amma ace wai har akwai wanda ya kaini koma ya fini bisa wannan daliline na yanke hukuncin nazo na hadu dakai domin muyi gasa guda mu banbance tsakanin aya da tsakuwa gasa ta farko itace gudun tseren da zamuyi tsawon kwana tara ba tare da tsayawa ba ta sama da dakika arba in ba gasa ta biyu itace akwai wani babban gari na arnan daji dake can kudancinmu na taheran ina son mu je mu sato gunkin da suke bautawa domin mu tsokano yaki dasu wadannan arnan daji suna da mugun yawanda ba asan iyakar adadinsuba ni dakai dai zamu yakesu domin mu tantance iyakar jarumtakarmu gasa ta uku wacce itace ta karshe zamu shiga daji kowannanmu yayi farautar dabbar da babu kamarta ya kasheta yazo da gawarta idan har dabbar da na kashe tafi taka hadari ka tabbata cewa nafika karfi da jarumtaka kenan Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai page nake typing nan take zamu rabu na koma kasata cikin farin cikin cewa nafi ka komai yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a zancenta sai hankalin alkasim ya dugunzuma ainun saboda zuciyarsa ta karaya akan wannan abu guda uku amma daya tuna cewa shifa mutum ne mai sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa sai yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin ransa don haka bai san sa adda ya dubi jaruma luslaiya ba yace na yarda da duk wannan sharadi na gasar da kika shirya mana kuma saina tabbatar miki da cewa nafiki karfi da jarum taka wow nima Guyson saina tabbatar muku da cewa jarumi ne ni. Yanzu idan na lashe wannan gasa menene sakamakona? Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama luslaiya tace inda dai ace kai ba dan sarki bane toda saina baka dukiyar da har ka mutu kai da danginka ba zaka yi talauci ba amma ai mahaifinka yafi mahaifina dukiya yanzu ban san dame zan iya biyanka ba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace ai kuwa kece kike da abin da zaki iya biyana yake jarumar jarumai kuma tauraruwar taurari ba komai nake so a wajanki ba face soyayyarki da aurenki idan har na lashe wannan gasa akanki to na siyi soyayyata kenan kuma babu abinda zai hana aurenmu koda jin wannan batu sai jaruma luslaiya taji zuciyarta tayi baki kirin kuma nan take taji ta tsani yarima alkasim fiye da komai a duniya saboda tunanin cewa ya na so yayi mata dole ta soshi kuma ta aureshi cikin tsananin fushi ta dubeshi tace nayi maka alkawari zaka sha bakar wahala da baka taba sha ba a rayuwarka a cikin wannan gasa wacce zata kaika ga rasa lafiyarka ko rayuwarka gaba daya kuma ina tabbatar maka da cewa baka da jarumtakar da zata iya burgeni har zuciyata ta kamu da sonka don haka duk yadda zanyi naga ka fadi wannan gasa sai nayi ya kasance ne ne na lashe gasar ka sani cewa babu hada kai a cikin wannan gasa ni dakai sai dai kowa tasa ta fishsheshi kuma kowannanmu zai iya shiryawa dan uwansa tarkon mugunta domin ya hallaka iana son mu zamo tamkar abokan gaba masu farautar rayukan juna lokacin da sarki alkasim yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa yarima kamsus sai yaga idanun yarima sun ciko da kwalla kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tari numfashinsa yaana mai cewa daka ta yakai abbana yanzu kana bani labarin wata jaruma a matsayin itace mahaifiyata to ita kuma junaina wadda na taso nake ganinta a matsayin uwata wacece ita?? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Alkasim yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can ya dago kai ya dubeshi cikin rawar murya yace yakai dana kayi hakuri zakaji amsawar wannan tambaya da kayi min a karshen wannan labari da nake baka kafin mu isa birnin masarul anjana Tabbas zaka tantance a tsakanin mahaifiyarka junaina da kuma mahaifiyarka jaruma luslaiya zaka san matsayin kowacce a wajenka koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da matsanancin kuka al amarin da ya dugunzuma hankalin yarima kamsus kenan ya shiga rarrashin sarki a lokacin da yaji ya kamu da tsananin tausayin mahaifin nasa sarki Alkasim da kyar ya shawo kansa ya daina kukan sannan yarima kamsus ya dubeshi cikin zakuwa yace na rokeka dakaci gaba da bani wannan labari domin naji yadda karshen gasarku da jaruma luslaiya zata kasance sannan kuna na gane banbancin dake tsakanin luslaiya da mahaifiyata junaina Al amin Ahmed Dan misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai nake magana tayaya zan karbi luslaiya a matsayin uwa ta alhalin ban san wata uwa ba face junaina gama fadin haka keda wuya sai hawaye ya kwararo bisa kumatun yarima kamsus take shima sarki alkasim yaji ya kamu da matukar tausayinsa don haka sai ya rungumeshi akan kirjinsa sannan yaci gaba da bashi labari yana mai cewa..... . LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA ta fadi cewar a cikin wannan gasa zamu zamo tamkar abokan gaba kuma zamu rinka shiryawa juna tarkon muguntar da zan iya hallaka sai hankalina ya tashi saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko shine na kamu da tsananin sonta dalilina biyu kuwa bazan iya shirya mata mugunta da zata hallaka ba nan take zuciyata ta gamsu cewar lallai zan sha bakar wahala a cikin wannan gasa musamman da na tuna cewa inda zamu je mu gabatar da wannan gasa acanne nahiyar su jaruma luslaiya don haka ban san sirrikan dazuzzukan dake can ba. Yayin da luslaiya taga na sunkuyar da kaina kasa ina tunani da nazari saita kyalkyale da dariyar mugunta sannan ta hade fuska tace yaro bai san wuta ba saiya taka ta yanzu saika tashi ka koma gida ka sanar da iyayenka duk abinda ya faru a tsakaninmu domin kayi musu sallama ka dawo mu tafi ka sani cewa tun daga nan gasar mu zata fara don haka kayi amfani da damarka ta kowa a gidansa sarkine duk yadda zakayi ka tabbatar kaga bayana kafin mu bar nahiyarku dajin wannan batu sai yarima Alkasim yayi murmushi ya mike tsaye ya juya mata baya har yayi taku uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira sunansa ya waigo ya dubeta cikin mamaki ita kuma sai tace da sassafe zaka fito gobe ka sameni anan wurin idan ka baata min lokacin zanyi tafiyata sai kayi da gaske zaka riskeni alkasim yayi murmushi yace babu matsala zanzo akan lokaci yana gama fadin hakan sai ya juya yayi tafiyarsa har yarima alkasim ya isa gida jikinsa a sanyaye yake kuma hankalinsa a tashe yake domin guiwarsa tayi sanyi ainun bisa wannan gagarumar gasa dake gabansa da isar yarima Alkasim a lokacin da magariba ta gabato sai ya nufi kai Tsaye bisa mamaki sai ya hango kofar dakinsa a bude al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan domin babu wanda yake da ikon shiga dakinsa ba tare da izininsa ba face mutum biyu daga sarki sai mahaifiyarsa a fusace yarima Alkasim ya kunna kai da sauri cikin turakar tasa da nufin yaci mutuncin wanda ya bude ya shiga koda yayi arba da wanda ke zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta buga da karfi ba wani bane ba face mahaifiyarsa tana zaune bisa shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye na diga daga idanunta cikin firgici ya karasa gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya rike hannayanta biyu yana dubanta cikin tsananin damuwa yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye daga cikin idanunki sa adda taji wannan tambaya sai tasa hannunta na dama ta share hawayan nata sannan ta janyo yarima izuwa jikinta ta rungumeshi akan kirjinta tace ya kai dana yau shekara talatin da kadan kenan ina tare dakai bamu taba rabuwa ba amma yau sarki ya tabbatar min da cewa a wannan karon zaka nisanta dani kuma zaka yi wata tafiya mai hadari wacce zama ka iya rasa rayuwarka koda jin haka sai yarima alkasim yayi murmushi cikin nutsuwa yace haba yake ummina akan wane dalili zaki damu kanki alhalin kin san duk ahalin gidan nan yana da sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa ke da bakinki kin sha bani labarin irin gwagwarmayar da sarki yayi a rayuwarsa tamkar ba zai tsira da rayuwarsa ba wai shin ma me yasa kika shigo cikin turakata kika zauna kina ta kuka? Shin yanzu kina nufin ki ce dake za ayi wannan muguwar tafiya ne? Nayi murna da ganinki a yanzu domin dama akwai wani abu daya shige min duhu ina son kiyi min cikakken bayani kada ki boye min komai taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro ya shigeta ta fara zargin anya kuwa sarki bai sanar dani sirrin da suka boye ba tsawon shekaru cikin karfin hali na budi baki nace yake umma ina sonki sanar dani matsayina kafin yarima alkasim ya karasa fadin abin dake bakinsa sai yaji motsi a bayansa don haka sai ya waigo da sauri sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a murtuke yana mai kada kansa wato yana yi masa nuni da kada ya fada mata abindake bakinsa.... ALLON-SIHIRI, Littafi na Shida (6) Part A Lokacin da aka ruguntsume da Azabebben yaki tsakanin suhailat da wadannan samudawan maridai su sarauniyya Akisatul sauwara suka fice daga tsakiyar da'irar da'akeyin gumurzun suna masuyin rarrafe tamkar kananun yara saboda tsananin razana dasukayi,. Nanfa jaruma suhailat tazamawa samudawan Alakakai yazamana cewa Anrasa Wanda zaisamu daman koda lakutan jikinta, haka itama takasa samun koda Kai guda daya kasa acikinsu, alokacin dasu sarauniya akisatul sauwara suka koma gefe duksu su ukun suka takura jinkinsu suka zama 'yan kallo, banda muzurai da rawar jiki babu abunda sukeyi, kamar Ace kyat!! Su fita da gudu. Saida akashafe kusan sa'a biyu Ana wannan mummunan dauki ba dadi ba tare da wani yasamu nasara ba Atsakanin jaruma suhailat da wadannan samudawan maridan. Al'amarin daya fusata samudawan maridan Kenan, bashiri sukaja da baya sunamai kurawa suhailat idanu suna huci da numfarfashi kamar do Dodonni. Hakika wadannan halittar sunyi matukar mamakin yadda wannan karamar halitta ta gagaresu Alhali Tana yakarsune da tsagoron KARFIN DAMTSENTA da iya takinta batare da nau'in wani sihiri tsafi ba. Itakuwa jaruma suhailat Ashe wannan ja da baya da samudawan maridan sukayi, dama suka bata takaranta Addu'ointa na neman tsari da sa'a. Duk da cewa jaruma sulailat batasamu wata nasara akansuba, Amma Sam zuciyarta bata karaya ba, saboda ta dogara ga Allah, kuma tasan cewa babu abunda zai gagareshi, nanfa suhailat tafarayiwa Allah kirari acikin zuciyarta Tana kiran sunsyensa tsarkaka guda Dari ba daya. Tana cikin wannan Addu'o inne taga samudawan sun hada kawunansu waje guda suna kus kus! Kawai Sai suka rugo da guda gaba dayansu izuwakan suhailat acikin sabon SALON YAKI na musamman. Komai jarumtar mutum da iya yakinsa idan yaga salon yakin da samudawan sukazo dashi dole ya firgita, domin arike sukeda hannunsu sunayin KAWANYA, sauran hannayennasu na rike

Chapter 12 of 19