Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baya ya hakura sai dai yayi alkawarin babu mai zuwa gareta idan bata kawo kanta gida ba. A ciki ma wurin Innarta sai murna da kukan farinciki. Ga 'ya'yanta duk aka taru ana kallonsu. Duk 'yan uwanta suka taru ana murna. Alhajinsu yayi ta godiya ga su Umma da suka dawo da ita gida. Zama suka yi ana jajanta irin wannan hali da yara ke jefa kansu a dalilin soyayya sun yarda su rabu da kowa. Asmau da Zulaiha sun zauna suna ta mayar da zancen halin da suka tsinci kawunansu a ciki. Ta yanke shawarar nema takardarta a wurin Gidado. Ita da aure kuma sai a aljanna. Asmau tayi dariya tace "zaki yi ne tunda na sami miji kema zaki samu in sha Allah" ta bata labarin Jikamshinta da bikinsu da za'a fara nan da sati biyu. Zulaiha tace biki kam da ita za'ayi komai in sha Allah. Ranar ma a gidan Mami suka kwana washegari sai Kano ta Dabo tumbin giwa. Biki ya gabato ana ta rabon kati ABINDA AKE GUDU🙆🏽52 Batul Mamman💖 Daga 'yan uwan Asmau har na Col. Ishaq kowa shirin biki yake yi sosai. Ita har mamaki suke bata. Hala sun manta wace ce ita suke son yi mata biki irin wannan. Mutanen da zasu zo karshenta duk 'yan kallo ne wadanda zasu tafi da ita a baki. Sake yiwa Jikamshi korafi tayi akan haka yace shi bai taba damuwa da biki ba sai yanzu. Idan suka yi abin shiru shiru a gida shine mutane zasu sami na magana ace dama ansan dole ayi abin kamar na marasa gaskiya. Yanzu kuwa biki zasuyi su nunawa duniya farincikinsu da ni'imar Allah garesu. Dama tasan tuni yabi zugar su Shemau da Ainau shiyasa batayi mamakin amsarsa ba. Kwanansu biyu da dawowa Walida tazo gidansu har ta rakata karbo dinkunanta na fitar biki. Kokari suke su ajiye komai su mayar da kawancensu na da. Bata da niyar gayyatar sauran kawayen makaranta don basu nemeta ba a baya kuma dama bata dasu da yawa. Yanzu ma bata san ina yawancinsu suke ba. Duk wadda tazo bazai wuce bawa ido hakkinsa ba. Dinkuna sunyi kyau sosai. Kayan Amatullah ma ba'a magana. Musamman da yake kayan yara akwai daukar ido. Ita da su Mimin Shemau da Nanan Kawu Garzali mai sunan Hajjo duk anko akayi musu. A bangaren gyaran jiki da abinda ya shafi lalle kuwa takanas Nasiba yayar Abubakar tayiwa aminiyarta ta Nijar magana. Massouda kenan, matar da a Nijar din ma ji suke da ita. Taji labarin Asmau kaf a wurin kawarta kuma ta tausaya mata shiyasa tayi mata hadin kayansu masu kyau da tsada sosai don tace Asmau dole a gyarata a saya mata kima a wurin mijinta. Shi kanshi mijin wani girmansa take gani. Duk mutumin da zai iya auren mace kamar Asmau lallai ya cancanci yabo da jinjina. Dole a taya shi da adduar Allah Ya saka masa da alkhairi bisa wannan kyakkyawan aiki da yayi. A wannan lokacin idan kaga Asmau zaka so sake kallonta. Duk da dama can ita bata sahun farare amma fatarta ta kara kyau sosai tayi haske. Kuma duk wahalar nan ta baya da tasa ta rame yanzu cima ta canja ga kwanciyar hankali. Shiyasa jikinta ya dan dawo ta ciko. Idan Umma ta kalleta sai dai tayi godiya ga Allah. Bata ma so tayi tunanin halin da Asmau zata fada da bata hadu da mutanen kirki ba ko ta dawo gida. A dan tsukun lokacin Col. Ishaq ya damu sosai da rashin ganin Matarsa. Massoudan Nijar ta saba da irin wannan aikin na gyaran amare ta taho har gida ta murjeki da kyau. Saboda haka gidan Umma akayi mata masauki. Safe, rana, dare daga wannan turaren sai shafa wancan abin. Sau uku yana zuwa ana ce masa bazata iya fitowa ba. Ransa a bace a karo na hudu yace da Yassar idan bata fito ba wallahi bazai tafi ba komai dare. Yassar yayi murmushi wannan soyayya tana daukar hankalinsa sosai "ka bani dan lokaci zan fito da ita. Umma da matar da Anti Nasiba ta kawo ne basa bari ta fita. Yau kwana biyar ko kafar gidan nan bata fito ba" Fuskarsa sam babu walwala yace "Ka fadawa matar zan kara mata kudi amma gobe tayi shirin komawa garinsu aikin ya isa haka" Yassar ya kalli yadda yake magana kamar bashi yayi ba ya wani hade rai. Shi dai ya sosa keya ya tafi. To Col. Ishaq ba irin wanda zaiyiwa tsiya bane da ya sha tsokana. Yana komawa dakin Anti Bintu tace "Allah sarki bawan Allah, ya tafi kuwa?" "Ya ce komai dare zai jira a gama" Umma ta dan sha kunu "kaje kace ina wurin ka kasa fadin sakon, haba yayi hakuri mana. Nan da kwana hudu za'a fara bikin sai ya ganta. Kema da laifinki da baki fada masa lokutan da kuke farawa ba" Asmau ta rufe ido kawai. Ba karamin kewarsa take yi ba ita kanta. Gashi tasan abubuwa sunyi masa yawa tunda bikin ya matso amma kullum kokarinsa ya ganta ko yaji dadi. Sai ake rashin sa'a idan yazo an fara shafe shafe ko turara mata jiki. Da daga ita sai Massouda ne kawai yadda suke wasa da matar ficewa zatayi ba'a sani ba. Amma kullum ba'a rasa babba da take jin kunya. Har Yassar ya juya Hajjo ta dakatar dashi. Tace a goge jikin ta fita "gyaran nan ai saboda shi ake yi ko. Kwana nawa kullum yazo amsa daya ai babu dadi, sai kun sa ta fita a ransa. Ko dai ku barta ta fita ko kuma naje na kawo shi har dakin nan muga karshen gyara" Umma kunya ta kamata ta fice daga dakin su Anti Bintu suna dariya. Auduga ake tsomawa cikin ruwan wani humra mai bala'in kamshi ana goge mata jiki. Sai da aka gama tas ta zura dogon hijab akan rigar jikinta ta fita don ko kwalliya an hanata sai ranar kamu. ***** Tayi zaton yana waje sai ta ganshi a falo yana waya ga Yassar da Amatullah suma suna zaune. Cikin nutsuwa ta shigo falon Yassar ya dauki Amatullah a wuyansa suka fice. Col. Ishaq ko sallama baiyi ba a wayar ya kashe yana kallonta. Ya ciri tuta a iya kallo mai kashe mata jiki. Ashe ita ma tayi missing dinsa sosai. Sai yanzu da ta ganshi taji sauki a ranta. Ko hoda babu a fuskarta kuma iya abinda yake iya gani kenan amma tayi masa kyau. Ga wani kamshi mai sanyi da bai san da yadda zai fasalta shi ba yana fitowa daga jikinta. Kujeru biyu ne tsakanin wadda ta zauna da tashi ta gaishe shi amma da kai ya iya amsawa babu magana. Shirun nasa ya dameta tace "Jikamshina yaya, ko kayi fushi ne?" Yayi sassanyar ajiyar zuciya "Matar Jikamshi harda muryarki ma gyarata ake yi? Tunanin nawa zan karawa matar da take gyara min ke nake. I just love the way you look. Matsalata daya ce hanani ganinki da ake yi" Tayi murmushi "to kayi hakuri kaji _Jikamshina_ . "Na fada miki idan zan tafi ki dena kirana da sunan nan amma kinki ji ko?" Wani kalar tausayi yake mata tayi dariya sannan ta fara magana da shagwaba "haba Jikamshina yanzu fa na fito. Ko rabin ganinka banyi ba kake zancen tafiya" "Kina wasa dani yarinyar nan. Nace ki dena kin cigaba. Kada kice banyi warning dinki ba dai. Bari na tafi, da na sani ban matsa sai na ganki ba yau" Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace "Me yasa kace haka" Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada miki nan gaba. I love you. Sai da safe"Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace "Me yasa kace haka" Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada miki nan gaba. I love you. Sai da safe" Kasa amsa masa tayi tana kallonsa ya fita. Ta koma ciki duk tana jin babu dadi. To me tayi masa haka da ko minti shabiyar batayi ba da fitowa ya tafi. Ko dai yayi fushi ne da gaske? Bazata iya jurewa hakan ba kwanaki kadan kafin aurensu. Dakinsu ta koma ta dauko wayarta zata tura masa text don bata son kira yana tuki. Hakuri zata bashi idan ma tayi laifi ne. Tana dauko wayar ta ga sakonni a whatsap dinta. Idan ba 'yan gidansu dasu Rashidan Azare ba babu wanda take chatting dashi sai Jikamshinta. Budewa tayi zata tura masa text sai taga nashi ne a sama alamun yanzu ya turo sakon. _Allah Ya kaimu ranar aurenmu Matar Jikamshi. Ranar zaki san irin matsayin da Allah Ya baki a zuciyar Ishaq. Kada ki fassara tafiyata da komai, idan na dade tare dake *kamshin matar jikamshi zaiyiwa jikamshinta illah* Ji nayi kamar na tafi dake._ Asmau ta karanta sakon yafi a kirga tana murmushi ita kadai. Ko a yanzu ace zaiyi mata kishiya ta tabbatar zuciyarta zata iya bugawa. Duk wannan kalaman nasa da iya nuna kulawa ace ya nunawa wata matar bata san inda kishi zaiyi da ita ba. Adduar son kai tayi a zuciyarta. Allah Yasa Jikamshi nata ne ita kadai.... ***** Washegari da azahar sai ga Zulaiha a Kano ita da su Humaira, Muhsin da sauran 'ya'yanta. A bakin kofa suka rungume juna suna tsalle kamar wasu yara ita da Asmau. Yara na murnar ganin Amatullah. Gida mai dadi ba Zulaiha ba hatta yaranta sun dan murmure. Kayan jikinsu kuwa ya isa ya fada maka cewa babanta wani ne. Don ko gidan Mama da Asmau take yiwa kallon arziki sosai bai kai na mahaifin Zulaiha ba. Kaddara da rabon 'ya'ya ya kaita auren Gidado. Dreba mahaifinta yasa ya kawosu tare da kanwarta itama sunanta Asmau suna kiranta Ma'u. A tsarin bikin ranar Juma'a za'ayi Kamu da walima wanda gidan amarya ne suka dauki nauyi. Washegari asabar a daura aure sannan bayan magriba ayi Sword Crossing sai kuma ranar lahadi ayi yini a kai amarya. Yadda su Shemau suka ci burin kawata kamun ayi biki mai kayatarwa wasu mata suka dauko masu shirya biki da duk wani abu na bikin kamar abinci da harkar decoration. Ya da kanwa ne Aisha da Zainab Maiturare. Tunda suka ji sunan ango har ragin kudi suka yi musu sun ce ai su kannensa ne wannan biki na yayansu ne saboda haka zasu zage damtse wurin yin abinda za'a yaba. Rashida tazo itama da yaranta da kanwarta Harira. Yaya Tagwai ma ba'a barta a baya ba. Da ta shigo gidan harda kukata tana bawa Asmau hakuri da bata tausaya mata ba ta koreta. Sai a lokacin suka daidaita da Hajjo. Mutanen Wushishi da amarya Dijah wadda ta kafawa mijinta naci duk sun zo. Gida kam yayi albarka don ya cika da 'yan uwa da abokan arziki. Asmau gidan Jafar ta koma ita da Zulaiha. Rashida tana tare da Zubaida a nata gidan inda take kula da Uwargida. Sai bayan biki zasu je Jikamshi. Sabira ce ta kai Asmau wani salon aka gyara mata kai gashin nan yana ta kyalli sannan aka gyara kafa da hannu. Ta kalli Sabira tace "yanzu banda iyayi har hannu ma ana gyara shi. Na zata sai masu saka farce ake yiwa" "Ummin Amatullah yanzu gyara ai ko'ina ake yiwa. Matan da ake cewa suna kwacen miji a waje ba wata tsiya suka fimu ba sai gyaran da rashin kunya. Mu kuma Hausawa komai sai mu ce Allah Ya sauwake nayi kaza bayan kuma gidan mijinki kike" "Kuma fa gaskiya ne, shiyasa naga Yaya Jafar indai abu ya shafeki wallahi baya kyashi ko kadan. Ashe gyara ne da sauran sirrikan da zanzo ki bani. Muma Allah Yasa mu dace" Suka yi dariya, Sabira tace "ai dacewa dai kin gama. Wallahi ki rike baban Amatullah tsakani da Allah. Irin yadda yake sonki kadai ya isa ya nuna miki cewa Allah Yana jin adduar bayinSa. Abinda ya rage kawai ki bi duk wata hanyar kyautata masa yasan cewa shima ya auri mai sonsa." Ummy mai salon tana mata gyara tana nade shawarar da Sabira ke bata itama zata gwada a nata gidan. ***** Ranar da daddare Col. Ishaq ya dawo gida a gajiye saboda ya tsaya karasa wasu ayyuka kafin hutunsa na aure ya fara washegari. Har wani aiki za'a turo shi Liberia ya samu aka bawa wani. Suna magana da Mami da ta iso a ranar ne yaji waya. A zatonsa Asmau ce don yau aiki yasha masa kai tun wayar safe bai kara kiranta ba. Da ta kira ma bai ji ba sai daga baya ya gani ya aika mata da text. Bakuwar numba ce ya dauka tare da sallama. Muryar da yaji ko bata fadi sunanta ba bazai taba mantawa da ita ba. Badariyya... Ko aurenta ya mutu ne???? ABINDA AKE GUDU🙆🏽53 Batul Mamman💖 Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace "Uhmm Ishaq dama dazu naje yini gida ne aka bani katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari" "Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards nasan zaki ji labari" Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan murmushi. Wayar ma sai da ta nemi izinin mijinta dama ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki. "Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai naji wani labari a gida da ya tada min hankali...." Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar. Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting. "Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko? Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi" Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?" Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata maganar da zata dade tana mata ciwo a rai. "Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki gaida mijinki" Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin Asmau kafin ya yanke muku hukunci." "Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane baka iya ba a wurin wasu." Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki ce sannan ta kwanta. ***** Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba. Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan. Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu. Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi dai shine da laifi amma yafi kowa fushi. Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai dangi ba'a canza su. Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima ana cin amarci. Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke. Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba. A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi wasu daga ina suka zo. Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce "Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai fara'a kike yi." Allah Yasa dreban motar ya fita sai AC da aka ware musu. Walida tace "baki ga komai ba ita da Col. Ishaq nasu salon daban yake" Asmau tayi fari da ido kawai tana murmushi. Motar tasu mai tint ce ta waje ba'a ganinsu sun jiyo kida daga wurin bikin yana tashi ga mata suna ta shige da fice. Wurin cike yake da sojoji masu gadi. Da farko ma taron ba'ayi niyar yi da maza ba. Sai Mami ta roka akan cewa ango zai zo da abokansa suyi hoto da amarya ya tafi. Shima da kyar ya yarda da zuwan. Shemau ce ta fada mata kalar kayan da amarya zata saka suka yi gaggawar nemawa ango wanda zai dace. Bugu zuciyar Asmau ne ya karu da ta hango motar Jikamshinta. Wurin motoci bakwai ne suka shigo tare. Wai bikin da akace babu maza kenan. 'Yan kashe kwarkwarar ido da abokan arziki duk sun biyo shi. Saitin motar da take Dahiru da ya tuko motarsa ya daidaita tasu yadda zasu fito tare. Ya hakimce a baya yana waya. Sai da ya gama ya fito ko'ina ya dauki kamshi. Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar Jikamshi. Duk abinda kake so kuwa dole kaga kyaunsa. Indai haka ne Jikamshi da Asmau sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden lace ne peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali purple mara turowa akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi. Asmau tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me. Safiyya da Shemau ne masu tsari suka jera su MC din taro S.Kilishi ita ce ta sanar da shigowar ango da amarya. Suka taho suna taku daidai. Wuri ya kaure da sowa. _Qamshi qamshi yana tashi, 'yan mata zamu kamun amarya_ _Yaune muke shirin kamu...amarya_ _Asmau amarya zo gamu...amarya_ _Ki hakuri da zancenmu, kinsan aure yana kanmu_ Kafin mai wakar ta karaso gaban ango da amarya tuni 'yan mata sun fito ana ta rausayawa. Jajimaji kenan, idan ta bude baki ko Sangandali sai dai taja baya. Haka ta cigaba da waka har amarya da ango suka zauna. Bayan Hajiya YBK ta bude taro da addua aka shiga biki da gaske. Su Bilkisu da tawagar gidan Hajiya Lubabatu da 'yan Jikamshi ankonsu iri daya ne da nasu Ainau. Ga su Amatullah yau anyi kwalliya itama ta fito sosai. Yaran su Shemau da nasu Sadiya 'yan uwan Abubakar kowa fa yayi kyau. An bukaci dangin ango su fito fesawa amarya turare sai gasu mata biyar ne harda Mami kowacce da tsadadden turare a hannunta suka zo a rinka fesawa. Biki yayi biki mata sun sha rawa. A cikin taron mata 'yan taya ango da amarya murna sun gwangwaje. Saboda yawansu ba sunan kowa zaka iya kamawa ba. Akwai su Maman Afrah, Tash, Jatma, Zahida, Mrs G, Sadiya Jegal, Ibtihal, Shukriya, Ummu Rauda, Maman Sadiq, Ummu Aslam, Mrs Ambursa, Hauwa Ag, Mum Little, Farha, Jammu, Mardiya, Shafa, Ruqayya, Tafeesu, Ummi BK, Didi, Mjay, Zahra BB, Biebie Isah, Temseey, Khadija Candy.....(wai abin da yawa ni mai rubutu naji hannuna zai tsinke nace wallahi sauran ma duk ina sonku har raina). Taro kam ya kayatar. Anci an sha an kuma rausaya. Ana cikin daukar hotuna ne Mama Yalwa tazo zasu dauka ita da Asmau da ango. Suna hada ido da Asmau suka tuna abu daya suka fara kuka lokaci guda. Duk wanda yasan wadannan matan yasan kukan me suke yi. Allah Ya jikan Abubakar, mutuwarsa ce tasa har aka zo rana irin wannan. Suna yi ana tayasu har su Umma. Suwaiba karamar kanwarsa ce ta iya daurewa tana basu baki. Col. Ishaq duk kishi irin nasa ya dauke kai a yau. Abubakar wani bangare ne na rayuwar Asmau da bazai gogu ba. Haka aka kare taron kowa ya tafi gida cikin farinciki da annashuwa. 'Yan gulma basu sami abin fada ba sai san barka domin taro ya burge kowa. ***** Washegari sai shabiyun rana zaa daura aure. Asmau tun dare ta kasa baccin kirki. Yaushe zata manta ranar aurenta na farko da ango ya rasu. Ji tayi gabadaya bata da kuzari har gari ya waye. Col. Ishaq kuwa jin kansa yake kamar anyi masa wani albishir mai kyau. Farar shadda ya saka harda babbar riga. Anyi mata aiki da zare ruwan goro saboda haka hularsa da takalmi harda agogon hannunsa ruwan goron ne. Masallacin Hotoro ya dauki jama'a wadanda suke son shaida wannan babbar rana. Su Jafar da Yassar suna kan gaba, ga Kawu Garzali da wani abin mamaki Kawu Rabe yazo yana ta ra6e ra6e. Bisa amincewar Hajjo da sauran 'yan uwansu Alh Adamu Matawalle shine waliyin amarya. ASP Qasim ma gayya guda yazo da ita daga abokan aiki zuwa makusantansa a Shanono. Ga su Sada suma ba'a barsu a baya ba. Ango sai faraa yake yana gaisawa da jama'a. Har hoto suka yi da Qasim suka gaisa a mutunce. Shabiyu nayi Liman ya bukaci wakilin angon da waliyin amarya. An daura auren Col. Ishaq Muhammad Jikamshi da Asmau Shu'aib Yahya akan sadaki dubu sittin. ***** Asmau na zaune kowa yayi wanka ana ta shirin tafiya gidan Umma inda zasu zauna saboda baki masu son ganin amarya. Tamkar wadda aka zarewa laka haka take jin jikinta. Ga faduwar gaba da ta kwana dashi. Tana kwance text ya shigo wayarta ta dauka a firgice. Kalma daya ta gani daga Jikamshi wadda ta saka ta kuka sosai. *Alhamdulillah.* Su Sabira suka zuba mata ido har dakin ya fara cika da su Ainau da Zulaiha suna ta tambayarta me aka yi mata. Shemau rai a bace tace "ku kyaleta tayi kukan nan. Tun daren jiya take neman yinsa. Ni nayi mamaki ma da kika jira sai yanzu. Ace mutum bashi da sana'a sai ta zubar da hawaye." Tana kukan tace "Anti Shemau an daura fa" La'ila ha ilallah....shine abinda Shemau ke fada tana tafa hannuwa. "Amaryar zamani da kanta take sanar da aurenta" Wani hawayen ne ya zubowa Asmau bata ji haushin yayarta ba tace "na zata shima mutuwa zaiyi, tun jiya gabana ke faduwa" Jikin Shemau yayi sanyi bata san abinda ke ran kanwarta ta ba kenan taje ta rungumeta. Ainau ma ta matso ta rungumeta suka soma kuka. Sabira da Zulaiha aka bari da rarrashinsu. Sai da suka saka Asmau yin nafila godewa Allah sannan tayi wanka ta shirya suka tafi. Shigarsu gidan ke da wuya Yassar ya shigo yace ga ango a waje zasu dauki hoto da amarya. Umma tana cikin mutane ta girgiza kai tana murmushi. Wannan ango bashi da dama. Bare an daura aure ai shikenan kuma. Dakin da suke zaune da su Rashida Mimi taje ta kirawota. Yawanci sallah masu rakata sukeyi sai ta nemi takwararta Ma'u ta rakata. Mayafi tasa ta rufe fuska haka suka fito. Ashe tawaga guda ce domin harda su Jafar da Qasim. Ita dai duk kunya ta isheta haka akayi hotunan ta kasa sakewa. Shima bai matsa mata ba. Ko don idon mutane ya raga mata. Qasim tun fitowarsu idanunsa suka fada kan Ma'u. Yarinya ce kyakkyawa suna kama da Zulaiha sosai. Itama ta kula da kallon da yake mata sai ta sunkuyar da kanta cike da kunya. A take yaji wani abu a ransa game da ita. Sun gaisa da Asmau zata shiga ciki ya kalli Col. Ishaq. "Ango don Allah a bani dama zan roki amarya alfarma. Ta dan daga kai suka hada ido da Jikamshi yace "bari na matsa ga mutane can zamu gaisa. Idan kun gama sai kuyi mana jagora mu dauka dasu Hajjo" "Godiya nake yallabai, idan tarkona ya kama zan fada maka don kune masu nema" Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun nasara kenan. Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da iyaye da kakanni sannan suka tafi. ***** Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda suka shirya. Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran material din wanda ba'ayiwa shafi ba. Kowa sai cewa yake tafi jiya yin kyau. Komai da ta saka ya dace da kayan sai daukar ido take. Amatullah ma Najah sai da tayi mata kwalliya kada da ta dace da yara aka daukesu hoto da Umminta. Ana fara tafiya ango yazo daukar amaryarsa. Drebansa ke jan motar sai wani abokinsa a gaba. Ko kadan ba haka yaso ba amma wannan tsarin na Mami ne. Kasa dena kallon

Chapter 22 of 23