Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaki!Daga yanzu zai ci gaba da ajiye ALLON SIHIRI a wajensa har izuwa wannan lokaci don haka tun yanzu kuna da sauran damar da zakuyi shawara bisa abinda kuke ganin cewa shine zai fissheku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai su Yarima Lubainu suka dubi junansu suka rasa abinda zasu ce kawai sai Yarima Lubainu yajasu gefe daya ya dubesu cikin nutsuwa yace,abinda nake so daku shine,kada dayanku ya bigire sharadin wannan bakon jarumi domin yanzu a hannunsa muke sai yadda yayi damu,idan muka ce zamuyi masa tawaye dayanmu bazai tsira da rayuwarsa ba bare ya cika burin rayuwarsa.Ko kuwa akwai mai korafi a cikinku akan wannan shawara dana kawo? Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da sarki Darmanu suka budi baki a lokaci guda sukace bamu da wani korafi face bin sharadinsa.Dajin haka sai farin ciki ya lullube Yarima Lubainu yaja su suka koma wajen bakon jarumi ya sanar dashi cewa sun amince da dukkan sharadinsa kuma basu da wani korafi.Da jin haka sai bakon jarumi ya mike tsaye ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame shi kuma ya dubi su Yarima Lubaiun yace,shugabana yace kowa ya debo kayansa zamu cigaba da tafiya yanzu.Dajin haka sai kowa ya ruga izuwa cikin fadar Boka Darbusa ya dauko jakar guzurinsa ya dora akan dokinsa kuma ya hau kan dokin nasa ya zauna.Saida kowa ya gama kimtsawa sannan bakon jarumi ya hau nasa dokin ya wuce gaba,Dazyan ya jere dashi.Sarauniya Akisatul Sauwara ce ke biye dasu sannan Yarima Lubainu,Sarki Darmani ne na karshe.A wannan lokaci bakon jarumi ya lullube ALLON SIHIRI a cikin wani babban mayafi ya dora akan wuyan dokinsa ya daureshi tamau.Ana fara yin wannan tafiya ne sarauniya Akisatul Sauwara ta waigo ta dubi Yarima Lubainu sai taga ya sunkui da kansa kasa yana tunani mai zurfi.Koda ganinsa a wannan hali sai ta tsayar da dokinta har saida taga ya iso daf da ita sannan suka cigaba da tafiya a tare a jere,a sannan ne ta dubeshi cikin alamin tausayawa tace,yakai Yarima menene yake damunka ne?Tun jiya na lura da kai baka yin magana sosai,kuma baka cin abinci kamar yadda ka saba,sannan ko yaushe sai naga kayi shiru kana tunani mai zurfi ina dalilin hakan? Koda Yarima Lubainu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya Akisatul Sauwara sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,kiyi sani cewa tun jiya ne naji zuciyata tana yawa bugawa da karfi haka kawai ba tare da nasan dalili na,sannan kuma a daren jiyan nayi wani mafarki mai ban tsoro.A cikin mafarkin an nuna mini katon bakin kumurcin maciji yana bin inuwata da gudu a cikin daji har inuwar rawa tana yin tuntube tana faduwa amma a karshe sai inuwar tawa ta yanke jiki ta fadi kasa ta kasa cigaba da gudu har macijin yazo daf da ita ya fasa kai.Yana shirn saranta ne na farka daga barci a cikin daren naji jikina na kyarma saboda firgita danayi kuma gaba daya jikina a sannan ya jike sharkaf da gumi tamkar abinda na gami a mafarki ya faru ne a gaske.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi ajiyar zuciya sannan tace,indazaka tuntubi bakon jarumi akan wannan mafarki naka da zai iya gaya maka fassararsa.Koda jin haka sai mamaki ya kama Yarima Lubainu yace yaya akayi kika san cewa ya iya fassara mafarki alhalin bashi da bakin yin magana?Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ji nayi wancan bawan nasa dan wada Dazyan ya bashi labarin wani mafarki dayayi shi kuma ua fassara masa mafarkin a cikin yaren kurame,al'amarin daya bani sha'awa kenan na tambayi Dazyan nace yakai Dazyan naji kana gayawa shugabanka cewa kayi mafarkin wata kaza wacce tayi kwaikwaye biyu kala daban daban.Kwan farko data sako FARI ne fat na biyu kuma JA ne,kawai sai tayi kwanci akan farin ta kyankyashe UNGULU da kuma tayi kwanci akan jan saita kyankyashe ZABUWA.To waishin menene fassarar dayayi maka akan wannan mafarki naka? Lokacin da Dazyan yaji wannan tambata dana yi masa sai yace,fassarar da maigidana yayi mini itace,Allah ne yakeyi mini nuni dana nutsu nayi hankali da duniya.Wannan kasa itace duniya,kwan farko ya kasance FARI shine hali nagari idan mutum ya rikeshi zuciyarsa zata zama fara mara mugunta da kyakkyawan nufi.Kwai na biyu data kyankyashe wanda shine JA alama ce ta mugun hali.Ai bakaji karshen mafarkin nawa ba saboda a cikin yaren kurame na karasa bashi labari.Cigaban labarin kuwa shine,bayan kazar ta kyankyashe kwaikwayen biyu sai unguku taka jewa.Koda tazo giftawa ta gaban zabuwar sai zabuwar ta cafko kanta ta gutsure mata kai,kuma ta hau bayanta ta zauna.Wannan alama ce ta cewar mutane a yanzu sunayin UNGULU da KAN ZABO!Ma'ana idan sukaga yan'uwansu masu kyawawan halaye sai su jasu a jiki kamar suna koyi dasu,amma a karshe sai suyi amfani da wannan dama su turmushesu su hallakasu.Sa'adda maigidana yazo nan a jawabinsa saina dubeshi cikin alamun mamaki nace,to yanzu menene matakin daya kamata na dauka don kada irin haka ta sameni?Maigidana sai yace,kayi gaskiya,amana da rikon alkawari.Idan kayi hakan Allah zai kareka daga sharrin dukkan mai son cutar dakai.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara yazo nan a jawabinta sai Yarima Lubainu yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta tashi,take yaji a cikin ransa cewa lallai akwai alamun gaskiya a cikin wannan addina na bakon Jarumi saboda jin irn wannan hikima da aka zuba a cikin mafarkin dan wada Dazyan.Kawai sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ai kuwa duk sa'adda muka yada zango zanje na sami bako jarumi na sanar dashi nawa mafarkin don naji irin fassarar da zaiyi.Waishin ke bakiji wani abu a ranki ba ko a jikinki sakamakon labarin wannan mafarki mai dauke da dumbin hikima da basira.Sarauniya Akisatul Sauwara ta numfasa tace,tabbas naji gaba dayan tsigar jikina ta tashi kuma zuciyata ta daskare tamkar na tsomata a cikin ruwan kankara.Koda kin wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima Lubainu yace,ai nima irin abinda naji kenan sak da naki.Anya kuwa wannan addini na bakon Jarumi bashi ne ADDININ GASKIYA BA?Koda jin wannan tambaya sai sarauniya Akisatul Sauwara ta gyada kai tace,ai kuwa ita gaskiya bata buya har abada,idan har shine ADDININ GASKIYAR to da sanni zamuga babbar shaida dazata tabbatar mana da hakan.koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya girgiza kai yayi shiru bai kara cewa komai ba aka cigaba da tafiya ba sassauci.Ba'a tsaya ba har saida bakon Jarumi ya fuskanci cewa lokacin sallar Azahar yayi sannan ya bayar da umarnin a tsaya a yada zango,kuma sai akayi sa'a a wannan lokaci an iso wani wuri mai magudanar ruwa.Koda su Yarima Lubainu sukaga wannan ruwa sai suka kamu da matukar sha'awarsa suka ruga izuwa cikin ruwan suka kama shansa suna wanke fuskarsu suna zubashi a kansu.Koda bakon Jarumi yaga duk hankalinsu ya tafi izuwa cikin wannan ruwa hardashi kansa Dazyan ya tafi cikin ruwan ya tsugunna yana alwala.Nan take bakon jarumin ya sulale daga wajen ba tare da dayansu ya ganshi ba ya zagaya bayan duwatsun da wannan ruwa ke fitowa ta cikinsa inda babu mai ganinsa.Da zuwansa sai ya tsaye cak ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa yaga babu wani mahaluki mai ganinsa,kawai sai ya tsugunna a gaban ruwan yasa hannayensa biyu ya cire rawanin dake kansa,wanda ya rufe fuskarsa.Dogon bakin gashi ne mai tsananin haske da kyalkyalu ya zubo kasa bisa kafadunsa,a lokacin da kyakkyawar fuskar 'YA MACE ta gaban kwantace ta bayyana.Idan mutum ya kwatanta kyawun wannan mace dana sarauniya Akisatul Sauwara sai yaga ashe sarauniya Akisatul Sauwara ma mummuna ce akan wannan BAKUWAR JARUMA saboda bambancin a bayyana yake babu gami!"Ni kaina a matsayina na marubicin wannan littafi an shammaceni a cikin labarin,domin ban taba zaton cewa bakon jarumi MACE ce ba NAMIJI ba musamman da nayi la'akari da irin abubuwan dayayi na jarumtaka".Nan take kyakkawar jarumar ta ajiye rawanin nata daf da ita sannan ta sanya zara zaran yan yatsun hannayenta guda biyu a cikin ruwan ta kwarfoshi tana mai yin bismillah.Ina jin sautin muryarta zuciyata ta buga da karfi naji kamar kirjina zai tsage saboda tsananin zakin muryar,domin kamai dacin ran mutum idan kunnuwansa suka ji wannan murya mai zaki da taushi sai yaji kamar ruwan sukari aka watsa masa ya gauraye da dukkan JININ JIKINsa.Nan take ma'abociyar kyawun ta fara alwala a nutse cikin ilmi da kwanciyar hankali saida tazo kan wanke kafar hagu a karshen alwalar sai kawai taji takun sawu a bayanta.Cikin bakin zafin nama ta suri rawaninta ta kifa a kanta,take ya rufe gashinta da fuskarta kamar yadda ya saba rufeshi koda yaushe,sannan ta yunkura da nufin ta waiga don taga ko waye ke tahowa ta bayan nata,kawai sai taji ansamata tsinin takobi akan tsakiyar wuyanta ta baya ana bata umarnin kada ta kuskura ta motsa.Sautin muryar data bata umarni ne ta firgitata ainun fiye da tsinin takobin dake kan wuyan nata ba don komai ba sai saboda ta shaida cewa ba wani bane mai wannan murya face YARIMA LUBAINU.Yarima Lubainu ya kurawa kyakyawar jarumar idanu ta bayanta a lokacin da gaba dayan jikinsa ya kama kyarma saboda dimauta dayayi tun farko hango kyakkyawar fuskarta.Ko a mafarki Yarima Lubainu idanunsa basu taba siffanta masa mace mai irin kyawun ta ba.Inda za'a dauki matarsa Yazarina a ajiyeta kusa da bakuwar Jarumar da kyawunta disashewa zaiyi ta koma mummuna saboda kwarjini da haibar bakuwar jaruma.Yarima Lubainu ya sake budar baki da kyar muryarsa na rawa yace,saboda me zaki yaudaremu tun farko ki boye wannan kyakkyawar fuskar taki da kuma siffarki ta 'ya mace da wannan murya taki mai tsananin zaki da naushi tamkar sarewa?Koda jin wannan tambaya sai Jarumar ta mike tsaye ta juyo ta fuskanceshi tace,Kamar yadda bawana Dazyan ya gaya muku tun farko ina da hujjar da tasa na boye fuskata,muryata da jikina wacce ba lallai bane na sanar dakai a yanzu,amma kadan daga cikin hujjar ka gani yanzu da idanunka,kuma kaji ta a jikinka,domin naga yadda jikinka ya kama tsuma a lokacin dakayi arba da kyakkyawar fuskata.Ina mai tabbatar maka da cewa in da kuma gaba daya surata ka gani zaka iya fita daga hayyacinka.Har izuwa wannan lokaci da jarumar ke magan zuciyar Yarima Lubainu bata daina daka ba kuma jikinsa bai daina kyarma ba.Abinda zuciyar tasa ke raya masa shine,wannan ma'abociyar kyau dazata kasance sarauniya to zai iya yarda tsafanceshi ya zamo gadonta na barci don kawai ya kasance kullum yana tare da iya yana ganinta kuma yana jinta a jikinsa.Ai kuwa nan take ya fada cikin kogin tunanin yiyuwar hakan tamkar a mafarki.Koda jarumar ta lura da cewa Yarima Lubainu baya tare da ita ya tafi izuwa wata duniyar ta tunani sai tayi murmushi ta tafa hannyenta a daidai kunnuwansa.Yarima Lubainu yai firgit tamkar wanda ya farka daga barci mai nauyi ya kura mata idanu.Ita kuma sai ta dubeshi cikin nutsuwa tace,yakai wannan dan Sarki ka yi sani cewa tun a farkon danaji labarinka na kamu da tausayinka kuma a cikin zuciyata sai na yanke hukuncin taimakonka koda kuwa ba zaka karbi addinina ba saboda ina kishin halin da matarka zata shiga sakamakon rabuwarku.Abinda nakeso dakai shine ka cigaba da rufe sirrina kada ka kuskura ka nuna wata alama da zata nuna cewa ka gane cewa ni mace ce.In dai ka ruke wannan al'amari ni kuma zan cigaba da taimakonka harka rabu da wannan lalura.Amma inason nayi maka wata tambaya guda daya,kuma lallai ka bani amsarta bisa gaskiya idan kayi mini karya ka sani cewa anan gaba zakaji kunya.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu yayi ajiyar zuciya sannan yace,babu yadda za'ayi nayi miki karya saboda kafin na baro gida mahaifiyata ta bani guzurin abubuwa uku wadanda tace dani in dai na rikesu sai na sami nasarar abinda na fita nema.Abu na farko shine lallai duk abinda zan fadi ko zanyi nayi shi bisa gaskiya.Abu na biyu shine,na zamo mai cika alkawari.Abu na karshe shine na zamo mai rike amana idan har an bani na karba.Tace idan na rike wadannan abubuwa dukkan wani burina na duniya zan cikasu,kuma makiyana tasirinsu kalilan ne akaina na dan lokaci kankani.Yake wannan ma'abociyar kyawu na ban al'ajabi ki yi mini tambayarki ni kuma na rantse da darajar uwata da ubana zan baki amsa iyakar gaskiya.Koda jin wannan batu sai murna ta kama jarumar tace,daga lokacin dana hadu daku kawo iyanzu me kaji a zuciyarka dangane da addinina? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yayi murmushi yace,ai tun a ranar farko da muka kusan hallaka a cikin fadar Boka Darbusa naga kin baiyana tsulum,kin cecemu naga irin gagarumin karfinki na ban al'ajabi na gane cewa al'amari ne wanda yafi karfin tsafi ko na Aljan.Lallai karfi ne na wani ubangiki da babu kamarsa.Koda Yarima Mangul yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube jarumar tace,shin hakan yana nufin cewa zaka iya karbar addinina.?Yarima Lubainu yace,kwarai kuwa ko a yanzu ina muradin karbarsa,amma na fuskanci cewa sauran abokan tafiyar tawa basuyi imani dashi ba kuma akwai alamin cewa in suka sami dama zasu iya yaudararmu su sace ALLON SIHIRI su gudu.Koda Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube bakuwar jarumar saboda ganin cewa ko ba komai yanzu ta sami nasarar jawo hankalin mutum daya ga ADDININ GASKIYA.Jarumar ta dubi Yarima Lubainu cikin nutsuwa tace banaso yan'uwanka su san cewa ka karbi addina a yanzu saboda in hakan ta faru bazan sami damar jayo nasu ra'ayin ba.Ba komai ne yasa na amince na biku har izuwa kogin Bahar Imfal ba face saboda inason na nunawa sarakanku na wannan nahiya cewa nayi abinda su bazasu iya ba da taimakon ubangijina,saboda hakan ne kadai zaisa zuciyoyinsu su karaya su bada gaskiya ga Addinin nawa,saboda na fuskanci cewa ba karamin aiki bane a rabasu da addininsu da suka gada tun iyaye da kakanni.Koda Jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi ajiyar numfashi yace tabbas zancenki dutse ne kuma nima nayi miki alkawari zan taimaka miki iyakar kokarina wajen ganin mun shawo kan jama'a sun fuskanci gaskiya sun karbeta. 1 hr · PublicALLON-SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part C Mun shawo kan jama'a sun fuskanci gaskiya sun karbeta.Ina da wata alfarama guda daya danake so na nema a wajenki.Cikin mamaki bakuwar jarumar ta dubi Yarima Lubainu tace,kai kuwa wacce irin alfarma kake son nayi maka?Yarima Lubainu ya numfasa yace,sarauniya Akisatul Sauwara ta gaya mini cewa kina da.ilmin fassarar mafarki,kuma nayi wani mafarki ne wanda ya razanani ainun wanda nake son ki fassara mini shi.Nan take Yarima Lubainu ya kwashe labarin mafarkinsa ya zaiyana mata.Koda jin labarin wannan mafarki na Yarima Lubainu sai nan da nan fuskar bakuwar jarumar ta sauya izuwa alamun damuwa tayi shiru tana mai sunkui da kanta kas.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalin Yarima Lubainu kenan ya budi baki da nufi yace wani abu,sai kawai suka hango Dan wada Dazyan ya rugo izuwa garesu.Da zuwansa gaban bakuwar jaruma sai ya zube kasa cikin girmamawa yace,ya shugabana tun dazu nayi alwala nake jiranka kazo muyi sallah amma sai naji shiru ban ganka ba shi yasa na taho nema.Koda jin haka sai bakuwar jaruma ta mike tsaye suka nufi wani waje mai rairayi suka tsaya.Dan wada Dazyan ya tsaya a gaban bakon jarumi ya tayar da sallah ita kuma ta tsaya a bayansa tana binsa.A daidai wannan lokaci ne Yarima Lubainu yaji kamar daga sama an kirawo sunansa.Yana waigowa bayansa yaga ashe sarauniya Akisatul Sauwara ce ta nufoshi fuskarta cike da annuri.Saida tazo daf dashi sannan ta tsaya suka fuskanci su Dazyan dakeyin sallah.Sarauniy a Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu tace,nifa wani abu yana daure min kai duk sa'adda Dazyan da maigidansa suka zo yin wannan ibada tasu sai naga Dazyan ya wuce kan gaba,shi kuma maigidan nasa ya koma baya.Ai kamata yayi ace maigidan nasa ne yake jagorantarsa a komai.Abu na biyu kuma shine a duk sa'adda na kalli idanun wannan bakon jarumi sai naga kamar mace ce ba namiji ba!zuciyata zata dade tanayi mini zargi da wasi wasi akan hakan.Inda ina da iko danaje na tuje rawanin dake kansa munga gaskiyar al'amari.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya turbune fuskarsa ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin alamun fishi yace,kada ki kuskura kiyi irin wannan tabargaza domin idan muka sami matsala da wannan bakon jarumi nine zanfi kowa kwaruwa.Keda Sarki Darmanu kun fito ne domin neman duniya,ni kuma neman lafiya ne ya fito dani.Koda jin wannan batu sai jikin sarauniya akisatul Sauwara yayi sanyi tace,shike nan nayi maka alkawari bazanyi duk wani abu dazai kawo matsala a tsakaninmu da wannan bakon jarumi ba.Shin yayi maka bayani kuwa akan mafarkinka? Na san cewa saboda hake ne ka biyoshi izuwa nan bayan wannan dutse?Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yai caraf yace,to banda abinki ta yaya kurma zaiyi mini wani bayani na fahimta alhali ni ban iya zancen kurame ba,kuma babu Dazyan a lokacin danazo wajensa.Sarauniya Akisatul Sauwara ta jinjina kai ta dubi Yarima Lubainu cikin alamun rashin yadda tace,amma kuma ai naga ka dade anan tare dashi,hirar me kuke tayi ne?Cikin fishi Yarima Lubainu ya mike tsaye yace,ai wannan tambaya ce ta rainin hankali to gaki nan gashi sai ki bari ya gama ibadar tasa ki tambayeshi irin hirar da nayi dashi.Kinsa ance waka a bakin mai ita ta fi dadi.Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike zumbur tasha gaban Yarima Lubainu tace,ka gafarceni yakai Lubainu tabbas nayi kuskure bisa wannan tambaya danayi maka.Kodajin haka sai Yarima Lubainu yai shiru baice da ita komai ba,ya tafi ya barta tsaye a wajentana mai binsa da kallo sannan ta juya ta kurawa bakon jarumi idanu wanda keyin sallah tare da Dazyan tace a cikin ranta."Komai naka irin na mata ne,ta yaya zuciyata zata gamsu cewa kai namiji ne?Tunda muka hadu dakai ban taba ganin lokacin daka cire kayan jikinka ba bare naga zahirin jikinka,kaki ka bude fuskarka mu gani.Amma zan kafa naci da zuba ido har sai naga gaskiyar al'amari.Sarauniya Akisatul Sauwara na gama aiyana hakan a cikin ranta sai ta juya ta koma can inda aka yada zango.Bayan su bakuwar jaruma sun idar da sallah sai suka dawo wajen su Yarima Lubainu suka zauna akaci abincin rana.Daga nan aka mike kowa ya kimtsa aka cigaba da tafiya.Ba'a sake tsayawa a ko ina ba saida lokacin sallar La'asar yayi nan ma Dazyan da bakon jarumi suka gabatar da sallar aka sake cigaba da tafiya ba sassauci.Da yammaci ne sakaliya suka shigo cikin wani daji mai katon fili.Shidai wannan fili ana yi masa lakabi da sunan Dajin MUJALLUN HARBUN.Shidai wannan daji na Mujallin Harbun daji ne wanda sama da shekari dubu ba'ayin komai a cikinsa face yaki.Duk kasashen dake nahiyar idan zasu yaki juna a wannan fili suke haduwa a fafata.Da isowarsu Sarauniya Akisatul Sauwara farkon wannan fili,dama bakon jarumi ne akan gaba,sai kawai sukaga bakon jarumi yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak,yana mai daga hannunsa sama alamar cewa kowa ya tsaya.Nan take kuwa Yarima Lubainu,Dazyan, Sarau­ niya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu sukabi umarnin bakon jarumi kowa yaja linzamin dokinsa suka tsaya cak,gaba dayansu,sai suka kama kalle kalle suna duban gabas da yamma kudu da arewa amma sai sukaji shiru basuga komai ba kuma basuji motsin komai ba.Kawai sar Sarki Darmanu ya bushe da dariya ya dubi bakon Jarumi ya sake bushewa da dariya tace,yazaka tsayar damu haka kawai muna cikintafiya?To idan ma kana zargin akwai wani mugun abu ne anan babu komai face tarin kwarangwal na bil'adama saboda wannan wuri fili ne na yaki asali kimanin shekaru dubu baya.Koda jin wannan batu sai bakon jarumi ya dubi Dazyan yayi masa magana a cikin yaren kurmanci.Dazyan ya dubi sarki Darmanu yace shugabana yace na gaya maka cewa,lallai akwai alamun wani mugun abun daya buya a cikin wannan duhowoyi ko a sama kan bishiyoyi saboda haka kowa ya zauna a cikin shirin yaki.Gama fadin hakan keda wuya sai bakon jarumi ya daga garkuwarsa sama kuma ya zare takobinsa.Nan take kowa ma yayi koyi dashi suka sakarwa dawakansu linzami suka cigaba da tafiya suna masu ratsawa ta cikin filin Mujallun Harbun suna waife waige don ganin ta inda za'a fara kawo musu hari.Saida suka iso tsakiyar filin sannan sukaga kasa na tsagewa da darewa.Kafin suyi wani yunkuri sai sukaga wadansu dodanni gabza gabza suna fasowa ta cikin karkashin kasa suna dira kan turba rike da MUGGAN MAKAMAI su da yawa ba adadi.Tun da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo duniya bata taba ganin halitta mai tsananin muni da ban tsoro kamar wadannan dodanni ba.Saboda tsawonsi kuwa saisu Yarima Lubainu da dawakansu suka zamo 'yan kananu a gabansu bayan dodannin sun gama yi musu KAWANYA.Gurnanin da dodannin keyi ne ya fara firgita dukkan tsuntsaye da dabbobin dajin suka kama canja sheka.In banda bakon jarumi da dan wada Dazyan babu wanda jikinsa bai kama tsuma ba saboda razana sakamakon ganin wadannan dodanni.Kawai sai bakon jarumi ya mayar da takobinsa cikin kufe,shima Dazyan sai ya mayar da tasa takobin ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da Yarima Lubainu yace,maigidana yace yanzu sai ku yaki wadannan dodanni da karfin damtsenku gami dana sihirinku,kuma ku hada da neman taimakon ababan bautarku domin ya gani ko zaku iya kubuta.Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama su Sarauniya Akisatul Sauwara.Sarki Darmanu ya dubi dan wada Dazyan cikin alamun firgici yace,saboda me shugabanka zaiyi mana haka alhalin ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kasa?Dan wada Dazyan yayi murmushi yace,ai idan baka manta ba haka ka'idar take,kafin mu fara wannan tafiya tare daku saida muka yi sharadin cewa duk masifae data taso kune zaku fara tunkararta da dukkan karfin damtsenku da karfin sihirinku,saidai idan mun ga kun gaza saimu kawo muku agaji.Koda gami fadin hakan sai bakon jarumi da Dazyan suka sauko daga kan dawakansu suka zauna a kasa dirshen suka rintse idanuwansu suka kama karanta wata addu'a ta musamman.Faruwar hakan keda wuya sai suka bace bat daga filin tamkar basu taba wanzuwa ba awajen.Al'amarin daya sake firgita su sarauniya Akisatul Sauwara kenan kuma ya girgiza hankalinsu.Su kuwa dodannin nan da suka ga mutum biyu sun bace musu da gani sai suka fusata sukayo caa!izuwa kansu Yarima Lubainu suna masu yin wani irin ruri mai tsananin firgitarwa.Koda ganin haka sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da Yarima Lubainu tace bamu da wani zabi wanda yafi mu kare kanmu muyi iya kokarinmu..Kafin ta gama rufe bakinta tuni wani dodo ya dako tsalle ya dira a gabanta ya kawo mata wawan sara da wata irin kakakifar adda mai cako cakon tsini kamar zarto.Cikin bakin zafin nama ta sunkuya addar ta sari iska amma saita fille kan dokin sarki Darmanu fit,dokin da sarki Darmanu suka zube kasa.Nanfa wuri ya hargitse aka rincabe da mugun azababben yaki mai tsananin muni da tayar da hankali.Ai kuwa ana fara wannan yaki su sarauniya Akisatul Sauwara suka raina kansu suka gane cewa yau sun gamu da gamonsu,domin dai wadannan dodanni basa jin SARA DA SUKA da zarar an saresu saidai kaji kara kal!tamkar karfe da karfe ne suka hadu,kuma a fuska ne kadai suke jin naushi,kuma saboda zafin namansu su sarauniya Akisatul Sauwara basa iya naushin nasu ko saransu a fuskar.In badin ma suma suna da nasu zafin naman ba da tuni dodannin sun hallakasu farat daya.Haka dai su Yarima Lubainu suka cigaba da yin iya kokarinsu waje kare kansu gami da maida martani.koda aka shafe sa'a guda anayin wannan BAKIN GUMURZU sai yaki ya sauya salo,ya zamana cewa su Yarima Lubainu sun fara gajiya,ai kuwa a sannan ne dodannin suka fara samun nasarar gabza musu naushi suka rinka hada musu JINI DA MAJINA har ma ka yanki kowannensu sau daidai jini yayi tsartuwa a jikinsu.Su ukun suka kurma ihu a lokaci guda sakamakon jin tsananin zafi da zogi,suka durkushe a kasa yayin da jiri ya kwashesu.Ai kuwa sai dodannin sukai caaa!izuwa kansu da nufi su dasa musu wawa su daddatsa su.Kwatsam ba zato ba tsammani sai su sarauniya Akisatul Sauwara sukaga bakon jarumi da danwada Dazyan sun faso karkashin kasa a tsakiyar dodannin suna masu kwalla KABBARA sun tarwatsasu da karfin tsiya kuma suka hausu da SARA DA SUKA ba sassauci.Nanfa jinin dodannin ya kama fallatsi a sama sassan jikinsu ya rinka shawagi a sararin sama yana zubowa kasa suna ruri da kururuwa suna zubewa kasa mattatu.Koda su Sarauniya Akisatul Sauwara suka ga dan wada Dazyan yana yaki da wadannan dodanni cikin gagarumar jarumtaka ta ban al'ajabi sai suka sake kamuwa da tsananin mamakinsu,saboda su dai a saninsu rago ne bashi da wata jarumta tunda a baya ma da suka shuga rintsin yaki kan bishiya ya haye ya buya saida aka gama yakin sannan ya sauko.Haka dai bakon jarumi da dan wada Dazyan suka cigaba da ragargazar dodannin nan suna cigaba da kwallah Kabbara har saida suka karar dasu gaba dayansu,ya zamana cewa babu dayansu daya tsira da rayuwarsa.A sannan ne Dazyan ya ruga wajen su Yarima Lubaimu ya kama duba raunikan dake jikinsu.Sa'ar da sukayi ma shine babu wanda rauninsa yayi zurfi saidai darewa kawai da yayi.Nan da nan cikin gaggawa dan wada Dazyan ya dinke musu raunikan aka saka musu magani.Bakon jarumi ya taho garesu ya bisu da kallo daya bayan daya yana maiyi musu sannu da hannu.Koda yazo kan sarauniya Akisatul Sauwara da nufin yayi mata sannu sai ta murtuke fuska ta daka mata harara kuma ta tari numfashinsa ta dubeshi cikin fishi tace,yanzu a haka kake nufin zamu cigaba da wannan tafiya duk sa'adda muka hadu da masifa saidai ku barmu da ita?Ai kafin mu isa ma can duk jikinmu ya lalace da raunika kuma raunikan ma zasu iya zama sanadin ajalinmu.Koda jin wannan batu sai shima bakon jarumi ya fusata ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,idan bakwason jikinku ya lalace ko kuma ku rasa rayuwarku to ku karbi Addininmu.Idan kuka karbeshi munyi muku alkawarin zamu roki ubangijinmu akan ya biya muk dukkan bukatunku muddin bukatun bazasu cutar da wani ba!Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai jikin sarauniya Akisatul Sauwara yayi sanyi sai kuma kunya ta kamata ta rasa abinda zatace.Shi kuwa Yarima Lubainu kansa na sunkuye ko kallon bakon jarumi baiyi ba.Sarki Darmanu kuwa ya bata rai sai muzurai yakeyi kawai.Nan dai aka samu aka huta har izuwa lokaci mai dan tsawo,sannan aka kafa sansani aka kwanta domin a kwana a wajen in yaso gobe da safe a cigaba da tafiya.Har dare ya raba Yarima Lubainu bai iya yin barci ba a cikin tantinsa shi kadai.Gashi dai ya kishingida amma zuciyarsa cike take da tunani da wasi wasi gami da fargaba.Yana cikin wannan hali ne yaga bakon jarumi tsulum ya shigo cikin tantin nasa.Cikin kaduwa da alamun tsananin mamaki Yarima Lubainu ya mike tsaye zumbur ya kurawa bakon jarumi idanu amma alamomin tsoro duk sun bayyana akan fuskarsa.Koda gin haka sai bakuwar jaruma ta dubeshi tace,kwantar da hankalinka yakai Yarima Lubainu,kayi sani cewa babu wanda zai ganmu ko yaji zancen da zamuyi a yanzu saboda nayi wata addu'a barcin kowa yayi nauyi hatta na Dazyan kuwa.Ba komai ne yasa ba kowa maka ziyara a cikin wannan dare ba face saboda na fahimci kana cikin damuwa da tashin hankali wadanda bazasu barka kayi barci ba.Ta gama fadin hakan sai ta cire rawaninta ta ajiye gefe daya kuma ta zauna nesa kadan dashi inda suka fuskanci juna.Koda yai arba da kyakyawar fuskarta sai yaji cewa inda zai rinka ganin wannan fuska to bazai sake yin bakin ciki ba a rayuwarsa har abada,kuma yunwa da kishirwa bazasu taba damunsa ba.Saboda kallonta ne zai hanashi jinsu ya sanyashi cikin farinciki mara misaltuwa.Har bakuwar jaruma ta budi baki zata ce wani abu sai Yarima Lubainu ya tari numfashinta yace,kafin kice komai ina rokonki da girman ubangijin musulunci daki fara sanar dani sunanki.Koda jin haka sai bakuwar Jarumar tayi murmushi tace,gaskiya banso na sanar dakai sunana ba yanzu sai a karshen tafiyarmu,a lokacin dazan bude fuskata da jikina kowa ya ganni,to amma tunda ka hadani da girman Allah dole ne na sanar dakai.Da farko sunana SUHAILAT IBINI AFUWAN,kuma na fito ne daga can wata nahiya dabam a wata kasa da ake kira DARUL ILMUN.Yanzu sai ka nutsu ka saurari fassarar mafarkinka.A takaice wannan mafarki naka yanayi maka nuni da cewar matarka Yazarina ta baro kasarku ta fito nemanka amma kuma ta fada hannun wani babban abokin gabarka wanda ke kokarin rabaka da ita.Saidai mafarkin bashi da karshe bare musan halin data shiga,walau abokin gabar taka ya kamata ko kuma ta tsira daga sharrinsa.Koda Suhailat tazo nan a zancensa sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya,ya mike tsaye zumbur da nufin ya ruga waje ya hau dokinsa ya tafi neman Yazarina,amma sai Sulailat tayi wuf ta ruko hannunsa a karon farko da hannunta ya fara taba wani 'da namiji ba muharramin ta ba.Cikin sauri ta saki hannun nasa tana mai istigifari a cikin zuciyarta sannan ta sha gaban Yarima Lubainu tace,ka kwantar da hankalinka yakai Angon Yazarina,kayi sani cewa da izinin ubangijina babu abinda zai sami matarka domin zan cigaba da rokonsa akan ya bata kariya kuma ya kareta daga sharrin wannan makiyi naka.A yau din nan zanyi istihara domin na ga halin da take ciki,kuma kafin mu cigaba da tafiya zan sanar dakai duk halin da take ciki.Abinda nakeso dakai kawai shine ka cigaba da rike alkawari na boye sirrina ya zamo amana a tsakaninmu.Koda gama fadin hakan sai Suhailta ta juya ta fice daga cikin tantin sai Lubainu ya kira sunanta ta waigo ta dubeshi cikin mamaki tace,mene ne?Nan fa Yarima Lubainu ya rasa abinda zaice da ita,dama bashi da abin fadar,kawai ji yayi baison rabu da ganin fuskarta gami dajin muryarta.Ashe Suhailat ta fahimci hakan,sai kawai ta dubeshi tayi masa murmushi mai dauke da alamar tambaya(?)tace saida safe.Take ta sake juyawa ta fice daga cikin tantin ba tare data sake waigowa ba.Kashe gari kuwa da sassafe jaruma Suhailat ta fito daga cikin tantinta ta iske Dazyan kwance a filin

Chapter 11 of 19