Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.A Sannan ne Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara suka taho garesu da sauri domin suji abinda bakon jarumin zaice.Dazyan yayi gyaran murya sannan yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa shugabana yace inda zaka yi imani da UBANGIJIN MUSULUNCI ka karbi addininmu zaka iya samu lafiyarka a rana guda a cikin dakika guda daya ma jal ka yankewa kanwa duk wahalar dake gabanka.To amma ya fuskanci cewa zuciyarka da ta wadannan Abokan Gaba tana da rauni akan yin imani da ubangijin musulunci saboda kun yarda da Addinin iyayenku da kakanninku,kuma kuna gani kamar addinin naku shine addinin gaskiya,saboda kuga zahiri kuma ku gamsu cewar addinin musulunci shine na gaskiya mafin inganci da daraja akan naku,shugabana ya amince zai ci gaba dayin wannan tafiya tare daku amma duk inda akaje zai barku ku jarraba kafin sihirinku da na damtsenku wajen ganin cewa kun kawar da kowacce irin masifa da aka riska sai bayan kun kasa sannan shi ya kawar da masifar da taimakon ubangijin musulunci,amma fa sai idan kun dauki alkawarin cewar bayan anzo karshen tafiyar zakuyi imani da addinin musulunci,idan kuma baku yarda ba da wannan sharadi ba,to zai cigaba da binku kawai a cikin wannan tafiya ya zaman dan kallo ba tare daya taimaka muku da komai ba.Koda Dazyan yazo nan a jawabinsa sai hankali Sarki Darmanu dana Sarauniya Akisatul Sauwara ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe suka rasa abinda yake musu dadi a duniya,shi kuwa Yarima Lubainu sai farin ciki ya lullubeshi ya dubi bakon jarumin cikin murmushi yace tabbas ni na yarda da wannan sharadi naka.Koda jin hakan sai Bakon Jarumin yayi maganar kurame ga Dazyan shi kuma Dazyan sai ya dubi Yarima Lubainu yace mai gidana yana murna dajin bayaninka.Dazyan ya juya ya dubi Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara yace,maigidana yace ki kuma fa menene ra'ayinku? Cikin rawar murya da tuntuben harshe Sarauniya Akisatul Sauwara tace babu matsala muma mun amince da sharadin maigidanka to amma yanzu yaza ayi akan batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda mukazo nema a cikin gidansa? pls Like nd comments 15 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na uku (3) Part C Batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda mukazo nema yanzu a cikin gidansa.Koda jin wannan tambaya sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan ya sake yi masa zancen kurame da hannu.Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace yanzu zamu bazama neman wannan ALLON SIHIRI a cikin wannan gida,amma ku ukun ne zaku fara neman ALLON SIHIRIN da karfinku sihirinku,idan kuka kasa sai mu roki ubangijinmu ya nuna mana inda yake mu daukeshi da izininsa mu baku.Koda gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya dubi su Sarauniya Akisatul Sauwara yace to kunji yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi murmushi kuma suka budi baki cikin hadin murya suka ce muma mun amince da hakan.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da Yarima Lubainu suka sake kunna kai izuwa cikin gidan Boka Darbusa kowannensu na karanta dalasiman tsafinsa a cikin ransa.Shi kuwa Bakon Jarumi da Bawansa Dazyan sai suka bisu a baya kawai suna kallonsu kuma suna neman tsarin Allah daga dukkan mugun abun dake cikin gidan.Abu dai kamar wasa saida su sarauniya Akisatul Sauwara suka shiga duk wani sako,lungu da dukkan dakunan dake gidan kuma suka caje komai da ko ina a cikin gidan amma har suka gaji likis ko alamar ALLON SIHIRI basu gani ba.Daga karshe ne suka ga wani daki mai katuwar bakar kofar karfe a kulle wanda ya rage basu shiga ba.Ita kanta kofar wannan daki ta isa abar tsoro domin anyi tane da mulmulallen karfe mai kaurin gaske,sannan akwai hoton KWARANGWAL din kan BIL'ADAMA da kafafuwansa a jikinta alamar cewa wannan daki,daki ne me mugun hadari wanda mutum zai iya rasa rayuwarsa a ciki.Koda sukayi arba da kofar wannan daki sai sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi cirko cirko suna kallon kofar.Kawai sai Sarki Darmanu ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace ai sai fara jarraba taki sa'ar mu gani.Ba tare da wata gardama ba kuwa sarauniya Akisatul Sauwara ta kama kofar taja da nufin ta budeta amma sai ta kasa kawai sai ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa a kofar.Maimakon kofar ta bude sai wata irin iska mai karfin gaske ta fito daga cikin kofar ta doki kirjin Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sama da ita da karfi,bayanta ya gwaru da jikin bango ta fado kasa a galabaice.Koda ganin abinda ya faru sai hankalin Sarki Darmanu ya tashi jikinsa ya kama tsuma ya dubi Yarima Lubainu yace saura kai.Yarima Lubainu ya numfasa yace shin ka mantane kai abinda Sarauniya Akisatul Sauwara ta kasa yi nima bazan iya ba.Koda jin haka sai Sarki Darmanu ua ciza lebe sannan ya dunkule hannayensa biyu yayi nuni dasu izuwa ga kofar yana mai rintse idanu.Faruwar hakan keda wuya sai iska mai karfi ta fito daga cikin hannayensa ta rinka duka kofar dakin tana jijjigata kamar zata burma ciki amma sai hakan ya gagara.Maimakon ma kofar ta bude sai ta maido masa da iskar hannun nasa ta sureshi sama ta rinka katantanwa dashi a sama ya rinka ihu yana neman hallaka.Koda ganin haka sai Bakon Jarumin ya daka tsalle sama ya riko rigar Sarki Darmanu.Take iskar tsafin ta dauke dif sarki Darmanu ya fado kasa tim.Shi kuwa Bakon Jarumin sai ya diga a kasa bisa kafafunsa cikin koshin lafiya.Sarki Darmanu kuwa saida hancinsa da bakinsa suka kama yoyon jini.Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa zance da hannu sannan Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu yace shugabana yace zai bude muku wannan kofa da izinin ubangijinsa wato ubangijin musulunci.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu da Sarki Darmanu tayi musu kallon ko menene ra'ayinsu? Duk su biyun sai suka sunkui da kawunansu kas.Faruwar hakan keda wuya sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Bakon Jarumi tace mun baka dama.Dajin haka sai Bakon Jarumin ya tunkari kofar dakin kai tsaye ba tare da shakkar komai ba,da isarsa bakin kofar sai ya dungureta da dan yatsansa guda daya.Take kofar ta bude a hankali tamkar yaro ne karami wanda baifi shekara hudu ba ya turata ta bude din.Saida kofar ta gama wangamewa gaba dayanta sannan su Yarima Lubainu suka matso kusa da Bakon Jarumin suna leka cikin dakin jikinsu na tsuma saboda tsoro da fargabar ko wata masiface zata taso,amma sai suka ji shiri kamar maye ya ci shirwa.Koda ganin cewa su Yarima Lubainu sun kasa shiga dakin sai Bakon Jarumin ya juyo ya dubi Dazyan yayi masa inkiya.Take Dazyan ya rugo ya bishi a baya,suka kunna kai izuwa cikin dakin su biyu,ba tare da fargabar komai ba.Duk da haka sai su Yarima Lubainu suka kasa shiga dakinDaki ne babba mai girman gaske tamkar wata karamar unguwa.Babu komai a cikin dakin face durowa da tebura a jere a layi,layi kuma sahu sahu reras,iyakar ganin idanun mutum babu iyaka.Akan teburan da durowoyin kwalabe ne birjik.Cike da RUWAN SIHIRI kala kala.A cikin durowoyin kuwa kayan TSATSUBA ne iri iri kamar kahonni,Layu,Guraye,Kawunan Tsuntsaye da sauran sassan jikin dabbobi dana dan Adam dana Aljanu.Shi kansa bakon jarumin daya shigo cikin wannan daki saida ya cika da mamakin irin abubuwan dake cikinsa da yadda akayi aka iya tarasa.Koda Ya ga sun dan jima a ciki amma su Sarauniya Akisatul Sauwara sun kasa biyosu izuwa ciki sai ya dubi Dazyan yayi masa maganar kurame.Take Dazyan ya juya da baya ya ruga waje yace da su Yarima Lubainu maigidana yace ku cire tsoron komai a cikin ranku ku shiga ciki saboda kune kuka san abinda kukazo nema,kuma akwai rubuce rubucen sihiri da yawa a cikin dakin a jikin abubuwa da yawa wadanda ba zamu iya karantasu ba mu fahimta. Koda jin haka sai Sarki Darmanu yayi wuf ya wuce gaba ya shige cikin dakin.Koda Ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu ma suka bi bayansa da sauri.Shima dan wada Dazyan sai ya bisu da sauri sukaje suka riski bakon jarumin a tsaye a cikin tsakiyar daki.Da isarsu Dazyan ya dubesu yace maigidana yace ya baku damar ku dudduba ko za kuga abinda kukazo nema.Koda jin haka sai duk su ukun suka rarrabu suka rinka bude durowoyi suna duba kan tebura.Saida suka shafe sama da sa'a daya da rabi suna neman ALLON SIHIRIN Boka Darbusa amma basu ganshi ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsu kenan suka rasa abinda yake musu dadi a duniya.Koda Bakon Jarumi yaga yadda hankalinsu ya tashi sai mamaki ya turnukeshi yace a ransa"Hakika iska na yawo da mai kayam kara! Yanzu fa saboda kwadayin abin duniya ne yasa wadannan mutane idanunsu suka rufe akan neman wannan ALLON SIHIRI?A cikinsu ma babu wanda yafi cancanta a taimakawa sama da Yarima Lubainu,domin shine wanda aka zalunta kuma ake neman salwantar da rayuwarsa".Koda gama Aiyana hakan a cikin ransa sai bakon Jarumi ya tafa hannayensa sau uku.Koda jin sautin tafin sai Yarima Lubainu,Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka tsaya cak ga barin binciken da sukeyi suka dawo inda yake tsaye.Da zuwansa sai dan wada Dazyan ya dubesu yace,maigidana yace tunda dai kun kasa gano inda wannan ALLON SIHIRIN yake to shi zai bincikoshi da yardar ubangijinsa.Cikin alamun karayar zuciya Akisatul Sauwara tace shike nan mun amince ya dauko ALLON SIHIRI.Koda jin haka sai Bakon Jarumin ya nufi inda jerin durowoyin suke.Har yabi layi na farko domin ya fara bincikawa sai ya tsaya cak,ya kirga layi na tara ya shiga yana kirgasu saida yazo kan durowa ta tara sannan ya tsaya cak ya dubeta da kyau.Babu kofa a jikin durowar kuma a rife take ruf.Babu alamar akwai wani abu a jikinta inda za'a iya budewa har aga abinda ke cikinta.Kawai sai ya daga hannunsa ya doki tsakiyar durowar take ta wargaje,ai kuwa sai ga ALLON SIHIRI kaso na uku a cikinta.Koda Yarima Lubainu,Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara sukayi arba da wannan ALLON SIHIRI sai suka cika da tsananin mamaki.Kawai sai Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara suka yunkura cikin bakin zafina nama duk su biyun a lokaci guda suka kaiwa ALLON SIHIRIN cafka,kowannansu na kokarin yariga dayan dauka,amma sai bakon jarumin yayi caraf ya rigasu dauka ya dubesu cikin murmushi yace,ai dama nasan cewa sai hakan ta faru a tsakaninku.Da zancen kurame yayi wannan bayani kuma Dazyan ne yayi musu jawabin.Bakon jarumin ya cigaba da cewa Kunga wannan ALLON SIHIRI dakuke gani duk wanda ya hada gudu uku a cikinsu bai isa ya iya rikeshi ba a hannunsa daidai da tsawon dakika goma ba,amma idan kuma shakkar hakan ku kawo ragowar bari biyun dake hannunku kuga zahiri.Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka kama muzurai suna duru duru suka kasa miko Allunan Sihirin nasu.Koda ganin haka sai Bakon Jarumi yayi murmushi kawai sai ya ajiye ALLON SIHIRIN Boka Darbusa a tsakiyar dakin ya koma gefe daya zura musu idanu.Nanfa Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka kama Kallon juna kuma suna kallon wannan ALLON SIHIRI.Nan take kowannensu ya zaro nasa Allon Sihirin kuma lokaci guda sai kowannensu ya daka tsalla ya kaiwa Allon Sihirin Boka Darbusa cafka.Ai kuwa sai hannayensu suka cafki Allon Sihiri a lokaci guda.Nan fa suka mike tsaye a tare suka kama naushin juna kowannensu na kokarin ya kwace Allunan biyu ya hade da nasa.Gashi dai kowannensu yana dakuwa domin naushin junansu sukeyi a fuska da ciki amma saboda naci sunki yarda su saki ALLON SIHIRIN.Shi kuwa Yarima Lubainu dama ya koma gefe daya ya zuba musu idanu kawai yana jiran yaga yadda karshen al'amarin zai kasance.Bakon Jarumin da dan wada Dazyan kuwa sai suka kara matsawa can gefe daya suka zauna akan wata doguwar kujera suna morewa idanunsu da kallon fadan da akeyi.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu na cikin kwarmazuwa sai kawai suka ga wata irin GUGUWA ta shigo cikin daki.Nan take ta suri komai na cikin dakin har da Sarki Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu tayi sama dasu ta rinka gwara kansu a jikin bango.Amma bakon Jarumi da dan wada Dazyan kuwa ko kusa dasu wannan guguwa batazo ba kuma suma suka ki suyi wani motsi suka cigaba da zuba idanu kawai.Cikin yan dakiku kadan su Yarima Lubainu suka jigata suka fita daga hayyacinsu.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu basu san Sa'adda suka saki duka Allunan Sihirin uku ba suka fado kasa.Faruwar hakan keda wuya sai Allunan Sihirin suka hade waje guda suka manne da juna tamkar ba'a taba rabasu ba suka zama babban Allo guda daya.Faruwar hakan keda wuya sai wannan guguwa ta rikide ta zama wadansu irin SAMUDAWAN BAKAKEN ALJANU dauke da muggan MAKAMAN YAKI.Nan fa samudawan bakaken aljanun suka ruguntsume da masifaffen azababben yaki a tsakaninsu,ya zamana cewa kowannensu na kokarin ya dauki ALLON SIHIRI ya gudu dashi amma duk wanda hannunsa yaki kan ALLON SIHIRI sai kaga an dankara masa SARA ko SUKA ko kaga an mangareshi ya fadi can gefe daya sumamme,ko kallonsa babu mai yi saidai ma acigaba da tattakeshi a kokarin gwagwarmayar daukar ALLON SIHIRIN.Tunda aka watsar dasu Sarauniya Akisatul Sauwara gefe daya a galabaice suka kasa mikewa tsaye suka cigaba da zama dirshen a kasa suna kallon wadannan Aljanu kawai suna ganin masifaffan yakin da ake yi tsakanin wadannan samudawan bakaken aljanun.Su kansu sun san cewa basu isa su iya tarar wadannan aljanu da yaki ba bare su iya karbar wan Nan ALLON SIHIRI daga hannunsu.Saida aka shafe sama da sa'a biyu da rabi ana yin wannnan azababben yaki ya zamana cewa da yawa daga cikin aljanun sun zama nakasassu wasu ba hannaye,wasu ba kafafu,wasu ma an datse rabin jikinsu,amma saboda taurin rai irin na aljanu basu fasa cigaba da kokarin daukar ALLON SIHIRIN BA.Koda bakon jarumi yaga ana ta bata lokaci amma an rasa wanda zamo GWARZON JARUMIN da zai iya daukar ALLON SIHIRIN sai kawai ya mike tsaye zumbur daga inda yake tsaye yana mai kwalla KABBARA ya falfalo da gudu izuwa inda akeyin wannan gumurzun yako.Da karfin tsiya ya ratsa ta tsakiyar samudawan bakaken aljanun yana bankesu suna zubewa kasa tamkar yana sassabe a gona.Koda yazo tsakiyar aljanun sai ya sake saka tsalle sama izuwa inda Aljanun sukayi tsiri sama wani kan wani domin sukai izuwa kan wani Gansamemen Aljani mafi tsawo,kauri da Kirar SADAUKANTAKA wanda shi ne ya sami nasarar cafe ALLON SIHIRIN ya bude fuka fukansa yai sama da niyyar ya gudu,amma sai wadansu daga cikin aljanun suka ruko kafafun nasa suna janyoshi kasa don ya fado,amma sai suka kasa saboda tsananin karfin damtsensa.A haka sadaukin Aljanin ya cigaba da fuffuka yana kai yakushi SARA DA SUKA da faratan kafafuwansa.Lokacin da bakon jarumin ya daka tsalle a sama tamkar an harboshi daha cikin baka sai da ya iso inda basamuden sadaukin aljanin yake,yana isowa daidai fuskarsa sai ya takarkare ya zabga masa wawan naushi a fuska.Saboda karfin naushin take karan hancin aljanin ya karye ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji.Nan take ya dimauce bai san sa'adda ya saki ALLON SIHIRIN ba.Caraf sai bakon jarumin ya cafe Allon Sihirin da hannu daya alhalin su kansu samudawan aljanun basa iya daga Allon Sihirin da hannu daya saboda tsananin nauyinsa.Koda Aljanun suka ga wannan bil'adama ya karbe ALLON SIHIRIN sai sukayi caa!a kansa suka yanyameshi suna masu kai masa sara da suka ta ko ina domin su hallakashi.Ai kuwa sai ya tarwatsa su a lokacin da ya sake kwalla Kabbara ya zare takobinsa cikin bakin zafin nama ya shiga kare kansa gami da maida martani.Wohoho!wanda Allah ya kare yafi gaban Magauta!Duk da tsananin yawa na wadannan samudawan bakaken aljanu da tsananin karfin damtsensu da mugayen makamansu sai gashi bakon jarumi ya zame musu ALAKAKAI,Sai gashi yayi musu mummunar barnar datafi wacce sukayiwa kansu,domin kuwa duk aljanin da yayiwa duka daya tofa idan ya baje a kasa wanwar da kyar ma yake iya numfashi wasu ma kamar sun zama gawa.Kai!da bala'i yakai bala'i sai gashi aljanun suna cika wandunansu da iska suna ficewa daga cikin dakin da gudu.Kafin a jima duk sun tarwatse sun fice daga cikin dakinsu duka sun bar bakon jarumin shi kadai a tsaye rike da ALLON SIHIRIN a lokacin da dakin yayi tsit tamkar babu wani mutum daya mai rai a cikinsa.Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul Sauwara kuwa saboda tsananin mamaki bisa ganin irin gagarumar jarumtakar da bakon jarumin yayi sai suka kura masa idanu kawao suka kasa budar baki suce wani abu,kai mikewa ma tsaye sai ya gagaresu.Koda ganin haka sai bakon jarumin ya dubi dan wada Dazyan yayi masa wata inkiya,shi kuma sai ya dubi Sarauniyar Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu da Yarima Lubainu yace,Maigidana yace bazai baiwa dayanku wannan Allon Sihiri ba face an zauna an tattauna kuma koda ma ya baiwa dayanku shi bazai sami damar karantashi ba bare har ya cika burinsa saboda masu farautar Allon Sihirin suna da yawa kuma sunfi ku karfin damtse dana Sihiri.Wadannan Bakaken Samudawan Aljanu da sukazo yanzu maigidana ya fatattakesu Yaran Boka Darbusa ne anan gaba kuma akwai sauran Manyan MATSAFAN DUNIYA da MANYAN JARUMAI dazasu fito farautar wannan ALLON SIHIRI.Kuma shi kanshi Boka Darbusa ba hakura zaiyi ba zai cigaba da kokarin karbarsa ne.Yanzu sai kowa yaje ya nemi dakin da zai kwanta a cikin wannna fada domin ya huta tunda dare yayi in yaso gobe da safe mu tattauna akan abinda muke ganin cewar shi ya kamata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai Bakon Jarumin ya juya domin ya fice daga cikin wannan daki,amma sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi wuf,ta mike tsaye kuma tayi gyaran murya tace,yakai wannan JARUMIN JARUMAI kayi sani cewa mu muna cikin tsoro da fargaba don haka bazamu iya sakin jikinmu ba har mu kwanta a cikin wannnan fada ta Boka Darbusa mu iya kwana a cikinta saboda a ko yaushe zai iya kawo mana ZIYARAR BAZATO ya cutar damu.Koda jin wannan jawabi sai Bakon Jarumin yaji kamar ya bushe da dariya amma sai ya dake ya dubi dan wada Dazyan yayi masa zancen kurame.Nan take Dazyan ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ashe bakuyi mamakin yadda shugaban ya iya yakar Boka Darbusa ba da dukkan Aljanunsa? Shin bakuyi mamakin yadda ya gano inda Allon Sihirinsa yake ba ya daukoshi kuma har ya hana wasu saceshi?To ku sani cewa zamanku anan cikin wannnan gida tare da shugabana shine kadai abinda zai baku kariya amma da zarar kun fita daga nan to fa komai zai iya faruwa a gareku,kuma abune mayuwaci dayanku ya iya tsira da rayuwarsa bare har ya sami damar cika burinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon Jarumin ya saba ALLON SIHIRI a hammatarsa ya juya ya fice daga cikin wannan daki Dazyan na biye dashi.Koda ganin haka ai Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki Darmanu suka bishi da sauri cikin alamun tsoro suna ta waige waige,gani suke kamar ma a koda yaushe Boka Darbusa ko wakilinsa zasu iya kawo musu hari a ko yaushe. kuyi hakuri dangane da jinkirin post yauALLON SIHIRI Littafi na Uku (3) Part D LOKACIN da Bakom Jarumi ya fita daga cikin wannan daki na kayan sihirin Bokab Darbusa sai ya tunkari inda turakarsa ta barci take,kai tsaye sai kace dama can yasan kowanne lungu da sako na gidan.Da isowarsa kofar turakar sai ya tsaya cak sannan ya juyo baya.Take yayi arba dasu sarauniya Akisatul Sauwara suna biye dashi.Cikin matukar mamaki ya dubesu sannan ya dubi Dazyan sukayi magana kamar yadda suka sabaDazyan ya dubi su Sarauniya Akisatul Sauwara yace shugabana yace na gaya muku ba zai taba yiyuwa ba ya kwana da dayanku a cikin daki guda ba,shi kadai zai kwanta a cikin wannan turaka tare da ALLON SIHIRI,don haka ya zama wajibi kowannenku ma yaje ya nemi inda zai sa hakarkarinsa.Kuma yace lallai ku kwantar da hankalinku tamkar tsumma a randa,yayi muku alkawarin cewar babu abinda zai taba lafiyar jikinku koda kuwa kwarzane guda da izinin ubangijinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon Jarumi ya shige cikin turakar ya janyo kofar ya rufeta ruf ya bar Dazyan tsaye sororo a kofar dakin tare dasu Sarauniya Akisatul Sauwara,suma sunyi cirko cirko suna mamakin bakon jarumin.Abinda ya fara fado musu arai shine."Menene dalilin dayasa bakon Jarumin bazai iya kwana tare dasu ba a cikin daki guda?Kuma menene dalilin dayasa duk a tsawon wannan lokaci bai yarda anga fuskarsa ba? To waishin ma shi Namije ne ko Mace?Lallai akwai bukatar su tantance hakan domin su san hanyar dazasu bi su rabashi da ALLON SIHIRI.Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi dan wada Dazyan tace ashe maigidan naka ma bai yarda da kai ba tunda ya kasa kwana tare dakai a cikin daki guda?Koda jin wannnan batu sai Dazyan ya takarkare ya bushe da dariya lokaci guda kuma yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni kaina bansan ko waye maigidana ba,ban san matsayinsa ba ko asalinsa,hasalima haduwata dashi bata wuce ta shekara uku ba,kuma a tsawon wannan lokaci ban taba ganin fuskarsa ba,kuma ban taba jin muryarsa ba bare kuda kuka hadu dashi a yau din nan.Shawarar da zan baku kawai itace,ku yarda da duk abinda kukaji ya fada,kuyi imani dashi,in ba haka ba kuwa karshenku shine NADAMA gami da yin MUMMUNAN KARSHE!Nidai yanzu zanje na nemi inda zan kwanta saboda na gaji likis kuma nima barci nakeji.Amma maigidana yace na shaidawa miki ke Sarauniya Akisatul Sauwara cewa lallai kema ki ware dakinki ke kadai domin a ka'idar addininmu haramun ne kiyi cudanya da mutanen da basu kasance muharramanki ba.Koda gama fadin haka sai dan wada Dazyan ya hango wani karamin daki dake can gefe daya wanda kofarsa ke bude wanwar,kawai sai ya tafi izuwa cikin dakin ya kunna kai ciki.Koda ganin haka sai Sarki Darmanu ya bishi da sauri.Ita kuwa Sarauniya Akisatul Sauwara sai ta tsaya ta kama duru duru ta rasa dakin dazata shiga.Daga can kuma sai ta nufi wani babban daki wanda kofarsa ke rufe.Da isarta sai tasa hannunta ta murda kofar,bisa mamaki sai taga kofar ta bude da kanta.Sarauniya Akisatul Sauwara ta kunna kai izuwa cikin daki.Tana shiga sai kanta ya daure tamau ta kamu da tsananin mamaki,ba don komai ba sai saboda ganin irin kayan kawar dake cikin dakin.A tsakiyar dakin an ajiye wani lumtsumen gado mai girman gaske wanda aka cikashi da kayan taushi na alfarma.Sannan kuma akwai kofar kewaye a cikin dakin.Sarauniya Akisatul Sauwara ta leka cikin kewayen shima taga an kawatashi da bahon wanka na zinare.Kawai sai ta koma falon tayi tsalle ta fada kan wannan luntsumemen gado cikin jin dadin huce gajiya.Amma kuma har a sannan raunikan jikinta basu daina yi mata dan zogi da radadi ba.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara ta fada kogin tunani. ¤P¤H¤Y¤S¤I¤C¤I¤S¤T¤ AL'AMARIN Yarima Lubainu kuwa,bayan yaga kowa ya shige cikin daki an tafi an barshi shi kadai a tsaye sai ya kama yawo a cikin gidan yana neman dakin dazai shiga ya kwanta shi kadai.Ba don komai yake son ya sami inda zai kwanta ba shi kadai sai saboda ya sami damar dazai zauna yayi tunani da nazari ya yankewa kansa shawarar da zata fissheshi.Da yake wannan fada ta Boka Darbusa tana da tsananin girma tamkar gari guda,kuma gashi anyi gine gine da yawa a cikinta na kawa,sai Yarima Lubainu ya rude ya rasa ma bangaren dazai shiga domin da yayi yunkurin shiga wani dakin saiya hango wani wurin wanda ya fishi kyau da kawa.Yana cikin wannan kai kawo ne ya shigo wani bangare dabam na musamman wanda aka killaceshi a wuri mai ban al'ajabi.Shi dai wannan wuri ya kasance tamkar lambu kuma an kewayeshi da katangar zinare,sannan an zuba shuke shuke na 'ya'yan itatuwa na marmari kala kala ga kuma tsuntsaye masu kyau ababan sha'awa kuma kofar wannna lamby a bude take.Har Yarima Lubainu ya gifta kofar zai wuce gaba sai ya jiyo shesshekar kuka cikin muryar MACE!Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan,domin a zatonsa bandashi dasu bakon jarumi babu sauran wani mahaluki a cikin wannan gida.Yarima Lubainu ya dawo da baya ya tura babbar kofar kambun ya kunna kai ciki.Yana shia sai ya kame,idanunsa suka zazzaro sakamakon abinda yayi arba dashi.Ba komai ne abinda yayi arba dashi din ba face wata zabgegiyar kyakkyawar Budurwar ALJANA a daddaure cikin wata murtukekiyar sarkar tsafi waccce ta kanannade hannayenta,kafafuwanta da sauran sassan jikinta,kuma sarkar an zagayata ne a jikin wata dirkar tsafi mai tsananin kaurin gaske wacce fiye da rabinta ya nutse a cikin karkashin kasa.Abin daya daurewa Yarima Lubainu kai dangane da wannan Aljana shine ko a bakin masana labarai bai taba jin cewar akwai halitta mai siffarta ba.Rabin jikinta na bil'adama ne,daga kasan cibiyarta zuwa kanta.Daga gwiwar kafafunta zuwa tafin kafafunta kuwa na Aljanu ne.Kash!in badon wannan ratsin siffa ta Aljana ba dake jikinta da Yarima Lubainu zai iya cewa duk duniya babu wata 'YA MACCE mai kyan wannan budurwa ba.Koda Yarima Lubainu ya hada idanu da wannan budurwa yaga idanunta sunyi sharkaf da hawayemkuma gata a daure cikin sarka,sai nan take yaji ya kamu da tsananin tausayinta.Amma da ya tuna cewa nan fa gidan Boka Darbusa ne babu mamaki ma wani tuggun ne aka shirya musu aka ajiye wannan Aljana domin su fada tarkon wahala,sai kawai ya juya da nufin ya fice daga cikin lambun,kawai sai yaji aljanar ta budi baki cikin murya mai zaki da bai taba jin irinta ba kuma mai tsananin taushin gaske tace,haba yakai Yarima Lubainu,ya ya kai daka kasance mai tausayi da jin kai zaka tafi ka barni a cikin wannan hali?Ka sani cewa shekara uku kenan wannan azzalumin Boka Darbusa na tsare dani anan,ina jiran ranar da zakuzo ku koreshi daga cikin wannan fada ku ceceni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya sake turnuke Yarima Lubainu ya dubi Aljanar cikin alamun rashin yarda yace,wace ce ke kuma ya akayi kika sanni har kika san cewa zamu zo wannan fada mu kori Boka Darbusa?Sa'adda aljanar taji wadannan tambayoyi guda biyu ko uku sai hawaye ya zubo mata,tace ni sunana BADI'ATUL SARIRA,Kuma nice 'ya guda daya jal a wajen mahaifina Sarkin Bokayen Aljanu na duniya kaf,wato ZARHASU IBINI SAMBILA.A cikin wannan duniya kaf in banda Boka Darbusa babu wani mahaluki daya kai mahaifina karfin sihirin tsafi da kuma tarin sirrikansa.Loka cin da mahaifina da Boka Darbusa suka gano cewa karfinsu yazo daya a sirrin tsafi sai suka zamo manyan ABOKAN GABA ya zamana cewa kowannensu na kokarin ya hallaka dayan ya rabashi da dukkan sirrikan tsafinsa.Asalin wannan ALLON SIHIRI da kuka daukoshi a dakin tsafin Boka Darbusa a hannun mahaifina yake,daga baya ne bayan Boka Darbusa ya samu nasarar kashe shi ya daukeshi.Ba komai ne yasa Boka Darbusa yaki kasheni ba ya daureni anan face cewa koya hada ragowar bari biyun na ALLON SIHIRI dana Mahaifina bazai iya cika burinsa ba face nidin nan na karanta masa wadansu dalasiman tsafi dake jikinsa na fassara masa su yadda zai fahimta,saboda yaren a akayi rubutun dashi a jikin Allon Sihirin mahaifina ni kadai ce na iya shi a duk fadin duniya,saboda mahaifina ne ya kirkireshi kuma tun ina yarinya karama ya koya minshi.Ina mai rokonka daka taimakeni ka kwanceni daga cikin wannan sarka yanzu in dai kayi min haka ni kuma nayi maka alkawarin cewa zan iya raba bakon jarumi da wannan ALLON SIHIRI,a cikin dakika daya jal,sannan na daukeka na kaika KOGIN BAHAR IMFAL a cikin abinda baikai rabin sa'a ba mu shiga cikin karkashin kogin na tsinko maka dan itaciyar dazaka sha ka warke daga cutar da YARIMA MANGUL ya sanya maka ka dawo cikakken da namiji ka koma ga matarka,babbar masoyiyarka YAZARINA ku fara sabuwar rayuwar aure cikin farin ciki.Ladan wannan aiki nawa kawai shine ka bar min wannan ALLON SIHIRI.Koda Aljanar tazo nan a jawabinta sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun ya rasa irin amsar da zai bata.Abinda ya fado masa a rai shine,shin zai iya yarda da wannan Aljanr kuwa? To ai idan ma ya yarda da ita kamar yaci amanar su Sarauniya Akisatul Sauwara ne! WACE IRIN SHAWARA YARIMA LUBAINU ZAI YANKE AKAN WANNAN DAMA DA YA SAMU? MAI ZAI FARU TSAKANIN SU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DA BAKON JARUMI IDAN GARI YA WAYE? WANE HALI BOKA DARBUSA YAKE CIKI BAYAN YA FALFALA DA GUDU IZUWA CIKIN DAJI BAYAN SUN FAFATA AZABABBEN YAKI SHI DA BAKON JARUMI DON YA TSIRA DA RAYUWARSA? WANENE BAKON JARUMIN DAYA BAYYANA? YAUSHE YARIMA YAKE CIKA BURINSA NA SAMUN LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI? WAISHIN INA LABARIN YARIMA MANGUL? WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI. Mu hadu a littafi na hudu(ALLON SIHIRI-4)don jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari. An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also

Chapter 7 of 19