Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
take Ya yafe musu kuskuren da suka aikata wanda har yau yake bibiyar komai na rayuwarsu. Daga nan tayi adduar fatan samun nutsuwa da dukkan wanda Allah Ya kaddara zata aura. Tana sallar Anti Bintu ta shigo da niyyar sake bata baki ta tarar tana sallah. Gefen gado ta samu ta zauna tana jiran ta idar. Tunanin wannan al'amari ne ya rinka damunta. Idan akace *abinda ake gudu*to ba faruwar laifin ake ji ba. Abubuwan da zasu iya biyo bayansa. Asmau ta dade tana ganin tasirin hakan a rayuwarta tun ranar da Abubakar ya rasu. Miji ya rasu ranar daurin aure sannan a sami amarya da ciki. Ai ko a iya nan aka barta ta kafa tarihi a rayuwa wanda duk mutumin da ya santa idan suka hadu sai ya tuna. Ga 'ya ta haifa itama nan gaba tana kara wayo zata iya bukatar jin waye ainihin babanta. Idan kuma marasa tausayi cikin mutane suka goranta mata yanayin haihuwarta ko na sakan daya ne sai ta tsani mahaifiyar da ta sha wahalar rayuwa don ta haifeta. Babu dan da yake son jin shi shege ne. Sannan ga soyayyar wani Allah Ya dora mata amma saboda abinda ya faru a baya idan tace zata bijire ma kallon mara kunya kuma mara godiyar Allah za'ayi mata. Allah Sarki Asmau da matan da suka sami kawunansu a yanayi shigen nata. Tuba da tawakkali shine kawai kwanciyar hankali garesu. Anti Bintu tana ta tunani har bacci ya kwasheta a zaune Asmau bata idar da sallah ba. Itama sai gabanin asuba ta soma baccin. Ana kiran assalatu ta tashi dama baiyi nisa ba. Ta shi Anti Bintu da 'yan matan da suka shigo dakin kwanciya tun tana sallah. Sai wurin bakwai na safe bacci mai nauyi ya dauketa. ***** A kitchen Umma ta rabawa kowa aikinsa na taron gobe. Gidan Mama zasuyi meatpie da doughnut. Nan kuma cake zasuyi da pepper chicken sai lemuka da za'a siyo. Har dakin Yassar taje ta bashi kudin abubuwan da zai siyo a fara aikin yace mata da zazzabi ya kwana. Yassar da bashi da kyuyar aike yau kirikiri ya nuna mata bazashi ba. Dama tun jiya ta kula yana wani cin magani ta rasa dalili. Bata san Col. Ishaq yake tayawa kishi ba tun kafin ya fara nasa. Dayake Shemau zata zo sai kawai ta kirata a waya ta fada mata abubuwan da zata taho dasu. Ta fito tana mitar tasan Yassar kalau yake Anti Bintu tayi dariya. "Indai Yassar ne ranar daurin auren ma yana iya kirkiro ciwo. Don baki san irin shakuwarsu da Ishaq bane." "Ke kuma naga alama abin yayi miki dadi. Ni duk a yaushe ya tara masoya a gidan nan ne ban sani ba?" "duk abinsa ai dole yaji kunyarki. Don baki ga yadda mukayi dashi a Zaria ba. Hatta babansu Dijah sun sha hira sosai. Tamkar 'yan uwansa haka ya dauke mu. Gashi yanzu kun zo kun raba" Umma ta rike haba tana kallon kanwarta. Da gaske Bintu ta zama 'yar kamfen "kun mayar dani wata boss dai. Gani kuke yi kamar bana son Asmau. Bari ayi auren ku gani idan suka fara zaman lafiya. Yau fa ko gaisheni bata fito tayi ba." Anti Bintu tace "bacci take yi, jiya kwana tayi tana sallah da kuka" Hajjo dake tsaye a bakin kofa tana musu dariya tace "ta kwana sallah kika ce, to ni dai babu ruwana Bara'atu da Garzali ne suka yanke shawarar. Allah Yasa dai bata ambaci sunana a adduar ba. Ko dai na tasheta na tambayeta ne. Kunsan addua ba abin wasa bace" Duk su biyun dariya suka yi. Daga falo suka ji shigowar Zubaida da Sabira. Har kitchen din suka zo aka gaisa suna yiwa Zubaiba fadan dalilin zuwanta tace "Umma jiya banyi bacci ba tunda ya fada min gobe za'a kawo kudin Asmau. Mu dan shiga ciki akwai wani sirri da nake tsammanin bata fada miki ba" Anti Bintu tace "fadi a nan kawai, ba zancen Ishaq bane" Zubaida tace "wannan sojan ko. Ashe kun sani, to meyasa za'a hadata da Qasim?" Hajjo tace "kinga matar auta, jeki ki bawa 'yar uwarki baki kawai. Maganar nan an gamata tun jiya. Allah Ya sanya mana alkhairi" Jikin Zubaida duk sai yayi sanyi. Mata nawa ta gani a gidan Uwargida wadanda suka ce auren dole ne ya fito dasu daga gidan iyayensu. Allah Yasa Asmau ta iya hakuri dai. Ko sau daya Asmau bata fito daga daki ba. Abinci ma Dijah ce ta kai mata. Amatullah da bata iya komai idan Umminta bata walwala itama a dakin ta zauna. Har su Shemau suka zo yara sun cika gidan amma taki fita sai nanikar jikin Asmau take yi. Col. Ishaq yayi ta kiranta ta daure ta dauka tace masa baki ne a gidan yau duk ya cika. Har su Anti Bintu sun zo. "To bazan takuraki ba kije kuyi hira zuwa dare sai muyi magana. Ki gaishe min da Yayata Bintu" Tana ajiye wayar sai kuka. Yanzu da tasan za'ayi mata katanga dashi tafi jin sonsa ma a zuciyarta. Duk bayan dan lokaci kadan sai tayi mata text mai cike da kalamai masu ratsa zuciya. Shemau tazo tayi ta rarrashinta akan ta hakura ta karbi wanda Allah Ya zaba mata. Gudun kada su dameta yasa ta dan sake tana amsa musu idan an sakota a hira. Sunyi aikinsu sun gama zuwa yamma. Washegari kawai ake jira mutanen Shanono su iso. A daren ranar Ainau da bata sami zuwa tayasu aiki ba ta kirata harda kukanta. Ta kira Umma tana rokon kada a hana yayarta wanda take so. Umma dai ta rasa yadda zata yi. Duk sun hade mata kai. Jafar ne ma bai nuna ga wanda ransa tafi so da Asmau ba. Uban gayya ASP Qasim shima sai dare ya kira Asmau. Kana jinsa kasan yana cikin farinciki yace "Asmau kinga ikon Allah ko. Ina sanar da su Baba maganarmu suka ce kawai azo ayi komai. Ina fatan hakan zai karan kwantar miki da hankali kisan cewa komai ya wuce." Zuciyarta har wani zafi take yi don bacin rai ta daure tace "babu komai Yaya Qasim, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi" Yaji dadin furucinta "Amin Asmau, goben zanzo nima. Idan sum gama nasu sai mu fara tsara bikin. Sai da safe ko gimbiyata" Ta kakalo murmushi tayi "to sai da safe" ta ajiye wayar ido na cikowa da kwalla. ***** Washegari da wuri gidan ya cika kamar masu shirin biki. Yaya Abu da Anti Lami sun zo, Mama da 'ya'yanta mata harda matar Abdulhalim. Sai Aina'u da Shemau da Sabira. Falon aka share aka tura kujerun baya aka shinfida wani kafet din ko da wurin zaman zaiyi kadan. A bangaren maza ma akwai masu zuwa ta bangaren Hajjo da maigidanta sai Kawu Garzali da abokansa biyu. Ga mazansu Anti Lami da na Anti Bintu. Banda kuma gayyar Alh Adamu. So suke su nunawa dangin Qasim suna son 'yarsu kuma ita din 'yar dangi ce. Tun safe Asmau ta kashe wayarta don bata san me zata cewa Jikamshi ba idan ya kirata. Adduarta kada yazo ana tsakar taron. Yau ma a daki ta zauna sai dai 'yan uwanta su shigo tayata hira. ***** Ana la'asar mutanen Shanono suka iso gidan Alh Adamu. Daga nan suka dunguma zuwa gidansu Asmau. Mota biyu suka ciko da nasu 'yan uwan. Qasim dama ya rigasu zuwa ya sai zauna a cikin gidan idan taro ya watse zaije ganin Asmau gimbiyarsa. Kafin su iso Umma tace Asmau ta tafi gidan Jafar tare da wasu cikin 'yan matan tace kanta na ciwo bazata iya fita ba. Umma tayi murmushi kawai ta rabu da ita. Sauran suka tashi aka jera komai a falon sannan suka koma ciki suna hira a dakin Hajjo saboda yafi fadi. Asmau na kwance zazzabin dole ya rufeta taji hannuwan Amatullah sun rike mata wuya ta baya. Tun jiya taki sakewa itama. Idan ta korata tayi wasa bata dadewa take dawowa wurin Umminta. Murmushi tayi tana kokarin cire hannunwan don rikon ya danyi karfi "Ama sake min wuya mana" Jin tayi shiru yasa ta juyawa sosai. Amatullah ta gani tana kokarin numfashi bakinta a bude. "Subhanallah" ta fada a rude tana dagata. "Ama ki rufa min asiri, wayyo Allah" Gabadaya ta manta da inhaler din da aka basu a asibiti ta dauketa sai dakin Hajjo. Kuka take yi sosai tun kafin ta shiga su Umma suka fara fitowa saboda muryarta da suke ji. Ganin Amatullah na numfashi da kyar Shemau ta karbeta Sabira kuma ta kira Jafar a waya. Lokacin Umma har ta dauko mukullin tata motar. Yassar baya gidan shi tun safe ya fice. Sabira na fadawa Jafar ya tashi da sauri. Lokacin an gama gaisawa da dangin Qasim kenan. Abdulhalim ya tambayeshi abinda ya faru ya fada musu. Kowa sai salati suka tashi don ta nan su Umma zasu wuce. Kafin kace meye wannan suna mota Asmau ta cire dankwali sai hijabinta kawai tana yiwa Amatullah fifita. A can gidansu kuma Alh Adamu ya gama gigicewa. Yana matukar son jikarsa shiyasa hankalinsa ya tashi. Karshe yace don Allah suyi hakuri zai bisu asibitin. Idan komai ya lafa sai su karasa abinda ya tara su. Duk da wasu basu ji dadi ba to amma lafiya tafi komai. Haka suma aka samu wasu cikinsu suka bi bayansu aka tafi asibiti. Ainau ce ta kira Yassar ta fada masa. Kafin ya karasa asibitin ya kira Col. Ishaq ya sanar dashi da kuma sunan asibitin. Shima hankalinsa a tashe ya tafi. Dama yayi ta kiran wayar Asmau yau baya samu. Niyarsa bayan magariba yaje gidan. ***** Emergency suka kaita nan da nan likitoci suka fara aikinsu. Sun tabbatar musu ba abin damuwa bane asthma dinta ce ta tashi amma abin baiyi tsanani ba. Ana ta rarrashin Asmau ta kasa shiru. Dama can hankalinta ba a kwance yake ba. Suna nan aka canza mata daki lokacin numfashin ta daidaita ta sami bacci. Qasim ya shigo dakin aka gaisa ya duba Amatullah ya fita. Bai dade da fita ba Jafar yace taje waje Qasim na kiranta. Bata son nunawa mutane rashin son auren shiyasa ta fita ta same shi. Kokarin kwantar mata da hankali yayi tace ta gode. Suna nan tsaye Col. Ishaq ya iso. Tunda idonsa ya gano masa Asmau da Qasim yaji wani bacin rai sai dai jikin Amatullah ne a gabansa. Daya karaso suka gaisa da Qasim. Itama ta gaisheshi sai ya shareta kawai. Tana kallo Yassar ya fito ya kaishi dakin ya duba Amatullah. Kasa nutsuwa yayi ya fito ya dawo inda suke. Gaban Asmau sai faduwa yake yi. Yana zuwa yace "Naga dakin a ciki da mutane da yawa. Tun yaushe ta fara ciwon ban sani ba?" Qasim ne ya bashi amsa "ko awa daya ba'ayi ba. Mutanen ciki 'yan uwana ne dana Asmau. Kayi hakuri naso sanar da kai ma abin ne yazo a kurarren lokaci." Idon Col. Ishaq akan Asmau yace "wane abu kenan?" Da dan murmushi Qasim yace "kawo kudi aka zo sai ciwon Amatullah ya tashi" Guntuwar fara'ar fuskar Col. Ishaq tuni ta bace "kudin aure??? Na wa?" Kirjin Asmau sai bugu yake da karfi don tsoro. Gashi yq tsareta da ido. Qasim yace "kin barni ina ta magana ni kadai ko, wallahi daga fadawa iyayena kawai sai suka yanke shawarar gara ayi komai lokaci guda. kudin *aurenmu* aka zo kawowa." Sabanin bacin ran da tayi tunanin gani a fuskar Jikamshi sai taga yayi dan murmushi "Kasan mata da kawaici da kunya. Musamman ma dai _Matar Jikamshi_. Asma'una baki fada masa muna soyayya bane?" Qasim ne yaji kamar an sauke masa guduma a kansa. Sai ya kalli Asmau da tayi mutuwar tsaye sannan ya kalli Col. Ishaq wanda yake binta da kallo mai nuni da tsantsar soyayya kamar ya sanyata a jikinsa. Daga bayansu Yassar ne yazo kiran Asmau ya fada mata Amatullah ta farka. Jin abinda Col. Ishaq ya fada yasa shi daka tsalle ba shiri. ABINDA AKE GUDU🙆🏽43 Batul Mamman💖 Shiru suka yi gaba dayansu sai Col. Ishaq da yake murmushi kamar bai san abinda yayi ba. Shi kuwa Qasim nema yake maganar da yaji ta gama shiga kwakwalwarsa. Ihun tsallen Yassar ne yasa duk suka kallo inda yake. Baiyi wani dogon tunani ba don kada a gano shi ya durkusa kasa tare da rike kafarsa ta hagu "Wayyo Allah wani abu ne ya cije ni" Asmau tayi kansa da sauri dama neman hanyar da zata bar wurin take yi don ji take kamar idan ta kara minti daya itama sai dai a bata gado kusa da Amatullah saboda irin bugun da zuciyarta take yi. "Mu gani a ina ne?" Ya dago kansa yana kallonta, duk sai ta bashi tausayi. Karyar kafar ma saboda ita yayi "Barshi kawai bari na cire takalmin. Kije Amatullah ta tashi tana kuka" Kamar an harba walkiya haka ta bar wurin ko waigowa baya bata yi ba. Qasim da Col Ishaq suka dawo kusa dashi suna tambayarsa abinda ya sami kafar. "Ji nayi kamar abu ya cije ni. Ku shiga ciki Amatullah ta tashi." Qasim ya dawo hayyacinsa daga abinda Col. Ishaq ya fada har ya yiwa Yassar sannu harda kokarin cire masa takalmin zai taya shi duba kafar. Yassar yayi saurin jan kafar yana mai jin kunyar karyar da yayi "ya dena ciwon, zan karasa motar Umma ina da silifas a ciki ina jin cinnaka ne ya shiga." Daga haka ya samu Qasim ya shige. Kafin ya mike tsaye yaji an kama wuyan rigarsa an tayar dashi. Ba don yasan wanda ya rike shi ba sai yayi ihun gaske. Col. Ishaq yayi 'yar dariya yana kallonsa "ka kyauta da ka taimakawa yayarka don sauran kadan ta suma a wurin nan. Har na fara tunanin me zan fadawa su Umma" Shima Yassar dariyar yayi yana murza wuyansa "haka kawai kun sata a tsakiya. Ga soja ga dan sanda da wanne zata ji" "Laifinta ne da tasa duk muka kamu da sonta. Allah Yasa kada ta kwaso mana lauya ko alkali kuma." Murmushi Yassar yayi tare da jin kunyar amsar da aka bashi. Shi dai komai na Col. Ishaq yana burge shi. Ina ma ace shi zai aureta. Ba kuma don baya son Qasim ba sai dai wannan maganar aure ce. ***** Asmau na shiga dakin Amatullah ta dena kuka. Kan gadon taje ta zauna tana yi mata fadan dalilin kukan don bata ganta ba kamar bata san sauran mutanen wurin ba. Mama tace "kiyi mata a hankali Asmau. Yarinyar nan taji jiki. Haka muka sha fama da Abubakar da yana yaro. Idan ta kara wayo zata san yadda zatayi ta rinka kiyayewa sai kiga attacks din basa zuwa sosai." 'Yan uwan Qasim suka ce zasu tafi sai dai su dawo wani satin. Alh Adamu yayi ta basu hakuri yace tunda Amatullah taji sauki suna iya komawa a karasa. Hakan ya razana Asmau sosai ta shiga rarraba idanu taji me Jikamshi zai ce. Sai tayi sa'a yayi kamar baya jinsu. Su din ma sun nuna babu damuwa tunda yamma tayi zasu sake saka rana. Ita dai Asmau ko kallon Qasim din ta kasa. To da wane idon zata kalle shi bayan abinda Jikamshi ya fada masa. Shi a rayuwarsa ta kula baya jin shakkar fadin magana ko a gaban waye indai yana tunanin akan gaskiyarsa ne. Gashi yau ya fadi maganar da tasan dole Qasim ya kullaceta a ransa. Shima a nasa bangaren gani yayi gara ya kyaleta saboda asibiti ba muhallin maganar bane. Sannan ga Amatullah babu lafiya yanzu ko me zata fada masa zai zamto babu nutsuwa a tare da ita. Tare da su Alh Adamu suka fita raka 'yan uwansa zasu biya gidan Umma su dauko sauran. Kayan ciye ciye da aka tanadar musu Umma tasa Sabira da Shemau su bi bayansu sai su hada a basu su tafi dashi. ***** Suna zaune har akayi magariba sannan su Umma suka tafi aka bar Hajjo da Asmau. Kayan kwana za'a hadu musu sai Mama ta dawo su kwana tare. Col. Ishaq yana dakin amma shima yaki kallon inda Asmau take, shima bata da abin fada masa. Ba don ciwon Amatullah ba da yanzu an gama magana tsakaninta da Qasim sai batun saka rana. Biyewa Amatullah yayi tana ta shagwaba son ranta, sai Hajjo dake dan yi masa hira itan ma kunyarsa take ji tunda tasan komai. Duk yadda Asmau taso su hada ido yaki. So take ta bashi hakuri tunda tasan yanzu bata da sauran mafita. Karshenta kafin sati ya zagayo ma mutanen Shanono su sake dawowa. Shigowar Jafar da Qasim yasa shi tashi yayi musu sallama ya fita. Damarta kenan ta bashi hakuri a yau tunda wayarta tana gida. Bai dade da fita ba tace zata je tambayar likita ko zata iya bawa Amatullah abinci. Jafar yace ta bari yaje ta wayance "barshi Yaya Jafar so nake na dan fita na gaji da zaman wuri daya" Shi kuwa Qasim tuni ya gane inda take son zuwa sai kawai ya dauke kansa. Yana kallo ta fita cikin sauri don kada ya bar asibitin kafin ta karasa wajen. Tana fitowa ko alamunsa babu ta kara sauri harda dan gudunta. Tsoronta bai wuce kila daga yau yaki dawowa ba. Garin sauri tabi wata hanyar da zata kaita wurin ajiye motoci ta kusa karo da mutum har sai da taji tsoro saboda rashin wadatar haske a wurin. Tsaye yake ya sanya hannuwansa a aljihun wando yana kallonta. Kallo ne na tuhuma wanda har ranta sai da taji babu dadi don bata kyauta masa ba. Bai motsa daga inda yake ba yace "me yasa kika wahalar da kanki da yin gudu bayan kinsan dole zan jira fitowarki. You have alot of explaining to do" Fuskarsa yau babu fara'ar nan da take kara saka mata sonsa. Yau a sojansa ya fito sai ta daburce ta rasa ta ina zata fara bayani. "Kinyi shiru, na tafi ne?" "A'a don Allah kayi hakuri" sai ta soma kuka. "Matar Jikamshi" sai yanzu ta danji sanyi a ranta saboda yadda ya kirata. A hankali ta dago ido ta kalle shi. "Why?" Ya tambaya shima duk dakewarsa yana jin babu dadi. Idan ya rasa Asmau gani yake bazai taba samun madadinta ba. Yana mamakin irin wannan so da yake mata wanda ya shige shi lokaci daya. Idanunta cike da hawaye ta soma fada masa yadda abin ya faru." Kayi hakuri da ban sanar da kai ba. Babu yadda zanyi ne tunda duk iyaye sun amince" Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa." Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana sonsa fiye da yadda take tsammani a baya. "Jikamshi to yaya zanyi?" Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a cikin 'yan shekaru. "Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara. Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai. Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da Safina. Atleast ko school fees dinta ku bari ya zama responsibility dina." Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu shikenan?" Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike amana kamarsa ba" "Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne." "Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara." Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen. Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da yake mata. A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace "Jikamshi ina sonka" a hankali Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka. Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna "Matar Jikamshi kina so na hakura dake"? Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi. "To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi amfani." Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa. Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a daura auren" Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka nake yi ba." "Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu ajinki daban ne" Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta tace "zama da kai ne" "Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin kasa hakuri kin biyo ni. " Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A daidai inda suka gama magana yaga kamar alamar mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi. Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col. Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin. ABINDA AKE GUDU🙆🏽44 Batul Mamman💖A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi. ***** Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya. A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar. "ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare? "Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka" "Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu." Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa" Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa "Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?" "Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?" Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau. "Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye." Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba" Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa. "Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna" A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne." Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka" "Goro maigadon zinare" Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo" Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna

Chapter 16 of 23