Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 1 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ YANA TAFE bisa wani ingarman doki sanye da tufafi na alfarma ya ratso ta cikin Birnin. Duk inda ya wuce saidai kaga jama'a nata kallonsa saboda kwararan dalilai guda uku. Dalili na farko shine,tufafin dake sanye a jikinsa wanda babu mai iya sanyasu face shahararren ATTAJIRI ko kasaitaccen BASARAKE mai amsa sunansa. Dalili na biyu kuma ya kasance kyakkyawan saurayi na kwatance wanda dole 'yanmata su yaba. Dalili na uku kuwa shine ya kasance GWARZON NAMIJI mai kirar sadaukai. Kash!rashin sani yafi dare duhu,inda 'yan mata sun san matsalar wannan kyakkyawan sauarayi da sunce akai kasuwa.Haka dai wannan saurayi yaci gaba da tafiya a cikin babban birnin da ya shigo mai suna RAUHUL BAHADAR yana tambayar hanyar da zata kaishi izuwa fadar birnin ana nuna masa harya iso. Fadace kasaitacciya ta gani ta fada domin an kashe dukiya mai yawan gaske wajen ginata.Kaida gani kasan cewa an shirya Aljannar duniya a cikin wannan gidan sarautar. SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA na zaune bisa karagar mulki fadawanta sun kewayeta kuma fadar ta cika makil da jama'a ana gudanar da harkokin mulki,sai ga wannan bakon saurayi an shigo dashi dakaru kimanin su goma na zagaye dashi don tabbatar da tsaro.Ba'a bari wannan bakon saurayi ya kusanci inda karagar take ba har saida aka je aka gaya mata cewar yazo ne yana son ganinta sannnan ta bayar da izinin a gabatar dashi,aka rako shi aka gurfanar dashi da tazarar kimanin taku goma a tsakaninsu da ita. Bayan dukkanin dakarun dake cikin fadar sun tsaida hankalinsu a kansa kuma sun dafe kufen takubbansu suna jiran ko ta kwana. Saurayin ya zube kasa bisa guiwoyinsa a gaban sarauniya Akisatul Sauwar cikin biyayya ya kwashi gaisuwa.Cikin murmushi da annuri fuskar Akisatul Sauwar ta karbi gaisuwar sannan tace,ya kai wannan bakon saurayi ma'abocin kwarjini mene ne ya kawika kasata kuma menene dalilin dayasa kake son ka gana dani? Lokacin da saurayin yaji wannan tambaya sai ya sake risinawa cikin ladabi yace,ya shugabata ni dai sunana YARIMA LUBAINU IBIN SALLUR.Mahaifin a shine Sarkin wani babban birni da ake kira ZAMRUL a can wata nahiya dake yammacin wannan nahiya taku. Ba wani abu bane yasa na baro kasarmu ba face neman inda kogin BAHAR IMFAL yake.Koda jin wannan batu sai gaba daya mutanen dake fadar suka bude baki suna kallonsa cikin tsananin al'ajabi kuma suna yi masa kallon mahaukaci. Ba komai ne ya janyi hakan ba face sanin cewa babu wanda zai bukaci zuwa inda kogin Bahar Imfal yake ba face wanda ya gaji da duniyar yake neman ajalinsa. Duk da cewar Yarima Lubainu ya lura da irin kallon da jama'a keyi masa a cikin fadar sai ya basar ya sake duban sarauniya Akisatul Sauwara yace,Na sami labari cewa akwai cikakken tarihin kogin bahar imfal a wannan masarauta taki. Akwai wani magani da nake so naje na samo a cikin kogin Bahar Imfal kuma bokaye sun tabbatar mini da cewa saina sami cikakken tarihin kogin idan ina son na sami nasarar riskar inda yake har ma na sami nasarar shiga cikinsa na debo maganin danake nema. Koda Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara da dukkanin fadawanta da sauran jama'ar dake cikin fadar suka bushe da dariya. Al'amarin dayai mutukar bashi mamaki kenan ya rinka kallon kowa da kowa. Daga can sai kuma sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tsuke bakinta ta hade fuska tana mai duba Lubainu a cikin nutsuwa tace,Yakai wanna dan Sarki kayi sani cewa abinda kake nema daidai yake da neman jaki mai kaho.Tabbas akwai tarihin kogon Bahar Imfal a cikin gidan sarautar nan,amma wani sashi ne daga cikin tarihin ba gaba dayansa bane. Mahaifina kafin mutuwarsa ya tabbatar mini da cewa duk abinda mutum yake nema a cikin Kogin Bahar Imfal ba zai sameshi ba face ya karance gaba daya rubutaccen tarihin kogin.Shidai wannan tarihi an rubutashi ne a jikin wani Allo wanda aka rabashi gida uku.Akan wannan Allo anyi yake yake marasa adadi,kuma milyoyin rayuka sun salwanta.A yanzu haka kaso daya na wannan Allo ne a hannuna,kaso na biyu yana hannun Sarki DARMASU na birnin Kimras. Daya kason kuwa na uku yana hannun wani takadirin boka wanda ake kira Da suna SARYANU IBINI DAUMUR. Lokacin da sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Hankalin Yarima Lubainu ya DUGUNZUMA ainun ya rasa abinda yake masa dadi a duniya,cikin alamun damuwa ya dubi Sarauniya yace,Ya shugabata mene ne asalin tarihin wannan Allo mai dauke da tarihin Kogon Bahar Imfal,kuma yaya akayi ya rarrabu har kaso uku? Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatu Sauwar tayi murmushi tace,zan baka amsar wannan tambaya taka amma nima sai ka gaya min maganin da kake son ka debo a cikin kogin Bahar Imfal. Dajin haka sai hankalin Yarima Lubainu ya sake dugunzuma fiye da farko ya kama kallon jama'a ya kasa cewa komai. Daga can sai ya dubi Sarauniya yace,yake wannan sarauniya mai adalci kiyi sani cewa kin tambayeni wani babban sirri na rayuwata wanda bazan iya sanar dakeshiba anan cikin taro.Lallai akwai bukatar mu kebe kuma bazan iya gaya miki sirrin ba face kinyi alkawarin taimakona bisa tawa bukatar.Sa'adda sarauniya Akisatul Sauwara taji wanna jawabi na Yarima Lubainu sai itama jikinta yayi sanyi ta rasa abinda zatace,tayi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku,dagan can kuma saita dago kai ta dubi Yarima Lubainu tace,akwai bukatar nayi tunanin da nazari zuwa gobe,yanzu zan saka a kaika masaukin ka. Kafin Yarima Lubainu ya gama rufe bakinsa tuni Sarauniya ta kirawo wani hadiminta ta umarceshi daya tafi da Lubainu izuwa masauki. Tana gama fadin hakan ta mike tsaye daga kan karagar mulkinta ta juya ta shige izuwa cikin gidan sarautar,dakaru da kuyangi na take mata baya ana buga tambura ana busa algaita. Lokacin da aka kai Yarima Lubainu masaukinsa sai aka karrama shi ainun aka kaishi cikin wani daki na alfarma wanda ya kawatu ainun kuma aka kawo masa irin abincinsu na alfarma. Bayan Yarima Lubainu yayi wanka ya huce yar gajiyar dake jikinsa saiya zauna domin ya ci wannan abinci.Koda ya dauko lomar farko yakai bakinsa sai tunanin gida ya fado masa,nan take idanunsa suka ciki da kwalla ya kamu da tsananin bakin ciki har hawaye ya zubo masa.Bisa ba komai bane ya fado masa a rai ba face tunowa da masoyiyarsa YAZARINA.... pls Like nd comments......ALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 2 A can birnin Zamral Yazarina ta kasance tauraruwar mata wacce babu kamarta a fagen kyau,kuma tun suna yara ita da Yarima Lubainu jininsu ya hadu sosai har suka fara girma suka kama soyayya.Rana tsaka Yarima MANGUL da ga Sarki Alkas dake mulkin kasar dake makwabtaka da birnin Zamrul yaga Yazarina ya rude kuma ya dimauce a cikin begenta da kaunarta.Bisa wannan dalili ne mahaifinsa sarki Alkasa ya taso da kansa yazo har Birnin Zamrul ya nemawa dansa auren Yazarina a wajen mahaifinta wanda ake kira da ABU YAZARINA.Shi dai Abu Yazarina ya kasance gawurtaccen Attajiri a Birnin Zamral wanda babu kamarsa a nahiyar,kuma duk sarakunan dake nahiyar abokan kasuwancinsa ne.Lokacin da Sarki Alkas yazo birnin Zamral ya kadaita da Attajiri Abu Yazarina sai ya dubeshi yace,ya kai tsohon abokina kayi sani cewa dana Yarima Mangul ya kyallara ido yaga 'yarka yayin da taje bikin cin kasuwar birnina wacce aka saba yi duk shekara.Ina mai sanar dakai cewa tun daga wannan rana sai Yarima ya susuce tamkar wanda ya zautu,ya zamana cewa dare da rana bashi da wani aiki face ambaton sunan 'yarka.Kai sai datakai cewa ya daina ci da sha face anyi masa hirar Yazarina an koda ta ana baiyana masa irin siffofinta.Yakai abokina nazone neman alfarmar ka amince a daura auren 'dana da 'yarka cikin gaggawa domin ina tsoron cewa 'dana zai iya rasa lafiyarsa ko rayuwarsa muddin bai mallaki Yazarina ba a matsayin matar aure Koda Sarki Alkas yazo nan a zancensa sai hankalin Attajiri Abu Yazarina ya DUGUNZUMA ainun domin an sashi cikin TSAKA MAI WUYA.Abu na farko dai Sarki Alkas da Sarki Sailur duk abokansa ne kuma aminansa tun yarinta,babu wanda zai nemi alfarma a wajensa ya hanashi.Abu na biyu shine ya san cewa 'yarsa Yazarina da Yarima Lubainu sun dade suna soyayya tun suna yara kuma ya sance cewa Yazarina tana tsananin son Lubainu rabata dashi ba karamin aiki bane.Bayan Abu Yazarina yayi tunani na tsawon 'yan dakiku sai ya dago kai ya dubi Sarki Alkas fuskarsa cike da dumbin damuwa yana mai ajiyar zuciya sannan yace,yakai abokina kayi sani cewa 'yata Yazarina da Yarima Lubainu sunfi shekara goma sha daya suna soyayya kuma gashi rana daya danka ya ganta yana SO.Ka da sarki Sailur aminaine kamar yadda muke nida kai kaga bana son abinda zai kawo lalacewar zumunci a tsakaninmu.Hakika na tausaywa danka mutuka bisa halin daya shiga saboda nasan illar soyayya gami da sharrinta domin kuwa kwatankwancin hakan ya sameni a lokacin danake neman auren mahaifiyar Yazarina.Abinda nake ganin za'ayi yanzu shi ka labartawa Sarki Sailur wannan al'amari? Koda jin wannan tambya sai Sarki Alkas ya gyada kai yace,kawai ce masa zanyi nazone akan harkokin kasuwancinmu nida kai.Abu Yazarina ya gyada kai yace,ba za'ayi haka ba domin nan gaba wani abu ya faru sai yayi zaton munyi masa duk munafunci.Abinda za'ayi yanzu shine ka tashi muje fada musa ayi mana iso a wajen sarki mu fito zahiri mu baiyana masa duk abinda ke faruwa dominmu hada basirarmu waje guda mu yanke hukuncin da zai fi dacewa bisa adalci.Ba tare da gardamar komai ba kuwa Sarki Alkas ya amince da wannan shawara.Na take Attajiri Abu Yazarina yasa aka fito da keken doki suka hau aka tafi dasu izuwa fada.Da isarsu fadar suka tura akayi mus iso a wajen sarki.Na take Sarki yasa aka shigar dasu har cikin turakarsa saboda aminci.Bayan sun gaisa sai Attajiri Abu Yazarina ya zaiyane masa koma dangane da abinda ya kawoso.Koda Sarki Sailur yaji jawabinsa sai shima Hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun fiye da nasu.Saida ya jima yana tunani har ya mike tsaye ya kama kai kawo yana ta tunanin mafita.Daga can kuma ya dawo ya zauna ya fuskancesu su biyun yace,ni inda tason raina ne zan iya tilastawa Yarima Lubainu akan ya hakura ya barwa Yarima Mangul Yazarina amma idan akayi masa haka ba ayi masa adalci ba tunda ya riga Mangul son Yazarina,asali ma sun shafe shekaru masu yawa suna yin soyayar.Ni a nawa tunanin shawarar dana yanke a cikin zuciya itace kawai a shirya musu gasa wanda ya lashe shine zai aureta.Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Alkasa dana Attajiri Abu Yazarina Ya DUGUNZUMA.Cikin kaduwa Abu Yazarina ya dubi Sarki Sailur yace,wace irin gasa kenan za'a shirya musu? Sarki Sailur yace,tunda dai duk su biyun sun kasance GAWURTATTUN JARUMAI masu TARWATSA MAZA a filin daga kawai suyi yaki da junansu wanda duk ya kashe wani Yazarina ta zama tasa.Kafin Sailur ya gama rufe bakinsa tuni Sarki Alkasa ya daka masa tsawa yace,ashe ka sami tabin hankali ban sani ba? Ta yaya zamu sa 'ya'yanmu suyi gasar kashe junansu akan soyayyar 'ya mace alhalin su kadai garemu? Na sani cewa a duniya babu abinda kake so sama da danka Yarima Lubainu kamar yadda nima nake tsananin son Yarima Mangul.Menene hujjarka ta yanke wannan hukuncin? Koda jin wannan tambaya sai idanun sarki Sailur suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa sannan ya dubi sarki Alkas yace,yakai abokina kayi sani cewa mutum na iya rasa 'da ya sami wani amma zumuncin daya kullu a tsawon shekara da shekaru a tsakaninmu idan ya zube ba zai taba debuwa ba har abada.Na gama yanke hukunci don haka ka koma gida ka shaidawa danka cewa idan har son da yake yiwa Yazarina na gaskiya ne to yayi shiri yazo nan birnin domin suyi gasar kashe juna nan da ranar karshe ta wannan watan,kaga kenan bai wuce kwanaki goma sha hudu ba masu zuwa.Ina maka fadan komawa gida lafiya.Koda gama fadin haka sai Sarki Sailur ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ya barsu su biyu a zaune cikin tsananin kaduwa da mamaki.Nan dai suma suka mike tsaye jikinsu a sanyaye suka fice daga cikin turakar....Like nd comments pls 10 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 3 Da la'asar sakaliya Sarki Sailur ya tura aka kirawo Yarima Lubainu suka kadaita a wani wuri na musamman acikin gidan sarautar inda sarke ke shakatwa.Bayan Yarima Lubainu ya zube kasa a gaban sarki Sailur ya kwashi gaisuwa sai sarki ya dubeshi fuskarsa a daure yace,yakai dana kayi sani cewa kai ba rago bane,kuma baka kasance matsoraciba.Baya ga haka ban taba umartarka dayin wani abu ka kasa yi ba,saboda haka yanzu na shirya gasar yaki tsakanin da Yarima Mangul akan soyayar da kuke yiwa Yazarina.Wanda duk ya sami nasarar kashe wani a cikinku shine zai auri Yazarina.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya cika da tsananin mamaki kuma hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun ya dubi sarki cikin kaduwa yace,yakai Abbana ina dalilin yanke wannan danyen hukunci dakayi? Koda jin wannan tambaya sai sarki Sailur ya kwashe duk abinda ya faru tsakaninsu dasu Attajiri Abu Yazarina da kuma hujjarsa ta yanke wannan hukunci.Dajin haka sai jikin Lubainu yayi sanyi yayi shiru izuwa tsohon 'yan dakiku,daga can sai kuma hawaye ya zubo masa yace,yakai Abbana kayi sani cewa Yarima Mangul abokinane tun yarinta bazan iya kashe shi ba da hannuna amma kuma ba zan kaucewa umarninka ba.Lallai zanyi wannan gasa.Koda jin wannan batu sai Sarki ya fusata ainun ya dakawa Lubainu tsawa yace,idan har kaki yin wannan yaki da dukkan karfinka da jarumtakarka a bakacin auren mahaifiyarka!Yana gama fadin haka ya mike tsaye yayi tafiyarsa yabar Yarima Lubainu a zaune cikin tsananin damuwa da tashin hankali saboda yasan halin mahaifin nasa baya magana biyu.Saida Yarima Lubainu ya dade a zaune a wannan wuri yana kukan takaici.Yana cikin wanann hali ne yaji an dafa kafadarsa ta baya.Cikin firgici ya waigo da sauri kawai sai yaga she mahaifiyarsa ce ZUHAIMA tsaye a kansa tana zubar da hawaye.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya mike tsaye suka rungume juna kuma suka cigaba da kuka tare.Daga can sai Zuhaima ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna ta dubeshi cikin nutsuwa da murmushi tace,yakai 'dana na sanka tun kana yaro karami duk abinda kasa a gabanka saikayi nasara.Nasani cewa ko kadan baka sin yin wannan gasa da abokinka Yarima Mangul amma ya zama dole kayi ta tunda baka da wani zabin.Lallai kayi wannan gasa da dukkan karfinka da jarumtakarka kamar yadda mahaifinka ya umarceka domin bana son na rasaka.Idan kuwa na rasaka nima bazan dade ba a cikin wannan duniya.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya kara kankame jikin Zuhaima yacigaba da kuka yana mai cewa lallai bazan yadda ki rasani ba domin nafi kaunarki fiye da komai a wannan duniya hatta Yazarina kuwa.Wannan shine abinda ya faru a birnin Zamral. ¤¤¤••••••••••••••••••••¤¤¤ A can birnin DARUL HUNZUL kuwa lokacin. da sarki Alkas ya isa gida sai ya kirawo Yarima Mangul da mahaifiyarsa tare da dukkan fadawansa ya sanar dasu irin hukuncin da sarki Sailur ya yanke bisa neman auren kyakkyawa Yazarina dayaje nemawa Yarima.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma ainun shi kuwa Yarima Mangul farinciki ne ya lullubeshi ya kama ihu da murna domin yana ganin cewa tamkar ya mallaki Yazarina ne.Duk dacewa yana kaunar Yarima Lubainu tsawon shekaru amma a yanzu sai yaji ya tsaneshi kamar yadda ya tsani mutuwarsa.Daga wannan rana Yarima Mangul ya shiga shirye shiryen tafiya wannan kasa ya zamana cewa kullum da safe da yam2tnma a cikin baiwa kansa horon yaki yake kuma ya rinka ziyartar bokaye suna bashi sa'a gami da mugayen lakanunnuka don ganin bayan Yarima Lubainu.Daga cikin bokayen ne aka sami wani gawurtacce kuma maketacin gaske wanda ya baiwa Yarima Mangul wani sihiri yace dashi koda Yarima Lubainu ya sami nasara akanka to har abada shima bazai taba sani Yazarina 'Ya Mace ba.Abinda zakayi kawai shine kafin ku fara gasar ka tabbatar da cewa ka bashi hannunka kun gaisa.Na take bokan ya kama hannun Yarima Mangul na dama ya fidda wani garin magani ya shafa akan tafin hannunsa,sannan yace da zarar hannun Yarima Lubainu da hannunka sun hadu shikenan ya rasa darajarsa ta 'da namiji domin bazai sake jin sha'awar mace ba kuma bazai iya zaman aure ba,kaga kenan shi da mace duk daya.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta yace,da kyau yakai boka Mugaru hakika ka bani babban abin dogaro wanda ko dana mutu a wannan gasa bani da wata nadama ko bakin ciki amma inda tambaya guda daya.Naji daga bakin bokaye da yawa cewar dukkan cuta tana da magani.Menen makarin wannan sihiri dazan yiwa Yarima Lubainu?Fatana shi ne idan ya cinye ni a wannan gasa ya karasa rayuwarsa a cikin wannan hali har abada.Koda jin wannan tambaya sai boko Mugaru ya bushe da dariyar mugunta sannan yace,ai nemo makarin wannan sihiri daidai yake da mutum ya tafi FARAUTAR AJALINsa domin dole ne yaje kogin Bahar Imfal yayi nutso a karkashinsa ya tsunko tsuron wata itaciya ta aljanu da ake kira Saumul Asraru.Har yau har gobe babu wanda yasan a inda kogin Bahar Imfal yake walau a cikin mutane ko aljanu sannan kuma babu mahalukin da ya isa ya gano inda kogin yake har sai ya sami damar zuwa wajen ya shiga cikinsa face ya hada ALLON SIHIRI wanda aka rabashi gida uku.Hada wannan Allon Sihiri daidai yake da neman jaki mai 'kaho ko kuma ince mutum ya tunkari gaba dayan mutanen wannan duniya da yaki,saboda wadanda ke da mallakin allunan sunfi wuta zafi kuma sunfi ruwa sanyi.Mutum na farko mao rike da bari guda na allon Sarauniya Akisatul Sauwara ce mai mulkin Birnin Rauhul Bagadar.A yanzu haka wannan barin allo yana nan a ajiye a gidan tarihin Birnin cikin wata akwatun gilashi ta sihiri.Duk duniya babu wanda ya isa ya bude wannan akwati face Sarauniya Akisatul Sauwara ko Kuma Wanda ya gaji sarautar ta Wanda ya kasance jin in gidan......pls Like and comments is necessaryALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 4 Mutum na biyu mai mallakin barin Allon shine Sarki Darmasu na birnin Kimrasa,sai kuma barin Allo na uku dake hannun boka Saryanu Ibn Daumur.Karbar wadannan barikan alluna guda uku a hannun wadannan mutane daidai yake da tashin matacce ya zama rayayye saboda kowanne a cikin bashi da burin da yafi ya sami ragowar barikan biyun da nashi dasu ya hada nasa domin zama sarkin duniya,ya kasance komai da kowa na karkashin mulkinsa.Lokacin da boka Mugaru yazo nan a zancensa sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta.Nan take ya kawo alheri mai yawa ya baiwa boka Mugaru sannan sukayi sallama ya tafi. Daga sannanne Yarima Mangul ma ya dage da baiwa kansa horon yaki dare da rana kafin cikar lokacin ranar gasar ya gama shirinsa tsaf.Na take kuwa yayi shiri shi da mahaifinsa Sarki Alkas suka durfafi Birnin Zamral tare da dakaru masu yawa suna take musu baya. Ba isowarsu Birnin Zamral suka iske cewa garin ya cike makil da baki daga kowanne bangare na nahiyar. Ba komai ne ya haddasa wannan cikowa ba face anzo kallon gasar kisan juna da za'ayi tsakanin Yarima Mangul da Yarima Lubainu kan kyakkyawa Yazarina.Kai tsaye sarki Alkas tare da dansa yarima Mangul suka wuce fada.Tun kafin su karasa sarki Sailur ya fito kofar fadar ya tsaya tare da fadawansa suna jiransu. Ai kuwa da zuwansu sai Sarki Sailur ya karbesu cikin tsananin farinciki ya rungume sarki Alkas yana mai cewa lale marhaban da babban abokina.Hakika nayi mutukar farinciki dakuka amsa wannan gaiyata tawa. Abinda ya daurewa su Yarima Mangul kai shine basu ga Yarima Lubainu ba a wajen taryarsu.Nan take sarki Sailur ya kama hannun Sarki Alkas ya jashi izuwa cikin fada inda aka zauna gaba daya tare da dukkan jama'arsu.A sannanne kuyangi da hadimai sukai ta kawo abinci,ruwan inibi,ruwan sha kowa ya kimtsa kansa ana ta hira da dariya masu shewa nayi saboda santi. A wannan lokaci Yazarina da Yarima Lubainu nacan a zaune cikin lambun gidan attajiri Abu Yazarina suna hira irin ta ma'abota soyayya inda Yazarina ta dubi Lubainu a lokacin da hawaye ya zubo mata tace,yakai masoyina kayi sani cewa tun daga ranar dana sami labarin wannan gasa da mahaifinka ya shirya na rasa sukuni kuma na kasa yin bacci a kullum idan na kwanta akan gadona,har ya zamana cewa ina tayin mugayen mafarkai akan wannan gasa da zakuyi don haka ko yaushe zuciyata a cikin bugawa da karfi take.Bani da abinyi sai kuka saboda fargabar zuwan wannan rana gashi kuwa rana bata karya saidai uwar 'ya taji kunya tunda gobene za'ayi wannan gasa. Lokacin da Yazarina tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi murmushi kuma yasa tafin hannunsa biyu ya share mata hawayen a lokacin da ya dago habarta suka dubi juna yace,ki kwantar da hankalin yake abar kaunata kiyi sani cewa nine da nasara a cikin wannan gasa lallai da izinin gunki Salhat babu abinda zai sameni. Koda jin wannan batu sai Yazarina taji dan sanyi har murmushi ya subuce mata amma sai ta sake hade rai ta dubi Lubainu cikin alamun damuwa tace,yakai masoyina waishin menene dalilin da yasa mahaifinka ya shirya wannan gasa ne alhalin na tabbatar da cewa yana tsananin kaunarka fiye da komai.Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Yazarina yace,sau tari sarki yakan dannen son zuciyarsa domin ya nemawa kansa martaba da kima a idanun talakawa.Wannan shine abinda ake kira sarauta,kuma shine abinda sarki yayi domin ya kawar da rashin jituwa tsakaninsa da tsohon abokinsa kuma ya kawar da tsegumi da kace nace tsakanin al'ummar kasashenmu.Idan kin Fahimci wannan bayani nawa zaki gane cewa sarki yayi daidai bisa wannan hukunci daya yanke.Lallai ina son ki kwantar da hankalin kawai ki cigaba da yimin fatan sa'a da nasara.Haka dai Yarima Lubainu Da Yazarina suka cigaba da hira har izuwa lokacin mai tsawon gaske . Da zarar yayi mata sallama zai tafi sai ta bijiro masa da wata sabuwar hirar da hillatar da zance mai dadi saboda bata son su rabu.Yarima Lubainu dai bai ankaraba sai gani yayi dare ya soma kuma gashi yana son yaje yayi shirin karshe na gasar fadan da za'ayi gobe.Kawai sai ya mike zumbur ya ruga waje da gudu yana mai cewa sai gobe da safe su hadu a filin fada wajen gasa.Yazarina ta bishi da kallo kawai tana mai zub da hawaye cikin tsananin fargabar ganin wayewar gari,domin babu abinda ta tsana sama da wannan gasa da za'ayi da Yarima Mangul saboda da gasa ce wadda babu wanda yake da yakinin ya fadi zakaranta.Har Yazarina ta juya zata koma izuwa bangaren da turakarta take sai ta hango mahaifinta ya shigo cikin gidan tare da wani bakon mutum ma'abocin haiba da kwarjini a cikin shiga ta kamala.Ga dukkan alamu dai bafatake ne.Cikin biyayya Lazarina ta risina ta gaishe da bakon a sannane Abu Yazarina ya gabatar da bakon nasa a gareta yace,Wanna shine Abdul Nasiri Ibn Hamza daga birnin Misra.Mai gidana ne a kasuwanci domin shine mutum na farko daya fara aminta dani yabani tsabar kudi dinare dubu dari a rayuwata,kuma wannan kudi daya bani sune silar arzikina da nake kai yanzu.Koda jin wannan batu sai Yazarina ta sake dukawa cikin girmamawa tayi gaisuwa a karona biyu.Cikin murmushi attajiri Abdul Nasir ya dubi Yazarina sannan yadubi Abu Yazarina yace tabbas kyan 'da ya gaji ubansa,hakika wannan yarinya tana mutukar kama da kai.Koda jin wannan batu sai Attajiri Abu Yazarina ya bushe da dariya yace,Hakika kayi gaskiya mai gida.Na take Abu Yazarina

Chapter 1 of 19