Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ALLON SIHIRI Littafi na uku (3) Part AAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ LOKACIN da wadannan ALJANU na HASKE keta saran jikin su YARIMA LUBAINU,JINI na tsartuwa da feshi,shi kuma BOKA DARBUSA nata fama rusa dariyar mugunta da farin ciki,sai gaba dayansu su ukun suka zube kasa saboda jira sakamakon jinin dake zuba a jikinsu.Har mugayen fadawan na Boka Darbusa sun yunkura zasu karasa kashesu suyi musu KISAN GILLAH sai ga wani babban HADIMI na boka Darbusa ya shigo cikin fadar a firgice kuma a guje har yana tuntube,kuma yana mai kwallawa boka Darbusa kira.Al'amarin daya janyo hanakakin Boka Darbusa kenan da mugayen fadawan nasa suka juya izuwa kan hadimin suka kura masa idanu.Da isowar Hadimin sai ya zube kasa a gaban boka Darbusa yana haki kamar ransa zai fita,sai da numfashinsa ya dan dawo daidai sannnan ya iya budar baki yace,ya shugabana ga wani takadirin MAHAYI can ya durfafo wannan gida naka bisa wani BAKIN DOKI kuma sanye da FARAREN TUFAFI,ya rufe jikinsa da fuskarsa gaba daya,kuma yana rataye da wata zabgegiyar TAKOBI a bayansa.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Boka Darbusa,saboda a iya zamansa a cikin wannan DAJI babu wani mahaluki walau MUTUM ko ALJAN daya taba durfafo hanyar wannan gida nasa da tsawon kwanaki uku kafin isowarsa ba tare da ya sani ba,koma yasan ko wane ne,da kuma dalilin zuwansa,sai a wannan karon.Cikin alamun tsananin fushi da kaduwa boka Darbusa ya dubi wadannan fadawan nasa wato Aljanu na haske yace ku biyo ni a baya muje mu hallaka wannan shaidanin bil'adama daya tunkaromu,domin koma wane shi nasan cewa MAKIYINmu ne.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa ya zare takobinsa take wadansu bakaken DAWAKAN TSAFI na haske suka baiyana a gabansa.Kawai sai shida mugayen fadawan nasa suka haye dawakan.Cikin gaggawa wannan babban hadimin ya dubi Boka Darbusa yace,ya shugabana yanzu ya zamuyi da wadannan ABOKAN GABA namu su uku?Koda jin wannan tambaya sai Boka Darbusa ya dubi su Jarumi Lubainu wadanda ke kwance cikin jini,kuma rai a hannun Allah,ya bushe da dariyar mugunta yace,ai wannan gawa ce kawai taki rami,nan da dan kankanin lokaci duk zasu zama gawa tunda babu wanda zai kawo musu dauki a cikin halin da suke ciki sakamakon wannan jini dake zuba a jikinsu babu wanda zai tsira da rayuwarsa a cikinsu.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa da wadannan mugayen aljanu nasa sa dawakan da suke kai duk suka bace bat!daga cikin fadar. Bacewarsu keda wuya sai wanann babban hadimi na boka Darbusa ya dubi su SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ya bushe da dariyar mugunta yace,yanzu ku in banda wauta irin taku wane tsautsayi ne zaisa kuyi gangancin zuwa nan gidan domin ku dauki ALLON SIHIRIN shugabana? Tabbas biyu babu zakuui yanzu babu biyan bukata kuma babu rayuwarku.Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi hadimin cikin karfin haki tace ina farin cikin zan mutu a matsayun jarumar data sami nasarar shigowa har nan cikin fadar shugabanka,kuma nayi yaki da dakarunsa,amma ina da wata alfarma guda daya da nake son kayi min ita bayan mutuwata.Ka taimaka ka matso kusa na rada maka wannan alfarma saboda bana son kowa yaji.Koda sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai hadimin ya sake bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu sannan ya matso kusa da sarauniya Akisatul Sauwara ya tsugunna a daidai fuskarta domin tayi masa rada a kunnensa.Sarauniya Akisatul Sauwara ta yunkura kamar zata gaya masa magana a kunnesa sai ta shammaceshi cikin bakin zafin nama ta zaro sharbebiyar wuka a kugunsa ta cala masa ita a KAHON ZUCIYA!!!Nan take hadimin ya kurma uban ihu a lokacin da jini yai feshi ta cikin kirjinsa ya sulale kasa matacce.Koda ganin abinda ya faru sai ragowar dakarun dake cikin fadar suka rugo da gudu izuwa kan sarauniya Akisatul Sauwara,kawai sai gani akayi ta mike zumbur!ta yagi rigar jikinta ta daure babban raunin dake kan cinyarta sanna ta daka tsalle can gefe daya izuwa inda takobinta take ta sureta ta sake daka tsalle sama ta dira a tsakiyar dakarun ta hausu da SARA DA SUKA.Nan da nan kuwa ta rinka ragargazarsu tana zubar dasu kasa matattu. Koda Sarki Darmanu da Yarima Lubainu sukaga irin jarimtakar da Sarauniya Akisatul Sauwara takeyi sai suma suka yunkura cikin tsananin juriya suka kama daure raunikan jikinsu suka mike tsaye suka kaiwa sarauniya Akisatul Sauwara Dauki aka sake ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki. A¤A¤¤H¤A¤D¤A¤H¤A¤D¤A A CAN WAJEN gidan boka Darbusa kuwa lokacin da wannan BAQON JARUMI ya durfafo kofar gidan sai yaja linzamin dokinsa ya tsaye cak,sakamakon ganin Boka Darbusa da mukarrabansa.Nan da aka tsaya ana kallon kallo tsakanin Boka Darbusa da Bakon jarumin. Daga can sai Boka Darbusa ya budi baki yace yakai bakon jarumi wane ne kai,kuma menene ya kawoka wannan daji harka durfafo wannan gida nawa? Koda jin wannan tambaya sai Bakon Jarumin yayi shiru baice komai ba,kawai sai ya sauko daga kan dokinsa ya zare takobinsa daga cikin kufe.Koda ganin haka sai Dakarun Boka Darbusa ma suka zare nasu Takubban saboda a zatonsu yakarsu zaiyi. Kawai sai sukaga ya kama zane akan kasa da tsinin takobinsa ya rubuta KALMAR SHAHADA,gami da bayanin cewa yazo ne ya yada ADDININ MUSULUNCI a wannan nahiya.Koda ganin hakan sai Boka Darbusa ya fusata ainun ya dakawa bakon jarumin tsawaya yace kai kurmane da bazaka budi baki kayi magana ba,kuma mummunar fuska gareka da harda kake boyeta? Koda jin wannan tambaya sai bakon jarumin ya tafa hannunsa sau uku,faruwar hakan keda wuya sai ga wani dan guntun mutum ya fito daga cikin daji da gudun tsiya tamkar tashi sama yakeyi. Karfin gudun nasa ya cika abin al'ajabi.Da zu wan wannan dan wada gaban bakon jarumin sai ya risina yayi gaisuwa yace me kake da bukata? Take bakon jarumin yayi masa magana cikin yaren kurame,wato da hannu yayi masa magana.Nan take dan wadan ya fahimta sannan yajuya ga Boka Darbusa yace,ni Sunana DAZYAN kum na kasance bawa ga wannan bakon jarumi dake gabanku! Ku sani cewa maigidana ba kurma bane,kuma yana boye muryarsa da fuskarsa ne saboda wani sirri da ba lallai bane ba ku sanshi,amma dai kamar yadda yayi muki bayani mu baki ne daga wata nahiya daban,kuma munzo ne domin mu gabatar muku da addininmu wanda ake kira da ADDININ MUSULUNCI! kuma shine ADDININ GASKIYA.Addinin daku ke kansa na BAUTAR GUMAKA gami da ALJANU da TSAFI duk shirka ne kuma bata ne mabayyani!! Koda dan wada yazo nan a zancensa sai Boka Darbusa ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa ya dubeshi cikin alamun tsananin fushi yace tabbas kai da maigidan naka kun cika wawaye,kuma marasa hankali da tunani harda kuke tunanin cewa zaku zo mana da SABON ADDINI kuma mu karbeshi alhalin mun saba da addininmi tun IYAYE da KAKANNI!!! Tabbas kun kawo kanku GIDAN MUTUWA,kuma bama ku ba hatta ire irenku ma sai sunyi nadamar zuwa wannan nahiya tamu,kuma yanzun nan zansa a yi muku kisan wulakanci irin wanda ko a tarihi ba'a taba yin kamarsa ba a ko ina a cikin wannan duniya.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa ya dubi wadannan Aljanun haske dake kewaye dashi yayi musu wata inkiya.Nan take su duka suka sakarwa dawakansu linzami suka zaburesu da gudu izuwa kan Dazyan da maigidansa bakon jarumi.Koda Dazyan ya hangosu sun yiyo kansu sai ya daka tsalle sama ya dane kan wani bishiya mai tsawon gaske yana mai motsa bakinsa alamar cewa yana karanta wata addu'a ne ta neman tsari.Shi kuwa maigidan nasa bakon Jarumi sai ya daka tsalle sama ya haye kan dokin nasa tamkar daukarsa kayi aka ajiyeshi akan dokin sannan ya daga takobinsa sama yana mai kwallah KABBARA ya tunkari aljanun.Ai kuwa tun kafin ma su hadu aljanun hasken da dawakan nasu suka firgice suka razana ainun saboda tasirin wannan kabbara da bakon jarumin yayi.Ai kuwa suna haduwa aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI mai tsananin tayar da hankali,sai gashi bakon jarumin yana tsarge wadannan aljanun haske da dawakan nasu suna zubewa kasa matattu sun kamawa da wuta su kone kurmus,saidai kaga iska na diban tokarsu.Koda Boka Darbusa yaga yadda Bakon Jarumin yake yi masa mummunar barna sai ya fusata ainun kuma yasha JININ JIKINsa ya tabbatar da cewar lallai wannan bakon jarumi ba kanwar lasa bane,tsafi bazaiyi tasiri akan sa ba.Amma da yake Boka Darbusa ya yarda da kansa akan jarumtakarsa da KARFIN DANTSE Sai kawai shima ya zare takobinsa kuma ya sauko daga kan tsafaffen dokin nasa take dokin ya bace bat! shi kuma sai ya falfala da gudu izuwa kan bakon jarumin.Koda ya rage baifi saura taku goma ba tsakaninsu sai Boka Darbusa ya daka tsalle sama tamkar an cillashi daga cikin Baka ya kaiwa bakon jarumin mummunan sara a wuya da nufin ya cisge masa kai.Cikin tsananin bakin zafin nama Bakon Jarumin ya daga tasa takobin ya kare saran,amma saboda karfin saran saida ya kusan tuje rawanin bakon jarumin.koda ganin haka sai bakon jarumin ya fusata ainun kawai sai shima ya daka tsalle ta baya akan dokin yayi wata irin alkafira ta ban al'ajabi.Hatta wannan dan wada nasa wato Dazyan daya buya a can sama bishiya bai san sa'adda yayi masa tafi ba saboda ganin irin wannan gagarumar BAJINTA da yayi. Bakon jarumin ba sama shima ya maida martanin saran da Boka Darbusa ya kawo masa adazu.Sai gashi shi nasa saran ma yafi na Boka Darbusa nauyi da karfi,don har saida Boka Darbusa ya durkushe kasa bisa gwiwarsa guda kuma sai da kaifin takobin ta farka rigar Boka Darbusa.Al'amarin dayasa Boka Darbusa yayi wuf ya mike tsaye kenan yana mai gyara tsayuwa yana mamki saboda tunda yake GUMURZU da MANYAN MAZAJE bai taba haduwa da mai karfin damtse da iya yaki kamar wannan bakon jarumi ba.Saidai wani abu ya jefashi cikin wasi wasi ba komai bane ya jefashi cikin wasi wasin va face duk sa'adda ya dubi wannan bako jarumin sai yaga surar jikinsa tana kama data MATA,amma kuma idan yayi la'akari da irin zafin namansa da kuma KARFIN DAMTSENsa sai yaga cewa babu yadda za'ayi ya kasance 'YA MACE.Nan take Boka Darbusa ya aiyana a cikin ransa cewa duk yadda zaiyi sai yaga fuskar wannan bakon jarumi ko da kuwa bazai sami nasarar hallakashi ba.Bayan anyi kallon kallo na tsawon yan dakiku tsakanin Boka Darbusa da Bakon Jarumin sai suka rugo da gudu a lokaci guda izuwa kan juna,suna haduwa kuwa suka ruguntsume da azababben yaki na gaban kwatance ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama,juriya da jarumtaka. Saidai suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan BAKIN ARTABU ba tare da dayansu ya sami nasara ba. Koda bakon jarumin yaga Boka Darbusa na neman bata masa lokaci sai ya sauya salon fada ya hada da kai naushi da bugu ta ko ina kuma yana tsalle tsalle da kwance kwance.Ai kuwa nan da nan ya rikirkita Boka Darbusa har ya sami nasarar gabza masa mugayen naushi guda uku a fuska.take Hancin Boka Darbusa da bakinsa suka kama yoyon jini,kuma idanunsa suka kumbura sukayi suntum!Haka suka ci gaba da kwabsa wannan masifaffen yaki mai tsananin muni da tayar da hankali a tsakaninsu,tun Boka Darbusa yana iya kare naushi da bugun da bakon jarumin yake kawo masa har ya gaza balle ya samu damar mayar da martani. Ana cikin hakane bakon jarumin ya shammaci Boka Darbusa ya daka tsalle masa ya doki fuskarsa da kafa.Saboda karfin dukan saida Boka Darbusa yayi katantanwa sau uku a tsaye kuma take hakorinsa guda na sama ya yi fitar burgu daga cikin bakinsa tare da Wani GUDAN JINI,saboda tsanani zafi da zogin dayaji saida yaga taurarin wuya a cikin idanunsa a lokacin daya kife kasa,kuma yaji kansa ya kara girma yana neman rinjayar gangar jikinsa. Koda Boka Darbusa ya tabbatar da cewar wannan bakon jarumi ya fishi karfin damtse nesa ba kusa ba,kuma yafi shi iya yaki,sai ya mike tsaye zumbur,cikin matukar karfin hali da numa 'ki fadi,kamar cigaba zaiyi da yaki,amma sai ya juya da baya ya falfala da gudu izuwa cikin daji kamar dunduniyar kafarsa zata tabo keyarsa saboda karfin gudun.Koda ganin abinda ya faru sai dan wada Dazyan ya sauko daga kan doguwar bishiyar da yake kai ya ruga izuwa gaban bakon jarumin ya shiga yi masa kirari yana cewa,Ga 'ki gudu maganin sa gudu!!Ga mai dogaro da Allah,dodon kafirai.Koda jin wannan kirari sai bakon jarumin ya dagawa Dazyan hannu yana mai yi masa nuni da yai shiru,kawai sai ya nufi cikin gidan Boka Darbusa da sauri,shima Dazyan sai ya bishi da sauri. Nima ganin Boka Darbusa ya gudu,sannan Bakon Jarumin ya nufi gidan Boka Darbusa yasa nima nabi bayansa. Zan dakata anan dafatan yayi. pls Like nd comments idan naga yamin Anjima sainayimuku post din 3b 7 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na Uku (3) Part B A CAN FADAR Boka Darbusa kuwa bayan an shafe kusan rabin sa'a ana gumurzun yaki tsakanin su Yarima Lubainu da dakarun dake cikin fadar,su Lubainu nata samun nasara suna ta ragargazar dakarun saida suka karar dasu gaba daya.A lokacin ne suka gaji likis don haka sai suka zube kasa suna haki da numfarfashi kamar ransu zai fita.Faruwar hakan keda wuya sai suka ji takun sawaye da yawa daga can wasu bangarori na gidan da yawa ana rugowa izuwa inda suke.Al'amarin dayai matukar firgitasu kenan suke mimmike tsaye a tsorace,kafin suyi wani yunkuri sai ga wadansu samudawan dakarun mutane masu kirar MUTANEN FARKO,rike da mugayen makamai suna ta tuttudowa cikin fadar ta gabas da yamma,kudu da arewa,su da yawa ba adadi.Nan da nan suka yiwa su Yarima Lubainu KAWANYA.Koda ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta yarda takobinta,ta dubi sarki Darmanu da Yarima Lubainu cikin alamun karayar zuciya tace,ai shike nan kuma tamu ta kare,domin babu yadda zamu iya kare kanmu daga sharrin wadannan dakaru a wannan yanayi da muke ciki.Babu wani karfin dantse ko na Sihiri dazai cecemu.A yanzu duk burinmu ya rushe,kuma karshen rayuwarmu yazo,saidai mu rungumi kaddara.Idan muka ce zamu yaki wadannan dakaru ma zamu bata karfinmu ne a banza ba tare da mun samu koda nasarar sisi a kansu ba.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai jikin Yarima Lubainu dana Sarki Darmanu yayi sanyi,take shima Sarki Darmanu ya yarda takobin hannunsa,shima Yarima Lubainu har ya yunkura zai yarda takobinsa sai ya fasa yace kai! Aida dai na mutu RAGO gwara na mutu JARUMI,tsakanin mutum da sa'a da rabo,mutuwa ce don haka dole ne na jarraba sa'ata.Yana gama fadin hakan sai ya daga takobinsa sama ya riketa da hannu biyu.Koda ganin haka sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta yace,kai yaro hakika ganganci ne ya kawoku nan gidan domin babu abinda zaku samu face AJALINku.Koda gama fadin hakan sai shugaban dakarun ya daga hannunsa sama ya bayar da inkiyar a afkawa su Yarima Lubainu.Kafin daya daga cikin dakarun nasa yayi wani yunkuri sai aka jiyo KABBARA ta cika fadar gaba dya.Take kowa ya waiga baya izuwa inda sautin kabbarar ya fito,kawai sai aka hango BAQON JARUMI rike da takobinsa ya falfalo da azababben gudu,tazarar dake tsakaninsa da wadannan dubban samudawan dakaru yakai taku ashirin amma daua daka tsalle guda daya sai gashi ya fado a tsakiyarsu ya hausu da sara da suka.Nanfa ya tarwatsasu shi kadai ya zame musu GUGUWAR ANNOBA.Da zarar sun yunkuro da nufin su yanyameshi sai kaga ya tarwatsasu yana filfilawa a kasansu da samansu tamkar katantanawa ake murza wa,kuma duk inda yakai sara guda sai dai kaga Mazaje sama da arba'in sun zube kasa Matattu.Koda su Sarauniya Akisatul Sauwara sukaga wannan gagarumar jarumtaka ta ban al'ajabi wacce tafi gaban hankalinsu da tunaninsu sai suka cika da tsananin mamaki suka zazzaro idanu suka zubawa sarautar Allah idanu kawai.Nanfa YAKI ya kara TSAMARI ya zamana cewa dakarun sun fusata ainun suna dada afkawa bakon jarumin ta ko ina da dukkan karfinsu suna kai masa sara da suka,duk da cewa ragargazarsu bakon jarumin yake,JINI na feshi da fantsama kuma sassan jikinsu na yawo a sama yana zubowa kasa suna ihu da kururuwa suna zubewa kasa.Saida aka shafe sa'a biyu da rabi ana wannan mummunan azababben yaki daya daga cikin dakarun bai sami nasarar koda kwarzanar jikin bakon jarumin ba,kuma basu ga ya gajiya ba.Cigaba yake da ragargazarsu kawai amma saboda tsananin yawansu sai kaga kamar karuwa sukeyi.Duk wannan abu dake faruwa dan wada Dazyan ya shige karkashin wani tebur ya buya yana morewa idanunsa kallo,kuma yana karanta addu'ar neman tsari don kada tsautsayi ya haushi domin shi a rayuwarsa ko rike takobi bai taba yi ba bare ya iya yaki ko ya kare kansa.Haka dai aka cigaba da wannan mugun azababben yaki har aka sake shafe wata sa'ar gudu,a sannan ne fa samudawan dakarun suka gane cewa SHAYI RUWA NE!Domin tuni bakon jarumin ya gama kashe kaso biyu cikin kaso ukinsu.Wadanda basu mutu ba kuwa sun zama nakasassu,wasu sun rasa kafafu,wasu hannaye,aki wasu ma sai kaga an zabtare rabin kafadarsu,tsabar taurin rai ne yasa basu mutu ba.Koda ragowar samudawan dakarun suka tabbatar da cewar lallai bazasu iya kashe wannan takadirin jarumi ba,kuma indai aka cigaba da wannan yaki sai ya karar dasu gaba dayansu sai suka ciki wandunansu da iska suka bar ragowar nakasassun a wajen.Nan take fadar tayi tsit,tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a cikinta,kuma sai aka fara kallon kallo tsakanin bakon jarumin dasu Yarima Lubainu.Shi kuwa dan wada Dazyan ya fito daga inda yake boye ya tsaya a bayan bakon jarumin yana murmushi gami da karkade kurar jikinsa sakamakon kurar data baibaye masa jiki saboda a lokacin da bakon jarumin yake yaki da wadannan samudawan dakaru,sun ragargaje duk wani abu mai amfani dake cikin fadar an tashi 'kura mai yawa.Bayna anyi kallon kallo tsakanin bakon Jarumin dasu Sarauniya Akisatul Sauwara sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tako kafafunta ta matso kusa da bakon Jarumin ta dubeshi tace wanene kai kuma menene dalilin dayasa ka ceci rayuwarmu?Koda jin wannan tambaya sai bakon jarumin ya dubi Dazyan shi kuma sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara ya risina a gareta cikin alamun girmamawa yace,yaku wadannan jarumai guda uku,kuyi sani cewa shugabana baya magana ba don ya kasance kurma ba,kuma ya rufe fuskarsa ba don bashi da kyau ba,saboda wani babban sirri ne yasa yake aikata hakan da fatan bazaku damu ba.Kuyi sani cewa mu baki ne daga wata nahiya dabam,kuma munzo nan nahiyar ne domin mu gabatar muku da Addinmu wanda ake kira ADDININ MUSLUNCI!ADDININ MUSULUNCI shine ADDININ GASKIYA,don haka duk wani addini da kukeyi walau na BAUTAR GUMAKA ko RANA ko WATA ko ALJANU duk bata ne mabayyani!!!Tsafi shima shirka ne babba saboda haka muna kira agareku daku tuba ku bar wadannan addinai naku ku karbi namu.Ba komai ne yasa shugabana ya ceci rayuwarku ba face saboda ya fahimci cewa wannan Boka da kuke yaki dashi AZZALUMI ne kuma mushriki.Shin yanzu zaku karbi wannan Addini namu ne ko kuwa zaku bijire masa?Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu da Sarki Darmanu suka dubi junansu sukayi shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi gyaran murya sannan ta dubi dan wada Dazyan tace,yakai wannan gutun mutum..."Koda jin haka sai Dazyan ya turbune fuskarsa kuma ya tari numfashin Sarauniya Akisatul Sauwara yace ke yarinya kada kici min fuska ko kiyi min rashin kunya.Ki sani cewa na haifi kamarki don haka bai kamata ki kirani da dan guntu ba!!!Koda jin haka sai Sarauniya Akisatuk Sauwara ta risina cikin biyayya tace,k gafarceni amma bansan sunan da yakamata na kiraka dashi bane.Dan wada Dazyan yace sunana na yanka shine DAZYAN! Amma ana kirana da ABUL YAZRIN.Sarauniya Akisatul Sauwara tace,daga yau nayi alkawarin zan rinka kiranka da Abul Yazrin don girmamawa.Ka gayawa mai gidanka cewa muna bukatar cikakkiyar hujja wacce zata sa mu gamsu da cewa lallai wannan addini dakukazo dashi shine ADDININ GASKIYA.Baya ga haka kuma muna bukatar muyi nazari da shawara domin mu sanar dakai abinda muke ganin zaisa mu sami nutsuwa da yarda akan wannan sabon addini naku.Koda jin wannna batu sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa zance da hannu.Dazyan ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace yaki bayananku,kuma ya aminta da duk uzurin dakukazo dashi amma kuma yana son yasa abu guda biyu a tare daku.Abu na farko da yake son sani shine shin me ya kawo ku nan gidan har yaki ya barke tsakaninku da wannan Boka?Abu na biyu kuma shine yana son yasan iya tsawon lokacin dazaku yanke shawara da kuma abinda kuke son yayi muku wanda zaisa ku gamsu cewa addininsa shine ADDININ GASKIYA?Ya ce na gargadeku akan cewa ku tabbatar da cewar duk abinda zaku fada masa ku fadi iyakar gaskiya,in ba haka ba kuwa bazai sake taimakonku ba kuma zaku iya zama ABOKAN GABA a gareshi!!Kuma yace a sanar daku cewa har yanzu fa baku tsira daga sharrin wannan Boka ba,domin ba mutuwa yayi ba guduwa yayi,babu mamaki ma yana nan a labe wani wurin yana fakonku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai Hankalin Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu ya dugunzuma ainun,sukayi tsuru tsuru suna kallon junansu suka kasa cewa uffan.Kawai sai Sarauniya Akisatul Sauwara taja su izuwa can gefe daya inda su Bakon Jarumin basu ji abinda zasu tattauna ba.Cikin nutsuwa Sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da Yarima Lubainu tace me kuke ganin ya kamata muce da wannan hatsabibin bakon jarumi?Kowannenmu ya ga irin tsantsar jarumtakarsa ta ban al'ajabi.Tabbas idan muka yi kuskuren yi masa karya ko yaudara zamu iya yin nadama.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya numfasa yace ai dama tun kafin na baro gida na dauki alkawaron cewa bazanyi karya ba,kuma bazanci amana ba,sannan zan zamo mai cika alkawari saboda haka idan kun amince zan wakilceku naje na yiwa wannan bakon Jarumi bayanin komai bisa gaskiyar al'amarin kuma mu nemi taimakonsa bisa hada wannan ALLON SIHIRI tunda a yanzu haka bamu san a inda Boka Darbusa ya boye nasa ALLON SIHRIN ba kuma bamu san irin tsaron da ya bashi ba bare har mu iya daukoshi.To amma fa akwai matsala guda daya,a tsakaninmu mu ukun nan babu wanda yasan abinda kowannenmu ya shirya a zuciyarsa.Babu mamaki bayan an hada ALLON SIHIRI dayanmu ya shammaci sauran ya cutar dasu ya gudu da ALLON SIHIRIN don cika burinsa shi kadai tunda dole dai mutum daya ne daga cikinmu zai iya cika burinsa a lokaci guda,kuma dole sai yana tare da ALLON SIHIRI zai iya kammala sauran aikin cikia burin nasa.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu suka dubi juna kowannensu yai shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai Sarki Darmanu yace kai yaro ne tayaya zamu hadu da mutum a yau dinnan rana daya jal,kuma mu saki jikinmu dashi har mu gaya masa sirrinmu?Shin baka tsoron cewa zai iya cutar damu ko kuma yayi amfani da sirrin namu sami Damai-Akala?Kawai muyi amfani dashi wajen cika burinmu in yaso mu a tsakaninmu mu sasanta yadda kowa zai amfana.Koda jin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi murmushi tace tabbas kazo da shawara mafi alheri,shi kuwa Yarima Lubainu sai ransa ya baci ya dubesu su biyun yace,ni kam daga yanzu na fita daga cikinku domin bazan iya baku yarda da amanata ba,tunda har zaku iya yin karya da yaudara,gwara na baiwa wannan bakon jarumin amincina saboda akwai alamun cewa zaifiku iya rike amanata.Koda gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya juya ya bar wajen su Sarki Darmanu ya nufi inda Bakon Jarumin da dan wada Dazyan ke tsaye.Koda ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta ruga izuwa gareshi tasha gabansa tace haba yakai wannan dan Sarki,ka tuna irin halaccin danayi maka lokacin dakazo gareni bisa neman taimakona.Ka tuna yadda na dauko ALLON SIHIRI NA kuma na biyoka a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske don kawai na taimake ka ka sami nasarar samo lafiyar jikinka ka koma ga matarka kuma masoyiyarka YAZARINA?Idan ka tarwatsa mini nawa shirin saboda cikar burinka kaci amanata kuma ka nuna mini cewa kai ba dan Halak bane!Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo daidai nan a zancenta sai Jikin Yarima Lubainu yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma har idanunsa suka dan ciko da kwallah,amma daya sake tuno da nasihar da aka bashi kafin ya baro gida ta rike gaskiya,amana da alkawari sai ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,kiyi hakuri akan fadin gaskiay saidai kice naci amanarki.Yana gama fadin hakan ya tunkari bakon jarumin gadan gadan yana shirin ya isa daf dashi sai dan wada Dazyan yai sauri ya shiga tsakiyarsu ya dubeshi a fusace yace,doka ta farko ba a kusantar maigidana don yin magana dashi.Na gaya muku cewa ba kurma bane ba,don haka ko daga nesa zaka iya fadin duk abinda kakeson fada masa.Koda jin haka sai Yarima Lubainu yayi murmushi yace hakikanin gaskiya ni neman magani ne ya fito dani daga kasarmu.Nan take Yarima Lubainu ya kwashe labarinsa kaf ya zayyane bai boye komai ba harda batun soyayyarsa da YAZARINA wacce ta haddasa gaba a tsakaninsa da abokinsa YARIMA MANGUL har sukayi gasar neman aurenta ta hanyar yakar juna ya cirewa Yarima Mangul hannun daya shi kuma yayi masa asiri ya kashe masa Mazakuta.Yarima Lubainu ya cigaba da bayani akan fitowar da yayi don neman ALLON SIHIRI ya karantashi don ya gano inda KOGIN BAHAR IMFAL yake yaje cikinsa ya tsinko dan itaciyar da zata warkar da wannan cuta tasa domin ya koma gida a matsayin Namiji lafiyayye yaci gaba da ZAMAN AURE da masoyiyarsa YazarinaLokacin da Yarima Lubainu yazo nan a labarinsa sai bakon Jarumin da Dazyan suka ji sun kamu da tsananin tausayinsa.Bakon Jarumin yayi shiru yana tunani da nazari izuwa tsawon dan dakiku kadan sannan

Chapter 6 of 19