Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
danna wayarsa aka turo masa wani text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu suka saka a gaba. Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je nema a asibiti basu sameta ba. Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta. *BAYAN SHEKARA BIYAR* Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu. Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya "Ummina tuwo kike yi?" Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?" Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_ kema kinsan akwai abinda take so". Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka fadi me ya dawo daku ai" Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na rako ta". Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku koma". Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai abinda take so ta janyota jikinta "Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji" Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau ta ga kamarta da babanta ta fito sosai Nabila ce take shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo ta bani biyay na siyo". Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai" Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba biyay ba". Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi kuma tace sam ba haka ba. Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi. Asmau tace " da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa zatayi." "Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar. Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu 'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi. Manyan yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta. Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽28 Batul Mamman💖 Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta. Da sauri ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka. Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata tana dukan karamar yarinya haka. "Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?" "Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?" Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi su Ali me suka yi. Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku" Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita. A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane." Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada miki bamu da 'yan uwa?" Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya saboda soyayya. Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun zo sun dubata har lokacin bacci take yi. Bata farka ba sai bayan magriba da zazzabi mai zafi jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata mutu." Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta. Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata ta cika. Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta. Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har wani sama yake yi. A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama kirjin yara). Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane." Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka. Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar, Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah." Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin babana? Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta dokeni. Sai ya yama min ko." Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar addini kin tara yara da yawa". Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi. Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai mu tafi namu gidan ko?" "Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin. Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo. Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen. A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko musu kayan kwana. Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi. Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da kura don tana ganin alamun asthma gareta ba pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan 'yarsa tayi. Amma irin halin da taga yana shiga ga kashe kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali. Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar gudan jininta ba. ***** Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta fada mata ranar da ta zane Amatullah "Wato Kande maganganun sun kona min rai. Yarinya kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman mata ya iya." Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa 'yar masu kudi". "Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya. Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya suka yi." "Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko." Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a sayi kayanta. ***** Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare Asmau ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta. Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi. Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren jari da ita." Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita ma sonta nake yi." "Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen 'yar masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda nace." Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado. Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta soma kwalawa Zulaiha kira. Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya sakeki mu tafi mu bar miki gidan." Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki? Zinaru ki bashi baki don Allah." Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya sakeki ki bar musu gidan". Zinaru ta kalli Gidado "Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a gidan nan ana wulakanta ni ba". "Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu tafi" Yaransu duk suna kallo ita Asmau har ta soma jindadi sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da yaran nan." Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai wanke masa" Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar wurin nan kafin na bata muku rai." Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na roki nawa iyayen gafara". Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa amma ka kasa rabuwa dashi. Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau ki zauna gobe zan sake rokonsu." "Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki roki gafarar su Inna". Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya harda kaisu kara. ***** Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta. Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili ya koreta. Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike hannun Amatullah suka fita. Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito. Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara ashirin ba. Dreban farko kamar kada ya tsaya sai kuma yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike. Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya. Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata murmushi. "Yan mata yaya sunanki" "Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce min ko Ummi" Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya. Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba" Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai zane saboda tana duka na." Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya jikansa" Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a idonta. Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take kokarin numfashi yaki sauka. Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare. Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji matar tana waya tana sanar da wani inda suke. Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban mukami. Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace " Ummi wannan ne baban nawa?". ABINDA AKE GUDU🙆🏽29 Batul Mamman💖 Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi." Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah sai matar ta girgiza kai. Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi. Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa. "Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na barki ba kinji" Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka yama min". Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu. Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an tafi aljannah an barsu. Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake tabaki sai na rama miki kinji." Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta kanta. Tun dazu ake kawo kararta." Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba". Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda. Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai da na turo mota daga Jos din." Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi." Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a san halin da kuke ciki kada suji shiru" Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan zasu kira idan suka ji shiru." Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane layi gareki?" Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba tace "MTN". Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka" Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan dawo" Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma ya isa. Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni" "Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?" Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun. Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya don karfin hali harda kwatancen asibitin. Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta. Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya Lubabatu wannan jikata ce." Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar sunansa" Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki maganinta." Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da dan nata. Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi" "Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu" Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani numbarki saboda kira ko da akwai wani abu." Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya. Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu tawa numbar a wayarta ko." Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma zan saka chaji idan an kawo wuta" Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki lafiya kinji". Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci. Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa. ***** Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne saboda kada tayiwa mamanta rigima. Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi. Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka dagawa babarta hankali." "Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya" Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo" Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani. ***** Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau take yi mata. "Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba aljannah bane kuma na fada miki yana can.

Chapter 11 of 23