Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jiya. Asmau tayi murmushi mai ciwo sannan ta fara sanar da Zubaida dalilin watsewar farincikinta. *FARKON LABARI* Alh Shu'abu Yahaya sunan mahaifinsu Asmau. Iyayensa duk 'yan Kano ne kuma a nan cikin Kanon suka tashi. Su biyar ne a gidansu shine na biyu. Babbar yayarsa suna kiranta Yaya Abu sai shi sannan mai binsa Rabe sai Lami da Garzali. Babansu mazan kawai yake sawa a makaranta. Saboda haka Shu'aibu yayi karatu har matakin digri inda ya karanci Agric Science harkar aikin gona. Shi mutum ne mai saukin kai da kirki shiyasa mahaifinsu yake ji dashi. Sauran 'yan uwansa kuwa kusan duk halin Hajjo mahaifiyarsu suka debo na fada da sa ido. Lokacin bautar kasa aka tura shi makaranta a wata karamar hukuma a jihar Niger mai suna Wushishi. A can ya hadu da Bara'atu tana ajin karshe na sakandire. Farkon haduwarsu duk da baya koyar da 'yan ajinsu soyayya ta kullu a tsakaninsu. Abu kamar wasa har lokacin komawarsa gida yayi inda yayi mata alkawarin turo iyayensa. Dama a hannun kawunta take ita da kanwarta Bintu marayu ne ko kadan basa jindadin zama da matar kawun. Da ya koma Kano ya sanar da iyayensa Hajjo ta dage indai tana da rai danta bazai auri banufiya ba. Duk 'yan Niger mayu ne a cewarta. Ita a son ranta ya auri 'yar kanwarta. Akayi ta jan zance ita da mahaifinsu shi kuma ya dage Shu'aibu sai ya auri wadda yake so. Rigima sosai akayi sai bayan wata biyu iyayensa suka je Wushishi. Lokacin Bara'atu har ta fitar da rai. Ba wani dogon lokaci aka saka bikin ba gashi ko aiki bai fara ba. Wurin hada lefe yasha wahala Bara'atu ta bashi kudi cikin kudin gadonta ya cika ya siya mata kaya masu kyau. Haka aka yi biki aka kawo amarya Kano ita da kanwarta Bintu saboda bazata iya barin kanwar a hannun matar kawunsu ba ta cigaba da azabtuwa. Wani bangare aka gyara musu a cikin gidan iyayensa suka tare a ciki. Zaman lafiya sosai suke yi da mijinta sai dai a wurin Hajjo da 'yan uwansa tana ganin wulakanci mara misaltuwa. Daga ita har kanwarta basu da sunan da ya wuce Mayya. Gashi dama duk suna da idanuwa Tubarakallah. Duk wani aiki na gidan ya dawo wuyansu amma bata taba korafi ba. Kullum Shu'aibu sai dai ya bata hakuri lokacin yana ta fafutukar neman aiki. A haka ta samu ciki har sau uku yana barewa saboda aikin wahala. A karo na ukun ne da safe Hajjo ta shigo taga Bara'atu bata sha kunu da kosan da ta aiko mata dashi ba wanda babansu Shu'aibu ne ya tilasta mata dama. Fuska babu walwala tace "Au baku karya ba har yanzu saboda ki jawo min fada wurin Malam yace bana kula dake?" Daga kwance inda take saboda rashin kuzari Bara'atu tace "Kiyi hakuri na koshi ne". Hajjo tayi dariya "yo ba dole ki koshi ba, kunyi kalaci da jikana ke da kanwarki. Ai Shu'aibu ya gama janyo mana masifa. Nan gaba kadan ma mu zaku bi ku lamushe." Bayan ta gama fadanta ta fita Bara'atu babu abinda take yi sai kuka. A wannan yanayin Shu'aibu yazo ya sameta. Hakuri ya bata kamar kullum tare da kyakkyawan albishir na cewa ya sami aiki a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a matsayin lecturer matakin farko. Kuma har da gida aka bashi. Murna a wurin Bara'atu ba'a magana. Kafin su tattara su koma Zaria ne mahaifinsa ya fara cuta yana ta ramewa. Hajjo tasha kuka tana rokon Bara'atu akan ta sakar mata kurwar miji. ABINDA AKE GUDU🙆🏽12 Batul Mamman💖 *BAYAN SHEKARA DAYA* Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta gama da abinda yafi mahimmanci. Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya. Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta yasa ta hade rai. Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri jin kwaf. Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace " Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu tashi" Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar ma zai saki Sagira. "Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan." "Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na kammala gini na." Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....." Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara. "Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa cikinsa wuta ne." Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki sani babu ni babu su." "Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa gaisheki tunda ba nisa mukayi ba." Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta. ***** *Sabuwar Rayuwa* Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba. Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi. Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da 'ya'yanta. Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim, Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma sunyi kokarin jansu a jiki. Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara. Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba. _Asmau S. Yahya_ Ranar farko da zasu je makarantar kowa yana doki banda Asmau. Haka take da tsoron mutane. Duk gidansu ita ce ta kasa sakewa da yaran Mama. Kowa ya shirya ta kwanta ciwon cikin karya saboda taji ance kowa karatunsa shi kadai malam zai biyawa. Yadda zata yi karatu a gaban su Suwaiba ne yake kara tsorata ta. Umma na ganinta tasan ciwon karya ne. Da rarrashi ta lallabata suka tafi suna idar da sallar magriba. Cikin gidan suka fara zuwa suka gaishe da Mama sannan suka fito waje. Suwaiba 'yar Mama ta hudu ita ce kusan sa'ar Shema'u amma duka ita da Sadiya sun zama kawaye da Shema'un. Tare suka fito zuwa masallacin Asmau na bin bayansu rike da hannun Aina'u. Malam Hadi yana zaune tare da Abdulhalim, Abubakar da Umar. Suna zuwa gaishe shi suka yi kowa ya sami wurin zama. Sai da ya gama da manyan sannan yaji karatun su Suwaiba. Daga nan ya fara jin inda su Asmau suka tsaya yace kowa sai ya biya surar karshe inda ya tsaya. A nan ake yinta ana zuwa kan Asmau da ta fuskanci idanu sun dawo kanta tana yin Bismillah sai hawaye. Malam yace ta barshi ya gama da sauran .Shema'u tayi tsaki tace " malam wallahi ko a islamiyya haka take yi sai taji bulala take kawo hadda." Murmushi yayi "ni bana duka kinji Ma'u. Bari na gama da kannenki sai ki biya min." Hatta Aina'u sai da ta karanta suratul Ikhlas amma ana dawowa kan Asmau sai kuka. Jafar yace Ummansu tace a zaneta idan bata yi karatu ba. Tunda ta fara kukan farko Abubakar yake kallonta. Dariya abin ya bashi sai da yaga taki denawa ta soma bashi tausayi. Malam Hadi yayi har ya gaji taki karatu sai kuka da rawar murya. Yace kowa ya fita banda manyan yayye. Suna tafiya ya nuna mata Abdulhalim da Abubakar "Waye a cikinsu kika yarda zakiyi karatun a gabansa tunda kin kasa a wurina." Tana daga kai suka hada ido da Abdulhalim ya hade rai. Da shine malamin zaneta zaiyi fes baya daukar rainin hankali. Da sauri ta nuna Abubakar. Malam Hadi yace "to Sadiq ka kwatanta gaskiya ka ji karatun. Ke kuma gobe ki tabbatar zakiyi a gabana ko na samo bulala". Da haka suka fita saura ita da Abubakar. Fuskarsa a sake ya fara tambayarta "shekarunki nawa Asmau?" "Shahudu" "Ashe ma kin girmeni da shekara takwas" Ta dan saki fuska amma muryarta bata dena rawa ba "so kake kace ka girmeni da shekara takwas dai" Yayi murmushi dama so yake ta saki jikinta "Haka ne, ni yanzu ina level two a BUK ina karanta computer science. Ke fa?" "SS1 nake a science class. Likita nake son zama" yadda take maganar yasan ba karamin son hakan take ba. "Very good, sai dai bakiyi kama da likita ba saboda tsoro yayi miki yawa. Likitoci kuma basu da tsoro". Yana kallon bata ji dadin maganarsa ba ya sake yin murmushi. "Kada ki damu akwai maganin tsoro. Shine ki daure ki rinka magana a cikin mutane. Babu mai yanka ki. Iyaka idan kinyi kuskure a gyara miki. Karatun Qur'ani karfin zuciya yake sawa ba ragwanta ba." Shiru tayi tana sauraronsa yana ta janta da zance. Sai karshe yace ta biya masa yaji. Da kyar ta daure hawaye wani na bin wani ta karanta. Kafin tayi rabi kukan ya dauke sai karatun ake ji. Tana kaiwa karshen surar yayi kabbara sannan ya sake karfafa mata gwiwa wurin bude baki a gaban jamaa. Da murmushi ta fito suka tafi gida ran Shema'u a bace saboda tasa sun dade. Tun daga wannan lokacin ko ta fara kukan idan Abubakar yana masallacin sai ta daure. Karshe dai sunanta ya koma Idon kuka saboda kullum sai tayi. Gashi ta tsani sunan. Haka rayuwa ta cigabar musu har lokacin bikin Nasiba. Gidajen biyu suna ta shiri duk da su Umma basu fi shekara daya a unguwar ba. Haka suka yi bikinsu lafiya kalau kamar dangin juna. Su Asmau an kara zama 'yan mata. Yanzu tana dan sakewa har ayi hira da ita. Wani lokaci da Umma zata Wushishi gashi basu yi hutu ba a nan gidan Mama Yalwa ta barsu. Abdulhalim ya tafi bautar kasa Jos yanzu Abubakar ne babba a gidan. Duk da yanayin karatunsa bai hana shi cigaba da zama daukar karatu a wurin malam Hadi ba. Duk cikinsu yafi kowa mayar da hankali akan karatun addini shiyasa Baba yake matukar ji dashi. Watarana an gama karatu kowa ya fita daga masallacin sai Asmau dake zaune tana kokarin kammala aikin da malam ya bata na fitar da hukuncin (NUUN saakina) a thumunin da ya biya mata ranar saboda washegari test gareta a makaranta karatu take son yi. Abubakar yana can wurin zaman liman yana tilawa aka soma iska mai karfi alamun ruwa zai iya sakkowa a kowane lokaci. Da dan gudunta ta tashi zata rufe tagogi kafin ta fita saboda kurar dake shigowa. Har ta gama rufewa Abubakar baiyi yunkurin tashi ba. A take kuma aka dauke wuta saboda wata tsawa da akayi mai karfi. A dan tsorace tace "Yaya Abubakar kazo mu fita kafin ruwan nan ya sauko" Shiru taji sai numfashinsa da ya kara karfi. Gabansa ta karasa sai dai duhu yasa bata ganinsa sosai. Wayarsa da ta taka ta dauka ta haska shi. Kwance yake numfashinsa yana sama-sama da kyar yake fita. Hannunsa daya kuma yana nuna mata aljihun wandonsa. Asmau duk ta rikice ta kuma fahimci abu yake so ta miko masa daga aljihunsa. To kuma Umma tayi musu gargadi sosai akan taba maza wannan yasa ta kasa tabashi ta fita da gudu a cikin ruwan ta shiga gidansu ta fadawa Mama Yalwa. Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?" Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi masa sannu. Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru. ABINDA AKE GUDU🙆🏽11 Batul Mamman💖Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi. Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar mugunta. Don tsabar wulakanci yace "A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?" Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban Hajjo "Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku tare batare da izini ba". "Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace. "Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki." Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi." Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta "Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa." Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan. Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka. ***** A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka. Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda. Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku." Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci su Rabe su fita. Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina. Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje haka. Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida. Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama. Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi." Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu. A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je. Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki. Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari 'ya'yanta sun raina kakarsu ba. Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata kenan. Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta sami wani abokin aikinta ya samo mai siya. Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin. Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi. "kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"? "Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana tafa hannuwa. Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba. Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na sayar na cinye kudin. Shikenan ko." Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min daidai. Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana harararsa. "Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi. Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai" Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa. Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa." Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba saboda son da yake mata. Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan. Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena kasuwanci ba. Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu. Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana. Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa. Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin tace "Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki wannan rungume rungumen ba?" Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu tana yiwa dansu fada. Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu iyawa" mtws. "Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi ba". "Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama muharraman juna". Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma ciki Hajjo ta dakatar da ita. "Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda kin gama fetsare kafafunki". "Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta tsakaninku shine muharrami." Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?" Bara'atu ta fahimci neman kureta suke yi sai dai kuma tana da hujja ba da ka tayi magana ba. "Alakar jini bazata hana aure tsakaninsu ba wannan yasa ya zama ba muharraminta ba. Mutanen da suka amsa wannan suna a garemu sune kaka(namiji),'yan uwansa wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Haka kuma yake ga bangaren kaka (mace), sai 'yan uwan uwa da na uba suma wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Sannan sai 'ya'yan kanne maza da mata. Babban misali shine Sayyadina Ali RA kani ne ga Annabi Muhammad SAW domin iyayensu wa da kani ne. Nana Fadima bazata iya auren Abu Dalib ba saboda kawun babanta ne amma ta auri dansa duk da cewa kani ne ga mahaifinta. Sannan ko a gidan nan Rabe da ya auri Sagira ai kanwarsa ce tunda Hajjo da babar Sagira shakikan juna ne. Muna yawan yin kuskure sai muce 'ya'yanmu 'yan uwa ne mu bari suna taba juna ko suna shiga dakin juna kai tsaye da sunan 'yan uwan taka.( A labaranmu na soyayya muna yin wannan kuskuren duk mu saka cousins ko 'ya'yan riko sun gama tabe taben jikin juna duk da sunan 'yan uwan taka sannan daga baya mu kulla soyayya tsakaninsu). Aya ta ashirin da uku a suratun Nisa'i ta iyakance mana su waye muharramai. Kuma _An karbo daga Ma'qal ibn Yassar yace Manzo SAW yace: ya fiyewa dayanku a buga masa kusa a kansa da ya taba jikin macen da ba muharramarsa ba.At-Tabarani ya rawaito shi, Sheik Nasiruddeen Albani ya inganta shi a Sahih Jaami'."_ Wani kallon raini suka rinka binta dashi tunda dai ga hujja ta basu. Yaya Abu tace da Kamilu " Kai, daga yau babu ku duka babu wadannan 'ya'yan gwal din." Bara'atu dai kyalesu tayi ta wuce tana addua'ar kammala gininta su huta da wannan masifa. ABINDA AKE GUDU🙆🏽13 Batul Mamman💖 Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi. Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin. Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana ba. Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki amsawa har sai da Qasim yayi masa magana. "Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba" Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa Qasim ba. Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke ce Asmau ko?" Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace "eh" tare da mikewa ta tafi masallaci. An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa. Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai ba ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da kanta. "Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai" Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne kuma duk lissafi ko daya bata yi ba. "Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin duka yake yi." "To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido, uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics. Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero shikenan" ta fada da dariyarta. Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin. Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan science a gidan Mama." "Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya amsawa idan naje nasan bazai kulani ba" "Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?" "Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba". Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani rashin fahimta suka samu. Ko

Chapter 4 of 23