Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ku rinka tunanin lahirarku. Nagode sosai." Daga haka ta lallaba ta karasa bakin gate din. Wannan karon sai da Gaddafi yayi da gaske Annur ya ja motar suka tafi. Kasa daga kafarta tayi taji kamar zata fadi wata mata mai uniform din masu shara da wanke bandaki ta tareta daga baya tana yi mata sannu. Daga nan bata san da yadda aka shigar da ita asibitin ba. Ko awa daya bata cika ba Allah Ya taimaketa ta haihu. Tana jin wannan kukan na jarirai taji gabadaya damuwarta ta gushe burinta kawai taga abinda ta haifa. Nurse din da ta karbi haihuwar tace mata kin sami 'ya mace. Asmau tayi murmushi tare da dago kai ta kalli kyautar da Allah Yayi mata tana hamdala. Gata da 'yar Abubakar sai dai babu shi kuma babu iyayensu. Kaddara ta riga fata a kansu. Ba don haka ba da yanzu iyayensu za'a mikawa jaririyar. A wani dan zani aka nade 'yar aka miko mata. Ta zuba ido tana kallonta. Sai kuma kuka ya kwace mata da ta tuna bata da wata hanyar kulawa da 'yar. Ko suturar da zata saka mata bata da ita. Wannan mai sharar tayi mata Allah Ya raya sannan ta fita daga dakin. Ba jimawa ta dawo da wasu tsofaffin riga da zani amma a wanke ta bawa Asmau fuskarta a sake. "Ga wannan akwai ruwa a bandaki ki gyara jikinki sai ki saka. Idan kin fito sai ki fadi wa za'a kirawo a danginki." Asmau kamar kada ta bata yarinyar haka take ji. A rayuwarta bata taba son wani kamar yadda take jin son jaririyarta ba. Tayi godiya ta karbi kayan ta wuce bandakin. Bata dade ba ta fito aka kaita dakin hutu. Wani likita yazo ya dubata yace babu wata matsala amma sai da safe zasu sallameta. Ya bata takardar magungunan da zata siya. Bayan fitarsa mai sharar ta kara dawowa wurinta ta sake tambayarta ina 'yan uwanta saboda a bakin gate ta ganta ita kadai. Ya kamata a sanar dasu ko don su kawo mata abinci da kayan baby. Asmau bata da amsar da ta wuce kuka. Matar sai ta kyaleta ta koma bakin aikinta. Ita kuma ta cigaba da kallon jaririyarta tana bacci. Ikon Allah, yarinyar kama take yi da Mama Yalwa. Asmau sai ta rantse duk 'ya'yan Mama babu mai kama da ita kamar wannan yarinyar. Dama duk sunfi kama da Alh Adamu. Da namiji ta haifa dama sunan Abubakar zata saka masa. Amma tunda mace ce zata saka sunan mahaifiyarsa kamar yadda suka yiwa juna alkawarin sai sun sakawa 'ya'yansu sunayen iyayensu. Da wannan tunanin ta danyi murmushi. Babbar matsalarta yanzu bata san ta ina zata fara ba? Bata da komai bata da kowa. Sannan bata san irin tarbar da za'ayi mata ba idan ta koma gidansu. Wannan tunanin ya isheta ga kudin asibiti duk da na gwamnati ne tasan ko yaya za'a bukaci ta biya kudin wani abin. Hakan ne yasa tana ganin duhun dare yayi ga cikinta kamar anyi mata yasa don yunwa ta kwance dankwalinta ta goya jaririyar da shi sannan ta zura hijab dinta tayi waje. Gara ta gudu tun kafin ace ta kawo kudin da tasan bata da su. Ta kusa karshen barandar da zata kaita bakin gate ne taji muryar mai sharar nan tace "ba dai guduwa zakiyi ba". ***** Hajjo ce ta farka daga bacci a gigice ta rinka juyi akan gado har ta tabbatar dai a dakinta take. Hawaye ne kwance a fuskarta sakamakon mafarkin da tayi da jikarta Asmau. Kuka ta ganta tana yi tana kiran Hajjon da ta taimaketa. Duk yadda taso ta kama hannun Asmau ya gagara har ta farka. Jikinta sai karkarwa yake ta tashi ta dauko mayafinta a gefen kujerar dakin ta tafi dakin Garzali. Ko agogo bata duba ba tayi sa'a ta same shi yana fesa turare da alama fita zaiyi. Tsayuwar kirki ta kasa cikin tsawa tace yazo ya kama karnukansa zata fita. "Hajjo ina zaki je da yamman nan. Biyar da rabi fa". Harararsa tayi fuska a murtuke don kada ya kawo mata wargi "inda ka aike ni zani. Kaga kada ka bata min lokaci wuce muje". Suna fitowa yayiwa karnukan fito suka yo kansa Hajjo ta samu ta fice. Don sauri kafarta har zafi take yi mata taji takun mutum kamar ana binta da gudu. Duk da a tsorace take haka ta dake bata juya ba take magana "Rabe wallahi yau ko me zaka ce sai naje wurin Bara'atu. Ba kai ka haifa min Shu'aibu ba shiyasa baka san ciwon iyalinsa ba." Garzali yayi yar dariya "Ni ne Hajjo. Raka ki zanyi. Nima rashin mu'amala dasu ba karamin damuna yake yi ba." Tayi murmushi "Allah Yayi maka albarka" daga nan ta bashi labarin mafarkin Asmau da tayi suna tafiya. ***** Tun kafin azahar Zubaida ta iso garin Kano ta samu mai tasi suna ta yawo a unguwar Hotoro basu gane gidan ba. Gajiya yayi ya sauketa bayan ya karbi dubu biyu a hannunta. Har zai tafi sai ya dawo saboda ta bashi tausayi yace ta sami mai adaidaita sahu sunfi sanin layukan cikin unguwa. Tayi sa'a kuwa ta sami wani ta fada masa inda take nema. Da ya kula bakuwa ce a garin ya tsula mata kudi sai dai bata damu ba. Biyan bukata yafi dogon buri. Kusan dubu talatin ta dauko a cikin kudin da Uwargida ta bawa Yaya Babba. A cikin layin mai adaidaita sahun ya nuna mata gidan kwamishina. Tayi masa godiya ta bashi kudinsa. Daga nan tasan Asmau tace gidansu babu nisa. Wata tsohuwa ta hango da wani mutum a bakin gate din wani gida tayi saurin karasawa kafin su shiga. Sallama ta rinka yi musu suka juya suna kallonta a tare. Riga da siket ne a jikinta sun dameta sosai ga katuwar jakar kaya sai wani siririn mayafi da ta rataya a wuya. Da murmushi a fuskarta ta dan rissina ta gaishesu sannan tace "don Allah gidan Umma nake nema. Umman Asmau". Garzali ya sake kallon Zubaida sannan yace "nan ne". Ko jiransu batayi ba ta shige ciki tana kwalawa Asmau kira. Yassar da yake shanya ne ya fara ganinta bai san lokacin da ya saki wandon da yake kokarin dorawa a igiya a kasa ba ya nufota. Zubaida na ganinsa ta saki murmushi. "Tabbas nan ne gidan don naga kamarku. Kai ne Yasir ko?" Kallon rashin sani yake mata yace "a'a sunana Yassar" Zubaida tace "hakane kaini wurin Asmau". Hanyar falon ya nuna mata sai ya kula da Hajjo da Kawu Garzali. Har dan tsorata yayi sai yaga Hajjo tana hawaye "Zo nan Yassar, zo naji duminka a jikina" Ji yayi kamar mafarki yake ya fara tunanin gudu Garzali ya damko wuyan rigarsa ya hada shi da jikin Hajjo. Kuka ta fashe dashi na takaicin yadda jikanta yake nuna tsoro da fargabar ganinta har yana neman gudu. Tana rike da hannuwansa tace "kuyi hakuri Yassar. Ku yafewa wannan tsohuwar". Shima kukan ne ya zo masa ya kankameta. Ashe akwai ranar da Hajjo zata nuna masa so? Tana rike da hannunsa suka shiga cikin falon. Umma suka gani da Aina'u da kuma Jafar sun saka Zubaida a gaba suna kallonta jin tace daga Azare tazo wurin Asmau. ABINDA AKE GUDU🙆🏽25 Batul Mamman💖 Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai biyoni mu koma ciki". Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin albashinta. Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya. Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan." Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare. Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da yaso kwarai ta kai washegari. Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya nazo muje gidana tunda dare yayi". Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda babu ta dauko tabarma ta shimfida mata. Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh. Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora" Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki. Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi. Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda suka yi masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane. Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace " Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara kuka". Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon. Wata dattijuwa ce rike da wani mutum yana ta tangal tangal kamar zai fadi. Daga bakin kofa ta tsaya tana jifan Zulaiha da harara "yau kuma wani sabon iskancin ne ya tashi kina jina ina fama da Gidado bazaki zo ki taimaka mu kaishi daki ba?" Idonta ne ya sauka akan Asmau ta daure fuska "Wannan kuma fa, daga ina?" Zulaiha tana saka hannuwan mutumin a kafadarta tace " 'yar haya na samo dazu a asibiti. Zata karbi hayar daki daya a gidan nan, kinga kudin ko cefane sai mu kara dashi". "Cefanen banza, ni zan rinka karba ina karawa a jari na." Asmau ta dan duka ta gaishe da matar ko kallonta bata yi ba ta fara tambayar ina abincinta. Shi kuwa mutumin da Zulaiha ke ja surutai yake marasa kan gado. Da suka zo wucewa ta gabanta wani irin wari yake fitarwa. A falon ta jira Zulaiha ta kaishi daki sannan ta nuna mata wurin da zata kwana. Tana kwance rungume da 'yarta tana jin wannan dattijuwa tana masifar anyi kaza anyi kaza ba daidai ba. Can kuma taji mutumin wanda ta tabbatar mijin Zulaiha ne ya soma zage zage bata bashi abincinsa ba zata kashe shi da yunwa. Har Asmau tayi bacci babu abinda take ji yana fitowa daga bakin Zulaiha sai "kuyi hakuri". ***** A can Kano kuwa lokacin da Yassar ya shigo ciki rike da hannun Hajjo sai da gaban Umma ya fadi. Aina'u tayi saurin labewa a bayan Umma a tunaninta daukarsu tazo yi. Hankalin Umma ya bar Zubaida ya koma wurin Hajjo. Cikin sanyin jiki ta gaisheta sai dai sabanin da sai taji Hajjon ta amsa cikin kuka. Har inda Umma ke tsaye taje ta kama hannuwanta tana hawaye "Bara'atu nasan ke mai hakuri ce da kawaici. Ki dubi girman Allah ki yafewa wannan tsohuwar banzar hakkinku da ta dauka." Umma ta saki baki cike da mamaki. Me kunnenta yake jiye mata ne? Hajjo ta cigaba da magana tana kuka "nayi nadamar abinda nayi miki tsahon shekarun nan. Ni kaina bansan dalilin yin hakan ba. Bakiyi min komai ba na dora miki tsana da tsangwama." "Alhamdulillah" Umma ta fada a fili itama da nata hawayen. Hajjo ta cigaba da rokon gafara Umma tace ai zuwanta kadai yasa komai ya wuce. Hajjo ta mika hannu "zo nan autar Bara'atu. Taho wurin kakarki kinji 'yar albarka. Jafaru baka ce komai ba. Ku yafeni ko don darajar babanku" A darare Aina'u ta matsa jikin Hajjo. Garzali ma a kunyace ya gaishe da Umma ta amsa bakinta yaki rufuwa don murna. Jafar ma murna yake yi sai dai hankalinsa yafi karkata ga Zubaida dake tsaye tana kare musu kallo. Sai da aka dan sami nutsuwa a falon sannan Jafar yace "Umma bakuwar nan fa tana jiranki" Hakuri Umma ta bata ko wurin zama basu bata ba suna farincikin fara daidaituwar al'amuran danginsu. Aina'u ta kawowa Zubaida lemo da abinci tana ci suna kallonta. Jira suke yi ta gama ta fada musu abinda ta sani game da Asmau. Da ta gama ne Umma ta fada mata Asmau tayi wata bakwai rabonta da gida. Zubaida ta dan cije lebe fuskarta ta nuna rashin jindadi "nayi tunanin gida da dawo da na koma aka ce min bata nan. To ina ta tafi?" Hajjo tace "kinga yarinya, bayani zakiyi mana yadda zamu fahimceki sosai. A ina kika ga Asmau'un?" Zubaida ta fada musu komai game da zamansu da Asma'u. Umma da Hajjo sai kuka jin Asmau ta zauna a gidan karuwai. Tace hatta yadda ta sami cikin duk ta fada min. Umma ta share hawaye "Ta fada miki sunan wanda yayi mata cikin?" "Eh tace sunansa Abubakar". Umma ta toshe bakinta da hannu tana wani kukan. Dama Qasim ya tabbatar musu cikin Abubakar ne amma basu bawa wacce abin ya shafa damar bayani ba. Yassar ta nuna "tashi maza kaje ka kira Mama Yalwa. Ka fada mata bakuwa ce tazo daga Azare wadda tasan Asmau". Ba'a dade ba sai ga Mama suka zauna Zubaida ta fada musu duk labarin da Asmau ta bata na waya da yadda al'amarin ya cigaba. Falon sai salati suke yi ana jimamin wannan abu. Ace tarbiyar shekara da shekaru wasu can da basa kishin addini suyi ta fito da samfurin yada alfasha salo salo suna turawa 'ya'yan musulmi. Hajjo tace "to shi shegen giruf (group) din aje a tarwatsa mana kowa ya huta. Haka kawai an janyowa marainiya fadawa mummunar rayuwa. Kada na kaiku da nisa ko mu da babu waya a zamaninmu waye ya koya mana yadda ake yi tsakanin mata da miji. Gashi mun rayu dasu cikin kwanciyar hankali mutuwa ce ta raba. Duk wannan shaidancin kuma da ake yadawa ai bai hana mutuwar auren yara kanana ba." Mama da batasan yadda akayi Hajjo ke nuna damuwarta akan Asmau ba tace " ai group din a waya ake bude shi. Ni abinda ya fi damuna bai wuce yadda zakiga yara da matan aure a dauki waya tun safe har dare ki rasa me ake gani. To ashe duk harkar lalacewa ce duk da dai ana samun karuwa ta wani fannin. Yaranmu da sunyi waya sai kiga basu da lokacin komai sai nata." Zama sukayi ana ta mayar da zance kowa na tofa nasa. Kawu Garzali a fusace yace "ita wacece wannan Walidar ne? Tayi fatan kada mu hadu don wallahi sai nayi mata rauni. Kawaye da abokan banza sunfi saurin lalata tarbiya. Ni ba daga abokin bane muka kare a haka." Ya dubi Jafar da Yassar " yanzu kuna da uba saboda haka duk yaron da na gani baiyi min ba kafin na kore shi ta kanku zan fara". Umma tayi murmushin jindadi. Duk da tasan Garzalin kansa baya sahun mutanen kirki amma dai taji dadin kulawarsa ga 'ya'yan dan uwansa. "Walida kawar Asmau ce tun primary. Kuma itama nata mahaifin yana kokari. Don ranar da abin ya faru kafin mu dawo daga asibiti yazo ya dauketa." Hajjo taja tsaki wanda har Zubaida da Aina'u sai da suka yi dariya "anyi ta baya ta rago. Shi da 'yarsa ta bata ta wani ai ya jira nasa lokacin. In Allah Ya yarda sai ta dauko masa abin...." Mama da Umma suka dakatar da Hajjo daga yin mummunar addua. Daga nan suka yanke shawarar washegari da sassafe zasu tafi Azare neman Asmau. Anti Bintu da Shemau duk an sanar dasu haka Abdulhalim da Qasim. ***** Annur da Gaddafi tunda suka isa masaukinsu ko abinci sun kasa ci. Abokin da suka zo wurin party dinsa yayi ta damunsu da su tashi suyi wanka a tafi sai su kalli juna su sunkuyar da kawunansu kasa. Gabadayansu dana sanin baro gidajensu suke yi. Sun baro iyayensu musamman matan cikin tashin hankali domin sun san yanzu ana nan ana nemansu. Yau da suka ga yadda mace ke wahala wurin haihuwa kowannensu shiriya ta saukar masa. Sannan ga adduar da tayi musu bayan taimakonta da suka yi. Suna kallo aka shirya duk 'yan samari sa'aninsu suka fice sai su kadai. Karshe ma shawara suka yanke gobe zasu koma asibitin neman wannan matar daga n [truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽26 Batul Mamman💖 Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi "Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba". Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa. "Wane suna zaki saka mata?" Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani. "Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne". Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?" "Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu." Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi. "Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki". Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa. "Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu". Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa. "Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?" Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi." Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?" Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa. Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki." Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"? "Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri." Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan. Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin. "Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar. A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba." Zulaiha ta share hawaye "A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya." A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai "Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan." Asmau taji tausayin Zulaiha sosai. "Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya" "Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri". Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba. ***** Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho. Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan. Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau." Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?" "Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa. Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya

Chapter 9 of 23