Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta hadasu kayan amfanin jiki ne. Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene kuma Asmau?" "Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma ....." Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka. Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan dabaru na mutane basa taba zama daya. "Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki matsalolinki na baya." Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda 'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya. ***** Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo. Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai, Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya. Asmau ta zauna ta hada abinci mai rai da lafiya wanda ya dace da tarbar bako. Bata taba yi masa abinci ba. Idan yazo lemo kawai take bashi da snacks saboda tana kunyar irin wannan. Yau ma Umma ce ta bawa Yassar kudi akan a siyo abubuwa na abinci yau kwadayi take ji. Tasan yau Ishaq zai dawo amma saboda kunya Asmau bazata yi yunkurin yi masa wani abu daban ba. Itama kuma hakan yafi mata. Bata taba bawa 'ya'yanta kofar idan saurayi zai zo ayi ta girke girke kamar maigida ba. Sai kaga 'ya'ya basa kunyar iyayensu. Bayan ta gama Umma tace "ki dibarwa Ishaq mana kinsan matafiyi kila yayi sha'awa." A kunyace ta diba ta ajiye masa nasa. Da ya iso Amatullah ta dafe shi tana ta murnar ganinsa. Yayi musu tsaraba ta doya da sauran abubuwan kudancin kasarmu. Idonsa kyam a bakin kofa har Asmau ta fito. Ji yake inama dai anyi auren. Yayi kewarta sosai, ga wani haske da kyau da ta kara saboda mayuka da sabulun gyara jiki da Zubaida ta hada mata da kanta. Itama ganinsa ba karamin dadi yayi mata ba. Tana zama yace "Yi a hankali kada na narke da wannan kallon da kike yi min" Sam ta kasa boye murnarta shiyasa yake ta tsokanarta. Da ta gaji da kunyar ta soma ramawa. Yaci abinci ya kuma yaba da iya girkinta. Daga nan ne suka dasa hira har ta fada masa cewa ita dasu Umma zasu je Azare da Jos nan da sati daya. "Wannan tafiyar dani za'ayi in sha Allah. Dole naje har gida na godewa mutanen da suka taimaka wurin kare min martabar iyali." "Kuma har gidan Uwargida zamu je. Umma tace dole Zubaida ta ga mahaifiyarta" "Tabbas uwa komai munin halinta ba'a canja mata suna. Kila kiga rabon shiriyarta ne idan taga 'yarta tayi aure har da 'ya'ya. Ki fada min da wuri ranar da aka yanke yin tafiyar sai na shirya da wuri." Ta danyi ajiyar zuciya "Yaya Qasim ma yace zashi" Murmushi Jikamshinta yayi "Matar Jikamshi bazan taba rabaki da Qasim ba. Ina son halayensa kuma nasan mutum ne nagari. Ko jiya munyi waya dashi. Yasan Asmau matar Jikamshi ce wannan ya isheni kwanciyar hankali. Ke dai Allah Ya kaimu muje mu dawo a fara biki " ABINDA AKE GUDU🙆🏽51 Batul Mamman💖 Shirin tafiya sosai suke yi. Umma ta nemi Shemau da Jafar su kawo abinda ya sauwaka wanda zasu kaiwa mutanen Azare da Jos tsaraba. Duk da bata san Zulaiha ba amma ta yaba da taimakon da tayiwa Asmau. Sune suka rufawa 'yarta asiri ba don haka ba Allah kadai Yasan irin rayuwar da zata tsinci kanta a ciki yanzu. Shemau dai katan din taliya hudu ta kawo da maggi. Shi kuma Jafar galan din mai da katan din macaroni bibbiyu. Suna zaune a falo ana ganin kayan tana saka musu albarka. Idon kuka sai da tayi sana'ar tata kafin tayi godiya. 'Yan uwanta sun rufa mata asiri. Bata san mata nawa bane irinta a duniya wadanda kyama da hantara ta dangi ta kara tura su ga aikata sabo. Umma tace "na bawa Yassar ya siyo min buhun shinkafa biyu sai a bawa su Rashida daya ita ma Zulaiha daya." Asmau ta kara yi musu godiya "nima zan duba cikin kayan da kuka bani wanda ban dinka ba na daukar musu." "Hakan yayi kyau" inji Hajjo "kai Yassar ina naka ne? Ka zauna sai washe baki kake yi ban ga wani abu daga gareka ba" "Hajjo ni da ban fara aiki ba ina ni ina gudummawa. Ai ma na kyauta tunda zan tuka mota." Sai ya kara fadada murmushinsa "ashe da Yayanmu za'ayi tafiyar." Shemau tace "haka Umma ta fada min. Ni fa har kunyar Qasim nake wallahi. Nutsuwarsa tayi yawa. Gashi dai bashi zata aura ba amma ko kadan bai bari hakan ya zama sanadiyar bacin zumunci ba" Yassar ya dan tabe baki "au shima zuwa zaiyi? Ni da mutumina nake yallabai baban Amatullah" Umma ta rike haba "oh ni Bara'atu, nagode Allah a namiji kazo Yassar da ina tsammanin sai kunyi fada da yayarka. A take takenka da gani zaka iya kwacen saurayi. Idan Ishaq yazo gidan nan aka yi rashin sa'a kana nan kayi ta rawar kafa kenan. Jiya ina jin ku kana mita wai Asmau taki fitowa da wuri" Dariya suka yi, Yassar ya sosa keya "wallahi Umma burgeni yake yi. Nifa gaskiya idan an gama bikin nan zan nemi short service nima na zama soja. Baki ga ba idan yana tafiya ko magana....kai" Hajjo tace "anya Bara'atu kin tabbatar yaron nan namiji ne ba mata maza ba?" Su Jafar sai dariya Yassar ya tashi yana tura baki. Shi ba'a kyauta masa ba. Yabonsa fa kawai yayi saboda ya burge Asmau. Da taga anyi masa taron dangi sai ta koma bayansa tana kare masa. Yace "rabo dasu sai sun ga matar da zan aura ma sis. Kowa sai ya yaba harda tsohuwa mai ce min mata maza" aka sake dariya. ****** Lokacin da Col. Ishaq ya fadawa Hajiya zaiyi tafiyar nan dasu Asmau ta dage itama sai taje. "Ke da kike fama da kafa Hajiya" "Kada kaga laifina. Ba wai na karyata abubuwan da Asmau ta fada mana bane amma ance gani ya kori ji. Kai sonta kake da aure ni kuwa son 'ya nake mata. Ina so idona ya gane min inda ta rayu kafin haduwarku. Ina son samun hujja ga mutanen da tuni suka fara kawo min sukar auren nan. Da yawa cewa suke karuwanci tayi lokacin da ta bar gidansu. Bazan tura kowa a dangi ba bare a sami na gutsiri tsoma. Kai dai kawai ka hadani da dreba idan motarka ta cika" Ji yayi jikinsa yayi sanyi. Mutum ba'a iya masa. Mahaifiyarsa kuma da gaskiyarta. Da yana da yayye kila su zata wakilta tasan bazasu yi mata karya ba. Kuma gara taje din akan ta tura wani. "Shikenan Hajiya Allah Ya kaimu. Bilkisu sai ta koma gidan Safiyya ko su Dahiru" "Tare zamu je kasan rabonta da gida tun haduwarmu da Asmau. Ita ma gara taje ta kwana biyu kafin bikin tunda ta gama jarabawa" Da ya kira Asmau ya fada mata ko kadan bata nuna damuwa ba. Har zuciyarta dadi taji ko babu komai idan akwai wani zargi da yake ransu zasu ganewa idanunsu cewa ba karya tayi ba. Ranar da zasu tafi sammako suka yi. Yaran Shemau duka ta kawosu gidan Umma zasu zauna da Amatullah da Hajjo. Asmau da ita taso tafiya Shemau tace gara ta barta ta fara sabawa da rashin ganinta saboda idan anyi biki sai kamar bayan sati biyu ko uku za'a kawo mata ita. Ta dai amince don babu yadda zatayi ne. Basu saba rabuwa da juna ba. Wani abin ma sai sunje kwanciya ta mayar da kanta yarinya ta biyewa Amatullah suyi ta hira tana sauraron shirmenta. Burinta ta dasawa kanta babban matsayi a zuciyar Amatullah yadda nan gaba yarinyar bazata nuna mata kyama ba idan taji tarihin haihuwarta. Soyayya kuwa zata nuna mata hadda wadda take tunanin da Abubakar yana raye shima zaiyiwa 'yarsa. Allah Sarki bai ma san da cikin ba bare haihuwarta. Sun gama loda kayansu a motoci aka fara shiga. Asmau, Bilkisu da Zubaida suna motar Jafar da yaran Zubaidan. A motar Umma kuma kawu Garzali ne a gaba Yassar zai tuka. Baya ita da Mama ne. Shi kuma Col.Ishaq drebansa ne zai tuka su. Yana gaba a baya kuma Hajiyarsa da Shemau. Tun zuwansu gidan ya samu Asmau ta dan fito kafin a fara shiga mota "yanzu ina kallo zamu je wuri daya amma ba motarmu daya ba? Wannan tsarin baiyi ba gaskiya ki dawo motarmu Shemau ta koma ta Jafar. Wa zan rinka satar kallo ta madubi" Zaro ido tayi "sai na zauna kusa da Hajiya don rashin kunya kai kuma kana kallona?" Yace "to meye a ciki? Naga auren danta zakiyi karewa." Ta kawar da kai tana murmushi "ni dai kayi hakuri don Allah kada a fito ka fara cewa na dawo motarku. Kada ka sani jin kunyar da ban shirya ba". "Dama kina da kunyar ne? Ana shirin tafiya kin kasa hakuri kin fito ki ganni" Asmau ta rasa me zata ce sai bude baki kawai da tayi cikin mamaki. Shine fa yayi mata waya yana magiyar ta zo ya ganta. Dariya yake mata don yasan ya kureta "rufe bakin kada ya makale a haka" Ta dan juya ido "gara ya makale kowa ya huta" "Tuba nake Matar Jikamshi, shi bakin nan naki da kike gani ba karamin mahimmanci gareshi ba. Idan ya makale an cuce ni." Ta soma dariya ganin yadda ya kara marairaice fuska "meye amfanin bakin banda cin tuwo. Idan ya zauna a haka kaga na dena shan wahalar bude shi" Yace "da gaske kina so na fada miki kadan daga cikin mahimmancin bakin Matar Jikamshi" Wani jan zancen yake yana kallonta kasa kasa. Ko baa fada ba tasan ko me zai fada karshenta sai taji kunya shiyasa ta saka hannuwanta biyu ta toshe kunnenta tana ja da baya. "Ka barshi kawai na yafe. Wani ilimin ba sai na sani ba" Yayi murmushi mai kyau "kaji min yarinya. To ba abinda kike tunani zan ce ba. Shiyasa nace kinfi karfina dama" Sosai Asmau taji kunya ta koma ciki da sauri tana jiyo dariyarsa. Yanzu da suka shiga motocinsu zasu tafi ji yake ina ma motarsu daya. Ko yaya suka juya su kama juna suna kallon junansu. ***** A titin Zaria road suka hadu da Abdulhalim da Qasim a motar Qasim din. Daga nan suka mika sai Azare. Tun fitowarsu Zubaida ana ta hira a mota amma jikinta yayi mugun sanyi. Ba don Umma tayi mata nasiha sosai ba ita ko kadan bata son tuna asalinta. Yanzu duk mutanen nan kowa sai ya ga a irin kazantar da ta tashi. Addua take Allah Yasa kada su je su tarar da irin tsofaffin yan tashan nan da basa tsoron Allah masu zuwa wajen Uwargida a dakin. Sai su zo suce wai banda tsufa ya fara zuwar mata duk tafi yaranta iya aiki. Wani sa'in ma idan taji kudi sosai komai kuruciyar mutum bata jin komai take bashi dama. Koda yake ina wata kunya ga mace irin wannan. Motarsu ce a gaba Zubaida tayiwa Jafar kwatance. Su Asmau ma jiki ya mutu suka dena hirar saboda ganin yadda yanayinta ya canja. Asmau tana zancen zuci tace kada Allah Ya kawo ranar da Amatullah zata kyamaceta irin yadda Zubaida take yi a yanzu. Gidan yana nan yadda yake ko fenti ba'a canja ba. 'Yan bakin kasuwa suna kallon abin mamaki. Motoci irin wadannan a kofar gidan Uwargida. Kuma gashi harda mata bare ace wasu kadangarun barikin ne suka zo neman 'yan matan gidan. Asmau da Zubaida aka rasa me fara shiga. Ita Zubaida ma hawaye take yi har Kawu Garzali ya gani. Da sauri yazo ya karbi baby dinta mai suna Shuaibu suna kiransa Aiman sannan ya rike hannunta suka fara shiga. Zuciyar Asmau ta tsinke, yanzu haka Jikamshi zai shiga gidannan. Allah Yasa kada shi ko Hajiya wani yace a fasa auren. Zuga guda suka shiga da sallamarsu. Matan a gaba maza a bayansu. Kaya ne tarkace kala kala a tsakar gidan. Wasu matan na wanki wasu suna girki. Kowacce da sabgar gabanta. Kadan a ciki Asmau ta gane. Duk barin abinda suke yo suka yi kallo ya dawo kan baki. Daga kofar dakin Uwargida Bulayi ya fito. Mutumin da ya fara kawota gidan nan. Dama can a dattijo ta san shi. Yanzu kuwa tsufa ya kara bayyana a tattare dashi. Yana kokarin zura takalmansa ne idonsa ya sauka akan Zubaida. Fuskarsa ba karamin mamaki ta nuna ba yace "Zuby???" Ranta a dagule yake dama ta harare shi "Zubyn uwarka" a duniya yana cikin mutanen da ta tsana. Duk yarinyar da aka kawo gidan sai yayi amfani da ita kafin kasuwarta ta bude. Maimakon ta ga bacin rai a fuskarsa sai ya washe baki cike da fara'a yace "Shegiya ita ce kuwa, kina nan da bakinki kamar reza" Cikin dakin ya koma da sauri har yana tuntube. Suna jin muryarsa yana kiran Uwargida tazo ga Zuby ta dawo. Zubaida ta ji muryar mahaifiyarta tana cewa "Bulayi kada kayi min wasan da zai tayar min da hawan jini" "Yasin da gaske nake, bari na kamaki muje wajen" Kunya ta kara kama Zubaida, yanzu haka zasu fito hannu da hannu kamar wasu mata da miji a gaban mutanen nan masu daraja a idonta. Dukkansu kallon kofar suke zasu ga wannan Uwargidan ga wadanda basu taba ganinta ba. Bulayi ne ya fara fitowa hannunsa rike da sanda yana cewa "yi hankali da matattakalar kofar" Rike da sanda ta fito wacce Bulayi ya daga mata daga waje yana mata jagora. Tana nan da tsayinta fuskar nan tayi wani irin dabbara dabbara saboda mayukan bleaching da taji a baya. Sanye take da tubarau baki wuluk irin na makafi. Tana mika hannu cikin iska alamar lalube tace "Zuby kina ina?" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zubaida bata san lokacin da ta saki hannun Kawu Garzali ba ta tafi wurin babarta tana kuka "Mama makancewa kika yi? Wayyo Allah na, kinga ni fa jikokinki na kawo miki nayi aure. 'Ya'yana hudu. Mama ki bude ido ki gansu don Allah" Uwargida tayi dan murmushi tana rungume da 'yarta. Hawaye ya zubo mata tana ta shafa fuskar Zubaida tace "Ashe zamu gana kafin na mutu Zubaida. Allah nagode Maka. Ina yaran? Wane dan albarkan ne ya rufa min asiri ya aureki? Kinga yadda Allah Ya mayar dani ko. Karyar karuwanci ta kare bani da wani mataimaki sai Allah sai Bulayi da bai gujeni ba" Zubaida ta kalle shi sai taji kunyar zagin da tayi masa. A yadda taga mahaifiyarta ta kara tsufa da yankwanewa sai ta godewa Allah da Umma ta dage lallai sai tazo. Bulayi ne yace "Uwargida tare da baki take fa. Ina jin surukanta ne mu shiga daga ciki ko kuma ina zuwa dai" dakin ya koma ya dauko tabarmi gudu uku. Kamar hadin baki Qasim da Col. Ishaq suka ki zama. In da sabo tsayuwa ba komai bace wurin soja da dan sanda. Sai akayi dace kyamarsu tazo daya basa son zama a tabarmar da ta fito daga dakin matar. Sauran dai sun zauna sannan Zubaida ta fara yi mata bayanin kowa. Yaranta kuwa sai da Uwargida tabi tana shafasu tana binsu da kiss a fuska. Manyan biyu mace da namiji dai kyankyaminsu suke. Tana yi suna gogewa duk ta yaba musu yawu. Da Zubaida tace tare suke da Asmau Uwargida ta mika hannu zata kamata. Balayi yace "Yar dabas kin canja Yasin. Jikinki duk ya murje kinyi fresh. Dama naso naga kama to kuma sai naga ta yanzu tafi ta da kyau da daukar ido." Wani mugun kallo Col. Ishaq ya sakar masa wanda ya girgiza har hanjin cikinsa. Ba arziki yayi shiru. Asmau ta dan matsa gaba Uwargida ta kama hannunta. "Nayi sanadiyar lalacewar 'ya'yan mutane da yawa Yar dabas, iyayenki har nan sun zo nemanki. Nagodewa Allah da baki kama sa'a kamar yadda naso ba. Hakkin wadancan shegun kadai ya isheni. Ni shaida ce akanki har kika bar gidannan namiji bai taba zuwa kofar dakinki ba. Ke kam kinji dadi 'yan uwa basu kyamaceki ba har Allah Yasa rayuwarki ta koma kan layi. Me kika haifa? Tausayi Uwargida ta rinka basu. Asmau ta soma kuka saboda yadda ta tuna Uwargida da iya gayu duk girmanta. Yanzu kuwa sai da dauriya zaka iya zama kusa da ita saboda warin jiki. Su Umma sun gama gaisawa da Uwargida sai Haj Lubabatu ta dan yunkura zata tashi. Col. Ishaq yace "Hajiya kafar ce?" Bata bashi amsa ba sai matsawa da tayi gaban Uwargida ta zauna kusa da Zubaida tana kare mata kallo. Kuka sosai ya kwace mata tace "Habiba" Uwargida ta fara mika hannu inda taji kira. Rabonta da amsa wannan sunan tun ranar da ta baro garinsu. Hannunta har rawa yake tana ta mika shi ko zata kama mai kiran tace "wace ce don Allah, babu wanda yasan sunana sai 'yan garinmu" Hajiya sai kuka ta kara shigewa kusa da Uwargida. Col. Ishaq ji yake kamar ya janyota. Me ya hadata da wannan matar. Hannuwanta duka biyu ta rike "Lubabatu ce, Luban gidan Sarkin dorin Jikamshi" Salati sosai Uwargida ta saka kafin ta rungume Hajiya. Babu kyama Hajiya ta rungumeta itama suka barke da kuka. Kowa sai kallosu yake. Matan gidan sun fito ganin kwaf Qasim ya daka musu tsawar da ta kidimasu suka bar wurin suna karo da juna. Uwargida ta share majina da kasan zaninta tace "Allah mai iko, ashe zan sake ganin na gida. Luba ina Baba da Inna, ina 'yan uwana?" Cikin kuka Hajiya tace "Liman da Inna sun dade da rasuwa. Yayarki Indo ma babu ita. Sauran 'yan uwanki duk suna nan an tara 'ya'ya da jikoki" "Allahu Akbar, Allah Ya jikanku Baba, Allah Yasa sun yafe min kafin su rasu" Tana kuka ta labarta musu yadda almajirin Liman yayi mata ciki ashe ma fyade ne yayi mata kuma ya gargadeta kada ta fada har ciki ya bullo. Babu uzuri ko neman ba'asi iyayenta suka tsine mata. Wannan kuskure ne babba. Yana da matukar amfani jurewa wajen kula da yara idan sunyi kuskure domin a toshe kofar gaba. Tunda ta fiti take aikatau da ayyukan wahala domin taci abinci. A haka cikin ya bare tana yawo a gari. A wani gidan aikinta ne a Bauchi maigidan ya kuma yi mata fyade da ta fada matarsa tayi mata duka duk da lokacin shekarunta sunyi gaba don da jima tana rayuwar kunci da wahala. Maigida ya karyata kamar yadda aka saba ji. Shine da ta fito ta sami uwardaki. Bata zubar da cikin ba ta haifi Zubaida. Da girmanta ta fara sana'ar karuwanci kuma tace ta gwada rashin imani kamar yadda mutane suka gwada mata. Sai shekaru biyu da suka wuce da ta kamu da lalurar ido tayu nadamar rayuwarta. Duk matan gidan sun dena bata kudin haya ga rashin abinci. Ta kare da bawa mutane shawara da su rinka taimakawa masu raunin imani da wadanda ke cikin matsanancin hali don gujewa samuwar karin mugayen dabi'u a cikin jamaa. Su Mama duk anyi kukan tausayin labarin Uwargida da kuma dadin handala da Asmau tayi dacen haduwa da mutane nagari. Wannan kuma zamu iya cewa harda adduar da suke yi mata ba tsinuwa ko zagi ba. A gidan aka bar Zubaida da Kawu Garzali. Sun yanke shawarar idan zasu koma Kano a tafi da ita sai a kaita Jikamshi taga 'yan uwanta ko da basa maraba da dawowarta. ***** Daga nan gidan Rashida suka wuce. Dama tasan da zuwansu. Sada ma yana gida yana jira ga su Abba duk an zama samari. Cikin gidan aka yi musu shimfida mazan kuma suna dakin nan da Asmau ta taba zama. Tana shiga gidan sai kuka da ta tuna lokacin da ta zauna ga ciki ga rashin iyaye a kusa. A falo taga Sada ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yace "Asmau kece kuwa?" Tana kuka ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Sada ne mutum na farko da ya fara taimakonta a rayuwa sosai bayan Zubaida mai bata shawarar kada ta zabi gurbatacciyar rayuwa. Wurinsu Abdulhalim yaje inda aka ajiye musu kayan abinci. Sai da suka yi sallah suka ci abincin. A ciki suma matan sallar suka yi aka ci abinci. Nan hira ta barke ana tuna baya ana kuka da dariya. Rashida tace "yakamata watarana muje kiga Yaya Tagwai fa" Asmau tayi murmushi, Yaya Tagwai ai ta janyo mata kara shiga garari. Cikin yaran kuwa babu wanda ya tuna ta sai Abba. Sai da suka yi laasar a ranar dai suka kama hanyar Jos. Rashida da Sada sai lokacin biki zasu taho Kano. Sun sha tafiya jiki kuma ya fada saboda zaman mota. Duka matan a gidan Mami akayi musu masauki sai gari ya waye zasu gidan Zulaiha. Asmau ta damu sosai da ita saboda dena samunta da tayi a waya. Col. Ishaq ne ya samarwa mazan masauki a cikin barikinsu na sojoji dake garin. Shi da Matarsa sai dare suka sami damar yin waya aka biya bashin soyayyar da ba'a yi ba a ranar. Mami da yaranta sunyi kokarin karrama bakin Kano. Bilkisu sai murna anzo gida. Da safe wurin shadaya suka gama shiri aka dunguma zuwa gidan Zulaiha. Motarsu na tsayawa Asmau ta hango Humaira da karuwar roba a kanta cike da ruwa. Da sauri ta fito ta kira sunanta. Ai tuni Humaira ta saki robar ruwan ya kware a jikinta ta rugo da gudu ta dafe jikin Asmau. Sai ga kannenta suma duk ruwan suka. Yara sai murna suke suna tambayarta ina Ama. Kusan janta cikin gidan suka yi tawagarsu Umma suka biyo baya suna mamakin yadda yaran ke murna haka. A durkushe bakin murhu tayi tozali da Zulaiha tana ta hura wuta tana tari. Tsaye a gefenta kuma Zinaru ce ta harde kafa tana masifa "malalaciyar banza, tun dazu hada wuta ya gagareki. Yanzu idan suka fito da me zasuyi wanka. Kinsan Gidado baya son ruwan sanyi...." Zulaiha tace "Zinaru kiyi hakuri itacen ne mai danshi" Tun a bakin kofar Asmau ta soma hawaye. Rayuwarta ta gyara ga Zulaiha cikin matsanancin kunci har yau. Duk ta kara figewa sai dan wuya kamar kazar mayu. Cikin sauri ta karasa shigowa tace "Zulaiha" Tashi Zulaiha tayi da sauri itama ta nufo Asmau cike da murna da mamaki. Rungumar juna sukayi suna kukan yaushe gamo. Zinaru babu bakin magana saboda yadda gidan ya cika da mutanen da Asmau tazo dasu. Borin kunya ta soma da taga su Shemau na binta da mugun kallo. "Haka ake tarbar baki kin tsareta a hanya kuna kuka. Ke Humaira maza shimfida tabarmar nan a rumfar babanku. Kai kuma Ali jeka ka taso babanku. Yau Asmaun da yake ta jira ta dawo" Wata mace ce wadda da kadan zata girmi Humaira ta fito tana yatsina fuska. "Hayaniyar me nake ji haka? Zinaru wannan banzar ta dafa min ruwan wankan ko kuwa?". Zinaru ta galla mata harara zata bata musu harka. A yadda taga mutanen da shigar Asmau tasan akwai maiko. Har ta fara nadamar barin Gidado da tayi ya auro 'yar mutumin da ya bashi shago a kasuwa. Zulaiha sai murna take ta shimfida musu tabarma da zannuwanta wankakku biyu don babu abinda zata basu su zauna. Basu zauna ba sai tausayinta da suka rinka ji. Zulaiha tana cikin mawuyacin hali. Yaranta kaf babu mai zuwa makaranta yanzu. Duk abinda ya rage mata dashi Gidado yayi aure. Watarana ya sha giya ya bugu yayi mata duka cikin jikinta ya bare. A yanzu haka babu irin wukakancin da basa gani ita da 'ya'yanta a wurin Zinaru da amaryar Gidado. Yi sukayi kamar basa ganin su Zinaru suka shiga hirarsu da Asmau da yan uwanta. Col. Ishaq ba karamin haushinsa yaji ba bare da ya fito yana tangadi alamun mayen jiya bai sake shi ba. Ya dubi Zulaiha da take gaishe da su Umma. Wahala ta mayar da ita wata iri. Idan za'a bashi dama daga Gidadon har uwarsa sai ya kullesu. Zulaiha tace "Ummi kinji dadi iyayenki sun yafe miki. Ji yadda kika koma nayi miki murna" Hajiya ce ta ce "kema in sha Allah bazamu tafi ba sai mun hadaki da naki iyayen. Asmau ta fada mana komai game da rayuwarki" Zibaru ta cafe "to tace muku tana bukatar taimako ne? Yarinya tana zaman auren soyayya da mijinta zaku shiga tsakani" Qasim ya taso mata "idan baki kiyaye bakinki ba wallahi idan nasa aka rufeki babu wanda ya isa ya fito dake" "Kaiiiiii, babar tawa kake yiwa tsawa" Gidado ya fada. Darajar 'ya'yansa tasa duk mazan nan su Jafar, Yassar, Abdulhalim ga soja da dan sanda basu rufeshi da duka ba. Zulaiha tana kuka tace "nasam bazasu yafe min ba. Shekarun da yawa. Kara na kaisu na zabi wannan rayuwar akan su" Asmau tayi ta bata baki ta amince da shawararsu ta zuwa gida. Zinaru tace "idan kika fita a bakin aurenki" Yau da Zulaiha ta sami masu tsaya mata bata ji maganar Zinaru ba tayi gaba 'ya'yanta na binta. Tana ji Zinaru tace Gidado ya sake ta. Dama me ya rage mata a auren nasa. Suna kallo duk suka fita. Zinaru tasan sun gama yawo domin kuwa korarsu zaayi daga gidan. Zulaiha ke kwatance har suka iso bakin gate din wani makeken gida. Gida ne babba na gani a fada. Asmau tace cikin tsantsar mamaki "nan ne gidaku?" "Nan ne Asmau" su Humaira ma duk mamaki suke wai daga nan mahaifiyarsu ta fito amma suke ganin kuncin rayuwa. Daga bakin gate kenan ma. Maigadi yayi musu iso akan cewa bakin mamanta ne. Jikinta a sanyaye suka shiga. Gidan ya kara fadi gashi ya dace da zamani. A wurin ajiye motoci ta hango kaninta da Alhajinsu. Zuciyarta tana dar dar Alhaji na hangota ya taho wurin da suke yana kallon Zulaiha. Shekarunta sha bakwai rabonta da gida. Ana jiran aji da wacce zai tarbi yarsa. A hankali yace "sai yau uwata? Sai yau kika iya tunawa kina da iyaye?" Abin tausayi Zulaiha ta fada jikin mahaifinta. Saboda yadda ta kode sai ka zata wa da kanwa ne ba uba da 'ya ba. Farinciki yake ji mara misaltuwa. Allah Ya karbi adduarsa 'yarsa ta dawo. Ba karamin fushi yayi da ita ba a da amma daga

Chapter 21 of 23